shiga kitchen ta kunne waƙarta a waya kamar yanda ta saba ta hau ƙoƙarin ɗora girki. Sai da ta fere dankali mai yawa sannan ta yayyanka ta ɓare maggi ta yanka albasa,Man gyaɗa ta ɗora a wuta ya yi zafi sannan ta tsame dankalin daga ruwa ta zuba masa maggin nan da curry da albasa ta juya sosai ta zuba shi cikin mai. Nan da nan gida ya kaure da ƙamshin girki,naman kaza ta ɗakko a fridge ta wanke ta yanki iya yanda zai isheta ta mayar da sauran,wankewa ta yi ta ɗora farfesu ta zuba masa kayan ƙamshi ta rufe. Ta na nan tsaye ta na rawa tare da jiran girkinta ya yi ta juye ta koma ɗaki ta ji ƙamshin turarensa da ta haddace a cikin kanta kamar karatu. Tsayawa ya yi ya zuba hannayensa cikin dogon wandon jikinsa,jikinsa babu riga sai ɗigar zufa yake yi. Da dikkan alamu ko motsa jiki ya gama ko kuma wani aikin ya yi na ƙarfi da ya sanya zufa ke kwaranya a jikinsa. Kasa juyawa ta yi,sannan bata dena yin rawarta ba don bata son ya gane ta san da zuwansa. Ta na sane ta sake narke jiki ta na wata lanƙwasa kamar tarwaɗa,a haka ta isa ta kwashe dankalinta sannan ta zuba wani ta koma ta ci gaba da takawa. Gajiya ta yi da yanda take jin idanunsa na yawo a jikinta sai ta juya hannunta a sama,hakan sai ya bawa rigar jikinta damar ɗagawa har fiye da rabin cinyoyinta suka bayyana. Wani abu Aminullahi ya haɗiya mai ƙarfi da zafi,wanda ya yi sanadiyyar buɗe fridge da ya yi cikin gaggawa ya na neman ruwa mai sanyi ya jiƙa maƙoshinsa. Murmushin mugunta Lamyah ta yi sannan ta hau rufe jikinta za ta wuce shi,cikin zafin nama ya ajiye ruwan ya riƙe hannunta,abinda ya saba ji a duk sanda ya riƙe hannunta ya ji ya mamaye shi,babu ɓata lokaci ya riƙe ta da kyau a jikinsa ya hau yi mata salon da ya kashe mata jiki,cikin fitar hayyaci ta ke ƙoƙarin ture shi amma Aminullahi ya yi nisa,gaba ɗaya hankalinsa ya tashi yana jin kamar su kaɗai ne ke rayuwa a duniyar. A zafafe ta fizge jikinta daga nasa bakinta na rawa hawaye na zuba daga idanunta ta ce.
"Me za ka yi da karuwa kuma ka na a matsayin tsaftatacce wanda bai taɓa zina ba?."
Wata iriyar kunya ce ta kama sa,sai dai kamar yanda aka ce su maza basu da kunya,to hakan ce ta faru tsakanin Lamyah da Aminullahi,domin kuwa murje idanunsa ya yi ya baɗe su da toka ya ce.
"Taimaka miki zan yi,saboda na san kin jima rabon ki da ƙattin da kike bi,shi ne dalilin da ya sa kika sa irin wannan kayan a cikin gida na don ki ja ra'ayi na,to ki sani idan mata ta ta fito ta gan ki a haka akwai yaƙi."
Hawaye ne masu tsananin zafi da ƙuna suke zuba mata,ji ta yi dama ta barsa ya cimma burinsa akan ta,wataƙila zai gane ita ɗin ba ragowar kowa bace,cikin sauri ta share hawayenta ba tare da ta bashi amsa ba ta kwashe dankalinta da ya fara yin brown ta kashe gas ɗin dika ta juye abincinta ta wuce ɗaki. Bayanta Aminullahi ya bi da kallo,sai ya ji kamar ba daga wajen Layuzah ya fito ba,ta na can ta gajiyar da shi ta gajiyar da kanta,sai kwasar baccin gajiya take yi. Tabbas ya sani ko sau dubu zai kasance da Layuzah ba zai taɓa samun yanda yake so ba matsawar ba Lamyah ce ta bashi haɗin kai ba. Wannan karon a shirye yake da ya kasance da Lamyah ko da kuwa ragowar wasu ce,after all itama Layuzah ai ba intact ya same ta ba,haƙuri yake yi da kuma juriya,tinda shi dai ya sani bai taɓa kusantar zina ba,ya ɗauki hakan a matsayin jarabawar rayuwarsa.
Ruwa ya ɗauka a gora ya koma parlour ya zauna,ba tare da sanin gaba ɗaya ruwan da ke cikin ƙatuwar gorar gidan ba Lamyah ta yi musu ayoyin ruƙya ta mayar ta ajiye. Kafa kai ya yi ya kwankwaɗi ruwan sannan ya mayar ya ajiye a saman table ɗin. Kallo ya kunna a cikin ransa ya na fatan ta sake fitowa ya yi tozali da kyakkyawar surar ta. Ita kuwa Lamyah da ta koma ɗakinta ta jima tana aikin kuka kafin ta lallashi kanta ta ɗauki abincinta ta ci ba dan daɗi ba,sai dan yunwar da ke addabar ta. Ta na gamawa ta shiga banɗaki ta watsa ruwa sannan ta shafa mayukanta masu kyau tare da gyara fata sannan ta sanya doguwar riga marar hannu,turaruka ta fesa a jikinta ta tada sallahr azahar. Ta na idarwa ta kalli kwanikan da ta kasa fita ta mayar saboda gudun kar ta haɗu da Aminullahi. Tsaki ta ja kafin ta zare hijabinta ta ninke ta ajiye,kwashe su ta yi ta fita ta na ƙunƙuni. Gani ta yi babu koma a parlourn ga TV na aiki ita ɗaya,kauda kanta ta yi ta wuce kitchen ta wanke kwanukan da tukwanen da tayi amfani da su sannan ta juya ta koma parlour,ta na nan zaune ta na kallo ta ji an buɗe ƙofar gidan nasu da ƙarfi,a razane ta kalli ƙofar,sai ta ga Aminullahi ya shiga parlourn a rikice kamar wanda aka koro,bai ƙarasa cikin parlourn ba sai da ya kulle ƙofar gidan da makulli sannan ya isa parlourn,tin kafin ya ƙarasa wajen Lamyah ya hau cire rigarsa ya na faɗin.
"Taso mu je na taimaka miki kafin Layuzah ta gama da wajen wankin kai ta kira ni na ɗakko ta. Ke! Ba magana nake yi miki ba? Na ce ki tashi mu je na taimaka miki."
Wani irin yanayi Lamyah ta ji yana taso mata a ƙirjinta,takaici,haushi,baƙinciki tare da tsantsar mamakin furucinsa,tsawar da ya sake daka mata ne ta dawo da ita hayyacinta,zumbur ta miƙe ta na ja da baya ta ce.
"Noo bana so ka ƙyale ni,ni ban ce maka ina neman taimakon ka ba,kar ka takura min."
Ba tare da Aminullahi ya tsaya ya saurare ta ba,kawai ya damƙi hannunta,janta ya yi ɗakinta ya fara aika mata da saƙonnin da suka fara sanya ta yin luf a jikinsa,cikin wani irin yanayi Aminullahi yake sarrafa ta har ya samu biyan buƙatarsa,wanda da ga ƙarshe kuka mai tsanani ya fashe da shi tare da rungume Lamyah da ke tsiyayar da hawayen azaba,cikin kuka da shan majina ya ce.
"Ki yafe mini ƙanwata,ki yafe wa Yah Amee ɗin ki,domin Allah ba domin halinsa ba. Na sani na zarge ki akan abinda baki aikata ba,amma kika yi shiru kika ƙyale ni,na ci miki mutunci akan zargin banza,duk da haka baki tada hankalin ki ba,na ƙi ki a matsayin matar aure dik da cewa na rayu da son ganin ki,sannan na aure ki kamar yanda na yi wa Baaba alƙawarin zan aure ki na kula da ke. Lamyah na faɗi a matsayi na na ɗa,na gaza a matsayi na na yaya,sannan na gaza a matsayi na na mijinki,na rasa me yake danne zuciyata game da ke,sai na ji ni garau ina son na rungume ki na yi farinciki da bayyanar ki a gare mu,tare da murnar kasancewar mu inuwa ɗaya,sai kuma na ji bana ƙaunar na buɗe ido na gan ki a cikin gidan gaba ɗaya. Lamyah don Allah ki ƙara haƙuri da ni,sannan kar ki bari Layuzah ta san da akwai wata alaƙa a tsakanin mu please."
A kaf kalaman shi babu wanda ya tsaya mata a rai da ya wuce ƙoƙarin ɓoye alaƙar su da yake so ta yi kada Lahuzah ta sani. Me yake nufi da hakan? Ya na nufin zai karɓe mata abu mafi daraja da mahimmanci a tattare da ita ne sannan ya tsallake ta ya barta ya kuma nuna bai santa ba a gaban matarsa? Kafin ta yi wani yunƙuri Aminullahi ya sanya kayansa ya bar ɗakin cikin sauri,banɗakinsa ya je ya tsarkake jikinsa ya na zabga wani irin murmishi mai cike da nishaɗi da annashuwa. Tinda ya yi aure da Layuzah ko a wasa bai taɓa cin karo da irin wannan ni'imar a jikinta ba,ga kuma uwa uba budurcin Lamyah da ya samu intact babu wanda ya taɓa ta. Shi ne ya fara kusantar ta a duniya. Hamdala ya yi tare da sanya mata albarka ya huɗe gidan ya fita ba tare da ya waiwayi halin da ya bar ta ba.
Lamyah kuwa tana nan tana cin kuka da baƙin cikin irin wulaƙancin da Aminullahi ya yi mata,sai ta yunƙura da ƙyar ta zaro wayarta ta kira Zahrah,Zahrah na jin Lamyah na kuka sai ta rikice,tsaye ta miƙe ta na tambayar bahasin kukan nata,cikin kuka Lamyah ta ce.
"Don Allah...Zahrah...ki ce Iya ta zo....zan mutu."
Kuka ne ya ƙwace mata ta kife wayar ta ci gaba da rera abunta mai tsuma zuciyar mai saurare. Zahrah kuwa bata ɓata lokaci ba wajen tsallake girkin da suke yi ta nufi ɗakin Iya,cike da tashin hankali ta labarta wa Iya abinda ke faruwa. A rikice Iya ta sakko daga katifarta ta zira riga ta sanya Hijabi ta na faɗin.
"Sake kira min ita na ji me yake faruwa,kin tabbata kuka kika ji tana yi?"
"Da gaske nake yi Iya,kuka take yi sosai wanda ban taɓa jin ta yi irinsa ba,har ta na kiran kalmar mutuwa."
Dafe ƙirji Iya ta yi ta zaro idanunta waje sannan ta ce.
"Ke bari Zara'u ! To banga ta zama ba,bari na je na sanar da Hajiya abinda ke faruwa."
Sashen Momma ta nufa,ta na isa ta tarar da ita da Mubarak suna zaune ya na cin biscuit ita kuma tana latsa waya. A rikice Iya ta yi mata bayanin komai,nan take Momma ta ce.
"To ko tare za mu je ne Iya?"
"Ah ah Hajiya ki yi zaman ki,ni zan je na ji menene,idan abinda ya zama wajibi ne ki zo to sai na sanar da ku."
"To Iya Allah Ya jiyar da mu alkhairi,yanzu ki wa Tanimu magana ya kai ki."
"To Hajiya."
A gaggauce Iya ta bar gidan Zahrah na jin kamar ta je ta ji me ya samu Lamyah. Iya kuwa sai addu'a take yi tana fatan komai ya zo da sauƙi.
Lokacin da mota ta tsaya a bakin gate ɗin gidan Iya bata jira wata-wata ba ta buɗe mota ta shiga ciki. Mai gadi kuwa dake ya santa sai kawai ya gaishe ta ta wuce ciki. Kai tsaye ɗakin Lamyah ta shiga wadda azaba ta sanya ta fara baccin wahala,Iya na ganin Lamyah ta fahimci abinda ya faru,hamdala ta fara yi da ƙarfi ta na murmusawa,ko babu komai kalmar Karuwa da Aminullahi ke jifan Lamyah da shi za ta kau a tsakanin su. Ƙarasawa ta yi ta zauna a gefen Lamyah ta hau shafa gashin kanta,Lamyah na buɗe ido ta sauke su a saman fuskar Iya,kyaɓe baki ta hau yi irin na shagwaɓaɓɓun nan tana so ta kece da kuka,kai Iya ta girgiza mata sannan ta ce.
"Alhamdulillah Lamyah kin kawo mutuncin ki ɗakin mijinki. Fatana Allah ya baku zuri'a mai albarka ya daidaita zaman ku."
Kuka Lamyah ta fashe da shi sannan ta ce.
"Ji nake yi kamar zan mutu da baƙinciki Iya,Yah Amee ya ci amanar ƙauna,Iya ya yi min mafi munin wulaƙanci a duniya,ki duba ki ga abinda ya yi min kuma ya tafi ya barni a haka."
"Ki ƙara haƙuri da shi Lamyah,tinda har aka zo wannan matakin muna gaf da samun nasara,yanzu tashi na taimaka miki kin ji?"
Cike da cije baki Lamyah ta miƙe za ta tashi,wata ƙara ta saki kamar za ta shiɗe ta koma ta kwanta. Ganin halin da Lamyah ke ciki ne ya sanya Iya yaye abun rufar da Aminullahi ya lulluɓa mata,baki Iya ta kama ta na salati,tabbas ba karamar ɓarna Aminullahi ya yi ba,dan haka fita ta yi daga ɗakin sannan ta zaro ƙaramar wayarta ta kirawo Mommaa,bata jima tana ringing ba ta ɗauka,cike da zumuɗin son jin abinda ya sami Lamyah. Nan take Iya ta labarta mata abinda ke faruwa,da sauri ta katse kiran ta kira Nurse Shamsiyya,dan kuwa ita take duba ta idan bata da Lafiya.
Sai da suka kai rabin awa suna jiran nurse Shamsiyyah kafin ta iso,kan ta iso Lamyah ta yi wanka Iya ta gasa ta,ta na zuwa ta duba Lamyah sai ta ce lallai sai ta yi mata ɗinki, Lamyah na kuka nurse ɗin ta ɗinke ta tsaf sannan ta bata maganin da zai kashe mata raɗaɗi da saukar da zazzaɓi.
Sai da ta biya gida ta haɗu da Momma sannan ta wuce. Iya kuwa na nan wajen Lamyah da baccin azaba ya fara ɗaukanta,zuciyarta na yi mata ƙunci akan wulaƙancin da Aminullahi ya yi wa Lamyah. Ta shirya tinkarar sa a yau dan haka waje ta samu ta zauna a parlour ta na jiran dawowarsu.
[9/11, 10:50 AM] zee hussain: ƳAR RAWA.
RUBUTAWA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✍️✨
PAGE 39.
Tinda suka tinkaro gidan gabansa ke faɗuwa,domin bai san me Layuzah za ta yi masa ba idan ta gano ya angwance cikin sirri. Hankali tashe ya shigar da motar tasa cikin gidan,sai dai ganin Tanimu zaune suna hira da abokinsa ne ya sanyaya jikinsa,tambayoyi ne cike da bakinsa,amma ya barwa cikinsa,dole ne ya je ya ji baƙon da suka samu a cikin gidan,gudun kar ya afka kai tsaye ya samu matsalar rufuwar asirinsa.
Layuzah na fitowa daga motar sai ta jira ya fito su shiga gidan tare,kamar yanda ta saba kasawa ta tsare dan kar ya je wajen Lamyah. Gani ta yi ya nufi wajen masu aikin nasu sai kawai ta ce.
"Da ka gama gaisawa da su ka shigo,zan nuna maka wani abu. Baby kar fa ka jima please."
Ta ƙarasa maganarta ta na wani kashe masa ido. Yaƙe ya yi mata kawai a ransa ya na faɗin.
'Ai ni yanzu kwaɗayina da burina bai wuce na sake ji na a gonar da ni ne kaɗai na fara shuka a cikinta ba,ina kuma roƙon Allah da ya tsare ni da sake shiga gidan aro.'
Gaisawa suka yi da masu aikin nasu sannan ya ce.
"Tanimu yau ka yi kewar abokin ka ne ka biyo shi?"
Dariya Tanimu ya yi sannan ya ce.
"Ah ah Alhaji,ai na kai awa ɗaya zuwa biyu anan,Iya na kawo,kuma da dikkan alamu tare za mu koma,domin bata ce na tafi ba har yanzu."
Rass gaban Aminullahi ya faɗi,cike da tashin hankali ya ce.
"Ikon Allah,wataƙila ta zo ganin ƴar lelenta ne,bayan ita mun sake yin baƙi ne?"
"Eh Nurse Shamsiyya ta zo,ta ɗan jima itama kafin ta tafi."
'Innalillahi wa inna'ilaihirraji'una,Momma ta san me na aikata kenan,kai wannan yarinya ba a sirri da ita,da alama sai ta faɗawa Layuzah mun kaɗaice,yanzu ya zan yi?'
Ya ayyana a ransa,a zahiri kuma sai ya ce.
"Masha Allahu,to ni bari na ɗan fita,ka gaida gida ko?"
Sallama ya yi musu cikin sauri ya bar gidan ya gudu restaurance ɗin da ya kan je ya ci abinci ya kuma zauna dan ya samu salama daga harigido da maitar Layuzah. Zaune yake ya na tina yanda ya kasance da Lamyah yana jin wani irin shauƙin sonta da ƙaunarta na shigarsa,a cikin ƙanƙanin lokaci soyayyar da ya taso yana yi mata ta ninka ta da,ji yake yi zai iya fito -na-fito da duk wanda zai shiga tsakanin su,ko da Layuzah ce kuwa,wani irin ƙwarin guiwa yake ta samu a ransa kamar idan ya je gida zai iya zazzagawa Layuzah masifa akan ta barsu su gudanar da rayuwarsu cikin ƴanci kamar kowanne ma'aurata.
Aminullahi na nan zaune aka kira sallar la'asar,alwala ya fita ya yi ya je masallacin jikin restaurance ɗin ya yi sallah,a wajen ya zauna ya na ta latsa wayarsa har akai magariba da Isha'i,ya na idarwa ya miƙe ya koma restaurance ɗin nan ya cika cikinsa dam,sannan ya yi wa iyalan nasa takeaway ya wuce gida a ƙafa. Yana shiga ya ga Tanimu baya nan,sai ya sauke ajiyar zuciya ransa fess ya miƙawa maigadi abincinsa sannan ya wuce ciki,ko da ya shiga cikin gidan ya tarar da TV na aiki babu kowa a parlour,ɗakin Layuzah ya je ya murɗa ƙofa ya ji ta a rufe, ƙwanƙwasa wa ya dinga yi ta na jinsa ta ƙi buɗewa,a zaton ta buƙatar ta ce ta kawo shi,cikin ɗaga murya da jin haushinsa ta ce.
"Ka san tsawon lokacin da na ɓata ina jiranka kuwa? Amma saboda ka mayar da ni ƴar iska shi ne ka yi tafiyar ka ba ka dawo ba sai yanzu,to ina nan buƙatar kasancewa da kai bata kashe ni ba,don haka dole kaima ka je ka jure taka."
Dogon tsaki ta ja kamar za ta tsinke harshen ta,sannan ta juya ta yi kwanciyarta ta na jin daɗin abinda ta yi masa. Shi kuwa hamdala ya yi tare da sauke ajiyar zuciya ya koma kitchen ya ajiye nata abincin a fridge sannan ya taka cikin sanɗa ya isa ƙofar ɗakin Lamyah,a hankali ya murɗa hannun ƙofar ya rufta ciki,ya na shiga ya tarar da Iya zaune a bakin gado ta zabga tagumi ta na gyangyaɗi,a hankali ya taka zai ajiye ledar da ya kawowa Lamyah Iya ta farka,rintse ido ya yi sannan ya buɗe su tare da sakin yaƙe yana sosa kai ya ce.
"Ahh Iya kuna nan dama baku tafi ba?"
"Ina zan je na bar marainiyar Allah a halin da kai ka tsallake ta ka barta? Anya Aminullahi rayuwar da kake kai yanzu za ta ɓulle da kai hanyar tsira kuwa? Ka saki Allah,sai Ubangiji ya sake ka shima,da ace ka kusanta kanka da Allah da baka cikin wannan ƙulli da dabaibayin da kake ciki a yanzu,Aminullahi ina kyautata zaton da iyayenka basu raye suna taya ka da addu'a mu masoyanka muna yi maka da sai ka fi haka taɓarɓarewar lamura,saboda ka saki ibada ka kama mace. Yaushe rabon da ka tafi Nigeria? Yaushe rabon da duk safiya da maraice ka je gaida iyayenka kamar yanda ka saba? Ni kuwa dama ka tsane ni baka son gani na,ga marainiyar Allah da aka baka ita amana ka yagalgala ta ka tafi ka barta,sai da Hajiya ta kira Nurse Shamsiyya ta ɗinketa kamar ƙwarya. Aminullahi don girman Allah ka dinga azkar ɗin safe da maraice,ka dinga yawan karanta ƙur'ani da sauraronsa. Ina son Aminuna da na ke so yake so na ya dawo,bana son wannan Aminun da zuciyarsa ta cire son kowa daga kansa sai matarsa marar tarbiyya ya sani."
Kuka Iya ta fashe da shi har sai da Aminullahi da ya durƙusa tin farkon fara yi masa nasiha da tai, ya rarrafa ya rungume ta a faffaɗan ƙirjinsa. Ji ya yi wani abu mai kama da ƙarfin zuciya da yayewar ƙunci,damuwa, tsoro da shakkar kowa na yaye masa,a hankali Iya ta ce.
"Ka dinga yawan karanta Hasbunallahu wa ni'imal wakil,ka dinga yin istighfari mai yawa,tare da lahaula wala ƙuwwata illa billah. Muna son ka Aminullahi,muna son ka dawo da kyakkyawar rayuwa da mu'amalar dake tsakaninka da mu. Ka tarairayi marainiyar Allah ka gatanta ta ka maye mata gurbin da ta rasa,kar ka zamo silar sake afkawarta cikin damuwa da baƙinciki."
Hawaye ne masu zafin gaske suka hau zubowa daga idanun Aminullahi,don haka ya kasa magana sai gyaɗa wa Iya kai kawai yake faman yi,cike da sanyin jiki da nadama ya leƙa Lamyah dake sharar bacci,fita Iya ta yi ta bashi waje dan ya ga matarsa,zama ya yi a bakin gadon ya kamo hannayen Lamyah,jin ƙamshin turarensa ne ya sanya ta farkawa,sai dai ta ƙi motsawa gudun ya gano ta farka,sumbatar yatsunta ya yi yana murmushi tare da zubar da hawaye. Cikin wata iriyar muryar da ta tabbatar wa da Lamyah kuka yake yi ya ce.
"Ki yafe min ƙanwata,ki yafe min domin Allah ba don halina ba,na yi alƙawari daga yau komai zai sauya,ba zan sake yi miki riƙon sakainar kashi ba,ke ce mace ta farko a cikin matan da ya halatta na aura da na fara so a rayuwata,da soyayyar ki na reni zuciyata,zargi da mugun zato ne ya so ya shiga tsakaninmu,ki yafe min akan munanan kalamai da sunaye da na dinga jifan ki da su. Ina son ki Lamyah, Ina son ki sosai A'ishana."
Murmushi ne ya so ƙwacewa Lamyah sai ta ƙwace hannunta ta juya masa baya,a zaton sa baccin ya mata daɗi ne ya sanya ta juyi,sake rufe ta ya yi sannan ya miƙe daga gefen gadon,duƙawa ya yi ya sumbace ta sannan ya fita. A tsaye ya tarar da Iya ta na ƙoƙarin komawa ɗakin,dan sai da ta fito ta ga wautar barin su su kaɗai da ta yi,karo suka ci ya yi saurin ja da baya,kansa a ƙasa ya ce.
"Iya ku yi haƙuri ku yafe min,In Shaa Allahu za a gyara,ba za ku sake kama mu da wani abu mara daɗi ba."
Hamdala Iya ta dinga zabgawa tare da yi masa addu'o'i masu yawa,cike da farinciki ta shige ɗaki ta kwanta. Aminullahi kuwa kasa baccin ya yi,zuciyarsa na ta saƙa masa yanda zai kawo gyara a lamuran gidansa,a yanzu ne ya gano kuskuren da yake aikatawa kuma ya ci alwashin gyarawa. Har ƙarfe ɗaya da rabi idanunsa biyu bacci ya ƙi kai masa ziyara. Banɗaki ya shiga ya watsa ruwa sannan ya ɗaura alwala ya fito,jallabiyya ya sanya sannan ya hau abun sallah ya tada sallah,shi kansa jinsa yake yi kamar wani sabon mutum,rabon shi da sallar dare har ya manta, ballantana kuma yana zaune babu abinda yake yi ya yi tasbihi ga Allah. Tun a cikin sallarsa ya fara kuka da neman gafarar Allah na nesanta kansa da ya yi da Ubangijinsa. Ya na idarwa ya zauna ya dinga kwararo addu'o'i da larabci,wanda sama da rabin su Aminee ce ta koyar da shi tin yana ƙarami. Lokacin da ya girma kuwa idan abu ya shige masa duhu ya kira ta haka za ta faɗa masa wasu addu'o'in da ya kamata ya dinga yi ta waya har sai ya haddace. Sosai Aminullahi ya yi kukan nadama da kewar Ammin tasu da Baaba,a wajen bacci mai daɗi cike da mafarkan da suka sanya shi yin dariya ya ɗauke shi.
Washegari da asuba da ya tashi sai ya ji shi kamar sabon mutum,wanke bakinsa ya yi sannan ya yi alwala ya wuce masallaci. Bai dawo ba sai da gari ya fara haske sannan ya koma gidan,a kitchen ya tarar da Iya tana haɗa musu abincin karyawa da abinda ya fi so. Murmushi ya sakar mata tare da gaishe ta,amsawa ta yi cikin jin daɗi har ƙwalla na taruwa a idanunta,yaushe rabon da Aminullahi ya kalle ta da idanun tausayi da soyayya? Idan bata manta ba tin satin da suka gama amarcin su da Layuzah ya sauya mata,yanzu kuwa gasu sun yi watanni da aure. Hamdala ta yi wa Allah a ranta tare da bin Aminullahi da ya nufi hanyar ɗakin Lamyah da kallon ƙauna irin wadda uwa ke yi wa ɗanta.
Suna haɗa ido da Lamyah jikinta ya fara rawa,hankalinta ya tashi,banda ɗaure fuska babu abinda take yi dan kar ma ya taɓa ta. Murmushi ya sakar mata sannan ya ce.
"Shagwaɓaɓɓiyar Iya da Momma kin tashi lafiya? Ke yanzu lamarin naki babu sirri a cikinsa ashe sai da kika gayyato Iya ta zo ta san sirrin mu?"
Murguɗa masa baki ta yi sannan ta ce.
"Ai ka riga da ka san karuwai basu da sirri amma ka shiga gonar su duk da haka."
Kalmar karuwa da ta jingina kanta da ita ta sosa ransa,amma ya zai yi tinda shi ya fara kiranta da wannan kalmar? A hankali ya taka ya isa gabanta ya tsaya yana kallon fuskarta,idanunta na kallon yatsun ƙafarsa ta ji ya shafa kuncinta,zabura ta yi cikin ƴar ƙara ta kama jikinta ta ce.
"Wayyoo Allah na Iya,akwai ciwo."
Iya na jin haka ta ƙarasa ajiye food flask a saman dinning ta nufi ɗakin Lamyah a guje,a bakin ƙofa ta tarar da Aminullahi ya na zare ido alamun rashin gaskiya ya bayyana a tattare da shi,Lamyah kuwa sake ƙanƙame jikinta ta yi tana hawaye,Iya na ganin haka ta hau hararar sa, buɗe baki ya yi zai wa Iya bayani sai ya ga Lamyah ta sakar masa gwalo,cikin sauri ya ce.
"Kin gani ko? Ƙarya take yi babu abinda na mata,gaishe ta da jiki kawai na yi...."
"Ni ba zan hana ka kusantar matarka ba,anjima kaɗan ma ni zan tafi,amma dai ka yi haƙuri har ta ji sauƙi."
Iya ta faɗa ta na nuna masa hanyar fita,kallon Lamyah da ta shagwaɓe fuska ya yi cike da mamaki,nan take ta tina masa lokacin suna yara haka take yi masa,be yi mata abu ba idan ta
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 24 Chapter of 30