Allah zai iya duba zuciyar yaran yaki
jarabtar su?"
Girar Nawfal ta hade waje daya cike da mamaki
da kuma son fahimtar in da tambayar Khalid din
ta dosa
"Kamar zina da akace maiko take da shi, kana
tunanin yara zasu iya kubuce ma wannan
maikon kuwa?"
Wannan karin akwai bayanannen tsoro a
muryar Khalid da yasa Nawfal mika mishi
hankalin shi duka, a iya sanin shi Khalid bashi
da wani hali marar kyau, ko a mugun mafarki
kuwa ba zai hada shi da aikata laifi mai munin
zina ba. Shisa yake neman dalilin da tunanin
Lubna sufyan
Hausabook.com 415
Khalid din zai dibe shi zuwa inda yake yanzun
har ma wannan tambayoyin su hade mishi
"Banajin na fahimci tambayar ka Hamma..."
Nawfal ya fadi da dukkanin gaskiyar shi,
numfashi mai nauyi Khalid ya sauke, idanuwan
shi cike da wani firgici da Nawfal ya rasa dalilin
shi hadi da furta
"Hmmm..."
Sosai Nawfal ya juya dan saida ya motsa kujerar
da yake da kai
"Banda amsar tambayar ka, abu daya na sani,
kaima kuma ka sani, babu wani abu da yafi
karfin Allah, wanda Ya so a cikin kowanne hali
zai iya kubutar da shi"
Kai Khalid ya jinjina ma Nawfal yana juyawa da
alamar da take nuna ya gama maganar. Mikewa
Nawfal din yayi ya karasa wajen kwan fitilar
dakin ya kashe ma Khalid din, ba zai daice ya
kashe ba, amman yasan hasken zai iya takura
mishi. Ya bada wajen mintina sha biyar a
tsakani, baiji Khalid din ya motsa ba, cikin sanda
ya karasa ya leqa fuskar Khalid, idanuwan shi a
Lubna sufyan
Hausabook.com 416
rufe suke, da alama bacci ya dauke shi. Abin rufa
Nawfal yaja ya rufe shi yana tsaye akan shi, duk
wata addu'a ta tsari da neman sauki sai da yayi
yana tofa mishi, baisan me ya same shi ba,
amman baya son tsoron da ya gani a cikin
idanuwan shi
"Allah zai kare mun kai Hamma, daga dukkan
abin ki"
Ya furta a kasan numfashin shi yana komawa ya
zauna, Khalid na jin shi, yana ji yaja mayafi ya
rufa mishi, yana jin addu'ar daya tofa mishi,
haka kuma kalaman shi da suka rufe Khalid din
ruf, fiye da mayafin da Nawfal ya rufa mishi,
kirjin shi yanayin nauyi da sirrin da yake
tunanin shi kadai ya san da shi.
Mutane zasu tsammaci ganin kunshi a
hannuwanta ko da yaushe kasancewar ta wadda
ta iya. Amman tana daya daga cikin mutanen da
lalle bai dame su ba sam. Asalima sai ta dade ko
a farcenta bata saka ba, baifi kagani a jikin
babban yatsan ta da kuma mabiyin shi, shima
baka raba kowacce mai kunshi da shi, sai dai
Lubna sufyan
Hausabook.com 417
wanda suke saka safar hannu. Tana da su da
yawa, irin na asibiti ma, kwali daya Salim ya
bata, rashin sabo yasa duk sai taji ta takura,
kwarkwaron kunshin ma yana zamewa daga
hannunta idan ta saka. Tun yana mitar baya son
ganin tana bata hannun ta harya gaji.
Yau din ma sauran wanda ya rage a
kwarkwaron da tayiwa wata yar islamiyyar su
ne kawai ta zauna tana zanawa a jikin hannun
ta, ba wani mai yawa bane ba, amman ko ita da
tayi sai taga yayi mata kyau bayan ta gama tun
ma bai bushe ba, hannun harya zama na mace,
tana tunanin yanda in ta wanke lallen har wasu
zobuna masu yawa da Adee ta bata zata dauko
ta bude kwalin ta gwada ko da kwara biyune a
yatsun taga yanda zasuyi. Adee akwai son
kwalliya, kuma kyau takeyi ma Madinar, zobe
zaka gani a kasa da saman yatsun ta, in gidanta
kaje yanzun da tayi aure ma har a yatsunta biyu
na kafar dama zaka sameta da su ta saka.
Daki ta koma ta dauki remote sannan ta samu
kujera ta zauna duk da la'asar ake kira tunda
Allah ya hutar da ita, shisa ma ta zana kunshin
ta hankali a kwance. Tashar India ta kai ana
Lubna sufyan
Hausabook.com 418
tsakiyar yin film din Kabhi Khushi Kabhie Gham,
labarin film din take ji ana yawan yi, tana kuma
sakawa a ranta da zata nema ta kalla, sai dai ba
littafi bane ba, film ne. Kallo na karshen
abubuwan da ta damu da su, idan tana zaune
kamar yanzun ma tana iya taita wasa da remote
din tana rasa inda zata tsaya ta kalla, karshe
tashar labarai ko documentary ne abinda zaiyi
nasarar rike hankalin ta. Da yake ana rubuta
fassarar da turanci sai ta bama tv din dukkan
nutsuwar ta.
Tana iya juyo sautin bugun zuciyarta da ya zarta
har cikin kunnuwan ta da wani yanayi da ba zai
misaltu ba, bakinta na gaurayewa da dandanon
gishirin da bata san inda ta samo shi ba, ko
dandanon hawayen da take jine cike taf da
idanuwan ta da take kokarin hanawa su zubo
suka koma suka gangara cikin bakinta,
shakuwar da take tsakanin jarumin film din da
mahaifiyar shi na jijjiga duniyar da take zaune
tana sa hanjinta yamutsawa kamar suna son
sake mazauni saboda hargitsin da take ji har su
ya tarar a cikin nata. Idan tace Yelwa bata fado
mata lokaci zuwa lokaci tun kafin ta karanta
Lubna sufyan
Hausabook.com 419
wasikar nan zai zamana karya, duk lokacin da
idanuwanta zasu sauka akan wani shafin littafi
da yake magana kan mahaifiya sai tunanin tata
ya kutsa mata.
Haka idan taji wasu suna labarin ta su, ba zatace
ta rasa nagartacciyar soyayya da kulawa a wajen
Daada ba, amman akwai ramin da take ji a
zuciyar ta kamar wajen an halicce shi domin
Yelwa ne, kasancewar ta a rayuwar ta ko akasin
hakan baya nufin wani zai taba iya zama a gurin.
Sai take jin da za'a bata dama guda daya zata
koma ta goge ranar da taga wasikar nan, yanda
duk ta so ta koma dai-dai, ta koma kamar kafin
ta ga wasikar nan sai ta kasa. Abu kadan daya
danganci mahaifiya take jin yanda yake samun
tasirin raunana mata zuciya.
Ko jiya taga kallon da Daada take yiwa Julde,
batasan ko raunin zuciyarta bane ya sa ta ganin
zuciyar Daada a cikin idanuwanta duk idan tana
kallon Julde, kaman in dai yana karkashin
kulawarta zata kareshi daga dukkan wani abu
da yake ikon ta, kamar rayuwar ta na da
muhimmanci ne tare da dan nata. Da bata gani,
amman yanzun tana ganin wannan kaunar,
Lubna sufyan
Hausabook.com 420
murmushin Daada ma akwai banbanci a cikin
shi idan Julden yana kusa. Tsakanin mahaifiya
da yaranta wata sirrantacciyar kauna ce da
Allah daya halitta musu ne kawai Ya san girman
ta.
Sai take tunanin meye bambancin sauran iyaye
da tata mahaifiyar? Me yasa tabar ta? Ko dan
rashin tabbacin da yake cikin halarcin haihuwar
ta? Idan ta duba wannan kawai ya isa ya zama
babban dalili a wajen Yelwa, takan ji kamar tana
neman wani uzuri ne da zai saukaka mata
abinda takeji. Salim yace ta jira Daada idan ta
shirya zata fada mata komai a lokacin da take
tunanin ya dace, tana kuma kokarin ganin tayi
hakan, sai dai da duk wata rana da zata wuce da
yanda tarin tambayoyin ta suke kara ninkuwa.
Har mamaki takeyi yanda Daada ta kasa
karantar tambayoyin a cikin idanuwanta.
Wanne lokaci ne ya dace? Yaushe ne Daada zata
fada mata komai? Ko ma tana da niyyar fada
mata din? Duka amsoshin tambayoyin nata na
wajen Daada. Zuciyarta da nauyi kamar an dora
mata dutse ta kai hannu ta dauki remote din
tana canza tashar. Mikewa ma tayi tana komawa
Lubna sufyan
Hausabook.com 421
daki, bayi ta wuce ta wanke kunshin da yanzun
ya fita daga kanta saboda zuciyar ta da take ji
cunkushe. Sai kewar Salim ta danneta har tana
sakata karasawa kan gadon dakin nata ta dauki
wayarta ta duba taga bai kirata ba, bai kuma
tura mata ko da text bane ba. Sun yi waya da
safe, amman gaisawa kawai sukayi, tun
shekaranjiya rabon da ta saka shi a idanuwanta.
Jikin ta yana bata akwai abinda yake damun shi,
amman shi din ba mai yawan magana bane ba,
bai taba bude baki yace mata ga damuwar shi
ba, sai dai ta karanci yanayin shu taita jan shi da
hirarrakin da take tunanin zasu saka shi
murmushi ko kadan ne, ta kuma dinga tuna
mishi yaci wani abu, dan in yana cikin yanayi
irin wannan sai kaga idanuwan shi duk sunyi
zuru-zuru ko idan aiki ya sha mishi kai, in tace
ya rame baya cin abinci yanda ya kamata sai
yace mata
"Mantawa nake yi Mug, bakya tuna mun,
mantawa nakeyi idan abubuwa sun mun yawa"
Yanzun idan ta ganshi haka sai taita jin kamar
harda lefinta, kamar in shi ya manta bai kamata
Lubna sufyan
Hausabook.com 422
ita ta manta ba. Ko ba komai Salim ne, komai
nata damuwar shine, shirme da hankali zai bata
nutsuwar shi kamar duk duniya babu wani abu
mai muhimmanci kamar sauraren ta da abinda
yake damunta. Ya kamata shima tashi damuwar
ta zama tata, ta kamanta mishi kalar karamcin
da yake nuna mata. Tun dazun ta manta basu yi
magana ba, bata ma tuna da shi ba sai yanzun da
damuwar da take neman ya taimaka ya saukaka
mata ta taso.
Tsintar kanta tayi da jin kunya har tana kasa
kiran shi, ta dai dauki wayar ta sake komawa
falon ko da shi zai kirata. Daada ta samu a zaune
ta fito itama, yanzun tafi zama cikin dakinta fiye
da yanda take zama a falon. Canjine Madina take
gani bayyane a tare da Daadar da ya girmi tsufa
kamar yanda take yawan fada, kullum gani
Madina takeyi tana kara ramewa kamar bata cin
abinci, da ba gida daya suke ba kuma ba ita take
kula da cin safe, rana harma na daren Daadar ba
zatace ba'a kula da ita yanda ya kamata.
"Assalamu alaikum"
Lubna sufyan
Hausabook.com 423
Muryar Nawfal ta daki kunnuwan Madina tana
sakata saurin daga idanuwanta da zuciyarta da
tayi tsalle zuwa cikin su tana kallon Nawfal da
ya sakko kafar shi cikin dakin fuskar shi dauke
da murmushi, manyan kayane a jikin shi, yadi
kalar sararin samaniya sai hula mai kalar
amman mai duhu, kayan sun karbi jikin shi,
rigar na nuna fadin kafadun shi da cikar halittar
shi duk da bata matse shi ba. Sai dai akwai
banbanci a yanayin yanda muryar Nawfal ta
sauka a kunnuwan Madina da kuma na Daada.
Muryar Bukar taji, muryar dan ta da rayuwa ta
zabi ta rabata da shi a karo daban-daban.
Da ta daga ido ma ta sauke akan Nawfal fuskar
Bukar ta gani, murmushin shi mai sanyi kamar
halayen shi take gani, duk da ko kusa da sanyin
halin Bukar din Nawfal bai kai ba, ita kam yau
Bukar take gani kamar yanda yanzun da karfin
alaka ta jini tasa take ganin Yelwa a tattare da
Madina duk da kowa yasan Yelwa zaice bata
kama da Madina, amman jini yafi karfin wasa.
Da duk wayewar gari da yanda nauyin kirjinta
yake karuwa a tsayin shekarun nan, yanzun ya
kai inda take jin anya bashi zaiyi ajalin ta ba
Lubna sufyan
Hausabook.com 424
kuwa? Idan ta kwanta bata tunanin komai sai
yanda zata sauka daga gado da safe, yanda za
tayi rayuwa a yinin ranar batare da ta kara ma
Madina damuwar da take gani cikin idanuwan
ta ba.
A satikan nan tana bude bakin ta yafi a kirga sai
ta kasa furta komai, me zata ce? Me zata fadama
Madina? Ta ina ma zata fara? Yarinyar bata taba
tambayar ta komai ba, kamar sun zauna sun
hada baki da Nawfal suka zabi shirun da ya
saukaka mata komai saboda bata da kwarin
gwiwar fuskantar su da labarin da ba zai amfane
su da komai ba, bata son ko na minti daya su
raba nauyin da take ji tare, duk da tasan nauyin
ba nata bane ita kadai, wata rana dole ta raba
shi tare da su, yanzun tana jin kusancin ranar
fiye da kowanne lokaci. Girma sukeyi su duka,
shekaru na riskar su, rashin tabbas din yau da
kullum na kara lullube Daadar.
Tana jin ina ma ace ta san sauran kwanakin da
suka rage mata, da tafi tsara yanda komai zai
kasance
"Daada Am"
Lubna sufyan
Hausabook.com 425
Muryar Nawfal ta kutsa cikin tunanin ta
"Soyayyar tawa ce ta motsa haka kike ta kallo na
harma bakyajin me nake cewa?"
Murmushi tayi tana jin wani abu ya rabe a cikin
kirjinta
"Ko bata bakina ma ba zanyi ba"
Dariya yayi yana karasawa ya tsugunna a
gabanta
"Bana son ramar nan dake cikin idanuwan ki
Daada... Duka kwana nawa ne ban ganki ba yau
amman kin kara ramewa"
Kai Daada ta girgiza tana sauke idanuwan ta
daga cikin na shi saboda bata son yanda yake
kallon ta kamar yana neman tono dukkan
sirrikan da take boyewa
"Wai ba zaku kyaleni ba ne? Idan ma bana
ramewa yanzun surutun da kuke mun zai sa in
fara"
Ta karasa maganar tana kokarin mikewa,
Nawfal na tayata cikin hanzari, yana tuna mata
lokuttan da ta taimaka mishi ya mike haka, ta
Lubna sufyan
Hausabook.com 426
ma daga shi gabaki daya tana mikarwa. Sai da ya
tabbatar ta tsaya da kafafuwan ta tukunna ya
saketa a hankali yana nazarin ta bayan ta juya,
yanda take cira kafafuwan ta dakyar yasa
zuciyar shi yin nauyi. Ko lafiyar ta kalau akwai
abinda ta saka a ranta, shisa take boye mishi
haka, daya shigo gidan suka gaisa take tashi
tabar falon, idan dakin ta ya bita sai ta kwanta
kamar bacci ya dauketa, wata rana ya dauki filo
ya kwanta anan kasa, ko ya dora kan shi akan
gadon har saiya gaji da zama.
Yanzun da yake kallon ta babu komai cikin
kanshi sai rokon da yake ma Allah na ya ara
mishi lokaci mai tsayi tare da Daada saboda
itace cikon komai na rayuwar shi, ko Murjanatu
bata gani ba sai dai a waya, akwai tarin
abubuwan da yake bukatar aron lokaci ya
gudanar da su tare da Daada a cikin rayuwar
shi. Itama tana jin idanuwan Nawfal din, tasan
kallon ta yakeyi, kanta take ji yayi nauyi fiye da
misali, kamar babu iska a cikin shi duk da bata
san ko akwai yiwuwar cewa iska zata kasance
cikin kai ba, kawai hakan zata iya amfani da shi
wajen misalta yanayin da take ji.
Lubna sufyan
Hausabook.com 427
Hasken daya gilma cikin idanuwan ta na sakata
runtsa su ta bude, sai taga duhu, ba duhu irin na
gabatowar magriba ba, duhu fiye da na tsakar
dare saboda bata iya ganin kyallin komai, sake
runtsa idanuwan nata tayi wannan karin duhun
na karasawa har cikin kanta
"Daada..."
Taji an kirata kamar daga wata duniya saboda
nisan da kwakwalwar ta tayi da kanta duk kuwa
da suna hade waje daya, hakan na sa wani abu
cikewa a kirjinta kafin komai ya tsaya mata cak.
*
Kamar shirin film haka komai yake dawo ma
Madina da Nawfal, da murmushi a fuskokin su,
komai na tafiya lafiya kafin ya birkice a kasa da
minti daya. Kowa ka tambaya zaice shi ya fara
ganin alamar Daada zata fadi, amman babu
lokacin wannan musun tunda babu wanda ya
iya karasawa ya tare ta a cikin su sai bayan da ta
kai kasa tana faduwa tare da wani bamgare na
zuciyoyin su. Sai sakanni suka dinga wuce ma
Nawfal da nisan awanni, komai baya sauri har
shi kan shi, haka yaji daga daukar Daada daga
Lubna sufyan
Hausabook.com 428
cikin gidan zuwa motar shi haka shigowar su
asibiti, haka dorata akan gadon da ya kama aka
gungura har zuwa dakin da wani likita ya kai
hannu yana turo shi baya kafin su maido kofar
su rufe.
Tsaye yake amman ya rasa inda zai sa kan shi
yaji sanyi, numfashi ma kokawa yake da shi a
wannan lokacin
"Ka zauna Hamma..."
Madina ta fadi cikin sanyin murya tana saka shi
juyawa ya kalleta, nutsuwar ta na bashi mamaki,
akwai damuwa shimfide saman fuskarta amman
a nutse take
"Tashin hankali baya taimakon marar lafiya,
nutsuwa yake bukata fiye da komai. Nutsuwar ki
ita ce taimakon farko, ki rufe idanuwan ki kiyi
numfashi mai nauyi ki fitar har sai kin tabbata
kin samu nutsuwar da kike bukata..."
Shine abinda Salim ya fada mata, ya maimaita
mata har saida ya tabbatar ta fahimta bayan ta
haddace kowacce kalma. Shisa yanzun ita ta
fada ma likitan sunan Daada, shekarun ta da
Lubna sufyan
Hausabook.com 429
kuma lambar katinta da ta haddace ko da zasu
taho asibiti a hargitse bata dauko ba za'a iya
amfani da lambobin a binciko file din ta kamar
yanda tasan anyi yanzun din, ko ana kanyi
"Ina wayar ka?"
Ta bukata ganin gardamar da take cike da
idanuwan Nawfal din akan tayin zaman da tayi
mishi, ta masa uzuri, wannan ne rashin lafiyar
farko da Daada tayi yana nan. Aljihun shi Nawfal
ya laluba yana dauko karamar wayar da yaji a
jikin shi ya mika mata. Lambar Salim da ta
haddace ta saka tana kiran shi, sai da ta kira sau
uku ana hudun ya daga da fadin
"Yanzun na shigo na dauki wayar Bajjo,
menene?"
Numfashi taja tana fitarwa
"Hamma ni ce"
Da mamaki a muryar Salim yace
"Madina?"
Cike da alamar tambaya kafin ya dora da
Lubna sufyan
Hausabook.com 430
"Lafiya? Me ya faru? Ina Bajjon?"
Sai da ta kalli Nawfal sannan ta amsa
"Gashi nan, yana lafiya. Muna asibitin ku...
Daada ce ta fadi"
Ta karasa tana jin yanda bugun zuciyar ta yake
karuwa cike da tsoro, girman abin da ya faru a
gabanta yana danne ta
"Ki tashi ki duba saiki fadamun inda kuke?"
Mikewar tayi kuwa, ya nuna mata yanda zata
karanta sunan kowanne ward a asibitin ta kuma
gane in da take, dubawar tayi tana fada mishi
"Gani nan zuwa yanzun... Daddy ya sani?"
Kai Madina ta girgiza
"Kai na fara kira..."
Ta fadi cikin sanyin murya
"Karki kira kowa tukunna, gani nan"
Wayar ta sauke daga kunnenta tana kashe
kiran. Riga da wando ne a jikinta, ta dora ta
sanyi doguwa akan tshirt din da takai mata har
Lubna sufyan
Hausabook.com 431
gwiwar ta, akwai maballai a jikin rigar daga
farko har karshe, an yi kwalliya da wasu har a
gefe, sai hula da ta dan tura baya batare da
gashin ta ya bayyana ba, haka take zaune sanda
Nawfal ya zo, haka kuma ta fito batare da ta saka
komai ba sai takalmin da daman akwai shi a
kafarta na yawo cikin daki. Tsaye take har Salim
ya karaso yana kai hannu ya tura mata gilashin
dake fuskarta ganin ya dan sakko ita kuma bata
mayar da shi ba.
Tayi mishi kyau kamar ya dauketa ya boye,
zuciyar shi ta yamutsa lokacin da ya yawata da
idanuwan shi akan fuskarta
"Wanne daki suka shiga da ita?"
Da hannu ta nuna mishi saboda idanuwanta da
taji sun cika da hawaye, tana yin magana
zubowa zasuyi, kai ya jinjina yana kama hannun
nata ya jata ya karasa da ita inda ta tashi a
waiting area din yana zaunar da ita. Nawfal ya
kalla da yake tsaye
"Bajjo..."
Lubna sufyan
Hausabook.com 432
Ya kira a hankali, tun yarinta zaka iya cewa
Nawfal na da juriya, tunda kafin kaji kukan shi
zai wahala komin dukan da Saratu zatayi mishi
kuwa, sai ta mare shi ya fadi ya tashi yayi tsaye
kamar yana son ganin iya abinda zata iya yi.
Kowa zai ce yana da karfin hali, abinda zai taba
shi mai girma ne. Shi ne zai karyata, Nawfal ne
yaro mafi rauni daya taba cin karo da shi, ko
idanuwan shi ka kalla zaka ga wannan raunin,
yana da babbar zuciyar da yake yawo da ita rike
cikin hannuwan shi yana jiran mai rabo ya gifta
dan ya karbe shi cike da karamci.
Akwai vulnerability a tare da Nawfal din da
baisan yanda zai misalta ba. Kullum ya gan shi
sai yaga kamar akwai abinda yake bukata da su
duka suka kasa ba shi, ya dauka zai ga abin ya
kau bayan yayi aure, yana nan, matar shi ma
bata bashi wannan abin da yake nema ba, har
yanzun bai cika ba, akwai rami mai girma a tare
da shi. Wannan raunin kuwa shine a bayyane
yanzun, karasawa Salim yayi yana kamo hannun
Nawfal din da yake kokarin kwacewa, sai dai ba
girman su bane kadai bambancin, harma da
Lubna sufyan
Hausabook.com 433
karfin su, jan shi yayi yana amfani da karfi
wajen zaunar da shi gefen Madina.
"Har yanzun ba su fito ba Hamma? Bata
numfashi sanda muka zo...bata numfashi...
Daada bata numfashi Hamma..."
Kai Salim ya daga mishi kamar a gaban shi
akayi, saboda fahimta Nawfal yake bukata, so
yake wani ya fahimci abinda yake ji ko zai samu
sauki. Kirjin shi kamar zai tsage gida biyu, da
gaske labarin tashin hankali yake ji, bai taba
fahimtar ya yake ba sai yau, wancen karin
abinda yaji wasan yara ne, ya dauka idan yazo
yaga Daada, ana komai a gaban idanuwan shi sai
yafi samun sauki. Ashe ba haka abin yake ba,
ashe nisan da yayi sauki ne, bai ganta ba, bai ga
kamar ya rasa ta ba.
Tare da wani bangare a zuciyar shi suka fadi, ko
Daada ta tashi bayajin wannan bangaren zai
mike, faduwar da yayi ba wadda zai mike bace
ba.
"Breath..."
Salim ya furta cikin umarni
Lubna sufyan
Hausabook.com 434
"Yanzun Bajjo, in... Out.... In... Out"
Numfashin kuwa yake ja, yana fitarwa, muryar
Salim na mishi jagora, har sai da ya dan fara
samun nutsuwa tukunna
"Ka zauna nan, ku duka ku zauna nan"
Ya fadi yana kallon Madina da ta kai hannu tana
share hawayen da ya zubo mata. Bayajin ta
kamar Nawfal, tana da karfin hali duk da
kankantar ta. Idan ta kama ya san zata ture
damuwar ta a gefe ta kula da Nawfal din. Yana
shirin karasawa dakin likitan na fitowa. Daga
inda su Nawfal suke basa iya juyo abinda su
Salim din suke fadi, ta gaban su dai suka wuce,
sun fi mintina sha biyar kuma kafin Salim ya
dawo shi kadai.
"Me yace? Ta tashi? Me yace ya same ta?"
Nawfal ya jera ma Salim tambayoyin da kafin ya
zabi wadda zai fara amsawa ya kara da
"Zamu iya shiga mu ganta? In shiga in gan ta
Hamma?"
Kai Salim ya girgiza mishi a hankali
Lubna sufyan
Hausabook.com 435
"Sai ta kara hutawa...za'a kara mata wasu tests
din tukunna..."
So yake ya basu tabbacin da yaga suna nema
akan fuskar shi kamar duk wani wanda zai
kawo marar lafiya, amman a yanzun ya ture
batun cewa su din na shi ne, likita ne shi a
yanzun, su kuma yan uwan mai jinya.
"Zamu san komai idan aka karasa sauran tests
din...banda abinda zan fada muku yanzun da ya
wuce tana samun dukkan taimakon da take
bukata"
Hannuwa Nawfal ya saka yana dafe kan shi da
su, likita ne a gaban shi ba Salim ba, ya gani, ya
kuma ji a muryar shi, numfashi yake ja yana
fitarwa a hankali sannan ya dago ya kalli Salim
din
"Hamma..."
Ya kira amman Salim yaki kallon cikin
idanuwan shi
"Hamma ka cire rigar nan kayi mun magana,
dan Allah kayi mun magana"
Lubna sufyan
Hausabook.com 436
Nawfal ya karasa cikin roko, muryar shi na
fitowa cike da rauni.
"Ka fadamun... Kaji"
Yayi maganar cikin karfin hali yana son Salim ya
fahimci zai iya daukar koma menene akace yana
damun Daadar, so yake yaga ba yaro bane shi
karami da yake bukatar kariya. Dan murmushi
Salim din yayi mishi
"Sai an gama running tests Bajjo..."
Gardama zai karayi Madina ta katse shi
"Zaka zauna damu ko zaka kara dawowa?"
Numfashi Salim ya sauke yana godema Madina,
idanuwan shi ya sauke cikin nata yana fatan
taga godiyar shi
"Zan sake dawowa...da sun gama abinda sukeyi
zasu sake mata daki, sai ku zauna da ita"
Madina ce kawai ta iya daga mishi kai
"Idan kuna bukatar wani abin sai ki kirani"
Kan dai ta sake daga mishi, ya kalli Nawfal daya
kauda na shi kan gefe da alamar fushi yakeyi
Lubna sufyan
Hausabook.com 437
saboda yaki gaya mishi me ya samu Daada,
numfashi kawai ya sauke yana wucewa yabar su
a wajen. Office din shi ya koma ya zauna yana
sauke wani dogon numfashi hadi da kai hannu
ya murza kan shi daya fara alamar ciwo, ya
gama round din shi sai kuma nan da awa daya,
idan ba an shigo da marar lafiyar da yake
bukatar agajin gaggawa ba. Ya kira Julde bayan
sun gama magana da likitan yana kuma jira ne
ya karaso asibitin.
Da gaske ne da yace ma su Nawfal sai an gama
gwaje-gwaje tukunna, amman yana da abinda
zai fada musu, zuciyar da zaiyi amfani da ita ya
fada musun ne bashi da ita. Da Madina ce ita
kadai zai san yanda zai gaya mata yayi mata
bayanin da zata fahimta, Madina ce zai ma iya
neman wasu takardu akan matsalar ya bata ta
karanta, zai sha tarin tambayoyin da yasan ba
zai iya amsa mata ba tunda shi ba likitan zuciya
bane ba, amman ya san likitan zuciyar, ya kuma
san zaiyi farin cikin amsa ma Madina dukkan
tambayoyin ta.
Nawfal yake ji, yanda yake a hargitsen nan yana
ce mishi akwai yiwuwar sai an ma Daada aiki,
Lubna sufyan
Hausabook.com 438
akwai yiwuwar ba toshewar jini bane da rashin
kai kawon shi yanda ya kamata a tsakanin
jijiyoyin ta da kuma zuciyar ta kamar wancen
karin, matsala ce da ta girmi a dora ta akan
magunguna, zai iya yiwuwa sashe ne kacokan a
jikin zuciyar tata ya gaza yake kuma bukatar a
sake shi cikin gaggawa kafin ya haifar da wata
sabuwar matsalar, duka hasashe ne yanzun,
babu abinda aka tabbatar sai likitan da aka kira
ya zo. Bashi da karfin halin da zai sake daga ma
Nawfal din hankali akan hasashe, sai an
tabbatar da komai tukunna.
Ya godema Allah da bai fada ma su Nawfal
komai ba ganin yanda Julde ya hargitse bayan ya
zo asibitin ya karasa Office din Salim din ya
kuma yi mishi bayanin hasashen da likitan yayi
"Dan Allah Daddy, kar su Bajjo su ganka haka su
dauka wani babban abin ne, bafa wata matsala
bace da ba za'a iya shawo kanta ba, idan ma
surgery dinne bashi da wata matsala..."
Salim yake fadi cikin tausasawa
Lubna sufyan
Hausabook.com 439
"Ko kasar za'a bari da ita, Alhamdulillah akwai
halin yin hakan... Dan Allah ka kwantar da
hankalin ka"
Kai kawai Julde yake daga ma Salim din ba dan
yasan ta inda zai fara kwantar da hankalin shi
ba. Har ruwa ya bashi mai sanyi, da kan shi ya
bude mishi robar, kurba daya yayi yana jin
ruwan ya wuce dakyar, kan shi ya dora a jikin
teburin office din Salim din yana maida
numfashi, yaji dadin shirun da Salim yayi yana
bashi dama ya nemi nutsuwa da kan shi. Bugun
da zuciyar shi takeyi shi dinma in aka auna za'a
iya bukatar yi mishi aiki a cikinta.
"Ina jin kamar ba zan sake saka su a idanuwa na
ba Julde"
Muryar Daada a waccen jinyar da tayi ya dawo
mishi, shirun da ya biyo bayan maganar tata na
biyo shi tun daga wancen lokacin zuwa yanzun
da yake zaune a ofishin Salim. Shiru ya zaba,
Daada bata matsa mishi ba, bata ambaci sunaye
ba, amman yasan me take nufi, bata bukatar ta
ambaci sunan kowa. Ya zabi shiru ne ya kuma
zabi danna tambayoyin ta can kasa tare da duk
Lubna sufyan
Hausabook.com 440
wani abu daya danganci Yelwa da Bukar din.
Bata sake daga mishi zancen ba, shima bai sake
bari ya dawo mishi ba sai yanzun. Saboda ya
zabi ya so kan shi, ya dora bukatar shi akan tata.
Son kan da sai yanzun yake ganin shi
Su duka Yelwa ta
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 16 Chapter of 18