Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ga Momma sai ta yi masa sharri har Momma ta dake shi,amma idan ta yi a gaban Aminee sai Aminee ta ce. 'Ki rantse da Allah ya dake ki.' Nan take asirin ta yake tonuwa saboda Aminee ta riga ta nuna musu girman Allah,da gudun rantsuwa akan ƙarya. Ƙwafa ya yi ya fita,a ransa ya na ayyana ai Iyan za ta tafi ne,zai ga me ƙwatarta a hannunsa. Sai da suka karya sannan Iya ta tafi gida da ƙafa cike da farinciki,ta na isa ta shiga sashen Momma ta labarta mata duk abinda ya faru,hamdala sosai Momma ta yi tare da yi wa Iya godiya akan ƙoƙarin da ta ke yi wa Iyalanta. Hira suka ci gaba da yi,a nan Iya ta samu labarin Abii ya tafi Nigeria. Tinda suka raka Abii mota Mubarak ya tsaya wasa  da sabuwar motarsa babba irin wadda yara ke iya shiga ciki ɗinnan su tuƙa. **************** Bayan sati ɗaya Lamyah ta warke kuma Aminullahi na ƙoƙarin daidaita lamuransa,duk da cewa har a wannan lokacin yana yin komai da taka tsantsan,Layuzah bata san wainar da ake toyawa ba. Yau ma kamar koda yaushe ta ci kwalliya ta fito hannunta riƙe da jakarta da wayoyinta masu tsada,makullin motarta take ta kaɗawa ta tsaya a saman kan Aminullahi ta ce. "Na tafi gidan Hajiya sai na dawo." Kallonta Aminullahi ya yi fuska a haɗe ya ce. "Ban gane kin tafi gidan Hajiya ba sai kin dawo,wai ke me ya sa kike yi min magana da gadara ne? Ko ki na manta cewa ni ɗin mijin ki ne?" Gabanta ne ya yi mummunar faɗuwa,lallai da alama ta na buƙatar sabunta riƙon da ta yi wa Aminullahi,dan haka sai ta sassauta muryarta ta ce. "Haba baby, ta ya zan manta matsayinka a waje na? Ka san jiya na nuna maka ƙurjin da ya fito min a cibiyata to fa shine zan je Hajiya ta kai ni wajen me magani,kasan irin abubuwan nan maganin gargajiya ya fi." Ba tare da ya bata amsa ba ta sa kai ta bar gidan zuciyarta na bugawa da sauri da sauri. Ta na shiga mota ta rintse ido saboda yanda take jin zogin ƙurjin da ya fito mata a bakin cibiyarta. A hankali ta furta. "Bari na je na ga likita akan wannan ƙurjin dake son hana ni rawar gaban hantsi na dawo kan ka." Mota ta kunna ta fita ta bar gidan cike da tinani kala-kala a cikin ranta. Aminullahi kuwa na ganin ta fita ya lallaɓa ya rufe gidan tare da kunna talabijin ya nufi ɗakin Lamyah. Ya na shiga ya ci karo da ita a gaban madubi ɗaure da towel ta fito daga wanka ta na shafa HAMIBRAH SKIN OIL a jikinta,banda ɗaukar ido da sheƙi babu abinda cinyoyinta da ta gama mulkewa da man ke yi. Wani irin abu ne ya tsarga masa wanda bai taɓa jin sa akan kowacce mace ba. Da sauri Lamyah ta juya ta na kallon sa idanunta kamar za su faɗo ƙasa saboda tsoro tare da fargaba. Hannu ta fara yarfewa ta na kukan shagwaɓa tare da bubbuga ƙafafunta a ƙasa. Murmushi Aminullahi ya sakar mata sannan ya ce. "Wato kin ma san me ya kawo ni ko? To zo nan ki sauke nauyin dake kan ki,in dai kina so na ɗaga ƙafa ta ki shige aljannah a guje." Hawayenta ta share ta na tura baki,ta maƙale kafaɗarta ta dama,a hankali take bin bango ta na son guduwa cikin banɗaki,gane hakan da ya yi ne ya sanya shi yin takun da bai fi uku ba ya damƙe ta. Bayan awa guda da wasu mintuna Aminullahi ne ɗauke da Lamyah da ta kwanta a jikinsa ta na kukan shagwaɓa,shi kuwa haƙuri kawai yake bata tare da yi mata daɗaɗan kalaman da suke nitsar da ita a cikin kogin ƙaunarsa. A haka bacci mai daɗi cike da nishaɗi ya ɗauke su. ***************** Layuzah bata bar asibiti ba har sai da aka fasa ƙurjin da ya fito mata aka ɗebi sample aka kai lab saboda a gwada a ga me yake damunta,bayan nan har gwajin sugar an yi mata aka tabbatar bata ɗauke da ciwon sugar. Daga asibiti gidan Hajiya ta wuce ta bata labarin halin da take ciki da Aminullahi,Hajiya ce ta kalle ta ta ce. "Ni fa na fara gajiya da bawa waɗannan mutanen maƙudan kuɗi,aiki duk wata sai an sabunta shi kamar aikin gwamnati,ina laifin su dinga yin aikin da zai kai shekara bai karye ba? Amma bini-bini muna hanyar gidan bokaye da ƴan bori suna cacumar kuɗaɗe akan aiki ƙalilan? Ke ma dai Layuzah ki fara gwada ƴan dabarun nan namu na mata mana,ai rayuwar nan mutum ba zai dogara da asiri kaɗai ba." "Ni kaina abun na damu na Hajiya,da ace tara kuɗaɗen da muke kai wa masu taimakon nan muke yi to da mun sayi babban fili ko wata kadarar. Amma zan je na yi iya tawa dabarar na gani,idan ban samu yanda nake so ba dole ne mu koma gidan sabon malamin nan,dan gaskiya ni ba zan so Aminullahi ya juya min baya ba." Sallama suka yi da Hajiya ta tinkari hanyar gida. Hankalinta ta ji yana tashi har tsigar jikinta na miƙewa,rashin sanin abinda ya dace ta yi ne ya sanya ta kunna waƙa ta hau bi ko zai ɗauke mata damuwar dake ranta. Ta na isa gida ta danna oda mai gadi ya wangale mata gate ta shige,ta na shiga ta ga motar Aminullahi,sai ta kalli mai gadi ta ce. "Alhajin naka bai fita bane yau?" "Eh Hajiya,babu wanda ya fita tin bayan da kika fita,sannan babu wanda ya zo." A hasale ta ce. "Ban tambaye ka ko an yi baƙi ko ba a yi ba,shegen shisshigi da iyayi ya maka yawa." Tsaki ta ja ta nufi ƙofar gidan,sai ta ji ta a kulle,makullinta ta sanya ta buɗe amma ta fuskanci ta ciki aka rufe,hakan ne ya sanya ta jin mamaki da tsoro sun dabaibaye ta a lokaci ɗaya,da sassarfa ta bi ta ƙofar kitchen ta shiga cikin gidan ranta a ɓace. Ta na shiga ciki ta tarar da talabijin na aiki,gidan shiru kamar babu kowa. A hankali ta lallaɓa ta nufi hanyar ɗakin Lamyah............. [9/11, 10:50 AM] zee hussain: ƳAR RAWA. RUBUTAWA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✍️✨ PAGE 40. Tin lokacin da Layuzah ta buɗe ƙofar kitchen ta shigo gidan Lamyah ta farka,sai dai irin riƙon da Aminullahi ya yi mata ne ya sanyata kasa motsawa daga inda take,sake lafewa ta yi a jikinsa ta lumshe idanunta ta na tina soyayya da kalaman da Yah Amee ya dinga zuba mata. Ƙarar buɗe ƙofar ɗakin nata ne ya firgita Aminullahi dake sharar bacci har ya farka a firgice,wani irin mugun kallon tsana da ƙiyayya Layuzah ke bin su da shi. Ƙafarta ta ɗaga ta na takawa zuwa cikin ɗakin da ƙyar,sai dai nauyin da suka yi mata ne ya sanya ta faɗuwa a inda take,cikin kuka mai tsanani ta ce. "Tsawon wanne lokaci kuka ɗauka kuna cin amanata a gidan nan?" Shiru suka yi mata babu wanda ya amsa ta,Lamyah kuwa tashi zaune ta yi ta na miƙa tare da tattare gashinta ta ɗaure shi waje ɗaya da ƙaramin hair band ɗin hannunta,Aminullahi kuwa jan numfashi mai nauyi ya yi ya sake maida kansa cikin pillow ya na shafa fuskarsa zuwa wiyansa,ganin yanda suka maida ita mahaukaciya ne ya sanya ta miƙe wa da wani irin ƙarfin da bata san tana da shi ba ta yi kan Aminullahi ta hau shi da duka,domin a yanzu tsoron taɓa jikin Lamyah take yi kar ta illata ta,ganin Aminullahi na kwance ko gezau bai yi bane ya baƙanta ran Lamyah,a zuciye ta tashi daga inda take ta ɗaga Layuzah sama ta buga da ƙasa,ƙara ta saki mai razanarwa. Sai da Lamyah ta sanya rigarta da Aminullahi ya yi cilli da ita sannan ta isa gaban Layuzah ta duƙa tana nuna ta da yatsanta manuni,cikin kakkausar murya ta ce. "Daga yau sai yau kar ki sake ɗaga hannunki ki daki mijina a gabana,domin shi ɗin ba ɗan ki bane,idan baki da ilimin mace bata dukan mijinta to ni zan koya miki,dan kuwa mai waje ta zo mai tabarma sai ta naɗe kayanta,idan kunne ya ji jiki ya tsira." Kafin Lamyah ta bar inda take tsaye Layuzah ta ce mata. "Ke tsinanniya matsiyaciya ragowar mazan bariki,kin isa ki nuna min isa akan mijina? Har ki mutu ba zaki sake samun damar nan da kika samu ba,ki rubuta ki ajiye ke da Aminullahi kun rabu kenan rabuwa ta har abada." Dariya Lamyah ta yi kafin ta juya ta kalli Layuzah ta ce. "Ke baki gane cewa aron shi na baki ba shi ɗin mallaki na ne? Da ni da ke zan ga wadda za ta bar Yah Amee bari na har abada." Banɗaki Lamyah ta faɗa ta na jin takaicin yanda Aminullahi ya zauna yarinya ƙarama kamar Layuzah ta na juya rayuwarsa,da alama har a wannan lokacin be dena jin tsoronta ba. Ta na wanka ta jiyo Layuzah na ɗura masa ashar irin na tasha ɗin nan,ba tare da ya ce komai ba ya taimaka mata ta tashi suka wuce ɗakin ta. Kuka ta dinga yi masa tana jera masa Allah ya isa da tsinuwa,bai kula ta ba ya wuce ya shiga ɗakinsa ya yi wanka sannan ya fito ya yi sallah. Da dare Layuzah na kwance ƙafarta ta yi tsami Aminullahi ya shiga da man zafi,kama ƙafar ya yi ya ja mata sosai ya shafa mata man, sannan ya miƙe zai fita,cikin zafin nama ta riƙe masa hannu ta na faɗin. "Ina za ka je baƙin munafuki? Ai da ga yau babu kai babu wannan karuwar..." Kallon da Aminullahi ya sauke mata ne ya sanya ta kasa ci gaba da zagin cin mutuncin da take yi wa Lamyah. Hannunsa ya fizge ya fita daga ɗakin rai a ɓace,kai tsaye ɗakinsa ya nufa ya hau gado ya na tina moment ɗin su da Lamyah,murmushi ne ya kuɓuce masa,ji ya yi kamar ya tashi ya je gare ta,sai dai kunyar haɗa ido da ita yake yi,a gabanta mace ta gama zaginsa,zagi irin na cin mutunci wanda ko zaman dadiro yake da Layuzah a ganinsa akwai girmamawar da ya kamata ta basa a matsayinsa na me sauke nauyin duk da ya rataya akan shi,amma sam bata duba hakan idan ta tashi rashin mutuncinta idonta rufewa yake yi. Da misalin ƙarfe ɗaya da rabi na dare Lamyah ce kwance ta na ta daure wa,saboda bata son ta ci abinci saboda fushin da take yi da Aminullahi. Ji ta yi yunwa ta addabe ta ba za ta iya jurewa ba,sai ta miƙe ta ɗauki ƴar ƙaramar kimono ɗinta da take iya cinyarta ta ɗora a saman ƙaramar shimin da ta sanya iya cinyoyinta. Kitchen ta nufa kai tsaye ta kunna fitila ta buɗe fridge ta na duba abinda za ta iya ci,cake ɗin da ta yi tin kwanaki uku da suka wuce bata ci ba ta ɗakko ta saka a microwave ta dumama,ta na gamawa ta ciro shi ta ɗakko lemo,gani ta yi an kashe fitilar kitchen ɗin duhu ya mamaye ko ina sai iya na fridge da ta buɗe,murya na rawa ta ce. "Waye a nan?" A hankali Aminullahi ya amshe lemon da plate ɗin ya kulle fridge ɗin da ƙafarsa,ajiye abincin ya yi sannan ya ɗauke ta cak ya ɗora ta a saman dinning ɗin dake tsakiyar kitchen ɗin, buɗe baki Lamyah ta yi zata zunduma ihu Aminullahi ya rufe mata baki,tin tana tirjewa riƙon sa da abubuwan da yake yi mata tare da ban haƙuri har ta haƙura ta saki jikinta ta bada kai bori ya hau. Sai da komai ya lafa a tsakanin su sannan ya ɗakko mata cake ɗin ya kunna wuta ya na yankowa da ƙaramin spoon ya na bata a baki,kallonsa take yi cike da so da ƙauna shima ya na aika mata nashi salon,a haka Layuzah ta tarar da su, zage-zagen da bata gajiya ta hau auna musu,hakan ba ƙaramin ƙona ran Aminullahi ya yi ba,cikin zafin nama ya juya ya wanke ta da mari,sannan ya nuna ta da yatsa ya ce. "Na gaji da rashin tarbiyyar da kike yi min a cikin gidan nan,ni fa mijinki ne ba ɗan ki ba. Dan haka ki tattara ki bar min gidana a yanzu ba sai gobe ba ki koma can wajen uwarki ta sake baki tarbiyya,na gaji da halin dabbobin da kike yi min a gida." Hannunta ya ja ƙi ya wurga ta ɗakinta,ya na tsaye yana yi mata masifa tare da gorin irin haƙuri da kulawar da ya yi mata,kwasar kayanta ta hau yi ta na kuka tare da mamakin yanda cikin ƙanƙanin lokaci Aminullahi ya rikiɗe ya koma wani mutum na daban da bata taɓa gani ba. Lamyah ce ta kama hannunsa ta ce. "Yah Amee ƙarfe biyun dare ta wuce fa,ka yi haƙuri zuwa gobe sai ta tafi." Kallon da ya zuba mata ne ya sanya ta yin gefe ta na ƙyafta idanu, Layuzah kuwa harara ta banka mata sannan ta ce. "Ke makira munafuka,ni za ki yi wa bariki? Zuciyar ki fal farinciki an kore ni,amma kin zo kina magana kamar ta Allah. Zan tafi a yau tabbas,amma ki sani za ki yi danasanin fita ta a gidan nan da zan yi a yau,don haka ki rubuta ki aje watan shigar ki tashin hankali da masifu ne ya kama, shashasha kawai." Ta na gama faɗar haka ta ja akwatinta guda ɗaya da ta cika da kaya da ƴan abubuwan da ta tara,sai handbag ɗinta da wayoyinta tare da makullin motarta. Ko da ta je za ta fita mai gadi ƙin buɗewa ya yi,ya hau kiran Aminullahi,Aminullahi na zuwa sai ya ce. "Buɗe mata ta tafi,daga yau kar ka sake ka barta ta shigo gidan nan sai da izini na,idan kuma ka barta ta shiga a bakin aikin ka." Da sauri mai gadi ya buɗe mata gate ta figi motar ta ta bar gidan. A hanya banda kuka babu abinda take yi,sai da ta yi nisa da gidan sannan gabanta ya hau faɗuwa tsoro ya kamata, addu'a ta fara yi Allah ya tsare ta ta isa gida lafiya. Lokacin da ta isa gida ƙarfe biyu da rabi na dare ta yi, ƙwanƙwasa ƙofa ta dinga yi saboda kada ta yi oda a gane ita ce ta zo da tsohon dare. Da ƙyar Hajiya ta iya buɗe idanunta da suka yi mata nauyi saboda bacci,maganinta na hawan jini da ta sha shi ne yake sanya ta bacci mai nauyi. Ta na gama buɗe ido ta ji an sake buga ƙofa,tsoro ne ya sanya ta wartsakewa gaba ɗaya,a tinaninta ɓarayi ne suka kawo mata ziyara. Wayarta ce ta hau ringing babu ƙaƙƙautawa,hannu na rawa ta ɗauka,Layuzah ta gani a jikin screen ɗin wayar,cikin hanzari ta amsa ta ce. "Na shiga uku layuzah ɓarayi ne ke buga min gate yanzu haka da tsohon daren nan." "Hajiya ba ɓarayi bane ni ce zo ki buɗe min na shigo,na ga maƙota sun fara buɗe gate ana hasko ni." A rikice Hajiya ta sauka daga gado ta nufi waje,sai da ta wangale wa Layuzah gate ta shiga sannan ta koma ta rufe,cikin jimami ta kama hannun Layuzah dake ɗingisa ƙafa suka shige cikin gidan. A daren Layuzah ta labartawa Hajiya duk abinda ya faru,haƙuri ta bata sannan ta lallashe ta ta ce. "Ki yi haƙuri,bari idan Allah ya kaimu gobe zan kirawo kawun ki Sale ya je ya bashi haƙuri ki koma ɗakin mijinki,yaushe zan ɗauki ƙaddarar rabuwar ki da Aminullahi? Inaaa ba zai yuwu ba ai,idan ya rabu da ke ina na kama?" Haka suka kwana hira ko rintsawa basu kara yi ba. Washegari tin ƙarfe bakwai na safe Hajiya ta rangaɗawa ƙaninta da suke uwa ɗaya uba ɗaya waya ta labarta masa duk abinda ya faru,alƙawari ya yi mata da ya samu lokaci zai shigo a cikin satin. Bayan sun yi sallama ne Hajiya ta ci gaba da baiwa Layuzah baki tana lallashinta. Tin daga wannan rana Lamyah da Yah Amee ɗinta suka buɗe sabon shafin soyayya a cikin gidan,a cikin satin suka kai wa Momma ziyara har Aminullahin,wanda rabon da ya taka gidan nasu har ta manta,Momma ta yi kuka sosai sannan ta yi farinciki tare da godewa Allah da ya nuna mata ranar da ta jima tana roƙon zuwanta. Har Iya aka taru ana ta hira,Iya sai murna take da fatan Allah ya sa ma daga ƙarshe Aminullahin ya aika wa Layuzah takardar saki kowa ya huta. A cikin satin Abii ya dawo daga Nigeria,bayan ya huta ne ya sa aka kira su Aminullahi,takardun kadarori da dukiyar su Lamyah ya damƙa mata ya ce ta na da damar yin duk abinda ya dace da dukiyarta,idan tana so a ci gaba da juya musu ma duk za a iya yi musu hakan,sannan kuɗaɗen da ya tura mata a bankin su sabo da aka buɗe musu ita da Mubarak ya shawarce ta da karta taɓa su,ta bari har yaron ya girma sannan a yi masa bayani,daga nan duk yanda suka ga za su yi da ita shikenan sai su yi. Godiya sosai Lamyah ta dinga yi wa Abii har da kukanta. Bayan kammala tattaunawar tasu ne suka yi wa Baaba da Ammi addu'a. Tare suka ci abincin dare kafin su yi musu sallama su koma gida. Washegari da safe wayar Afrah ce ta tada Lamyah daga bacci,Aminullahi ne ya miƙa mata wayar cikin magagin bacci tare da toshe kunnensa da pillow. Idanunta na kullewa ta amsa wayar Afrah,kamar wadda aka mintsina ko aka fallawa mari Lamyah ta buɗe idanuwanta ta kwalla ƙarar farinciki,saman Aminullahi ta haye ta na ihun murna,a can ɓangaren kuwa Bala da Afrah suma dariyar suke ta faman yi,cikin tsananin murna Lamyah ta ce. "Da yaushe kika gano kina ɗauke da ciki?" 'Jiya da dare muka je asibiti,saboda yawan kwaɗayi da nake fama da shi da tara yawu,sai kuma zazzaɓin cikin dare da nake yawan yi. Likita na dubawa ya gano ina ɗauke da cikin watanni huɗu da sati biyu. Tin a jiyan na so na sanar da ke na ce bari dai na bari yau na tashe ki da daddaɗan labarin da zai sa ki wuni kina murmusawa.' "Wannan labarin zai ci gaba da sanya ni murmushi har ƙarshen rayuwata ne Afrah,Allah Ya raya mana ya inganta,Allah kuma ya sauke ki lafiya,Ina yayana Baba Bala?" Dariya sosai suka fashe da shi,kafin Afrah ta ce. 'Ai na faɗa masa Baba yaranmu za su dinga kiransa shi kuma ya ce sam baya so,be kira mahaifinsa da Baba ba,babu ɗansa da zai kirasa da Baba,sai dai Abbah ko Daddy.' "Su Daddy manya,bani shi mu gaisa." Cikin sauri Aminullahi ya karɓe wayar ya amsa sallamar Bala. Congratulations ya yi masa sannan ya ce a gaishe da Afrah,Allah Ya sauke ta lafiya. Yana gamawa ya kashe wayar,kallon Lamyah ya yi sannan ya ce. "Kar ki dinga mantawa,mijinki na da tsananin kishi,haka kawai da sassafe a lokacin da muryar ki ke tsaka da zaƙinta zaki yi wa wani namijin magana." Dariya sosai Lamyah ta yi ta faɗa jikinsa ta na jin daɗin yanda yake nuna mata so da ƙauna,a shagwaɓe ta ce. "To Allah na tuba Bala meye nawa be sani ba kuma?" "Wannan,da wannan da wannan da wancan." Aminullahi ya faɗa ya na nunnuna ta,tare da kashe mata jiki da salonsa,da ƙyar ta kwaci kanta ta shiga banɗaki. Tin daga wannan rana kullum sai ta yi waya da Afrah ta ji me take so,menene bata so da kuma abinda ke damunta. Haka ta ɓangaren Mama Tani da Baba Musa,suna matuƙar ƙoƙari wajen nuna wa Afrah gata,sai hakan ya wanke mata kewar iyayenta da take yi a koda yaushe. Ƙannen mahaifanta kuwa ba a cinye wata guda sai wani daga cikinsu ya kai mata ziyara,gaba ɗaya sun nuna mata sun yi danasani akan watsar da rayuwarta da suka yi a baya,a yanzu suna so su gyara alaƙar su da ita,ita kuwa ta ce ta yafe musu amma bata son kowa ya raɓe ta,gaisuwa dai da sada zumunci za a yi shi saboda Allah,amma babu wanda ta amincewa da ya shiga rayuwarta su zama ƙut da ƙut saboda tsoron abinda zai iya zuwa ya dawo. *********************** *DUBAI* Ganin jimawar da su Zaid suka yi ne basu kawo wa Muhammad wani labari ba game da Nigeria da tafiyar da yake so su yi dan nemo su Lamyah ne ya sanya shi siya musu tikitin jirgi su huɗu har da shi,domin zuciyarsa ta gama raya masa kar ya yarda da ƙannen nasa,dan suna iya samo dukiya mai yawa su ɓoye wani kaso su yi masa ƙarya tinda akan wannan tafarki suke gaba ɗayan su. Lokacin da ya sanar da su shawarar da ya yanke sai suka ji ƙwarin guiwar yin tafiyar,ko babu komai gaba yake da su,kuma ya fi su zurfin nazari,sun tabbatar da zai zamo jagoransu a tafiyar. Hankali kwance suka fara shiri dan zuwa Nigeria tattara kan dukiyar ɗan'uwansu........ [9/11, 10:50 AM] zee hussain: ƳAR RAWA. RUBUTAWA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✍️✨ PAGE 41. A Jihar Lagos ta Nigeria jirgin su Muhammad ya sauka daga Dubai. Tun a airport idanuwansu suka fara raina fata,domin kuwa hotunan Lamyah da Mubarak kawai Zaid ya samo a Facebook,wanda sau ɗaya ta taɓa posting tin buɗe account ɗin nata,babu wani information da ta sanya da zai nuna musu inda take da ya wuce sunanta da na mahaifinta da ta sanya. Cikin yaren turancin da ba wani ƙwarewa El-Hassan ya yi ba ya nuna wa wasu masu taxi hoton Lamyah ya ce musu. "Please my brozar did you know herr?" (Don Allah ɗan'uwana ka san ta?) Kallon juna Emmeka da Ezikel suka yi,cikin ƙanƙanin lokaci suka yi wa junansu magana da idanunsu,nan take Emmeka ya washe baki ya ce. "Yes I know her na,who no know this girl for this town i beg? Come i go take you to her na na na na." (Eh na santa mana,waye be san wannan yarinyar ba don Allah? Zo na kai ku wajen ta yanzu yanzun nan.) Cike da tsananin farinciki su Muhammad suka shiga mota suna gyara lulluɓin kansu suna zuba larabci. Cikin harshen larabci Zaid ya ce. "Lallai El-mustapha ya shahara da kuɗi a Nigeria,ku duba ku ga tin a filin jirgi an samu wanda suka san ƴaƴansa?" Gasgata shi suka dinga yi,tare da jaddada plan ɗin su na yanda za su ƙwace dukiyar yaran sannan su tasa ƙeyar su gaba su maida su Dubai. Emma da Ezi kuwa hira suka dinga yi da yarabanci,dan haka har suka gama maganar da suke yi babu wanda ya san abinda suka tattauna a tsakanin su.Sun jima suna tafiya mai nisa kafin su shiga wata unguwa mai bala'in kyau,da ganin wajen sai mutum ya rantse babu ƴan Nigeria a wajen ko ɗaya saboda yanda unguwar take kamar a turai. A wani kantamemen gida da ya fi kowanne gida kyau a unguwar suka tsayar da taxi ɗin,oda suka dinga dannawa mai gadin gidan wanda yake sanye da wasu baƙaƙen kaya,kansa kuma ya ɗaura jan ƙyalle,damtsen sa ma haka. Sai da ya tabbatar da su Emma ne sannan ya wangale musu gate suka shigar da motar. Cike da mamaki su Muhammad ke kallon yanda aka bar Taxi ta shiga ƙaton gida kamar haka, El-Hassan ne ya ce. "Da dikkan alamu sun gane mu ƴan'uwan mahaifinta ne shi yasa aka karrama mu haka aka shigar da mu har ciki don kar mu wahala." Mazaje suka dinga gani baƙaƙe wuluk da baƙin kaya tare da ɗaurarren jan ƙyalle a goshin su da damatsan su,haka dai suka tattago akwatinan su suka fito,jagora su Emma suka yi musu fuska sake har suka isa wani ƙaton parlour,kasancewar su ma masu arziƙi ne sai abun bai ɗaɗa su da ƙasa ba,sai dai sun yi mamaki sosai da aka samu irin wannan gidan a cikin Nigeria,nan take yanda suka raina ƙasar a ransu ya kau,sai da suka wuce manyan parlour guda biyar kafin su isa wani madaidaici mai ɗauke da sassauƙan ado da kujeru,anan Ezi ya yi musu nuni da su zauna,suna zama suka shiga wata ƙatuwar ƙofa,durƙusawa suka yi a cikin ɗakin dake da tsananin duhu suka kwashi gaisuwa kafin wata ƙatuwar murya ta ce. "Well-done Emma and Ezikel,you two de do your work well oo,oya make una go inside and carry two boxes." (Jinjina a gare ku Emma da Ezikel,lallai ku ɗin nan kuna yin aikin ku da kyau fa,to ku shiga ku ɗakko akwatina biyu.) Cike da ladabi Emma da ya fi Ezi mugun son abun duniya ya ce. "Ah boss only two boxes na four men dey there oo,i beg give us four boxes na." (Ah yallaɓai akwati biyu kawai? Mutane

Chapter 25 of 30