ita ba? Su waye ke buga musu gida kamar za su ɓalla ƙofar? Sun kai kimanin awa guda a wajen kafin jirgin su ya ɗaga zuwa Nigeria.
Jirgin su na tsayawa a Nigeria Lamyah ta ji wani irin tsoro da fargaba ya dira a zuciyarta,me yasa Baaba ya turo su Nigeria bayan ya san bata san kowa ba? Me yasa bai kai su Niger ba wajen Abii da Yah Amee ɗinta? Yanzu wajen wa za ta je? Ina za ta dosa? Suna gama fita daga jirgi suka kammala duk wani abu da ya kamata, sai Lamyah ta riƙo hannun Mubarak ta ɗage niƙabinta tana zare ido,jakar hannunta ta sake damƙewa da kyau har suka fita inda tarin mutane ke tsaye suna jiran ƴan'uwansu,cike da matsanancin tsoro ta sake damƙe hannun Mubarak,zuciyarta na bugawa take taka ƙafafunta zuwa wajen da ta ga babu mutane sosai a wajen,sai dai kafin ta isa ta ga wani matashi da ba zai wuce shekara ashirin da bakwai ba ya isa gabanta ya tsaya,kallon wayar hannunsa ya yi sannan ya kalle ta ya ce.
"Ke ce A'isha ko?"
Da sauri ta hau girgiza kai tana ja da baya,hawaye na zuba daga idanunta,cikin gurɓatacciyar hausarta ta ce.
"Ni..ni suna..naaa...Lamyah ba A'isha ba,dan Allah kar ka cutar da ni."
Murmushi matashin ya yi kafin ya ce.
"Ni suna na Bala,Idris shi ne ya kirani ya ce na zo na ɗauke ku,jirgin ku zai sauka sha biyun rana."
Tana jin sunan Idris a bakinsa sai ta ji kamar ta tafi da gudu ta rungumesa,da sauri ta hau ɗaga kai tana faɗin.
"Suna na A'isha,dan Allah ka taimaka min,ka taimaka wa ƙaramin kani na."
Kukan da Lamyah ke zubawa ne ya fara jawo hankalin mutane gare su,cike da damuwa Bala ya ce.
"Dan Allah ki yi haƙuri ki dena kukan nan,za ki iya jawo min matsala idan kina kuka haka,mu je ku shiga mota na kai ku gida."
Cike da mamaki ta sake damƙe hannun Mubarak ta ce.
"Gida? Wanne gidan?"
"Gidan ku da mahaifin ki ya siya da sunan ki,a can nake zaune ni da mahaifina wanda yake gadi a ciki,ni kuma zan zama direban ki da zai dinga kai ki duk inda kike so."
Jakar hannunta ya miƙa hannu zai karɓa dan ya saka a bayan mota,cikin zafin nama Lamyah ta rungume jakar da Mubarak gaba ɗayansu a ƙirjinta ta fashe da kuka,ganin haka ne ya sanya Bala ja da baya ya ce.
"Dan girman Allah ki dena kukan nan,za ki jawo min bala'i a zaci sace ki zan yi,tashi to ki shiga mota mu tafi tinda ba ki so na taɓa jakar ki."
Da sauri ta miƙe ta bi bayansa,da kanta ta buɗe mota ta shiga,tana zama ta lumshe ido wasu zafafan hawaye suka zubo mata,Mubarak ta rungume tare da sumbatar kansa,rungume ta shima ya yi har suka bar airport bata sani ba. Tafe suke babu wanda ya sake tanka wani a tsakaninta da Bala har suka isa gidan da mahaifinta ya siya mata,wanda yake a unguwar sharaɗa,gida ne mai masifar kyau da ya amsa sunan gida,suna zuwa Bala ya saki horn mahaifinsa ya tashi cikin sauri ya buɗe gate ɗin,babu ɓata lokaci Bala ya danna hancin motar cikin ƙayataccen gidan da ya yi matuƙar burge Lamyah. Cike da fara'a Malam Musa ya isa gaban Lamyah yana washe baki ya buɗe mata mota,Bala kuwa tsayawa ya yi yana kallon yarinyar dake da matsanancin kyau,sai dai baƙin ciki da damuwa da ɗimuwa tare da makuwa sun tattaru sun zauna a saman fuskarta.....
[9/11, 10:50 AM] zee hussain: ƳAR RAWA.
RUBUTAWA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✍️✨
PAGE 15.
Baba Musa ne ya buɗe wa Lamyah parlour da kansa ta shiga,bakinta ɗauke da sallama,hannunta riƙe da Mubarak da jakarta da ta yiwa riƙon rai da rai. Gaishe ta Baba Musa ya yi dan ya dawo da ita hayyacinta daga dogon nazarin da ta lula,cikin dasasahiyar muryar da ta gaji da kuka ta gaishe shi,sannan ta gaida Bala,tinawa da halin da ta baro mahaifinta a ciki ne ya sanya zazzafan hawaye gangarowa a kuncinta. Murya na rawa ta ce.
"Tin a mota na fahimci layin da Baaba ya saka a wayar nan ba na ƙasar mu bane,kuma babu lambar kowa a ciki sai taka da aka rubuta wa Bala. Yanzu ta ya zan samu labarin halin da Baaba yake ciki? Su waye suke bibiyar rayuwar mu?"
Kuka ne ya ci ƙarfin ta har ta kasa furta komai,cike da tausayawa Baba Musa ya zauna a ƙasa ya ce mata.
"Ƴannan ki yi haƙuri da duk jarabawar da take bibiyar rayuwar ku da ke da mahaifin ki,wanda a yanzu haka bashi da rai,domin kuwa gwamnatin ƙasar ku na zargin wasu ƴan ta'adda da kashe shi,na samu wannan labarin ne ta hanyar labaran da aka baza a kafar sada zumunta kafin ku iso,gashi nan Bala shine wanda ya sanar da ni komai,har ya nuna min abinda ke faruwa,ba iya mahaifin ki aka rasa ba,an samu gawar ɗaya daga cikin yaran sa mai suna Anwar,sai sauran ma'aikatan gidan da aka tarar ba sa cikin hayyacin su. Da fari an zaci gobarar da ta tashi a cikin gidan ce ta yi sanadiyyar rasuwar mahaifin ki,sai dai binciken da jami'ai suka yi ya tabbatar da cewa duka ne aka yi masa da mummunan makami,sannan aka sakawa wajen wuta da fetur. Dan haka dan Allah ki yi haƙuri,ki zauna anan har lokacin da komai zai lafa abokin mahaifin ki ya zo ya ɗauke ki ku tafi,sannan...."
"Abbah bata motsi fa !"
A zabure Baba Musa ya miƙe tsaye ya kalli Mubarak dake jijjiga Lamyah yana kuka ya ce.
"Innalillahi wa inna'ilaihirraji'una,na shiga uku ni musa ɗan Mamman,Allah ka tashi kafaɗar wannan yarinya kar na zamo sanadiyyar ajalinta. Bala tashi mota a kai ta asibiti."
Cikin sauri Bala ya kinkimi Lamyah a hannu Mubarak na matsanancin kuka ya fita da ita daga gidan ya saka ta a mota,bai zame da ita ko ina ba sai asibitin dake babban titin shiga unguwar tasu,nan take aka fara bata taimakon gaggawa,shi kuwa ya wuce buɗe mata file da sauran abubuwan da duk ake da buƙata. A can gida kuwa Mubarak ya gigita Baba Musa da kuka ya rasa yanda zai yi,ƙofar gida suka fito yana ta lallaɓa yaron ya sai masa biscuits da alewa ya bashi dan ya yi shiru amma ya ƙi,banda kiran Lamya babu abinda yake yi,danasanin sakin bakin da ya yi ne ya taru ya cunkushe zuciyarsa har ya sanya ƙwalla taruwa a idanunsa,a cikin wannan halin Afrah ta same shi,durƙusawa ta yi tana gaishe da Baba Musa,cike da damuwa ya amsa ta,har za ta wuce sai ta dawo ta ce.
"Baba wannan yaron fa? Ko ɓata ya yi ne ? Ko kuma mutanen da aka ce za su zo unguwar nan ne suka zo? Dan na gan shi fari ƙal kamar balarabe."
Cike da damuwa Baba Musa ya labarta wa Afrah katoɓarar da ya tafka,sannan ya ƙara da cewa.
"Yanzu haka tana asibiti,na kira Bala domin na ji halin da take ciki,ya ce min na dai yi addu'a kawai,amma tana cikin mawuyacin hali."
"Ya salam,Allah Ya jiƙan mahaifinta ya bata lafiya,shike nan mun yi babban rashin mai taimako,Allah Ya sa aljannah ce makomarsa,Allah ya tashi kafaɗunta,kawo yaron na gani ko zai yi shiru."
Karɓar Mubarak ta yi ta saɓa a bayan ta babu ko zani ta hau jijjiga shi,tin yana ƙi yana kuka har ta samu ya lafe a bayanta ya yi shiru yana sauke ajiyar zuciya,cikin gidan suka rankaya ta duba kitchen,anan ta samu kayan abinci kala-kala,har da madarar yara da abincin su,da dikkan alamu ba a jima da zuba su bama,nan take ta hau tinani wataƙila lokacin da ta ga Bala ya fita da mota ya dawo da kaya niƙi-niƙi da safe a lokacin ya siyo,taɓe baki ta yi ta hau haɗawa Mubarak abinci, tana yi tana rawa tare da raira waƙoƙin turanci. Parlour ta dawo ta zauna ta ciyar da shi abinci ta bashi ruwa har ya yi gyatsa sannan ta goya sa da mayafin ta,abinka da ba sabanba da goyo sai gashi ya yi bacci cikin ƙanƙanin lokaci,kwantar da shi ta yi a ɗaki sannan ta kalli jakar da Lamyah ta bari a parlour,har za ta taɓa sai ta bar wajen da sauri ta fita zuwa farfajiyar gidan,anan ta gamu da Baba Musa,yana ganinta ya taso ya ce.
"To yaya? Na ji shi shiru."
Murmushi ta sakar masa kafin ta ce.
"Ya ci abinci,ya yi bacci Baba ka kwantar da hankalin ka,ka zauna kai ma ka huta kafin Allah ya dawo da su gida,idan kuma kana so na zauna da shi har sanda za ta dawo babu damuwa,sai na zauna tinda na kulle gidana."
"Da za ki yi min haka kuwa da kin kyauta,na gode na gode Afrah."
"Haba Baba ka dena yi min godiya haka,ai yiwa kai ne."
Waya farha ta zaro ta na tafe ta na dannawa,kiran da take yi na gama shiga ta kara wayar a kunnenta ta ce.
"Yah ! Faisal ka fito ne?"
Shiru ta yi alamar tana sauraron abinda ake sanar da ita ta ɗayan ɓangaren, ɗan gyara tsayuwarta ta yi kafin ta ce.
"Ok,to dama na kira na sanar da kai cewar yau ba zan samu fitowa ba,sai dai zuwa gobe ko jibi haka."
Sallama suka yi sannan ta riƙe wayarta ta koma cikin gidan ta samu waje ta zauna ta kunna TV,tashar Zee cinema ta kai ta ci gaba da kallon ta kamar dama ta saba da gidan,lokaci zuwa lokaci idanunta na sauka a kan jakar Lamya dake tsakar parlour,zuciyarta ke ta raya mata ta buɗe domin ta ga abinda ke cikin jakar,tashi ta yi ta isa gaban jakar tana ƙare mata kallo, gyaɗa kai ta yi tana jinjina yanda shape ɗin jakar yake,a buɗe take babu makulli,amma sai ta ji ta kasa buɗewa,ɗauka ta yi ta kai ɗakin da ta ajiye Mubarak ta saka a ma'ajiyar kaya,sai da ta tsaya ta ga manyan abaya da ƙananan kayan da aka cika wajen da shi,girgiza kai ta yi sannan ta ce.
"Wasu dai Allah ya basu arziƙi,Allah ka dubi marainiya Afrah ka bata arziƙin da zata wataya,ko da an zage ta ta watsawa kaji tsaba su tsattsaga tai gaba ta na musu dariya."
Rufe wajen ta yi ta fito parlour ta na ayyana abubuwa da dama a cikin ranta.
*****************
Kwanan Lamyah biyar cur a asibiti kafin ta samu sauƙi a sallamo ta,Bala ne ya dawo da ita gida yana ta jera mata sannu kamar zai aro baki,Lamyah kuwa kai kawai take jinjinawa saboda bata son magana ko kaɗan,ganin Afrah ta fito ɗauke da Mubarak a hannunta ne ya sanya Lamya rugawa da gudu ta karɓi Mubarak ta rungumesa,sai a wannan lokacin ne ta samu damar yin kukan da ta kasa yi tin da ta farfaɗo. Da ƙyar Afrah ta ɗaga ta daga durƙuson da ta yi a saman guiwowinta suka shiga parlour,ji ta yi gidan na ta ƙamshin girki,sai ta kalli Afrah wadda ke gaishe ta ta ce.
"Ke ɗin wacece?"
Murmushi Afrah ta sakar wa Lamyah kafin ta ce.
"Suna na Afrah, ɗaya daga cikin mazauna wannan unguwar ta sharaɗa,ni ma marainiya ce kamar ke,bani da uwa bani da uba,ni kaɗai nake zaune a gidan iyayena da na gada,na zo wucewa ne a ranar da aka kwantar da ke a asibiti naga wannan yaron na kuka a hannun Baba,shi ne na karɓe shi na ke kula da shi,tinda yanzu Allah yasa kin dawo,ni zan tafi,amma ina so ki sani,wannan kukan da damuwar da kika sanya a ran ki har suke son su yi sanadiyyar taki rayuwar ko lafiyar ki,babu inda za su kai ki,domin kuwa ba su iyayen ki ke da buƙata ba,ki kasance ƴa ta gari mai kare musu mutuncin su,sannan ki zamo mai yawan yi musu addu'a,ki ƙarfafa kan ki saboda wannan ɗan naki kar ya yi maraicin da kema ki ke cikinsa a yanzu,sai watarana."
Mayafinta ta ɗauka zata yafa,ta ji Lamyah ta rungumeta ta fashe da kuka,rungumeta da kyau Afrah ta yi a ƙirjin ta tana jin yanda ƙwalla ke ƙona mata idanuwanta, tinawa da nata mahaifan ne ya sanya ta tausayawa Lamyah sosai. Bata ɗaga Lamyah a jikinta ba har sai da ta tashi da kanta,kallon Afrah Lamyah ta yi kafin ta ce.
"Na gode,Allah Ya saka maki da alkhairi,na ji daɗin shawarwarin ki,in Sha Allahu zan bi su. Wannan yaron sunan sa Mubarak,ƙanina ne ba ɗana bane,tin yana jariri mahaifiyar mu ta rasu ta barsa,gashi yanzu mun rasa Baaba."
Hawaye ne suka zuba daga idanunta,murmushi Afrah ta yi sannan ta ce.
"Alhamdulillah ki godewa Allah kuna da junan ku,ni kuma kin ga ni kaɗai nake rayuwa,babu wanda ke damuwa da na ci? Ban ci ba? Ta ya nake samun abubuwan buƙatun yau da kullum? Me yake damuna? Ina da lafiya ko bani da ita? Haka nake rayuwa ni kaɗai,ba dan bani da dangin Uwa da Uba ba,sai dan kawai iyayena sun rasu ina da wayo na da hankali na,na hana kowa danne min haƙƙina,sai suka tattara ni suka watsar,zumuncin yanzu sai dai mu yi masa addu'a kawai,ke kuma ki dage ki riƙe ƙanin ki da amana,ni zan tafi,na ajiye maki wata jaka da na gani anan a cikin ɗaki a ma'ajiyar suturar ku."
"Na gode Afrah,dan Allah ki dinga zuwa wajena idan kin samu lokaci."
"Babu damuwa,Balana sai watarana ko?"
Hararar wasa Bala ya yi mata sannan ya ce.
"Kamar gaske,idan har kin yarda ni naki ne ki bari na aure ki mana."
Dariya ta yi kawai ta bar gidan cike da fara'a. Tana fita Bala ya zauna ya sake bawa Lamyah labarin Afrah.
"Afrah yarinya ce mai hankali,sai dai tana da rawar kai sosai,kullum tana fita ta bar gida musamman da yamma,ba zata dawo ba sai dare sosai,wannan dalilin ne ya sa mutane ke yi mata zargin tana yawon banza,ni kuma na san inda take zuwa,da abinda take yi,sai dai na yi iyakar yi na domin ta dena zuwa wajen da za a dinga zarginta da aikata mummunan abu ta ƙi bari,a cewar ta zunubi ake rage mata idan an yi gulmar ta,Afrah na da saurin sabo,amma tana da kafiya,na jima ina nuna mata soyayyar da nake yi mata,sai dai ita sam ta ce babu maganar aure a lissafin rayuwarta,ba dan komai ba sai dan tana tsoro ta haihu ta mutu ta bar yaranta su tagayyara."
Cike da tausayawa Afrah Lamyah ta ce.
"Kowanne ɗan Adam yana tafe ne da zanen ƙaddararsa a tare da shi,ba za mu gushe ba har sai mun kai ƙarshen abinda Allah ya hukunta zai faru da mu a rayuwarmu,dan Allah ka roƙar min ita ta zo ta taya ni zama a gidan nan,ya yi min girma,zan dinga biyanta albashi idan ta amince."
"Tab ! Anya Afrah za ta amince kuwa? Ita fa bata yarda ta zauna ƙarƙashin kowa ba,ta fi so ta je ta yi aikin da zata samu kuɗi ba wai ta zauna haka kawai ba,amma zan yi mata magana domin mu ji abinda za ta ce."
Da wannan maganar Bala ya yi mata sallama ya koma ɗakin sa dake a waje inda mai gadi yake. Lamyah kuwa kitchen ta je ta duba abincin da Afrah ta dafa,shinkafa ce dafaduka ta ji kayan lambu,sai ta soya naman kaza ta rufe,anan ta gane ashe Afrah ke yin girki a kai mata asibiti,kaɗan ta ɗiba ta koma wajen Mubarak suka zauna suka fara ci tare,suna tsaka da cin abincin shi kuma yana ta yi mata surutu yana bata labarin Afrah da larabci,wani abun ta gane,wani kuma sam bata gane inda ya dosa,sai dai ta fahimci cewar Mubarak na son Afrah saboda ta kyautata masa,fata ta dinga yi a ranta Allah Ya sa Afrah ta amince ta dawo gidan da zama ko dan ta dinga ɗebe mata kewar rashin iyayenta........
[9/11, 10:50 AM] zee hussain: ƳAR RAWA.
RUBUTAWA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✍️✨
PAGE 16.
Zaune yake a ƙofar gate ɗin gidan hannunsa riƙe da littatafai guda biyu yana haskawa da wayar sa,lokaci zuwa lokaci sai dukan saurayen dake cizon ƙafafunsa yake yi. Tsaki ya ja a daidai lokacin da ya danna wayarsa ya ga ƙarfe sha ɗaya da arba'in da biyar ta yi,ransa ne ya ɓaci sosai sai ya miƙe ya na ayyana abubuwa da dama cikin ransa zai shiga cikin gida,gate ɗin gidan ya buɗe tare da sanya ƙafarsa ta dama a cikin gidan. Ƙarar babur ya ji yana tafe tare da hayaniyar Afrah tana faɗin.
"Yau kam ai dole na yi murna irin wannan kuɗi da na samo masu tada kwanya? Anya tinda na fara wannan harkar na taɓa riƙe manyan kuɗi irin waɗannan?"
Dariya matashin da ya goyo ta a babur ya yi kafin ya ce.
"Wai dan ma kin ƙi ki afka ɗaya harkar,ke yanzu da ba kina layin manyan yaran da za a dinga yin kwatance da su ba a wannan layin?"
"Humm ka raba ni da sa idon mutanen unguwa ka ji,wannan nuna ni da baki da hannun tare da bina da mugun fatan da ake yi ya isa,ba sai na ƙarawa kaina masifa ba akan wadda nake kai."
A daidai ƙofar gidanta ya dire ta ta sauka,hannu ta sanya a jakar ta ta zaro dubu uku ta ce.
"Dan Allah ka riƙe wannan,ba wai na biya ka bane akan taimakon da ka ke yi min,kawai na ji daɗin yanda na samu ƴan canji masu kauri ne yau ya sa kaima na yaga maka ka ji daɗin ka,banda shaye-shaye don Allah."
Dariya matashin ya yi kafin ya sa hannu biyu ya karɓi kuɗin,sannan ya yi mata godiya,yana tafiya ta ga Bala a tsaye a gefen ta ya harɗe hannayensa a ƙirji yana kallon su,murmushi ta yi ta ƙarasa gabansa tana faɗin.
"Masoyina baka yi bacci ba?"
"Ke da kike mace ma baki dawo gida akan lokaci kin kwanta ba,ballantana ni namiji da nake karatu a jami'a?"
Dariya Afrah ta yi sannan ta ce.
"Tooo yau baƙar magana za a faɗa min kenan,to alhuda-huda a yi karatu lafiya,ni zan je na gasa jiki na kwanta,dan na gaji matuƙa."
Tsayawa Bala ya yi yana karkaɗa hannunsa a gaban fuskar Afrah sannan ya ce.
"Afrah ki kiyaye ni,ki dena sanya kanki cikin zargin mutane,wani bakinsa bashi da kyau,kada ki je ki faɗa cikin tarkon shaiɗan watarana."
Haɗe fuska ta yi kaɗan kafin ta isa gaban Bala ta ce.
"Idan har bin muradi na zai jawo a zarge ni da aikata wani mummunan abun,to mutane sun yi jinkiri wajen tuhumata da aikata mugun abu. Sannan idan har kaima za ka shiga sahun masu zargina...."
Murmushi Bala ya yi kafin ya sassauta murya ya ce.
"Ke kin san na san inda kike zuwa,kuma na yi iyakar binciken da zan yi,ban taɓa jin wani mugun labarin da nake tsoro akan ki ba,shi yasa na dage nake so na aure ki,dan na sama maki mutunci a idanun mutane amma kin ƙi amince min."
"Idan ka aure ni kana karatu da me za ka ci da ni? Ko so ka ke yi na ƙare a ɗakin mai gadi shi Baba muna barin sa a harabar gida yana bacci? Ko kuma da albashinsa zai dinga ciyar damu gaba ɗaya ga nauyin makarantar ka akan sa tinda ka ƙi ka zauna a cikin gidana ko bayan auren? Dan Allah ka dinga dogon nazari akan abubuwa kafin ka afka kanka inda ba za ka iya fita ba."
"Kar ki manta tinda Allah ya haɗa mu da Mai taimako mahaifin Lamyah ya ɗauki nauyin karatuna, sannan..."
"Bala please mu bar wannan maganar,kai ka sani ban taɓa ƙin ka ba,hasali ma tinda nake a duniya babu wanda na ke so bayan kai,amma akwai abubuwan da suka zame mana katangar ƙarfe a tsakanin mu,mu jira har mu kau da su,idan baka da abin cewa ni zan shiga gida."
Ajiyar zuciya mai nauyi Bala ya sauke kafin ya ce mata.
"Na ji na amince,ina fatan Allah ya kaimu lokacin da za mu kau da duk wani abu da yake damun mu. Yanzu dai aiko ni aka yi wajen ki dan na nemi alfarmar ki."
Girar ta ta haɗe waje guda tana kallon sa ba tare da tace komai ba,ganin ta basa hankalinta ne ya sanya shi cewa.
"Lamyah ce ta roƙi arziƙin ki koma wajen su da zama saboda ta yaba da hankalin ki,da yanda ki ke kula da Mubarak,za ta dinga biyan ki albashi."
Tsalle Afrah ta yi sannan ta ce.
"Alhamdulillah,ka san dama tin da na shiga gidan na ga suna da abubuwan aiki wanda bani da su nake fatan mu ƙulla ƙawance da ita,to sai gashi faɗuwa ta zo daidai da zama,ka faɗa mata ni ko babu albashi zan zo,amma ina da sharaɗi."
"Sharaɗin me kuma Afrah?"
"Gobe zan sanar da ita,sai da safe,ina son ka Balana."
"Ƙarya ki ke yi ban yarda ba."
Dariya ta yi,ta ƙarasa buɗe gidan ta madaidaici mai kyau da shi,ciki ta shiga tare da kunna fitilun parlour,a kujera ta faɗi tana faɗin.
"Washh Allah na,na gaji,anya zan iya yin wani wanka yau? Kai sai da safe mun haɗe."
Daga kwancen da take ta dinga cire kayanta tana watsarwa a ƙasa, addu'ar bacci ta yi ta shafe jikinta da ita sannan ta rintse ido,babu jimawa kuwa bacci mai daɗi ya sace ta.
Da misalin bakwai da rabi ta farka daga bacci,cikin sauri Afrah ta miƙe ta faɗa banɗakin dake a cikin wani ɗaki a gidan,wanka ta fara yi sannan ta yi alwala ta fito,kaya ta sanya ta gabatar da sallar asuba ta yi karatun ƙur'ani da azkar sannan ta ɗan tattare parlourn,tana gamawa ta shiga kitchen ɗinta dake a tsakar gida ta hau dafawa kanta ruwan shayi tare da soya ƙwai guda huɗu,parlour ta koma ta baje a ƙasa ta dinga yagar bread ɗin da ta ɗauka a saman center table ta hau ci da ƙwai. Tana gamawa ta shirya cikin wasu riga da skirt ta sake gyara abinda taɓata sannan ta kulle gidan ta nufi gidan Lamyah.
Tana zuwa ta tarar da Bala ya shiga BUK da yake zuwa,sai ta gaishe da Baba Musa tare da tambayarsa Lamya,cike da sakin fuska ya ce.
"Ta na ciki tana jiran zuwan ki."
Murmushi Afrah ta yi cike da barkwancin da ya zame mata jiki ta ce.
"Na zama babbar baƙuwa kenan a gidan yau."
Murmushi Baba Musa ya yi Afrah kuwa ta sa kai tai cikin gidan,tun kafin ya bata amsa. Zaune ta tarar da Lamyah tana feeding Mubarak abincin shi,zama ta yi itama suka gaisa,sannan ta ce.
"A gaskiya ba dan kin sanar da ni ƙanin ki bane,da sai dai na ce ɗan ki ne,kuna kama sosai,sai dai shi fari ne ke kuma kalar chakulan."
Murmushi Lamyah ta yi,ta kula Afrah na da surutu da barkwanci,dan haka sai kawai ta ce.
"Allah sarki mun gode,uhumm..Bala ya sanar da ke abinda na ce ya sanar da ke kuwa?"
"Ƙwarai kuwa ya sanar da ni,har ma na ce ya faɗa maki ni ko babu sisi ai zan iya zama da ku,sai dai kawai ina da sharaɗi ne,wanda idan kin amince da shi shikenan,idan kuma baki amince ba shikenan sai dai a haƙura kawai."
Gyara zama Lamyah ta yi sannan ta ce.
"Ikon Allah,to wai menene sharaɗin naki da zai hana ki zama da mu?"
"Sharaɗi na mai sauƙi ne,bana so ana saka min ido akan shige da fice na,duk abinda zan yi,duk inda zan je a saka min ido bana son tambayoyi,idan har kin amince da wannan to zan zauna da ku."
Yaƙe Lamyah ta dinga yi,tana mamakin abinda Afrah ta ce,to ina take zuwa? Meye a cikin shige da ficen nata da bata so a yi magana akai? Kar fa ta je ta janyo masu jangwangwama ita da ƙaninta suna zaune ƙalau.
Murmushi Afrah ta yi dan ganin yanayin da Lamyah ta shiga,sai ta samu kanta da cewa;
"RAWA ita ce abinda na fi son yi a rayuwata a kowanne yanayi nake,baƙin ciki ko farin ciki ba su hana ni na taka,bayan haka ma RAWA ita ce ke biyan duk wasu buƙatuna manya da ƙanana,kin ga kuwa ba zan so na ajiye abinda ya zame min jinin jikina ba ko? Mutanen unguwa suna zargi na da aikata mugayen abubuwan da ban taɓa aikatawa ba saboda kawai ina fita da yamma na dawo da dare sosai,ni kuma surutun mutane da haniyarsu ba za ta sa na dena yin aiki na ba,tinda lokacin da bana aikin babu wanda ya taɓa bani hatsi,daga masu kyarata sai masu kirana da ƴar maula. Dan haka kamar yanda ba za a hana likita kula da marasa lafiya ba to fa babu mai hana Afrah bawa customers ɗinta nishaɗi su biyata."
Yawu Lamyah ta haɗiya cike da zumuɗi da wani irin farin ciki,sai dai tinawa da mahaifinta da halin maraicin da suke ciki sai ya sage mata guiwa ta koma ta zauna,hawaye ne suka hau kwaranya
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 8 Chapter of 30