Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ne ma ya fi amfani da shi,yana zama ya lalubo lambar Zahrah ya ce ta kai masa abinci a ƙaramin parlour,cike da ladabi ta amsa shi sannan ta hau shirya masa abinda aka gama dafawa na dare. Lamyah kuwa ta warware har sun fara wasa da Mubarak,Abii da Momma suna zaune suna kallon su cikin jin daɗi da tsantsar farinciki. Mubarak ne ya ƙwacewa Lamyah Apple ɗin da take ci ya ruga waje da gudu,babu ɓata lokaci ta mara masa baya suka hau gudu suna zagaye gidan,babu zato babu tsammani Mubarak ya faɗa parlourn da Aminullahi ke zaune yana jiran abincinsa ya ci ya bar gidan babu wanda ya gansa. A guje Lamyah da ke sanye da wata doguwar riga irin ta larabawa koriya shar sai tashin ƙanshi take yi kanta babu ɗankwali gashin nan ya sha gyara ta afka parlourn tana faɗin. "Idan na kama ka sai na wahal da kai,ko an faɗa maka ni Afrah ce?" Muryarta ce ta sanya shi saurin tashi daga zaman da ya yi ya kalle ta,itama kallonsa ta yi a hargitse,a tare suka furta. "Ke/kai? Me ka/ki ke yi a gidanmu?"..... [9/11, 10:50 AM] zee hussain: ƳAR RAWA. RUBUTAWA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✍️✨ *Jama'ar musulmi ina mai tallata muku kayan gyaran jiki natural,wanda ke sanya fata glowing ba bleaching ba. Ki yi kyau ki yi suɓul kamar sabuwar jinjira akan farashi mai sauƙi,sannan ina sayar da HAIR PRODUCTS masu kyau da za su gyara maki gashi,siyan ɗaya ko sari ga duk mai buƙata ta min magana a wannan lamba. 09031416423. Idan kuma ke amarya ce kina so a yi miki haɗin body scrub,skin oil da Body butter ki yi magana saboda ki fita kunyar ango.Sannan akwai Paid novels masu daɗi da ma'ana,akwai littafin MAIDA TSOHUWA YARINYA wanda ya ƙunshi natural kayan gyaran jiki,ga mai buƙata kuma tana tsoron siyan littafi online ya goge bata mora ba...email address ɗin ki kawai za ki bayar a tura miki ta can ki adana abunki,ko shekara nawa kike son karantawa zaki leƙa ki karanta abunki.* PAGE 34. Shiru suka yi gaba ɗayan su suna bin junan su da wani irin kallo. A hankali Lamyah ta matsa gefe Zahrah ta shiga ta direwa Aminullahi abincin da ta kawo masa jikinta a sanyaye saboda furucin da ta ji sun yi wa junan su da kallon da suka kafe juna da shi. Cikin azama ta bar parlourn ta nufi sashen Momma,ta na shiga ta zube a gaban su ta ce. "Hajiya ga fa Alhaji ƙarami ya shigo ya ce na kai masa abinci ƙaramin parlour,ina komawa kai masa na tsinkayi muryoyinsu shi da Hajiya Lamyah a sama,da alama dai babu lafiya." Cikin sauri Abii ya miƙe har ya na tuntuɓe ya nufi hanyar ƙaramin parlour,Momma ma ba a barta a baya ba wajen mara mishi baya,a tsaye suka tarar da su Lamyah na zubar da hawaye saboda baƙaƙen maganganun da Aminullahi yake gasa mata,cikin tsananin ɓacin rai ya ke faɗin. "Uhumm ki bani amsa mana? Kina ji ina miki magana kin tsaya ki na ƙure ni da shegun idanuwanki da kika saba kallon maza da su,idan ma karuwancin na ki ne ya sa kika biyo ni har ƙasar mu kuma kika zo har gidan mu,to ki gaggauta barinsa dan kuwa ko a mai aiki ba za mu ɗauke ki ba ballantana na haɗa jikina da ke." A tsawace Lamyah ta ce. "Ya ishe ka haka! Kar ka sake jifa na da wannan mummunar kalmar ta karuwa,ni ba karuwa bace,ban taɓa kusantar zina ba tinda nake a duniya,kuma ina neman tsarin Allah da ya kare ni daga aikata ta har na koma gare shi." "To idan ke ba karuwa bace me ya ke kai ki wajen maza ki dinga yi musu rawa ki na juya jikin ki,har su dinga kallon wasu sassa na jikin ki wanda mijinki ko wani muharramin ki ne kaɗai ke da ikon gani? Ko an faɗa maki ita zina sai mutum ya aikata ta a aikace ne kawai take zina?" "Ban sani ba! Na ce ban sani ba ɗin! Ba zan baka amsa ba,ka ɗauke ni a duk yanda kake so ka ɗauke ni,bani da haɗi da kai na kusa ko na nesa da zan tsaya yi maka bayanin rayuwa ta,ni naga dama na zamo ƳAR RAWA a baya,kuma ko a yanzu na samu damar da na samu har na cika burin raina zan sake maimaita wa,idan kana da abinda za ka yi sai ka yi." "To ba dai a nan gidan za ki yi iskancin da kika saba ba,duk uban da ya kawo ki cikin gidan nan ya zo ya maida ki inda kika fito,karuwa kawai." Gyaran murya Abii ya yi wanda ya sa Lamyah juyawa ta kalle su,domin kuwa shi Aminullahi tin zuwan su ya gansu bai ga damar barin musayar yawu da macen da ta ke bashi rikitaccen yanayi a cikin zuciyarsa ba ne kawai,ganin ta a gidan su ya tado masa da tsantsar ƙauna da soyayya tare da kewar da yake yi mata,sai kuma baƙin cikinsa ɗaya da ta zamto karuwa wadda maza da dama suka gama ganewa surar jiki,har a cikin ransa bai gama yarda wai bata bin maza ba kamar yanda Faisal ya ce masa,gani yake yi kamar raina masa hankali kawai ake yi. Cikin wata iriyar murya Abii ya ce. "Ni ne nan uban da na kawo ta gidan nan,ban kuma ji zan mayar da ita inda na ɗakko ta ba,saboda itama nan ɗin gidan ubanta ne." Da sauri Aminullahi ya kalli Abii,sannan ya juya ya maida kallon sa wajen Momma kafin ya dire idanunsa akan Lamyah da ke sharɓen kuka,cikin kakkausar murya Aminullahi ya ce. "Idan kuwa na tafi daga gidan nan kada wanda ya neme ni,dan ba zan zauna inuwa ɗaya da karuwa ba." "Dama ai ka jima da ɗauke ƙafafun ka a gidan nan,dan haka idan ka tafi ka yi zaman ka a inda ka ga ya fiye maka nan ɗin,fatan mu a duk inda ka ke Allah ya kare ka." A zuciye Aminullahi ya ratsa ta tsakanin su ya bar wajen,Lamyah da Momma ji suka yi kamar su bi sa da gudu su rungumesa,wata iriyar soyayyar Handsome ce ta yunƙuro ta toshe wa Lamyah kafar shaƙar numfashinta,nan take ta fara jan numfashi kamar mai cutar fuka,a daddafe ta kama gini ta wuce ɗakinta,Iya ta jiyo tana wanke mata banɗaki,ba tare da ɓata lokaci ba Lamyah ta faɗa gadonta ta rushe da wani irin kukan da ke sarƙe mata numfashi,Momma na isa ɗakin nata ta zauna a bakin gado ta ɗago ta ta rungume ta,a gigice Iya ta fito daga banɗaki tana bin Lamyah da kallo,cikin tashin hankali ta ce. "Hajiya Lafiya take irin wannan kuka haka?" Murya ɗauke da jimami Momma ta ce. "Humm ina fa lafiya? Yau wannan yaron ya zo gidan nan,ban san a inda suka san juna ba amma dai sun yi ɗauki ba daɗi a tsakanin su,na rasa dalilinsa na kiran ta da mummunan sunan da ya kirata da shi. Kin ga bani ruwa mai sanyi ta sha ko zuciyarta za ta sanyaya." Cikin sauri Iya ta fito daga banɗakin jikinta na rawa ta buɗe fridge ta ɗauki ruwa mai sanyi ta miƙa wa Momma,buɗe marfin robar Momma ta yi ta kafawa Lamyah ruwan a baki,babu ɓata lokaci kuwa ta hau shan ruwan kamar rayuwarta ta ta'allaƙa a jikinsa,bata ɗauke kanta ba sai da ta shanye gora guda sannan ta hau ajiyar zuciya. Suna nan zaune Momma na rungume da ita tana lallashi bacci mai daɗi ya fara satar ta. Duk da cewa la'asar ta wuce bai sa Momma tashin ta ba,sai ma gyara mata kwanciya da Momma ta yi suka rufe mata ɗakin suka barta ta huta. Cikin bacci Lamyah ta hau mafarkin Aminullahi a wani gida mai duhu,shigarta cikin gidan sai duhun ya ƙara mamaye gidan har bata iya hango shi kamar yanda ta gan sa da farko,a hankali kuma duhun ya fara yaye wa ta gansa da kyau,sai dai wannan matar ta rannan da ta zo gidan na gefen sa ta na cin wani irin ɗanyen nama ta na wata muguwar dariya kamar a horror film,a firgice ta farka daga baccin bakinta ɗauke da addu'ar tashi daga bacci. Kiran sallar magaribar da ta jiyo ne ya sanya ta nufar banɗaki ta yi tsarki sannan ta ɗaura alwala. Ta na fitowa ta gyara shimfiɗar sallayarta ta hau yin sallar magariba,bayan ta idar sai ta zauna ta hau yin azkar ɗinta da bata yi ba,ta na nan har aka kira Isha'i bata fita ba. Sallar Isha'i ta gabatar sannan ta sake yin addu'o'in ta na bayan kowacce sallah ta miƙe ta naɗe hijabinta da abun sallar,ajiye su ta yi a muhallin su ta haye gado bayan ta kashe fitila. Fuskar Aminullahi ce ke yi mata gizo,idanunta ta lumshe ta na sauraron yanda zuciyarta ke sanar da ita yana kusa da ita har ma yana so ya haɗa fuskarsa da tata. Hasken da ya gauraye ɗakin ne ya sanya ta buɗe ido ta juya,Momma ta gani a tsaye bayanta Iya ce ta na ɗauke da babban faranti,zama suka yi suka hau yi mata hira tare da ƙoƙarin mantar da ita damuwarta,abinci Momma ke bata a baki,Mubarak ya shiga,hannayensa ya goya a ƙirjinsa sannan ya tura baki ya ce. "To ni wa zai bani abinci a baki yau?" Murmushi Lamyah ta yi sannan ta ja shi jikinta ta hau gutsurar sinasir tana dangwalar miya tana bashi a baki,a haka suka dinga hira Iya na basu labarai na abun dariya,duk da cewa Lamyah ta ɗan saki jikinta kaɗan amma a cikin zuciyarta tana son sanin wai shi Handsome da ta gani meye matsayinsa a gidan? Suna kammalawa Iya ta kwashe kwanukan ta kai kitchen,ko da ta dawo ta tarar da Momma ta yi mata sallama ita da Mubarak sun tafi,itan ma sallama ta yi mata tare da ja mata ƙofa ta tafi. Lamyah hamma ta yi sannan ta kwanta tana kallon sama,zuciyarta na saƙa mata abubuwa masu tarin yawa. **************** A ɓangaren Aminullahi kuwa gidansa ya koma kai tsaye,yana zuwa ya ga Layuzah ta garƙame shi da ƙaton kwaɗo,gashi bai fita da nasa makullin ba,cikin ƙunar zuciya da ɓacin rai,da kuma wata munafukar yunwa da ke kartar masa ciki ya daki gate ɗin,ina mai gadin gidan ya tafi? Meye amfaninsa? Me yasa Layuzah ke caja masa kai ne? Duk abinda zai yi domin ya samar musu sauƙin rayuwa sai ta mayar masa da shi mummunan abu,shikenan ita idan za ta fita yawon ta sai ta kori mai gadi ya koma gidan Abii har sai ta dawo saboda tsabar rashin yarda? Dafe kansa ya yi da ya ji yana mugun sara masa,cikin tsananin damuwa ya ce. "Ya Allah ka kawo min mafita a rayuwata,Allah ka sani ina tsananin buƙatar taimakon ka,Allah ka shiryar min da mata." Yana gama addu'o'in sa ya juya ya bar gidan,wani restaurance ya nufa ya ci abincinsa,sannan ya zauna yana danna wayarsa,bai bar wajen ba sai da aka kira magariba,sannan ya koma masallacin unguwarsu,sai da aka yi sallar Isha'i ya koma gidan sa,a bakin gate ya ga Mai Gadi a tsaye yana jiran hamshaƙiyar ta dawo,yaƙe Aminullahi ya yi saboda jin nauyi da kunyar mai gadin,shi da gidansa ya zama kamar yaron gida,hira suka dinga yi har tara da rabi na dare a ƙofar gidan,suna nan tsaye gimbiyar ta dawo,a gaban su ta tsaida mota sannan ta buɗe ta fito cike da yanga ta buɗe kwaɗon ba tare da ta ce musu komai ba,da sauri Mai gadi ya buɗe mata gate ta shiga da motar ciki. Jiki na rawa Aminullahi ya bi bayanta ya buɗe mata ƙofa fuskarsa ɗauke da maɗaukakin murmushi,a gajiye ta zuro ƙafafunta waje ta kalle sa tana wani langwaɓar da kai gefe. A shagwaɓe ta ce. "Baby na gaji sosai,ji nake yi kamar kar na taka ƙasa na ganni kawai a ɗaki na cire kaya na yi wanka na ci abinci kana yi min tausa." Cikin wani irin yanayin da za a kira shi da na bawa da uban gidansa Aminullahi ya sunkuya ya sunkuci Layuzah,ta na a hannunsa ya rufe ƙofar motar ya ɗauki jakarta ya wuce da ita cikin gida,banda dariya da murna tare da farinciki babu abinda take yi. Shi kuwa Aminullahi duk wani ƙunci da ɓacin rai tare da masifar da ya yi nufin ya zazzaga mata neman su ya yi ya rasa. A saman gado ya dire ta sannan ya hau cire mata kayan jikinta,wanka ya yi mata kamar yanda ta buƙata sannan ya ɗakkota ya ajiye a saman gado,da kansa ya shafa mata mai ya nemo rigar bacci a cikin kayanta ya saka mata,kallon sa Layuzah take yi cike da so da ƙauna,cikin ranta take ayyana. 'Lallai wannan sabon bokan duniya ne,ji yanda Baby ke yi min hidima kamar wata sarauniya? Alhamdulillah Allah na gode maka,Allah ka ƙara nesanta rayuwarsa da duk wata mace a duniya,Aminullahi nawa ne ni kaɗai,ba zan taɓa sharing ɗinsa da kowa ba.' Tsaye yake yana binta da wani shu'umin kallo,cikin muryarsa da ke tafiya da imaninta ya ce. "To na gama yi miki duk abinda kike so,saura abu ɗaya,ba kuma zan huta ba har sai na yi miki shi,dan haka ki jira ni na nemo miki abinda za ki ci kafin ki yi bacci." Lumshe idanuwanta ta yi sannan ta ware su akan kyakkyawar fuskarsa tace. "A cikin kaso 100 na buƙata ta ka sauke min 60,don haka na yafe maka nemo abinda zan ci,dan kuwa na ci na ƙoshi a gida zo nan ka zauna gefe na,hakan zai wadatar da zuciya da gangar jikina." Kamar wani raƙumi da akala haka Aminullahi ya zauna a gefenta,ita kuwa ta ci gaba da sarrafa shi yanda take so. ********* Washegari da safe Lamyah ta tashi da matsanancin ciwon kai saboda baccin da bata samu damar yi ba da kyau,cikin tsananin damuwa ta shiga banɗaki ta yi alwala ta yi sallar asuba,karatun ƙur'ani ta yi sannan ta yi azkar,ta na idarwa bacci mai daɗi ya ɗauketa a wajen. Da misalin takwas da rabi Abii ya leƙa ɗakin cikin shirin fita office,kwance ya ganta a saman abun sallah ta ƙudundune saboda sanyin Ac da na ƙasa dake shiga jikinta,ƙarasawa ciki ya yi ya rage mata ACn sannan ya ɗauki bargo da pillow,ya saka mata pillown sannan ya rufe ta,a hankali ya fita tare da ja mata ƙofar ɗakin. Sai da ya sanar da su Momma kar a tashe ta har sai ta tashi da kanta,sannan ya wuce office. Tin daga wannan ranar walwalar Lamyah ta ragu sosai,sannan zaman ɗaki ya zamo abokin rayuwarta,a koda yaushe tana jin tsoron fita saboda kar ta sake haɗuwa da Handsome,duk yanda zuciyarta ke kwaɗaita mata son fita dan ta gansa sai baƙin cikin kalaman da ya gasa mata su hana ta motsawa zuwa koda ƙofar ɗakinta ne. Ana haka wata ranar Juma'a da yamma Abii ya dawo shi da baffanin Aminullahi da kawunansa,wato ƴan'uwansa da kuma ƴan'uwan Momma,kowannen su fuskarsa ɗauke da fara'a suka zauna a babban parlourn gidan,wanda ya kasance nan ne ɗakin Lamyah da Iya suke,huhun goro ne guda uku a gabansu da kuma ledojin sweets kala-kala,cike da raha suke tattaunawa,ƙaramin ƙanin Abii mai suna Ɗalhat yana duƙe yana kasafta musu goro da alewar da kowa zai tafi da shi gida. Cikin tashin hankali Aminullahi ya faɗa cikin gidan babu ko sallama,Abii bai dena hirar da yake yi ba,domin kuwa ya san haka za ta faru,kuma a shirye yake da ya ji duk wasu kalamai da za su fito daga bakin ɗan nasa da ya kasa gane kansa a yanzu. Cikin ɗaga murya Aminullahi ya ce. "Abii wai wanne Aminullahin aka ɗaurawa Aure da Lamyah? A ina aka gano Lamyahn har da za a ɗaura auren mu da ita?" Lamyah da ta tashi daga saman abun sallah kasancewar babu jimawa ta yi sallar sai ta fito parlour baki buɗe,saboda mamakin kalaman wanda ke magana da ƙarfi a parlourn nasu,tana fita ta ci karo da Aminullahi tsaye yana faman cika yana batsewa kamar wani kumurcin maciji,cikin wani irin yanayi na halin ko in kula Abii ya kalli ƙofar ɗakin Lamyah da ke tsaye kamar an shuka ta ya ce. "Gata nan a gaban ka,wannan ita ce Lamyahn ka da kake jira,wannan ita ce ƙanwarka,farin cikin ranka,amanarka da iyaye ka El-mustapha da Aminatu suka bar maka. Ita ce kuma matarka ta biyu Aminullahi,domin kamar yanda ka ji na ɗaura maka aure da ita a masallacin Juma'a a yau ranar Juma'a to haka abun yake,ina fatan za ka riƙe amanarka da ka jima kana nema." Ja da baya Lamyah ta fara yi tana girgiza kai hawaye na yi mata tseren doki a kuncin ta,cikin wani irin tashin hankali da faɗuwar gaba ta sanya wata iriyar gigitacciyar ƙara ta silale a wajen........... [9/11, 10:50 AM] zee hussain: ƳAR RAWA. RUBUTAWA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✍️✨ PAGE 34. Cike da tsananin tashin hankali Abii ya isa ƙofar ɗakin Lamyah ya tallabo kanta ya ɗora a saman cinyarsa,wani irin numfashi take fitarwa da ƙyar kamar mai ciwon asima,hawayen da ke zuba a kuncinta Abii ya sanya hannu yana sharewa,wani irin raɗaɗi zuciyarsa take yi masa dan ganin Lamyah a cikin mawuyacin hali,bai taɓa zaton haɗa aurenta da Aminullahi zai tada mata da hankali haka ba,duba da yanda ita da kanta take neman Yah Amee ɗin nata,sai dai labarin da Faisal ya bashi akan yanda Aminullahi ya tsane ta,da kuma abinda ya gani da idanunsa ya tabbatar masa da sai an sha fama kafin lamarin nasu ya daidaita. Tattausan lafazin da ya yi amfani da shi ya kira sunan ta da shi ne ya dawo da ita hayyacinta har ta ƙura masa ido tana kwaɓe baki irin na shagwaɓaɓɓun yaran nan. Kuka ta sake fashewa da shi ta ce. "Abii ya tsane ni,ba ya so na,ba zai yi zaman aure da ni ba,in dai shi ne ni dai na haƙura." A hasale Aminullahi ya isa gaban ta yana binta da wani mugun kallo sannan ya ce. "Ki faɗa da babbar murya ni Aminullahi na tsani halayen ki,ba zan taɓa iya jure zaman aure da sa karuwa ba,dan haka a yanzu ba sai an kai da nisa ba zan yanke duk wata alaƙa da ta ƙullu a tsakanin mu. Ni Aminullahi na....." Wani gigitaccen mari Abii ya sauke wa Aminullahi a kunci,wanda ya sanya shi ganin duhu da wani haske ya gilma wa ganinsa na wasu daƙiƙun da ba zai iya tantance su ba. A hankali ganinsa ya fara dawowa ƙarar da kunnensa ta ɗauka ta tsagaita,idanunsa ya zube a fuskar mahaifinsa wanda tin tasowar sa baƙar magana bata taɓa haɗa su ba ballantana har ya kai masa duka,yanayin da ya ga mahaifinsa a ciki ne ya sanya shi zubewa a saman guiwowinsa duka biyun ya sadda kansa ƙasa,cikin wata iriyar kakkausar muryar da ta sanya Mubarak ɓuya a bayan Momma da ta zo wajen babu jimawa Abii ya ce. "Idan har ni Mus'ab ni na haifi Aminullahi,to ko a mafarki ka saki A'isha Lamyah ban yafe maka ba,na yafe wa duniya kai,babu ni babu kai,ko saman gawata ka zo Allah ya isa ban yafe maka ba. Har ni zan zartar da hukunci a kanka ka nuna min ban isa ba? A gabana za ka tsaya kana ƙoƙarin sakin yarinyar da iyayenta suka yi maka halaccin da mu da muka haife ka ba mu yi maka shi ba? A gabana za ka tozarta yarinyar da take amana a wajen mu? Menene banbancinmu da dangin mahaifanta da suka guje ta suka yanke duk wani zumunci da alaƙa da su kenan? Ashe baka da hankali ban sani ba Aminullah ! Ka bani kunya,ka bani mamaki,ka karya yarda ta da amincin dake tsakanina da kai. Ashe da babu rayuwata yarinyar ta bayyana a gare mu haka za ka tozarta iyayenta ka juyawa jinin su baya? Ka san wanene silar dukiyar da nake da ita a yanzu? Na yanke hukunci ba za ka koma sabon gidan da na gina maka ba har sai ka san daraja da mutuncin matarka. A zato na ko da ƴar maye kuma magajiyar karuwai A'isha Lamyah ta zamo kai mai iya rufa mana asiri ka aureta ne a haka,amma sai ka nuna min kai ɗin albasa ne,wanda bata yo halin ruwa ba. Ka wuce gidan ka ka sanar da matarka zuwa ƙarshen satin nan Aisha za ta tare a gidan mijinta,idan ka so ka yanka ta ko ka kunna wuta ka jefa ta ciki saboda ƙiyayya." Abii na gama maganganunsa masu cike da tsananin ɓacin rai Momma ta ce. "Kar ka yi zaton samun sauƙi daga ɓangare na Aminullah, matuƙar ka ƙuntatawa marainiyar Allah,Allah ba zai barka ba,idan kuma ka kuskura ka saki yarinyar nan babu ni babu kai har a lahira ba zan so gamuwa da kai ba." Kalaman Momma sun girgiza shi matuƙa. Jagwab ya faɗi ya zauna a wajen yana fitar da wani irin zazzafan numfashi,zazzaɓi mai zafi ne ya kama shi a cikin ƙanƙanin lokaci,ita kanta Lamyah kalaman su Abii akan Yah Amee ɗin nata sun girgizata,sam bata taɓa tsammanin sun bata irin wannan matsayin a rayuwarsu ba. Yau ace akan ta suke barranta kansu da ɗan cikin su? To wanne irin so suke yi mata? Tana nan durƙushe ta na numfarfashi Momma ta bi bayan mijinta hannunta riƙe da na Mubarak. Iya ce ta durƙusa a gaban Aminullahi ta kama hannunsa,wani mugun kallo ya zuba mata ya warce hannunsa, ƴan'uwan mahaifan sa na kiran sunan sa dan su zaunar da shi su yi masa nasiha,amma ya yi kunnen uwar shegu da su ya bar gidan cike da ƙunar zuciya. Kai tsaye motarsa da bai kashe ba ya faɗa ya ja ta ya bar gidan a fusace. Tin a hanya ƙirjinsa yake bugawa saboda matsanancin tsoron Layuzah da ya mamaye zuciyarsa,ta yaya zai sanar da ita wannan mummunan labarin idan ta dawo daga kai Hajiyanta wajen mai maganin da ta tambayesa tin safe? Wanne irin bala'i da masifa Abii ya gingimo ya ɗora masa? Zazzafar iska ya furzar daga bakinsa ya furta. "Na shiga uku,ina zan saka kai na? Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un,Allah ka shiga lamari na." Tin kafin ya ƙarasa ƙofar gate ɗin gidansa ya ke danna oda,mai gadinsa da ya gane irin odar mai gidansa sai ya tashi da azama ya buɗe masa gate. A guje ya shige da motar ya faka ta ya fice,mai gadi ne ya sake buɗe motar ya rufe da ƙarfi,ganin Aminullahi cikin damuwa ne ya sanya shi jinjina kai tare da yi masa fatan samun sauƙi a lamuransa. Kai tsaye banɗaki Aminullahi ya shiga ya hau zazzage wani zazzafan zawon da ya sanya shi zubar zufa a jikinsa,ya jima a ciki sosai kafin ya yi tsarki ya yi flushing ya cire kayansa ya hau wanka,ruwa mai sanyi ya kunna ya na dukan fatar jikinsa dan samawa kansa sauƙin zafin da ke tsattsafowa tin daga naman jikinsa zuwa saman fatar sa. Lumshe idanu ya yi yana jin wannan sannanen yanayin da ya saba ji a duk sanda ya tina da Lailah ƳAR RAWA,tin ranar da ya gano Lailah ce Lamyah har wannan lokacin da yake ƙoƙarin kashe shower da ya kunna ya kasa yarda wai Lamyahnsa ita ce Lailah karuwa mai rawa a gaban maza suna ihu suna zuba mata kuɗi. Towel ya ɗaura a jikinsa sannan ya fito zuwa ɗaki,kasa shafa mai ya yi a jikinsa balle turare,jallabiya kawai ya saka da gajeran wando ya kwanta a saman gado yana kallon sama cike da damuwa. Layuzah kuwa tinda ta dawo daga gidan kakanninta ita da Hajiya a sabuwar motar da Aminullahi ya saya mata sai suka wuce wajen wata shahararriyar mai sayar da maganin mata mai suna Hajiya Laure Mai Kayan Mata.Hajiya na zaune a wajen ake ɗaga kalolin magungunan mata mai ɗauke da munanan hotuna a jiki ake yi wa Layuzah bayanin su,Layuzah kuwa sai dariya take sheƙawa ta na hango yanda Aminullahi zai gigice idan ta fara amfani da su,Hajiyanta ma sai washe baki take yi tana cewa mai siyar da kayan. "Hajiya Laure a samo mata masu kyau fa don Allah,ko nawa ne za mu biya,mu dai fatan mu a bata masu kyau da za su kankaro darajar ta a wajen mijinta." Hajiya Laure mai kayan mata ta ji kuɗi sai ta washe baki har haƙoran makkanta na bayyana ta ce. "Kar ki ji komai Hajiya,ai ba a banza suna na ya yi fice a garin nan ba,zan yi mata haɗin ƴar gata na gobe ki dawo. Bari dai ki gani ma na taso da kai

Chapter 20 of 30