An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
Lubna sufyan
Hausabook.com 1
Lubna sufyan
Hausabook.com 2
RAI DA KADDARA
1
RAI DA KADDARA 1
01
2002
Kamar ko da yaushe a ranakun da Nanna ce
takan zo daukar su daga makaranta, yau ma
yana leko kai yaga motar ta ya koma cikin
makaranta. Mintina kusan sha biyar ya bayar a
tsakani kafin ya fito, yasan babu wanda zaice ya
neme shi sai Khalid, shima Nanna zatayi nasara
akan shi bayan wasu yan mintina dole ya hakura
su tafi. Titi ya nufa ya tari mashin da zai kaishi
Hotoro daga nan makarantar su ta Greenfield da
take cikin Sharada. Bai wahalar samu ba kuwa,
shi yaune ranar shi ta karshe ma na zuwa
makarantar tunda ya kammala jarabawar aji
Lubna sufyan
Hausabook.com 3
uku ne, duk da yaji suna cewa zasuyi musu wata
jarabawar bayan sati daya da zasuyi amfani da
ita wajen canza musu aji ba sai a jira fitowar
JSCE din ba.
Kusan hakan shine tsari na makarantun kudi,
bai wani damu ba tunda ba'a nan zai cigaba ba.
Sun riga da sun gama magana da Daddy akan
Science and technical zai tafi ya cigaba acan
kuma har ya amince. Bakin titi ya sauka ya
sallami mai mashin din ya taka zuwa kwanar da
zata hada shi da gidan nasu. Ko kadan baya son
komawa, ba zaiki yayita zagaye layi har bayan
Magriba ba, idan dai-dai lokacin shigowar
Daddy yayi sai ya dawo su shiga tare. Amman
bashi da wani zabi, ba abokai yake da su ba balle
yace zai wuce wajen su.
Kwankwasa gidan yayi, dattijon maigadin su ya
bude mishi
"Nawfal, an dawo kenan"
Baba Isa kamar yanda suke kiran maigadin ya
furta da fara'a a fuskar shi da tasa Nawfal yin
dan gajeran murmushi yana amsawa da
Lubna sufyan
Hausabook.com 4
"Na dawo Baba Isa, sannu da kokari"
Sannan ya wuce cikin gidan, bangaren su da
yake wajen gidan, wanda dakuna ukune na bacci
a ciki, kowanne da bandakin shi, falo sai kitchen
matsakaici ya nufa. Mukulli ya zaro a aljihun
wandon uniform din shi ya saka a jikin kofar
yana budewa. Daddy yace bangaren nasu ne su
hudu lokacin da suka dawo wannan gidan
watanni hudu da suka wuce, a gaban shi a gaban
kowa yayi maganar, amman shi kadai yake
kwana a bangaren, ko da Daddy ya sani bai taba
magana ba. Shima kuma ba damuwa yayi ba, ya
rigada ya saba rayuwar kadaici ba tun yanzun
ba.
Sanin ba kowa bai hana shi shiga cikin gidan da
sallama ba. A falo ya ajiye jakar da take rataye a
kafadar shi yana takawa zuwa dakin daya zaba a
matsayin na shi ya wuce bandaki, ranar da akeyi
ba ta wasa bace ba, shisa ya watso ruwa harda
alwalar sallar la'asar ya dauro sannan ya fito.
Riga da wando ya saka, yana son kamshin a
rayuwar shi, tun zai iya tunawa ko turare ya
gani dakin Daddy zai tambaye shi ya dauka.
Shisa Daddy baya rabo da siyo mishi turaruka,
Lubna sufyan
Hausabook.com 5
kala-kala, wasu ko bude su baiyi ba ma, yanzun
kala biyu ya fesa a jikin shi sannan ya baro
dakin baccin yana fitowa falo inda yaci karo da
Khalid da yake rike da kofi a hannun shi sai filet
a dayan hannun da Nawfal yaga kamar cincin ne
a ciki.
"Jalof Nanna tayi..."
Cewar Khalid din yana mikawa Nawfal kofin
daya karba yana dubawa, shayine da akewa
laqabi da ice-tea a turance, dan kankaru ne a
ciki. Khalid ne kadai yasan baya hada hanya da
duk wani abu me zafi, ko abinci ne saiya ajiye
shi ya huce sannan yake ci. Zai iya cin abincin da
ka fito da shi daga fridge amman ba zai iya cin
wanda ka zubo daga tukunya ba sam. Amman
kowa a gidan yasan baya cin yaji, idan yace baya
cin yaji sai mutane su dauka abincin da yayi yaji
da yawa ne baya so. A nashi yanayin ba haka
bane ba, ko attaruhu daya kasa ka gabaki daya
miyar ka zai mishi illa, cokali daya zaiji kamar
ya zuba garwashin wuta a cikin bakin shi, awa
daya ba za'ayi a tsakani ba kuraje zasu cika
mishi baki, zai iya sati yana fama a haka.
Lubna sufyan
Hausabook.com 6
Tun yana karami kowa yasan hakan, allergy ne
yake da shi na duk wani abu daya danganci yaji.
Duk da ya zamana dama ce da Nanna ta kara
samu wajen gallaza mishi, da yake duka gidan
kowa yana son abinci masu yaji har Daddy, a
gaban Daddyn sai ta nuna abincin Nawfal daban
take dafa mishi. Bai kuma taba karyatata ba,
idan farin abinci ta dafa da miya zai diba ya saka
mai da Maggi yaci, ranakun da yake da
makaranta ma inya dawo baya bi takan abinci,
da yaci sau daya shikenan zaici gaba da hidimar
shi, kusan jikin shi ya riga da ya saba da yunwar.
"Ban san ko sugar din yayi maka ba, ka sha kaji"
Khalid ya sake fadi yana mika mishi farantin
cincin din
"Nanna ta san ka dibo mata cincin?"
Nawfal ya tambaya, dan daga kafadu Khalid yayi
"Abinda Nanna bata sani ba yana da yawa..."
Dan murmushi kawai Nawfal yayi, Khalid ya
saba saka kanshi cikin hatsari saboda shi. Jibga
ta Nanna babu wanda ya kai Khalid din shanta,
kuma fiye da rabin lokuttan akan shine. Kurbar
Lubna sufyan
Hausabook.com 7
shayin yayi, sanyin shi yana saukar mishi da
wani yanayi mai dadi, yana son kayan sanyi.
Suna saka shi nutsuwar da ba zai iya misaltawa
ba. Kai ya jinjina ma Khalid
"Komai yayi dai-dai... Nagode"
Sannan ya karbi filet din cincin din ya karasa
yana samun kujera ya zauna ya ajiye shi akan
hannun kujerar. Khalid dinma waje ya samu ya
zauna
"Zanje gidan Daada idan nayi sallar la'asar. Kila
in kwana acan. Ka fadawa Daddy idan ya dawo"
Kai Khalid yake girgiza mishi
"Kabari idan ya dawo yau sai mu fada mishi
gobe kai baka da makaranta, ni ina da. Idan na
dawo sai a kaimu nima ina so inje, na dade banje
ba..."
Kallon shi Nawfal yakeyi harya gama maganar
"Ko Daddy ya barka Nanna ba zata bari ba, ka
sani. Zan tafi yau, idan ka tambayi Daddy saika
biyoni daga baya"
Lubna sufyan
Hausabook.com 8
Baki Khalid ya bude zaiyi magana Nawfal din
yayi saurin katse shi
"Zan tafi yau, ba zan kwana a gidan nan ba"
Shiru Khalid din yayi, duk wani abu da zai fada
yasan ta bayan kunnen Nawfal din zai wuce.
Shisa ya zauna har ya gama shanye shayin,
cincin din kwara budu yaci yana kallon shi. Yar
karamar jakar shi Nawfal ya dauka. Tare suka
fita masallaci sallar la'asar.
***
Da sallama ya shiga gidan Daada, kallo daya
zaka yiwa fuskar shi idan kagan shi awanni
kalilan da suka wuce zaka ga sauyin da tayi.
Idan zaka tona zuciyar shi mutane uku zaka
samu a cikinta, Daada na daya daga cikin
mutanen
"Nawfal..."
Daada ta fadi itama da alamun jin dadi a
muryarta bayan ta amsa sallamar tashi, anan
bakin kofa ya zare takalman shi yana shiga cikin
dakin, zaune take a kasa kan kafet, akwai kujeru
a cikin dakin, zama a kan su bai dameta ba, sai
Lubna sufyan
Hausabook.com 9
tayi kwanaki bata hau kai ba, tafi jin dadin
saman kafet din, idan ma wani ne yazo yayi
mata magana takan ce
"Ina zan iya zaman kujera, kafafuwana duk su
tara jini, ga jikin tsufa"
In Julde ne dariya yakan yi
"Daada idan kikace jikin tsufan nan sai wani ya
dauka kin bawa shekaru tamanin baya"
Ita ma takan dara
"Ko dai banba tamanin baya ba ni din ba ta yau
bace ba"
Yau din bata ma zauna falon ba sai yanzun nan,
da yake tana zuwa Islamiyya anan cikin
unguwar tasu ta Gadon kaya. Da karfe goma na
safe zuwa sha biyu. Da ta dawo tana da miya,
farar shinkafa ta dafa ta shige daki, bayan
azahar bacci ta sha har uku da rabi.
"Ai kuwa gara da kazo, sai ka dauko mun
Madina daga makaranta, yanzun nake shirin
tashi naga hudu da rabin ta kusa"
Kallon Daada yayi
Lubna sufyan
Hausabook.com 10
"Daga shigowata Daada? Kika san kalar gajiyar
da na kwaso?"
Cewar Nawfal
"Raggwanci dai ba gajiya ba. Jakar nan zaka
ajiye kaje ka dauko ta..."
Jakar ya sauke daga kafadar shi yana ajiye
saman kujera, akan Madina ne kawai Daada ba
zata saurari komai ba, yasan ba zata bar shi ya
zauna idan ba zuwa yayi ya daukota ba.
Makarantar da take din ba wani nisane da gidan
Daada ba, da ka fita titi tsallakawa zakayi, hade
take da islamiyya shisa ma take kaiwa har hudu
da rabi, kamar yaji Daada na cewa ta kusan
komawa tashi karfe shidda. Bai maida hankali
kan zancen ba. Ka'ida irin ta makarantar su
Madina sai da aka tsaya ana mishi yan
tambayoyi, da Madina bata hango shi tace
"Hamma..."
Ba yasan zasu bata mishi lokaci, da gudunta
kuwa ta karaso tana fadawa jikin shi hadi da
zagaya hannuwanta a bayan kafafuwan shi.
Lubna sufyan
Hausabook.com 11
Dakyar ya bambarota yana rike hannunta suka
fito daga cikin makarantar
"Yaushe kazo? A gidan mu zaka kwana?"
A shekarun ta har mamakin yanda take magana
babu gargada yakeyi. Dan tsamin baki da yara
sa'anninta sukeyi babu shi a Bakin Madina, babu
kalmar da bata iya furtawa, sai dai wasu
kalaman idan tayi saboda fulatanci da Daada
takeyi mata kuma kusan dashi bakin nata ya
bude zakaji fitar haruffan nata daban. Gashi
tana cikin yaran da suke da surutu, sai dai fiye
da rabin nata surutun akan tambaya ne, kome ta
gani tana so ta gane. Idan gidan yazo bakin shi
ba zai huta da tambaya ba sai tayi bacci.
"Hamma meye wannan? Hamma me yasa kasa
wannan kayan yau?"
Tambayoyi kala-kala, yanda tambaya bata
karewa a bakin Madina har mamaki yake bashi
"Idan zan kwana me zaki bani?"
Dan jim tayi sannan ta amsa shi
"Tuwo..."
Lubna sufyan
Hausabook.com 12
Dariyar da ya kwana biyu baiyi ba ta kwace
mishi
"Duk abubuwa masu dadi ki rasa me zaki bani
sai tuwo"
Ya karasa maganar yana daukarta ya sabe a
kafadar shi saboda titin da suka karasa
"Tuwo da dadi, Daada tana yi mana"
Tace da dukkan gaskiyar ta, ranta yana son
tuwo fiye da komai a abinci, sai kuma nama, dan
ko abinci zaka zuba ma Madina hannunta akan
naman ciki zai fara sauka, sai ta cinye sannan ta
fara cin abincin
"Saboda kina zaune da yar tsohuwa shisa tuwo
yafi dadi"
Da rashin fahimta take kallon shi yanzun
"Ni da Daada nake zaune ba yar tsohuwa ba"
Dariya ya sakeyi
"Wacece yar tsohuwa Hamma?"
Numfashi ya sauke, dan har sukaje gida duk
amsar da zai bata sai ta nemi tambaya a ciki.
Lubna sufyan
Hausabook.com 13
Yakan ji zuciyar shi da take tare da wani dutse
danne da ita ko yaushe ya daga duk idan yazo
gidan Daada. Wasu ranakun yana zuwa ko ba zai
kwana ba, kamar yana da wani batiri na hakuri
da komai da Daada ce kadai take da hanyar caza
mishi batirin, shisa yake jin zuwa gidan nata ya
zame mishi dole, tana saka komai yayi saukin
dauka. Akwai mutum daya bayan Daddy da
Khalid da suke kaunar shi, da suka damu da shi,
hakan ba abu bane karami a wajen shi.
"Hamma kunnen ka manya"
Sosai yake dariya
"Madina dan Allah ki kyale kunnuwana su huta
haka, ke kullum sai kince kunnuwana manya?
Kamar naki ne"
Kai take girgizawa tana kama kunnen nashi ta
lankwasa, hannunta ya ture
"Sakko wallahi tunda munzo gida"
Sosai ta makale a jikin shi, sallama yayi yana
shiga cikin gidan
Lubna sufyan
Hausabook.com 14
"Ai kuwa sai kin sakko tunda kunnena babba
ne"
Daada da take jinsu tayi murmushi
"Yarinya dai gaskiya ta fada, bata taba ganin
kunnuwa irin naka bane shisa"
Fara'ar da bata bar fuskar shi bace ta sake
fadada
"Daada kunnen Hamma ya kara girma"
Samu yayi yana saukota
"Kema kunnen ki babba"
Kan yar karamar hijabin da take jikinta ta saka
hannunta tana taba nata kunnuwan
"Daada wai kunne na babba?"
Tayi maganar tana shiga cikin dakin ta zauna
akan cinyar Daada da ta kamata ta gyara mata
zama tana cire mata jakar makarantar ta ajiye a
gefe, sannan ta kamo kafarta daya tana fara
kwance igiyar takalmin don ta cire mata
"Ko dai zaiyi girma ba zai kai na Hamman ki ba,
na shi kunnuwan daban suka zo"
Lubna sufyan
Hausabook.com 15
Nawfal da ya samu kujera ya zauna yace
"Daada..."
Dariya tayi tana karasa cirewa Madina takalman
"In dauko riga ki sake mun?"
Kai Daada ta daga, da sauri kuwa ta mike daga
jikinta tana rugawa da gudu
"Karki janyo mun kayan nan Madina, ki dauko
wadda hannun ki ya fara kaiwa"
Ai da wahala ma idan Madina ta saurare ta, kai
kawai ta girgiza. Doguwar rigace ta dauko kalar
bula mai haske Daada ta saka mata. Kallon ta
Nawfal yakeyi, rigarta na tuna mishi yanda yake
son kalar bula, musamman mai haske kamar
sararin samaniya, yana kuma son farin abu. In
har Daddy zai sai musu kaya ya tambaya wacce
kala zaice
"Sky blue ko fari"
Duk da wani lokacin Daddy zai siyo mishi wata
kalar daban. A cewar shi
Lubna sufyan
Hausabook.com 16
"Fiye da rabin kayan ka fari ne da blue Nawfal,
gara ka sirka da wata kalar"
Yasan wata kalar a cikin kayan shi na dan wani
lokacine, zai saka wata kalar saboda Daddy a
yanzun, a gaba babu abinda wata kalar zatayi a
cikin jerin kayan sawar da zai mallaka. Wajen
shi Madina ta karaso
"Hamma zan sha ruwa"
Ta fadi
"Da ban zo ba waye yake baki ruwan? Da nazo
ba zaki barni in huta ba..."
Shagwabe mishi fuska tayi yana kallon kanta da
yake dauke da kitso kwara biyu, wajen keyar
gabaki daya babu gashi. Kamar an sude
mangwaro
"Kunne na manya, amman jibi gashin ki kamar
anci giginya ba wuka"
Turo baki tayi
"Daada tace gashi na zai fito kamar nata.. Ko
Daada? Nima dogo har bayana"
Lubna sufyan
Hausabook.com 17
Madina ta karasa maganar tana juyawa ta kalli
Daada, kai Daada ta jinjina
"In shaa Allahu gashin nan zai fito har gadon
baya, so nake ma yafi nawa idan ya tashi"
Hankalinta ta mayar kan Nawfal tana mishi
kallon kaji ko? Daman na fada maka, kafin ta
sake cewa
"Zan sha ruwa, kaji... Daada ta hanani bude
fridge dinta, ka zo ka bani"
Mikewa Nawfal yayi ta kuwa kama hannun shi,
dole tare suka nufi kitchen din da yake hade da
katon falon Daada din. Bin su tayi da kallo, wani
abu na matsewa a cikin kirjinta. Tunda Nawfal
ya shigo ta kula idanuwan shi sun fada yayi
zuru-zuru kamar wanda baya ci yana koshi. Ta fi
kowa sanin halin Saratu ba tun yanzun ba.
"Yaran nan amanata ne Julde, ina tsoron halin
matar ka, ba tafiya da shi nake son hanaka ba,
ka isa ka rike dan Bukar, da bana raye dole a
cikin ku wani ne zai rike shi, amman ina nan,
zan so ya zauna a hannuna"
Lubna sufyan
Hausabook.com 18
Kalamanta akan Nawfal shekarun baya suka
dawo mata, ko yanzun in da zai dawo gidanta
gabaki daya zata so hakan. Julde ya daure ta ne
da kalaman shi, kalaman da har yanzun suke
saka harshen ta yin nauyi wajen ce mishi Nawfal
din ya dawo wajen ta, gashi bata da wata
bayananniyar hujja tunda duk yanda zata
tambayi Nawfal ya zaman su da Saratu yake
zaice
"Daada lafiya kalau fa, ki daina damuwa dan
Allah, muna zaune lafiya"
Amman tasan karya yakeyi, alamun shi basu
nuna haka ba, shatin duka a farko-farkon
dawowar ta garin Kano da Nawfal din yakan ce
mata dukan na makaranta ne, laifi sukayi
amman tasan karya ne. Ta taba tambayar Khalid
"Makarantar ku haka suke dukan yaran mutane
Khalid? Na ga jikin Nawfal ko ina shatin bulala
ne"
Yanayin fuskar Khalid din tun kafin ya furta
"Duka kuma Daada? Ana duka a makarantar mu,
amman ba da yawa ba, kuma Daddy na zuwa
Lubna sufyan
Hausabook.com 19
yayi magana idan mun fada, ba sosai ake dukan
yan gidan mu ba"
Ta san Nawfal karya yayi mata, a yan shekarun
shi a lokacin yasan ya adana damuwa a kirjin shi
harya boye mata itama. A gidan ya kwana a
ranar, da zazzabi ruf a jikin shi, zazzabin da sai
da ta bashi magani, kuma tasan dukan ne. A
lokutta da dama Nawfal ke karya mata
alkawarin da ta daukarwa kanta na daina kuka
akan su shida Madina, daga randa tasa kafa ta
tsallake komai tayi nufin barin komai din a
matsayin shudadden tarihi, sai dai ko tarihi
yakan dawo maka lokaci zuwa lokaci, saboda
akwai mutanen da labarin shi ba zai taba barin
bakin su ba balle su barka ka manta.
Ita a nata bangaren ma bata bukatar wadannan
mutanen, ko ya Madina zata gitta ita din babbar
tunasarwa ce, ga Nawfal shima
"Wani abu a zuciyata yana fada mun shi kadai ne
kwan da nake da rabo a duniya Daada, ga
amanar dana, gatan da na hasaso ma rayuwar
shi mai yawa ne, ga amanar shi nan kafin in
Lubna sufyan
Hausabook.com 20
samu dawowa, dalilin da zaisa ni barin shi mai
karfine..."
Nawfal amanarta ne, amanar da Bukar ya
damka a hannunta, amanar da Julde ya karbe
mata take ganin ya kasa tayata rikewa
"Sai dai in har yanzun kina duba bayana, kina
duba abubuwan da na bari, idan kin kasa
mantawa ki daina kallona da halayen dana bari
Daada waye zai daina? Ke kadai ce dalilina na
shigowa garin nan, sai kuma Nawfal yanzun,
idan kika hanani rikon yaron nan zanji kamar
saboda kina dubana da abinda nake sa Allah ya
shafe mun shi a littafina... Halayena ba zasu taba
kulawar shi ba Daada, na rantse miki tarbiyar
shi ba zata samu tangarda ba, kina kallon
kaunar da take tsakanin mu, ko ita ki duba"
Wannan kaunar kuwa ta ganta tun a ranar farko
da Nawfal ya fara dora idanuwan shi akan Julde
yana da shekaru uku a duniya, sati biyu bayan
tafiyar Bukar, sati biyun da daga ita har Nawfal
din sukayi su a matukar jigace saboda kukan
Daddyn shi da yake yi mata. Amman yana ganin
Julde ya ruga ya makale shi yana kiran
Lubna sufyan
Hausabook.com 21
"Daddy..."
Ta ga Julde da yaran shi, ta ga kalar kaunar da
yake yi musu, amman yaro daya taga ya kalla da
kallon da yake yiwa Nawfal, yaron da yayi
sanadin komai. Har yanzun idan Nawfal da Julde
na waje daya zaka ga yana kallon Nawfal din
kamar shine tilon abu a duniya da yake cike
mishi gurbin duk wani abu daya taba rasawa,
kamar Nawfal ne hasken da ya yaye duk wani
duhu daya taba samun rayuwar shi. Kome zata
gani, ko me zatayi tunani bata da zuciyar da zata
yiwa Julde maganar Nawfal ya dawo wajen ta, ko
da ya yarda bata da tabbas akan Nawfal din zai
amince, yanda Julde yake kallon shi, haka take
ganin Nawfal din na kallon shi shima, kamar
duka duniyar shi ta tsaya ne duk inda Julden
yake.
Dawowar da su Nawfal sukayi falon da surutun
Madina na katse mata tunanin da takeyi, bata
san ya akayi daga rike hannun Nawfal Madina ta
koma kan wuyan shi ba. Dariya takeyi cike da
wani irin farin ciki da zuwan Nawfal kadai
yakan bayyana shi a fuskarta.
Lubna sufyan
Hausabook.com 22
"Da shiriritar nan da kukeyi da zuwa kayi kayo
mun cefane ka siyo mun kifi"
Kafin ya amsa Madina ta riga shi da
"Zan bika Hamma, dan Allah zan bika"
Saukota yayi a hankali
"Je ki dauko hijabin ki da takalmi..."
Da gudunta ta tafi, Daada ya kalla
"Ina kudin?"
Itama mikewa tayi tana bin bayan Madina zuwa
dakin baccin su. Ita ta dauko mata takalmi da
yake mai madauri ne sai da ta saka mata, ta bata
hijabin a hannun ta, bata jirata ba ta fita da
gudu, haka Julde yake kwaso mata su, duk
yawancin takalmanta irin sune. Kudi ta dauko ta
fito ta same su a tsaye suna jiranta, bashi tayi ta
kuma fada mishi na yanda take so. Yana rike da
hannun Madina suka fita, Daada na tsaye tana
kallon su. Zuciyarta da adanannen tunanin da
takeyi akan su, jikokinta biyu da suka fi har
'yayanta matsayi a zuciyar ta.
Amanar ta
Lubna sufyan
Hausabook.com 23
Kaddarar ta
Sai dai taya zata san abinda kaddara ta tanadar
musu yasha bamban da tunanin ta?
A lokacin da ta hade Madina da Nawfal a waje
daya
A lokacin da ta hango su karkashin inuwa daya
suna tayata rike amanar junan su
Kaddara ta rubuta musu yin hannun riga da
juna
Inuwar guda daya ce kamar yanda Daada ta
hango
Amman hannun rigar da zasuyi da juna dole
mutum daya inuwar zata bi
Dole dayan su zaiyi gararamba a ranar da babu
tabbacin samun inuwar fakewa.
Kamshin turaren shi ya fara cika mata hanci ta
zo juya kwanciya, dan tana daya daga cikin
mutanen da in har zasuyi juyi komin baccin da
suke sai sun farka. Wani lokacin ma sai ta tashi
Lubna sufyan
Hausabook.com 24
zaune, kamar yanzun dinma haka ta faru da
Saratu. Idanuwanta ta sauke akan Julde cikin
shaddar shi ruwan toka da tayi matukar amsar
farar fatar shi, agogon da yake manne jikin
bango ta kalla tana ganin karfe sha daya harda
wani abu na dare
"Ina zaka cikin daren nan?"
Ta bukata tana jin wani abu da ya tokare mata
makoshi. Sai da tayi tunanin ba zai amsa ba, dan
har hula sai da ya saka sama kan shi batare da
ya juyo ba yace
"Yaushe inda zanje ko karfe nawa ya fara damun
ki?"
Gyara zamanta tayi, dan batayi magana akai ba
baya nufin abin baya damunta. Halayen shi kaf
ta san su, zata rubuta littafi akan halayen nashi
da ko shi ya karanta sai ya sha mamaki. Yau
dinma bata san me yasa take son mishi magana
kan fitar da zaiyi ba, tafi alakanta hakan da
gajiyar da take jin tayi da halayen shi a satukan
Lubna sufyan
Hausabook.com 25
"Karfe sha daya na dare, idan ba maza masu
aikin kwana ba, kowanne namiji mai mutunci
yana tare da matar shi..."
Numfashi ya sauke yana dan tabe bakin shi,
surutun ta ko a jikin shi, ita dinma bawai ta
dame shi bane ba balle kuma abinda ya fito daga
bakinta
"Me kake tunanin Daada zatayi idan taji babu
wani abu daya canza daga halayen ka? Sai ma
abinda yayi gaba?"
Wannan karin juyawa yayi ya kalleta da
murmushi dauke akan labban shi
"Babu abinda zatayi tunani saboda ba zaki fada
mata ba, saboda zaman ki a cikin gidana yafi
miki komai muhimmanci, kuma fadama Daada
abune da zaiyi barazana da zaman"
Abinda yake tsaye a makoshinta take kokarin
hadiyewa amman yaki wucewa, tana kallon shi
ya dauki mukullin motar ya fice daga dakin hadi
da ja mata kofar. Runtsa idanuwan ta takeyi
tana bude su da sauri-sauri cikin son mayar da
hawayen da suka cika su taf. Ta gama kuka akan
Lubna sufyan
Hausabook.com 26
Julde, ta gama zubar da hawayenta akan kishin
shi, ba zai zamo karshenta ba. Bata san ko tun
farko bata nuna mishi wadatacciyar soyayya
bane shisa yanzun yake ganin duk wani abu da
zatayi domin kudin shine, dan arzikin da yake
da shi.
Ko kanta ba zata yaudara ba, tana son rayuwar
hutu, tana jin dadin kudin da yake da shi, sauyin
da rayuwarta ta samu a tare da shine babban
cigaban da zata mutu tana alfahari da shi. Shisa
bata son taga kwandala ta fita daga aljihun shi
da sunan yiwa wani alkhairi bayan ita da yaran
su. Har wani duhu take ji ya lullube mata
idanuwa saboda bakin ciki. Amman hakan baya
nufin bata son shi, tana son shi, tana jin
soyayyar shi a ranaku mabanbanta, yau na daya
daga cikin wadannan ranakun. Ko da ba zasu
kasance da juna cikin raya daren ba taso duk
juyin da zatayi taji shi a kusa da ita.
Kamshin shine gauraye da dakin, kamshin da
zai cika dakin wata ko dakin otel a tare da wata
da ba ita ba. Dumin shi da take son ji fiye da
komai a daren shine wata zata kwana tana
mora. Ta ya zata ce abin baya mata ciwo? Ance
Lubna sufyan
Hausabook.com 27
lokaci na sa ka saba da abubuwa da yawa,
amman kullum Julde saiya karyata mata hakan,
saiya nuna mata ba zata taba sabawa da halin
bin matan shi ba. Duk yanda take kishin shi, duk
yanda bata son wani ya rabar mata shi bai
hanata tsugunnawa kan gwiwoyin ta ta roke shi
daya kara aure ba
"Idan uku zaka kara dan Allah ka karo, da
wannan biye-biyen da kakeyi
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 1 Chapter of 18