Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ƴar wajen ka wadda ake kira da Aminee,kuma ta yi min,ina sonta da aure idan har za ka yarda ka aura min ita." Cike da fara'a Malam Muhammadu ya kalli El-mustapha kyakkyawan balarabe da cikar haiba,matashin da ba zai haura shekaru talatin ba mai jini a jika da sanin yakamata ya ce. "To ai wannan maganar ba ta yu muyi ta mu kaɗai ba Alhaji El-mustapha,magana ce da ya kamata a yi ta a gaban mai unguwa,dan ya zame mana shaida,dan haka mu je wajen Mai unguwa ka maimaita abinda ka zo da shi gabana." Babu musu El-mustapha ya bi Malam Muhammadu suka je wajen Mai unguwa,anan El-mustapha ya sake bayyana ƙudirinsa na son auren Aminee,nan take Mai Unguwa ya sa albarka,Malam Muhammadu ya ce. "To ranka ya daɗe,kamar yanda ya ce a bashi dama ya je ƙasar su ya sanar da magabatansa,to ina so idan Allah ya dawo da shi lafiya,idan bai same ni a raye ba na yi maka izinin ka aura masa Aminee,Aminatu bata da mijin da ya wuce El-mustapha." Godiya sosai El-mustapha ya dinga yi,Mai unguwa ya ce. "Ballantana ma da kanka za ka aurar da ƴarka da izinin Allah." Bayan sun gama tattaunawa da ƙulla alƙawura ne El-mustapha ya tafi ya koma gidasa,Malam kuwa da ya koma gida ya samu Aminee na aiki tuƙuru kamar ita ke siyar da kalwar,ba tare da ya ce komai ba ya samu waje ya zauna ya yi shiru,dan a wannan lokacin ya gama gane halayyar Delu,babu yanda ya iya da ita ne shi yasa yake danne ɓacin ransa ya na tausar Aminee. Kiran Delu ya yi ya labarta mata duk abinda ke faruwa, fara'a ta yi ta haɗa da addu'ar fatan alkhairi,har ta sa Malam ya ji daɗi a ransa,haka suka ci gaba da hira Aminee na can tana hura wuta. Bayan fitar Malam sallar magariba ne, baƙin cikin kalaman Malam ɗin suka sanya Delu sauke haushin akan Aminee,da ta yi abu ko ba laifi bane,sai ta juya shi ya koma laifi ta hau ta da faɗa,wani lokacin ma har da ranƙwashi take kai mata mai azabar zafi,haka yarinyar zata kama kai tana sosawa cike da damuwa,cikin masifa ta ce. "Za ki wuce ki je ki yi alwala ko kina nan zaune gaban murhu,har sai uban ki ya dawo ya ce ina saki wahala ko? Munafuka annamimiya,ke da auren balarabe sai dai a mafarki Aminee,ba dai a zahiri ba,idan dai ina numfashi a duniya ba zan taɓa barin ki ki yi aure a inda zaki huta ba,yanda na kare da auren ubanki malamin makaranta,haka kema zaki ƙare da auren wahala." Aminee da bata gane akan me take ta faɗa ba sai ta wuce ta ɗaura alwala,ta shige ɗakin Tabawa ta tada sallah idanunta na zubar da ruwan hawaye,tana idarwa ta hau karatun ƙur'ani saboda ta samu zuciyarta ta yi mata sanyi akan raɗaɗin da take yi mata. Ana washegari El-mustapha zai tafi Dubai ya zo gidan Malam ya sallama,Aminee ce ta fito cikin shirin zuwa makaranta,amsa masa sallamar da yake ta zabgawa ta yi ta raɓe a jikin ƙofa kanta a kasa;hannunta riƙe da littatafanta na zuwa makaranta, cikin zuciyarsa yake ayyana. 'Tabbas na yi dacen matar aure,neman matar auren da nake yi na tsawon shekara da shekaru ya kare,Allah ka mallaka min Aminee a matsayin matar aure na.' A zahiri sai ya ce mata. "Ina zuwa haka na gan ki da littattafai a hannu?" Cikin fara'ar ta dake ƙara mata kyau ta ce. "Makaranta zan je,na makara ina da ajin da zan koyar da yammar nan." Ɗaga gira El-mustapha ya ɗan yi yana kallon ta,cike da mamaki ya ce. "Ki na nufin kema koyarwa ki ke yi a makarantar?" Ɗaga masa kai ta yi,sannan ta ƙara da cewa. "Eh, tin da na sauke ƙur'ani da hadisai da wasu littattafan Abbah ya ce in dinga zuwa ina koyarwa saboda kar haddata ta zube." "Barakallahu fiki,Masha Allah tabarakarrahman." Da ƙyar El-mustapha ya bar Aminee ta wuce makaranta,ko Malam bai tsaya gani ba ya wuce,dan kuwa ya samu wani ƙwarin guiwa da tabbacin ya samu matar aure. Bayan tafiyar El-mustapha Dubai da sati ɗaya ne,Malam Muhammad ya tafi gidan Mai Unguwa cikin wani irin mawuyacin hali,yana zuwa ya yi sa'a babu mutane a wajen kamar koda yaushe,zama ya yi suka gaisa da mai Unguwa sannan ya nisa ya ce. "Ranka shi daɗe wata alfarma na zo nema wajen ka,ina fatan za ka daure ka yi min ita." Zama mai Unguwa ya gyara sannan ya kalli Malam ya ce. "Ina jin ka Malama,ka faɗi ko menene in har bai fi karfi na ba zan yi maka." Cikin wani irin yanayi mai matuƙar ban tausayi Malam ya ce. "Tinda Tabawa ta tafi ta barni zuciyata bata huta ba ranka ya daɗe,tafe nake kawai zaka iya kira na gawar da ta ƙi rami,tsananin son da nake yiwa matata ne ya shafi ƴata,har ya zamanto ina jin ciwon halin da take ciki a gidana,yarinyar nan na fama da musgunawar kishiyar uwa ranka ya daɗe,duk wata hanya da zan bi na bi,amma har yanzu babu sauƙi,idan ma na nuna na sani yarinyar ta fi shiga damuwa a gidan,shi yasa na tattara na barwa Allah komai. Shi yasa na yanke shawarar zan zo na roƙi alfarma a wajen ka,ko bayan raina idan wannan yaro El-mustapha ya dawo ka aura masa Aminee,shi kaɗai ne nake saka ran zai riƙe min ita da amana,kuma zata huta daga wahalar rayuwar da take sha." Jikin Mai Unguwa ne ya yi sanyi sosai,mamakin halin mata duk ya sanyaya masa jiki,baya taɓa manta yanda Tabawa ta yi faɗi tashi ta sa Malam ya auri Delu,shi ne yanzu take azabtar da marainiyar Allah, cike da tausayawa Mai Unguwa ya karɓi amanar da aka damƙa masa,sannan ya ce. "Ka kwantar da hankalinka Malam Muhammadu,da yardar Allah da kan ka za ka aurar da Aminatu,ai cuta ba mutuwa bace." Jinjina kai kawai Malam ya yi,domin kuwa shi kaɗai ya san yanda yake ji a zuciyarsa,bayan sun ɗan taɓa hira ne ya yiwa mai unguwa sallama ya koma gida. Tin daga wannan rana Malam bai sake lafiya ba,har sai da ta kai ta kawo baya iya fita ko ƙofar gida ne balle ya je makaranta. Aminee kullum cikin tashin hankali da damuwa take,ta rame ta lalace saboda tashin hankalin da take ciki. Malam kuwa ko ƙarar mota ya ji ta wuce a kofar gidan sa sai ya zaci ko El-mustapha ne ya dawo maganar aurensa da Aminee. A haka har ya cika sati biyu ya na jinya,wani daren Juma'a da ya zamto baƙin dare a wajen Aminee da duk wani masoyin Malam,Malam Muhammadu ya sallama duniya ya koma gidansa na gaskiya,cike da wasiyyar a aurawa El-mustapha Aminee da zarar ya dawo. Wannan wasiyya ta Malam ba ƙaramin baƙanta ran Delu ta yi ba,duk da ta na cikin alhinin rashin Malam bai sa ta dena ƙulla yanda za ta raba wannan muguwar wasiyya da Malam ya bari ba...... [9/11, 10:50 AM] zee hussain: ƳAR RAWA. RUBUTAWA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✍️✨ PAGE 3. Tafiyar kilomita shida ce tsakanin Dubai Airport zuwa Deira. El-mustapha Hussain na isa gida,wanka kawai ya yi ko abinci bai tsaya ci ba,saboda tsananin zumuɗi da farin cikin da yake mamaye da zuciyarsa. Kai tsaye babban gidan su ya nufa dan sanar da ƴan'uwansa daddaɗan labarin da ya dawo da shi daga tafiyarsa. Yana isa ya tarar da su kamar yanda ya yi tsammani,manyan raguna ne aka gasa ga shinkafar da ta ji kayan ƙamshi da wadataccen kayan lambu,shayin gahwa da sauran abubuwan sha da kayan marmari suka yiwa da'ira sai hira suke yi cike da nishaɗi da barkwanci,ganin El-mustapha tafe ne ya rage annashuwar dake tattare da su har suka koma yin ƙus-ƙus a tsakaninsu, waje ya samu ya zauna tare da gaishe da su cike da fara'a,ƙalilan daga cikinsu ne suka amsa shi sannan babban yayansu ya yi musu izinin fara cin abinci,duk yanda El-mustapha ya so ya fara sanar da su labarin da yake tafe da shi bai samu dama ba,har sai da suka kammala cin abinci suka hau hira,masu shan sigari sun bata wuta suna ta busawa sama hayaƙi. Sallama ya yi musu sannan ya labarta musu abinda yake tafe da shi na maganar aurensa da Ameenee,nan da nan kuwa wajen ya kacame da hayaniya,gaba ɗayan su juyawa El-mustapha baya suka yi,saboda dama zuƙatansu cike suke da ƙiyayyarsa, cike da mamaki ya ke bin su da kallo, cikin karyewar murya da zuciya El-mustapha ya ce. "Shin me na yi muku ne ku ka tsane ni har ku ke son ku ware ni a cikin ku,a matsayina na ɗan'uwanku kuma ƙaramin ƙanin ku?" Wani ɗan gajeran balarabe ne mai masifar ƙiba ya hau nuna El-mustapha da hannu ya na magana yawu na zuba tsabar masifa. "Saboda kai ka ware kan ka a cikin mu,idan mabuƙata ne bamu da su ne a wannan ƙasar tamu har sai ka je wata uwa duniya? Hakan bai ishe ka ba shine za ka kawo mana baƙar fata a matsayin matar da zaka aura,to ni dai babu hannuna a maganar aurenka,na tabbata kuwa kowa anan ba ya maraba da wata ƙabilar da ba tamu ba,kuma har abada ba za mu yi maraba da ita a zuri'ar mu ba." Ya ƙarasa maganar yana huci tare da neman waje ya dafe ƙasa ya zauna da ƙyar,a hasale sauran ƴan'uwan El-mustapha suka hau nuna ƙin amincewarsu a game da auren da yake da niyyar ni,cikin wani irin yanayi na tsananin damuwa ya ɗaga kai ya kalle su,a sanyaye ya ce. "Sanin kan ku ne ina yin taimako a wannan kasa tamu fiye da yanda nake yi a inda nake zuwa,burin raina ne tafiye-tafiye,shi yasa na zaɓi hakan ba wai dan bana taimakon ƙasata da dangina ba,yarinyar nan hafizar ƙur'ani ce,tana da kyau,ta na da halaye masu kyau,to me nake nema a wajen macen da zan aura da ya wuce wannan? Kar ku manta abu mafi mahimmanci shi ne ina son ta,kuna so kenan na yi watsi da soyayyar da nake yi mata na fasa auren ta?" A hasale babban yayan su da gaba ɗaya ya ɗauki rayuwar El-mustapha a mara amfani da wasa ya ce. "Eh ka rabu da ita,ka dawo nan ka yi aurenka,ga ƙanwar matata nan Sahlah kyakkyawa mai nasaba,ƴar manyan mutane,ka ƙi ta ka maƙale a inda suke kama da birrai,na tabbata dan ka rabu da ita ba za ka mutu ba." Wasu dariya suka sanya,wasu kuma suka ci gaba da goyon bayan Yayan nasu, El-mustapha da ya ga basu fahimci juna ba sai kawai ya yi musu sallama ya bar wajen. Kai tsaye gidansa ya koma, ma'aikatansa ya tara gaba ɗaya ya yi musu gagarumar kyauta ta ban mamaki,sannan ya sallame su,ya na kammalawa sai ya koma ɗakinsa ya kwanta yana hutawa,tinanin iyayensu ne ya sanya shi zubar da ƙwallar kewarsu,a yanda iyayensu ke tsananin son sa ya tabbata da suna raye ko bera ya kawo ya ce yana so,za su goya masa baya,ya tabbata wannan ƙiyayyar ta samo asali ne ta dalilin soyayyar da iyayensu suka nuna masa mai tarin yawa,ajiyar zuciya ya sauke sannan ya miƙe tsaye ya hau haɗa duk wasu mahimman abubuwansa da zai buƙata,bai kammala abinda zai yi ba sai da aka fara kiran sallar asuba,sannan ya wuce ya yi alwala ya yi sallah ya koma ya kwanta. Gari na wayewa ya wuce kamfaninsa ya duba duk abinda zai duba,sannan ya yi cike-ciken takardu,ya damƙa muƙamin kula da kamfanin a hannun wani ɗan'uwan mahaifiyarsu,ya na gamawa sai ya wuce wajen shan iska,ya sha lemo ya ɗan jima a wajen yana ganin gilmawar mutane,cikin gari ya shiga a motarsa yana zagawa shi kaɗai ba tare da driver ba,dan kuwa ya sallame su tin a jiya. Sai da El-mustapha ya yi matuƙar gajiya sannan ya dawo gida ya ɗauki biro da takarda ya yi rubutu ya kai parlour ya ajiye a saman kujera,ɗaki ya koma ya yi wanka ya ɗauki akwatinansa guda biyu ya kulle gidan ya ajiye makulli a inda ya saba ajiyewa ya wuce airport. A Niger El-mustapha ya sauka,Mus'ab ya je ya ɗakkosa a filin jirgi suka wuce gida,daga yanda Mus'ab ya kula da yanayin El-mustapha ya gane bai yi nasarar karkato da hankalin ƴan'uwansa ba,dan haka bai ce masa komai ba sai kawai ya ajiye sa a gidansa ya koma gida ya kawo masa abinci daga wajen matarsa, sannan ya zauna suka gaisa, anan yake samun labarin yanda ƴan'uwan El-mustapha suka juya masa baya suka ƙi amincewa da aurensa da Aminee,cikin ɗacin da zuciyarsa ke yi masa ya ce. "Na baro musu garin su yi yanda suke so,dama basu ƙaunata tin iyayenmu na raye,da suka rasu abun sai ya girmewa tunani na,gashi a yanzu ma suna nuna min dukiya ta fi soyayyata,to na baro musu dukiyar da garinsu su yi yanda suka so." Cike da tausayawa Mus'ab ya ce. "Ba za ai haka ba abokina,kana da ilimin ka na addini,bai kamata ka biye musu ba ka yanke zumunci da su." Cike da rauni El-mustapha ya ce. "To yaya zan yi musu Mus'ab? Ba sa buƙatata a rayuwarsu,idan zan shekara goma bana ƙasarmu babu mai nema na ya ji daga gareni,idan ina gari ma basa nema na su ji daga gareni,a kullum ni ke bibiyarsu,idan ka ga sun neme ni wata kadara tawa suke so na basu ko wata dukiya tawa suke da buƙata,na zame musu saniyar tatsa." Wasu irin zafafan hawaye El-mustapha ya share daga idanunsa sannan ya ce. "Dan Allah ina neman alfarma a wajen ka,ka taimaka min ka raka ni ka karɓa min auren Aminatu,ina son ta sosai,ina ji a jikina ita ce mahaɗin rayuwata,ita ce za ta cike min gurbin kewar iyayena da ƴan'uwana da suka guje ni." "In Shaa Allahu zan raka ka,ka gama shirin ka a tsanake sai mu je,da ace ma baka da zuwa taron gidan marayu na Arlit ai da a cikin satin nan za mu tafi Nigeria." "Haka ne,babu komai da yau da gobe duk na Allah ne,Allah ya zaɓa mana abinda ya fi zama alkhairi,na gode sosai da amintar dake tsakanina da kai,ka zame min ɗan'uwa ba ma aboki ko amini ba kaɗai,Allah Ya bar mana zumuncinmu har aljannah?" "Amin Ya Allah gwauro,bari na wuce gida kar na sa Madam ta yi ta jira na." Cike da barkwanci Mus'ab ya faɗi hakan har sai da ya sanya murmushi a fuskar El-mustapha da ke a haɗe da ɓacin rai,cikin fara'a ya ce. "Au abun haka ne? Lallai ka ce wani abu,nima ai kamar yau ne,mu je na raka ka,a gaida Madam ina godiya da hidima da ni,amma kwanan nan za ta huta itama da Aminee ta zo." "Ka na nufin a nan ƙasar za ka zauna da matarka? Ai na zaci za ka barta can ko dan mahaifinta." "Gaskiya anan nake so mu zauna,na fi jin daɗin zama anan,bayan haka ma shi aure ai babu inda baya kai mace." "Haka ne,Allah Ya kai mu lokacin nan dai mu sha biki." A haka El-mustapha da Mus'ab suka rabu cike da barkwanci da yiwa juna fatan alkhairi. Bayan sati ɗaya da kammala duk wani abu da El-mustapha zai yi Mus'ab ya zo suka shirya tafiya Nigeria,ranar da suka tsara tana zagayowa suka bi jirgi suka tafi Nigeria. Malam Isa ne ya je ya dauke su kamar koda yaushe,suna isa gidan nasu suka tarar an gyara an share,har abinci an girka musu,bayan sun yi wanka sun ci abinci ne suka zauna suka sha hira da Malam Isa da sauran ma'aikatan gidan,anan El-mustapha ya ke jin duk buƙatun su,kuma bai ɓata lokaci ba wajen basu kuɗaɗen da za su ishe su. Washegari da misalin sha ɗaya na rana suka shirya suka nufi Rijiyar lemo,kai tsaye gidan Malam Muhammadu suka nufa,a ɗan nesa da gidan Malam Isa ya ajiye mota a ƙasan wata ƙatuwar bishiyar maina,cike da zumuɗi El-mustapha ya taka ya nufi kofar gidan Malam,yana zuwa sai ya tsaya a bakin ƙofa ya rabka sallam. Aminee ce duƙe da guiwowinta a gaban murhu tana ta iza wutar kalwa,duk ta yi fururu da ita,idanunta sun yi ciki-ciki hancinta na zubar da majina,idanunta sai tsiyayar da hawaye suke yi,hijabin jikinta da ta ɗaura a ƙugunta ta kunce ta nufi ƙofar gidan da sassarfa saboda gane mai maganar da ta yi,tana zuwa kofar gidan kuwa idanunta suka sauka a cikin nasa,wani irin abu ta ji ya ratsa mata tin daga kanta har kafafunta,nan take wani irin kuka ya ƙwace mata,a wajen ta durƙusa ta dinga rizgar kuka kamar ana zarar ranta,cike da damuwa El-mustapha ya durƙusa a gaban Aminee da ta yi buɗu-buɗu da ƙura take ƙaurin hayaƙi,cikin murya mai sanyi El-mustapha ya ce. "Aminee lafiya ki ke kuka haka? Ko dai baki yi farin cikin gani na bane?" Girgiza masa kai ta yi,kafin a hankali ta ɗaga kan nata ta zuba idanunta cikin nasa,wani iri El-mustapha ya ji dan ganin yanda idanunta ya kumbura,nan take ya ɗiga ayar tambaya akan kukan nata,anya kuwa yanzu ta fara wannan kukan? Anya babu abinda ke damun zuciyar yarinyar nan? Muryarta ya ji daga sama tana bashi labarin da ya kusan sanya shi zama a wajen ya kurma ihu,cikin murya mai amon kuka ta ce. "Abbah ya rasu,shi yasa ka ga ina wannan kukan,bani da uwa bani da uba,bani da kowa a duniyar nan saboda ko ƴan'uwana ba sa kaunata,ina zan ɗora kai na na jingina na ji daɗi?" "A kafaɗata zaki ɗora Aminatuna ! Rayuwata da taki basu da banbanci ta fannin alaƙar jini da dangantaka,dan haka kar ki sake damun kan ki ki tada min hankalin ki,Allah ya jiƙan Malam,Allah ya gafarta masa,Allah ya bamu haƙurin rasa nagartaccen mutum kamarsa." Muryar Delu suka ji akan su ta na salati tare da faɗin. "Yanzu ashe Aminee iskancin naki gaba ya yi ba baya ba dama? Abun naki ya zarta baƙaƙen fata da muka sani ya koma wajen fararen fata? Ashe ki na nan ki na yawon ta zubar kin bar min kalwa baki hura min wutar ba." Hannu ta sanya ta kaiwa Aminee duka a tsakar baya,zata sake dukanta ne yarinyar ta ɗiba da gudu ta yi cikin gida ta na gunjin kuka, dika-dika kwana goma kenan da rasuwar mahaifinta,mugun halin Delu ne ya hana mutane zuwa zaman makoki,gashi tin ba a je ko ina ba ta fito da irin ƙiyayyar da take yi mata fili kowa na gani. Cikin ladabi El-mustapha ya gaishe da Delu tare da yi mata ta'aziyya,asheƙe ta amsa sannan ta ce. "Kai nunar rana,bar ganin ka siye Malam da ƴan canjin da ka ke watsa masa,ni nan da ka ganni bana ƙaunar ka,balle ƙaunar haɗa zuri'a da kai da Aminee,dan haka tin kana gane hanya ka saita ka bar garin nan kanka a likkafa,idan kuma ba haka ba za ka ga ruwan rashin mutuncin da baka taɓa gani ba." Cike da tashin hankali El-mustapha ya ce. "Ai Malam ya yi min alƙawarin aura min Aminatu." "A lokacin da yana raye ba?" Shiru El-mustapha ya yi ya miƙe tsaye dan ya kula Delu bata daga cikin mutanen da za a yiwa ladabi balle biyayya, cike da wani irin yanayi ya wuce ya bar ƙofar gidan ya shige mota. Yana tafiya Delu ta shiga gidan ta tarar da Habeebu kwance a ɗaki yana zaman banza,a cewarsa har yanzu mutuwar Malam na dukansa shi yasa baya zuwa ko ina,babu ɓata lokaci Delu ta aika shi gidan Baffa Na Lado akan ya gaggauta kiran sauran ƴan'uwansa su zo tana son yin wata magana da su mai mahimmanci. Da ƙyar Habeebu ya tafi dan isar da saƙonta gare su. Ya na zuwa sai ya tarar da Baffanin nasa gaba ɗaya suna tare suna tattauna wata maganar da suna ganinsa suka yi shiru suna jiran su ji me ke tafe da shi,nan take kuwa Habeebu ya isar musu da saƙon Delu sannan ya wuce,basu wani ɓata lokaci ba suka haɗa kai suka tafi gidan Malam Muhammadu,suna zuwa Baffa lado da ya fi kowa rashin mutunci a cikinsu da halin ko in kula akan zumunci ne ya kalli ƙatuwar tabarmar da Delu ta shimfiɗa musu a tsakar gidan,ga abinci nan har da balangu ta bayar an siyo an zuba musu akai,ruwan sha ta aika Aminee ta ajiye musu sannan ta ce. "Sannun ku da zuwa,bismillah ku zauna ku ci abinci daga baya sai mu tattauna akan abinda ya tara mu anan ko?" Kallon kallo suka fara yi a tsakanin su,dan kuwa sun riga da sun sani, Delu bata taɓa basu abincin gidan Yayansu tin yana da rai,saboda tsabar rowar da take yi musu,Tabawa ce kawai take basu abinci ta kyautata musu da matan su,sai gashi yau har da ruwan randar sanyi aka kawo musu sai washe musu baki take yi. Basu ɓata lokaci ba kuwa wajen gyarawa abincin nan zama,suna kammalawa Delu ta labarta musu kaf alƙawarin da Malam ya yiwa balaraben da ke taimaka wa makarantun su. Cike da kukan kirsa da munafurci ta ce. "Yanzu Na Lado ka na ganin idan muka bari wannan balaraben ya ɗauketa zai sake dawo mana da ita? Ina tsananin tausayin Aminee bana so ta je inda bata da kowa ta sha wahalar rayuwa,dan Allah ku yi wani abu akan wannan lamari,tinda ku ne ƙannen ubanta." Na Lado ne ya kalli ƴan'uwansa sannan ya ce. "Ni dai kun riga da kun san hali na,babu abinda ya dame ni da wata Aminee ko wacece,harkokin gabana kawai na sa a gaba,amma tinda har kin kiramu kin sanar damu abinda ke faruwa,yanzu da mun je wajen mai gari zamu sanar da shi ra'ayin mu na ƙin amincewa da wannan auren,domin kuwa a shirye Habeebu ya tarar damu za mu je wajen mai unguwa akan wannan maganar." Na Duduwa ne ya ce. "Ƙwarai da gaske Yaya,yanda ka ce haka za a yi ku tashi mu tafi." Babu ɓata lokaci suka ɗunguma suka nufi hanyar gidan Mai unguwa,suna zuwa sai suka tarar da wajen babu kowa daga mai unguwa sai aminin Malam Muhammadu wato Malam Abubakar sai kuma El-mustapha da baƙin da ya zo da su guda biyu a zaune suna jiran zuwansu. Kallon kallo aka fara yi a tsakanin su kafin Mai gari ya ce................ [9/11, 10:50 AM] zee hussain: ƳAR RAWA. RUBUTAWA : HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✍️✨ PAGE 4. "Malam Lado da sauran ƴan'uwan Malam Muhammadu. Na sa a kirawo min ku ne ba don komai ba,sai dan ina so da ni da ku mu haɗu mu cika wasiyyar da ya bari,ta aurawa Aminee El-mustapha a duk sanda Allah ya dawo da shi lafiya. Dan haka..." Cikin sauri Lado ya ce. "Allah ya taimake ka ban katsi numfashinka ba,amma dai kaf garin nan kowa ya san ni ne nake biwa Mamman,shi ya sau mama na kama,kuma daidai gwargwado akwai shaƙuwa ta ƴan'uwantaka a tsakaninmu, Mamman be taɓa zartar da wani hukunci ba musamman akan Aminee ba tare da ya sanar da ni ba,dan haka ni bani da wata masaniya akan wasiyyar auren Aminee da wannan baƙon farar fatar." Baffah Lado ya faɗa yana muzurai,su Na Duduwa na zaune suna gasgata shi,cike da takaici Malam Abubakar ya riga Mai Unguwa yin magana,a hasale ya kalli Lado ya ce. "Ka ji tsoron Allah Lado,kar ka manta za ka maimaita wannan maganar da ka yi a gaban ubangiji da kuma shi kansa Malam Muhammadun da ya baka wasiyya,saboda son abun duniya da ɗaurewa ƙarya muhalli za ka ce baka san da zancen ba." Cike da borin kunya Lado da ƴan'uwansa suka hau yiwa Malam Abubakar rashin kunya,cikin rashin jin daɗin abinda ke faruwa El-mustapha ya kalli Mai Unguwa yana neman agaji,nan take Mai Unguwa ya daka musu tsawa ya ce. "Ko Malam ya sanar da ku,ko bai sanar da ku ba ni dai babu ruwana da neman izinin ku,domin kuwa har nan inda ka ke zaune Ɗantiye Malam ya zo ya roƙe ni arziƙi idan yaron nan ya dawo na ɗaura masa aure da amina,kun ga kuwa a matsayina na shugaba ina jin ko shari'a ta yarje min na aura mata wanda ya dace da ita,kai El-mustapha miƙo sadaki yanzu ba sai gobe ba zan ɗaura auren ku,Malliman a matso kusa." Babu ɓata lokaci El-mustapha ya karkace ya fiddo da kuɗi daga aljihunsa kimanin dubu talatin ya miƙawa mai Unguwa,Malam Isa direba, Mus'ab da Malam Abubakar,sai Malam Liman da Mai Unguwa,su ne suka shaida ɗaurin auren Aminee da El-mustapha,su kuwa Lado da Ɗantiye da Na Duduwa suna ganin za a ɗaura sai suka koma gefe suna muzurai tare da faɗin su dai ba da yawun su za a ɗaurawa Aminee wannan aure ba. Sai da komai ya kammala suka bar wajen suka nufi wajen Delu faram-faram da takalma dan su labarta mata abinda ya faru. Bayan tafiyar su ne El-mustapha ya durƙusa

Chapter 2 of 30