dare, da na kira
kinji muryar shi"
Tun tana yarda harta fara saka kokwanto a cikin
ranta, ta san damuwar da Julde yake karanta a
fuskarta yasa shi hada mata wayar tafi da gidan
ka ta telephone tunda salular ta hannu da ake
yayi tace bata so. Sanyin daya ratsa zuciyar ta
bayan jin muryar Nawfal sai da ya saukar mata
da wata kasala ta ban mamaki.
"Bajjo"
Ta kira kamar ta kasa yarda muryar shi ce take
ji cikin kunnenta kamar yana gabanta. Sai ma da
yayi dariyar nan tashi sai taji idanuwanta sun
cika taf da hawaye, tsoron da take kwana tana
tashi da shi ta nema ta rasa.
Lubna sufyan
Hausabook.com 110
"Ka dinga kirana kullum ina jin lafiyar ka kaji
ko? Shirun nan shine yake daga mun hankali
fiye da rashin dawowar ka"
Ya kuma ji maganarta, kullum karfe tara na dare
agogon Najeriya yake kiranta, wasu ranakun
sukan dauki fiye da mintina talatin suna hira,
wasu ranakun kuma gaisawa kawai sukeyi zaice
mata yana da ayyuka da yawa da zaiyi.
"Wata rana ki rike mun Madina da hira mana
Daada, kar tayi bacci mu gaisa"
Nawfal ya roke ta, sai dai ta amsa shi da to, dan
bata san ta inda zata fara mishi bayanin canjin
da Madina takeyi da duk rana ba, a yan
shekarun yarinyar komai nata da ka'ida takeyi,
in ta dawo daga makaranta karfe shidda zata
sake share gidan ko da kuwa Daada ta share,
tayi sallar Magriba, taci abinci, a tsakanin ne
kafin isha'i zatayi nazarin litattafan ta, ko tayi
aikin gida idan tana da shi, tana idar da sallar
isha'i take kwanciya. Wani kallo duk yanda take
son shi baya shiga tsakaninta da baccin da tasan
tana bukata. Yan kunshi yanzun har sun gane, in
Lubna sufyan
Hausabook.com 111
dai ba alhamis da juma'a ba da yamma, in kazo
ma ba zaka samu ba.
Sai dai ko lokacin hutu, kallo kuwa ran asabar
da lahadi zata zauna tayi da rana haka, karatu
dai dakin Madina cike yake da takardu da
litattafai, shisa lokacin da ta fara wani irin
ciwon idon da bayan kaita asibiti saida suka yi
mata gilashin da gashi nan tana ta fama da shi
Daada tace
"Kallon takarda, ace mutum idon shi ba zai huta
ba, kullum cikin karatu ba dole ido ya lalace ba"
Yanda duk Madina da Julde suka so fahimtar da
ita cewa ba karatu bane ba ya ci tura, sai gajiya
sukayi suka kyale ta. Har yanzun bata daina
mita lokaci zuwa lokaci idan ta ga Madina
manne da littafi, takarda ko ta kosai ce suka siyo
suka cinye sai Madina ta dauka ta karanta taga
meye a ciki. Littafi duk wanda ta rubuta sai
Julde ya siyo mata.
"Hamman ki na gaishe ki, yace in rike ki da hira
har lokacin kiran shi yayi dan ku gaisa"
Lubna sufyan
Hausabook.com 112
Daada ta gwada fadawa Madina da ta saka
hannu tana gyara gilashin daya cinye kusan
rabin fuskarta kan karan hancin ta tana yin
murmushin da baka raba fuskarta da shi sannan
tace
"Hamma baya kira da wuri Daada, kice in yana
so mu gaisa ya kira kafin lokacin bacci na yayi"
Shima da ta gaya mishi abinda Madina ta ce
dariyar yayi yana amsawa da
"Daada komai na a tsare yake, bana son shigar
da wani abu cikin lokacin yin wani abin"
Kai kawai ta girgiza, Nawfal yayi mata nisan da
bata ganin canjin da yau da gobe take yi wa
rayuwar shi, amman iya hakan ta fahimci sun
hadu waje daya tare da Madina, sun dauki wata
akida ta kayyadaje yanda ranakun su zasu
kasance, har suna ganin ba zasu iya canza hakan
dan wani ba. A kauye ta tashi, kauyen da
karatun addini ma sai da ta shigo binni ta neme
shi da kanta, shisa bata shiga cikin irin wannan
rayuwar ta su Madina da tafi karfin fahimtar ta,
Madina ma da take gabanta da yawan abubuwa
Lubna sufyan
Hausabook.com 113
sai dai ta bita da addu'ar neman shiriya ko
samun sauki, balle Nawfal da yake wata duniyar.
Sallamar da akayi ta katse ma Daada dogon
tunanin da take zaune tana yi, sai da ta sauke
numfashi sannan ta amsa tana mikewa jin
kamar karar sauke wani abu mai nauyi, tana
fitowa kuwa Salim ne ya ajiye buhun shinkafa a
tsakar gida
"Karka ajiye anan, ka shigo da shi daga ciki"
A hankali ya daga idanuwan shi yana kallon ta,
idan wani yana wajen zaice kamar a takure
yake, wani ma idan yaga kallon zai dauka shine
karo na farko da ya taba ganin Daada, yana
kallon ta ne da mamakin dalilin da zaisa tayi
mishi magana, kamar ba zai amsa ba yace
"Akwai wasu kayan..."
Cikin muryar shi da take a bude amman yanayin
kalaman sun fito ne cikin sanyi da abinda
mutane izzar da tasa mutane da yawa suke
daukar ya fito tsatson sarauta, ko da Daada tayi
niyyar fadin wani abu Salim bai tsaya ba balle
yaji, juyawa yayi abin shi, tana bin shi da kallo,
Lubna sufyan
Hausabook.com 114
shigar kananun kayane, dogayen kafafuwan shi
basu sa yaji akwai bukatar ya dinga suturta su
ba, wandon da yake jikin shi ruwan madara da
kadan ya wuce gwiwa, sai riga da tayi ma Daada
kama da ta sanyi kalar ja, mai dogon hannun da
yadan tattare yana ja sama, sai hular sanyi daya
tura baya rabin gashin shi a waje, ita kuma kala
daya da wandon shi.
Gashin in da yake a bude, yanzun daya dawo
dauke da kwalaye biyu da alamu suka nuna na
taliya ne, Daada ta kula da a cukurkude gashin
yake, yayi wani irin aski da in ka ganshi cikin
masallaci mamaki zai kamaka na kasancewar
shi musulmi, ko hausa kaji yayi saika juyo ka
kalle shi. Daga yanayin kirar jikin shi, tsayin shi
har shigar shi bata nuni da cewar ba bahaushe
bane shi, bafullatani ne gaba da baya, kuma
mabiyi addinin musulunci. A cikin yaran Julde
duka daga Adee sai Khalid ne suke zuwa wajen
ta akai-akai.
Da dalili ko babu sukan zo harma su kwana,
Salim in ba aiko shi akayi ba, ko kuma motar
Julde ta samu matsala yasa ya kawo shi, da kan
shi bai taba wanko kafa yace yazo ya gaishe da
Lubna sufyan
Hausabook.com 115
ita ba. Idan zuwan yayi ma gaisuwa ce take
hadata da shi, yanda yake magana kamar an
shaqe shi an saka shi dole na daya daga cikin
dalilin da yasa ko tambayar shi ya sauran yan
uwan shi batayi. Tas ya gama shigo da kayan
abincin da suka hada harda doya da mai fari da
na ja, tukunna ya kalli Daada yana furta
"Ina kwana"
Murmushi tayi
"Lafiya kalau babban dan aike, sannu da kokari,
Allah yayi albarka"
Salim ya amsa da
"Kitchen zan shiga da su?"
Maimakon amsa addu'ar da tayi mishi, ya jita, ya
kuma amsa a zuciyar shi, maganar duk da zai
motsa labban shi yayi ta in yana da halin
takaitata zaiyi. Kai Daada ta jinjina mishi tana
komawa cikin dakin dan ta bashi hanyar
wucewa, haka ya dinga daukar kayan yana
kaiwa Kitchen, ya kuma yi mata magana dan ta
nuna mishi inda zai saka mata komai, yana
karasawa yace
Lubna sufyan
Hausabook.com 116
"Gas fa? Daddy yace in dauka a sake filling"
Kofar da zata hadaka da bayan kitchen din inda
cylinder din gas din take Daada ta nuna mishi ya
wuce ya kwanto, daman ya kare, ko da safen a
risho Madina ta soya musu dankali, basa rabuwa
da kalanzir a rishon su tunda gas idan ya tashi
karewa babu ruwan shi da ka cika tukunya da
shinkafar da ta dauko dahuwa.
"Da ka taimaka in kira Madina sai ka kaimun ita
kasuwa tayo mana cefane...siyayyar da dan
dama kar in saka yawo a kasuwa"
Numfashin Salim ya fitar yana dan daga mata
kai a hankali, in ba ita ba, babu mai saka shi
wannan aikin. Shi Madinar ma rabon daya saka
ta a idon shi harya manta, idan zai fadi gaskiya
ya ma manta da ita ne gabaki daya sai yanzun da
Daada ta ambace ta, ba zai manta surutun
yarinyar da yake hau mishi kai tun tana yar
mitsitsiyarta ba. Balle kuma yanzun da yasan ta
fara jin tashen yan matanci, yasan waye shi, tun
kafin mata su kara nuna mishi shidin wani ne
yasan ko da bashi da kudi yana da kyan da suke
bi kamar zasu lashe shi. Yanzun ko matan da
Lubna sufyan
Hausabook.com 117
yake bi yana da mugun zabe, kuma kashe din shi
na farko shine
"Bana son surutu, komai zai mun dai-dai idan
zamuyi abinda zamuyi mu gama banji muryar ki
ba..."
Manyan mata ma, riqaqqu suna rikicewa a kan
shi balle yan yaran nan da yake gani yan aji daya
a makaranta suna bin shi kullum da
"Yayaa Salim dan Allah zaka duba mun
assignment dina"
Har rasa yanda akayi ya zama Yayaa a wajen su
yake yi, yakan karba a wajen ya nemi bango ya
dora idan na abin rubutawa ne ya rubuta musu,
su kadai kuma yake tsayawa har ya danyi wa
bayani wasu lokuttan, saboda 'yan yara ne,
saboda yana da kanwa shima, zai so in ta nemi
wani ya taimaka mata da abinda ya shige mata
ta harkar karatu ya taimaka mata din. Balle
kuma Madina da ba zai iya kiyasta shekarunta a
yanzun ba, ko yace zai iya hasaso matakin
karatun ta.
In da yake tsaye anan Daada ta dawo ta same shi
Lubna sufyan
Hausabook.com 118
"Ka zo ka zauna kafin ta fito"
Kai ya girgiza saboda baya son cire takalmin da
yake kafar shi, in dai zai karasa cikin falon ya
zauna dole saiya cire, ba zai taka mata kafet din
da yake shimfide kusan cikin dakin da takalma
ba, ko da zai shiga kitchen ta gefe-gefe wajen
tayal ya dinga bi. Agogon da yake daure a
tsintsiyar hannun shi ya dan daga hannun yana
kalla. A cikin kan shi yake hango wasu mintina
sha biyar zuwa ashirin kafin Madina ta fito, ya
tabbata zata tsaya iyayin kwalliyar nan da yake
saka shi kwankwasa dakin Adee ya watsa mata
zagi in dai tare zasu fita, baya son jira.
"Banga biro bane ba fa, da zan rubuta abubuwan
kar in manta, amman na samu fensiri"
Muryar Madina ta fara dukan kunnuwan shi
kafin ya sauke idanuwan shi akan ta, wani dan
karamin sauti ya kwace daga makoshin shi da
yafi alaka da tsantsar mamaki. Yanda ya ganta
yanzun ya goge duk wani hoton yarintarta da
yake da shi cikin kan shi balle ya nemo ya gwada
ya tabbatar da wannan yar mitsitsiyar halittar
ta gaban shi itace Madinar da ya sani. Zai dawo
Lubna sufyan
Hausabook.com 119
da batun kankantar ta da ya gani, shigar jikin ta,
shigar ta ita ce abinda yasa sautin kwace mishi.
Wando ne jeans da ta lankwashe daga kasan
kusan ninki biyu kamar yayi mata yawa, sai
takalmi kafa ciki, rigar da take jikinta yana da
tabbacin ko shi ya saka zai iya yawo a ciki
saboda girmanta, hijabin da ta saka da alamu
yar karama ce fara, sai ta dora rigar a sama ta
yanda kanta da wuyanta kawai hijabin ta rufe.
Bai san me zai kira rigar jikin Madina da ita ba,
kaurinta yayi yawan da bai kamata ace ta sakata
a yanayin zafin da akeyi ba, ga dogon hannaye
rigar take da shi da ta dan ja baya kamar yanda
yayi. Rabon da yaga kalar yellow harya manta,
sai yau da ya ganta a riga da takalman da suke
kafar Madina. Ji yayi kalar har shigar mishi
idanuwa takeyi, gilashin da yake idonta ya kai
kuncinta saboda girman shi. Daga inda yake
yana hango maikon da fuskar Madina takeyi ga
kurajen da suke fuskarta da ake kira da
pimples, ita din gabaki dayanta kamar an cirota
daga wani shirin fim din kasar ketare aka direta
a inda take yanzun.
Lubna sufyan
Hausabook.com 120
Murmushine ya bayyana akan fuskar shi da
yake jin girman shi na kara fadada da duk
dakika, rabon da wani abu ya saka shi nishadi
irin yanda ganin Madina ya samar mishi harya
manta, ko matan da yake bi da ya ture su daga
jikin shi yake jin wani duhu ya rufe shi ruf,
nishadin daya samu ya dishe kamar anyi ruwa
an dauke. Dariya ce mai sauti ta kubce mishi da
Madina ta kalle shi tana yin murmushin ta daya
bayyana duka hakoranta, sannan ta dan daga
hannunta cikin alamar gaisuwa tana son tuna in
da ta san shi, kafin cikin mamaki ta ja gilashinta
kamar zata cire shi tana sake gyara mishi zama
"Hamma Salim... Hamma Salim ne ko?"
Ta karasa maganar da alamar tambaya tana
kallon Daada da ta jinjina mata kai, itama
murmushin takeyi. In dai akan zabin suttura ne
na Madina ta hakura. Ba don ita ta wanketa tun
jariranta ka ba, haduwa sukayi a hanya zatayi
zaton ko mata-maza ce, sai jinsin namijin yayi
rinjaye a kanta, ba kwalliya takeyi ba, mai ma
kafafuwan ta kawai take shafawa da Daada zata
rantse ko tambayar Madina akayi abinda tafi so
a jikinta to kafafuwan zata zaba, fuska kuwa in
Lubna sufyan
Hausabook.com 121
ba muku-mukun sanyi ya shigo ba da sauran
jikinta bata damu da shafa musu mai ba,takance
fuskarta da kanta take maiko ko bata shafa mai
ba.
Yanda bata kaunar hada hanya da duk wani abu
daya danganci kyale-kyalen mata yana ba Daada
tsoro. Kafafuwan dai sune matsalarta, kullum
cikin safa suke, takan ce
"Daada bakya jin iska na shigar miki kafa?"
Ko
"Daada haka zaki fita baki saka safa ba? Kar
wani ya taka miki kafa"
Haihuwa ta fara bambanta Madina da sauran
mata, yanzun kuma kaf dabi'unta. Bata son
kazanta, kamshine abu daya da tafi so a
rayuwarta, ko dakinta ka shiga wani kamshi mai
sanyi ne zai fara dukan hancin ka. Sai dai tana
cikin mutanen da basu damu da su mayar da
duk wani abu da zasu dauko a mazaunin shi ba,
kayane akan gadon ta a cike, Daada tayi fadan
harta gaji. Banda litattafan ta, babu wani abu da
yake a kammale cikin dakin, ga wajen ajiye
Lubna sufyan
Hausabook.com 122
takalmanta, Madina wani kwali ta samu tana
zuba su a ciki, kayan wanki ma kwalin ne ta
samu, har kwando Daada ta siyo mata, a store ta
tsinto ko sati daya ba'ayi ba tsakani
"Kwandon ne kika watsar Madina? Asarar kudi
nayi kenan?"
Ta tambaya
"Wallahi duk ya cika mun dakine fa Daada, ba
watsarwa nayi ba, ajiyewa nayi idan na sake
shirya dakin sai in masa waje"
Kyaleta kawai Daada tayi, tasan babu wajen da
zatayi mishi, duk shirgin da yake dakin ta,
kwandon ne bata so a ciki, tafi gane ta zuba su
cikin kwali, irin Madina kam, Daada bata jin ko
an tona a fadin Kano zasu kai su biyu. Da wahala
ma idan ba ita kadai bace ba, kullum cikin
neman wani abu nata da bata san in da ta ajiye
ba take. Safa kuwa ko makaranta zataje da
wahala kaga iri daya a kafarta, hankalinta a
kwance zata hada bakar safa da ja taci gaba da
hidimarta, idan anyi magana zata ce
Lubna sufyan
Hausabook.com 123
"Banga yan uwan bafa, kuma a cikin wata jaka
na saka"
Tunda dai taji kafarta a rufe shikenan, shisa
duka fata da addu'ar ta akan Madina take
zagaye da Nawfal. Burin ta mai girma ne, zata
kirga lokuttan da ta taba ganin fara'a a fuskar
Salim, amman yau ba murmushi bane kawai, har
dariya yayi. Ko ba shiga da yanayin Madina ba,
ita din takan saka nishadi a tare da duk wanda
zata ci karo da shi. Ko bata sanka ba kuka hada
ido zatayi maka murmushinta da zai wahala ka
kasa mayar mata da shi.
"Muje kafin rana ta bude da yawa"
Madina ta ce tana wucewa da kara fadin
"Daada sai mun dawo"
Bin bayanta Salim yayi yana mamakin yanda
take iya sauri da gajerun kafafuwanta, ko
"Allah ya tsare ya dawo da ku lafiya"
Da Daada ta furta bataji ba balle ta amsa, a
bakin mota ya sameta a tsaye. Da kadan kanta
ya wuce kugun shi, yar dariya ya sake tsintar
Lubna sufyan
Hausabook.com 124
kan shi dayi yana zagayawa ya sa mukulli ya
bude murfin motar ya shiga. Hannu ya mika ya
bude mata itama tana shiga ta zauna hadi da jan
murfin motar.
"Wacce kasuwar zamu je?"
Salim ya tambaya yana yin baya da motar, dan
jim Madina tayi sannan ta amsa shi
"Kasuwar cefane...in da ake saida su nama da
kifi"
Kai Salim ya jinjina, ya kan kai Saratu lokaci
zuwa lokaci.
"Hamma Khalid yace likita zaka zama ko?"
Kan dai ya sake daga mata, haka kawai saiya
tsinci kan shi da son tambayarta
"Ajin ki nawa? Me kike son zama ke?"
Kallon shi tayi yana ganin girman gilashinta ta
gefen idon shi
"Aji hudu uku zan shiga hudu yanzun..."
Kamar tasan gilashin yake tunani a ranshi ta kai
hannu tana gyara zaman shi, ya kula takan yi
Lubna sufyan
Hausabook.com 125
hakan ne saboda ta saba, ya zamar mata kamar
habit, bata mintina bata kai hannu fuskarta ta
gyara zaman gilashin kamar wanda zai fado ba.
"Ina son zama yar jarida"
Kai Salim ya jinjina
"Glasses dinki..."
Ya soma kafin ya karasa ta amsa da
"Blurred vision...bana ganin abubuwa da kyau
sai da shi"
Dan kallonta Salim yayi yana maida hankalin shi
kan tukin da yakeyi. Baisan me yasa yake son
tambayar ta abubuwa haka ba, rayuwar mutane
ba abinda ya shafe shi bace ba. Tauna bakin shi
yayi ta ciki don ya gujema wata tambayar kafin
ta sake kubce mishi. Shirun ne yayi ma Madina
yawa, saboda ita mutum ce da Allah ya halitta da
tambaya da kuma son hira, ko bakunta bata iya
ba, ko mun girmanka tasan kalar hirar da zatayi
da kai da ba zaisa zaman ku ya gundure ka ba.
Lubna sufyan
Hausabook.com 126
"Baka jin kida kai a motar ka? Hamma Khalid da
kida a motar shi, duk idan yazo zamu je waje
yana kunna mana"
Cikin sanyin murya Salim ya amsa da
"Bana son hayaniya"
Bayajin ya taba kunna ko da radio din cikin
motar ne tunda Daddy ya bashi ita. Ko TV zai
kalla da yawan lokutta sautin gabaki daya a
kashe yake, sai dai yayita kallon hotunan
"Ko kai ma kana da matsalar kunne ne kamar
yanda nake da ta idanu?"
Murmushi Salim yayi
"Nace bana son hayaniya kina ta mun surutu"
Dariya Madina tayi
"Ni bana so idan ba karatu nakeyi ba inji nayi
shiru...baya mun dadi"
Bata kuwa yi shirun ba har suka karasa kasuwa,
sai dai a karo na farko a rayuwar shi da surutu
bai hau mishi kai ba, asalima ko bai amsa ta ba
nishadi take saka shi. Bai fita daga mota ba,
Lubna sufyan
Hausabook.com 127
anan ya jirata, da yake ta iya wahalar da kanta
duk abinda ta siyo sai ta dawo ta kawo sannan
ta sake komawa. Da ta siyo kifi harda lemon
roba na coke ta hado mishi
"Kana ta zama ko? Yanzun zan gama, saura abu
guda biyu"
Ta fadi tana mika mishi lemon
"Ka sha wannan, ko kana jin yunwa in samo
maka wani abin?"
Yanda take mishi maganar sai ka rantse yaron
goye ne ta bari a mota, dariya ta bashi ba kadan
ba
"Wannan ma ya isa, nagode"
Ya fadi bayan ya karba. Ya kuma ji dadin lemon,
da ta gama zasu koma hira ta dinga mishi tana
bashi labarin yanda sukayi da inda tayi siyayyar
ta.
"Me yasa baka zuwa? Ka dinga zuwa dan
Allah...kaga ni ban sanka ba sosai"
Madina tayi maganar cike da roko tana kallon
shi ta cikin gilashin ta, sai ya tsinci kan shi da
Lubna sufyan
Hausabook.com 128
daga mata kai, murmushin da tayi na saka shi
jin wani bakon yanayi
"Dan Allah da gaske? Ko zaka dawo anjima?
Miyar kifi zanyi, da dadi wallahi, Daada tace na
iya abinci, ko Hamma Khalid ma yana so inyi
idan ya zo"
Kai ya girgiza mata
"Makaranta zanje Madina... Zan dawo ba yau ba
dai"
Cike da fahimta tace
"To shikenan, Allah ya baka sa'a, Allah ya tsare
ka ya taimake ka"
Addu'ar ta fito mata a saukake
"Amin"
Ya furta yana tsintar kan shi da dorawa da
"Nagode"
Kai ta jinjina tana mishi murmushi, tsaye tayi a
kofar gidan kamar tana jiran ta ga tafiyar shi
tukunna, shisa yaja motar, ta mudubin shi yake
Lubna sufyan
Hausabook.com 129
hango tana daga mishi hannuwan ta duka biyun,
murmushi yayi, a hankali ya furta
"Madina..."
Batare da ya san girman rawar da
madaukakiyar sunan zata taka a rayuwar shi ba.
Sake gyara zaman shi yayi a cikin mota a karo
na ba adadi, bacci yake ji ba dan kadan ba,
saboda bai samu wadatacce ba da dare. Da ace
babu hayaniya lafiya kalau zaiyi baccin shi.
Tunda motar a kashe take dole ya sauke gilashin
kadan dan shige da ficen iska. Amman hakan sai
kwaso mishi surutan da baya bukata zuwa
kunnuwan shi yakeyi. Harda yara da a lokacin
ya kamata ace suna islamiyya amman sun cika
unguwa da hayaniya sun hana kowa sakat. Inda
unguwar su Daada yake yana da tabbacin da
anyi gangami an tashe su ko da gidan nasu ne
sai an sa sun siyar sun tashi.
Yaran da zai jera ya zane ma jiki ya kirga sun fi
goma sha daya cikin kan shi daga parking din
motar shi zuwa yanzun. Baya son hayaniya, baya
Lubna sufyan
Hausabook.com 130
son surutu gabaki daya, iya zaman da yayi ya
gama tsara kalar unguwar da yake son siyan
gida in har ya samu wadatar hakan. Kwankwasa
gilashin motar yaji anyi ta gefen da yake, bude
idanuwan shi yayi yana yatsina fuska saboda
kamar cikin kwakwalwar shi aka kwankwasa
haka yaji. Juyawa yayi yana sauke idanuwan shi
kan fuskar Madina da take mai dariya da duka
hakoran ta a bude
"Hamma..."
Ta fadi cike da fara'a tana saka shi kai hannu ya
kara sauke gilashin motar kasa
"Yaushe ka zo?"
Ta tambaya tana dorawa da
"Me yasa baka shiga cikin gida ba?"
Ya san kafin ya amsa tambayoyin biyu in dai
Madina ce ta kara jero mishi wasu, shisa yayi
shiru yana jiran ta gama. A cikin watanni biyu
baya jin akwai wata halayya ta Madina da bai
sani ba, don tana cikin mutanen nan da ake ma
rayuwar su lakabi da budadden littafi, ba su da
wahalar fahimta. Haka kawai idan gari ya waye
Lubna sufyan
Hausabook.com 131
a tsayin rana bai ganta ba bayajin dadi, tunda ya
san makarantar da take wasu lokuttan yakan
dai-daici lokacin tashin su sai yaje. Ba zai manta
ranar farko daya fara zuwa ba, yana tsaye ya
jingina da motar shi ya hango ta.
Duk yaran da suka fito zaka gansu su biyu har
fiye da hakan ma, Madina ita kadai ya hango, ba
gilashin fuskarta yasa ya fara gane ta ba,
uniform din jikinta da yake tunanin zai wahala
bai iya shigar da jikin shi cikin kafar wandonta
daya ba, bai taba ganin wando irin na jikin
Madina ba, har rigarta tasha bamban da ta
sauran, hijabinta ce kawai bata ma kai ta wasu
tsayi ba, idan iska me karfi akeyi zata iya yawo a
samanta saboda girman kayan da suke jikinta,
tana hango shi ta washe mishi baki tana kara
saurin tafiyar ta, sanda ta karaso kasa rike
dariyar shi yayi
"Madina..."
Ya iya kira, bata san dalilin dariyar shi ba ta fara
taya shi
"Wanne irin kaya ne wannan?"
Lubna sufyan
Hausabook.com 132
Dan juyawa tayi har lokacin dariya takeyi
"Bana so inji kaya sun matseni"
Kallon ta Salim yakeyi, komai nata daban yake,
ba zai kirga yawan matan da ya sani ba, amman
ko mai shigen muryar Madina bai taba cin karo
da ita ba. Bambanci da take da shi da sauran
mutane ne abinda yaja shi. Ko yanzun da take
mishi murmushi da dukkan hakoranta a waje
bambanci yake sake gani
"Yau baki dawo da wuri ba..."
Ya soma a gajiye, kafin ya karasa ta katse shi
"A'a mun tashi fa, ai kullum-kullum karfe biyar
da rabi ake tashin mu, akwai wa'anda suke zuwa
daga unguwa mai nisa, ni ce na tsaya na siya
awara, akwai layi kuma. Ban san ka zo ba da na
taho"
Numfashi Salim ya sauke yana nuna mata alama
da hannun shi da ta zagaya ta shigo motar. Sai
da ya dakuna fuska dan karta fadi a gudun da
tayi tana bude murfin motar, ledar awarar da
sai lokacin ya ganta ta ajiye akan kujerar motar
tana fadin
Lubna sufyan
Hausabook.com 133
"Bari in kai jakata ciki in fada ma Daada na
dawo kar ta dauka na tsaya wani waje"
Bata ma jira amsar shi ba, ko murfin motar bata
rufe mishi ba ta juya. Numfashin dai ya sake
saukewa da murmushi a fuskar shi. Hannun ta
da ta dauke ledar awarar ya fara gani dan yanda
ta shigo motar kamar an jehota sai da ya sake
yin dariya, duk idan yana tare da Madina sai ya
dinga jin tamkar yana biyan bashin duka
lokuttan daya kamata ace wani abu ya saka shi
nishadi bai ji nishadin ba, da wahala kaga fuskar
shi babu murmushi duk idan suna tare, ko ita
din ya gani kafin ta bude bakinta ta ce wani abu
shigar jikinta ta bashi dariya.
"Ga ruwa na dauko maka"
Ta fadi tana sauke numfashi hadi da mika mishi
ledar ruwan da ya karba ba dan yana jin kishi
ba, ya siyi ruwa har roba biyu a hanya, tsintar
kan shi yayi da fasa ledar ya dan sha ruwan yana
rike ledar a hannun shi
"Daada tace tana gaishe ka"
Lubna sufyan
Hausabook.com 134
Kai ya jinjina mata yana kallo tana bude ledar
awarar da tayi mishi kyau a ido, harda albasa da
kabeji yankakku a ciki sai yaji kulle a farar leda
ta bude tana ajiyewa daga gefe a cikin ledar
awarar.
"Ka iya cin awara? Ka san awara?"
Yar dariya yayi mai sauti
"Lallai yarinyar nan..."
Cewar Salim yana sata yin dariya
"Nasan unguwar ku ta yan gayu ce, ba masu sai
da awara shisa"
Tayi maganar da dukkan gaskiyar ta, tana
daukar awara daya ta saka cikin bakinta.
"Adee tana mana a gida ai"
Tauna awararta Madina takeyi tana mika mishi
ledar da ya saka yatsu ya dauki guda daya ya
dangwala yajin ya saka a bakin shi
"Hamma Nawfal baya son yaji shi"
Maganar ta kwace mata batare da tasan dalilin
da yasa tayi ba, numfashi Salim ya sauke, Nawfal
Lubna sufyan
Hausabook.com 135
din da ta kira na saka shi jin wani yanayi da bai
da fassarar shi. Wani irin shiru ne ya ratsa cikin
motar saboda. Ita kanta Madina ji takeyi kamar
anyi wasu shekaru ne masu yawan gaske da
tafiyar Nawfal din, ba zata ce tunanin shi baya
fado mata ba, ko agogon shi da yake ajiye akan
gadon ta yana tuna mata shi, da tana sakawa, sai
ta cire ta ajiye, ko karatu takeyi wani lokacin
zaka ganshi a hannunta tana ta jujjuya shi. Idan
zatayi bacci ma lokutta da yawa agogon na
hannunta ko da ba tunanin Nawfal takeyi ba ta
riga da ta saba dauka.
Daina saka agogon ya zama hanyar ta guda daya
ta nuna fushin ta da karya alkawarin shi da
Nawfal yayi na cewar shekara daya kawai zaiyi
ya dawo. Amman yanzun kam anya akwai
wannan fushin?
"Kullum kike siyan awarar?"
Salim ya tambaya saboda yau ne karo na farko
da shiru yayi mishi yawa, baisan ko dan in dai
tana waje ya saba da hayaniyar ta bane ba
"Um um fa, ni kadai nake ci. Daada wai mai yayi
yawa yana saka mata
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 5 Chapter of 18