yana mai kallon "Nasan
abinda kake shirin aikatawa". Tun daga lokacin
da suka fita daga cikin makarantar da Victoria
ta saka hannunta cikin nashi tana dumtsewa
yake jin kuskuren da yake a cikin duk wani taku
da zasuyi. Shiya bata kudin da ta kama musu
hotel na kwana daya, sai dai suna shiga cikin
dakin ta mayar ta rufe yaji ta rufe da wani abu
daya bari a wajen dakin.
Bayan sun fito da safe, kowa yayi wajen shi
daban yaji canjin da yayiwa gabaki dayan
rayuwar shi. Dararen da kuma ranakun da suka
biyo bayan wannan daren na biyu daya hadu
dana farko wajen yin jagorar canza gabaki daya
rayuwar Salim zuwa sukeyi suna wuce mishi da
wani irin yanayi da yake kara dishe wani haske
da baisan dashi a kirjin shi ba saida ya fara
Lubna sufyan
Hausabook.com 83
dakushewa. Dan ya fahimci Julde ya fara, sai ya
budema kan shi wata irin duniya da bai taba
sanin akwaita ba.
Ruwa ya kare a bangaren su, na famfon gidan
kuma burtsatse ne ba dadi gare shi ba, shisa ya
shigo bangaren su Julde da fadan su yasa shi
tattara komai nashi yabar musu. Da badan
karatun jarabawar da yake yi ba sam ba zai
shigo ba, zai hakura da ruwan. Duk maganganun
da suke fadama juna a cikin kunnuwan shi suke
direwa suna karasawa zuciyar shi da yanayin da
yake nisantata da son kusantar aure da duk
wani rikici da zai biyo bayan shi. Rayuwar
hayaniya ce sam ba zai iya ba, aure kuma cike
yake da hayaniya, nashi iyayen babban misali
ne.
Sai da ya sauke numfashi da yaji karar rufe kofa,
tsaya yayi sai da ya sake jin budewa da rufewar
kofa a karo na biyu tukunna ya fito daga kitchen
din da robar ruwan daya rike kamar ya sato. A
hankali yaja kofar gidan bayan ya fita, iska yake
shaka yana fitarwa kamar mai son raba huhun
shi da iskar daya shaka a cikin gidan. Yau ya
kara fahimtar Julde, akwai shirun da yake
Lubna sufyan
Hausabook.com 84
tattare da dayar rigar dayake sakawa a wajen
gidan aure, ba mai tsayi bane shirun, na
kankanin lokaci ne, amman shiru ne, shi da baya
tare da hayaniyar aure yakan bukaci wannan
shirun. Balle kuma Julde, shisa yanzun da yake
komawa bangaren su yake kara hango tazarar
da take tsakanin shi da kusantar duk wani abu
daya danganci aure.
Ya bude zip din jakar shi ya rufe ya kai sau goma
sha biyar ko fiye da hakan, da ba sabuwar jaka
bace ba shi kan shi yasan zip din da ya samu
matsala. Ba tunani yake ya manta wani abu ba,
amman jakar tayi mishi kadan, abubuwan da
yake son dauka sun girmi wajen da ya rage a
cikin jakar. Daya daga cikin misalin abubuwan
ya hada da Khalid da yake tsaye ya jingina bayan
shi da bangon dakin
"Har yanzun fushi kake mun Hamma? Jirgi zan
hau, komai zai iya faruwa..."
Kallon da Khalid ya watsa mishi yana saka
sauran maganar koma mishi, sai da ya hadiyi
yawu kafin ya sake cewa
Lubna sufyan
Hausabook.com 85
"Idan kasan zakayi kewa ta har haka me yasa da
Daddy yace mu tafi tare kaqi?"
Numfashi Khalid ya sauke, shi bai taba tunanin
barin gida da sunan karatu ba, asalima banda
jami'ar Bayero babu wani waje da yake
sha'awar zuwa da sunan karatu. Shima fannin
ilimin kimiyya da fasaha ya karanta, baiyi
tunani mai tsayi ba da ya tashi neman gurbin
karatu wajen cike bangaren magunguna wato
Pharmacy a matsayin zabin shi na farko. Duk
lokacin da zai ma Nawfal din zancen zabin
makaranta sai yayi kokari wajen canza maganar
kamar baya son amsawa.
Shisa ya kyale shi, a zaton shi Nawfal na daya
daga cikin mutanen da sukan kasa tsaida
hankalin su waje daya akan zaben makaranta ko
kuma fannin da zasu karanta. Akwai su a ajin su,
dan da yawa har suka siyi Jamb suna tararrabin
abinda zasu cike, wasu suna da zabi fiye da biyu,
wasu kuma basu da ra'ayin kansu ne sai abinda
iyaye suka cusa musu tun tasowa. Ya san Nawfal
baya daya daga ciki, banda shi baya tunanin
wani ya taba tambayar shi abinda yake son
zama ko inda yake son yin karatun shi.
Lubna sufyan
Hausabook.com 86
Nawfal ya sani, shine mutum na karshe da zaiki
goyon bayan shi akan duk wani zabi da zaiyi, in
har zabin ba wanda zai cutar da shi bane ba. Zai
karya idan yace jin zancen zabin Nawfal din
daga wajen Julde bai mishi ciwo ba
"Kasar waje Bajjo yake son tafiya, ko zaka duba
makarantar kaga idan akwai abinda kake son
karanta sai ku tafi tare, bana son ya tafi shi
kadai"
Shine abinda Julden ya fadi da Khalid bai ma
bari ya karasa ba ya fara girgiza mishi kai
"Daddy ni bana sha'awar zuwa ko ina, anan zan
zauna. Shi Bajjon da ya zabi tafiya Allah ya
taimaka, ba yaro bane ba, na tabbata zai iya kula
da kan shi"
Amsar da ya ba Julde kenan yana mikewa yabar
wajen zuwa bangaren su. A ranar ko da Nawfal
yabi bayan shi ya bude baki bai barshi ya furta
komai ba
"Kar mu fara maganar nan Nawfal, baka so in
sani ba, Daddy bai san baka so in san tsarin da
Lubna sufyan
Hausabook.com 87
kayi wa rayuwar ka ba shisa ya fadamun, karka
damu, in da akayi maganar nan na barta..."
Rubutun shi ya ci gaba da yi duk da a lokacin in
zaka saka mishi wuka baisan me yake rubutawa
ba, Nawfal ya dade a tsaye kafin ya fita daga
dakin. Duk wani shirye-shiryen tafiyar Nawfal
din da ake tayi baya saka baki a ciki. Kwanakin
dai ne bai kula suna ta gudu tare da su a ciki ba
sai yau da tun safe yake jin zazzabi ya rufe mishi
jiki ganin Nawfal na ta hada jaka. Zazzabi ne mai
hade da dana sani na satikan daya dauka yana
fushin da ya ga rashin amfanin shi a yanzun.
"Ban ki fada maka ina son barin kasar ba dan
bana son kasan plans dina Hamma, wallahi ba
dan bana so ka sani bane ba...na kasa ne saboda
zan dinga hango yau, bana son idan na kalle ka
in dinga jin ba kasar nan kawai zan bari ba har
da kai..."
Iska Nawfal ya furzar ta bakin shi da yake jin
kamar idan yaja numfashi maimakon ya wuce
inda ya kamata sai iskar ta dawo tana taruwa
cikin bakin na shi, ga zufa da yake ji har a bayan
kunnuwan shi da tafukan hannuwan shi
Lubna sufyan
Hausabook.com 88
"Kuma kana fada, ba zakayi ni sa da gida ba, ko
da sunan aiki ba zaka iya barin gida ba shisa
kake mamakin yanda bi da Adee muka iya tafiya
makarantar kwana, ban san ya zan fara fada
maka batare da na roke ka mu tafi tare ba,
Hamma ba zan so kaina da yawa ba, dan Allah
kayi hakuri..."
Gyaran murya Khalid yayi dan bai yarda da
kanshi yayi magana kai tsaye ba, yanda yaga
zuciyar Nawfal shimfide a cikin idanuwan shi, ya
kuma ganta a karye, idan ya nuna alamar rauni
bai da tabbas kan abinda zai faru
"Me yasa sai wata kasar? Wani garin bai isa ba?"
Dan daga kafadu Nawfal yayi
"Kullum jina nake kamar tsuntsu, ina da fukafukai, amman ina tsare cikin keji tun haihuwata,
nasan suna da wani amfani tunda an halliceni da
su, amman babu sarari a kejin da nake balle in
gwada miqe su har in san ya kamata in tashi..."
Sosai Nawfal yake kallon Khalid, kalaman shi
yake zabe iya yanda zai iya, yana so koda kowa
bai fahimce shi ba Khalid ya fahimta
Lubna sufyan
Hausabook.com 89
"Hamma ina numfashi kullum, amman bana jin
yana kai mun inda nake so, idan ina tare da
Daada nakan ji kokawar da nake da numfashi na
ya danyi sauki, idan muna tare da kai ko Adee
ma haka, ina bukatar in fita daga kejin da nake
ciki ko zanji, banda tabbas amman ina ji a jikina
barin kasar zai iya cike ramin da yake tare da
ni"
Wannan karin ta baki Khalid yake jan iska yana
fitarwa ta hancin shi a hankali, ga idanuwan shi
da yake kiftawa da sauri-sauri ko ruwan da yake
jin ya taru a cikin su zai koma, babban dan
yatsan shi ya kai yana goge gefen idan shi
"Kamar wani abu ya fada mun a ido"
Ya furta a hankali, muryar shi na fitowa a karye
"Ka dauki duk abinda kake bukata kuwa?"
Kai Nawfal ya iya jinjina mishi
"Sai karfe goma naji Daddy na cewa zamu tafi
kaika airport"
Lubna sufyan
Hausabook.com 90
Kan dai Nawfal ya sake jinjina wa cikin alamar
eh. Numfashi mai nauyin gaske Khalid yaja yana
fitarwa
"Bari in dawo"
Ya furta yana juyawa ya fice daga dakin hadi da
ja ma Nawfal din kofar. Dan dafe kai Nawfal yayi
kafin ya sauke hannun nashi yana mayarwa kan
tsintsiyar hannun shi dan ya murza agogon shi,
ya riga da ya saba in dai tunani yayi mishi yawa
idan yaja iska ya cika bakin shi, to zai fitar da ita
ne bayan ya dora hannun shi kan agogon ya dan
murza shi, shisa baya daure shi gam gam,
lokutta da yawa da shi yake alwala, har wanka
ma. Sai ya manta cewa yana hannun shi. Duk
agogunan shi haka zaka ga basa aiki, sai da Julde
ya bashi wani fari, da alama mai tsada ne
"Ruwa baya lalata shi, ga ka da agogo a hannu,
sai an tambaye ka lokaci kace ba yayi, yan gayun
zamani"
Dariya yayi yana mika ma Julde hannun shi
maimakon ya karbi agogon kamar yanda ya
miko mishi, da kan shi kuwa Julde ya zagaya
agogon yana daura ma Nawfal din. Tun lokacin
Lubna sufyan
Hausabook.com 91
zai kirga ranakun daya cire agogon daga hannun
shi sai jiya da yaje yi wa Daada sallama, dan
suna gaisawa yace
"Dan Allah Daada banda kuka, in kikayi kuka
zaki sa inji kamar na tafi kenan, bayan da anyi
hutu In shaa Allah zan dawo"
Yana kuwa ganin yanda take ta kokawa da
hawayen ta har ta raka shi bakin kofa, inda
kamar fitar su Madina take jira ta karyo kwana
jikin ta sanye da uniform din islamiyya. Hango
sun da tayi yasa ta taho da gudu
"Na hanaki wannan gudun Madina, amman ba
zaki daina ba"
Daada ta fadi cikin fada, muryarta dauke da
kulawa, dariya Madina tayi, dimples din da suke
a kuncinta duka biyun suna bayyana, da
murmushin ta kalli Nawfal da yayi dariya mai
dan siririn sauti, babu yanda za'ayi Madina tayi
murmushi a gabanka baka iya mayar mata ba,
ko da kuwa baka santa ba. Da take yar karama
tayi haske, amman yanzun a hankali asalin
kalarta take fitowa tana nuna alamar cewa ita
sam bata dauko hasken fatar da su duka suke
Lubna sufyan
Hausabook.com 92
dashi ba. Ita ce mutum ta biyu daya sani da take
murmushi da duka hakoranta a waje,
idanuwanta ba su cika girma ba, idan tayi
murmushi sai su kankance, kusan ma baka
ganin su gabaki daya.
Yanayin fuskarta idan tayi murmushi shine zai
sa fara'a ta kwace maka batare da kama sani ba,
sai dai ya dauka kankanta a zuri'ar su zata tsaya
ne akan Adee, sai ga Madina kuma yanzun da
take son ce musu da duk sun adana tsokanar da
suke wa Adee sun jira sun ga yanda nata girman
zai kasance in yaso sai su kamanta idan ita
kadai zasu tattara wa tsokanar ko kuma zasu
rabata ne tsakanin ta da Adee.
"Hamma..."
Ta kira kafin lokaci daya murmushin da yake
fuskar ta ya bace, baki ta turo
"Da tafiya zakayi ba zaka jira in dawo ba?"
Daada ta kalla
"Ko anan zai kwana?"
Kai Daada ta girgiza mata
Lubna sufyan
Hausabook.com 93
"Sallama yazo mana daman, gobe zai tafi
makaranta"
Kallon shi Madina tayi
"Baka ce ka gama ba?"
Dan murmushi yayi yana mata bayani cikin
yanayin da yake tunanin zata fahimta a
shekarun ta, yayi mamakin ganin yanda take
kallon shi idanuwanta cike da hawaye, wani abu
ya taso yayi mishi tsaye a kirji ganin hawayen ta
ido daya ya fara zubowa kafin dayan, yanda
zubowar su ta budema yan uwan su hanya,
muryar ta dauke da wani yanayi da ya kasa
barin kunnuwan shi tace
"Ba zaka dawo ba ko? Shisa baka fada mun ba?
Saboda ba zaka dawo ba?"
Kai yake girgiza mata ya juya wajen Daada dan
ta taimaka mishi, amman sai yaga tabar wajen
da sauri, hakan yasa shi karasawa yana riko
hannun Madina da ta fisge ya sake riko shi da
sauri, yana ganin yanda take kokarin sake
kwacewa
Lubna sufyan
Hausabook.com 94
"Waye yace ba zan dawo ba? Makaranta fa, ko
wadda na gama baki ga ina dawowa ba?"
Kafada ta makale
"Zaka bar kasar, jirgi fa zaka hau, ba dawowa
zakayi ba ni na sani"
Ta karasa tana fashewa da kuka me sauti,
baisan yanda zai fara lallashin ta ba, janta yayi
yana hadata da jikin shi
"Wallahi zan dawo Madina, kinji na rantse ai"
Shesshekar kukanta duk da babu sauti yana ji ta
yanda jikinta ke amsawa, dagota yayi yana rike
fuskarta, amman hawayen da takeyi ya hana ta
tsaya ta kalle shi
"Ki kalleni mana, Madina, na taba miki karya?
Zan dawo, me yasa ba zan dawo ba? Wa nake da
shi acan din? Dole zan dawo...kina jina, zan
dawo"
Duk da ta saka idanuwan ta cikin nashi yana
kallon rashin yarda a cikin su, fuskarta ya saki
yana kai hannu ya kwance agogon da yake
daure da shi ya kama hannunta ya saka a ciki
Lubna sufyan
Hausabook.com 95
"Ga agogo na ki ajiye mun, idan na dawo zan
amsa..."
Ganin ta dumtse agogon yasa shi saurin dorawa
da
"Mai tsada ne, Daddy ya bani, ki adana mun kar
komai ya same shi, idan ya fashe cikin kudin
kunshin ki na wajen Daada za'a biyani"
Dan murmushi tayi da yasa shi sauke ajiyar
zuciya, hannuwa yasa yana goge mata fuskarta
"Kin girma ba zaki daina kukan nan ba..."
Hannuwan shi ta ture
"Da ka tafi baka yi mun sallama ba ko Hamma..."
Dariya yayi
"Kashe di ne haka Madina? Ni ake ba kashe di
yau?"
Wannan karin tare sukayi dariya. Da nauyin
zuciya yabar gidan Daada, amman kamar yanda
ya fadawa Madina ne, bashi da wani dalili na
zama inda zai tafi, bashi da kowa a can, duk
wani da yake da kusanci da zuciyar shi yana nan
Lubna sufyan
Hausabook.com 96
inda zai bari. Jakar shi ya sake budewa yana zira
hannu a cikin aljihun da yake daga can gefe ya
laluba yana zaro agogon da Adee ta bashi, ita
kalar bula ne ta siya, makaranta ma ya same ta
dan yayi mata sallama
"Na rasa me zan siya fa, tunda watan nan ya
kama nake tunani, kaga inda karshen tunani na
ya kaini"
Karba yayi yana dariya
"Kinsan ba sai kin sai mun komai ba"
Harar shi tayi
"Kanina zai bar kasar ace ba abinda na bashi"
Sosai ta bashi dariya, idan wani ya hango su a
inda suke zaune zai iya dauka saurayin ta ne
"Kina da son girma Adee"
Kallon shi takeyi
"Kasan har goya ka nayi ko?"
Da murmushi a fuskar Nawfal yace
Lubna sufyan
Hausabook.com 97
"Ko da can Adee kafafuwan ki sunyi gajarta su
iya dauka ta"
Duka ta kai mishi a kafada yana rike wajen
"Ouchh... Hannun ki yayi kankanta ace yana da
zafi haka"
Wani dukan ta sake kai mishi
"Adee... Da zafi fa..."
Ganin ta daga hannu yasa shi mikewa tsaye yana
murza inda ta daka, ganin yanda take harar shi
yasa shi yin dariya
"Yi hakuri babbar Yayaa"
Itama dariyar tayi ya koma yana zama
"Sai ka cire agogon Daddy kasa nawa"
Noqe kafada yayi
"Me yasa? Zan ajiye naki dai in ta kallo, amman
agogon Daddy ai ba zai ciru ba kema kin sani"
Kai Adee ta jinjina
Lubna sufyan
Hausabook.com 98
"Laifina ne dana bata baki na, bani agogo na
tunda ba zaka sa ba"
Ta karasa tana kama hannun shi daya janye
yana saka agogon a aljihu. Da gaske yake a
lokacin zai ajiye ne ya dinga daukowa lokaci
zuwa lokaci amman ba yanda za'ayi ya cire
agogon da Daddy ya daura mishi da hannun shi,
bai taba dauka akwai dalilin da zaisa ya cire
agogon nan ba sai jiya da Madina ta hargitsa
mishi duk wani lissafi da yake tunanin yana tare
da shi. Agogon da Adee ta bashi ya daura yana
ganin yanda ya amshi farar fatar shi.
*
"Malam sake jakar nan"
Salim ya furta kamar zai kai mishi duka yana
fisge jakar daga hannun shi ya wuce, bin shi da
kallo kawai Nawfal yayi, bai ma yi tsammanin
yana falon a zaune sai da ya fito daga daki, ba
dan tafiya zaiyi ba sam ba zai ko kalli inda Salim
din yake ba
"Hamma na tafi"
Lubna sufyan
Hausabook.com 99
Shine abinda ya furta, sai da ya dan tsorata da
yaga Salim din ya mike, yaga duk yanda ake
kiran shi dogo sai da ya daga kan shi sannan ya
iya ganin fuskar Salim din daya miko hannu da
nufin karbar jakar da take hannunshi, shi kuma
ya girgiza mishi kai.
"Ba zaka taho ba?"
Salim ya fadi daga bakin kofa yana saka Nawfal
din bin bayan shi da sauri. Duk da haka takun
Salim daya shine kusan na shi guda uku saboda
kafafuwan Salim din, yanzun da Nawfal ya ke
bayan shi sai da murmushi ya kwace mishi,
randa Khalid yace
"Bajjo kaga kafafuwan Hamma? Ban san me yasa
ya ke karantar aikin likitanci ba, kaddarar shi
na ga aikin nepa, ba sai ya taka komai zai dinga
yanke wayoyi ba"
Dariyar da ta sake kwacewa Nawfal din mai
sauti ce dan har sai da Salim ya juyo, sai yayi
saurin boye dariyar da yin tari har sau biyu. Duk
da haka murmushi bai bace mishi ba har suka
karasa wajen motar Daddy da Salim ya zagaya
ya bude gidan gaba yana zama da jakar Nawfal
Lubna sufyan
Hausabook.com 100
din a hannun shi. A bakin motar Nawfal ya tsaya
yana dube-dube, ta inda Khalid zai bullo yake
nema, da ya kalli hanyar bangaren Saratu sai
zuciyar shi ta rage gudun da takeyi a kirjin shi.
Kwakwalwar shi ta fara ce mishi ya bude mota
ya shiga, amman zuciyar shi sai ta kasa, kamar
na umarni tayi wa kafafuwan shi da su fara
takawa zuwa bangaren.
Wata murya cikin kan shi tana fada mishi
"Saboda Khalid da Adee, ko ba dan kowa ba dan
su biyun"
Da ya shiga ma ya ganta zaune a falo, bayan yayi
mata sallamar da ta bishi da kallon "Lafiya? Me
ya faru?" a maimakon ta amsa abinda yake
fadawa kan shi kenan, saboda Khalid da Adee.
"Nanna zan tafi..."
Ya furta a hankali, kallon shi takeyi zuciyar ta na
kara tafasa fiye da yanda takeyi kafin ya shigo.
Yau kwana na takwas kenan da Julde baya mata
magana saboda shi. Akan tayi magana kan
tafiyar shi kasar waje
Lubna sufyan
Hausabook.com 101
"Duka cikin yaranka babu wanda kayi tunanin
turawa karatu wata kasar? Sai shi? Komai na
rayuwar ka akan Nawfal zai kare ne Julde?"
Kai ya daga mata, a karo na farko yana dorawa
da
"Akan shi zan kare Saratu, me zai faru? Nace
akan Nawfal rayuwata zata kare idan kina da
matsala da hakan kofar gida a bude take zaki iya
kama gaban ki, ban taba rike ki ba, ban taba
hanaki ba, saboda Daada ne ban taba ce miki ki
tafi ba, wallahi zaki saukake mun abubuwa da
yawa idan kika tafi da kanki"
Maganganun shi sun mata zafi
"Nawfal ya fini kenan?"
Wani irin kallo yake mata
"Da hada kanki kike yi da shi? Ban taba fada
miki ya fiki ba? Duk tsayin zaman shi a gidan
nan ban taba ce miki ya fiki ba daman?"
Wasu hawaye masu zafin gaske ne suka zubo
mata, tsaki kawai Julde yaja ya fita ya barta a
tsaye. Maganar duniya babu kalar wadda bata yi
Lubna sufyan
Hausabook.com 102
mishi ba a kwanakin nan, in da take ma baya
kallo. A cikin kwanakin wata irin tsanar Nawfal
take ji fiye da wadda take mishi a da.
"Kar ka dawo... Dan Allah idan ka tafi kar ka
dawo"
Ta furta tana saka shi tsayar da idanuwan shi a
kan ta. Tsanar shi yake gani karara a fuskarta,
bai zaci zuciyar shi zatayi mishi zafin da takeyi
yanzun ba. Saboda bai taba tsamannin wani abu
daga wajen ta ba, ya san ta tsane shi daga ranar
farko da kafafuwan shi suka taka cikin gidan ta
"Me yasa?"
Ya tambaya yau a karo na farko yana saka
idanuwan shi cikin nata
"Me yasa Nanna? Me nayi miki haka? Me yasa
kika tsane ni?"
Tabe baki tayi jin yanda muryar shi ta karye a
karshen tambayar kamar shi dinne wanda aka
yiwa wani abu, kamar zuwan shi bai kara mata
matsaloli ba, kamar ita din bai kamata a tausaya
mata ba saboda duka laifin nata ne
Lubna sufyan
Hausabook.com 103
"Matsala ka kara mun Nawfal, zuwan ka matsala
ya kara mun, shisa bana so ka dawo. In ka tafi
karka dawo"
Iskar dai yaja yana cika baki da ita kafin ya fito
da ita a hankali, kirjin shi na kara daukar dumi,
juyawa yayi yana cin karo da Salim da ya rike
mishi kafadu dam, da yake bai tsammaci zaiyi
karo da wani abu ba, da Salim din bai rike shi ba
baya zaiyi ya fadi, gefe Salim ya janye shi batare
da yace komai ba ya nufi hanyar kitchen, shi
kuma Nawfal yana ficewa. Tsaye yayi bakin kofa
ya sa hannu ya dafe kirjin shi da yake zafi, anan
Salim ya fito rike da robar ruwa
"Muna ta jiran ka"
Ya fadi yana wucewa, bin bayan shi Nawfal din
yayi har wajen mota. Sai da ya bude baya ya
shiga sannan ya ga Khalid a ciki. Zama yayi yana
jan kofar ya rufe. Ba zaice ga abinda Daddy yake
fada ba dan hankalin shi yayi wani wajen,
hannun Khalid da yaji kamar yana saka mishi
wani abu a cikin na shi ne ya saka shi kallon
hannun na shi yana dago abinda yake ganin
kamar wata silver, dubawa yayi, abin hannu ne
Lubna sufyan
Hausabook.com 104
da ake kira da bracelet a turance, tsuntsu ne ya
bude fuffuke a tsakiyar abin hannun, Khalid ya
kalla da yaki yarda su hada idanuwa
"Ya zama mukullin kejin ka..."
Khalid ya fadi cikin sanyin murya
"Fly Bajjo, iya inda zaka iya"
Kai kawai Nawfal ya jinjina mishi, su duka babu
wanda ya sake cewa komai har suka isa Airport
din, ba zama sukayi ba tunda jirgin karfe sha
daya na dare zai tashi.
"Kana sauka saika samu ka kira ni, ka dai
rubuta lambar wayar ko?"
Cewar Julde da alamu suka nuna baya cikin wata
nutsuwa mai yawa, dan murmushin karfin hali
Nawfal yayi
"Na haddace fa Daddy, zan kira dana sauka"
Kai Julde ya jinjina, Nawfal din yana mikawa
Khalid hannu, shima hannun ya mika mishi yana
jan shi bayan ya rike suka rungume juna, Salim
da yake tsaye ya dakuna fuskar shi yana furta
Lubna sufyan
Hausabook.com 105
"Ewww"
Sakin juna sukayi suna dariya, Nawfal ya juya ya
kalli Salim din da yake ta bata fuska har lokacin
"Marin ka zanyi sai ka ga taurari"
Dariya Nawfal yayi
"A gaban nawa zaka marar mun yaro?"
Daddy ya fadi yana murmushi
"Allah ya tsare mana kai Bajjo, dan Allah ka kula
da kyau kaji ko?"
Julden ya nanata mishi ya kula idan wani yaji
saiya dauka yaron goye ne shi din. Kai kawai ya
jinjina yana kallon Khalid da yake bin shi da ido
"Zan kira ku"
Ya furta su duka suna daga mishi kai, kafadar
shi yaji Salim ya dafa yana dan tura shi, hakan
na sawa ya juya suka dan taka, kafadar shi Salim
ya saki yana kamo hannun shi ya saka mishi
jakar shi da yake rike da ita a ciki yana hadiye
yawu, sosai yake kallon Nawfal din
"Abin da Nanna ta fada..."
Lubna sufyan
Hausabook.com 106
Yace yana saka Nawfal ware mishi idanuwa dan
ko kadan Salim din bai nuna alamar yaji
zantukan da sukayi da Saratu ba
"Kar ka saka su a zuciyar ka, idan nace maka
bata nufin abinda ta fada karya zanyi, ka san
karya zanyi Bajjo..."
Kai Nawfal yake dagawa
"Nanna ta fada maka maganganu da yawa, baka
saka su a ranka ba, wannan ma ka watsar.
Dalilin ta na ce maka karka dawo nata ne ita ka
dai, karka watsar da kowa saboda ita"
Kokari yake kar yayi kuka tun safiyar yau, ya
dauka Khalid ne zai saka shi kuka, hakan bai
faru ba. Maganganun Salim ne suke karya mishi
zuciya, saboda Salim ba mai yawan magana
bane ba, asalima Salim baya shiga rayuwar
kowa a gidan shisa bai taba tunanin ya damu da
ko Khalid ba balle shi, balle ya kula da wani abu
daya danganci rayuwar shi
"Ka yi abinda zaka yi ka dawo, idan zaka zauna
ka tabbata ba saboda abinda Nanna ta fada bane
ba, saboda kana da naka dalilin ne... Khalid da
Lubna sufyan
Hausabook.com 107
Adee zasu so ka dawo, ga Daddy ma, ba saina
fada maka Daada ba... Ni ma ina so ka dawo
saboda in kama ku kuna zagina da Khalid in
muku dukan dana dade ina tarawa"
Yanda ya karasa maganar yasa Nawfal yin
dariya, duk da hawaye ne cike taf da idanuwan
shi, jakar Salim ya sakar mishi yana fadin
"Allah ya tsare ya dawo mana da kai lafiya"
Kai kawai Nawfal ya iya dagawa, idan yayi
magana kukan da yake tarbewa ne zai kwace
mishi. Takawa yayi kawai yana cigaba da tafiya
kafin ya juyo ya hange su tsaye, hannun shi ya
daga musu, da Khalid da Daddy ne suka daga
mishi hannu suma. Salim kai kawai ya jinjina,
baya shiga harkar kowa saboda baya son jin
wani abu kusa da zuciyar shi, baya son saka
kowa da komai cikin ran shi, duk wani abu daya
danganci hayaniya baya so. Yau yayi ma Nawfal
magana saboda kunnuwan shi sun sha kwaso
mishi maganganun Saratu da take yiwa Nawfal
din da baya son ji.
Yanda yaron yake rayuwa da wannan hayaniyar
har mamaki yake yi. Fata daya ya tsinci kan shi
Lubna sufyan
Hausabook.com 108
da bin Nawfal da shi yanzun da suka juya hanya.
Allah yasa da jirgin su ya tashi ya bar duk wata
hayaniya da take cikin rayuwar shi, tafiyar ta
samar mishi da wani shiru a rayuwar shi.
Sai dai abinda Salim bai hango ba shine addu'ar
shi da ta karbu
Nawfal ya bar duk wata hayaniya da tafiyar shi
Ya barta tana jiran dawowar shi
Dawowar da idan tayi mishi maraba sautin ta
bashi kadai zaiji ta ba
Har su da suke zagaye da shi sai ta taba.
"Karatu ne ya rike ni Daada..."
Shine uzurin farko daya fara kawo mata a cikin
shekaru biyu, a kuma karo na farko da taji
muryar shi ba sakon gaisuwar shi a bakin Julde
ba. Yanda take kwana tana tashi a cikin
shekarun Allah ne kawai shaida, sai kuma ita da
ta san kalar damuwar da take ciki, tunani babu
kalar wanda batayi. Duk idan Julde yace mata
"Munyi waya da Bajjo, yace a gaishe da ke sosai"
Lubna sufyan
Hausabook.com 109
Sai ta dauki dakika tana kallon kwayar
idanuwan shi ko zata ga karyar da take tunanin
yayi mata. Amman saiya fada murmushin shi da
cewa
"Kinsan akwai banbanci awa kusan biyar
tsakanin mu da su, sanda zai kira zakiga sai
wajen karfe goma da rabi na
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 4 Chapter of 18