Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
buɗe ɗakin ta ajiye wa Lamyah kayanta sannan ta duba ta ga komai a share yake a tsabtace,dan kullum sai an share an gyara saboda kar a yi baƙi a ji kunya. Innoh kuwa bata saki ranta a gaban kishiyoyin nata ba sai da suka shiga ɗaki da ɗan nata ta saki rai ta hau yi masa lale maraba. Innoh ita ce uwar gidan Mai Unguwa suna da yara biyar da shi,huɗu mata sai namiji ɗaya wato Musaddiƙ,Asabe ita ke bi mata,tana da yara shida dika mata,kuma sun aurar da su suma,sai kuma Larai ita ce mace ta uku a wajen Mai Unguwa tana da yara biyu mata wanda suma an yi musu aure,dan kuwa Mai Unguwa na ganin yarinya ta yi jinin al'ada ɗaya a gidansa to kuwa a gidan mijinta za ta yi na biyun,duk da cewa yana sanya yaransa mata yin ilimin addini da boko amma fa a gidan miji duk suka zama abinda suka zama a yanzu,dan kuwa a cikin yaransa mata yana da ma'aikatan lafiya har da malaman makaranta,wanda dika mazan su ne suka ɗauki nauyin ilimin nasu har suka zama abinda suka zama,Musaddiƙ kuwa El-mustapha na daga cikin mutanen da suka taimaka masa wajen kammala karatunsa dan kuwa da kuɗin da ya bayar a biya wa yara makaranta da shi shima aka biya masa har ya kammala. Innoh ƙawar Delu ce ƙut da ƙut,halayyar su ɗaya ta fannin kishi,bayan wannan kuma idan mutum ya zauna da Innoh ba tare da ya zaƙe wajen nuna mata ya fita son miji ko ɗanta ba to za ku zauna lafiya da ita har ka yi tinanin ma bata da wata matsala. Abinci Innoh ta gabatarwa da Musaddiƙ wanda yake ta bata labarai akan wajen da ya gama bautar ƙasa,ita kuwa sai farin ciki take yi tana jin daɗi kamar a ranar ta fara ganin an kammala bautar ƙasa a gidan. Innoh na kammala ajiye masa soyayyar zabuwar da ta kiwata da kanta da kyau dan zuwan wannan ranar sai ta buɗe masa shinkafa da miya da salad ɗin da aka yankawa kayan miya akai da dafaffen ƙwai guda biyar,miyar kuwa nama ne zuƙu-zuƙu da zoɓo mai sanyi sai pure water a faranti mai sanyi. Murmushi Musaddiƙ ya yi na jin daɗi sannan ya hau zuba wa mahaifiyar tasa godiya,cikin fara'a ya ce. "Tinda abincin da yawa bari na ɗakko kwano na ɗebarwa baƙuwar can,dan da ganin ta kin san ƴar gayu ce irin cimar nan take ci." Fara'ar da ke saman fuskar Innoh ce ta ɗauke cikin ƙanƙanin lokaci ta kalli Musaddiƙ ta ce. "To uban iya,ko uban ka ban ɗebawa ba balle wata baƙuwa,idan za ka ci ka ci,idan ba za ka ci ba bar min wahala ta zan ci." Cikin sauri Musaddiƙ ya hau bata haƙuri tare da sauka ƙasa ya fara kwasar garar da mahaifyarsa ta haɗa masa,zuciyarsa na hango masa wannan abinci Lamyah ya kamata a kai wa ba shi ba. Tinda Asabe ta fita ta bar Lamyah da Mubarak a ɗaki,Lamyah ta ke kallon ɗakin,tabbas babu ƙazanta amma kayan cikinsa sun tsufa,ƙyanƙyamin zama take yi a wajen balle har ta kwanta,ji ta yi kamar ta kira Bala ya dawo ya maida su gida,tinda dangin Mahaifiyarta sun ƙi karɓarta to me ya rage mata da za ta zauna ta yi anan ɗin? Wata zuciyar ce ta ce mata 'Zaman jiran Yah Amee ɗin ki da Abii'  Hawayen da take ta riƙe wa ne suka zubo mata,cikin sanyin jiki ta goge su ta kwantar da akwatinta ta zauna a kai tare da rungume Mubarak a jikinta. A haka Asabe ta shiga hannunta ɗauke da plate mai kyau ta zuba shinkafa da wake da lettuce da aka yanka wa tumatur da albasa,sai dafaffen ƙwai guda ɗaya da aka yayyanka,ajiye mata ta yi sannan ta ce. "Ki saki jikin ki sosai nan duk gida ne,bari na kawo miki ruwan sha." Shirun da Lamyah ta yi ne ya sa Asabe jin cewa Lamyah fa bata jin hausa,dan dama bata yi mata kama da mutanen Nigeria ba,ta fi yi mata kama da buzayen Niger ɗin nan da basu cika haske ba. Fita ta yi daga ɗakin ta na maganganu akan tabbas Lamyah bata jin hausa. Nan suka haɗu da Larai suka dinga jinjina lamarin,tare da tinanin yanda zaman nasu zai kasance da yarinyar da ko sunanta ba su sani ba. Mai unguwa bai shigo gida ba sai da suka dinga gwada layin Mus'ab da na Aminullahi ba su samu ba,cike da damuwa suka yanke shawarar Lamyah ta zauna a gidan Mai Unguwa har lokacin da Allah zai sa su samu layin su Mus'ab da Aminullahi idan yaso sai su sada su da mutanen da za su riƙe su a madadin iyayen nasu da suka ƙi su. A bangaren Aminullahi kuwa,ya kasa samun natsuwar zuciya akan ingiza mai kantun da zuciyarsa ke yi masa akan Lamyah,yana jin kamar ya biye wa zuciya da shaiɗan tare da zugar Faisal akan ya nemi Lamyah kawai tinda ƳAR RAWA ce,idan ya so daga baya sai ya tuba zuwa ga Allah tinda dama ai kowanne ɗan Adam yana aikata saɓo. Ganin zuciyarsa na neman ta rinjaye sa ya aikata saɓon Allah ne ya sanya shi shiryawa ba tare da ya yi shawara da kowa ba ya bar Nigeria gaba ɗaya ya koma gida Nijer............ [9/11, 10:50 AM] zee hussain: ƳAR RAWA. RUBUTAWA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✍️✨ PAGE 23. Cike da murna tare da maɗaukakin farin ciki Momma ta tarbi Aminullahi. Iya kuwa tarewa ta yi a parlour ta na zuba masa abinci ta na yi masa hira,a haka Abii ya dawo ya same su. Sai da ya zauna suka ɗan taɓa hira tare da jajanta rashin kiran da basu samu ba daga Rijiyar Lemo har tsawon wannan lokacin,sannan ya shiga ɗaki ya watsa ruwa. Sallamar nutsattsiyar budurwa kuma kyakkyawar yarinyar da ba za ta wuce shekaru ashirin da uku ba ce ta katse hirar Aminullahi da Iya,cike da fara'a Momma ta kalli Layuza da ke sunne kai hannunta riƙe da wani babban kwano. Cikin ladabi Layuza ta durƙusa har ƙasa ta ce. "Barka da hutawa Momma,na same ku lafiya? Barka da yamma Iya." A gwasale Iya ta amsa gaisuwar tana me maida hankalinta kan Aminullahi,wanda ko ɗaga kai bai yi ba, ballantana ya kalli matashiyar yarinyar. Cikin fara'a Momma ta ce. "Lafiya ƙalau Layuza,ya Hajiya da jiki? Ina ta waƙen zan je asibitin na duba ta gashi har an bata sallama ta dawo ban je ba,idan kin koma ki bata haƙuri In Shaa Allahu zuwa dare dai yau zan shigo na duba jikin nata." "Allah sarki,ai ta ji sauƙi ma,sai ɗan abinda ba a rasa ba,ita ce ma ta aiko ni ta ce na kawo wa Yah Aminu wannan." Yatsina baki Iya ta yi kafin ta ce. "Ta aiko ki ko dai kika kawo masa? Har yaushe ya shigo ƙasar ma da jama'ar gari za su san ya dawo?" Momma ce ta yi saurin cewa. "Allah sarki Aminu yana godiya,gashi can je ki ki kai masa da kan ki." Dariya Momma ta gimtse ganin yanda Iya ke bankawa ƴar mutane harara tare da ƴan surutai,cikin wata iriyar murya dake bayyanar da rashin son yarinyar Iya ta ce. "Yaran yanzu na da abun mamaki, ƙirƙiri yarinya sai ta fito tana bayyana wa namiji ƙauna,dauri/da mu duk ba a haka,Allah dai ya kyauta." Layuza kuwa ko kallon Iya bata yi ba har ta isa gaban Aminullahi ta ajiye masa kwanon da ta kawo masa alkakin da ya sha zuma,ido ta kafe shi da shi har sai da ya ji alamar ana kallon sa,sannan ta maƙale siririyar muryarta ta gaishe sa,a hankali ya ɗaga kansa daga plate ɗin da yake cin abinci ya ce. "Lafiya ƙalau Layuzah Ya Hajiya? Idan kin je ki gaishe min da ita ki ce na gode." Wani irin farin ciki ne ya mamaye zuciyar Layuza,ji ta yi kamar ta yi tsalle ta maƙale masa wuya ko da kuwa za su faɗi ƙasa ba za ta damu ba,duk duniya babu wanda ya iya kiran sunan ta sama da Aminullahi,ko iyayen da suka sanya mata sunan dole su bashi lambar yabo dan ya fisu iya kiran sunan. Cike da ladabi ta zaro wani plate ɗin a gefen sa ta saka cokali ta zuba masa guda uku sannan ta miƙe tare da faɗin. "Na tafi Momma sai anjima,Yah Aminu ka huta gajiyar hanya." Ko kallon gefen da Iya da ta banka tsaki take bata kalla ba,ta wuce ta bar parlourn zuciyarta fes,domin kuwa ta tabbata Aminunta ba zai sake barin ƙasar nan ba ba tare da igiyar auren sa akanta ba. Tana fita Momma ta fashe da dariyar da take ƙunshewa,Iya kuwa sabon tsaki ta ja sannan ta ce. "Kin san Allah Hajiya? Ke ce ki ke saka yarinyar nan wannan tsalle-tsallen ya jinjirar Barewa, yanzu fisabillahi kun manta da alƙawarin auren Lamyah da Aminullahi ne? Me yasa ki ke sakar mata fuska tana shige masa? Wannan karon har da samun ƙwarin guiwar shigowa har parlourn ki ta kawo masa abinci? Ni ban ma yarda da alkakin sharrin nan b, kai Aminullahi kul ka ci alkakin nan." Dariya Momma da Aminullahi kawai suke zubawa,sun rasa dalilin da ya sa Iya ta tsani yarinyar da yawa. Layuza yarinyar maƙotan su ce wadda take makaranta a can Unguwar kakanninta na Uba,sai dai takan shigo wajen mahaifiyarta a duk sanda ta samu hutu,mahaifinta ya jima da rasuwa tin tana yarinya,mahaifiyarta bata sake wani auren ba,ita kaɗai take kula da Layuzah sai taimakon da take samu daga danginta da na mahaifin yarinyar. Mutane da dama na yaba wa da tarbiyyar yarinyar,sai dai abinda basu sani ba shine,makira ce ta ƙarshe sannan bata da kamun kai ko kaɗan,tsananin makirci da iya takunta ne ya sa mutanen unguwarsu basu san halayyarta da take ɓoye wa ba,duba da cewa gida biyu gare ta. Layuza ta jaraftu da son Aminullahi ne tin watarana da ta dawo daga gidan kakarta,a ranar shi kuma Aminullahi ya sha wanka zai tafi Nigeria driver na tuƙa shi zai kai shi airport,idanuwansu ne suka sarƙafe a cikin na junan su,babu jimawa Aminullahi ya ɗauke kansa ya zaro wayarsa ya na latsawa har suka bar wajen,ita kuwa Layuzah tana nan tsaye kamar wadda aka dasa a wajen tana bin bayan motar da kallo,tin daga wannan ranar ta tsiri dawowa gida hutun ƙarshen mako ko zata sake ganin sa,daga nan ne kuma ta fara shiga gidan,duk da cewa ta jima sosai kafin masu aiki su fara barinta shiga har cikin gidan,Layuzah bata taɓa wuce parlourn baƙi ba a gidan sai yau da ta samu labarin dawowar Aminullahi ta wajen ƙawar da ta samarwa kanta a cikin masu aikin gidan saboda irin wannan ranar,tana yi mata waya ta sanar da ita dawowar Aminullahi sai ta ɗebi alkakin da mahaifiyarta ke siyarwa ta cika kwano da shi ta zabga masa zuma,sannan ta zuba maganin da suka jima da karɓowa daga wajen wani boka,sai kuma ta sanya kwallin da ya bata wanda ya ce in dai ta haɗa ido da wanda take so to fa da kansa zai kawo kansa ya ce yana son auren ta. Wannan abu da ta aikata ne ya sanya ta shiga cikin matsanancin farin ciki,bata bar gidan ba har sai da ta zagaya wajen masu aikin gidan ta bawa ƙawarta zahrah kuɗin da ya rage mata gaba ɗaya kyauta,cike da maɗaukakin farinciki ta isa gida. Ko da ta shiga gidan sai ta samu Mahaifiyarta na zaune ta na shafa man zafi a ƙafarta,rungumeta ta yi sannan ta ce. "Ummah yau buri na ya cika,na kammala aikin da Malam ya ce na yi,na tabbata nan ba da jimawa ba za ki ji an kawo kuɗin aure na daga gidan Alhaji Mus'ab." Washe baki Mahaifiyarta ta yi sannan ta ce. "Da gaske kike Layuzah? Alhamdulillah Allah ka nuna min wannan rana da raina da lafiya ta,zan so ki shiga wannan gida mai tarin dukiya Layuzah ko talauci ya yaye mana,tinda mahaifin ki ya rasu muka shiga ƙangin takauci har yau bamu fito daga cikinsa ba,na tabbata auren Aminullahi shi ne warakar talaucin mu." "Ai Mommarsa ma ta ce za ta shigo anjima ta gaishe ki da jiki,kin ga idan hakan ta faru ai alamu ne na nasara,matar da bata hulɗa da mutane kullum tana kime a gida a kujera?." "Au haba ita ta ce maki za ta zo da kanta?" "Ƙwarai da gaske Ummah ita ce za ta shigo duba ki da kanta." "Maza to tashi ki sake gyara waje a saka turaren wuta, nima bari na shiga wanka,da dai na ce ba ruwan da zan watsa amma ya zama dole na gyara gudun kar ta tarar da ni cikin dauɗa." Dariya Layuzah ta yi kafin ta ce. "Ummah kina bani dariya wajen rashin son wanka,sai kace wata akuya." Duka mahaifyarta ta kai mata tare da lafta mata wani bahagon ashar,cike da farinciki Layuzah ta tashi ta hau gyaran gidan tana fatan kar Momma ta saɓa alƙawari. A can ɓangaren Aminullahi kuwa sai da ya cinye alkakin plate ɗin nan tas har ya ƙara sannan ya rufe saura ya ce a ajiye masa,idan ya dawo daga masallaci zai cinye abunsa. Iya ce ta kyaɓe baki sannan ta ce. "Dama waye ya yi maka kama da wanda zai ci wannan baƙin abun? Da ka ce kana so duk da yanzu bana shiga kitchen ai da da kaina zan shiga na yi maka." Momma ce ta ce. "Iyar Aminullahi,ko dai kishi kike yi da Layuzah ne? Dan Allah kar ki zama daga cikin iyaye masu kishi da surukan su,abun ba zai muku daɗi ba ke da ƴar taki,kin san yaran zamani basu da kunya,sai ku kwashi ƴan kallo." Iya ce ta kalli Momma da fuskar da ke nuna gaskiyar maganar da za ta fito daga bakinta ta ce. "Wai Hajiya kina nufin za ki bar Aminullahi ya auri wannan yarinyar da ke da ruwan munafukai?" Momma ce ta rage fara'ar fuskarta kafin ta ce. "Idan har matarsa ce Iya mu bamu isa mu hana ba,na ga take taken yarinyar tin lokacin da ta maƙalewa abota da Zahrah,bata huta ba har sai da ta samu shaƙuwa da ni,idan kuwa kika ga kare na sunsunar takalmi to fa ɗauka zai yi,duk wulaƙanci da shariyar da Aminullahi ke yi mata bata fasa zuwa ba,dan haka mu yi addu'ar Allah Ya zaɓa abinda ya fi zama alkhairi kawai,tinda ɗan naki girma yake yi tin kafin ya zama tuzuru ya kamata a aurar da shi." "Ita kuma Lamyah fa?" Wannan karon Aminullahi ne ya bawa Iya amsa,cikin ladabi da kulawa ya ce. "Iyata kar ki damu,ko yanzu Lamyah ta bayyana ba zan ƙara awa guda ba a duniya face na aure ta,amma kafin nan zan iya daurewa na karɓi soyayyar yarinyar nan da ta jima tana nuna min ina kauda kai,ke da kan ki kike hana ni wulaƙanta mutane musamman matan da ke nuna min ƙauna,yau me ya faru kike kyara da tsangwamar Layuzah?" Ƙwalla ce ta taru a idanun Iya,ta kasa cewa komai saboda bata son ta yi kuka akan abinda bata da ikon hanawa,amma ita dai haka nan ta ji bata son Layuzah,da ace ma wata Aminun nata zai aura ba Layuzah ba to da ta taya shi murna,su kuma ci gaba da tsananta addu'a har Lamyahn su ta bayyana a gare su,ganin cewa Iya ta shiga damuwa sosai ne ya sanya Momma miƙewa ta ce. "Bari na je na duba Abiin ka,na san yanzu ya kammala cin abinci.Iya a ci gaba da taya shi addu'a kawai,duk abinda yake alkhairi ne Allah ya zaɓa mana shi,kar ki manta da faɗin bahaushe da ya ce,matar mutum kabarinsa,wataƙila a zo a haifa maki jikokin da za ki yi ta murna har ki manta da ƙin da kike yi wa mahaifiyarsu. Ki shirya anjima ki raka ni mu gaishe da mahaifiyarta da bata da lafiya.". "To Allah Ya tabbatar mana da alkhairi Hajiya,ni dai ki gafarce ni ba zani wata dubiya ba,shi uban gayyar ya raka ki,ya gaida surukar tasa." Dariya kawai Momma ta yi ta wuce ɗaki ta bar Aminullahi na tsokanar Iya har sai da fara'ar fuskar ta ta dawo. Da dare bayan an yi sallar isha'i Momma ta tasa Aminullahi suka shiga gidan su Layuzah,babban gida ne wanda da ka gan shi za ka tabbatar da a baya gidan masu hannu da shuni ne,sai dai babu da talaicin da ta yi musu katutu a yanzu ne ya sauya gidan gaba ɗaya sauyawa. Bakunan su ɗauke da sallama suka shiga gidan,a zaune suka tarar da Layuzah a saman sallaya tana ta addu'a Allah ya sa Momma ta zo kar ta fasa zuwa,sai kuma gashi bayan Momma ma har da Aminullahin suka zo,ji ta yi kamar ta ƙwalla ƙara dan farin ciki,kanta a ƙasa ta ɗaga hannu ta yi hamdala a ranta ta shafa kamar wadda ta yi addu'a sannan ta naɗe abun sallar ta tsugunna har ƙasa ta gaida Momma da Aminullahi,Hajiya ce ta fito daga ɗaki sanye da Hijabi hannunta riƙe da carbi ta samu waje ta zauna a kujera ta na ɗingisa ƙafa,Momma ma waje ta samu ta kime a kujera,gefenta kuma Aminullahi ne ya zauna. Bayan gaishe-gaishe da suka gudanar a tsakanin su ne sai Momma ta ce. "Yau dai Allah ya nufa gani na shigo mun gaisa,kullum ina samun labarin rashin lafiyar da kike fama da shi wajen mutanen unguwa idan sun shiga da kuma Layuzah,ina ta waƙen zuwa ban samu na fita ba sai yau." "Allah sarki,babu komai Hajiya,abun ne ai da yawa,mutane wannan ya shiga wancan ya fita baku da lokaci dole a yi muku uziri." "Haka ne,Allah to Ya baki lafiya Ya sa kaffara." "Amin Ya Allah Hajiya na gode." Aminullahi ma addu'a ya yi mata,lokaci zuwa lokaci ya na kallon hanyar da Layuzah ta bi ta shige tin bayan da ta gaishe su. Suna gab da tashi za su tafi ne ta shiga hannunta ɗauke da faranti da kofuna tare da babban jug a kai,ajiye wa ta yi a gaban su sannan ta durƙusa tana tsiyaya masu zoɓon da ta haɗa shi da kanta. Murmushi Momma ta yi sannan ta sanya mata albarka,Aminullahi ne ya fara miƙe wa tsaye ya fita ba tare da ya sha zoɓon ba,Momma ma tashi ta yi tana godiya tare da yiwa Hajiya addu'ar samun sauƙi,a haka suka tafi gida Layuzah na yi musu rakiya har bakin ƙofa. Tin daga wannan rana idan Layuzah ta je gidan su Aminullahi take neman dalilin da za su haɗu da shi,har sai da aka yi sati biyu Layuzah na manne wa Aminullahi kafin ta fito fili ta bayyana masa yanda take ƙaunarsa,ba tare da ya amsa mata ba ya miƙe ya bar parlourn ya shige ɗakin sa. Da an ambaci kalmar so idanun Lailah ƳAR RAWA su ne suke giftawa a zuciyarsa,hasashen kyawun jikinta da lallausar fatar hannunta da ya damƙe dan ya sanya ta a mota na tada masa da wata iriyar fitina a tare da shi,lokuta da dama baya iya bacci da dare sai ya haɗa da sallar dare da addu'a akan halin da yake shiga idan ya tina ta. A yanzu ya tabbatarwa da kansa auren Layuzah shi kaɗai ne zai yi masa maganin halin da yake ciki,idan yaso daga baya duk sanda LAMYAH ta bayyana a gare su sai ya auri amanarsa,wataƙila idan ya samu mai ɗebe masa kewa zai rage tinanin Lailah ƳAR RAWA. A ɓangaren Lamyah kuwa da ƙyar ta iya amfani da banɗakin gargajiya ta yi fitsari, dan kuwa bata taɓa ganin shaddar ƙasa ba sai a ranar da ta shiga banɗaki dan biyan buƙatar bahaya da ya kama ta,rasa inda za ta yi bahaya ta yi sai ta dinga zarya tsakanin banɗakin da cikin ɗakin da aka sauke ta. Babu wanda ya gano halin da take ciki,dan haka sai ta koma ɗakin nasu ta kwanta kamar mara lafiya,Mubarak ma tinda suka je sai dai ta saka masa pampas idan ya yi lalurarsa ta cire ta wanke masa,ko banɗakin bata bari ya leƙa ba ballantana ya san ya yake. Duk halin da Lamyah ke ciki Musaddiƙ na kula da ita,sai dai nauyi yake ji ya je ya same ta ya yi mata bayanin yanda za ta sauke lalurar ta,dan haka sai ya leƙa ɗakin Innoh ya zauna,hira suka fara yi sama-sama har ya ji kamar ya sanar da ita halin da Lamyah ke ciki,tsoron faɗan da za ta dasa masa ne ya sanya shi yin gum da bakinsa, hankalinsa gaba ɗaya ya tattare sa zuwa wajen Lamyah da ke kwance a ɗaki tana ta murƙususu tare da yarfe zufar wahala,jin kashin ya sake matso ta ne ya sanya ta miƙe wa ta fito waje fuskarta sharkaf da gumi idanuwanta sun yi jawur alamar ta ci kuka ta gode Allah,hanyar banɗaki ta nufa sai Musaddiƙ ya yi wuf ya fito waje,haɗa ido suka yi da Lamyah sai ya ji nauyi da kunyarta sun hana shi bayyana mata yanda za ta yi amfani da banɗakin,cikin sauri ya bar wajen ya wuce ɗakin sa. Ita kuwa Innoh wani irin baƙin ciki da kishin ɗan nata ne ya dirar mata a zuciya,a hankali ta furta. "Me hakan yake nufi? Kar dai Musaddiƙ ɗina ya kamu da soyayyar wannan nunar ranar? Kan uban can kayyasa,lallai kuwa ranar barin ki gidan nan ta gabato balarabiya."......... [9/11, 10:50 AM] zee hussain: ƳAR RAWA. RUBUTAWA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✍️✨ PAGE 24. Har bayan magariba Lamyah na nan na fama da shige da ficen neman inda za ta sauke lalurarta,zuciyarta ta gama yanke mata hukuncin idan ƙafa ta ɗauke ta samu pampas ɗin Mubarak ta yi a ciki sai ta yar a shara kamar yanda take yi masa. Da wannan dabarar ta dinga addu'ar Allah Ya sa kowa ya shiga cikin ɗaki da wuri. Tana jin dawowar Mai Unguwa amma bata fita gaishe shi ba saboda yanda take jin ta a matse,gani take yi da ta fita tusa ko kashin ma kansa zai iya ƙwace mata a gaban sa. Duk wanda ya san Lamyah kwanaki bakwai da suka gabata ya ganta a yanzu zai tabbatar da mummunan sauyin da fuskarta ta samu,ta faɗa sosai ta yi duhu idanunta duk sun zurma ciki. A yau balarabiya Lamyah ta fassara barin kashi a ciki baya maganin yunwa da azabar da take sha,sam wajen zaman kashi ba ciki bane,dole a fitar da shi sannan a ci wani abincin,ita kuwa saboda rashin fitar da nata ya jawo mata rashin cin abinci. Lokuta da dama yanda aka kawo mata shi,haka take fitarwa,Asabe ta ɗauka rashin sabo da cimar su ne ya jawo hakan,tinda Mai Unguwa ya warware musu komai sun san ita ɗin wacece. Da misalin ƙarfe goma na dare ƙafa ta ɗauke kamar yanda Lamyah ta yi ta fata,cikin sanɗa da tafiya a hankali saboda rashin kuzari da tsoron abinda zai je ya zo Lamyah ta fito,buta ta ɗauka ta sake cika wa da ruwa ta juya dan ta nufi banɗaki,hannunta riƙe da pampas guda biyu. Tana juyawa ta yi karo da Musaddiƙ dake tsaye yana jiran fitowar ta dan ya yi mata bayanin yanda ake amfani da banɗakin nasu. Tsananin tsoron da Lamya ta ji ne ya yi sanadiyyar ƙwacewar wata muguwar tusa mara ƙara mai bala'in wari,dan kuwa da fitar tusar wari ya gauraye wajen gaba ɗaya,cikin sauri Musaddiƙ ya toshe hancinsa ya na sake haska Lamyah dan ya tabbatar da inda tusar ta fito,kuka mai tsanani ta fashe da shi sannan ta ce. "Don Allah ka nuna min Hammam,ina nufin real Hammam ba irin wannan ba,ina so na yi amfani da Hammaaammm." Lamyah ta ƙarasa maganarta tana wani irin kuka a hankali mai ban tausayi,butar Musaddiƙ ya karɓa ya wuce gaba tana biye da shi,a daidai wannan lokacin ne Innoh ta fito daga ɗaki saboda motsin da take ji a tsakar gida,ganin Musaddiƙ ta yi riƙe da buta Lamyah na biye da shi tana kuka suna tafe kamar waɗanda ba su son a gan su,wata iriyar faɗuwar gaba ce ta kama Innoh har sai da ta yi baya da sauri tana dafe ƙirji,wani irin bugu zuciyarta ke yi har tana iya jiyo sautin a kunnenta,shin me ya faru tsakanin Lamyah da Musaddiƙ? Ina zai kai ƴar mutane cikin daren nan? Lallai idan abinda take zargi ne ya tabbata gum za ta yi da bakinta,gobe ta rura wutar masifa yarinyar ta bar musu gida. Ko a mafarki bata hango yanda za ai zaman aure da Musaddiƙ ɗinta da wannan balarabiyar ba,cike da tashin hankali Innoh ta ce. "Inaa ba za ta saɓu ba bindiga a ruwa,ta zo ta koma

Chapter 13 of 30