Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Tarbiyyar da nake baki kenan? Kin taɓa gani na ina wannan shiriritar da sunan rawa?" Iya ɓacin rai Aminee ta gama dasawa a zuciyar masoyin nata da yake yi mata ƙololuwar so,sai dai a yau ta fahimci soyayyar da yake yi mata shafar mai ce akan wadda yake yiwa Lamyar tasa,da wasu irin jajayen idanun da suka kawo ruwa ya kalli kuncin ƴarsa da yayi jawur har ya tasa,banda kuka da hawaye da yawu da majina babu abinda take yi,ba tare da ya kula Aminee ba ya gegare ta ya bar ɗakin. Ita kuwa bin bayansu ta yi tana ci gaba da faɗa kamar za ta ari baki,sai da El-mustapha ya isa ƙofar ɗakin Lamya sannan ya ja ya tsaya ya juya cike da ɓacin rai ya kalli Aminee ya ce. "Kin mare ta akan ta yi rawa a gabana ko kunyar idanuna baki ji ba,kin kirata da sunayen da kika ga dama ko nauyin idanuna baji ji ba,to ya ishe ki haka,ki tsaya a matsayinki na Uwa nima ki bani dama na yi nawa aikin na Uba,kin bani mamaki Aminatu,yarinya ƙarama zaki yiwa wannan dukan kamar wata sa'arki? Me ta sani ita banda soye-soyen zuciyarta? Idan gyara zaki yi mata haka ya kamata ki yi mata? To ƴata rawa take so,za ta yi rawa har sai sanda ta ji bata son yin rawa,ni da kaina zan saka ta a ajin da ake koyar da rawa idan ita take son yi,babu kuma wanda ya isa ya hana!" Wani irin mamakin El-mustapha ne ya kama Aminee har yayi sanadiyyar jinginuwarta da ginin dake kusa da ita tana kama bakinta,cike da zubar da hawaye take bin ƙofar da El-mustapha ya shige da ƴarsa a hannu ya bugata kamar zai ɓalla,a zuciyarta take ayyana. 'Ya Allah kar ka jarabce ni da mugun ji da mugun gani a zuri'ata,ƴar cikina da RAWA? ina ƴar malamai jikar malamai? El-mustapha kar ka ci amanar tarbiyya,yara nawa ne suke burge ka saboda ilimin su na addini da na zamani har ka ke taimakawa rayuwarsu ta ci gaba? Me yasa ba zaka ɗora ƴarka a wannan turba ba sai ka biyewa shaiɗan? Ya Allah ka kawo min mafita mafi alkhairi,Allah ka tsare min zuri'ata daga lalacewar zamani.' A hankali Aminee ta ja jiki zata bar ƙofar ɗakin Lamya,tana juyawa ta ci karo da Aminullahi yana tsiyayar da ruwan hawaye,da sauri ta hau goge idanunta tana ƙaƙalo murmushin dole,girgiza masa kai ta yi saboda ta kasa magana,da gudu yaron ya isa gare ta ya rungumeta ya fashe da kuka,cikin kuka yace. "Ammi ki yi haƙuri,Baaba ne yayi miki faɗa ko?" Aminee bata iya bashi amsa ba sai shafa cikakkiyar sumarsa mai taushi da santsi take yi,a haka ta ja hannusa suka koma parlour,Iya ta gani zaune jiki yayi mata sanyi ƙalou,nan take Aminee ta gane ta ji duk faɗan da El-mustapha ya yi mata kenan,share hawayenta ta yi cikin yaƙe ta cewa Iya. "An ganta,ashe tana ɗakina,duk bamu yi hasashen zuwa can ba." Girgiza kai kawai Iya tayi,cikin sanyin murya ta ce. "Ki yi haƙuri Uwar ɗakina zan yi maki wata maganar da bata shafe ni ba,amma don Allah ko dan gaba kar ki sake marin yarinyar nan a gaban mahaifinta,ke marin ma da kika yi mata ya fi ƙarfin shekarunta,kin kuwa kula da yanda ta gigice? Yanzu da da akwai tsautsayi ai sai ta kurumce. Na sani kalaman mahaifinta sun yi maki zafi ƙwarai,to ki sani Allah ne ya taimake ki,yana girmama ki,yana ganin mutuncin ki,sannan wata fuskar tafi gaban mari,amma ba dan haka ba,da wani ne kina ajiye hannun ki zai falla maki mari har da ƙari akan wanda kika yi mata." A razane Aminee ta kalli Iya ta ce. "Kina nufin sai namiji ya ramawa ƴarsa mari dan uwa ta hukunta ƴar da ta haifa?" "Fiye da haka ma,dan wasu sanadin rabuwar auren su kenan,suna son juna amma akan tarbiyyar yara sai a raba jiha,dan haka ki dinga kai zuciyarki nesa. Addu'a ita ce babban abinda za ki dinga yi mata,sannan ki dinga yawan zama da ita kina yi mata nasiha tare da nuna mata illar abinda take so,sai kuma kema ki haƙura da kallon fina-finan hindiya a gidanan." Nan take Aminee ta gano inda ta yi kuskure,bata mantawa tin Lamya na da ciki,idan ta zo motsa jiki akai sa'a an saka waƙoƙin india ko na turanci takan bi waƙoƙin dake tashi a Talabijin ɗin ta hau juya jikinta,wanda ita a wajenta ba rawa take yi ba,hasalima bata iya rawarba,bayan kuma ta haihu nan ma bata da aiki sai kallo,har Lamya ta yi wayo ta gane me ake yi a talabijin,sai rawa da waƙa suka fi burgeta da ɗaukan hankalinta,ko an saka wa'azi ko karatun ƙur'ani za ta bar parlour ta shiga ɗakin mahaifiyarta ta kunna inda tasan ana rawa da waƙa ta hau kallo tana bin su,shi yasa ta ƙware sosai a rayawa ta kuma iya waƙoƙi da yawa fiye da yanda ta iya karanta ƙur'ani. Nan take Aminee ta ƙudurta a ranta zata dage wajen koyar da ƴarta binda ya dace ta kuma dena kallon idan hakan zai kawar mata da tunanin dake kanta. Ga Aminullahi nan zama da ita har ya kusan sauke sittin, me yasa ƴar cikinta zata zamo daban? Tin daga wannan ranar El-mustapha ya ɗaukewa Aminee wuta,abinda basu taɓa yi ba kenan tin farkon auren su,da kansa ya siyo sabuwar TV ya haɗa a ɗakin Lamya sannan ya bata damar kallon duk tashar da take so,duk wata shaƙuwa dake tsakanin Lamya da mahaifiyarta sai ya ragu,saboda tana ganin bata yi mata so irin wanda mahaifinta ke yi mata. Ga alƙawarin sanyata a ajin koyon rawa da yayi mata. Watarana suna kwance a ɗaki El-mustapha ya juyawa Aminee baya kamar yanda ya tsiri yi,sai ta matsa kusa da shi ta ɗora hannunta a bayansa ta hau shafawa a hankali,har ta zagaya cikinsa,rintse idanu yayi yana jin kewarta da yayi na bijiro masa,ji yayi kamar ya juya ya rungumeta,sai dai ba zai yi hakan ba gudun kar ta ji daɗi ta ga abinda ta yi daidai ne,a shagwaɓe Aminee ta ce. "Haba Baaban Aminullahi ka yi haƙuri mana,yau fa satin mu uku baka kula ni,baka cin abinci in dai ni na dafa,me yayi zafi haka,ko dai ka dena so na ne? Na shiga uku ni Aminatu marainiya ina zan saka raina idan ka dena so na mutuwa zan yi." Kuka Aminee ta fara yi,tun tana yin na ƙarya har hawaye suka fara zuba a idanunta,kasa jure sauraron sautin kukanta yayi,sai ya juya a hankali ya rungumeta,sumbatar goshinta yayi,sannan cikin wata iriyar murya mai fitar da sauti a ƙirji ya ce. "Ki yi shiru haka ya isa,waye ya ce miki na dena son ki? Idan na dena son ki wa zan so? Halayyar da kika ɗauka ta dukan yarinyata ne ba zan ɗaukar maki ba,duk rashin jin da Aminullah yake yi kin taɓa dukansa? Me yasa zaki dakar min yarinya irin haka? Kin san da cewa sai da ta yi kwana biyu tana zazzaɓi kuwa? Me yasa...." Bakinsu ta haɗe waje ɗaya ta hana sa ci gaba da janjanin maganar,dan ta kula El-mustapha mita ne da shi,idan wani namijin ne da yayi faɗa a ranar ya wuce,sai gashi shi har an yi satittika bai manta ba,bata taɓa sanin wannan ɓangaren nasa ba sai da ta taɓa ƴar gwal. Wata iriyar soyayya suka darza wadda suka yi kewa,suka jima ba su yi kalar ta ba,tun daga wannan ranar suka shirya,suka koma rayuwarsu kamar babu abinda ya taɓa faruwa a tsakaninsu. Aminee tana iyakar ƙoƙarin ta dan ganin bata takurawa Lamya ba,sannan kuma a gefe tana ta koyar da ita karatun addini da bayanai akan haramcin rawa da waƙa,duk wani karatu Lamya na kwashewa amma fa zuciyarta bata taɓa  mantawa da rawa da waƙa ba,balle ta ji wai ba zata ci gaba da yinsu ba a rayuwarta. Bayan wata uku da faruwar hatsaniyar gidan El-mustapha,suna zaune suna kallo da daddare wayarsa ta hau ringing,cikin azama Aminee ta tashi ta cire a caji ta miƙa masa,karɓa yayi yana bin lambar da kallon mamaki,yau shi ake kira kuma daga garin su? Tunda ya baro ƙasar su babu wanda yake kiransa daga danginsa,sai dai shi ya kira yaransa ko ya tura musu kuɗi,sai gashi yana zaune ya samu kira da lambar ƙasar su. Cikin sanyin jiki Aminee ta yi masa nuni da ya ɗauki wayar,a hankali ya sa hannu ya ɗauki kiran ya kai kunnensa. Sallamar da aka yi masa ya amsa cikin sanyin jiki,ya jima yana sauraren mai kiran nasa kafin ya ce. "Hasbunallahu wa ni'imal wakeel." Sauke wayar yayi daga kunnensa sannan ya kalli Aminee ya ce. "Yayana ne ya kira,wai ƙanin mahaifina ne bashi da lafiya yana kwance a gadon asibiti,shine ya bada umarnin a kira masa ni duk inda nake akwai abinda yake so ya bani." Cike da mamaki Aminee ta ke kallon El-mustapha,kafin ta ce. "Ikon Allah! Allah Ya bashi lafiya ya sa kaffara,to yanzu ya kenan? Za ka je ɗin ne ko kuma yaya?" "Babu inda zan je gaskiya,baki san me suka yi min ba a rayuwa,koma me zai bani ya bawa wani bana so." Ganin ransa ya ɓaci ne ya sanya Aminee yin shiru bata ce komai ba,sai kawai suka ci gaba da kallon su,a hankali ta kula gaba ɗaya yayi sanyi ƙalaou,a jima a jima sai ya duba wayarsa ya sauke ajiyar zuciya,ganin haka ne ya sanya ta tashin yaran kowa ya nufi ɗakinsa,kashe kayan kallon ta yi suka koma ɗaki. Bayan sun yi shirin bacci ne Aminee ta zauna a gefen El-mustapha ta kwantar da kanta a saman kafaɗarsa,cikin taushin murya ta ce............. [9/11, 10:50 AM] zee hussain: ƳAR RAWA. RUBUTAWA:HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✍️✨ PAGE :9 "Na tabbata mijina baya daga cikin mutane masu yanke zumunci da ƴan'uwansu saboda ɓacin rai ya haɗa su ko saɓanin fahimta,domin kai mai ilimi ne,ka san cewa Annabin Rahama ya gargaɗe mu akan yanke zumunci,duk wanda ya yanke zumunci da ƴan'uwansa to ya yanke hanyar shigarsa aljannah ne,dan haka na baka goyon baya ɗari-bisa-ɗari ka je ga ƴan'uwaka,idan har ka gayyace mu ni da Lamya ba zamu ƙi karɓar goron gayyatar ba." Kallon kyakkyawar fuskar Aminee El-mustapha yayi,ya ga babu wasa ko zolaya a cikin maganarta,rungumeta yayi,yana jin wasu irin zafafan hawaye na sauka daga idanunsa zuwa kuncinsa,lallai Aminee mace ce mai fahimta,sannan kuma mace ce mai dogon nazari da son sa da alkhairi,da wata ce zuga sa za ta yi ta hana shi komawa zuwa ga danginsa. Ya amince zai koma ya duba ɗan'uwan mahaifinsa,amma fa ba zai taɓa sakin jiki da ƴan'uwansa ba,dan ya san ko su ɗin su wanene. Washegari da safe El-mustapha ya fara yiwa su Aminee shirin tafiya Dubai,suna dawowa daga immigration office sai suka wuce gidan su Mus'ab da yamma,a daidai wannan lokacin Aminullahi yana makaranta. Suna zuwa suka zauna suka sha hirar su,sai suna daf za su tafi gida ne El-mustapha ya sanar da su Mus'ab maganar komawa Dubai da za su yi. Cike da matsananciyar damuwa Mus'ab da Aisha suka yiwa ɗan'uwan mahaifin El-mustapha fatan Allah Ya basa lafiya,cikin ƙunci A'isha ta ce. "Amma dai ɗan'uwana idan kun tafi kuna dawowa da wuri ko? Dan dai gaskiya tafiyar ku za ta taɓa rayuwar Aminullahi sosai,ni kaina zan yi kewar ku." Jiki a sanyaye Aminee ta ce. "Tun jiya da muka yi maganar tafiyar tunanin Amin ɗina ne ya hana ni sukuni har na kasa isasshen bacci,ga Lamya yanzu da ta saba da Yah Amee ɗinta,matuƙar aka raba su zata yi kewa." Haka su A'isha suka dinga tattaunawa aka shaƙuwar yaran nasu suna jajantawa,Lamya kuwa tinda ta gane ana maganar raba ta da Yah Amee ɗin ta ne sai ta fara kuka,duk yanda suka yi dan su ga sun bata haƙuri ta dena kuka ƙi ta yi,a haka suka yiwa su Mus'ab sallama suka tafi kowa zuciyarsa babu daɗi. A hanya Aminee ke cewa El-mustapha. "Oumry ka san me? Ba dan kar a ga haɗamata ba Allah da mun tafi da Aminullahi,to idan muka tafi da shi Yayata za ta zauna ita kaɗai,duk da naga hakan ita bai dame ta ba,amma mutane za su yi ta surutu akai." "Gaskiya dai kam,be kamata mu ɗauke sa mu tafi da shi ba,saboda idan muka yi haka mun yi son kai,mu yi addu'a kawai Allah Ya sassauta mana raɗaɗin rabuwa da juna,sanin Mus'ab da iyalansa alkhairi ne babba a rayuwata Rouh." "Na sani,ni kaina ina jin su a raina tamkar ƴan'uwana na jini." Da ire-iren wannan hirarrakin suka isa gida,a lokacin Lamya ta gaji da kuka har ta yi bacci. El-mustapha ne ya ɗauketa ya kai ta ɗakinta ya kwantar da ita. A zaune a parlour Aminee ta tarar da Aminullah yana cin abinci yana kallo,cike da so da ƙauna tare da tausayawa ta zauna kusa da shi tana shafar sumarsa,kallonta yayi cikin kulawa yace. "Ammi dan Allah idan Baaba zai fita ki dena binsa,bana jin daɗi a duk sanda na dawo daga makaranta na ga gidan babu ke a cikinsa." Murmushin ƙarfin hali Aminee ta yi kafin ta ce. "Ka yi haƙuri Aminullahi na,in Shaa Allahu watarana zamu kasance a inuwa ɗaya,mu zauna a tare zama na har abada." Kasa sanar da shi zancen tafiyar tasu tayi kamar yanda ta ƙudirta,sai kawai ta baza masa sumar kansa irin yanda baya so a yi masa,ta na murmushi ta tafi,gyara kansa ya fara yana mita har ta ɓacewa ganinsa. Abincinsa ya ci gaba da ci yana kallo. Har su Aminee suka kammala duk wani cuku-cukun tafiya basu sanar da Aminullah ba,saboda basu son ganin damuwarsa,shi yasa ta gargaɗi Lamya da sanar da shi,tare da tsorata ta ce mata idan ta sanar da shi to fa za su tafi su barta a Nijer,a ranar da za su tafi da yamma ne El-mustapha da Aminee suka ɗaukesa a mota suka kaisa gida haɗe da kayansa shi da Iya. Iya kanta hawaye take ta sharewa,saboda tsananin kewar su da ta fara ji,ga kuma uwar kyautar da El-mustapha da Aminee suka cika ta da shi. Suna isa Mus'ab ya tare su suka gaisa,sannan ya kwashe kayan Aminullahi ya kai ciki, A'isha ce ta fito daga cikin gidan idanunta sun yi jawur saboda kukan da ta ci,a mota ta tarar da Lamya da Aminee wadda ta ke ta sharar hawaye da sharce majina,tana hango A'isha na tafe sai ta buɗe marfin motar ta isa gareta da gudu suka rungume juna,Lamya kuka su A'isha kuka,a wannan lokacin ne Aminullahi yake tambayar abinda ke faruwa,cikin kuka Aminee ta rungumesa ta na yi masa bayani,wani irin ƙwacewa yayi daga jikinta yana bin kowa dake gurin da wani irin kallon kun ci amanata,cikin tsananin zubar hawaye ya kalli Aminee ya ce. "Ammi me yasa? Me yasa baki sanar da ni shige da ficen da kuke ta yi ba kenan? Me yasa za ku yankewa zuciyata farin cikinta a lokaci ɗaya? Me yasa ba za ku tafi dani ba? Ko dan ba kune ku ka haife ni ba?" Kuka sosai Aminee take yi,har ta kasa tsayuwa sai da ta zube guiwowinta a gaban Aminullahi ta kama hannayensa,da sauri ya fisge hannayensa yana bin Lamya dake kuka da kallo,cike da wani irin kallon da kowa ya kasa fassara irinsa ya ce mata. "Kin iya surutu kamar aku,amma kika kasa sanar dani abinda ke faruwa,na ɗauka ke ɗin ƙanwata ce,ashe kallon ɗan da ake yiwa riƙo a gidan su kike yi min,sai watarana Lamya,nima daga yau zan zauna a gidan Ubana ba zan sake zama da kowa ba." Cikin zafin nama ya kaucewa riƙon da El-mustapha yayi masa ya ruga da gudu cikin gida yana wani irin kukan dake fita daga zuciyarsa. Aminee ce ta yunƙura zata bisa ciki ta lallashesa,amma Mus'ab ya hana ta,cikin damuwa ya ce. "Idan kuka shiga rarrashin wannan sarkin zuciyar tabbas za ku makara,jirgi kuwa baya jiran kowa,mu je kawai,na tabbata fushin na yau ne kawai,da kun isa kuka yi waya zai warware,ai har abada Aminullahi ba zai taɓa fushi da iyayensa ba." Haka suka tafi ba dan sun so ba,har Airport su Mus'ab suka raka su Aminee,basu dawo ba sai da jirgin su Aminee ya tashi. Ko da suka dawo sai suka tarar da Aminullahi mai shekara goma zuwa sha uku yana zaune a ɗakinsa baya uhm baya um um,ya ƙurawa waje ɗaya idanu hawaye na zuba,gefen sa abinci ne da abubuwan sha da kayan marmari Iya ta ajiye masa. Cike da damuwa A'isha ta ce. "Aminuna ɗauki ka ci abinci mana? In Shaa Allahu watarana za ku gana,ni da kaina zan kai ka har ƙasar su ka gansu." Cikin sauri ya kalli mahaifiyar tasa ya ce. "Kuna tunanin abinci zai ɗauke min damuwar dake cikin raina ne? Sannan ni bana son zuwa ko ina,yanda suka yakice ni suka tafi ba tare da sun sanar dani abinda ke faruwa ba tin fari,sun nuna min cewa ni ba nasu bane,Lamya ita kaɗai ce ƴar su,to nima zan jure rashin kulawar da nake samu daga wajen ki,zan zauna da ku duk rintsi,duk wahala,domin kune iyayena,na tabbata ba za ku taɓa guduna ba." Duk yanda su Mus'ab suka so fahimtar da Aminullahi dan kar ya shiga damuwa ne yasa ba a sanar da shi ba,ya ƙi ya saurare su,ƙarshe ma bar musu ɗakin yayi yana kuka ya koma parlour. Su Aminee kuwa tinda suka hau jirgi suke tunanin ɗan nasu da suke matuƙar ƙauna,labarai kala-kala Lamya ke ta basu game da kyautatawa da soyayyar da Yah Amee ɗinta ke bata. Bayan sun isa filin jirgin ƙasar Dubai ne,jirgi na tsagawa suka sauka,riƙe da ƙananun akwatunan su a hannayensu,suka tura suka sauka kamar kowa,sai da suka yi duk wani formalities da ake gabatarwa idan an sauka a jirgi kafin suka fita farfajiyar wajen da ake ɗaukan kaya,suna hango akwatunan su El-mustapha ya tafi ya kwashe musu suka tura suka fita waje,masu allon sanarwa na tsaitsaye suna jiran ƴan'uwansu. A nan take El-mustapha ya hango ɗaya daga cikin tsofaffin ma'aikatansa riƙe da allon sanarwa mai ɗauke da sunansa,cikin fara'a suka isa wajensa ya tafi da sauri ya rungume El-mustapha yana sumbatarsa,kayan su ya ja musu suka nufi wata hamshaƙiyar mota ya zuba kayan a ciki sannan El-mustapha ya buɗewa Aminee mota ya saka Lamya a ɗaya gefen,sai da ya tabbata sun zauna sannan ya shiga gaba driver ya ja suka tafi. Tinda suka shiga ƙasar Aminee ke rarraba idanu,bata taɓa ganin waje mai kyau irin wannan ba a duniya,to dama ita ina da ina ta je balle ta san duniyar? Dan haka ita da Lamya sai suka ci gaba da kalle-kalle har suka isa wani makeken waje,wanda Aminee na karantawa ta gane asibiti ne. El-mustapha ne ya buɗe musu mota da kansa ya kama hannun Aminee ya ɗauki Lamya,suna tafe cike da tsantsar soyayya da kulawa El-mustapha ya ce. "Idan mun shiga duk kallon da kika ga ana yi miki a ciki ki jure,kar ma ki nuna musu kin ga suna yi balle ya dame ki kin ji? Abu ɗaya zaki saka a ran ki zuwa biyu;mijinki na masifarrr son ki,da ace iyayensa na raye da zaki ga gatan da baki taɓa ganin an yiwa wata suruka ba a duniya." Da sauri ta gyaɗa masa kai tana murmushi,sumbatar goshinta yayi, suka ci gaba da tafiya kamar tsofaffin masoyan nan da soyayyar su bata tsufa. Kamar yanda El-mustapha ya sanar da ita kuwa haka ta gani a idanun wasu gungun maza dake sanye da fararen jallabiyya sai ɗan rawanin nan na larabawa,da sauri Aminee ta sake maƙalewa a jikin El-mustapha ta damƙe rigarsa ta baya,a haka suka isa gaban mutanen,cikin fara'a El-mustapha ya kalli ƴan'uwansa dake ta muzurai ya gaishe su,amsawa suka yi sama-sama,sanan cikin kallon tsana babban yayansu yayi masa nuni da ɗakin da Baffan nasu ke kwance. Ko tsayawa gabatar musu da Aminee da Lamya bai yi ba ya dirfafi hanyar ɗakin,yana zuwa sai ya kama hannun ƙofar ya murɗa suka shiga. Kwance farin dattijon yake yana kallon ƙofa,suna haɗa ido da El-mustapha sai ya hau hamdala tare da yin wani irin tari,ƙarshe sai ya fashe da kuka,cikin shaƙaƙƙiyar muryar da bata fita sosai ya kira El-mustapha yana yafitarsa akan ya je gare sa. El-mustapha na zuwa dattijon nan ya hau laluba jikinsa,a haka ya zaro wani envelope mai ɗauke da takardu ya miƙawa El-mustapha,yana hanninta masa takardun ƴan'uwan El-mustapha suka shiga ɗakin,idanun su ya sauka a kan envelope ɗin da ke hannunsa. Kalmar shahada suka ji dattijon na yi yana shaƙuwa,cikin sauri yaran dattijon da kuma su El-mustapha suka yi kansa cike da damuwa,duk yawan danginsa dake wajen da kulawarsu a gare shi bai hana mutuwa ɗaukansa ba. Kuka wajen ya rikice da shi,basu wani jima ba aka basu gawarsa suka yi gida da ita. Bayan an yi masa wanka ne an sallaci gawar Baffan su El-mustapha ne,sai suka kaisa gidan su na gaskiya suka rufe. A wannan rana El-mustapha ya tuna da mahaifansa ya yi kukan rashin su sosai,da ƙyar Aminee ta rarrashe sa ya haƙura,daga gidan Baffansa sai driver ya ɗauke su ya kai su gidan su. Aminee ta yi mamakin ganin kalar dangi da gidan da El-mustapha ke ciki,daga baya sai ta dena mamaki,saboda ta san ko a Nigeria da Nijer yana da tarin dukiya mai ɗinbin yawa,haka suka shiga gidan suna ta kalle-kalle ita da Lamya. El-mustapha kuwa ɗakin sa ya shiga ya zazzage takardun dake cikin envelope ya hau dubawa,wata takarda ce ta ɗauki hankalinsa a ciki,cikin sauri ya ɗauke ta ya hau karantawa......... [9/11, 10:50 AM] zee hussain: ƳAR RAWA. RUBUTAWA:HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✍️✨ PAGE 10. Hannayensa na rawa ya ƙarasa warware takardar,cikin sanyin murya ya fara karantawa. _Assalamu alaikum Ya kai ɗan ɗan'uwana. Ina fatan sanda wannan takarda zata riske ka kana cikin ƙoshin lafiya. Da fari dai ina mai neman afuwar ka bisa ga riƙe maka dukiya da na yi ba tare da sanin ka ko amincewar ka ba,ban yi hakan da nufin cutar da kai ba. Na yi ne saboda in janye hankalin ƴan'uwan ka daga ƙiyayyar da suke yi maka,sai dai kashh ! Na gano cewar ba za su taɓa hutawa ba a duniya har sai sun raba ka da dukiyar ka gaba ɗayanta,ko kuma su raba ka da rayuwar ka kamar yanda suka haɗa baki da ƴaƴan cikina suka bani gubar da na tabbata ita ce za ta yi ajali na. Ka yafe min ya kai ɗan ɗan'uwana,ina fatan kafin in koma ga Allah in damƙa maka dukiyar ka da hannuna._ Hawayen da suka wanke wa El-mustapha fuska ne suka yi sanadiyyar rufe ganin sa,a ƙasa ya zauna tare da dafe kansa da dikkanin hannayensa,fashe wa ya yi da kuka a lokacin da ya tuna ranar da iyayensu suka rasu,sun rasu yana matashin da babu cikakken hankali a gare shi,ya tabbata shi ne dalilin da ya sa baffan nasa raba dukiyarsa biyu ya adana masa rabi,babu wanda bai san irin ƙiyayyar da ƴan'uwansa ke yi masa ba,da ace yasan soyayyar da iyayensu ke nuna masa a zahiri zata zamo silar ƙiyayyar nan da ya hane su nuna masa tsananin so da ƙaunar da suke yi masa a fili,a yau ya gano dalilin da ya sa ko ƙur'ani yake karantawa ya zo suratul Yusuf yake kuka kamar zai haɗiye zuciyarsa. A cikin wannan yanayin Aminee ta tarar da mijin nata,ba tare da ta dame sa da son jin dalilin kukan sa ba,sai kawai ta karɓi takardar hannunsa ta ninke ta mayar cikin envelope ɗin ta je ta yi musu kyakkyawar ajiya sannan ta dawo wajen mijin nata,a tsakiyar ƙafafunsa ta zauna tana fuskantarsa,sumbatar laɓɓansa ta fara yi zuwa hanci da idanuwansa kafin daga baya ta sanya hannayenta ta rungumesa da kyau a ƙirjinta,sake kwantar da kansa ya yi a saman kanta yana ƙoƙarin daidaita kansa saboda hango damuwa da yayi a idanunta,shiru suka yi suna sauraron bugun zuciyoyinsu ba tare da sun cewa juna komai ba. Sun jima a haka kafin a hankali El-mustapha ya ce. "Ban taɓa sanin dukiya na zamo wa bawa musiba ba sai a kaina,Rouh ina son ƴan'uwana sosai,sai dai dukiyata ta yi min katanga da samun soyayyar su,ban san me yasa suke so su karɓe tawa dukiyar ba su ƙara akan tasu wadda ban san iyakarta ba." "Kar ka manta Allah da kansa ya ce dukiya da ƴaƴa ado ne na gidan duniya,wannan dalilin ne ya sanya kowa yake da burin mallakar su,sannan su ɗin kuma fitina ne ta wani ɓangaren,shi yasa ba kowa ke iya mallakar su ba ya basu kulawar da ta dace har ya more su duniya da lahira,ko kuma su amfanar da shi ta hanyar da ta

Chapter 5 of 30