Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
shi halin mamakin da ya shiga ya biye mata. (Shi yasa aka ce kar mutum ya dinga yanke hukunci cikin rashin sani,gashi nan ana zaton wuta a maƙewa....) ******************* Hayaƙin da ya turniƙe madafin ne ya sanya Lamyah fitowa a guje ta na kokowa da nunfashinta,tarin da ya sarƙe ta ne ya sa ta gigice ta rasa inda za ta tsaya ta ji iska mai daɗi,shewa Innoh ta yi sannan ta ce. "Lallai ne Balarabiya,ni za ki yi wa makirci? Ko an faɗa miki bama ganin ƙasashen naku ne a wayoyin hannu da talabijin,talauci da babun ai kuma kuna ɗanɗanar ta,shi ne za ki wani fito kina wani shiɗewa kamar wadda ta shaƙi barkono ba hayaƙin itace ba. Wuce mu je ki tuƙe min tuwo tass,dan ba zai yiwu kina zaune na tuƙa na kawo miki har ɗaka ba,kamar yanda waɗannan masu neman gindin zama a wajen mijin ke yi miki." Idanun Lamyah na zubar da hawaye sun yi jawur ta sake shiga kitchen ɗin,tari ne ya sake sarƙe ta,yanda take yin tarin ne ya sanya Asabe da Larai fitowa suka tsaya cirko-cirko kamar su karɓa mata girkin,tinda dama ba ranar ne kaɗai Innoh ke dasa bala'i ba dole su karɓi girkin su yi ko a kwana da yunwa. Kallon da ta bi su da shi ne ya sanya su komawa su tsaya su na kallon ikon Allah da ƙarfin halin Innoh. A haka Musaddiƙ ya shiga gidan ya tarar da Lamyah na ta tari riƙe da muciya a hannunta,cikin sauri ya shiga kitchen ɗin ya karɓe muciyar sannan ya kalle ta ya daka mata tsawar da ta sanya Innoh saurin dafe gini,Lamyah kuwa durƙushewa ta yi a wajen ta na kuka da dasasshiyar muryar ta. "Ki yi min shiru ki wuce ɗaki ki zauna ! a gidan uban wa ki ka iya girki a irin wannan kitchen ɗin har da za ki shige shi?" Ganin Lamyah ta ƙi tashi ta na nan duƙe rungume da Mubarak da ya isa gare ta ya rungume ta suna kuka ne,ya sanya shi kama hannunta ya na janta zai kai ta ɗaki. A ɗan tsorace Innoh ta ce. "To ubanta ai sai ka sakar mata hannu in dai ba abinda na zargi kun aikata bane a daren jiya ka ke so ka tabbatar min a gaban kishiyoyi su samu abun tsegumi a kai." Tsayawa Musaddiƙ ya yi cak ya na wani irin huci,a zaton sa sun gama da wannan babin tinda ta tambayesa ya tabbatar mata da cewa babu abinda ya shiga tsakaninsa da Lamyah,me yasa take son tozarta marainiyar Allah? Da gudu Lamyah ta ƙwace hannunta ta shiga ɗaki, ta na kuka ta lalubo wayarta ta nemo lambar Bala,bata wani jima ta na ringing ba ya ɗauka,a daidai wannan lokacin yana tare da Afrah a jikin mota suna zance,jin tana wani irin kuka ne ya sanya Bala saka wayar a handsfree hannunsa na rawa,Afrah na jin muryar Lamyah na kukan da bata taɓa jin ta yi irin sa ba tin farkon haɗuwar su sai jikinta ya hau tsuma kamar ana kada mata gangi,cikin rawar murya Bala ya ce. "Lamyah me ya same ki? Me aka yi miki?" Cikin tsakanin kuka da neman iskar da za ta shaƙa ta ce. "Ba...Bala...ka zo...ka ɗauke ni daga nan...zan...zan mutu Balaaa Innoh za ta kashe ni." Kuka ta sake rushewa da shi ta labarta musu irin halin uƙubar da Innoh take gasa mata tin zuwanta gidan,kafin ta kashe wayar ta yi wurgi da ita ta hau haɗa kayan su,Afrah ce ta hau ƙoƙarin buɗe murfin mota,ganin haka ne ya sanya Bala zaro makullin motar ya buɗe Afrah ta ɓalle murfin ta shige ta rufe kanta tana ta jijjiga ƙafa,Bala na shiga ya tada motar suka wuce Rijiyar Lemo. A gigice Lamyah ta fito tsakar gida tana kwashe shanyar kayan su da ta yi,Asabe sai sharar hawaye take yi dan ba za ta iya cewa komai ba,to ana tsoron Iya in ji ƴaƴan mayya, Larai kuwa ta na ta yaɓawa Innoh magana a tsorace,dan kuwa gaba ɗaya gidan tsoronta ake ji har shi mai rawanin gidan. Da jin irin wayar da ta yi sai jikin Musaddiƙ ya mace,cikin sauri ya isa gaban Lamyah dake kwashe kaya a igiya tana kuka ya damƙe rigar ta da take ja ya ce. "Haba Lamyah,me yasa za ki yi waya ki kira a zo a ɗauke ki? Ashe ba za ki iya haƙuri da ƙaddarar da Allah ya ɗora maki ba?" Cikin sauri Lamyah ta kalle shi ta ce. "Na ɗorawa kaina dai Yah Musaddiƙ,Allah bai ɗora min wannan rayuwar ba,ina da gata ina da dukiya mai tarin yawa,tsananin kwaɗayin ladan sada zumunci da dangin mahaifiyata ne ya jawo min wannan wulaƙancin,ni ce nan na ɗorawa kaina wannan wahalar,a yau kuma zan yayewa kai na ita, Yah Musaddiƙ ban taɓa zaton wannan rayuwar zan tarar a dangin mahaifiyata ba,a barni da ƙunar da raina take yi na ƙin karɓar mu da dangin Ammi suka yi mana,amma shine za a zo a dinga azabtar da ni kamar babu zuciya a ƙirazan wasu mutanen? Ba zan taɓa iya zama anan ba ana wulaƙanta ni." "Ya kike so na yi da raina idan kika barni?" "Ka auri Saddiƙa,ita ce zaɓin mahaifanka,tinda Innoh da kanta ta sanar dani ita ce matar da ta zaɓa maka." "Yarinyar da bata da kamun kai kike cewa na aura?" "Idan kuma ta samu shiriya ta sanadin ka fa? Dan Allah ka sakar min kaya na na wuce,ni dama ban taɓa yi maka so na soyayya ba,ina ƙaunar ka ne a matsayin ɗan'uwa amma ba mijin da zan yi zaman aure da shi ba." Tana gama faɗar haka ta fizge rigarta ta kwashe sauran kayan ta wuce ɗakin ta zuba su a akwati babu ko ninki. Musaddiƙ ma ɗakin sa ya wuce zuciyarsa na raɗaɗi da ƙuna akan kalaman Lamyah,cikin wata iriyar murya ya ce. "Bata so na fa? Kuma wai na auri Saddiƙa, ko dai wannan shi ne sakayyar soyayyar shan mintin da na yi da yaran mutane lokacin ina bautar ƙasa? Innalillahi wa inna'ilaihirraji'una, ina zan kai soyayyar yarinyar da bata so na kallon ɗan'uwanta take yi min?" Wasu zafafan hawaye ne suka zubo masa,Lamyah na ɗaki tana haɗa kayayyakin su,Asabe da Larai suna ɗakin Larai suna gulmar abinda ya faru,Innoh kuwa ta na tsakar gida ta na ci gaba da zagi tare da aibata Lamyah da mahaifiyarta da ta auri Balarabe saboda son abun duniya a cewarta. Sallama Afrah ta yi idanun ta sun yi jawur ta ce. "Nan ne gidan mai unguwa?" A sheƙe Innoh ta kalle ta ta ce. "Da akwai wani gidan ne banda wannan ɗin?" A ƙufule Afrah ta yi ƙwafa sannan ta sake cewa. "Ke ce Innoh?" "Ni ce nan Innoh ke ɗin wa...." A guje Afrah ta yi kanta har ta na yarda takalmin ta guda ɗaya ta ce. "Dama saboda gudun kuskure ne ya sanya ni tambaya,yau kin gamu da gamon ki Innoh ki fara kalmar shahada kawai." Akan Innoh Afrah ta dira ta hau jibgarta tare da shaƙe mata wuya ta na janta a ƙasa ta na faɗin. "Yau sai kin ɗanɗana azabar da tinda uwarki ta kawo ki duniya baki taɓa shan kalar ta ba,sai kin yi danasanin sanya hannun ki a jikin marainiyar Allah,sai na kulle ki a ɗakin duhun da kika so sanya ƴar mutane yau."........ [9/11, 10:50 AM] zee hussain: ƳAR RAWA. RUBUTAWA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✍️✨ PAGE 26. "Subhanallahi ! Wayyoo ni Allah na shiga uku za ta ɓalla min baya,ke baiwar Allah daga ina kika diro kamar an harbo kibiya? Wayyoo ƙugu na me na yi miki za ki hau duka na kina ja na a ƙasa? Babu kowa a gidan ne? Asabee Larai, kai Musaddiƙ kana ina jikar aljanu za ta kashe uwarka?." "Au ni ce ma jikar aljanun? To ba jikar su ba ce aljanar ce da kan ta,yau sai kin shiga ɗakin duhun da kike ƙoƙarin saka ƴar mutane a cikinsa ki ji idan da daɗi." "Na jima ina zargin dama yarinyar nan ba mutum bace,dan Allah ku yi min rai daga yau ko kallon inda take ba zan sake yi ba, kai Musaddiƙ taho bakin ka ɗauke da ayoyin Allah dan ba lallai ka ga abinda nake gani ba,wayyooo Allah Yallaɓai ka zo za a kashe uwar ƴaƴanka." A zafafe Musaddiƙ ya ƙwace Innoh daga riƙon da Afrah ta mata tana huci,cikin ɗaga murya ya ce. "Ke mahaukaciyar ina ce da za ki zo ki hau dukan mace a gidanta? To maza kibar gidan nan kafin na ɓaɓɓalla ki." "Ga mahaukaciya nan azzaluma ka riƙe,na rantse da...." A guje Lamyah ta fito daga ɗaki ta faɗa jikin Afrah ta rushe da wani sabon kukan,jin Lamyah na kuka sai ya ƙara tinzira Afrah ta ƙwace jikinta daga na Lamyah ta sake yin kan Innoh,dan ita bata ƙi su daku da Musaddiƙ ɗin ba ma akan Lamyah,ganin Afrah ta zabura ta yi kan Innoh ne ya sanya Innoh kwasa da gudu ta yi ɗakinta ta banke ƙofa tare da sanya sakata,ta window ta leƙo ta na goge majinar da ta yi tsartuwa ta fito daga hancinta tana ƙwai ta ce. "Kai Musaddiƙ ci min uwarta,in dai ka cika ɗan halak ba wahalar naƙudar ka na yi ba ka haɗa su dika ka dakar min shegu." Wani irin kallo Musaddiƙ ya bi Innoh da shi,a iya tinaninsa ita ce fa bata da gaskiya,sai dai abinda Afrah ta yi itama bai dace ba,ko babu komai Innoh ta haife ta,dan haka bai kamata ta hau ta da duka ba,amma kuma ta wani ɓangaren zai iya cewa tsuntsun da ya jawo ruwa,shi ruwa ke duka,dan haka babu abinda zai iya yiwa Afrah da ya wuce ya kora ta waje ta bar musu gida. Cike da zafin nama ya kama hannun Afrah dan ya kai ta waje,sai dai abun mamaki ko gezau bata yi ba,hasali ma ido ta kafe shi da shi kamar za ta kai masa duka,da jin haka ya gane lallai wannan yarinyar irin su ake kira da masu ƙashi ɗaya,dan haka babu abinda zai kai shi yin faɗa da ita ta kunyata shi,sassauta riƙon da ya yi mata ya yi yana kallon idanunta da suke a bushe suka yi jawur saboda bala'i,a hankali ya ce. "Dan girman Allah ki yi haƙuri ki fitar mana a gida bama son bala'i da masifa." Nuna Innoh da ke leƙe ta window Afrah ta yi ta ce. "Ga wadda ta jawo muku bala'i da masifa can,dan haka dole ku yi haƙuri ku karɓe shi a yanda ya zo muku." Lamyah ce ta ƙarasa fitowa da kayan su ta kama hannun Afrah za su bar gidan,Bala ne ya shiga soron gidan ya kwashe kayan tas ya loda a mota,cikin sauri Musaddiƙ ya isa gaban Lamyah ya ce. "Yanzu haka za ku tafi ba za ku jira a kirawo Abbah da Baba Abu ba ku yi sallama ba?" "Ba za ta yi sallama da uban naka ba,yana ina ake cin zalinta ake cin zarafinta? Ya san ba zai iya riƙon amanar ta ba ya ce ta zauna a gidansa? An faɗa muku bata da gata ne?" "Ke ba da ke nake ba,ki matsa ki bani waje ni." Sassauta muryarsa ya yi tare da kallon Lamyah dake kuka tana share hawayenta ya ce. "Shikenan yanzu idan kika tafi ba zan sake ganin ki ba? Don Allah ki karɓi soyayya ta ki..." "Yah Musaddiƙ dan Allah ka yi haƙuri,aure ni da kai ba zai taɓa yiwuwa ba,ka auri Saddiƙa Allah Ya baku zaman lafiya,idan Abbah ya dawo ka yi masa godiya akan ƙoƙarin da yake na sada ni da Abii,in Shaa Allahu za mu haɗu ne ko bajima ko ba daɗe." Hannunta Afrah ta ja suka bar gidan,wajen da Mai Unguwa ke zaune wayam babu kowa,da alama ya tafi wani wajen da mutanen sa,dan haka ba tare da saninsa ba su Lamyah suka bar gidan,sai da suka bar Rijiyar Lemo gaba ɗaya hankalin Lamyah ya kwanta,kwance take a jikin Afrah dake zayyanawa Bala yanda suka kwashe da Innoh,cike da takaici ta ce. "Ai na so na samu dama na cire mata haƙori ko ɗaya ne,ka ga gobe idan an ce ta zalunci wani za ta tina da ni,murmushi wannan sai ya gagari azzaluma." Dariya Bala ya bushe da ita dan hango yanda fuskar Innoh za ta koma, a haka suka isa gida Lamyah bata tofa musu komai ba a hirar tasu. Ruwan zafi Afrah ta haɗa mata da abubuwan wanka a ciki ta jata banɗakin,sai da ta ga shigarta kwamin wankan sannan ta fito, ji take yi da da hali ma da kanta za ta yi mata wankan. Tana jin son Lamyah a zuciyarta kamar ƙanwarta da suka fito ciki ɗaya,a da da babu lamyah tana rayuwa ita kaɗai lafiya ƙalou,amma zuwan Lamyah rayuwarta ya sanya ta samun natsuwa da kwanciyar hankali,tare da jin cewa ta samu dangin da ta rasa,shi yasa tayi alƙawari a zuciyarta zata zauna da Lamyah da amana da kulawa kamar yanda ƴan'uwa na jini za su yi wa junan su. Lamyah ta jima a kwance cikin kwamin wanka tana kukan baƙin cikin rayuwar da take ciki,ashe kuɗi ba su ne farin cikin rayuwa ba, tinda gata da su amma basu wanke mata ƙuncin zuciyarta ba. Kowanne dangi ne suke fuskantar matsaloli game da zumunci kamar nata ko dai su kaɗai ne suka maida zumuncin ba komai ba? Sai yanzu ta gane abinda mahaifiyarta ta rubuta a littafin da Baaba ya bata,dama ƙiyayyar da dangin ta suke yi mata har ta kai su ƙi ƙarɓar ƴaƴanta da ta haifa? Lallai duniya abun tsoro ce. Muryar Mubarak da Afrah dake guje-guje a cikin ɗakinta suna wasa ne ta dawo da ita daga duniyar tinanin da ta faɗa,a hankali ta sa soso tana cuɗa jikinta har ta gama wankan ta ɗauraye jikinta ta yi alwala,tana fitowa ta ga duhu ya yi alamu ne na magariba ta kawo jiki. Kaya ta sanya ta rama sallolin da ke kanta sannan ta je parlour ta zauna a kusa da Afrah,kwantar da kanta ta yi a cinyarta tare da ƙurawa TV ido. Hawaye na zuba,cikin baƙin ciki Afrah ta ce. "Look Lamyah kukan ya isa haka,kar ki hasala ni na bi dare na koma na shaƙe matar mutane,tashi Yanzu Mama Tani za ta kawo abinci ki ci. Ina so ki manta da komai da ya faru a wancan gidan,wata makaranta ce kika shiga wadda kika koyo darasi a cikinta, In Shaa Allahu ko da su ko babu su za ki ga Abii watarana har ya aura maki masoyin ki Aminullahi." Murmushi Lamyah ta yi ta sake rungume ƙugun Afrah da ke magana kamar wata uwarta,cikin ranta take maimaita kalmar. 'Masoyin ki Aminullahi,anya kuwa ina wani son Yah Amee kuwa a yanzu? Da an ambaci kalmar so fuskar Handsome nake gani a idanuna,ta ya zan iya rayuwa da Yah Amee a yanzu bayan zuciyata na son wani?.' Mama Tani ce ta yi sallama cike da jimami ta gaishe da Lamyah,cikin sauri Lamyah ta tashi zaune ta gaishe da Tani,sannan ta karɓi abincin da ke hannunta ta ajiye a table ɗin gabanta,Tani ce ta ce. "Afrah ta faɗa min ba a dace ba da abinda kuka je nema,to Ubangiji Allah ya sauƙaƙa dikkan lamura,Allah Ya bayyana maki Abiin naki cikin aminci,rayuwa yanzu ta zamo abun tsoro,naka shi ke bayar da kai,bare sai ya so ka ya zauna da kai lafiya,amma akan abu ƙalilan sai hassada da ƙyashi ya raba ka da naka." Gyaɗa kai Lamyah ta yi sannan ta ce. "Maganar ki gaskiya ne Mama Tani,lallai zumunci yanzu ba dole sai da ɗan'uwa na jini bama yinsa ake yi,domin yanzu ni bani da kowa sai ku,ku ne y'an'uwana,ku ne dangi na." Ƙwallar dake barazanar gangarowa Afrah ta yi saurin sharewa ta ce. "Kin san Allah kika sani kuka sai na yi maganin ki,ko na cicciɓe ki nida Bala mu mayar dake wajen surukar ki Innoh." Dariya sosai Lamyah ta yi,ta ja abinci gabanta ta fara bawa Afrah labarin zamanta a gidan,da yanda ta sha wahala lokacin da kashi ya matse ta,dariya suka dinga yi sosai kamar babu abinda ke damun su. Cikin kwana biyar da dawowar su Lamyah Mubarak ya maida jikinsa,walwalarsa da kuzarinsa suka dawo,nan take Lamyah ta hau danasanin ƙin dawowa gida a lokacin da yaron ya dinga ce mata su dawo,hamdala ta yi da Allah ya kuɓutar da su suka dawo gida. A kwana na shida da dawowar su ne Faisal ya gaji da rana da lokacin da Afrah ke saka masa za ta je wajen rawa bata zuwa,sa ga shi ya yi tattaki ya zo har gida ya same ta,bai bar gidan ba sai da ta yi masa alƙawari fara zuwa washegari. ***************** Layuzah bata bar Aminullahi ya sarara ba sai da suka yi sati ɗaya cur suna murzar amarcin su da tsinke,a cikin sati ɗaya da auren ta ta yi kumari ta yi kyau sosai,hasken fatar ta ya sake fita tar,duk da cewa Aminullahi na jin takaicin yanda ya same ta amma yana jin daɗin yanda a kullum take nuna masa tsananin so da ƙauna,bata son ɓacin ransa ko kaɗan. Yau da gobe suna tare ya gane Layuzah babbar ƙazama ce,kuma bata yin sallah, shi yasa a koda yaushe kafin ya fita sallah masallaci sai ya sanya ta yin alwala ya ga ta tada sallah sannan ya ke barin gidan, duk da ƙoƙarin da yake yi bai hana yana barin gidan Layuzah ta yi wurgi da hijabinta ta haye gado ko kujera ta ɗauki wayarta ta na chatting ko kallo. Yau tin safe Layuzah ke girki saboda Aminullahi ya ce mata za su je gaishe da iyayen su,daga gidan Hajiyarta za su wuce gidan Momma,ita kuma ta ce tana so su fara zuwa gidan Momma daga can ya kai ta gidan Hajiya,idan suka gaisa sai ya baro ta a can da dare ya koma ya ɗakkota,ba dan ya so ba dole ya haƙura da abinda ta ce,dan kuwa wata iriyar shakkar ta yake ji ba ya iya tsallake umarnin ta. Layuzah na kammala girkin ta ta faɗa wanka,sai da ta sille jikinta tass sannan ta fito ta shirya cikin wani baƙin material mai korayen fulawa da fari a jiki,koren mayafi da takalmi da jaka ta ɗauka gidan kaca-kaca suka fita ɗauke da manyan kulolin abinci guda biyu. A bayan mota Aminullahi ya ajiye su tana tsaye tana gyara zaman mayafinta a kafaɗarta,gaba ɗaya shi bai taɓa zaton zai bar matarsa ta sunna ta fita da irin wannan shara-sharan mayafin ba,sai gashi Layuzah har da fito da jelar gashin kanta wuyanta duk a waje ta bayyana sarƙar da ta saka,ga kuma hannayenta a waje,cike da takaici ya buɗe mata motar ta shige ya zauna a mazaunin direba ya ja suka tafi. Suna isa mai gadi ya bude musu gate suka shiga gidan,masu aikin gidan sai suka taso suna washe baki tare da tsokanar Aminullahi,murmushi ya dinga sakar musu yana miƙa musu hannu suna gaisawa,yana gama gaisawa da su ya zagaya ya buɗe wa gimbiyar mota ta fito tana ta zabga ƙamshin da Aminullahi ya ji kamar ya maida ta cikin motar ya rufe. Ita kuwa Layuzah bata san ma yana yi ba ta juya baya ta buɗe mota ta ɗauki kular da ta zubowa Momma abinci a ciki,ta kira Zahrah da ke ta washe baki ta miƙa mata,cike da fara'a Zahrah ta ce. "Shegiya Layuzah kin ga yanda kika koma kuwa? Kaiii gaskiya na yi miki murna." Wani irin mugun kallo Layuzah ta watsawa Zahrah sannan ta ce. "Don Allah matsa na wuce ni rana na duka na,idan ke baki da abun yi ni ina da shi." Har ta fara taku ɗaya zuwa biyu ta dawo baya ta kalli Zahrah da wani mayaudarin murmushi,sannan ta ce. "Ahh na manta fa,ta yaya hadimar gida za ta rasa aikin yi? Maza biyo ni da kular na kai wa surukata abinci tin kafin ya huce." Wasu irin zafafan hawayen baƙin ciki ne suka fara wanke fuskar Zahrah,mamaki da tsoron ɗan Adam ne ya cika zuciyarta,Layuzahn da ta nemi ƙawancen ta da ƙyar da siɗin goshi ce ke wulaƙanta ta saboda ta samu biyan buƙatar ta,lallai lamarin ɗan Adam akwai mamaki a cikin sa. Haka ta bi bayan Layuzah kamar kazar da ƙwai ya fashewa a mahaifa,suna shiga Zahrah ta ajiye abincin a saman center table za ta fita,cike da gadara Layuzah ta ce. "Ke ! Anan na ce ki ajiye? Dalla malama kawo nan." Jiki babu ƙwari Zahrah ta ajiye a inda Layuzah ke zaune,tsaki Layuzah ta yi sannan ta ce. "Ɓace min da gani,banda warin dauɗa babu abinda ke tashi a jikin ki." Murmushin takaici Zahrah ta yi sannan ta share hawayenta ta bar parlourn,Iya dake zaune a can gefen kujerar da za ta sada ta da ɗakinta tana lazumi ce ta yi murmushi tare da gyaɗa kai,shafa addu'ar da ta gama ta yi sannan ta miƙe tsaye,a tsorace Layuzah ta kalli inda Iya ta miƙe ta hau in-ina ta na gaishe da Iyan,ba tare da Iya ta amsa gaisuwarta ba ta girgiza kai ta wuce ɗakinta da ke parlourn farko na cikin gidan. Aminullahi ne ya shigo bayan ya gama gaisawa da ma'aikatan gidan nasu,zaune ya tarar da ita ita kaɗai a parlourn,zama ya yi sannan ya ce. "Ah ah,ya na gan ki ke kaɗai anan baki ƙarasa wajen Momma ba? Ina Iya?" Langwaɓe kai ta yi sannan ta matsa jikinsa kamar za ta shige cikinsa ta ce. "Na gaisheta yanzu da ta tashi a can,amma sai ta yi min tsaki ta shige ɗaki,ban san me na yi mata ba daga zuwa na yanzu har na cancanci haka a wajenta." Murmushi kawai Aminullahi ya saki,dan kuwa ya tabbata Iya na nan akan bakanta na tsanar Layuzah,wanda tin a daren su na farko ya gano dalilinta na ƙin Layuzan,hasashe ta yi akan yarinyar kuma shi ya tabbatar da abinda Iyan ke tsoro,dan haka bai ce komai ba ya miƙe ya leƙa ɗakin Iyar,sai da suka gaisa sannan ya fito,babu jimawa Iya ta wuce sashen Momma ta sanar da ita zuwan su Aminullahin,cike da fara'a da farinciki ta ce su shiga. Kafin Iya ta fito Aminullahi ya ɗauki kular abincin da suka zo da shi ya kama hannun Layuzah da ta maƙale masa kamar za a ƙwace shi suka shiga parlourn Momma,Momma tashi ta yi zaune ta na yi musu lale maraba. Cike da ladabi Layuzah ta zare hannunta daga na Aminullahi ta isa gabanta ta durƙusa ta hau gaisheta,amsawa Momma ta yi cike da fara'a,sannan ta ce. "Sai yau nake ganin idanun ku? Ina nan ina zuba ido na ga ango da amarya amma shiru." Sunne kai Layuzah ta yi kamar ta Allah,cikin jin kunya ta ce. "Ba laifi na bane Momma,baby ne ya hana mu fita ya ce sai na yi sati ɗaya ina hutawa kafin na leƙa ko ina,kuma da yake ban ɗan ji daɗi ba ne a washegarin bikin shi yasa...." Jin yanda ta taƙarƙare tana zuba ƙarya ne ya sanya Aminullahi saurin cewa. "Ina Abii? Ko ya fita ne?" "Abiiin ku ya tafi Nigeria ai,tinda ya kira layin ka ya ji an kashe kiran sau biyu ya ce to bari shi ya je kan kasuwancin kar a bar wajen babu mai kulawa da komai,gashi yana saka ran za a yi baƙi a wannan satin da zai gana da su." Shafa fuskarsa ya yi cike da takaici,domin kuwa ya san babu mai kashe kiran Abii sai Layuzah,ganin halin da ya shiga ne ya sanya Layuzah ɗaukan kular gabansa ta ce. "Momma ga alkaki na yi miki da kaina,dan na san idan kika ci za ki so kullum na dinga yowa ina kawo miki." "Ah ah ahhh ai kuwa na gode sosai Allah Ya miki albarka." Karɓar kular Momma ta yi ta buɗe ta ɗauki alkakin ta fara ci, daɗin da ya yi mata ne ya sanya ta lumshe ido,cike da farin ciki Layuzah ta dinga kwarzanta kanta akan yanda ta iya girki da sauran abubuwan da mata da yawa basu iya ba,shi dai Amunullahi jinta kawai yake yi,dan kuwa ya san banda alkaki da dubulan da cincin babu abinda Layuzah ke dafawa ya yi ma'ana,suma kuma dan sana'ar mahaifiyarta ne shi yasa ta ƙware,to sai kuma ƙwai da indomie idan ta dafa suna daɗi. Sai da aka yi la'asar sannan Aminullahi ya kai Layuzah gidan su,har parlour ya shiga suka gaisa da Hajiya,da zai tafi ya kawo dubu goma ya bata,godiya ta dinga zabga masa kamar za ta kwanta a ƙasa,sai da Layuzah ta raka sa har mota ta ɓata lokaci wajen sumbatarsa da nunawa mutanen unguwarsu kalar soyayyar da take yi da mijin nata sannan ta baro motar ta koma gida. Aminullahi na barin unguwar su Layuzah,suma suka shirya

Chapter 15 of 30