Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
dace,ka yi haƙuri ka ƙara haƙuri,sannan ka riƙe addu'a,ka kyautata musu fiye da yanda kake yi musu a yanzu,na tabbata watarana wannan ƙiyayyar zata koma soyayya." "Humm Aminnatu ba zaki gane yanda ƙiyayyar balaraben mutum take ba,idan ya ƙi abu sai ya ga bayansa hankalinsa ke kwanciya,haka zalika idan ya so abu,sai ya mallaki abun hankalinsa ke kwanciya,yana da matuƙar wahala balaraben mutum ya saki abinda ya ke zuciyarsa cikin sauƙi,wannan dalilin ne zai sa na yanke hukunci,zan tattara wannan dukiyar gaba ɗaya na damƙa musu ita,ina da arziƙin da ban san iyakarsa ba a Nigeria da Niger,Allah Ya sanyawa kasuwanci na albarka,dan haka zan rabu da dukiyar nan na huta Rouh, wataƙila idan na yi haka su sassauta min." "Idan ka yi hakan ma ba ka faɗi ba Oumry,kai ne ke da riba in Allah ya yarda,ina son ka mijina mai haƙuri da tawakkali,Allah Ya tsare min gaban ka da bayan ka,Allah Ya shiga dikkan lamuran ka." Murmushin jin daɗin addu'o'in da ta yi masa ya saki,a hankali ya fara sauke mata zazzafar sumbatar da ta sanya ta sake mannewa a jikinsa tana sauke numfashi da sauri da sauri. Bayan sati biyu da rasuwar Baffan El-mustapha,ranar Juma'a da yamma lis suka shirya shi da Aminee da Lamya suka shiga mota,da kansa ya tuƙa su ya kai su babban gidan su,wanda anan ne iyayensu suka yi rayuwa, sannan kuma anan ne suke haɗuwa duk Juma'a domin sada zumunci,suna yanka raguna su gasa su,sannan ayi girke-girke da kuma dafa shayin gahwa,da sauran kayan marmari a haɗu manya da ƙanana a ci a sha,a yi wasanni da raye-raye irin nasu na larawa,masu shan sigari da bushe-bushen shisha kuwa haka za su yi ta hura hayaƙi abun su,idan sun gama kuma za su rabu cikin farin ciki. A irin wannan taron ne kuma idan suna da wata matsalar da take fuskanto su suke tattaunawa akanta har su samar wa kawunan su mafita. Gida ne mai matuƙar girma da manyan parlour guda takwas, sai wajen shaƙatawar dake gefen gidan wanda idan ana tsananin zafi a ƙasar anan suke taruwa da yamma su yi walimar su kowa ya watse. Da isar su mai gadi ya buɗe musu kantamemen gate ɗin gidan, El-mustapha ya shigar da motarsa ciki,Aminee da Lamya baki suka buɗe suna kallon makeken gidan da suka shiga,wanda ya kasance anan iyaye da dangin gwarzon su ke,da kansa ya buɗe musu mota suka fita,ɗaukar Lamya ya yi sannan ya riƙe ƙugun Aminee suka taka suka nufi cikin gidan,a nan take aka samu wani daga cikin masu kula da gidan ya kira babban yayan su El-mustapha ya sanar da shi zuwan sa da iyalinsa,da jin haka shi kuma sai ya sanar da sauran ƴan'uwansu babban baƙon da suke da shi,nan da nan hayaniya ta tashi a tsakanin su,kowa na faɗar ra'ayinsa game da yanda za su yi wa ƙaramin ƙanin nasu da bashi da wani buri a rayuwarsa sai na su so shi su ja shi a jiki. El-mustapha kuwa bai je ga ƴan'uwan nasa ba har sai da ya kai su Lamya wajen matar babban yayansu dake cikin gidan da zama tare da dika iyalansa,a wulaƙance ta karɓi gaisuwar da su El-mustapha suka yi mata,tana bin Lamya da kallo,bata haƙura ba har sai da ta kai ga taɓa fatar Lamya da bata da makusa ta ko ina ta ce. "Da ace ka auri Zainab ƙanwata da tuni kun haifi fararen yara kamar ka,sai dai kashh! Taurin kai ya hana ka zaɓi macen da ta fi maka alkhairi." Cike da murmushin takaici El-mustapha ya ce. "Na rantse maki babu wata mace da ta fi min Aminatu alkhairi a rayuwata,babu kuma macen da zata fi min ita alkhairi har ƙarshen rayuwarmu." Hannun Lamya ya kama suka bar sashen nata suka nufi wani waje da yake a buɗe,yana ɗauke da kujeru gefe kuma ga ruwa nan mai kyau an saka fitilu suna ta haska wajen gwanin ban sha'awa,kallon Aminee ya yi ya ce. "Bari in je in dawo,kar ku bar nan wajen komai rintsi komai wahala,duk wanda ya takura maku ki kira ni a waya zan zo gare ku,komai mutuncin da wani zai nuna maku kar ku yarda da shi,kar wani ya baku abinci ko abun sha ku karɓa." Gyaɗa kai Aminee ta yi cike da tsoro ta samu waje ta zauna,tare da rungume Lamya a jikinta sosai,kalaman matar da suka je wajenta ne ke ta dawo mata a rai,sai dai amsar da El-mustapha ya bata ya wanke mata baƙin cikin ranta,sai ta hau murmusawa tana bin bayan gwarzon mijin nata da kallo har ya ɓacewa ganinta. A zazzaune ya tarar da su fuska a cunkushe,hakan ne ya tabbatar masa da cewar sun san da zuwan sa,dan haka sai ya saki fuska ya isa gare su ya dinga gaishe su ɗaya bayan ɗaya. Yana gamawa sai ya yi musu ta'aziyyar ɗan'uwan mahaifinsu,cikin sauri babban yayansu ya katse shi,ta hanyar ɗaga masa hannu ya ce. "Dakata malam,sanar damu dalilin zuwan ka gare mu,bayan da kan ka ka bar ƙasar ka ta gado,ka tafi ƙasar talakawa har ka yi aure a can,gashi ka gurɓata mana zuri'a da baƙar fata." Nan take fara'ar fuskar El-mustapha ta ɗauke,cikin tsananin nuna ɓacin ransa ya wurga takardun dukiyarsa tsakiyar wajen sannan ya kalli babban yayansa ido cikin ido ya ce. "Kada ka sake kiran zuri'ar da Allah ya bani a matsayin gurɓatacciya,a wajen ku ne take gurɓatacciya,amma a waje na ta fiye min ku da duk wani nawa da yake baƙin cikin samuwa ta a cikin wannan ahali,dukiya kuke so ko? To ga dukiya nan,ku riƙe ku barni na rayu a ƙasa ta cikin salama da iyalina." Cikin sauri wani ɗan lukuti ya ja mazaunan sa ya ɗauki takardun fuska a washe ya hau dubawa,yana gama dubawa ya ɗaure fuska,harshe na zazzagowa yawu na tsartuwa ya ce. "Ina sauran? Wannan ai ba ita kaɗai ba ce,kar ka manta,Baffan mu na daga cikin mutane goma da ake lissafa wa suna da arziƙi a garin nan,dan haka na tabbata ba iya dukiyar ba kenan." Murmushin takaici El-mustapha ya saki kafin ya ce. "Abinda na yi niyyar baku kenan,tunda dai dukiya ta ce ba ta wani ba,sauran na bawa iyalan Baffan mu suma su juya su ci gaba da rayuwa cikin walwala kamar yanda suke yi da rayuwarsa,dan haka ku karɓi abinda na yi niyyar baku idan za ku karɓa." Har wani zai sake yin magana,sai Babban yayansu da ya kafe El-mustapha da kallo tun sanda ya yi masa magana akan zuri'arsa ya ɗaga musu hannu yana murmushi, kallon El-mustapha ya yi ya ce. "Mun gode za ka iya tafiya." Ko sallama El-mustapha bai yi musu ba ya sa kai ya wuce,zuciyarsa na tsananin ƙuna da raɗaɗi,yanda ya bar su Aminee haka ya tarar da su zaune suna zarar idanu,suna ganinsa suka miƙe suka nufe sa,ba tare da ya ce musu komai ba ya kama hannun su suka wuce motar su,sai da ya buɗe musu motar suka shiga sannan ya zagaya ya buɗewa kansa ya tashe ta,a guje ya bar gidan ya hau babban titi da su,ba gida ya kai su ba,sai ya wuce da su wani mall,Lamya ya kai wajen wasan yara,suka dinga wasannin su suna raha,kafin daga baya su shiga wajen da ake saida abinci,sai da suka ci suka ƙoshi sannan suka samu waje suka yi sallar magariba da isha'i,daga nan sai suka wuce cikin wajen da ake saida kaya,suka yi siyayya sosai. Haka suka bar wajen da kaya a hannayen su niƙi-niƙi,a mota kuwa Lamya surutu ta dinga yi tana cewa. "Baaba da ma mun zo da Yah Amee,na san da sai ya sa ka saya masa sabon video game ɗin da na gani,Baaba next time zan siya masa a kai masa,ko ya zo ya karɓa." Aminee ce ta taɓe baki saboda ɓacin ran siyowa Lamya wasu CD na waƙe-waƙen yara da yanda ake koyar da su rawa da El-mustapha ya yi,kallon ta ya yi ta gefen ido ya ga yanda take cika take batsewa,murmushi ya yi sannan ya zira hannunsa ya shafi kuncinta,kau da kanta ta yi ta kalli waje tana murmushi. Cikin wata iriyar murya El-mustapha ya ce mata. "Ki yi haƙuri Rouh,yarinya ce,watarana ba zata yi rawa da waƙa ba,ko da kuwa za a bata duniya da abinda ke cikinta ne." "Kafin lokacin kuma idan ta zubar da mutuncinta akan rawa da waƙa fa?" "Da yardar Allah hakan ma ba za ta taɓa faruwa ba." Ajiyar zuciya mai ƙarfi Aminee ta sauke kafin ta ce. "To Allah Ya yarda,Allah Ya kare mana ita daga sharrin shaiɗan da zamani." "Amin Ya Allah,haka nake so dake matata,ki dinga faɗar alkhairi game da rayuwar yarinyar nan,ki cire tsoron komai a ran ki." "Humm." Shi ne abinda ta ce kawai ta sake kauda kai gefe,a haka suka isa gida cike da matsananciyar gajiya. Wani irin duhu suka ga gidan nasu ya yi tin kafin su shiga cikinsa,cike da mamaki El-mustapha ya ke danna horn,shirun da ya ji ne ya sanya shi saurin fita daga motarsa ya shiga gidan da ƙafa, sai dai yana shiga hasken wutar ta dawo,idanunsa ne suka yi masa mummunan gamon da ya sanya shi ja da baya a firgice.......[9/11, 10:50 AM] zee hussain: ƳAR RAWA. RUBUTAWA:HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✍️✨ PAGE 11. Ɗaure ya tarar da mai gadin gidan nasa da sauran masu aikin sa da wasu irin robobo kamar na ɗaurin shanu,sai bakunan su da aka rufe da salatif bayan an cusa tsumma cikin su,cikin nishi mai gadin yake ƙoƙarin jan jikinsa zuwa wajen El-mustapha wanda tsananin tsoro da mamaki suka sanya sa tsayawa kamar wani gunki. Ganin mai gadin na ta yunƙurin kwance kansa ne ya sanya El-mustapha dawowa cikin hayyacinsa,da sauri ya ƙarasa gaban sa ya kunce sa,sannan ya isa wajen sauran masu aikin mutum uku ya kwance su,kallon ƙasa ya yi ya ga makaman su da suka ɗakko a yashe a ƙasa,cikin haki mai gadi ya ce. "Ba su yi nisa ba yanzu suka haura,za a iya kiran hukuma su nemo su da gaggawa,bamu san me suke so ba kawai muna zaune suka diro ta sama,suka hau mu da duka,suka ɗaure mu,sannan suka afka cikin gidan,sun ɗan jima a ciki kafin mu ga sun fito a gaggauce suka bar gidan ta inda suka shigo." Shiru El-mustapha ya yi yana nazari,cikin ransa ya ce. 'El-Hassan,El Hussain, Muhammad da Zaid sune za su yi min wannan abun,kuma duk yanda akai sun san duk wani motsina da na iyalina,da alama su suka sanar da su muna hanyar dawowa shi ne suka gudu.' Cikin dakiya da nuna jarumta El-mustapha ya danne damuwarsa ya ce. "Kar ku damu da kiran hukuma,tinda sun tafi shike nan,ga wannan ku sayi magani saboda ciwon jiki,Allah ya kiyaye gaba." Kuɗi ya basu masu ɗan dama sannan ya koma mota,ya ce wa Aminee su jira shi,zai shiga ya dawo akwai gyaran da ake yi a cikin gidan. Cikin sauri ya rufe motar bayan ya buɗe musu windows sannan ya sa mai gadi ya wangale gate suka tsaya kamar wasu dakaru suna gadin su Aminee da ke cikin mota,a gurguje ya shiga cikin gidan shi kaɗai,zuciyarsa a matuƙar tsinke,dan bai san me zai shiga ya tarar ba,kayan su ya gani a wargaje,alamar an duba wani abun a cikin gidan,murmushin takaici ya yi,cikin sauri ya hau gyara duk abinda suka ɓata,sai da ya ɗauki tsawon mintuna sha biyar yana gyara gidan,saboda har ɗakunan su suka shiga suka watsar da abubuwa,yana kammalawa ya koma waje a gajiye ya buɗe motar sannan ya shiga cikin gidan. Sai da ya taya su kwashe kayan sannan suka shiga ciki a tare,Aminee kuwa sai baza ido take yi ta ga gyaran da aka yi amma bata ga komai ba,hasali ma sai ƙasan tayals ɗin ta da ta ga alamar ƙasa,sai kace wanda aka tattaka,kallon El-mustapha ta yi za ta yi magana,sai ta ga fuskar shi a mugun ɗaure,damuwa bayyane a cikinta,shiru ta yi da bakinta ta shige da kayan ta ajiye su a inda ya dace,Lamya da ta yi bacci kuwa sai ya wuce da ita ɗaki ya kwantar da ita a gadon ta, addu'a ya tsaya ya yi mata sannan ya rufe ɗakin nata da makulli,ji yake yi ba zai iya rintsawa ba har sai ya yi magana da ƴan'uwansa da suke da tsananin son kan su da son duniya. Yanayin da yake ciki kaɗai Aminee ta kalla ta gane baya cikin walwalarsa,duk yanda ta so ta kwantar masa da hankali abun ya gagare ta,magana ake ta rayuwar ahalinsa da ya fi so da ƙauna a rayuwarsa. A haka Aminee ta wuce ta kwanta cikin umarnin da El-mustapha ya bata,ba dan ta so ta bar sa da damuwa a rai ba. Sai da ya tabbatar sun yi bacci sannan ya ɗauki wayarsa ya kira Muhammad,ta jima tana ringing tare da katse wa kafin daga baya ya amsa kiran nasa a zafafe ya ce. "Wai me yasa ka ke ta kirana haka kamar kana bina bashi?" A zafafe shima El-mustapha ya ce. "Kar ka ga kai ne babba a cikin mu ka saki jikin ba zan iya ɗaukan matakin hukuma akan ka ba,ina da ƴancin miƙa ku gaba ɗaya wajen hukuma akan abinda kuka saka a yiwa gidana,shin me kuke so daga gare ni ne? Rayuwata da ta iyalai na? Na faɗa maku na baku komai,na mallaka maku dukiyar gado na da wannan da na samu daga baya ko duba yawanta ban yi ba amma kun dame ni,to ku sa a ran ku zan fara farautar ku ɗaya bayan ɗaya idan baku ƙyale ni ba." Tsoro ne ya shiga zuciyar Muhammad da ya sanya wayar a handsfree sauran ƴan'uwan nasu suna saurara suma, El-mustapha kuwa yana gama isar da saƙon sa sai ya kashe wayar ya faɗa saman kujera yana maida numfashi mai zafi kamar wanda ya yi tseren gudu. A can ɓangaren su El-Hassan kuwa maganarsa bata wani shige su ba,Muhammad kuwa ya ɗauki gargaɗin El-mustapha da gaske,nan take ya ce. "Kun ga shawarar da muka yanke ɗazu ta rushe,mu dakata da duk wani shiri da muke yi akan yaron nan,mu barsa ya ci gaba da rayuwarsa,na tabbata tunda ya ce babu abinda ya rage to fa babu ɗin in dai ba rayuwarsa muke nema ba" A ɗage Zaid ya kalle sa ya ce "Idan kai ka janye ni ban janye ba,akan yaron nan babu abinda mahaifiyarmu bata yi min ba,tin da na taso nake jin tsanarsa a cikin raina,babu irin fifita war da ba a yi masa ba,komai akai sai ta ce ya fi mu hankali,ya fi mu natsuwa,haka zalika Abbun mu,komai zai yi sai ya kirawo ƙanin bayan mu ya ce shi zai ɗora akai,mu mun zama taron tsintsiya babu shara,ku ka sani ma ko cutar mu aka yi wajen raba gadon aka bashi mai yawa shi yasa dukiyar sa ta ƙi ƙarewa? Ina da labarin manyan kamfanonin da yake da su a Niger da Nigeria abokin sa da wasu amintattun sa suna juya masa,da ace za mu gano abokin da mun haɗa kai da shi an salwantar da dukiyar tasa baki ɗaya kowa ya huta da baƙin ciki." Zaid ya ƙarasa maganarsa yana numfarfashi tare da muzurai,sai wata uwar zufa yake zubarwa kamar wanda ya motsa jiki tsabar ƙiba. Murmushi Muhammad ya yi kafin ya ce. "Ina mai shawartar ku da ku ƙyale yaron nan ko da na wani lokacin ne,kar ku matsa masa,mutum mai haƙuri idan ya fusata ba ya yin aiki da hankali." Shiru suka yi suna nazarin maganar yayan nasu kafin daga baya su haƙura kan dole ba dan zuciyoyinsu sun so ba. Tin daga wannan ranar suka haƙura suka zubawa El-mustapha idanu cike da baƙin ciki da hassada,shi kuwa ya kama iyalinsa gam ya riƙe tare da ƙara matakan tsaro a gidansa da duk inda ya san yana da buƙatar hakan. Duk wannan bidirin da ake yi bai bari Aminee ta sani ba,balle kuma Lamya da bata jima da cika shekaru biyar ba a duniya. Mus'ab kawai ya kira ya sanarwa duk halin da yake ciki a ƙasarsa ta haihuwa,cike da damuwa Mus'ab ya ce. 'Ɗan'uwana ka dawo Niger ka zauna da iyalan ka cikin aminci,ko kuma ka koma Nigeria,kana da arziƙin da za ka kula da kan ka da iyalan ka koda baka ci gaba da neman kuɗi ba a yanzu,me yasa ka ke son ka ƙuntata wa kan ka akan mutanen da basu damu da kai ba?' "Ya Mus'ab shi zumunci ana yin sa ne domin Allah,to nima ina yin nawa domin Allah ne,babu abinda zai same ni da iyali na sai abinda Allah ya rubuta zai same ni,bayan haka ma na tauna tsakuwa dan aya ta ji tsoro,na tabbata a yanzu sun gane wannan El-mustaphan ba na da bane mai sanyin hali da kau da kai,na tabbatar musu da cewa akan iyali na babu abinda ba zan iya aikatawa ba." Ajiyar zuciya Mus'ab ya sauke mai nauyi,sannan ya ce. 'To shike nan Allah ya tsare ku ya kiyaye ku,Allah ya ganar da su ya haɗa kawunan ku.' "Amin ɗan'uwana,Allah ya saka maka da alkhairi akan yanda ka riƙe zumunci a tsakanin mu,ina ɗana? Yau bamu gaisa ba." 'Ya na makaranta,zuwa anjima idan ya dawo zan ce ya kira ka da sabuwar wayarsa,ka san sai da na bada cin hancin sabuwar waya sannan aka dena fushi.' Dariya El-mustapha ya yi,daga nan suka ci gaba da hira akan yaran nasu,da yanda suka yi kewar juna. *BAYAN SHEKARA TAKWAS.* Aminee ce zaune a saman kujera a parlour tana karanta ƙur'anin ta Lamya ta yi sallama ta shiga parlourn sanye da riga da dogon wando,kanta yane da mayafi kalar wandonta. Jakar bayan ta ta sauke ta ajiye a saman kujera sannan ta kwantar da bayanta a kujerar tana lumshe idanun ta,sai da Aminee ta kai aya sannan ta kalle ta zuciyarta babu daɗi ta ce. "Yanzu Aishatu ke kina ganin rawa abar so ce har kika yi duk yanda za ki yi mahaifinki ya sanya ki a makarantar koyon rawa? Humm Allah Ya shirya min ke." Mirgina kai gefe Lamya ta yi tana kallon mahaifiyarta da take ɗauke da tsohon cikin watanni takwas ta ce. "Ammi dan Allah ki dena damuwa akan rawar da nake yi,ba fa ta hana ni yin karatuna kin sani,kuma ba ita nake da burin ta zama aikin yi na ba,kowanne yaro akwai abinda ya ƙware akai, ma'ana baiwarsa,ni kuma rawa ita ce baiwa ta dan haka..." "Sam ba zan yarda ace wai rawa ita ce taki baiwar ba,kar ki manta a kullum ina faɗa maki cewar mahaifi na babban malami ne,mahaifinsa ma malami ne,sannan ni kuma na gado su dan sai da na koyar da manyan mata da yara kafin na auri mahaifin ki,mahaifin ki ya kasance mutumin kirki,mai taimakon talakawa,mai yiwa musulunci hidima,kawai sai ke ƴar mu ki zamo ƴar rawa da waƙa?" Shiru Lamya ta yi,dan kuwa ba wannan ne karo na farko da Aminee ke tasa ta a gaba da faɗa akan rawar da take zuwa koyo ba duk ƙarshen mako,da za ta iya cire son rawa da waƙa a zuciyarta da ta yi ta huta da surutun mahaifiyarta,amma a kullum jin son abun take yi a ranta,dan haka miƙewa kawai ta yi ta rataya jakarta a kafaɗa tana jin yanda ƙugunta da kafafunta ke yi mata ciwo ta ce. "Ki yi haƙuri Ammina,watarana sai labari,watarana da kuɗi aka ce ƴar ki Aishatu za ta yi rawa ba za tai ba,ki ci gaba da yi min addu'a,ni yanzu babbar damuwa ta be wuce na yanda ƙiriƙiri Yah Amee ya rufe ido ya ke kula kowa a gidan nan amma ni ya ƙi kula ni ba,sai dai saƙon gaisuwar da baya gajiya da aiko min,amma duk sanda na kira sa a waya da kaina daga gaisuwa baya sake ce min komai,ko dai ya tsane ni ne Ammi?" Murmushi Aminee ta yi kafin ta ce. "Da ace kin san yanda yake damuna da tambayar ki da baki damu kan ki ba,jan aji ne kawai irin na Aminuna yake yi maki,dan haka kema ki fara ja masa ajin,ki dena kiran sa idan ba shi ya kira ki ba,zaki gani,da kansa zai neme ki." "Na matsu na kammala makarantar nan mu kai musu ziyara." "To sai ki bada himma sakamakon ki ya yi kyau,dan dai kin san abinda Baaba ya ce,idan sakamakon ki be yi kyau ba babu inda za ki je,anan zamu bar ki mu je mu dawo." Tura baki Lamya ta yi,ta wuce ɗakinta a gajiye,tana shiga wanka ta faɗa ta gasa ƙugunta da cinyoyinta sannan ta yi alwala ta gabatar da sallar magariba,abinci ta koma parlour ta ci sannan suka hau kallo,babu jimawa El-mustapha ya dawo,cikin murna da farin ciki suka nufe sa gaba ɗayan su,cike da tsananin ƙaunar su ya rungume su tare da sumbatar su,sannan suka rankaya suka koma parlour,hira suka dasa kafin Aminee ta gama haɗa masa abinci ya sauka ƙasan shimfiɗar da ta yi masa ya fara cin abincinsa. Duk wata al'adar larabawa Aminee ta iya ta,sannan sun fi yin yaren larabci da hausa a gidan,duk da cewa Lamya na yawan yin turanci saboda makarantar boko da take halarta,amma dai yaren larabci suka fi yi,shi yasa ma hausarta take kamar ta ƴan koyo,watarana idan suka gaisa da Aminullahi sai ya jima yana dariyar hausarta a bayan idanunta. A ɓangaren Aminullahi kuwa zuciyarsa cike take da kewar su El-mustapha,saboda ya kasa manta karamcin da suka nuna masa da soyayyar da suka bashi wanda iyayensa ba su bashi irinta ba,yana jin ƙaunar Aminee a ran sa kamar ita ta haife sa. Lamya kuwa ya bata wani babban matsayi ne a ransa wanda yake jin zai iya bada komai nashi dan ya ganta ko da sau guda ne a rayuwarsa,sai dai kashh nisan da suka yi da kuma shekarun da ke ja a tsakanin su ya sa shaƙuwar da suka yi a hankali tana ja da baya,shi ne dalilin da ya sa bai cika sakewa da ita su yi hira ba,sai dai ya dami Ammin nasu a waya ta bashi labarin Lamya,babban abinda Ammin sa ke yi masa ƙorafi akan Lamya shine rawar da ta ɗauka da mahimmanci fiye da karatun ta,a duk sanda ta yi masa wannan ƙorafin sai dai ya bata haƙuri,ya ce mata yarinta ke damun ta,watarana za ta dena ne. A haka take haƙura da ƙorafin ta ta ce shima kamar Baaba yake basu son laifin ta. Cikin Aminee na da watanni tara da sati ɗaya naƙuda ta kama ta,cike da damuwa El-mustapha ya ɗauki waya ya kira nurses ɗin dake zuwa har gida suna kula da Aminee,a cikin zuciyarsa kuwa Iya yake tunawa,a lokacin haihuwar Lamya ita ce ta tsaya ta yi musu komai cikin so da ƙauna da kulawa,fatansa shine Allah ya sauki Aminee lafiya,sannan ya sa nurses ɗin su bata kulawar da ta dace. Nurses ɗin na zuwa sai suka haɗa duk wani abinda ya dace,ɗayar su ta duba Aminee ta ga haihuwar ta zo gab,sai ta kori Lamya da ta maƙale a jikin Aminee ta na kuka,tinda take a rayuwarta bata taɓa ganin mahaifiyarta cikin damuwa ko ciwo mai tsanani irin wannan ba. Murmushi Aminee ta yi mata sannan ta ɗaga mata hannu tana yi mata nuni da ta bi umarnin Nurse ɗin ta je waje. Tana fita babu jimawa kukan jariri ya karaɗe cikin gidan, hamdala El-mustapha ya dinga yi kafin ya leƙa waje hannunsa ɗauke da yaron da ko goge sa ba ai ba ya miƙawa Lamya shi,cike da murna Lamya ta karɓe shi idanunta na zubar da hawaye ta ce. "Baaba da wanne suna za a kira shi?" "Mubarak." Cikin tsananin murna Lamya ta ce. "Allah ya raya mana Mubarak Baaba,ina Ammi?" "Bari a gama gyara ta sai ki je ki ganta,kawo shi na kai musu shi a gyara shi." Babu musu ta miƙa yaron El-mustapha ya koma da shi ɗakin,fuskar sa ɗauke da matsanancin farin ciki,Lamya kuwa wayarta ta ɗakko ta hau neman layin Aminullahi,dan kuwa so take ta zama mutum na farko da zata sanar da shi wannan daddaɗan labarin......... [9/11, 10:50 AM] zee hussain: ƳAR RAWA. RUBUTAWA: HAMIDAH SUNUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✍️✨ PAGE 12. Da sallama ya amsa wayar tare da lumewa a cikin kujerar da yake kai, cike da shauƙi tare da kewar ta mai tsanani ya buɗe baki ya ce. 'Alhamdulillah,ya jikin Ammi? Ina fatan tana lafiya' Murmishi Lamya ta yi kafin ta bashi amsa da. "Eh tana nan lafiya,Baaba ya ce abinci take ci ma,ka ga yaron kuwa Yah Amee?" 'Da ni yake kama ko?.' Dariya ta yi sosai kafin ta ce. "To da ni ɗin dai da baka so yake kama." Shiru Aminullahi ya yi, yana jin wani irin yanayi a tattare da shi. Tinda ya ke a duniya bai

Chapter 6 of 30