Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
taɓa son wasu mutane ba bayan waɗannan mutane masu daraja da ƙima da basu haɗa alaƙa ta jini ba,soyayyar Lamya a ran shi kuwa abu ne da ba zai iya tantance kalar son da yake yi mata ba,kalmar da ta faɗa ta sanya shi jin wani irin shauƙin son ta na musamman,wanda bai taɓa jin irinsa ba a rayuwarsa game da ita. Lamya kuwa jin ya yi shiru bai bata amsa ba sai jikinta ya yi sanyi,kenan da gaske baya son ta? Saboda tana baƙar fata ko meye dalilinsa na ƙin ta? Ta tabbata a yanzu babu wanda zai kalle ta ya kira ta da baƙar fata kai tsaye ba tare da ya tsaya ya yi tinanin a ajin da zai saka ta ba. Bata da haske irin na mahaifinta,amma kuma bata kai Aminee baƙi ba,kalar fatar ta kala ce da ke da wahalar samu a cikin mutane,cikin kyawawan ma sai wanda Allah ya zaɓa ke da ita,jiki a sanyaye ta kashe wayr,murmushin takaici ta saki,a fili ta furta. "Zan kuwa baka mamaki Yah Amee,na yi alƙawarin duk ranar da ka ganni sai ka kamu da matsanancin so na,son da ba za ka iya jurewa ba har sai ka bayyana shi a gare ni." Baaban ta ne ya isa gare ta ya na tambayar sun gama waya da Aminullahin ne? Cikin yaƙe ta ɗaga masa kai, tare da cewa. "Ai yana ta murna da ya ji ya samu ƙani,na san yanzu zai dena so na ya koma son Mubarak." Lakace mata hanci El-mustapha ya yi sannan ya ce. "To ke yanzu kishi ki ke yi da ƙanin naki ko me? Ai ke da Aminullahi babu mai shiga tsakanin soyayyar ku,domin kuwa soyayyar ku daga Allah take,kin zame masa hanta,shi kuma tamkar jinin jikin hantar yake,kin ga kuwa babu mai raba ku,dan kuwa tare aka gan ku." Nan take zuciyar Lamya ta saƙa mata dama Yah Amee ne ya faɗa mata hakan da bakin sa ɗazu,sai dai ina babu wannan soyayyar tata a ran sa. Cikin sauri ta kawar da wannan zancen ta ce. "Baaba zan iya zuwa na ga Ammi yanzu?" "Lala bacci take yi,ki bari ta farka,na san da kanta za ta neme ki,dan ko ɗazu da na leƙa ta sai da ta tambaye ki." Murmushi ta yi ta koma ta zauna zuciyarta na yi mata saƙa kala-kala. A can ɓangaren Aminullahi kuwa,da ya ji ta kashe waya sai ya yi murmushi,ya ce. "Lamya sarkin kishi,yanzu fa sai ta fara kishi da ɗan jaririn da bai jima da zuwa duniya ba,humm Allah ya shirya min ke ƙanwata,bari na je na labartawa su Momma na yi ƙani." A parlour ya tarar da Aisha ta na kwance tana kallo,gefen ta kuwa cincin ne da juice sai soyayyan naman rago,tana kallo tana jefawa a baki,banda ƙara ƙiba babu abinda take yi,har wannan lokacin kuwa bata iya aikin komai a gidan,daga ta yi wanka ta sha gayu da tsadaddun tufafi,sai ta zuba zinare ta fesa turaruka ta zauna a parlour tai ta ciye-ciye tana kallo,duk wani kula da gida da Aminullahi yana hannun masu aiki,shi kansa Mus'ab ƴan aiki ne ke kula da shi,abu ɗaya ya san yana mora a wajen Aisha shi ne haƙƙin auratayya da bata hana shi,hasali ma ta ƙware a wannan fannin,gashi bata wasa da gyara,shi yasa ya toshe kunnensa akan zigar da ake yi masa na ya ƙara aure. Zama Aminullahi ya yi a kujera ya kalle ta ya ce. "Momma kin san albishir ɗin da na kawo miki kuwa?" Kallon sa ta yi sau ɗaya ta ɗan yi masa murmushi kafin ta maida hankalinta zuwa ga ƙatuwar talabijin ɗin dake manne a bangon parlourn,cikin halin ko in kula ta ce. "Me ya faru? Ko ka samu nasarar samun aikin sojan ne? Na faɗa maka bana son wannan aikin,kai kaɗai Allah ya bani bana so na rasa ka,ka maida hankali ka bi mahaifinka ku yi kasuwanci, amma ka kafe kai sai soja za ka je." Murmushin takaici ya yi kafin ya ce. "Magana ki ke yi Momma ko dibinina ba ki yi,gaba ɗaya hankalin ki ya na ga talabijin,to dan na tafi aikin soja ma ba damuwa za ki yi ba. Ni dama zuwa na sanar dake Ammi na ta haihu,na samu ƙaramin ƙani Mubarak,ɗazu wannan yarinyar mai shegen iyayi ta kira take sanar dani." Rasa abinda zata ce ta yi,sai kawai ta tsaya ta kafe shi da ido har ya ɓacewa ganinta. Ta ya za ta fahimtar da Aminullahi tana son shi? Ita fa uwa ce,ita ce ta haifesa ba wata ba,to dama za ka iya haifar ɗanka sannan ka ƙisa? Ko so yake da girman sa ta dinga goya shi tana nunawa duniya shi a matsayin ɗanta da take so? Kawar da wannan tunanin ta yi,kafin ta ce. "Ba kuwa za ka samu aikin sojan nan ba da izinin Allah,kana nan muna tare da kai, ko kuma ka bi mahaifin ka kasuwanci Nigeria,bari na kira Abbu na sanar dashi ƙaruwar da muka samu." Ƙwalawa mai aikinta kira ta yi,ta na zuwa ta bata umarnin ta ɗakko mata wayarta da babu wata tazara mai yawa a tsakaninsu,miƙewa tsaye mai aikin ta yi ta isa bakin soket ɗin da aka saka mata wayar a caji ta ciro ta kai mata,godiya ta yi mata sannan ta ce a yanko mata kayan marmari a kawo. Mus'ab ta kira ta sanar da shi ƙaruwar da suka samu,cike da farin ciki ya yi mata barka,bayan sun kashe ne ya kira El-mustapha ya yi masa barka,sai dai yanayin da El-mustapha ya amsa masa wayar ne ya sanya shi natsuwa ya ce. "Ɗan'uwana me yake damun ka ne? Ko dai Aminatu ce babu lafiya?" Ajiyar zuciya El-mustapha ya sauke kafin ya ce. 'Ɗan'uwana ina cikin damuwa,na rasa yanda zan yi da dangina,ina jin tsoron kar su cutar da yarana.' "Wai ka na nufin har yanzu suna nan akan bakan su ba su sauya mummunan ƙudirin su akan ku ba?" 'Kwarai da gaske,domin kuwa yanzun nan mai gadi ya harbi wani mutum yana so ya hauro gidan nan,kafin a kama shi ya gudu,na tabbata babu wanda zai aiko shi sai su,ina jin tsoro kar su cutar min da yarana.' "Na sha faɗa maka ka aiko su zuwa Nijer,hankalinka da nawa zai kwanta idan ba su kusa da su,ban san me yasa baka son dawowa nan ba,bayan ka san muna son ka,ba zamu so wani abu na cutarwa ya same ka ba." 'Zan duba na ga yanda za a yi,ka gaishe min da Aminullahi da Ayshah.' "Za su ji,Allah Ya tsare ku Ya baku kariya daga dikkan masu neman ku da sharri." 'Amin Ya Allah,na gode Ɗan'uwana.' Suna gama sallama da Mus'ab a waya,Nurses ɗin da suka karɓi haihuwar Aminee suka yi musu sallama suma suka tafi cike da murna,saboda kyautar da El-mustapha ya yi musu ta ban mamaki. Lamya na zaune cikin tsoro saboda haura musu gida da aka yi da kuma ƙarar bindigar mai gadin gidan da ta ji,kallonta El-mustapha ya yi a zuciyarsa yana addu'ar Allah Ya sassauta ƙiyayyar da ƴan'uwansa suke yi masa akansa,Allah Ya tsare yaran sa kar su taso da wannan mummunan halin. Washegari da sassafe El-mustapha da kansa ya taya Aminee wanka,ita kuma ta yiwa Mubarak wanka,ta bashi madara,sannan ta jijjiga shi a kafaɗarta ya koma bacci,waje ta samu ta kwanta itama tana lumshe idanu kamar mai jin bacci,tinda ta haihu take jin jikinta babu ƙwari,ga shi jini yana yi mata zuba sosai fiye da yanda ya kamata ace yana zuba,ta kasa sanar da El-mustapha saboda ganin yanda yake ta ɗawainiya da su,hatta da mai aiki ya ƙi ɗauka saboda yana tsoron kar ya ɗakko wadda za ta cutar masa da iyalinsa, lumshe ida ta sake yi,ta na kallon Lamya dake ta lailaya hannun jaririn dake bacci tare da sumbatar shi. Murmushi ta yi murya can ƙasa irin ta marasa ƙarfi a jika ta ce. "Lamya me yasa baki je makaranta ba? Ki na wasa da karatun ki fa." "Ammi zan je ne zuwa gobe In Shaa Allahu,dan Allah ki barni na zauna da ku na yi ta kallon ku ina jin farin ciki a rai na." Murmushin ƙarfin hali Aminee ta yi kafin ta ce. "Lamya kenan,idan kuma mutuwa ta zo lokaci ɗaya ta ɗauke ni fa?" Cike da tashin hankali El-mustapha da ya shiga ɗakin ɗauke da mug ɗin da ya haɗo mata shayi ya saki mug ɗin ƙasa,wani irin tarwatsewa zuciyarsa ta yi da jin kalaman Aminee,cikin sauri ya tsallake kwalaben dake gabansa ya isa gabanta ya durƙusa ya kama hannunta,murya na rawa ya ce. "Dan Allah kar ki sake yin irin wannan furucin,me yasa za ki ambatarwa kan ki mutuwa muna zaune lafiya?" Wasu zafafan hawaye ne suka zuba a saman kuncin Aminee, cikin sigar lallashi ta kama hannun Lamya dake hawaye sosai ta ce. "Dan Allah ku dena wannan koke-koken,wasa nake yi muku,amma kuma ku sani fa kowanne mai rai watarana zai zamo gawa,dani da kai da ke da wannan jaririn duk bamu san gawar fari ba, dan haka kowa ya zauna cikin shiri,dan kuwa tana iya zuwa a kowanne lokaci,a kuma kowanne yanayi,ni dai babban buri na ko bayan ba raina Lamya ta je Nigeria,ta haɗu da dangi na,ta sadar da zumunci a tsakaninta da su,dan Allah ka cika min wannan buri nawa." Cikin sauri El-mustapha ya ɗauke ƙwallar da ke barazanar sauka a kuncinsa,miƙewa tsaye ya yi sannan ya kalli Aminee ya ce. "Ko dai baki da lafiya ne na kai ki wajen doktor?" "Lafiya ta ƙalau Oumry, haka kawai na ji ina son na sanar da ku abinda na jima ina so na yi,wato na kai Lamya wajen dangi na su ganta,wataƙila ƙiyayyar da ke tsakanin mu za ta kau,wataƙila ƴan'uwana ba kamar Innah Delu suke ba,suna so na zasu sada zumunci dani ko dan mahaifin mu,na so ace Abbah na nan a raye,da ya ga kyawawan yaran da muka haifa tare da balarabe mai taimako." Murmushi El-mustapha ya sakar mata,saboda tinawa da mahaifinta mai karamci da ya yi,itan ma murmushi ta sakar masa kafin ta ce. "Ai sai ka je ka haɗo min wani shayin,tinda ka zubar da wannan." "Yanzu kuwa ran ki ya daɗe." Juyawa ya yi cikin sauri ya bar ɗakin,Lamya kuwa har a wannan lokacin bata dawo daidai ba,hawaye take ta sharewa,murmushi Aminee ta yi sannan ta sake damƙe hannunta ta ce. "Ki yi haƙuri idan kalamai na sun tada hankalin ki abar ƙaunata,fata na shine ki cika min wannan burin nawa,ki kaiwa ƴan'uwana ziyara dake da ƙaninki,sannan ki kula da shi kamar yanda uwa za ta kula da ɗanta,ki zamo mai haƙuri da bada uziri,sannan ki riƙe ibada kar ki yi wasa da ita." Kuka Lamya ta sake fashewa da shi ta faɗa jikin Aminee ta ƙanƙame ta ta ce. "In Allah Ya yarda da kan ki za ki kai ni wajen dangin ki,kuma da yardar Allah za su so mu,za su ƙaunace mu,za su manta da duk abinda ya faru a baya,Ammi ina son ki,bana so na rasa ki,dan Allah ki dena irin waɗannan maganganun kina tsinka min zuciyata." "To na dena,ba kuma zan sake ba har abada, shi kenan?" Ɗaga mata kai Lamya ta yi tana tura baki,murmushi Aminee ta yi sannan ta shiga banɗaki ta sauya ƙunzugun jikinta,yanayin yanda jinin ke zuba ne ya sake rikita ta tare da tsorata ta,cikin rawar murya ta hau kiran El-mustapha,Lamya dake kwance gefen Mubarak bata ji ba, El-mustapha na shiga ɗakin ya ji Aminee na kiran sa a banɗaki,cikin sauri ya tsallake mug ɗin da ya fashe ya ajiye farantin da ya kawo mata wani shayin da kayan marmari,sannan ya shiga banɗakin,jingine ya tarar da ita a jikin gini jini na bin ƙafarta,idanun ta sai lumshewa suke yi,tana ganin ya shiga ta hau miƙa masa hannayenta,da sauri ya kama sannan ya taimaka mata ta gyara jikinta suka fito,sai da ya zaunar da ita a saman gado sannan ya gaggauta buɗe ma'ajiyar suturar su ya ɗakko mata wata riga da wando irin na Pakistan. Lamya na ganin haka sai ta miƙe da Mubarak a hannunta za ta fita,hannun ta Aminee ta riƙe tana kallon ƙwayar idanun Lamya,wani irin abu Lamya ta ji tin daga ƙafarta ya dira a saman kanta,murmushin yaƙe Aminee ta sakar mata sannan ta saki hannun ta,baya ta yi da kanta tare da yin wani guntun tari,cikin sauri Lamya ta ajiye Mubarak a gefen Aminee ta riƙe hannayen ta dika biyun ta na faɗin. "Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un! Baaba yi sauri ka kai Ammi asibiti,Ammi ! Ammi! Buɗe idanunki ki kalle ni." El-mustapha kuwa ci gaba da sanya mata kaya ya yi jikinsa na wata iriyar rawa,da za a auna jininsa a wannan lokacin,to fa babu makawa za a ga ya hau fiye da kima. Yana gama sanya mata rigar ya zira mata wando,sai dai ɗaga ta ɗin da zai yi ya ƙarasa sanya mata wandon ya yi arba da jini mai yawa ya na ci gaba da zuba a saman gadon,cikin sauri ya ƙarasa saka mata wandon ya cicciɓeta ya fara takawa da ita zuwa waje,sai dai kafin ya kai bakin ƙofar parlour jikin Aminee ya saki gaba ɗaya,a gigice El-mustapha ya kalle ta ya ga yanda kanta ya yi baya idanunta na kallon sama,durƙushewa ya yi a wajen ya hau kiran sunan ta. "Aminatu ! Amina dan Allah kar ki yi min haka,bani da kowa kin sani ke kaɗai ce komai na,Aminatu dan Allah ki tashi na kai ki wajen likita zaki samu lafiya,Aminaaa!" Ya kira sunan ta da ƙarfin da ya jawo hankalin Lamya ta ajiye Mubarak a gado ta fito da gudu zuwa parlour,yanayin da ta ga mahaifinta a ciki ne ya sanya zuciyarta rawa,a hankali ta taka ta isa gaban su ta durƙusa,hannun Aminee ta ɗaga sai ta ji ya saki,tana kallon idanun ta ta tabbatar babu rai a tattare da ita,babu zato babu tsammani El-mustapha ya ga Lamya ta zame a wajen ta suma. Tashi ya yi tsaye cikin kiɗimewa ya fita zuwa wajen masu aikin gidan, a tare suka dawo da mutum biyu, durƙusawa ya yi ya ɗauki Aminee ya sanya ta a mota,dan bai yarda ta mutu ba, security kuma ya ɗaukar masa lamya ya saka a wata motar daban,a guje ya koma ya ɗakko Mubarak dake ta tsala kuka kamar zai fasa maƙoshinsa ya rungume shi tsam a ƙirjinsa,driver ne ya ja su suka wuce asibiti,suna zuwa motocin su suka parker a bakin asibitin, cikin sauri aka kawo musu gadaje biyu aka ɗora Lamya da Aminee a kai,suna shige wa da su El-mustapha ya durƙusa a wajen riƙe da Mubarak a hannunsa ya na kuka ya kalli sama ya ce. "Alhamdulillahi ala kulli halin Ya Rab. Allah kar ka jarabce ni da rasa waɗannan mutanen da ka bani nake farin ciki a rayuwata saboda wanzuwarsu a cikinta,Allah ka shiga lamurana kar ka barni da iyawata." Ganin likita ya nufo shi ne ya sanya shi miƙewa cikin sauri yana goge hawayensa da hannu ɗaya,cike da jimami likita ya sanar da shi Aminee fa rai ya yi halinsa,Lamya kuma ta suma ne saboda shiga tashin hankali da ta yi. Tsayawa El-mustapha ya yi a wajen yana jin wani irin jiri na ɗibansa, cikin sauri likita ya riƙe Mubarak,sannan Security da drivern El-mustapha suka kama shi suka zaunar da shi. Kujerar dake gefen su. Ya jima a zaune a haka,kafin su ga yana murmushi,a hankali ya ke furta. "Ya Allah ka jiƙan Aminatu,Allah ka gafarta mata ka karɓi ibadunta,Ya Allah ka yi mata afuwar manya da ƙananan zunubanta,Allah ka shaida na yafewa Aminatu duk abinda ta yi min wanda na sani da wanda ban sani ba,Allah ka sani ita baiwar ka ce mai yawan bautar ka,Allah na aminta da Aminatu Allah ka aminta da ita. Allah ka raya mana yaran mu ka albarkace su,Allah ka bamu haƙurin jure rashin Aminatu." Wasu zafafan hawaye ne suka shiga zarya a kuncin El-mustapha,babu abinda yake tunani sama da yanda rayuwar shi da ta yaran su zata ci gaba da gudana babu haske a cikin ta,Aminatu ita ce fitilar dake haska rayuwarsu,to gashi yanzu babu ita. Rasa wanda zai kira ya sanar wa wannan abun baƙin cikin da ya same shi ya yi,nan take Mus'ab ya faɗo masa a rai,hannu na rawa ya zira hannunsa a aljihu ya zaro wayarsa, Mus'ab ya dannawa kira.......... [9/11, 10:50 AM] zee hussain: ƳAR RAWA. RUBUTAWA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✍️✨ PAGE 14. Ƙaton cake Idris ya ɗakko ya na tafe ya na rangwaɗa tare da ɗaga hannu sama yana juya ƙugu har ya isa babban teburin da ke tsakiyar gidan ya dire. Rawa ya tsaya ya yi sosai kafin ya zabga guɗa da harshe ya tafa da Anwar dake kusa da abubuwan sha yana juyawa, Anwar na gama juya lemon da suke kira da asir sai ya hau zubawa a kofunan roba yana bin ma'aikatan gidan yana basu, babu jimawa kowa ya fara neman waje yana zama,wanda suka rasa kujera kuwa a wajen suka faɗi suka kwanta,cikin sauri Anwar ya zaro wayarsa ya danna kira,ana ɗagawa ta ɗaya bangaren ya ce. "Aikina ya kammalu ku nake jira,da zarar kun shigo parlourn za ku sameta a ɗakin dake hannun hagu ita da wannan shegen ɗan daudun,ku haɗa har da shi bana ƙaunar ganinsa a cikin gidan nan." Da sauri Idris da ya ɗakko milky donut ya koma baya jiki na yi masa rawa kamar mazari,sai da ya tabbatar ya bar inda Anwar zai gansa ya keta cikin gidan da gudun tsiya, karo suka yi da El-mustapha da ya yi wankan fararen kaya sai baza ƙamshi yake yi,ƙanƙame shi Idris ya yi tare da labarta masa duk abinda ya ji Anwar na faɗa a waya,da wani irin sauri El-mustapha ya janye Idris daga jikinsa ya nufi ɗakin da Lamyah ke shiryawa ya ɗauki Mubarak ya damƙa mata a hannu,cikin sauri ya buɗe ma'adanar kayan su ya ɗakko mata wani ƙaton hijabin Aminee da niƙabi ya bata ya ce ta saka a saman kayan ta,cike da damuwa ta ce "Baaba me yake faruwa ne?" "Lamyah babu lokacin bayani,ki hanzarta ki biyo ni,kar ki manta da dika nasihar da na ke yi maki a kullum,ki kasance yarinya ta gari mai tsoron Allah a duk inda kika samu kan ki,yau ce ranar da za ku tafi Nigeria ke da ƙanin ki,za ki zame masa Uwa da Uba,ku sani ina son ku,ba zan taɓa dena son ku ba har ƙarshen numfashina." Hawaye ne zafafa ke ta kwaranya daga idanun Lamya wadda ke biye da mahaifinta da Idris a guje,wata siririyar ƙofa suka nufa da sauri El-mustapha ya danna wani waje ta buɗe,ƙatoton ɗaki ne da ya ke cike da litattafansa a ciki,wata jaka ya janyo ya damƙa a hannun Lamya,sannan ya ɗakko passports guda biyu ya miƙa mata,kallon ta ya yi cike da so da ƙauna irin na uba da ƴarsa,Idris na jin ƙarar buɗe babban gate ɗin gidan ya tsure ya manne a jikin El-mustapha,kallon sa El-mustapha ya yi sannan ya ce. "Idris ga amanar yarana nan na baka ka kai min su airport,kai ma ga wannan ka koma ƙauyen ku,domin idan suka san ko kai waye a waje na ba za su bar ka da rai ba." Kuɗi masu yawa El-mustapha ya bawa Idris sannan ya amshe wayar Lamyah ya bata wata,wani waje ya danna ƙofa ta bayyana,makeken gareji ne da mota a wajen,da sauri ya ce. "Ku shiga ku tafi cikin amincin Allah,wannan jakar ki bawa Ɗan'uwana Mus'ab a duk sanda kuka haɗu,duk wani ƙarin bayani da kike son sani ki duba littafin dake cikin jakar nan za ki same shi." "Baaba kai fa? Su waye suke buga mana gida haka? Baaba me yake far...." Da sauri El-mustapha ya sumbaci goshin Mubarak dake matsanancin kuka ya tura su cikin wajen sannan ya rufe ƙofar,nan da nan Idris mai rangwaɗa ya warware ya koma cikakken namiji ya kama hannun Lamyah ya saka ta a mota,suna shiga ya tada motar ya bar gidan a guje. El-mustapha kuwa cikin gidansa ya koma cikin sanɗa da niyyar ya ɗakko wayarsa ya kira hukuma,tafe yake ya na leƙe har ya isa bakin ƙofar ɗakin sa bai ga kowa ba,hannun ƙofar ɗakin ya murza ya shiga,kafin ya ƙara yin wani takun ya ji saukar wani abu mai nauyin gaske wanda ya fi zaton ƙarfe ne a ƙeyarsa,nan take lakar jikinsa ta sake ya faɗi a wajen,jini ne ya hau zuba daga ƙeyarsa kamar an yanka raƙumi,yayunsa ya gani gaba ɗayan su,Zaid da yake bi wa ne riƙe da ƙaton ƙarfen da ya buga masa a baya,sai Anwar mai kula da shuke-shuken gidan da sharar harabar gidan,wata iriyar dariya suka bushe da ita,lumshe ido El-mustapha ya yi jini na zuba ya saki murmushi shima,kallon sa suka fara yi cike da mamaki,dariya ya saki yana ƙare musu kallo,a zuciye Zaid ya sake ɗaga ƙarfen ya dake shi a ciki,nan take jini ya yi tsartuwa ta baki da hancin El-mustapha,idanunsa kuwa wani irin ja suka yi kamar an tsoma su a jini,wata iriyar zufar wahala ce ta jiƙa masa lallausan gashin kansa har tana ɗiga a ƙasa. Cike da ɓacin rai Zaid ya ce. "Ina takardun kamfanin da ka ɓoye suke? Sannan ina waɗannan shegun baƙaƙen yaran naka?" Murmushin ƙarfin hali El-mustapha ya yi kafin ya ce. "Yarana ƴan albarka..su..suna cikin...kariya..da tsarewar Allah...sun yi muku...nisan da ba za ku iya....tardo su ba...dukiya kuma kun gama cin...wadda za ku ci...da ga yau rayuwar ku zata fara shiga ƙunci da masifa...ba za ku sake samun kwanciyar hankali ba....har ƙarshen...ƙarshen...rayuwar ku." El-mustapha ya ƙarasa maganarsa a wahalce,dariya El-Hassan ya yi kafin ya ce. "Yanzu da mu da kai za a ga wanda zai ƙarasa rayuwarsa a wahalce,kuma a ƙasƙance." Kallon El-Hassan El-mustapha ya yi,hawaye ne suka zubo daga idanunsa,cikin yanayi na jigata ya ce. "Tirr da kasancewar ku ƴan'uwa a gare ni...Allah ba zai bar ku ba tinda kuka yada zumunci,ku ka wulaƙanta zumunci...Allah zai azabtar da ku a bisa abinda kuka aikatawa zumunci..kun zaɓi duniya akan lahirar ku...kar ku manta,zumunci na Allah ne,ba ɗan Adam ne ya ce a sada shi ba....amma ku...kun take sanin da Allah Ya baku..saboda son duniya da abinda ke cikinta.. na barku da Allah shi zai yi hukunci a tsakanin mu." Wata shaƙuwa El-mustapha ya saki,cikin sauri Muhammad ya isa gaban sa ya ɗaga kansa ya ce. "Ina sauran dukiyar ka take !" El-mustapha tattaro yawun bakinsa mai jini da yauƙi ya yi ya watsa a fuskar yayan nasa,sannan ya sakar masa murmushi ya ce. "Su na can inda har abada ba za ku taɓa samun ta ba...." Tashi Muhammad ya yi daga durƙuson da yai yana goge fuskarsa da farin ƙyalle,kallon sauran ƙannen nasa ya yi sannan ya ɗaga musu gira,a fusace suka hau El-mustapha da duka,har sai da ya dena motsi,suna kammalawa suka hautsine ɗakin sannan suka zuba fetur suka kunna wuta. Har suka bar cikin gidan sauran masu aikin gidan basu farka ba,dan haka sai suka bar Anwar tare da bashi wani lemo suka ce ya sha ya kwanta shima,da sauran sun tashi za su gansa shima a cikin yanayin da suka shiga. Babu musu ya karɓa ya sha ya kwanta su kuma suka bar gidan yana ci da wuta. A hankali El-mustapha ke furta kalmar shahada,a zuciyarsa ya na mai kai ƙarar ƴan'uwansa da suka ci amanar zumunci wajen Allah,a cikin wannan yanayin wuta ta cinye gidan El-mustapha ya ƙone ƙurmus. Ta ɓangaren su Lamyah kuwa suna cikin mota sai kuka suke yi ita da Mubarak,suna zuwa airport Idris ya shiga ya yi musu duk wani abu da ya dace sannan ya koma wajen su ya same su fuska ta yi musu ƙozai-ƙozai, niƙabin Lamyah ya ɗaga yana kallon fuskarta da tausayawa sannan ya ce. "Ki kula da kan ki da ɗan'uwanki kamar yanda mahaifinku ya bar maki wasici,ni zan tafi saboda na tsira da rayuwata,dan kuwa Zaid ya sanni,ya san ko ni wanene a wajen mahaifinki,asalina ba ɗan daudu bane kamar yanda kika yi zato,ni mai tsaron lafiyar ku ne,mahaifin ki yana sane ya fara turo Rumaisah,sai aka yi dace kika ƙi amincewa da ita,daga nan ne ya yi amfani da wannan damar ya kawo ni gidan,tare da nuna bai sanni ba bai san daga inda nake ba,daga ke har masu aikin gidan duk kun amince da hakan,wannan shine dalilin da ya sa kika ga ko wajen karatu zaki je nake biye da ke.....ni zan tafi,Allah ya tsare ku." Baki sake Lamyah ke sauraro da kallon Idris,har ya ɓacewa ganinta bata iya furta komai ba banda hawaye da ke kwaranya a idanunta,shin me yake faruwa da rayuwarsu? Dama mahaifinta ya san da zuwan wannan ranar da za su rabu babu kyakkyawar sallama amma bai taɓa sanar da

Chapter 7 of 30