na ƙwace maka abokinka sai dai ka samo wani."
Murmushi El-mustapha yayi sannan ya kai bakinsa saitin kunnen Aminee ya ce.
"Eh toh dole ne na samo wani abokin,shi yasa ma jiya na yi ƙoƙari na yi ajiyata anan,wadda nake fatan ta zamo mana alkhairi."
Hannun shi Aminee ta janye daga jikinta tana sunkuyar da kai ƙasa cike da matsananciyar kunya,a haka suka karya El-mustapha na ta zuba santi,ciki yanayi na jin mamakin El-mustapha Aminee ta ce.
"Mahaifiyata ta ce min wannan irin abincin kune na larabawa,tunda Abbah ya je makka ya taɓa cin irinsa shikenan ya koya mata yanda ake yi,sai take yi masa a duk sanda Allah Ya hore mana,me yasa ka ji shi daban bayan kai balarabe ne?"
"Daɗin wannan daban da wanda na saba ci Rouh,ban taɓa cin kubza mai daɗin wannan ba."
Dariya Aminee ta gimtse kafin ta ce.
"Wannan fa funkaso ne ba gurasa ba."
"To koma dai menene sunansa yana da daɗi, sai dai bai kai...."
Da sauri Aminee ta miƙe ta na sunkuyar da kai ta gudu ɗaki,dariya El-mustapha yayi sosai yana jin daɗin yanda take da kunya sosai,sai dai kunyarta bata taɓa hana sa sakewa da jikinta,duk abinda ya koyar da ita ta riƙe tana yi masa,kuma yana yabawa matuƙa.
Tin daga wannan ranar Aminee da Aminullahi suka zama masoyan juna,duk inda kake neman Aminullahi,to zaka ga Aminee a wajen,bayan an saka sa a makaranta sai ya zamana Aminee ce ke tashi da sassafe ta yi masa nau'ikan abincin da yake so,ta haɗa masa abun sha sannan ta saka masa da fruit a jakarsa,drivern El-mustapha ya kaisa makaranta. Da zarar an tashi ake zuwa ɗakkosa, kafin ya iso gida Aminee ta sama masa da abinda zai ci mai daɗi. Cikin ƙanƙanin lokaci Aminullahi ya sake zama ƙaton yaro mai cike da kuzari,ga ilimin addini da yake ta kwasa a wajen Aminee,domin kuwa a iya zaman da suka yi na watanni,har yayi izifi biyu a wajenta. Mahaifansa ba ƙaramin jin daɗi suke yi ba a duk lokacin da Aminullahi ya kai musu ziyara,bashi da wata hira da ta wuce Ammi ta yi min kaza,Ammina ta sai min kaza. Wannan abun da Aminee take yiwa Aminullahi sai ya dasa zazzafar soyayyarta a zuciyar Aisha da Mus'ab,haka suka ci gaba da rayuwa cikin so da kauna da kulawa.
Wataranar lahadi ta kama babu makarantar boko,Aminullahi na gida suna ta karatun islamiyya da Aminee,suna kammalawa sai ya hau yi mata shagwaɓa kamar zai yi kuka ya ce yana son cin cake, murmushinta mai kyau ta sakar masa sannan ta ce.
"Shike nan abinda ka ke son ci masoyina?"
Ɗaga mata kai ya yi yana wasa da gashin kanta da ya ɓullo ta ƙasan ɗankwalinta,hannunsa ta kama suka wuce kitchen suka fara kwaba cake a tare,a haka Aminee ta dinga jawo masa ayoyin ƙur'ani yana ƙarasawa,sai da suka gama kwaba cake ta saka a oven sannan ta koma tana haɗa musu ɗan lemon da za su haɗa da shi,Iya ce ta shiga kitchen ɗin ta na murmushi ta ce.
"Yau kuma ƙwalamar da kuke yi kenan? Da alama dai yanzu kin fini iya girki Uwar ɗakina."
Murmushi Aminee ta saki mai sauti sannan ta ce.
"Ta yaya ɗaliba za ta fi malamarta iyawa Iya?"
"Sau nawa aka yi hakan a duniya? Ai ni yanzu na zama baƙauya a fannin girki in dai kina nan."
Dariya sosai Aminee ta yi sannan ta ce.
"Wannan dai zolaya ce Iya,amma ni na san ban kai ki ba,ina dai fatan watarana na kai ki ƙwarewa,kai har ma na fiki."
"To Allah Ya sa Aminatuwa."
Babu jimawa ƙamshin cake ɗin da a wajen ƙwabawa ta zuba cinnamon da vanilla flavor ya cika gidan baki ɗaya,ƙamshi ne da Aminee ke bala'in so saboda bata taɓa jin irinsa ba,sai da Iya ta koya mata haɗasu waje ɗaya,sai dai kash ! Yau madadin ta ji daɗin ƙamshin,sai ta ji yana yi mata wani irin warin da ba zata iya jurewa ba,cikin sauri ta bar kitchen ɗin ta gudu ɗakinta,amai ta dinga kelayawa a banɗaki kamar za ta amayar da ƴan hanjinta,da jin haka sai Iya ta tafi da gudu ta leƙa waje inda El-mustapha ke tare da mutane yana jin koken su,sallama ta yi masa ta ce ana buƙatar ganinsa a cikin gida,ko minti ɗaya bai ƙara ba ya miƙe ya bi bayan Iya. Suna shiga ya hau tambayarta abinda ke faruwa ya ganta cikin damuwa,a hanzarce ta ce masa.
"Aminatuwa bata da lafiya,amai take ta yi gata can a ɗa...."
Kafin Iya ta ƙarasa maganarta El-mustapha ya zaro wayar hannunsa ya danna kira,cikin gaggawa yake sanar da rashin lafiyar da Aminee take yi,a haka ya ƙarasa ɗakin nasu ya tarar da ita malale a ƙasan ɗakin,ƙofar banɗakin su a buɗe,jinjina kai ya yi tare da tabbatar da rashin lafiyar Amine babba ce,domin kuwa a duk sanda aka bar kofar banɗaki a buɗe koda da kuskure ne ta dinga magana kenan,takan ce,banɗaki matattarar shaiɗanun aljanu ne masu wahalar sha'ani,dan haka a dinga yawan rufewa tinda bature ya riga ya shigar mana shi cikin ɗakunanmu.
Ɗaga ta El-mustapha ya yi ya ajiye ta a saman gadonsu,numfashi take fitarwa da ƙyar,a hankali ta ce.
"Iya ta fitarwa da Aminullahi cake ɗinsa kuwa? Kar a bari ya ƙone dan Allah."
Cikin damuwa El-mustapha ya ce.
"Nima ban sani ba,shigowata kenan,me yake damun ki? Ina ne yake yi miki ciwo?"
Lumshe idanunta ta yi sannan ta lasho busasshun laɓɓanta masu tudu da faɗi kaɗan ta ce.
"Lafiya ta ƙalau fa muke yin aiki a kitchen,ƙamshin cake ne ya tada min zuciya, ina gama amai na ji zazzaɓi yana so ya rufe ni kuma."
"Allah Ya baki lafiya Rouh,bari yanzu likita zata zo,sai ta duba lafiyar ki mu ji abinda ke damun ki ko?"
Gyaɗa masa kai ta yi,cike da godiya ga Allah a ranta,yanda El-mustapha yake shagwaɓa ta da riritata yana tuna mata da rayuwarta ta baya, ta taso cikin gata da soyayyar iyaye,ƙaddara ta rabata da mahaifiyarta,ta sha wahala a wajen kishiyar uwa,mutuwar mahaifinta ta ta'azzara lamarin,sai gashi Allah Ya wanke miji ɗan gaske kyakkyawan balarabe mai kulawa ya bata,me zata yi da ya rage godiya ga Allah kuma?
Tana tsaka da wannan tunanin suka ji sallamar Iya,likita ta iso ɗauke da kayan aikinta,a gaban El-mustapha ta gama duk wani abu da za ta yi,da kuma tambayoyin da zata yiwa Aminee,tana kammala yi mata gwajin fitsari ta duba sakamakon,nan take ta gano Aminee na ɗauke da juna biyu,bata yi ƙasa a guiwa ba kuwa wajen sanar da El-mustapha, hamdala ya dinga jerawa tare da yin sujjadar godiya ga Allah,yana ɗagowa ya ɗauki maƙudan kuɗi ya baiwa likita a matsayin tukuici,godiya ta dinga yi,sannan ta basu shawarar su je asibiti dan a tabbatar da watannin cikin da kuma magungunan da ya kamata ta dinga sha da sauran su. Godiya El-mustapha ya dinga yiwa likita kafin ta yi musu sallama ta tafi.
Likita na fita El-mustapha ya rungume Aminee ya na yi mata godiya,kunya duk ta gama rufe ta tana jin damuwa a ranta na yanda za ta haɗa ido da Iya da su Aisha, Aminullahi ne ya shiga ɗakin bayan ya yi sallama ya nemi izinin shiga,idanunsa sun yi jawur saboda kuka,yana ganin Aminee a kwance ya tafi da gudu ya kwanta a jikinta yana kuka,murmushi ta ƙaƙalo ta hau shafa kansa ta na faɗin.
"Habaa Aminuna,me ya sa ka ke kuka? Ko dai Iya bata baka cake ɗinka bane?"
"Ni bana son cake,me yasa baki da lafiya Ammi?"
"Ka yi haƙuri Masoyina,na ji sauƙi,amai kawai na yi saboda ciki na ya juya,amma yanzu na samu sauƙi,kana so na je na baka cake ɗinka?"
"Ah ah ina so ki kwanta ki huta,Iya zata kula da ni."
"To masoyina zan huta,kai kuma ka je ka ci cake ɗinka ko?"
Da yamma sai ga su Aisha sun zo dubiya,Aminullahi ne yayiwa Aisha bayanin yanda Amminsa ta yi amai dalla-dalla,haka ta dinga ganin kamar tana wajen abun ya faru,murmushi ta yi sannan ta shafa sumarsa ta ce.
"In Shaa Allahu Ammin ka za ta haifa maka ƙani ko ƙanwa,dan haka wannan rashin lafiyar da ka ga tana yi zata warke a duk sanda ƙaninka ko ƙanwarka suka zo duniya."
Murna sosai Aminullahi ya dinga yi,yana tsalle,nan da nan damuwar dake ransa na ganin Aminee bata da lafiya ta kau,fatansa shine Allah Yasa ta haifa masa ƙani su dinga yin ball tare. Bayan tafiyar su Aisha ne El-mustapha yayiwa Aminee wanka,duk da jin kunyarsa da take yi bai sa ta hana shi yi mata ba,yana gama yi mata wanka ya bata dama ta yi alwala sannan suka koma ɗaki ya shirya ta,masallaci ya wuce shi da Aminullahi,ita kuma ta yi sallarta a ɗaki.
Wata iriyar tarairaya da kulawa Aminee ke samu a wajen mutanen gidan baki ɗaya,dan kuwa har Aminullahi ba a bari a baya ba,wajen zuwa gardine ɗin gidan ya samowa Aminee fruits ɗin da take so,wanda ba zai iya tsinkowa ba zai sa abokinsa Baba mai gadi ya tsinko masa ya kawo mata. Cikin ƙanƙanin lokaci Aminee ta ƙara buɗewa ta yi kyau sosai kamar wata babbar Hajiya. El-mustapha yayi mata alƙawarin kaita Umara da zarar ta haihu yaro ya yi ƙwari,Aminee ta yi murna har da kukan farin ciki,nan take ta dinga zuba masa addu'o'in ta masu sanya sa a cikin matsanancin farin ciki.
Cikin Aminee na da watanni tara a duniya, El-mustapha ya gama siyayyar kayan jariri gaba ɗaya da duk wani abu da za a buƙata a asibiti. Iya ma ba a barta a baya ba wajen fita daji da kanta ta samo bagaruwa,ganyen magarya,ganyen lalle,da citta da kaninfari,sai kuma ta shiga kasuwa ta siyo ƴaƴan habbatussauda da turaren farin musk,tana kammala nata haɗin ta ce wa Aminee.
"To Uwar ɗakina ko yau haihuwa ta zo,na shirya mata tsafff dan karɓarta."
Murmushi kawai Aminee ta yi,tana jin wata iriyar azaba a mararta da bayanta,wanda take ta daurewa ta kasa sanar da kowa. Bayan sun gama cin abincin dare sun yi sallah,sai Iya ta yi musu sai da safe ta gyra wajen sannan ta kinkimi Aminullahi da ya yi bacci a wajen ta wuce dashi ɗakinta,da ƙyar Aminee ta miƙe ta shiga ɗaki ta kwanta, El-mustapha na ganin haka sai ya bi bayanta yana tambayarta ko lafiya take? Cikin ƙarfin hali ta ce masa
"Lafiya ƙalou Alhamdulillah,ina dai jin ciwon mara ne kaɗan-kaɗan."
Cikin sauri El-mustapha ya ce.
"To ko a kirawo likita ne?"
Da sauri Aminee ta girgiza masa kai,fuskarta ɗauke da damuwa ta ce.
"Dan Allah kar ka kirawo min kowa idan ba Iya ba,bana son zuwa asibiti."
Jiki babu ƙwari El-mustapha ya ce.
"To,da kin ji alamun haihuwa ki sanar dani sai na kirawo ta."
"In Shaa Allahu."
Bacci ne mai daɗi ya ɗauke su baki ɗaya,da misalin uku na dare naƙuda ta murɗawa Aminee,duk yanda ta so daurewa abun ya gagari tunaninta,dan haka dole ta tada El-mustapha ta ce ya kirawo mata Iya,cikin sauri El-mustapha ya fita ya kirawo Iya,nan da nan Iya ta hau shirye-shiryen karɓar jaririn Aminee zuwa duniya.........
[9/11, 10:50 AM] zee hussain: ƳAR RAWA.
RUBUTAWA: HAMIDAH SANUSI AHMAD(HAERMEEBRAERH)✍️✨
PAGE:7
Tare da El-mustapha Iya ta yi duk wata gwagwarmayar karɓar haihuwar Aminee,cikin ikon Allah kafin a kira sallar asuba ta haifo kyakkyawar yarinyarta mai kama da ita sak.
Ƙanƙantar da yarinyar ta yi ne ya sanya El-mustapha kasa ɗaukanta bayan Iya ta gyara ta,sai ajiye ta tayi a jikin Aminee dake kwance tana maida numfashi tana bin su da kallo,yanda El-mustapha ke farin ciki da murna ne ya sanya Aminee share hawayen farin ciki itama. Ta jima tana jin mutane na yin mafarkin yanda suke son rayuwar gidan aurensu ta kasance,sai gashi ita hakan bai taɓa gittawa tunaninta ba amma Allah Ya yi mata babbar kyautar da a kullum take gode masa. A yau ta sake yin imani da Allah idan Ya yi maka kyauta,ka gode masa to tabbas zai ƙara maka,Ya bata El-mustapha ta gode masa,gashi ya ƙara mata da ƴar da zata cika farin cikinta.
Kafin gari ya waye Iya ta yiwa jinjira wanka ta yiwa Aminee wanka,shayi mai kauri ta haɗawa Aminee da bread ɗin da sukan gasa me nama a cikinsa,sai da ta ci ta ƙoshi sannan ta bata waje domin ta huta.
El-mustapha kuwa yana dawowa daga masallaci ya taso Aminullahi ya sanar dashi Amminsa ta haifa masa ƙanwa,a madadin yayi murna sai ya tura baki gaba ya kalli El-mustapha ya ce.
"Baaba to ina ƙanin nawa da zan dinga yin ball da shi?"
Murmushi El-mustapha yayi kafin ya ce.
"Ka yi addu'ar Allah Ya bawa Amminka lafiya nan da wasu shekaru biyun ta haifo maka ƙani,amma ina mai tabbatar maka wannan ma za ta iya buga ƙwallo,ka jira kawai ta girma ka gani."
Nan take Aminullahi ya hau murna tare da neman izinin yana son ya ga Amminsa,da ƙyar El-mustapha ya lallashesa ya ce ya jira su tashi daga bacci. El-mustapha bai yi tunanin rashin wayewar gari ba ya dannawa Mus'ab waya ya sanar da su abinda Aminee ta haifa musu,nan da nan kuwa suka hau taya sa murna tare da yiwa jinjira addu'a da fatan alkhairi. Suna kammala waya El-mustapha ya zauna ya zabga tagumi,ƙwalla ya ji tana ƙona masa idanunsa,saboda kewar danginsa da iyayensa da suka gabata,yanzu kenan ta tabbata bashi da kowa sai Aminee da yarinyarsu? Me yasa danginsa suka guje shi? A da da ya baro ƙasar su yayi zaton zai iya share su saboda abubuwan da suka yi masa,amma ya kasa sai da ya dinga neman su ta waya,lokuta da dama basu ɗaukar wayarsa,wani lokacin kuma idan sun ɗauka suka ji shine sai su kashe wayar su,lokacin da abun duniya ya taru yayi masa yawa har yana neman sanya masa ciwo,sai shima ya tattara su ya watsar da su,yanzu gashi an yi masa haihuwa,bashi da wani ɗan'uwa na jini da zai kira ya sanar masa da abun farin cikin da ya same su,ita kanta Aminee bata da wanda zai kira ya sanarwa da ta haihu bayan Malam Abubakar abokin mahaifinta.
Cikin sauri kuwa ya hau lalubo lambarsa a wayarsa,babu ɓata lokaci ya danna masa kira,sai dai amsar da baturiyar ta bashi ne ya kashe masa jiki,sake kira yayi a karo na biyu,amma baturiyar na sanar da shi lambar a kashe take,haƙura yayi ya shiga ɗaki ya zauna a gaban Aminee dake bacci da jinjirar su a gabanta.
Hamdala ya sake yi sannan ya shafa fuskar jinjirar a hankali,bakinsa ya kai saman goshin Aminee ya sumbata sannan ya ce.
"Allah Ya yi miki albarka Rouh,Allah Ya raya mana Aisha Ya yiwa rayuwarta albarka da sauran yara baki ɗaya."
Cikin magagin bacci ido a kulle Aminee ta ce.
"Aisha ? Ya akai ka san sunan mahaifiyata na asali?"
Murmushi yayi kafin ya ce.
"Dogon labari ne,kin ga bayan mun yiwa mahaifiyarmu takwara,Aishan Mus'ab ma zata yi murna da farin cikin jin wannan sunan."
Kwanciya Aminee ta gyara sannan ta buɗe idanunta a hankali ta zuba su akan fuskar El-mustapha,a hankali ta furta masa.
"Na gode Baaba."
Gira ya ɗaga mata sannan ya ce.
"Da me fa?"
"Da komai ma,kai ne rayuwata,ina son ka."
Baki El-mustapha ya buɗe tsabar mamaki,ita kuma sai ta yi sauri ta juya masa baya tana murmushi,murmushi ne ya mamaye fuskar El-mustapha nan take ya matsar da baby Aisha zuwa gaban Aminee ya kwanta a bayan ta ya rungumeta,sumbatar wuyanta ya dinga yi yana shinshinarta,a haka suka yi bacci mai daɗi.
Kukan Baby ne ya tada su a gigice Aminee ta ɗauke ta tana kwaɓe fuska kamar za ta yi kuka itama,kallon El-mustapha ta yi ta miƙa masa ita,da sauri ya miƙe yana sosa kai ya ce.
"Bari dai na kirawo maki Iya,ni tsoron ɗaukarta nake yi."
Da sauri ya fita waje ya kirawo Iya da ta kammala dafa farfesun naman rago da ya ji kayan ƙamshi,sai kunun alkama da ta zubawa nonon raƙumi da madarar ruwa da zuma,wajen dafa ruwan dama kunun ta saka ganyen shuwaka saboda jinjira ta samu ruwan nono. Ɗauka ta yi ta nufi ɗakin da su ta ajiye sannan ta karɓi jinjirar,ta na jijjigawa har sai da Aminee ta ci ta ƙoshi. A hankali Iya ta dinga lallashin Aminee ta ce ta gwada bata mama ta sha ta haka ne ruwan zai zo idan yarinyar tana zuƙa,duk zafin da take ji sai ta daure ta bata.
Da misalin sha ɗaya na safiya su Aisha suka iso, cike da murna da abinci mai yawa,ƙannen Aisha da na Mus'ab ma ba a bar su a baya ba,duk sun samu halartar ganin jaririyar. Ganin yawan mutanen da suka zo yiwa Aminee barka ya sanya ta ta manta da damuwar rashin dangi da bata da su a ƙasar,dan kuwa ko a ƙasar take iyakar abinda za ta gani kenan,ballantana ita da take da bauɗaɗɗun ƴan'uwa,sanin kanta ne bata da kwatan wannan gatan da ta samu a wajen mutanen da bata haɗa komai da su ba sai addini.
Baƙi basu bar Aminee ba har sai da yamma ta yi kowaccen su ta yi mata sallama ta wuce gidanta da alƙawarin sai sun sake dawowa. Iya na yiwa jinjira wankan yamma ta gasa mata cibi,sai Aminee ta shayar da ita,dan kuwa ruwa ya fara zuwa,sai da ta ƙoshi sannan suka miƙawa El-mustapha ita wanda ya karɓe ta da ƙyar suka wuce banɗaki,suna shiga Iya ta yiwa Aminee wanka tare da gasa mata jikinta da kyau.
Bayan kwana biyu da haihuwa Iya ta shawarce su da su je asibiti su ga likita,koda bata jin komai a jikinta,haka kuwa aka yi da yamma El-mustapha ya ɗauke su a mota har da Aminullahi da ya laƙabawa jinjira suna Lamya,da aka tambayesa dalilin sanya mata wannan sunan sai ya ce ai ita baƙa ce kuma siririya,haka ake kiran wata ƴar ƙanwar Umminsa saboda ƙanƙantarta da baƙinta.
Bayan gwaje-gwaje da dube-dube,likita ya tabbatar musu da lafiyar su ƙalau ita da jinjirarta,sai dai duk da haka ya rubutawa Aminee magungunan da za ta sha ta samu ƙwarin jikinta.
Suna dawowa gida Aminullahi ya wuce ɗaki ya kwanta bacci,saboda gajiyar makaranta da ta ƙiriniya da ya sha da rana. Abinci El-mustapha ya ci ya wuce waje dan ganawa da wasu baƙi da suka ziyarcesa.
Bakwai na zagayowa Aisha ta jagoranci taron sunan takwarar ta,wadda ta sha kayayyaki daga wajen dangin Mus'ab da na Aishan kanta,uban gayya kuwa lefen da bai yiwa Aminee ba ya haɗa mata akwati uku nata da guda biyu na jaririya,sai wata sarƙar zinare babba da zobenta da awarwaro guda huɗu,sai sarƙar ƙafa siririya mai kyau. Kuka Aminee ta dinga yi,har sai da ta sanya Aisha zubar da hawayen tausayinta.
Aminullahi ya koma gidan su saboda hidimar da ta yiwa Iya yawa na kula da mai jego da jinjira da kuma shirya shi dan tafiya makaranta,sai dai ana tasowa zai biyo mahaifinsa ko Aisha ta sa ɗaya daga cikin masu aikinta su rako sa gidan Aminee dan yaga Lamya,wata iriyar soyayya yake yiwa Lamya wadda ta kai ta kawo ko abu mai daɗi yaci sai ya rago ya kawo mata,da ƙyar Iya ta fahimtar da shi bata fara cin abinci ba sai nono kaɗai take sha,da jin haka idan ya kawo abu sai ya bawa Aminee ya ce ta ci,saboda Lamya ta sha a nono. Yau ma kamar koda yaushe Aminullahi na tasowa daga makaranta yayi wanka ya tsaya jiran Tsahare mai aikin su dan ta kai sa wajen Lamya. A leda ya zuba ragowar biscuits ɗinsa da alewa da ya ragewa Lamya,tana fitowa sanye da hijabi suka yiwa Aisha sallama suka wuce.
Yana isa ya tarar da ita an yi mata wanka tana bacci,Iya ta mulke ta da mai sai sheƙi take yi,cikin ɓata fuska ya kalli Iya ya ce.
"Iya ki dena ƙara mata baƙi da man nan da kike shafa mata dan Allah."
Dariya sosai Aminee ta yi kafin ta ce.
"Ni kam Aminullahi kana so ƙanwar nan taka ta ce maka Yaya kuwa? Ba fa wata baƙa bace ta azo a gani da ka damu akan baƙinta."
"Baƙa ce mana Ammi,yarinyar Tanti Ruma fara ce tass kamar ni."
Iya ce ta kyaɓe baki kafin ta dafa ƙasa ta miƙe,kallon sa ta yi ta ce.
"Mu na nan da kai watarana idan ka ganta aka ce maka wannan Aisha ce ba zaka yarda ba,kai baka san irin wannan baƙin tsada yake yi ba ko?"
Dariya Aminee ta yi sa'annan ta ce.
"Habaa Iya,duka-duka nawa Aminun nawa yake da zai san tsadar kala?."
"To ai na ga ya dame mu ne,na sani ko ya san tsadar kaloli shi yasa yake damun mutane da baƙinta?"
Iya ta faɗa tana mere baki ta wuce kitchen. Tin daga wannan ranar Aminullahi bai sake yin magana akan baƙin Lamya ba,sannan bai fasa zuwa ganinta ba kullum.
Bayan shekara biyu da haihuwar Aisha,yarinya ta yi girma ta yi wayo sosai,babu abinda bata iya faɗa a gane abinda take so. Shaƙuwar su da Aminullahi sai ta ƙaru sosai musamman ma da ya dawo gidan da zama. Idan ya dawo daga makaranta haka zai tasa ta a gaba da litattafansa ya dinga koya mata karatu,tin Aminee na ganin shiriritar Aminullahi har sai da itama ta maida hankali wajen koya mata na islama.
Haka rayuwar waɗannan mutane ta ci gaba da tafiya cike da so da ƙauna da kulawa ga junan su. El-mustapha bashi da buri a rayuwarsa da ya wuce na ya farantawa Aminee rai da tilon ƴarsu da yake jin zazzafan son ta a ransa. Haka zalika Aminee ta dage ta koyi duk wasu girke-girke na zamani da na gargajiya,kwalliya da gyaran jiki ciki da waje dan ta farantawa mijinta rai,babban abinda ya fi burge El-mustapha da Aminee baya wuce yanda take son koyon yaren faransa da turanci dan kawai ta samu sabbin kalmomin da zata dinga jaddada masa kalaman soyayya,wata rana idan ta faɗi wata kalmar dariya yake yi sosai,kafin daga baya ya gyara mata.
Lamya ta taso tana jin yaren larabci,hausa,buzanci,turanci,da kuma faransa. Tana da shekara huɗu zuwa biyar aka sanyata a makarantar su Aminullahi,a tare ake kai su makaranta kuma a maida su gida tare,lokuta da dama shi yake yi mata home work idan sun dawo gida.
Watarana Aminee da iyalanta suna zaune a parlour baki ɗaya suna kallo,sai ta nemi Lamya ta rasa a cikin gidan,tun tana neman nata da wasa har sai da ta kai Iya da Aminullahi sun fita har farfajiyar gidan suna neman ta,amma babu wanda ya ganta ko ya ji labarin wanda ya ganta,cike da tsoro da tashin hankali Aminee ta ɗauki waya ta hau kiran El-mustapha dan ta sanar da shi halin da ake ciki,yana ɗaukan wayar muryar Aminee na rawa ta ce......
[9/11, 10:50 AM] zee hussain: ƳAR RAWA.
RUBUTAWA:HAMIDAH SANUSI AHMAD(HAERMEEBRAERH)✍️✨
PAGE: 8
"Mun duba ko ina a gidan nan bamu ga A'isha ba Baaba."
"Kamar ya kun duba ko'ina baku ga A'isha ba? Me hakan yake nufi?"
El-mustapha ya faɗa a ɗan tsawace,saurin kauda wayar daga kunnenta tayi,kafin ta fara yi masa bayani jikinta yana rawa,yana kammala jin bayananta ya ce.
"Kwantar da hankalin ki,gamu nan mun kusa dawowa gidan dama muna hanya,ku ci gaba da dubawa,kun duba ɗakinta?"
"Eh duk mun duba har ɗakin baƙi bata can."
"Gamu nan mun shigo gidan kashe wayar."
Cikin sauri Aminee ta kashe wayar ta nufi hanyar waje da gudu babu ko hijabi a jikinta, El-mustapha da ya buɗe marfin motarsa a gaggauce ne ya ƙaraso gabanta ya rungume ta da ƙarfi,kuka Aminee ta fashe da shi jikinta na rawa,a haka El-mustapha ya jata suka koma cikin gidan,ɗakin Lamya suka leƙa bata ciki,daga nan ya shiga na Aminullahi,nan ma shiru,a hankali ya dinga bin dika ɗakunan gidan da parlours yana dubata,cikin sauri ya saki hannun Aminee dake biye da shi tana jaddada masa duk sun duba ko'ina. Ɗakinta taga ya nufa cikin sauri sai itama ta rufa masa baya,domin gaba ɗaya ta manta da nan,nan ne kuma basu duba ba,da gudu ta riga shi shiga ɗakin. Suna shiga suka tarar da ita sanye da ƙananan kaya,ta baza kayan kwalliyar Aminee da bata amfani da su, kasancewarta ba mace bace mai son cikawa fuskarta kwalliya,gefe ɗaya kuma TV ce ke aiki,ta kunno tashar India da suke waƙe-waƙe da raye-raye sai tiƙar rawa take yi tana wani karya jiki da juyasa kamar wata tarwaɗa,baki sake iyayen nata suke binta da kallo,a harzuƙe Aminee ta yi kanta ta ɗauketa da wani gigitaccen marin da ya sanya yarinyar tsayawa cak ta bar abinda take yi,kafin daga baya ta tsaga wani irin ihu mai ƙarfin gaske,a kiɗime El-mustapha ya isa gabanta ya ɗaga ta sama ya rungumeta yana lallashi,cikin ɓacin rai Aminee ta kashe TVn tana masifa.
"Tun ki na yarinyarki ƴar ƙanƙanuwa kike so ki lalace? Meye amfanin waƙe-waƙe da raye-raye? Duka-duka shekarar ki nawa? Shekarar ki biyar Lamya,har yanzu baki cika biyar ɗin bama,me ki ke so ki zama ne?
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 4 Chapter of 30