takawa yaje har kan kujerar da take
zaune mai daukar mutum uku ya zauna a gefe
yana dora murmushin da bayaji a zuciyar shi
kan fuskar shi
Lubna sufyan
Hausabook.com 361
"Na dawo ne gabaki daya Nanna, ba nida nufin
zama a garin Kano saboda dalilai da yawa, zaki
cigaba da gaba da gani na lokaci zuwa lokaci
saboda banda yan uwan da suka wuce su
Hamma, ban san me nayi miki ba, koma menene
ba zai taba zama dalilin da zanyi nisa da yan
uwa na ba, yaran kine duka, kiyi hakuri zaki
cigaba da raba su tare dani..."
Ya karasa maganar yana mikewa ya nufi hanyar
kitchen din, yanajin yanda take bin shi da kallo,
nauyin da yake ji a kirjin shi duk idan yagan ta
yaji ya daga mishi, tsanar da tayi mishi zabinta
ne, ya gaji da raba nauyin tare da ita. Taje ta
dauka ita kadai, ko babu wani abu ta bashi su
Khalid, shisa take kasancewa cikin addu'o'in shi.
Tana da wannan darajar a idanuwan shi, fridge
ya bude yana daukar ruwa roba daya
"Zuba abinci ne kamar zaka dafa sabo"
Ya ce ma Khalid da yake rike da filet a hannu
"Ina ruwan ka?"
Khalid din yace, Nawfal ya amsa da
"Babu"
Lubna sufyan
Hausabook.com 362
Yana ficewa daga kitchen din, murmushi Khalid
yayi, ranar farko da yaji dadin karfin halin da
Nawfal yayi. Sai dai yana juya maganar Nawfal
din da yace bashi da nufin zama a garin Kano,
ina yake nufin zai zauna? Shi bai fada mishi ba,
watakila sai sun samu zama tukunna. Koma ina
ne in dai yana kasar komai zaiyi dai-dai. Tuwon
shinkafa ne, zubawa yayi yana dibar malmala
biyu dan shi bai cika rike mishi ciki ba, yana iya
kai sha biyu a zaune yaji yunwa.
Dakyar yake iya daga idanuwan shi, ya san Allah
ne kawai ya tsare mishi hanya daga asibiti zuwa
gida
"Idan ka gaji haka ka dinga kwanciya a asibiti ko
baccin awa biyu ne kayi tukunna ka hau titi, ko
ka kira Hamma Khalid ya zo ya dauke ka"
Rokon da Madina tayi mishi kenan kwanaki
tana dorawa da
"Kaji Hamma, dan Allah, kaji"
Bai amsa ta ba, saboda inya amsa zai zama
kamar yayi mata alkawari ne. Bacci a asibiti ba
Lubna sufyan
Hausabook.com 363
zai iya shi ba kamar yanda yaga sauran abokan
aikin shi sunayi, saboda akwai hayaniya, duk da
ofishin shi ne can karshe, amman karar takun
tafiya na zirga-zirgar mutane kamar cikin
kunnen shi akeyi haka yake jin su, yana iya jiyo
karar wayar wani daga ofishin shi. Duk kananun
hayaniyar nan ba zai iya bacci a cikin ta ba. Tun
kafin ya tura kofar ya jiyo sautin hayaniyar da
yake da tabbacin tv ce a kunne.
Da tsaki a bakin shi ya tura kofar, sai da ya dan
runtsa idanuwan shi saboda karar da yaji ta sa
kan shi sarawa. Nawfal na zaune kan doguwar
kujera ya jingina bayan shi sosai, yanda
idanuwan shi suke a rufe ya tabbatar ma da
Salim din bacci ne ya dauke shi, wani sautin
mamaki Salim ya fitar yana karasawa cikin
dakin sosai ya kai hannu ya dauki remote din da
yake gefen Nawfal ya rage karar tv din gabaki
daya sannan ya zauna gefe don ya zare takalmin
da ke kafar shi.
Yana jin wata iska da ta ratsa kafafuwan tun
kafin ya cire safar shi, numfashi ya sauke yana
jin wani na mishi wahalar shaka saboda Nawfal
da ya doro kan shi a kafadar shi batare daya yi
Lubna sufyan
Hausabook.com 364
tsammanin hakan ba, kafin yayi wani motsi
Nawfal din ya zagaya hannuwan shi duka biyun
a damtsen shi yana kara kwantawa a jikin shi
"Ina ta missing din ki"
Nawfal ya fadi cikin bacci, shima gajiyar ce a
tattare da shi. Bai taba hasaso cewa haka kafa
kasuwanci yake da matukar wahala ba sai
yanzun da tun wajen karbar lasisin shi na tuki
ya fara jin kan shi na nauyi, balle kuma daya
fara zirga-zirga tsakanin Kano da Kaduna tun da
nan din ya zaba a matsayin garin da zai zauna ya
kuma kafa kasuwancin na shi
"Me yasa sai Kaduna? Duk fadin Kano Bajjo?
Baka ganin wasu daga Kadunan suna dawowa
Kano don kafa kasuwancin su, ka zabi duk inda
yayi maka a Kano zan sai maka fili idan akwai,
in babu zan sai maka ko meye a wajen in dai
zasu siyar mun saika rushe ka gina abinda kake
bukata, ina da kudin, in banda su kai kana da
kudin... Kaduna tayi nisa"
Julde ya karasa maganar muryar shi dauke da
nauyin da yake ji a zuciyar shi
Lubna sufyan
Hausabook.com 365
"Kadunan dai nake so Daddy, ai babu wani nisa
fa, zan zo in ganku duk sanda nake so. Don Allah
karkace a'a, kamun addu'a kawai"
Yana kallon yanda Julden yake kokawa da
zuciyar shi kafin ya jinjina kai a hankali
"Allah ya zaba abinda yafi alkhairi, amman ka
kara tunani dai"
Shima ya amsa ne da to ba dan akwai wani
tunani da zai kara ba. Ya dauke shi tsayin
shekara daya kafin ya yanke hukunci zama a
Kadunan. Tun kafin ya dawo kuma yake
binciken hanyoyin da komai zai zo mishi da
sauki. Sai dai ko da kudi ba zasu zamar mishi
matsala ba, hanyar tana da tsayin da bai hango
ba. Yau din ma yana dawowa ruwa ya watsa ya
fito da nufin shiga kitchen ya hada shayi, sai ya
zauna ya fara hutawa tukunna, bai san lokacin
da bacci ya dauke shi ba. Kamar jiya ya zo, gashi
harya shafe watanni biyu da dawowa amman
bambanci lokaci ya kasa barin shi.
Da daddare idanuwan shi kamar an soya gyada
a ciki, amman da rana kamar an bubbuge mishi
gwiwoyin kafa haka yake ji saboda baccin da
Lubna sufyan
Hausabook.com 366
zaita dawainiya da shi. Sunyi waya da Murjanatu
yana hanya, da tunanin yanda yake kewar ta ya
shigo gidan, har bacci ya dauke shi ma yana
tunanin yanda zata matsa mishi kafafuwan shi
da suke a gajiye da tana kusa. Shisa
kwakwalwar shi tayi mishi tunanin itace yaji ta
zauna a gefen shi kamar yanda ta saba. Suna da
bambanci lokuttan dawowa gida, tana rigan shi
fita, yana kuma riganta dawowa.
Ranaku da yawa sai tsakiyar dare take komawa,
saboda yanayin karatun su ma ba daya bane ba,
kuma in ta tashi daga makaranta zata wuce
aikin da takeyi na awa uku wani lokacin awa
hudu, ya danganta da yanda take jin gajiya
"Bajjo..."
Salim ya kira a tsakanin jan numfashi da
saukewa saboda ya kawo iya wuya. Amman
kamar ya tunzura Nawfal din daya kara riko shi
"Jikina ciwo yake"
Cewar Nawfal din, hannun shi Salim yake
kokarin fisgewa amman rikon da Nawfal yayi
mishi bana wasa bane ba, shisa yayi amfani da
Lubna sufyan
Hausabook.com 367
gwiwar hannun da yake rike da shi din ya
zungure shi a hakarkari, babu shiri ya bude
idanuwan shi yana kokarin gane inda yake da
kuma abinda yake faruwa, a hankali ya juyo ya
kalli Salim da yake watsa mishi wata irin harara
da yasan yana gab da kwada mishi mari idan bai
daina koma meye Salim din yake tunanin yanayi
ba, hannuwan shi da suke sakale da na Salim ya
kalla yana tunanin abinda sukeyi a wajen.
Bai san ihun da yayi cikin kan shi ya subuce
mishi ba sai da yaji sautin shi a kunnen shi,
hannuwan shi na nuna mishi bai isa da su ba
saboda sun ki sakin Salim din
"Ba zaka sakeni ba dan uban ka? Sai na karya ka
tukunna ko?"
Sai lokacin ya saki Salim din yana mikewa cikin
hanzari
"Me kake anan?"
Nawfal ya tambaya cikin tashin hankali, wani
irin kallo Salim din ya watsa mishi
"Me yasa baka tasheni ba?"
Lubna sufyan
Hausabook.com 368
Ya dora yana yarfe hannuwan shi hadi da goge
su jikin rigar shi, kai Salim ya jinjina, an kwana
biyu wani bai raina mishi hankali haka ba, ganin
yanda ya mike yasa Nawfal din rugawa da gudu
"Ka dawo kaji me yasa tashe ka ba"
Cewar Salim din yana kallon Nawfal da har ya
kai bakin kofar dakin su. Kwafa yayi yana
komawa kan kujerar ya zauna
"Karka dawo falon nan"
Salim ya fadi yana kwanciya akan doguwar
kujerar, yasan in yayi wanka da ruwa mai dumi
sosai sai yafi jin dadin baccin, amman kan shi
yayi mishi nauyi ba kadan ba.
"Hamma dan Allah... Shayi zan hada sai in koma
daki"
Nawfal yayi maganar daga in da yake tsaye
"I will kill you if you make another sound"
Dariya Nawfal yayi yana nufar kitchen, kafin ya
gama hada shayin Salim ya kira
"Bajjo!"
Lubna sufyan
Hausabook.com 369
Cike da kashedi ya kuma watsa mishi zagi yafi
sau biyar. Da gangan ya buga kofar dakin su
wajen rufeta yana jin zagin da Salim din yayi
mishi, dariya yayi ya saka mukulli a jikin kofar
dakin. Yasan har yanzun baiyi girman da Salim
din zai ki cin zalin shi in ya so ba, ko kafin ya tafi
Kaduna da ya zo ya same shi kwance a falo yana
kallo sai da ya kai masa wani duka da ya wuni
yana murza wajen
"Bana hana ku zama a falon nan ba"
Da bai saurin tashi ba wani dukan Salim zai sake
kai mishi. A ka'ida falo nasu ne su duka, amman
tuni Salim ya hada ya mallake da nashi dakin.
Ko wucewa zakayi in yana kwance saika dauke
numfashi kar kayi ya karasa kunnen shi. Da
suna zama suyi kallo in yana dakin shi, ya zo ya
hana saboda basa rage karar tv din a cewar shi,
yana jin surutan har cikin kwakwalwar shi kar
wanda ya sake zama. Shayin shi Nawfal ya
shanye ya kwanta ya dan runtsa ko na awa daya
ne tunda yaga har biyar ta wuce, yasan dai zai
tashi jikin shi yayi mishi nauyi.
**
Lubna sufyan
Hausabook.com 370
"Kin siyi jamb?"
Fatima Atiku ta tambayeta lokacin suna rubutu
Neco, kai kawai ta girgiza mata. Ita bata ga
saurin da dalibai da yawa masu zana jarabawa
sukeyi ba, tun kafin ma ta shiga aji shiddan tana
ganin sauran dalibai na wannan zumudin. In
tace bata hango rayuwar jami'a da yanda zata
kasance mata zai zamana karya, amman banda
haka bata wani zumudin shiga ko doki, a ganin
ta makaranta dai duk makaranta ce, karatu
kuma karatu ne, babu wani abu da zai canza
mata, yanda bata da wasu da zata kira abokai
haka ma acan din bata jin zata samu wanda zata
kira da wannan sunan.
Ta fi so sakamakon jarabawar ta su ya fito
tukunna, ta ga taci duk wani abu daya kamata
kafin tayi wata jamb, har Salim sai da yayi mata
maganar
"Ni nafi so jarabawa ta fito ne Hamma"
Kallon ta yayi
Lubna sufyan
Hausabook.com 371
"Zaman me zakiyi a gida Madina? Da kinyi jamb
din, result na fitowa a shekarar nan ma zaki iya
samun admission"
Shi yayi mata bayanin muhimmanci yin jamb
din shekarar da ka zana jarabawa, amman yayi
mata bayani a kurarren lokaci tunda har an
gama saidawa, ko da ba'a gama saidawa ba sai
dai tayi saboda shi bawai don ko daya a cikin
bayanin ya gamsar da ita ba. Ta fi son bin komai
a hankali, kuma daki-daki. Yanzun kuwa dadin
hutun ma take ji, daga islamiyya sai in tana da
wanda zatayi wa kunshi da kusan kullum ne, da
dare tana da isasshen lokacin da zatayi karatu
tunda tasan zata koma bacci da safe in ta gama
aikin ta.
Bambanci da yake cikin kowacce rana a wajen ta
shine yawan mutanen da ta yiwa kun shi sai
kuma sabon abinda zata karanta. Banda wannan
kullum iri daya ce, abu iri dayane. Sai kuma
Daada da take ganin kamar tana ramewa, kamar
kuma akwai rashin kuzari a yanda take gudanar
da al'amuranta ba kamar da ba, kusan kullum
sai ta kai hannu ta taba fuska ko wuyan Daada
dan taji idan akwai zazzabi sai taji lafiya kalau.
Lubna sufyan
Hausabook.com 372
Yau ma kuwa hakanne ya faru har ta sa Daada
yin murmushi
"Na ce miki lafiya ta kalau Madina"
Numfashi Madina ta sauke
"Kina ta ramewa Daada...ko dai in kira Daddy
muje asibiti a kara duba ki"
Dariya Daada tayi
"Allah da gaske, ni gani nake kina ta ramewa"
Kafin Daada ta amsa sallamar Nawfal ta katse ta
"Hamma dan Allah ba Daada ta rame ba?"
Madina ta tambaya bayan ta amsa mishi
gaisuwar shi, kallon Daada yayi sosai, yana kula
da yanda shekaru suka nuna a fuskarta, bai gani
ba da, amman akwai rama a fuskarta, duk da ita
din ba mai jiki bace ba tunda can ma, amman
fuskarta a cike take, yanzun kam har hancin ta
da yake dogo ya kara fitowa, kana ganin
kwanciyar karan hancin daya fara tun da
tsakiyar girar ta
"Baki da lafiya ne? Jikin ne?"
Lubna sufyan
Hausabook.com 373
Kai ta girgiza musu
"Ku me yake damun ku ne?"
Saboda bata son damuwar da take kan fuskokin
su
"Kuma bata yin komai da hanzari kamar da fa"
Madina ta fadi
"Yarinta nake karawa ne kullum? Jikin girma ne,
kuyi addu'ar samun jiki me kyau irin nawa"
Dariya sukayi gabaki daya, duk da a kasan ta
Nawfal akwai damuwa, waje ya samu gefen
Madina ya zauna har lokacin sai kallon Daada
yakeyi, musamman yanda sai da ta dafa kujera
sannan ta iya mikewa dakyar kamar tana jin
nauyin jikinta
"Bacci ma nake ji ni kam"
Shagwabe fuska Nawfal yayi
"Ko gaisawa ba muyi ba Daada shine zaki tashi?
Ba zaki zauna muyi labari ba?"
Murmushi tayi
Lubna sufyan
Hausabook.com 374
"Ai nasan kana nan har in tashin... Wacce
gaisuwar? Ba gani ba ka ganni ina lafiya, kaima
kuma nagan ka kana lafiya"
Kai kawai Nawfal ya jinjina yana sauke
numfashi, har ta shiga daki bai daina kallon in
da ta bari ba, haka kawai sai yake jin zuciyar shi
tayi nauyi. Sai dai bai ce wani abu ba har akayi
sallamar da ta sa Madina mikewa tana fita
tsakar gidan dan ta ga ko waye ya shigo, sanda
ta dawo yaja kafafuwan shi ya dora su kan
kujerar
"Kunshi zanyi Hamma, in zuba maka abinci?"
Kai ya girgiza mata, bayajin yunwa, wayar shi ya
ciro yana kwanciya kan kujerar sosai ya shiga
whatsapp yana sake kallon hotunan da
Murjanatu ta turo mishi yana murmushi shi
kadai, har Madina ta shiga daki ta dauko kayan
kunshin ta, ta sake ficewa bai ma kula ba. Bai
san lokaci na wucewa ba musamman da
Murjanatu kamar ta duba zuciyar shi ta ga
yanda yake kewar ta ta zo online. Earpiece din
shi da bai cika mantawa ba ya ciro a aljihu ya
saka saboda ta kira shi video call.
Lubna sufyan
Hausabook.com 375
Sallar la'asar da aka kira ne ya sa shi yi ma
Murjanatu sallama yana mikewa yaje ya dauro
alwala, batare da ya kalli matar ko yarinyar da
ta gaishe shi ba ya amsa yana wucewa, dan
lokacin ma kokarin maida links din hannun
rigar shi daya bude wajen alwala yake yi. Ita ma
sallar ta mike taje tayi, don sallah na daya daga
cikin abinda bata wasa da shi. Sanda ta karasa
ma matar hudu kusan da rabi. Kudin da ta bata
cikin wata jaka taje ta zuba, abinda take siye
bashi da yawa, Julde na bata kudin kashewa
sosai, Salim ya sa taje ta bude account a banki,
shi ya dauketa sukaje tare. Yanzun ma idan
kudin kushin sun kai dubu biyar ko fiye da haka
sai ta fada mishi yazo ya kaita taje ta saka a ciki.
"In sun taru da yawa zakiyi wani abu mai
muhimmanci da su"
Salim din ya fadi, sai da ta fara tarawa tukunna
zuciyarta ta raya mata tarin abubuwan da take
son tayi da kudin in har sun kai mata yawan da
take fata.
"Kunshi kamar kina ma mutum goma, tun
dazun"
Lubna sufyan
Hausabook.com 376
Nawfal ya fadi bayan ta shiga falon ta samu waje
ta zauna
"Kasan wahalar kunshi ne Hamma?"
Kallon ta Nawfal yayi
"Bawani wahala, ai na iya"
Dariya Madina tayi, sosai dariya ya bata
"Ka iya me? Bafa zanen kujeru ba Hamma,
kunshi...kunshi irin wanda mata sukeyi"
Kai Nawfal yake jinjina mata tunda ta fara
magana fuskar shi babu alamar wasa
"Ni nake yiwa Jaan, kuma kowa ya gani sai yace
yayi kyau"
Duk da taji wani iri a zuciyarta bai hanata cigaba
da dariya ba
"Baki yarda ba kenan? System dina dayan daya
baci ne nake da hotunan da kin gani"
Dariyar dai Madina ta cigaba da yi mishi
"Ki dauko kayan kunshin ki kawo hannun ki
kisha mamaki"
Lubna sufyan
Hausabook.com 377
Mikewa tayi ta nufi dakin ta tana dauko jakar
kayan kunshin, akwai saura da yawa a
kwarkwaron da tayi ma matar na bakin lalle ta
kuwa mikawa Nawfal da ya sauko daga kan
kujera shima yana zama kan kafet suka fuskanci
juna da Madina da ke kokarin gintse dariyar ta
tana son ganin iya ina Nawfal zai kai da maganar
ya iya zanen lalle kafin ya fito ya fada mata wasa
yake. Fuskar shi babu alamar wasa ya ware
mata tafin hannun shi na hagu yana daga mata
girar shi duka biyun. Wani irin tsalle zuciyar
tayi kamar tana son bayyana kan fuskarta,
hakan ya sata saurin sadda kanta kasa tana jan
siririn numfashi, hannun nata da taji yana zufa
ta goge jikin wandon ta sannan ta dora shi kan
na Nawfal.
Salim ya sha rike hannunta, a rana sai ta rike
hannun Daada babu adadi, tafin ta ne kawai kan
na Nawfal, amman ji takeyi kamar ta dora shi
kan murfin tukunyar da aka sauke daga wuta,
dumin na gangarawa har cikin wani lungu a
zuciyarta da sai yau ta san da zaman shi. Fuskar
shi ta ke kallo da yanda ya nutsu akan hannun ta
kamar a duniya kaf bashida wani abu mai
Lubna sufyan
Hausabook.com 378
muhimmanci da yafi zanen da yake mata,
wannan karin duka jikinta taji ya dauki dumi sai
kace zazzabi na shirin kamata.
Yawu ta hadiye tana dan daga wuya da nufin
hango abinda Nawfal din yake zana mata ya
kuwa sake yin sama da hannunta yana fadin
"Kibari in gama Malama"
Dariya tayi
"Karka bata mun hannu Hamma, ka tsaya inga
me kake"
Kafada Nawfal ya makale mata yana saka
idanuwan shi cikin nata
"Allah ki tsaya in gama"
Kai ta jinjina mishi haka kawai tana jin ba zata
iya musu da shi ba. Duka bai kara minti goma ba
yayo kasa da hannunta dai-dai lokacin da zata
hadiye yawu, ta kuwa sarke wajen kokarin yin
dariya, duk da haka ta kasa dainawa, taurari ne
Nawfal ya zana mata, daya kwandalele a
tsakiyar bayan hannunta, sai yayi yan kanana
Lubna sufyan
Hausabook.com 379
daga gefe, haka jikin kowanne yatsa yayi karami
guda daya
"Inalillahi..."
Ta fadi tana cigaba da dariya, turo baki Nawfal
yayi dan baiga abin dariya ba
"Kowa a makaranta yana tambaya wanda yayi
mun kunshin nan"
Murjanatu tace mishi, tunda da a yatsunta kawai
take saka ja idan ta siyo, shi yace ta kawo ya
zana mata, batayi musu ba kuma ta bashi, da
kanshi yake kirkirar zane kala-kala, mai
taurarin shine yake ganin yafi kowanne kyau, ko
kafin ya taho duka hannuwan Murjanatu biyu
saida yayi mata, da yan yatsun kafa ma
"Gidado ka kware da kunshin nan yanzun, kaga
yanda na kafar yayi kyau"
Har sumba ya samu ta godiya. Sai Madina ce zata
saka shi gaba da dariya
"Hamma... Hamma.. Meye wannan?"
Lubna sufyan
Hausabook.com 380
Tayi tambayar a tsakanin dariyar da takeyi,
kwarkwaron ta ya ajiye mata yana komawa kan
kujera ya kwanta
"Ai sai kiyi tayi tunda baki san abin arziqi ba"
Mikewa Madina tayi da sauri tana nufar dakin ta
ta shiga bandakin da yake ciki ta bude famfo ta
saka hannun, sai dai ya riga ya fito, zai kuma yi
aqalla kwana uku ko hudu bai gama fita gabaki
daya ba ko da tana yawan amfani da ruwa.
Dariya kawai takeyi, tana fitowa daga bandakin
taji wayarta da ta bari cikin dakin tana ruri, da
sauri ta karasa ta dauki wayar, muryar ta dauke
da dariya ta ce
"Hamma..."
Bayan ta kai wayar kunnen ta
"Ina kika je? Ina ta kiran ki. Ke da wa kike
dariya?"
Dariyar ce ta sake kubce mata
"Ina nan fa, nabar wayar a dakine, na ma wata
kunshi sai nima akayi mun..."
Lubna sufyan
Hausabook.com 381
Sai dai kafin ta gama dariyar da ta sake kubce
mata ta bashi labari harya katse ta
"Kunshi? Kikayi? Wayayi miki?"
Salim ya jera mata tambayoyin a numfashi daya
"Hamma Nawfal fa.. Wai ya iya, yana ma matar
shi, kaga abinda ya zana mun a hannu?"
Ta karasa tana dariya, shirun da taji ya biyo
bayan maganar ya sata fadin
"Hello..."
Har sau biyu tana sauke wayar daga kunnen ta
dan tunaninta kiran ya katse sai taga sakanni
suna tafiya, sake mayarwa tayi
"Hamma... Bana jin ka fa. Ka kashe ka sake kira"
Numfashi taji ya sauke cikin kunnenta, muryar
shi can kasan makoshi yace
"Ina zuwa"
Kafin ma ta amsa taji alamar ya katse kiran daga
bangaren shi, cajarta ta karasa ta ciro tana
daukar wayar ta nufi falo, har lokacin da
murmushi a fuskarta.
Lubna sufyan
Hausabook.com 382
**
Baiyi tunanin kafafuwan shi zasu dauke shi daga
dakin su zuwa na Salim ba saboda rawar da
sukeyi, tashin hankalin da yake ciki bai barshi
ya tuna cewa ana neman izini kafin a
kwankwasa daki ba, turawa kawai yayi yana
samun Salim a tsaye da alama wanka ya fito ya
sake kaya
"Bajjo..."
Salim ya kira ganin tashin hankalin da yake
shimfide a fuskar Nawfal din
"Hamma..."
Nawfal ya kira yanajin zuciyar shi akan harshe
"Meye? Menene?"
Numfashi Nawfal ya sauke
"Hamma Khalid..."
Kokawa yake da sauran kalaman
"Hatsari sukayi...ya kirani....banaji sosai...
Hamma ina ta kira ba'a dagawa...ba'a daga
wayar"
Lubna sufyan
Hausabook.com 383
Mukullin motar da yake kan gado Salim ya
dauka, Nawfal baya bukatar Salim yace mishi ya
wuce, gaba yayi yana bin shi a baya har suka fita
daga gidan. A wajen ajiye motoci suka ci karo da
Julde da zai fita, tashin hankali bai hana su duka
biyun jin kamshin da yakeyi ba. Ganin Salim
bashi da ko takalmi yasa shi tambayar
"Lafiya? Ina zaku? Me ya faru?"
Salim ne ya iya amsa shi da
"Khalid ne yayi hatsari"
Wani irin rugugi Julde yaji cikin kirjin shi har
hanjin cikin shi na taya zuciyar shi amsawa. Su
duka ukun motar Salim suka shiga, dan Julde
baya ya bude yana zama. Sai da suka hau titi
sannan Salim yayi tunanin bai ma san inda zasu
nufa ba
"Yana ina? Ina akace maka yake?"
Kafada Nawfal ya dan daga
"Nima ban sani ba, mu bi hanyar wajen aikin shi
kawai"
Kallon shi Salim yayi
Lubna sufyan
Hausabook.com 384
"Baka da hankali ne? Kasan hanyoyi nawa ne
zaka iya bi zuwa Asad?"
Kamar Nawfal zaiyi kuka yace
"Dan Allah ka zabi daya kawai kabi Hamma, kayi
sauri"
Dayar kuwa ya zaba yana karanta duk wata
addu'a da zata zai iya tunawa, tashin hankali
bakon abu ne a wajen shi. Ya sha ganin mutane a
asibiti suna faduwa suna tashi akan tashin
hankali idan sun kawo yan uwan su, ko kuma ya
fada musu rasuwar wani makusancin su, sai dai
ya kalle su kawai saboda ko da wasa ma baya
son ya hasaso me suke ji, don hakan na nufin ya
saka kan shi a takalmin su, ya kwatanta da wani
na shi, ba zai iya ba, baya so ya ma iya. Sai gashi
yau yana zaune tashin hankalin ya same shi har
cikin gida. Daman zuciyar shi a jagule take tun
wayar da yayi da Madina. Kai ya girgiza dan ba
wannan bane abu mai muhimmanci yanzun.
Suna hawa titin Kawaji kuwa suna ganin
cunkoson da aka hada a wajen, gurin ya cika, ko
gefen hanya Salim bai samu ya sauke motar ba, a
tsakiyar titi ya tsaya suna fita daga ciki gabaki
Lubna sufyan
Hausabook.com 385
dayan su. Sai da yaji shigar kwalta a tafin
kafafuwan shi tukunna yagane cewar bai saka
takalmi ba. Runtsa idanuwan shi kawai yayi
yana fitar da numfashi, ta tsakanin mutane suke
kutsawa. Nawfal najin kafafuwan shi na kara yin
sanyi da duk takun da zatayi
"Trailer ce akace ta kwace duk ta bi takan
motocin nan"
Ya tsinto muryar wani yana fada a cikin
mutanen yana sa makoshin shi bushewa kamar
an zuba yashi. Julde ya fara hango Khalid a
tsugunne ya hade kan shi da gwiwar shi, har
tuntube yakeyi wajen kokarin ya karasa wajen
shi, Nawfal kam jinin da yake gani ya kara daga
mishi hankali
"Khalid..."
Julde da Salim suka kira lokaci daya suna sa
Nawfal kallon inda suke, dagowa Khalid din
yayi, har idanuwan shi sun zurma ciki saboda
tashin hankali. Shi da yamma ma ya kamata
yabar wajen aikin, sai abokin aikin shi ya kira
cewar yar shi bata da lafiya suna asibiti, shine ya
karbe shi har daren, cunkoso ya samu akan
Lubna sufyan
Hausabook.com 386
hanya, tsaye motar shi take kamar ta sauran
mutane da dama, da kuma babura, ba zaice ga
abinda ya faru ba, ihu da kara kawai yaji sai
motar shi da yaga tana gaba da kanta, ashe
trailer din data kwace sai ta danne motocin da
suke can bayan su, da tafiya ake kilan sai
hatsarin yafi haka muni.
Sanda wani ya bude motar shi ya fisgo shi ya
juya bayan shi ya dora idanuwan shi kan wani
mutum da kafar shi ta fita kasa motsawa yayi,
tsaye yayi yana kallon yanda ake zaro mutane
musamman masu mashina daga karkashin
motoci, tunda yake bai taba ganin tashin hankali
irin wannan ba. Nan take zazzabi mai zafi ya
rufe shi, tunanin ya kira Nawfal ne ya zo mishi,
sai da ya ma rasa abinda zaice mishi, bai san ya
kiran ya kare ba ko ya akayi ya samu waje ya
tsugunna, kawai yasan ko kifta idanuwan shi
yayi sai ya dinga ganin mutane da jini na gifta
mishi
"Khalid..."
Salim ya sake kira yana kama hannun shi ya
mikar da shi tsaye
Lubna sufyan
Hausabook.com 387
"Kaji ciwo? Ina kaji ciwo?"
Yake tambaya yana bin jikin Khalid din da kallo
"Daddy..."
Khalid ya kira da dukkan zuciyar shi yana jin
yanda babu wani girma da zaiyi a duniya da
za'ace baya bukatar lallashin iyayen shi.
Karasawa Julde yayi da sauri
"Kaganni nan Khalid, baka ji ciwo ba dai ko?"
Kai Khalid din ya daga mishi yana jin wasu
hawaye masu zafi da suka cika mishi ido, da
shikenan fa, karshen ganin da zai musu yau da
safe kenan, dan Adam da gaske ba abakin komai
yake ba, kana tafiya ajali yana bibiyar ka, ko
tsautsayi, duka tarin mutanen da tsautsayin ya
fadama sun bar gidane batare da sanin ba zasu
koma ba, iyalai da yan uwa suna can suna dubar
hanyar komawar su, wasu sai dai suji ana
sallamar su matsa za'a shiga da gawa, ko suzo
asibiti kaza su dauka. Ko ina jikin shi bari
yakeyi, wani irin tsoro na shigar shi.
Bashi da rabon wahala, amman bayan motar shi
gabaki daya ya molaqe, ba dabarar shi ba, ba
Lubna sufyan
Hausabook.com 388
komai ba, ko addu'ar fita daga gida bai tuna yayi
ba yau din. Allah ne kawai ya kubutar da shi
"Baka ji ciwo ba?"
Julde ya sake tambaya, kai Khalid ya daga mishi,
kamar haka Nawfal yake jira ya tsugunna
saboda kafafuwan shi da yaji shima sunyi sanyi.
Fuskar shi ya saka cikin hannuwan shi yana jero
duk wata kalar godiya da zai iya wa Ubangiji da
ya tseratar da Khalid din
"Meye kai kuma? Ka tashi Bajjo, baka gan shi
ba? Lafiyar shi kalau babu abinda ya same shi"
Kai kawai Nawfal yake dagawa Salim din amman
shi kadai yasan yanda zuciyar shi ta girgiza,
baka isa ka hana kaddara
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 14 Chapter of 18