a gare shi,ni kuwa babu wata alaƙa a tsakanin mu da zai sa na bata taro na ballantana sisina,to duk da wannan bayani Kulu ta ƙi bari na na huta,yau dai har shago ta bini,cikin mutane ta hau ci min mutunci ta na ikirarin idan ke ce kika hana na mayar da ita to za ta same ki a yi ta ta ƙare."
"Allah Ya kawo ta lafiya. Kar ka sanya damuwar kowa a ranka,ka ɗauka ma kamar ba a yi ruwan Kulu a duniya ba,ballanatana ta wanzu a doron ƙasa. Yauwa ya ka ji wannan shinkafar,kamar ba ta hausa ba ko?"
Mama Tani ta sauya akalar hirar tasu fuskarta ɗauke da murmushi. Mamakin sanyin hali irin na Tani ne ya sanya Baba Musa jinkirtawa kafin ya bata amsa da.
"Ni ai ban ma gane ta hausa bace,lallai ta yi daɗi sosai."
Haka suka ci gaba da hirar su kamar babu abinda ke damun zuciyar Mama Tani,can cikin ƙasan ranta kuwa addu'a ta yi har ta samu ƙwarin guiwar kauda damuwarta. Fatan alkhairi ta yi musu gaba ɗaya idan da rabon sake zama a tsakanin Baba Musa da tsohuwar matarsa Allah Ya sanya alkhairi ya basu zaman lafiya,idan babu alkhairi Allah Ya barta da mijinta su zauna lafiya ya kauda musu duk wani wanda zai tada musu da hankali.
Da misalin ɗayan dare naƙuda ta kama Afrah,cikin sauri Bala ya kamata suka nufi mota,sai da ya saka ta a motar sannan ya koma ya kwaso kayan haihuwar,ya kulle gida ya ja mota zuwa ƙofar gidan Baba Musa,suna tsaka da bacci Bala ya taso Mama Tani suka wuce asibiti,ba ƙaramar baƙar wahala Afrah ta ci ba kafin ta haifi kyawawan yaranta guda biyu mace da namiji. Mamakin hukuncin Allah suka dinga yi,domin kuwa har dubawa sai da suka yi,aka tabbatar musu da mace za ta haifa,ashe namijin na nan maƙale shima. Godiya suka dinga yiwa Allah,nan da nan aka shirya yara aka gyara su tsaf,Bala kuwa ana bashi su ya yi musu addu'o'i sannan ya hau yi musu hotuna. A daren ya turawa Lamyah ya ci gaba da kallon yaran ya na jin soyayyar Afrah na ƙara huda zuciyarsa.
Washegari da misalin biyu na rana aka sallame su suka koma gida,nan da nan Mama Tani ta ɗora ruwa ta wanke su tass sannan ta saka musu kayan sanyi. Ta na gamawa da su ta bawa Afrah su dan ta shayar da su,cikin ikon Allah kuwa yara sun samu abincinsu sosai,domin dama tin da cikin ya tsufa ruwan ke zuba. Dariya Bala ya dinga yi yana cewa.
"Ohhh lamarin na Allah ne,abu dai gasu kamar lemon tsami amma tubarkallah yara sun sha sun ƙoshi har bacci ya ɗauke su."
Wani mugun kallo Afrah ta sakar masa ta na hararar sa,wayarta ce ta fara ringing sai Bala ya yi saurin miƙa mata ya na dariya,cikin sauri ya ce.
"Laa Lamyah ce ma,dama ta kira ɗazu kina bacci a asibiti,sai ta ce za ta sake kira."
Hararar sa ta yi sannan ta amsa kiran tana cewa.
"Ai baka sanar dani ba sai yanzu...masoyiya maman twins"
Afrah ta ƙarasa maganarta cike da ihun murna,Lamyah ma murna ta ke yi ta na tsalle,ji take yi kamar ta ganta a tare da su a daidai wannan lokacin. Layuzah na tsaye ta na wasar baki saboda ganin fara'ar da Lamyah ke yi.
'In Sha Allahu gobe muna nan tafe, na matsu na gan ku,ina kewar ku sosaiiii."
"Ni kaina na yi kewar ki masoyiya,Allah Ya kawo mana ku lafiya."
'Ga Layuzah za ta yi miki barka.'
Afrah na jin haka ta hau faɗin.
"Hello,ki na ji na ? Hello? Kai ina jin dai matsalar network ne."
Duk sallamar da Layuzah ke bankawa Afrah na jinta,ƙarshe sai ta kashe wayar,ta saka a ɗan jirgi,tsaki ta ja ta ce.
"Munafuka,ai ni idan ban yagalgala matarnan ba,ba zan samu salamar ruhi ba."
"Sannu ayagi,to ita wadda aka yiwa laifin ta yafe,kema be kamata ace kin huce haka ba?"
"Naƙi na hucen,na ce na ƙi na huce tinda ni abinci ce me zafi,don Allah ni kar ka jawo mu fara sa'insa da kai,bani da lafiya."
Haƙuri Bala ya bata yana jinjina halayyar Afrah ta riƙo,wanda har a wannan lokacin ta ƙi sakin jiki da danginta,tin a asibiti ma da suka je yi mata barka da ido kawai take bin su saboda tinawa da abubuwan da ya faru tsakaninta da su. Sai gashi yanzu da suka ga ta zama mutum,bata neman abinda za ta ci,mijinta na kasuwanci,rufin asiri ya samu gare su,sai suke neman manne mata.
Washegari da misalin ƙarfe uku na rana su Lamyah suka sauka a Nigeria. Duk yanda Lamyah ta so Aminullahi ya kaita wajen Afrah kai tsaye ƙi ya yi, ya ce su je gida ta fara hutawa tukunna. Momma kuwa banda santi da yabon Nigeria babu abinda take yi,sai a lokacin ta dinga jin takaicin ƙin zuwa da ta dinga yi a baya. Mubarak kuwa yana tare da Abii ya na ta zuba masa surutu.
Sai da dare bayan sun huta sosai Aminullahi ya ɗauke su suka tafi gidan su Afrah. Rungume juna suka yi ita da Lamyah kamar za su tsaga jikin juna su shige. Cike da tsuke fuska Aminullahi ya ce.
"Malama sakar min mata ta kar ki sata haihuwa lokaci be yi ba."
Hararar sa Afrah ta yi sannan ta ce.
"Masu mata manya,na ga dai nima ɗan nawa ne ba zan so wani abu ya same shi ba ko? Ke mu je ciki na ga nan akwai ɗan sa ido. Momma mu shiga daga ciki ki ga jikokin ki,akwai me kama da ke a cikin su,dan yanda macen nan ke kama da ke banga wanda ya kwaso kyawun ki kamarta ba."
Ta ƙarasa maganarta ta na hararar Aminullahi. Murmushi ya yi sannan ya kama hannun Mubarak suka shiga cikin gidan gaba ɗaya Bala na tintsira dariyar halin matar tasa, kallonsa Aminullahi ya yi ya ce.
"Laifin ka ne ai,yanzu ace duk tsawon wannan lokacin baka sauya bakinta ya koma ƙeyarta ba."
Kama baki Bala ya yi yana sake fashewa da wata dariyar. Abii kuwa murmushi kawai ya yi yana girgiza kai. Suna shiga suka tarar da Mama Tani tsaye ta sha gayunta daidai misali riƙe da yaran a hannayenta,cikin sauri Lamyah ta nufe su ta karɓi yaran tana hawayen farinciki,Abii ta miƙawa su ya yi musu addu'a sannan ta bawa Momma su,itama addu'a ta yi musu,sannan ta kaiwa Yah Amee ɗinta ta zauna daf da shi kamar za ta shige jikinsa,Bala ne ya yi musu hotuna a haka saboda kyan da suka yi. Mubarak na ganin haka shima ya shiga hotunan aka yi da shi. Jaririyar ya riƙe a hannunsa ya na murmushi,nan ma Bala sai ya ɗauke shi hoto shi da jinjirar.
Hira suka dinga yi da junan su,kafin Mama Tani ta hau gabatar musu da abinci. Babu wata jin kunya suka zauna gaba ɗaya suka ci abinci sosai suka ƙoshi,Momma sai santin abincin Nigeria take yi,ta na faɗin dama sun zo da Iya ko Zahrah su koya. Aminullahi ne ya ce.
"Ai kawai Momma ki koya da kan ki sai ki dinga yi wa Abii."
Yaƙe ta yi kafin ta ce.
"Idan babu wahala me zai hana."
Dariya Abii ya yi,dan dama ya san halin kayarsa ba iyawa za ta yi ba. Da misalin sha ɗaya da rabi na dare Abii da Momma,Aminullahi da Mubarak suka shirya tafiya gida,Afrah ta dinga kukan shagwaɓa ta na roƙon su da su zauna akwai enough wurin da zai ishe su dika,sai dai Abii ya bata haƙuri ya ce ga ƴar'uwata nan su yi hirar yaushe gamo,su kam za su tafi sai ranar suna za su dawo.
Tsarabar da duka zo mata da shi suka fitar daga mota Bala ya durƙusa yana ta zabga godiya, suna tafiya Afrah ta buɗe manyan akwatinan guda biyu,kayan jarirai ne da nata a ciki tare da turaruka. Kukan farinciki ta dinga yi tana godiya. Lamyah kuwa dariya ta dinga yi mata tana tsokanar ta da cewa ta girma fa ta dena kukan banza.
Haka mutane ƴan unguwa da dangin iyayen Afrah suka dinga zuwa barka ganin jarirai. Ba a bar Mama Kulu a baya ba. Domin kuwa itama ta zo gidan ya fi sau uku,rashin ganin fuska daga wajen ɗan nata da matarsa ne ya hana ta zama ta kwana a gidan. Duk zuwan da za ta yi kafin ta tafi sai ta samu abinda ta sibare, duk abinda take yi Bala da Afrah na sane,shi yasa ya ji sam ba zai iya zama da ita a waje ɗaya ba,tinda ta samu gida a rabon gadon iyayenta to ta yi zamanta kawai a ciki,zai dinga kyautata mata daga can. Rashin godiyar Allah ne kawai ya sa ta ke son sake shiga rayuwarsu.
Ranar suna yara sun ci sunayen mahaifan Afrah da suka rasu,wato Abdulƙadir da Zainab. Namijin suna kiransa da Amir macen kuma Amirah. An ci an sha an yi hidima sosai a bikin,domin kuwa Aminullahi ya yanka wa Amir rago biyu,ita kuma Amira rago ɗaya. Sai Abii ya yanka musu saniya saboda rabon nama. Ranar nan ba Afrah ba har Baba Musa sai da ya yi kukan farinciki suka dinga godiya har sai da suka bawa Abii kunya.
Lamyah ma kanta sai da ta gode wa iyayen nata sosai akan ɗawainiyar da suka yi da Afrah,duk saboda ita. Bayan suna da kwana biyar Abii ya ce Lamyah ta shirya za su kai ziyara rijiyar Lemo,Afrah ta so ƙwarai ta bi su,amma Abii ya ce ta zauna saboda ɗanyan jegonta. Haka suka shirya ɗauke da sha tara ta arziƙi suka tafi rijiyar lemo. Suna zuwa suka tarar da Mai Unguwa zaune da mutanen sa a fada ana ta hira ana cin gyaɗa me gishiri tare da shan rake. Me gyada da me rake na gefe suna sauraron su. Bayan sun gaisa da mutanen wajen ne,Mai Unguwa ya bada umarnin su Lamyah su shiga cikin gidan. Nan take ta ji hankalinta ya tashi domin bata san a wanne yanayi Innoh za ta karɓe ta ba wannan karon,murmushi Mai Unguwa ya yi sannan ya ce.
"Ai Innohn taki ta koma sanyi ƙalaou yanzu,ƙanwar ki Saddiƙa ta koya mata darasin zaman duniya me wuyar fassara,shiga ku gaisa babu komai ƴata."
Malam Abubakar abokin Kakan Lamyah ne ya fashe da dariya da ya tina dramar Innoh da saddiƙa,ba ƙaramar wahala yarinyar ta bawa Innoh ba,har sai da maganar cikin gida ta dinga dawowa fada ana warware ta gaban jama'a tsabar bala'i,da ƙyar Musaddiƙ ya yi nasarar gyara tsakanin Innoh da matar tasa da ke mutuwar son shi. Suna shiga suka tarar da Innoh duƙe ta na matse awarar da take yi ta siyarwa. Suna haɗa ido da Lamyah da Momma ta kwasa da gudu ta shige ɗakinta ta banke ƙofar ta na ihu. Kallon Lamyah Momma ta yi da neman ƙarin bayani,kafin Lamyah ta yi magana Innoh ta buɗe taga ta na leƙen bayan su Momma,ganin bata hango Afrah ba ne a cikinsu ya sanya ta rufe tagar ta buɗe ƙofa a hankali,baki na rawa ta ce.
"In ji dai baku zo da wannan ƙarmasasshiyar yarinyar ba me ƙashi ɗaya?"
Nan take Lamyah ta tina dukan da Innoh ta sha a hannun Afrah,dariya ta dinga yi sosai sannan ta ce.
"Innoh ai yanzu haka mun baro ta gida jego take,ta haihu yara biyu babu jimawa akai suna."
"Allah sarki,Allah Ya raya ya raba su da mugun halin uwarsu."
Dariya sosai Lamyah ta yi tana zama a tabarmar da Innoh ta shimfiɗa musu,su Asabe ne suka fito suna ta lalale maraba da su Lamyah. Kamar daga sama Lamyah ta ga Musaddiƙ ya fito daga wani waje da aka kewaye shi da Saddiƙa da ƴar su kyakkyawa,washe baki Saddiƙa ta yi sannan ta ce.
"Lallai na yarda da maganar ka Baban Shatu,ta fini kyau nesa ba kusa ba,ai ni da gani nake yi babu macen da ta fini kyau kaf zuri'ar mu."
Dariya Lamyah ta yi, ta miƙe da ƙyar ta isa gaban Saddiƙa ta karɓi yarinyar tasu,wasa ta fara yi mata ta ga tana ɓangale mata dasori,cikin fara'a ta ce.
"Meye sunan ta?"
Murmushi Saddiƙa ta yi sannan ta ce.
"A'isha. Muna kiranta da Shatu,wani lokacin kuma ina ce mata Lamyah ƙarama,domin kuwa sunan ki mahaifita ya saka mata."
Kallon Musaddiƙ da ya kafe ta da ido yana murmushi ta yi,itan ma murmushi ta sakar masa sannan ta ce.
"Na gode da karamci Yah Musaddiƙ,Allah Ya raya mana takwarata."
Su Lamyah na nan na hira a gefe su Momma da Innoh ma na tasu hirar,daga ƙarshe Innoh ta nemi yafiyar Lamyah,ta kuwa yafe mata,Mubarak kuwa ya ma manta da abinda ya faru da su,dan da ta nemi yafiyarsa ma kallon mamaki ya bita da shi. Suna nan suna hira Innon ta zubowa Momma da Lamyah ɗanwake,sannan ta soya musu awara,babu fulaƙo suka ci suka ƙoshi,Lamyah har da ƙara ɗanwaken saboda lasar yaji. Sai da suka yi sallar azahar sannan Mai Unguwa ya ce su shirya su je gidan su Delu. Cike da jimami Innoh ta ce.
"To kai Musaddiƙ ka yi musu jagora,Allah Ya sa wannan taƙadirin baya gidan."
Cikin sanyin murya Saddiƙa ta ce.
"Amin dai Innoh."
Su na isa gidan suka tarar da wani mutum a kwance a zaune kamar mahaukaci ya takure a jikin gini ya na ta sharar bacci,a ƙasan inda yake kwance duk karan sigari ne zun kai biyar. Hannu Musaddiƙ ya saka musu a baki alamar su yi a hankali su shige,da mamaki Lamyah ta kalli mutumin ta shige gidan,Abii da Aminullahi kuwa dama an basu labarin Hamzah da Habeebu tun a wajen Mai Unguwa. Tinda Habeebu ya dawo daga kudu unguwar bata zauna lafiya ba, saboda halin ɓera da ake zabgawa kamar a ɗauke mutum a siyar. Ga shaye-shaye da yake yi har ya fara koyawa matasan unguwar, har shunen NDLA aka yi masa,amma saboda rashin ƙwaƙƙwarar shaida dole aka sake shi,wata iriyar dabara ce da shi da wayo,shi yasa ba ya yarda a kama shi da kayan maye,duk da cewa kuwa yana ta'ammali da su. Ran Aminullahi a ɓace ya bi bayan Musaddiƙ suka shige. Shi da a son sa ma ba sai an zo ba,amma Abii ya dage sai sun zo.
Halin da suka tarar da Delu a ciki ne ya sanya Lamyah komawa baya a jigace ta na zabga amai,ƙafar Delu ce ke fitar da wani irin ruwa mai bala'in wari,ga wasu ƙananan fararen tsutsa a jiki,ta rame ta yi baƙi sosai kamar ba ita ba. Nan da nan Saddiƙa ta hau aikin da ta kan zo lokaci zuwa lokaci ta yi wa Delun,wanda in ba ita ba babu mai yi mata shi a yaran,wanke mata ƙafar ta yi da spirit da audiga warin ya ragu sannan su Momma suka kama Lamyah da ke nufashi a wale suka tsaitsaya,domin babu wajen zama a gidan sam. Hamzah ne ya shiga gidan kamar an wurga kibiya,burki ya ci a gaban Aminullahi da ke riƙe da robar ruwan da ya ɗakkowa Lamyah a mota, wani mugun kallo ya watsawa Hamzah sannan ya hau zuba wa Lamyah ruwa ta na wanke bakinta da fuskarta. Zubewa Hamzah ya yi a gaban Abii ya na kwasar gaisuwa,bayan ya gaida Abii ne ya hau gaishe da Momma da Lamya har da Aminullahi da ke zabga masa harara. A daƙile ya amsa sannan ya riƙe Lamyah a jikinsa kamar za a ƙwace masa ita,Momma ji take kamar ta kurma ihu ko ta kwasa a guje,tinda ta shigo Nigeria bata shiga tashin hankali ba sai da ta ganta a gidan masoyiyarta Aminee. Tana tsaka da tinani a ranta ta ji muryar Musaddiƙ na faɗawa Delu cewar Lamyah ce ƴar gidan Aminatu ta zo gaishe ta. Kuka Delu ta fashe da shi ta na miƙawa Lamyah hannu ta na faɗin.
"Ƴannan ki yafe mana ni da ƴaƴana don Allah da son Annabi ba dan halin mu ba. Idan baki yafe mana ba alhakin ki ba zai barmu mu ci gaba da rayuwa cikin salama ba."
Kuka sosai Delu ke yi Hamzah na taya ta,shima gafarar su Lamyah ya roƙa sannan ya ce.
"Kin ga yanda Delu ta koma ko? Alhakin ku ne ke da mahaifiyarki ya ke bibiyar mu. A ranar da Habeebu ya dawo ya tarar da na yi sabon aure,na auri wata bazawara sakin wawa. Ko tarewa da matar ban yi ba ya afka ɗakin ya nemeta ta karfin tsiya, lokacin da Delu ta shiga ƙwatar ta ne aka yi rashin sa'a a bige yake,sai ya rufe ta da duka ya wurgo ta waje ta bugu da wani tsohon ƙarfe,to tin daga nan ƙafar ta fara ciwo a hankali har ta zamo haka. Ni kuma babu yanda na iya dole na saketa ta koma gaban iyayenta muke zaune a haka,idan muguntarsa ta tashi haka zai kama mu ya yi ta duka kamar an aiko sa. Yarinyar nan Saddiƙa kuwa hana ta zuwa kullum na yi,saboda ya sha kwata keta mata haddi a matsayinta na ƴa a wajensa."
Ya ƙarasa maganarsa da kuka mai tsanani. Da ƙyar aka lallashe shi ya yi shiru yana ci gaba da neman gafarar Lamyah da Mubarak. Cikin kukan tausaya musu Lamyah ta ce.
"Na yafe muku,ina kuma kyautata zaton da ace Ammii na raye itama za ta yafe muku,Allah Ya baki lafiya. An kai ta asibiti kuwa?"
Ajiyar zuciya Delu ta sauke ta na godiya da yafiyar da Lamyah ta yi musu sannan ta ce.
"Ƴannan ana ta abinda za a kai baka,ta ina za a samu na kaiwa asibiti? Nan gidan wannan yaro Musaddiƙ ya kawo adaidaita sahu za a kai ni asibiti,amma wannan tsinannen yaron ya daki me adaidaitan ya kore sa. Shi kansa Musaddiƙ ɗin ai ɗauke yake da tabon barandamin da ya kwaɗa masa."
"Innalillahi wa inna'ilaihirraji'una. Lallai lamarin babba ne,amma kar ku damu zan san yanda za a yi,mu za mu wuce,Allah Ya ƙara lafiya."
Abii ya faɗa,dan ya kula da kallon da Momma take ta aika masa,ta matsu su bar gidan. Kuɗi mai yawa Abii ya basu sannan suka yi musu sallama suka bar gidan,har a wannan lokacin Habeebu na ta sharar bacci.
Maƙudan kuɗaɗe Abii ya turawa Musaddiƙ bisa amana ya ce a gyarawa su Delu gida,a kai ta asibiti,sannan a bawa Hamzah jari,shi kuma Habeebu zai sa a zo a ɗauke shi a kai shi rehabilitation center. Aminullahi kuwa karɓar contact ɗin Musaddiƙ ya yi,domin ba zai bar karar da ya yi masa ta tafi a banza ba,duk da ya san cewa ya so Lamyah a baya,amma dai ya ji daɗin takwarar da suka yi wa Lamyahn wanda ya kasance sunan mahaifiyarsa ne.
Haka suka tafi gida Lamyah na ta fama da tashin zuciya,suna isa gida Momma ta ce kowa ya zube takalminsa a waje,dan kuwa babu me ƙara amfani da shi,Abii dariya ya dinga yi mata,babu yanda ya iya duk son da yake wa takalminsa ya bar su waje, saboda umarnin gimbiya ne dole a bi. Wanka ta shiga bayan ta cire kayan jikinta ta saka a ledar zuba shara, duk sai da ta tattare kayan kowa bayan ta fito daga wanke hannaye ta fita da kanta ta bawa Malam Isa ta ce a bayar kyauta. Lamyah kuwa zazzaɓi ne ya rufe ta sosai,Aminullahi haka ya dinga jin haushin zuwan su gidan. Bayan kwana biyu suka yi wa su Afrah sallama suka koma Niger. Lamyah ta ci gaba da renon cikinta har ya kai lokacin haihuwa,a gida ta haihu,Iya ta yanke ciki,aka ɗauke su aka kai su asibiti,likita ya duba ta ya tabbatar da lafiyarta da jaririyarta sannan suka dawo gida. Layuzah da Iya ne ke ta hidima da mai jego da jaririya,ranar suna aka sanya wa yarinya Aminatu Aminullahi na kiranta da Ammiina a haka har sunan ya bi bakin mutane. Layuzah ce ke kula da yarinyar,wani irin so take yi mata mara misali,wanda ya wanke duk wata ƙiyayya da jin haushin da Aminullahi ke yi mata. Lamyah na matuƙar jin daɗin yanda Layuzah take kula da yarinyar,shan nono kaɗai ke haɗa su,komai Layuzah ke yi mata.
*****************
Bayan shekara biyu Layuzah ta haifi yaronta namiji kyakkyawa aka mayar da sunan mahaifinta Kabiru,suna ce masa Sultan,rayuwar gidan Aminullahi ta dawo gwanin sha'awa ga kowa, ya kai iyalansa gaba ɗaya har da Hajiyan Layuzah sun yi aikin hajji,Umara kuwa sun yi ta babu adadi,a gefe ɗaya ya buɗewa Lamyah babban shagon gyaran jiki na mata,inda take siyar da ingantattun kayan gyaran jiki wanda ba sa lalata fata,da kuma turarukan wuta da kayan mata wanda take haɗawa natural da kayan abincin mu na yau da gobe da basu da illa ga lafiyar jiki. Sosai littafin MAIDA TSOHUWA YARINYA na marubuciya HAERMEEBRAERH ya taimaka mata,sai ta ji ma ashe kuɗin da aka saka na siyarwar ba suyi tsada ba kamar yanda wasu suke ƙorafi,tinda akwai abubuwan amfani sosai a cikinsa.
Bayan shekaru sha uku.
Watarana Mubarak ya dawo daga lectures ya biya ta gidan Lamyah suna hira da yara yana ta yi musu wasa,wayarsa ta fara ringing,yana ganin me kiran ya ɗauka ya na murmushi,karawa ya yi a kunnensa ya na lumshe ido,Lamyah na ganin haka ta daki kafaɗarsa ta ce.
"Uhum yaro ya girma,lallai dole ne mu zo mu fara shirin biki,Ke Amirah ki rage kashewa ƙanina murya kin ga yanda yake wani narkewa kuwa?"
Da gudu Mubarak ya bar parlourn ya na dariya,Amira kuwa kunya ce ta kama ta ta kashe wayar.
Aminullahi dake zaune ya na karanta jarida ne ya ce.
"Ke dai ba za ki bar yaran nan su huta ba ko? Ita waccan ƙarmasasshiyar ta natsu ta dena tsokana ke kuma ta bar miki kin karɓe."
Murmushi Lamyah ta yi ta kwantar da kanta a kafaɗarsa, hamdala ta yi zuwa ga Allah sannan ta ce.
"Na godewa Allah da rayuwata bata ƙare a RAWA ba,lallai da ban samu wannan farincikin da nake ciki ba a yanzu. Allah ka yafe min kusakuran da na aikata a baya,ka ƙarawa rayuwar ahalina albarka."
"Amin Ya Allah. Ban tabbatar da abinda hausawa ke faɗa ba akan duk abinda ka shuka za ka girba, sai a ranar da waɗannan tantiran suka turawa Faisal videon ki kina tiƙar rawa babu kayan arziƙi a jikin ki. Sai dai alhamdu Lillah da komai ya zo mana da sauƙi hukuma ta ladabtar da su yanda ya dace, sannan an goge videos ɗin duka."
"Ni kaina sai a lokacin na gane illar abinda Ammii ke nusar damu a wancan lokacin. Allah ka jiƙan magabatan mu, ka yi musu afuwa."
Layuzah da ta tattaro kan yaran suka dawo cikin gida kasancewar Mubarak ya tafi ne ta amsa da.
"Amin,gasu nan suna so su dame ni,ni na wuce ɗaki na ɗan kwanta na huta,na matsu a gama hutun makaranta kowa ya koma."
"A fito lafiya maman biyu."
Lamyah ta faɗa ta na kallon ƙaton cikin Layuzah da ya girma haihuwa ko yau ko gobe. Murmushi ta yi ta wuce ciki ta na hamdala a cikin zuciyarta da Allah ya daidaita lamuran gidan nasu,gashi yanzu gidan su ya ƙara cika da albarkar yara har takwas,biyar na Lamyah Uku nata.
*Alhamdu Lillah anan na kawo karshen wannan littafi mai suna ƳAR RAWA. kusakuran dake ciki Allah ya yafe min ya shafe shi a cikin wannan rubutu nawa,Allah ya bamu ladan dake ciki da ni da ku masu karatu,Allah Ya bamu ikon ɗaukan darasin da ya ƙunsa mu yi aiki da shi. Sai mun haɗu a littafina na MUGUN MIJI,kar ku manta MUGUN MIJI littafi ne shima da na rubuta shi tin 2017 har zuwa 2018,sai dai zai zo muku da sabon salo ne wanda mafi yawancin labarin na gaskiya ne. Kar ku bari a baku labari,ku tanadi ƴan kuɗaɗen ku da ba za su gaza......*😂
*HAERMEEEBRAERH CE ✍️✨*
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 29 Chapter of 30