tsalla ke
Ba shi ka dai ta bari ba
Har da Daada.
A karo na farko a rayuwar shi da ya rike jaka a
hannun shi batare da yasan abinda zai zuba a
ciki ba
"Kana da passport Bajjo, Daada ma nata baiyi
expire ba, da kai ya kamata ku tafi, zan biyo ku
daga baya dan kar a bata lokaci"
Abinda Julde yace mishi kenan, yana kallon
gamsuwar da su Khalid sukayi da maganar
Julden a cikin idanuwan su tun kafin ma su
furta. Shisa yayi shiru, yanda duk ya so ya
girgiza wani ya fada mishi cewa ba yajin zai iya
tafiya shi kadai, bayajin yana da karfin halin da
Lubna sufyan
Hausabook.com 441
zai kula da Daada batare da zuciyar shi ta
rarrabu kashi-kashi a cikin kirjin shi ba, sai ya
kasa. Kai kawai ya daga musu cikin yarda shima.
Hadiye tsoron da fargaba yayi har sai da ya
koma gida a ranar, ya saka mukulli yana kulle
dakin bayan ya shiga sannan ya budema
Murjanatu zuciyar shi yana jin rashin ta fiye da
kowanne lokaci
"Bana jin zan iya Jaan, Daada ce, yau dana ganta
a kwance babu abinda naji ina so inyi sai in
zauna a gefen ta inyi kuka har sai ta bude
idanuwanta tace mun komai zaiyi dai-dai... Ban
taba kula da ita ba, ita ta saba kulawa da ni, taya
zan fara yanzun?"
Ya karasa yana jan wani irin numfashi hadi da
fitar da shi cike da nauyin da yake ji a kirjin shi,
saboda yanda yayi maganar batare daya ba
kanshi damar numfasawa ba
"Waya yace kai kadai zaka kula da ita? Ba India
kace ba? Zaka sameni a filin jirgi ina jiran ku
Gidado...idan na kula da kai zaka iya kula da ita?
Zan so ince maka zan kula da ku duka biyun,
amman Daada ce, zaka so kayi komai daya
Lubna sufyan
Hausabook.com 442
dangance ta da kan ka... Na san hakan, kaima in
ka nutsu ka duba zuciyar ka zaka ga hakane..."
Numfashin dai ya sake ja yana fitarwa
"Babu abinda ba zaka iya ba in dai akan Daada
ne, in baka yarda da kan ka ba, ka yarda dani,
kasan ba zan maka karya ba, duk da ina son ka"
Baisan murmushi ya kwace mishi da kalamanta
na karshe ba sai da yaji alamar shi har a zuciyar
shi da nauyinta bai ragu ba, amman numfashin
da yaja ya kai mishi har ciki
"Kinsan bangane komai da kikace sosai
ba...komai ya kare ne da yanda kika ce kina so
na"
Dariyar da tayi sai da ta kara fadada murmushin
shi
"Ina son ka... Ina son ka Gidado"
Kai ya jinjina, ya sani, saboda yanda bata gajiya
da nuna mishi duk rana haka bata gajiya da fada
mishi tana son shi. Wasu ranakun in ta fada sai
yaita kallon ta, musamman labbanta da yanda
kalaman suke fitowa kamar basu da wani nauyi
Lubna sufyan
Hausabook.com 443
a wajen ta. Da shi bahaushe ne, daya boye a
bayan yaren yace shisa fada mata yana son ta a
duk rana yake mishi wahala. To shi bafullatani
ne, babu kunya a tsakanin su, sun wuce wannan
matakin tuntuni, bashi da abinda zaiyi amfani
da shi a matsayin kariya.
Amman kalmomin suna masa nauyin furtawa,
zai iya kirga lokuttan daya fada mata su, yana
dai kokarin ganin a rana ya zama dalilin da
zatayi dariya ko sau dayane, yana kuma kokarin
kyautata mata dai-dai iyawar shi, fada mata
yana son ta na mishi wahala, amman nuna mata
abune mai sauki saboda ta cancanci fiye da
hakan a wajen shi, ta bashi abubuwan da zai
dauki lokaci idan an bashi dama yana bayanin
su.
"Wai har yanzun kana nan tsaye Bajjo?"
Khalid da ya turo kofar yana katse ma Nawfal
tunanin shi ya furta
"Na rasa abinda zan dauka, Murjanatu ta
shiryamun jakata da zan taho"
Gira daya Khalid ya daga
Lubna sufyan
Hausabook.com 444
"Nasan kana da aure Bajjo, ban manta kana da
mata ba"
Dariya Nawfal yayi
"Yi hakuri ba haka nake nufi ba"
Labban shi Khalid ya matse waje daya yana
jinjina kai, cikin yanayin dake fassara "Ka dai
cigaba Allah yana kallon ka". Dariya ya sake na
Nawfal
"Da gaske na rasa abinda zan dauka"
Numfashi Khalid ya sauke
"Me yasa kake fadamun? Ka kira Murjanatu
mana sai ta fada maka abinda ta shiryo maka
sanda zaka taho ka sake daukar su"
Kai Nawfal ya jinjina cikin yarda da shawarar
Khalid din yana nufar inda wayar shi take ya
dauko
"Me zakai?"
Cewar Khalid yana bude baki cike da mamaki
"Kiran Murjanatu mana?"
Lubna sufyan
Hausabook.com 445
Dafe kirji Khalid yayi yana samun waje kan
gadon ya zauna
"Me ka dafe? In zuciyar ka ce ba'a bangaren
dama take ba, saika dan matsar da hannun ka
tsakiya..."
Wani irin kallo Khalid yake ma Nawfal din daya
cigaba da fadin
"Daga bangaren haggu kadan"
Ta baki Khalid ya furzar da numfashi yana
sauke hannun shi
"Baka ga kallon da nake maka ba ko? Ba zakayi
shiru ba"
Dariya Nawfal yake yi
"Da gaske, wannan ai son kunyata Hamma Salim
ne, ace baka san inda zuciyar ka ta ke..."
Robar ruwan da Khalid din ya dauka na sa
sauran kalaman Nawfal din makale mishi tare
da dariyar da yayi niyyar yi
"I dare you Nawfal Bukar..."
Khalid ya fadi muryar shi babu alamar wasa
Lubna sufyan
Hausabook.com 446
"In kira Murjanatun ko..."
Kallon "Magana kake har yanzun" da Khalid ya
watsa mishi yasa shi daga hannun shi cikin
saranda yana mayar da wayar ya ajiye. A duniya
dai yasan in ta bangaren samun yan uwa ne
Allah ya gama masa komai, ko da ace dama aka
bashi zai wahala ya zabo irin su Khalid. Shisa
yake kara godema Allah da kyautar su da Ya yi
masa a cikin rayuwar shi. A cikin mintina kadan
Khalid kan saka shi yaji yanda zai iya jure duk
wani abu da zai faru da shi a cikin kowacce rana.
Numfashi da bai san yana rike da shi ba ya
sauke. Kananan abubuwa ya fara tattarawa
kamar su brush da cajar waya da duk wani abu
da yake tunanin zai bukata.
"Ba zance maka Daada zata zauna tare da mu
har karshen rayuwar mu ba Bajjo, amman
komai zai faru Allah ba zai dora mana abinda ba
zamu iya dauka ba, daga karshe komai zaiyi daidai... In shaa Allah"
Khalid ya fadi muryar shi na fitowa da wani
sanyi da yasa nauyin da Nawfal yake ji a kirjin
shi karuwa. Baice komai ba, kayan shi ya cigaba
Lubna sufyan
Hausabook.com 447
da hadawa, ko ya so ya fadi wani abu bai san me
zaice ba
"Hamma yaje ya dauko su"
Khalid ya fada dan ya rage musu nauyin shirun
da ya lullube su gabaki daya, kai kawai Nawfal
ya jinjina batare da yace komai ba, mikewa
Khalid yayi tare da fadin
"Matar ka kake son kira, na bar maka dakin
Bajjo"
Murmushi Nawfal yayi, ba dan zai kira
Murjanatu bane ya fita, abinda ya zo ya fada
mishi ne ya gama fada shisa ya bashi waje yayi
tunanin duk da yake bukata
"Nagode Hamma..."
Ya furta a hankali duk da Khalid din ya rigada ya
fita daga dakin. Kayan shi ya cigaba da hadawa
zuciyar shi da kan shi cunkushe da abubuwa
mabanbanta.
*
Da yawa kance lokaci sakarai ne, idan ya wuce
baya dawowa. Ta kuma ga hakan a al'amura
Lubna sufyan
Hausabook.com 448
daban-daban. Ta ga sauri da rashin saurin
lokaci musamman idan tana jiran wani abu.
Kwanaki bakwai dai basu taba zuwa sun wuce
mata haka batare da ta rike wani abu guda daya
mai muhimmanci da tayi a cikin su ba. Tayi
kuka har sai da ta fara tunanin anya ba duk rana
ake halitta ma bawa sababbin hawaye ba? In ba
haka bane ba tasan ta inda take samun hawayen
fitarwa bayan tarin wanda ta zubda ba.
Ta sha jin labarin kadaici, har ma take tunanin
idan ta runtsa idanuwan ta a wasu ranakun
takan ji shi, takan ji kewar iyayen da ko fuskar
su bata sani ba. Ashe wannan ba kadaici bane
ba, yaudara ce da zuciyar ta take yi mata, asalin
kadaici na cikin ranar da Khalid ya maida ta
gida dan ta dauko kayanta. Yanda ta shiga cikin
gidan tana tunanin ta inda zata fara inda ace ta
rasa Daada, lokacin ne ta duba tsakar gidan da
yayi mata fadi kamar duka duniyar ta ce ta
tattaru a waje daya, ta kuma ganta ita kadai a
tsaye. Ranar ne ta fara sanin menene kadaici,
yanayi ne da yayi matukar firgitata, ranar kuma
ta hango maraicin da bata fatan ya kusanto inda
take.
Lubna sufyan
Hausabook.com 449
Tun jiya aka sallame su, tunda daman sun kara
barin Daada ne dan a tabbatar ta samu saukin
da zata iya zaman jirgin tunda an riga an gama
kammala duk shirye-shiryen da za'ayi da ya
danganci tafiyar ta su. Ita dai ce take ta hada
kayanta tunda ance gidan Julde zata zauna har
su Daadar suje su dawo, ta so ta tambaya me
yasa ba za'a tafi da ita ba, me yasa za'a barta,
waye zai kula da Daada bayan bata tunanin
akwai wanda yasan abinda Daadar take so da
wanda bata so fiye da ita.
Amman tunda take bata taba ganin damuwa
karara a fuskar Julde ba irin wannan karin. Yau
ma da yazo gidan idanuwan shi duk sun
kumbura kamar wanda yayi kuka. Maganar
shima a shake take fitowa, shisa ta rasa kwarin
gwiwar da zata tsare shi da wasu tambayoyi. In
da zata iya daukar dakinta kacokan din shi da
haka zatayi, saboda komai da yake ciki bukatar
shi takeyi. Bata taba kwana wani waje ba bayan
asibiti tare da Daada tunda take.
"Kwana nawa zakuyi Hamma?"
Lubna sufyan
Hausabook.com 450
Tayi ma Nawfal tambayar da ta kasa yiwa Julde,
amman kafadu ya daga mata cike da rashin sani
kafin ya amsa da
"Ba zance ga exact kwanakin ba Madina...zan
fada miki da na san kwana nawa zamuyi"
Kai kawai ta iya jinjina mishi, tana ture tunanin
can kasan zuciyarta saboda bata son hasaso
kwanakin da zatayi batare da Daada ba. Ba zata
taba daukar duk abinda take da bukata ba, ta
sani. Shisa ta rufe jakar kawai tana daukarta ta
fito da ita falo ta ajiye. Dakin Daada ta nufa ta
sameta a zaune in da tayi sallar la'asar,
karasawa tayi ta zauna a gefenta tana matsawa
sosai yanda zata iya jingina da jikin Daadar, bata
da lafiya, amman tana bukatar hakan ko na yan
mintina ne ko zuciyar ta zatayi mata sanyi.
"Allah ya baki lafiya Daada Am... Allah ya kaiku
lafiya ya dawo da ku lafiya... Zanyi kewar ki"
Madina ta karasa maganar muryarta na fitowa a
karye, hannu takai ta dan daga gilashinta tana
sa yatsa ta goge hawayen da take jin ya taru a
gefen idanuwan ta. Numfashi Daada ta sauke,
akwai ciwo na daban da zuciyarta take fama da
Lubna sufyan
Hausabook.com 451
shi da yafi karfin ganin duk wani likita a fadin
duniya.
"Kina da tambayoyi Madina, na san kina da
tambayoyi masu yawa... Nagode da yanda baki
taba tsare ni da in fada miki ba"
Sake shigewa jikin ta Madina tayi tana jin zuciya
ta na kara karyewa
"Dan Allah kibar maganar nan Daada... Ke dai
Allah ya baki lafiya, in akwai abinda ya kamata
in sani ai ba saina tambaya ba na san zaki
fadamun"
Cewar Madina, tana jin gaskiyar kalaman har
ruhin ta. Koma menene bashi da muhimmancin
lafiyar Daada a wajen ta. A yanzun ma gabaki
daya babu wani abu da take so sama da ganin
Daada ta dawo lafiya, an duba ance babu sauran
abinda yake damun ta. Murmushi Daada tayi,
murmushin da ya fito daga wani tsagi na zuciyar
ta da har ya daina bugawa tare da yan uwan shi
ba zai daina godema Allah da kyautar su Madina
ba, akan su ta kara yarda da yanda Allah yake
fitar da mai kyau a cikin mummuna.
Lubna sufyan
Hausabook.com 452
Sallamar da suka ji na sa Madina mikewa, a daki
ta baro wayar ta, tasan da zai wahala Salim ya
shigo gidan. Zai kira ta ne yace mata yana kofar
gida, tana fitowa falon kuwa ta ganshi a tsaye,
kallon shi tayi tana ganin yanda yafi kofar tsayi.
Salim dogo ne, irin dogayen da ko a cikin masu
tsayi zaka duba da yawa baka sami kalar shi ba
"Hamma..."
Ta furta yana sauke mata numfashin da yake
rike da shi a matsayin amsa kiran sunan shi da
tayi, kallon ta yakeyi da gajiya kwance akan
fuskar shi, kasan idanuwan shi ya danyi duhun
da in baka san shi ba zaka dauka haka suke.
Madina ta san rashin wadataccen bacci ne
"Ina ta kiran ki..."
Salim yayi maganar yana daga mata karamar
wayar shi da yake rike da ita
"Nabar wayar a daki, amman ga jakunkunan mu
nan, na hada komai, bari ince ma Daada ta fito
sai mu tafi"
Kai Salim ya dan daga mata yana shiga cikin
dakin sosai ya dauki jakunkunan nasu kamar
Lubna sufyan
Hausabook.com 453
basu da wani nauyi ya fice daga dakin. Ita kuma
ta koma tana fada ma Daada ta fito su tafi. Sai da
ta shiga dakin ta ta dauko wayarta sannan ta
fito, tana kallon yanda Daada take daga kafarta
tana saukewa dakyar, amman ba zata yarda ka
kamata ba, in dai zata samu ta mike to zatayi
tafiya ko yaya ne. Ita ta kulle ko ina tana sauke
numfashi bayan ta fita kofar gida taga ta kulle
nan ma. Tana juyawa ta ga Salim ya fito daga
motar yana zagayowa ya bude ma Daada gidan
baya ta shiga.
Ya mayar ya rufe sannan ya zagaya yana
komawa mota, sanda ta taka ta shiga, tana rufe
kofar taji yace ma Daada
"Ya jikin naki Daada? Kan baya ciwo yau?"
Cikin yaren fulatanci
"Alhamdulillah, gashi ka ganni garas"
Dan murmushi yayi
"Allah ya kara lafiya"
Ya furta da hausa wannan karin, yana jan motar
tunda daman yayi kwana kafin ya ajiye ta. Shi
Lubna sufyan
Hausabook.com 454
Madina take kallo tana son gane abinda yake
damun shi a kwanakin nan, rashin maganar shi
ya karu, sai suyi zaman awa daya baice mata
komai ba, duk hirar da zatayi sai dai in
idanuwanta nakan fuskar shine zata kula da
yanda yake amsa ta da gira, kai ko nashi
idanuwan da zai lumshe ya sake bude mata a
kasalance. Salim najin idanuwan Madina da
suke yawatawa a jikin shi kamar tana son budo
duk wasu sirrikan shi.
Yana jin yanda kallon nata ke sa wani abu
amsawa a cikin kirjin shi. Sharewa yayi kamar
bai san tanayi ba har suka karasa gida. Kamar
wanda yake kan kaya haka ya fice daga motar da
sauri. Shi ya bude ma Daada da tace mishi
"Da ba sai na fito ba tunda zamu juya ne... Ko ba
yanzun za'a tafi ba?"
A kasalance Salim ya kalle ta
"Ki fito Daada, ko ruwa ki sha, ki dan mike
kafafuwan ki kafin kowa ya shirya, ba zakiyi ta
zama a mota ba"
Lubna sufyan
Hausabook.com 455
Har zuciyar ta zaman motar zata zaba in da wani
abu a muryar Salim ya bata damar hakan.
Amman tsaye yayi yana jiranta, dole ta sauko da
kafafuwanta daga motar. Rabonta da gidan tun
bikin Adee, shima ba dadewa tayi ba. Tunda har
gida mijin Adeen yaje ya gaishe da ita, ko
yanzun yakan biyo lokaci zuwa lokaci, bai taba
zuwa mata hannu biyu ba. Zatace yana da kirki,
amman ta san kirkin na shine ya hadu da yanda
Adee ta nuna mishi darajarta. Sai da yaga ta fito
ya rufe murfin motar. Madina ma fitowa tayi ta
zagayo suna jerawa da Daada.
"Jakar ki Mug...wacce ce jakar ki?"
Salim ya tambaya ganin ta bi Daada
"Babbar..."
Ta amsa mishi a takaice batare da ta juyo ba
tunda ta san zai biyo su. Tare suka shiga har
falon gidan suna dan hira da Daadar. Madina ce
tay sallamar da Saratu ta fito tana amsawa,
fara'ar da take fuskarta na ragewa da ganin
Daada.
"Ina wuni..."
Lubna sufyan
Hausabook.com 456
Ta furta a hankali tana dorawa da
"Ya karfin jikin? Ku zauna mana Madina"
Zaman Daada tayi sannan ta amsa gaisuwar da
Saratu tayi mata, Madina na gaishe da ita
"Ina jakar?"
Dan juyawa Madina tayi dai-dai shigowar Salim
da yayi sallama cikin sanyin murya. Saratu ta
karasa tana kai hannu zata karbi jakar hannun
Salim din
"Ina zan kai?"
Da hannu ta nuna mishi hanyar dakin da nashi
ne a cikin gidan kafin ya bar bangaren ya koma
in da yake yanzun. Can kuwa ya nufa ya kai
jakar ya dawo falon
"Ina Daddy?"
Ya bukata, dan murmushi Saratu tayi
"Yanzun zaka ga ya shigo"
Ta kirashi bai dauka ba, daman bata sa ran zai
dauka ba, idan da ta kira fiye da sau daya zai san
dole akwai wani abu muhimmi. Ace kai da mijin
Lubna sufyan
Hausabook.com 457
ka ba zaka kira kaji lafiyar shi ba, ba zaka kira
ka tambaye shi wani abu ba balle kasa ran
zakuyi hira idan yayi maka nisa. Bakowa bane
zai fahimci ciwon abin sai macen da take cikin
irin halin da take ciki.
"Madina a zubo muku abinci mana"
Saratu tace tana maida hankalinta kan su, kai
Madina ta girgiza
"Ko zaki ci Daada? Baki ci wani abu mai yawa ba
fa"
Kai Daadar ta girgiza a hankali
"Ni kam banajin yunwa fa"
Numfashi Saratu ta sauke
"Bari a kawo ruwa to"
Tayi maganar tana nufar hanyar kitchen, bata
jima ba ta dawo da ruwa da kofi, Madina ta
karba ta zuba ma Daada tana mika mata. Karba
tayi ta dan kurba ba dan tana jin kishi ba, ta
ajiye kofin a kasa. Sai lokacin Madina ta kula da
Salim ya bar dakin, sai Saratu da ta samu kujera
can nesa da su ta zauna. Wani irin shiru marar
Lubna sufyan
Hausabook.com 458
dadi na lullube dakin, su duka ukun an rasa
wanda zai ce wani abu. Sai dai motsin Madina da
kan gyara zamanta lokaci zuwa lokaci. Ta ji dadi
da Saratu ta mike ta kunna kayan kallon da suke
cikin dakin tana daukar emote ta koma in da ta
tashi ta zauna.
Sai ita da Madina suka maida hankali kan
labaran, Daada kuwa kara shigewa tayi cikin
kujerar da take zaune, kanta cunkushe yake da
tunani kala-kala. Ko shigowar Julde bata ji ba sai
muryar Madina da take gaishe da shi
"Daada kun gama shiryawa ko?"
Ya bukata yana murmushin da kallo daya zakai
mishi kasan na karfin hali ne, kai Daada ta daga
mishi a hankali tana mikewa. Sai take ganin
kamar ta dade bata kalle shi ba, kamar duk
shekarun nan akwai wani labule a tsakanin
idanuwan ta da shi da yake hana mata ganin shi
irin yanda take ganin shi yau. Ba Julden da yake
da mata da yara ba, ba Julden da ake ma kallon
babban mutum a wajen kasuwan ci da cikin
unguwa ba. Julde take kallo shi kadai batare da
duk wannan abubuwan ba, dan ta take kallo yau
Lubna sufyan
Hausabook.com 459
tana jin littafin da ta dade da rufewa a cikin
kanta yana budewa kafin ya tsaya a wani shafi
da yake da muni a rayuwar su gabaki daya.
Duk shekarun nan, watannin da suke a cikin
shekarun, ranakun da suka dinga zuwa suna
wucewa bata san dalilin da sai yau ba, sai yau ta
zabi ta kalli Julde da idanuwan da tayi mishi
alkawarin ta kauda su da kan shi har abada
"Allah ya tsine maka albarka Julde. Allah ya
kunyata ka a idanuwan zuri'ar ka yanda ka
zame mun abin kunya!"
Idanuwanta ta runtsa, gabaki daya kirjin ta na
daukar dumi kamar an hura mata wuta a ciki.
Me yasa sai yau? Shine tambayar da bata da
wanda zai amsa mata. Ta kuma kasa daina
kallon shi. Ko da ta runtsa idanuwan, tana bude
su akan shi suka sauka, sai dai yanzun taga
kamar yana cikin wani abune mai kama da
kwallon kafa, amman duhun abin bai hanata
ganin shi a tsaye a ciki ba, kamar yana tsaye ne a
cikin tsinuwar mahaifin shi da take jiran cikar
lokaci ta fashe tare da shi. Da Madina bata riketa
Lubna sufyan
Hausabook.com 460
ba da kafafuwanta sun kasa daukar ta saboda
firgicin da ya ratsa ruhinta
"Daada ba dai jikin bane ba?"
Madina ta bukata cike da kulawa da kuma
damuwa, kai kawai Daada take girgiza mata,
addu'ar duk da tazo mata karantawa takeyi tana
neman samun nutsuwa. Haka suka lallaba suna
fita waje. Saratu daga bakin kofa tayi musu fatan
Allah ya kiyaye hanya, lokaci ya koya mata kama
kanta da kinyi musu abinda ta dauka a matsayin
shisshigi a cikin rayuwar su. Tun farko Daada
bata karbeta ba, tayi biris da cewar ko da bata
auri Julde ba jinin da yake yawo a jikin ta yana
yawo a jikin shi, ita din dangin shi ce ko da aure
bai hada su zumunci ba.
*
"Hamma kana soka mun kashin hannun ka a
hakarkari na fa"
Nawfal yai maganar yana sake gyara zaman shi.
Motar da Julde ya so su dauka ya manta rabon
da ya hau ta, kin tashi tayi, Daada, Madina da
Salim baya suka shiga su. Khalid ya bude ta
Lubna sufyan
Hausabook.com 461
bangaren da Salim yake ya watsa mishi wani
kallo da yasa shi mayar da murfin yana rufewa
hadi da furta
"Allah ya baka hakuri"
Ta kasan makoshi, zagayawa yayi ya koma gaba
in da Nawfal yake zaune
"Ka dauko motar ka mana, matsewa fa zamuyi
anan...dan Allah ka dauki mota Hamma"
Amman Khalid yaki sauraren shi
"Zaka matsa ko sai na kwade ka"
Nawfal turo labba yayi yana kallon Julde da ya
shiga mazaunin direba ya rufo kofar
"Daddy kace Hamma ya dauki motar..."
Bai rufe baki ba yaji Khalid din ya turmotso
rabin jikin shi akan na Nawfal
"Kasheni zakayi ne wai, ka tsaya in matsa maka
mana"
Ya karasa yana ture hannun Khalid har yana
gabje hanci da murfin motar da yake kokarin
jawowa ya rufe
Lubna sufyan
Hausabook.com 462
"Wai dan uban ka Bajjo ni sa'anka ne?"
Sake tura shi Nawfal yayi
"Daddy kaji Hamma na zagi ko?"
Dakyar Khalid ya rufe murfin motar, yanda suke
tutture juna zaka dauka yarane yan shekara
bakwai ko kasa da haka. Murza kan shi da yake
ciwo Salim yakeyi tun da suka fara
"Bajjo ku fita daga motar nan"
Ya furta babu alamar wasa a muryar shi,
nutsuwa sukayi
"Ba ku jini ba kenan"
Ya sake maimaitawa
"Daddy kace ya barmu dan Allah, ba munyi
shiru ba"
Khalid ya fadi, numfashi kawai Julde ya sauke,
ya riga da ya koyi shiru ya kyale su, tuntuni
kamar suna Khalid da Nawfal na ganin hanjin
juna wasu lokuttan, sun girma, Nawfal harda
mata amman ba zasu daina fada kamar yara ba.
Da Salim yakan bar su tunda can ma. Yau bashi
Lubna sufyan
Hausabook.com 463
da karfin surutun kwata-kwata shisa yaja motar
suka tafi. Da suka ga an hau hanya shine suka
cigaba
"Wallahi zaku sauka a hanya ku biyo mu a
napep. Maganar da zan karayi akan ku sai kun
sauka daga cikin motar nan"
Salim ya fada, saboda Daada na tare da su, kuma
a tsakiya take zaune. Madina ce ta bangaren da
su Nawfal din suke zaune, daga inda yake zai iya
mika hannu ya kai musu duka, amman baya son
su duka su gwada hali a gaban Daada. Kan shi
har juyawa yake saboda surutun da sukeyi.
Amman dan su san da gaske sauka zasuyi shisa
ya rantse suka ji, yana kallon Nawfal na ture
hannun da Khalid yake kara dora mishi. Madina
kanta murmushi takeyi, tana son ganin Khalid
da Nawfal a tare, fadan su nishadi yake sakata,
ko yanzun ma sun saukaka mata damuwar da
take ciki.
Su dukan su basu kara nutsuwa ba sai da suka
fita suka shiga cikin filin jirgin, suka tsaya inda
zasuyi sallama da su Daada, lokacin tsoron da
Lubna sufyan
Hausabook.com 464
yake tare da Nawfal ya fito shimfide akan fuskar
shi
"Kace zaka biyo mu Daddy"
Yayi maganar yana kallon Julde da ya daga
mishi kai, Madina karasawa tayi ta rungume
Daada tana jin wasu hawaye masu dumi na zubo
mata
"Karki karya ni Madina"
Sake riketa tayi gam tana jin kamar ace in ta
raba jikinta da na Daada zata taho da dumi da
kamshin Daadar a tare da ita, iya wanda zata
rike har sai ta dawo
"Allah ya dawo mun dake cikin aminci Daada...
Ina son ki sosai.. Kin sani ai ko?"
Kai Daada ta daga tana kama Madina ta rabata
da jikin ta
"Bajjo zai kira mun ke ta hoton nan yanda naga
kunayi"
Hannu Madina ta sa tana goge fuskarta, sai da ta
dan ja hanci sannan tayi murmushi
Lubna sufyan
Hausabook.com 465
"Video call Daada"
Dan daga idanuwa Daadar tayi
"Oho ni ban san sunan shi ba"
Dariyar karfin hali Madina tayi, wasu hawayen
na sake zubo mata, hawayen da Salim yake ji har
kasan ran shi. Shisa ya saka hannuwan shi cikin
aljihu saboda kaikayi suke mishi, kaikayin ya
rikota ya hadata da jikin shi ya lallasheta ta
sigar da yafi kwarewa
"Hamma sai mun dawo"
Nawfal da yake tsaye gefen Daada ya fadi yana
sa Salim janye idanuwan shi daga kan Madina
yana mayarwa kan shi
"Allah ya tsare...komai zaiyi dai-dai ka sani ko?"
Kai Nawfal din ya jinjina mishi, sallama suka
kara yi gabaki daya, su suka fara juyawa suna
barin Daada da Nawfal a tsaye. Madina ce ta juya
tana daga ma Daada da taji zuciyar ta ta tsinke
hannu, lokaci daya taji tsikar jikinta ta mike.
Murmushi Madina tayiwa Nawfal da suka hada
ido, sai dai zuciyar shi tayi nauyin da ya kasa
Lubna sufyan
Hausabook.com 466
mayar mata da martani har ta juya, yabi bayan
ta da Kallo, da yanayin tafiyar ta.
Kallon ta Nawfal da Daada sukeyi
Kallon ta Nawfal yakeyi batare da ya san
kaddarar da take bibiyar su ta kusan cika ba
Kallon ta yake batare da ya hango doguwar
igiyar da take shirin kulle su a waje daya ba
Haka ya ga Salim yayi dabarar tsayawa Madina
ta karasa suka jera tare, yanda ya juyar da kai
na tabbatar ma da Nawfal din magana yayi ma
Madina
Salim magana yayi mata kamar ba su da wata
damuwa da ta wuce jiran dawowar Daada.
Nawfal ya fara juyawa ya na ba Daada passport
din su ta rike, ya dauki jakarta ya dora kan
akwatin shi yanda zasuyi mishi saukin ja,
sannan ya kama hannun ta yana fadin
"Muje Daada..."
Tana tunanin me likitoci zasu gani idan sun
bude kirjin ta saboda zuciyarta na tare da su
Madina, gabaki daya zuciyarta da ta kasa
Lubna sufyan
Hausabook.com 467
nutsuwa na tare da su. Haka tabi Nawfal suna
tafiya, tana jin littafin da yake cikin kanta yana
bubbudewa yana komawa shafin farko, takun
duk da zatayi da nufin barin garin na zamar
mata adon da yake janta don ta waiwayi in da
komai ya fara....!
*****
Anan zan kawo karshen kashi na daya. Bayanin
lokaci da kuma in da kashi na biyun zai zo na
nan tafe ba da jimawa ba da yardar Allah.
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 17 Chapter of 18