Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels [9/11, 10:50 AM] zee hussain: ƳAR RAWA RUBUTAWA : HAMIDAH SANUSI AHMAD (HAERMEEBRAERH ✍️✨) *Wannan novel ɗin ba sabon rubutu bane,shi ne novel ɗina na uku da na rubuta a duniya,na rubuta shi a shekarar 2017,yanzu zan yi masa kwaskwarima a wannan shekara da muke ciki ta 2025/3/06. Ku biyo ni dan jin ya zata kaya.* PAGE 1. Dattijo ne mai tsananin natsuwa da kamala a tsaye,ya goya hannunsa ɗaya a bayansa yana karanta wata takarda da aka kawo masa,daga ɗaya daga cikin islamiyyun da ya buɗe a unguwar tasu ta rijiyar lemo dake cikin garin kano. Ya jima yana kallon takardar kafin wani matashi ya isa wajen nasu ya tsugunna cike da ladabi,cikin damuwa matashin ya ce. "Allah ya gafarta malam na kai saƙon gida,sai dai fa Aminee ta sanar dani jikin Baaba Tabawa ya rikice,dan kuwa na barota cikin ɗimuwa ta ce na sanar da kai." Cikin sauri Malam Muhammadu ya miƙawa mataimakinsa takardar ya ce. "Subhanallahi,Ridhwan maza ka ƙarasa duba abubuwan dake ciki,ka yi duk abinda ya dace kafin in dawo dan Allah." Ba tare da ya jira cewar kowa ba ya nufi hanyar gidan nasa,wanda bashi da nisa da islamiyyar da ya fi zama yana koyar da yara. Ya na shiga bai samu kowa a tsakar gida ba,wanda makircin Delu ne ya sanya ta tattara kan samarin yaranta suka shige ɗaki,a daidai lokacin da ta ji Tabawa ta yanke jiki ta faɗi a ƙasa,Aminee na ganin haka sai ta sanya kuka,duk da haka bai sa Delu ta je taga me ke faruwa ba. Malam na shiga ɗakin sai ya tarar da Tabawa cikin wani irin mawuyacin halin da ya kusa sanya ƙwalla zuba daga idanunsa,tsohon cikinta ya kalla wanda ya yi tsini sosai kai ka ce ƴan uku za ta haifa,cike da tausayawa Malam ya tsugunna a gabanta ya ce. "Tabawa jikin ne? Ko na samo abun hawa mu tafi asibiti a tabbatar da lafiyar ki da abinda ke cikin naki? A ce ciki ya kwana uku babu motsin komai?" A jigace wadda aka kira da tabawa ta girgiza kai sannan ta yi tari,cikin in ina ta ce. "Ami...nee,ɗebo min ru...ruwa in sha ƙishirwa..nake ji." A gaggauce Aminee ta wuce deɓo ruwa,bayan fitarta sai Malam ya matsa kusa da matarsa ya na yi mata sannu,tare da roƙon ta bari a kirawo koda ungozoma ce ta duba lafiyar cikin nata,kafin Tabawa ta ba shi amsa Aminee ta dawo da ruwa a kwano,ɗago kan mahaifiyarta ta yi a hankali,sannan ta bata ruwan ta sha,tana gama sha sai ta yi hamdala ta riƙe hannun Aminee a nata ta ce. "Aminenena ki ƙara haƙuri da duniya da mutanen cikinta,ba a samun nasara da ci gaba sai an yi haƙuri,juriya,tare da jajircewa,ki ji tsoron Allah a duk inda ki ke,kuma a duk halin da ki ka samu kan ki,Allah zai kasance tare da ke,kuma zai zame maki majingina mai taimakon ki a koda yaushe. Malam ga amanar Aminee nan ka riƙe min ita amana..." Tari ne ya sarƙeta tin kafin ta ƙarasa maganarta,nan da nan Malam ya rikice ya sake ɗaukan ruwan zai bata,ji ya yi Aminee na karanta kalmar shahada Tabawa na maimaitawa,babu jimawa rayuwar Tabawa ta bar jikinta,kuka Aminee ta fashe dashi mara sauti,cikin kukan ta ce. "Allah ya jiƙan ki Baabata Allah ya sa ki amsa tambayoyin ƙabari cikin sauƙi,Allah ya haɗa ki da Annabin rahama." Tashin hankalin da Malam ya shiga ba abu ne da zai misaltu ba ko ya faɗu,Tabawa ita ce rayuwar shi,ita ce mace ta farko da ya taɓa so,aure suka yi irin na soyayyar nan da ta yi fice a gari,ta taimakesa a lokacin da yake da buƙatar taimako a rayuwarsa,ta rufa masa asiri a lokacin da yake da buƙatar hakan,bata ɗaukan sirrin gidansa ta kai waje,ko da kuwa za su kwana ba su ci ba,ba ta ɗaga masa murya idan yana yi mata magana ba,mace ce mai yi masa ladabin da bai taɓa gani ko jin wata mace tana yiwa mijinta ba a kaf unguwar tasu,mace ce mara rowa da zafin kishi,domin kuwa a lokacin da suka shekara uku bata haihu ba danginsa suka sakota gaba,sai ta basa shawarar auren Delu,ita ta tsaya akan komai har ya auri Delu da kuɗin da take yin sana'ar ƙuli da mai. Bayan auren duk yanda Delu ta so ta kawo ɓaraka a gidan da tashin hankali Tabawa bata taɓa biye mata ba,har aka kai lokacin da Delu ta samu ciki,ta gama rainon cikin ta haifi ɗanta namiji,ranar suna Malam ya sanya masa suna Hamza,hatta da ragon suna Malam bashi da kuɗin siya,ba shi da dalilin su,Tabawa ce ta bashi ɗaya daga cikin ragunan da take kiwo aka yanka akai bikin suna cikin rufin asiri. Bayan suna da watanni biyar Delu ta fara yiwa Tabawa gorin rashin haihuwa,da baƙaƙen maganganu,nan take kuwa Malam ya tsawatar mata,sannan ya saka mata dokar duk sanda ta sake yiwa Tabawarsa gorin haihuwa to a bakin auren ta. Delu na yaye Hamza ta haifi Habibu,a wannan watan ne Tabawa ta samu ciki wanda ita kanta bata san tana ɗauke da shi ba,sai da ya kai watanni biyu ta fara laulayi mai matuƙar wahala. A lokacin da Delu ta fahimci Tabawa na ɗauke da ciki sai ta fara ƙulla mata makirci da maƙarƙashiya dan kawai ta yi sanadin zubewar cikin,sai dai kash,haƙonta bai samu cimma ruwa ba,sai da Tabawa ta haifi yarinyarta kyakkyawa mai kama da mahaifinta,ranar suna aka sanyawa yarinya Amina,inda Tabawa ke kiranta da Aminee,Delu kuwa ta yi rawa ta yi juyi a ɗaka da ta ga ba namiji Tabawa ta haifa ba,haka ta wuni waƙa tana kwarzanta yaranta maza tana jin daɗi a zuciyarta. A lokacin da Aminee ta isa yaye aka yayeta,babu jimawa Tabawa ta samu wani cikin,sai dai fa a wannan karon Delu bata bar cikin ya girma ba,ta dinga ɗirkawa Tabawa magungunan gargajiya tana ce mata ai itama da cikin su Hamza shi ta sha,yana sanya yara su yi ƙwari tun a ciki,dan haka da zuciya ɗaya Tabawa ta dinga shan magani har sai da tai ɓarin cikin sannan hankalin Delu ya kwanta. Tin daga wannan lokacin Delu ta samu hanyar cutar da Tabawa cikin sauƙi,saboda Tabawa ta yarda da ita,tana zaune da ita ne da zuciya ɗaya. Ganin yanda take shan wahalar ɓari ne ya sanya Tabawa fara roƙon Allah da ya tsayar mata da haihuwa haka ta gaji,da Allah ya amsa roƙon ta kuwa sai da Aminee ta yi shekaru sha uku a duniya sannan ta sake samun wani cikin,ita da Malam har sun cire ran zata sake haihuwa a wannan lokacin,dan haka zumuɗin da Malam ya yi a lokacin samun cikin Aminee shi ne ya sake yi a wannan cikin ma,sannan ya hana Delu bata duk wani jiƙe-jiƙe da ta ke bata a baya,duk da haka Delu bata huta ba sai da ta shiga ta fita ta kwantar da Tabawa jinya,ga tsohon ciki ga jinyar da aka rasa gane kanta. Malam na gama tina rayuwar da ya yi da masoyiyarsa Tabawa sai ya fashe da kuka mara sauti,da ƙyar ya miƙe tsaye bayan ya rufe gawar Tabawa ya nufi tsakar gida,hango Delu ya yi zaune shaɓar a ƙasa,daga ita sai ɗaurin ƙirji kamar koda yaushe,sai masifa take yiwa matasan yaranta da za su kai shekaru sha hudu da sha shida,cikin hargagi ta ce. "Dan uban ku ku gama cin abincin nan ku je ku ɗebo mana ruwa,muna zaune gida babu ruwa amma kun ƙi samowa? Ubanwa ku ke jira ya ɗebo?" Zumɓura baki suka hau yi suna cin abinci suna ƙunƙuni,waigawa Delu ta yi bayanta ta hango Malam tafe cikin wani irin mawuyacin hali,da sauri ta isa gare shi ta ce. "Malam lafiya na ganka haka?" Hawaye ne masu zafin gaske suka hau gangarowa saman kuncin Malam,iska ya furzar mai hucin zafi daga bakinsa sannan ya ce. "Delu Tabawa dai lokaci ya yi,ta tafi ta barni cikin matsananciyar damuwa,har abada ba zan taɓa samun macen da zata maye gurbin da Tabawa ta ke da shi a zuciyata ba,na rasa Tabawa Delu na rasa farin cikina." Wani irin tuƙuƙin baƙin ciki kalamansa suka dasawa Delu a zuciyarta,amma a zahiri sai ta rushe da kuka ta ɗora hannayenta a kanta ta faɗi ƙasa shaɓar tana birgima tare da faɗin. "Na shiga uku na lalace na rasa abokiyar zamana mai so na da ƙauna ta,mai karamci da mutunci tare da tausayawa a gare ni da ƴaƴana,Allah ya jiƙan ki yaya ya bamu guzirin tarar da ke." Delu na daga cikin irin matan nan farare masu ƙiba sosai,sai dai tsabar datti da rashin wanka ya sanya ta rine ta yi duhu,da ƙyar malam ya iya ɗaga ta sama ya jawo ɗankwalinta da ta yi cilli da shi ya rufe mata dogon gashinta da ya sha zane,tsabar jimawa ya sa ya danƙare da dauɗa. Haƙuri Malam ya dinga bata,dan a iya saninsa suna zaman lafiya da Tabawa,shi yasa rasuwar dole zata taɓa ta kamar yanda ta taɓa shi. Babu jimawa ya fita ya samu abun hawa aka kaita asibiti aka duba abinda ke cikinta,bayan an gama dubawa ne aka tabbatar masa da abinda ke cikin nata ya rasu,cike da jimami malam ya maida matarsa gida ya yi mata wanka da kansa aka kaita gidanta na gaskiya. Aminee ta shiga wani irin mawuyacin halin maraici a gidan mahaifinta bayan rasuwar Tabawa,domin kuwa hatta da abinci ba bata ake yi ba sai idan Malam na gida,idan kuwa baya nan ko zata kai dare tana aiki ne a gidan ba za a bata komai ba,ita ce shara da wanke-wanke,ita ce ɗiban ruwa,ita ce wankin su Hamza da Habibu,wani lokacin ma har na Delu duk bata take yi ta wanke. Rayuwa ta yiwa Aminee ƙunci da matsi, duk wannan halin da take ciki ta kasa sanar da mahaifinta,domin kuwa bata manta watarana da ta taɓa sanar da Tabawa asalin mugun halin Delu,irin dukan da ta ci a wajenta ba,dan haka tana tsoron sanar da Mahaifinta ya ce ƙarya take yi,ta sake shiga wani taskun wahalar. Yau ma kamar koda yaushe,Aminee ta kammala duk wani aikin gidan Malam ya dawo daga makaranta,sai ya zauna a shimfiɗar da Delu ta sa Aminee ta yi masa,abinci Delu ta kawo masa ta ajiye sannan itama ta zauna riƙe da tukunyar tana cin ragowar,kallon Aminee malam ya yi ya ce. "Aminee lafiya ki ke kuwa na ga duk kin rame haka?" Cikin sauri Delu ta karya wuya da murya ta ce. "Humm ai Malam ni kaɗai na san irin halin kewar Yaya da yarinyar nan take kwana take tashi da shi,shi yasa nake yi mata faɗa akan ta ƙwarara jikinta ta dinga cin abinci sosai,sannan ta sanyawa zuciyarta salama,dukan mu nan muna tare da kewar Yaya,dan kuwa na tabbata da kewarta zan koma ga mahaliccina,amma ina yarinyar nan ta ƙi kwantar da hankalinta,taso ki karɓi wannan ki ci,tinda dama ɗazu baki wani ƙoshi ba ki ka ajiye." Cikin sauri Aminee ta isa gaban Delu ta karɓi abincin tukunyar,wanda ya kasance kusan rabi duk ƙanzo ne da naman da Delu ta ɓoye a tukunya,Malam ne ya kalle Aminee ya yi mata nasiha sosai,kafin ya ce ta tashi ta je ta ci abinci,ɗakin su ta nufa ta zauna ta hau cin abincin hannu baka hannu ƙwarya,hawaye na zuba daga idanunta,sai da ta cika bakinta da shinkafa ne ta tuna irin wahalar da take sha a gidan,da kuma yanda ake ɓoyewa mahaifinta dan kar ya sani,wani irin marayan kuka ta saki sannan ta ci gaba da tura abincin babu ruwa. Delu ce ta shiga ɗakin ɗauke da ruwa a hannunta ta miƙawa Aminee ta ɗaga murya ta ce. "Karɓi ki kora,ki dinga sanyawa ranki salama kin ji?" A hankali ta ranƙwashi kan Aminee tana zabga mata harara da ƙananan idanunta,sannan ta kama kunnenta ta murɗa ta ce. "Kin ci abincin ki na dare kenan yarinya,in ga kin fito da yamma in za mu ci abinci,idan ki ka fito har ki ka sa malam ya gane halin da kike ciki a gidan nan sai na kashe ki da duka." Tana gama faɗin haka ta fito suɓur-suɓur ta koma wajen Malam,godiya Malam ya yi mata yana yabawa ƙoƙarin da take yi na kula da Aminee,murmushi ta yi tana jin kunya ta kauda kanta gefe ta ce. "Humm malam kenan,ai yiwa kai ne,dan Allah daga yau ka dena yi min godiya,in dai ka ɗauke ni a matsayin uwa ga Aminee." Haƙuri Malam ya bata suka ci gaba da hirar su cike da nishaɗi,wanda tun farko haka ta so ta kasance a tsakanin su da mijin nata,sai gashi Tabawa bata mutu a lokacin da ta so ba har sai da ta aje mata mugun iri a cewarta. **************************** El-mustapha Hussain wani matashi ne da ya shigo ƙasar Nigeria daga maƙociyar ƙasar wato Nijer. Asalin El-mustapha da iyayensa larabawan Dubai ne,yawan taimakon talakawa da ƙaunar marayu ne ya sanya El-mustapha tattarawa ya koma ƙasar Nijer da zama,daga nan ya ji labarin ƙasar Nijeriya sai ya shigo ya sayi gida a kano,duk sanda ya zo ƙasar anan yake zama ya nemi gidajen marayu da mabuƙata ya kashe dukiyarsa da ya gada daga mahaifansa,yana gamawa sai ya koma ƙasarsa,ya ci gaba da kasuwancin da ya taso ya tarar iyaye da kakanninsa na yi. Ƴan'uwan El-mustapha na jini sun tsane shi matuƙa gaya,ba dan komai ba sai dan yanda ya ke kashe dukiyarsa kamar baya so,matayen su sun yi masa tayin ƙannensu dan ya aura amma ya ƙi amincewa ya zaɓi ko ɗaya a ciki,a cewarsa yana son ya auri yarinyar da ta fito daga gidan tarbiyya,sannan iyayenta talakawa ne masu buƙatar taimako,ta yanda zai taimaka mata da iyayenta su fita daga ƙangin talauci,wannan furucin nasa ya jawo masa wata gagarumar tsanar da bai taɓa zaton ɗan'uwa zai iya yiwa ɗan'uwasa irinta ba,sai dai shi a ɓangarensa yana son dika ƴan'uwasa,kuma yana yi musu biyayya a matsayinsa na ƙaraminsu. Islamiyyun Malam Muhammadu na daga cikin makarantun marayun da El-mustapha zai kaiwa ziyara a wannan shekara,dan haka Malam Muhammadu bashi da lokacin zama,a koda yaushe yana makaranta suna koyawa yara karatu da ƴan waƙoƙi na larabci da za su tarbi El-mustapha Hussain da su. Malam Muhammad da ɗalibansa sun shirya tsaf dan tarbon babban baƙon su da suka ji ana yabon halayensa da kyawun surarsa a gari...... *Ina fatan kuma kun shirya tsaf dan karanta wannan labari mai taɓa zuciyar mai karatu?* [9/11, 10:50 AM] zee hussain: ƳAR RAWA RUBUTAWA : HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✍️✨ PAGE 2. A gajiye El-mustapha da babban abokinsa Mus'ab suka iso Nigeria,inda jirgi su ya sauka ta garin kano. Mai kula da gidan El-mustapha ne ya zo a mota ya ɗauke su ya wuce dasu Rijiyar lemo,kai tsaye gidan mai unguwa suka nufa suka gabatar da kan su,bayan mai unguwa ya gama jin bayanan su ne cikin fara'a ya yi musu maraba da zuwa,sannan ya sa aka kirawo masa Malam Muhammadu,dan kuwa baƙin kusan nashi ne da ɗalibansa. Da zuwan Malam Muhammadu sai suka gaisa da baƙin nashi sannan ya yi musu jagora a motar El-mustapha suka zaga makarantun islamiyyun da Malam Muhammadun ya assasa. El-mustapha ya ji daɗin yanda ake koyar da yara ƙur'ani da tajwidi,ga kuma hadisan Annabi Muhammad ƙananan yara na ta biyawa,waƙar maraban da suka raira masa ta sa ya yi farin ciki sosai,ya tabbata idan suka samu tallafin da ya dace za a yaye yara haziƙai da nagartaccen ilimin islama. Dan haka bai bar makarantun ba sai da ya rubuta maƙudan kuɗi a cak ya damƙa a hannun Malam Muhammadu gaban shaidu,godiya suka dinga yi masa tare da fatan alkhairi sannan suka shiga mota za su koma wajen Mai unguwa,suna cikin mota suna hira ne Malam Muhammadu ya ce. "Idan babu damuwa,kuma ba zan takura muku ba,zan so mu je gida na da ku ku ci irin abincin mu da na tanadar muku." Cike da fara'a El-mustapha Hussain ya ce. "Muna godiya da wannan gayyata da ka yi mana,babu matsala,Malam Isa mu je." Cikin farin ciki Malam Muhammadu ya nunawa Malam Isa hanyar gidansa suka tafi suna hira. Suna isa Malam Muhammadu ya fita daga mota cikin sauri ya buɗe ɗakin dake ƙofar gidansa wanda Aminee ta share ta gyara aka shimfiɗa sabuwar tabarmar Tabawa, sai ƙatuwar dadduma da buta cike da ruwa a bakin ƙofa. Cikin sauri ya yi musu izinin shiga suka shiga suka zauna tare da yaba kirkin Malam ɗin,yana shiga gidan sai ya tarar da Delu ta na gyara kalwa,kai babu ɗankwali kan nan daƙal-daƙal,girgiza kai ya yi ya wuce ɗakin Aminee wadda bata jima da fitowa daga wanka ba,kallonta ya yi ya ce. "Amineen Abbah maza ki je ki kaiwa baƙi ruwa a ɗakin baƙi,sai ki dawo ki kai musu abinci kin ji? Ni bari na ɗan zaga." "To Abbah bari na saka kayana." "Yauwa a hanzarta dan Allah." Cikin sauri Aminee ta sanya kayan ta riga da zani na atampa, sannan ta sanya hijabi a saman su,ruwa ta ɗiba a babban kwanon sha guda biyu daga randar dake kusa da madafi, wadda asalinta ta Tabawace,ta na zuba ruwan sanyi a ciki ta baiwa Malam ɗin a duk sanda ya fita ya dawo da gajiya. A saman babban faranti ta ɗora su ta nufi ɗakin baƙin ta yi sallama a bakin ƙofar shiga,bata shiga ba sai da aka amsa mata sannan ta ɗaga labule kanta a ƙasa ta shiga ta durƙusa ta ajiye musu ruwan,ta na ajiyewa ta buɗe zazzaƙar muryarta ta ce. "Barka ku da zuwa,da fatan kun iso lafiya?" Cikin sauri El-mustapha da ya ke kallon wani littafi da ya samu a ɗakin ya ɗaga kai ya kalli Aminee;wadda kanta yake a kasa,amsawa suka yi gaba ɗayan su amma banda El-mustapha da ya kafe ta da kyawawan idanunsa,har ta fita bai iya cewa komai ba,suna nan zaune babu mai cewa komai ta sake dawowa ɗauke da wani babban farantin mai ɗauke da babban kwano irin na mutan da ɗin nan mai murfi,ajiyewa ta yi a tsakiyar su,cokula na gefe ta yi musu sallama za ta koma cikin gida, El-mustapha ne ya yi gyaran murya ya ce. "Ya ya sunan ki?" Cikin natsuwar da ta zame mata jiki ta ce. "Aminatu." Jinjina kai El-mustapha ya yi kafin ya sake cewa. "Wannan abincin fa, buɗe mu gani?" A sanyaye Aminee ta sanya hannu ta buɗe babban kwanon,sai ga taliya ƴar murji ta sha manja da yaji,tare da soyayyan kifi manya a samanta,gefe ga tumatur da albasa an yanka ƙanana,yawu abokan tafiyar El-mustapha suka haɗiya,dan kuwa su sun san daɗin abincin, El-mustapha kuwa kallon Aminee ya yi ya ce. "Wa ya dafa wannan abincin? Meye sunan shi kuma?" "Ni na dafa,uhmm taliya ce da manja,sai kuma kifi soyayye." Maimaita kalmar soyayyen ya yi da gurɓatacciyar hausarsa da bai gama ƙwarewa ba,dariya Aminee ta gimtse ta sa hijabinta ta rufe fuskar ta,murmushi El-mustapha ya yi sannan ya ce mata,ta tashi ta tafi, cike da murmushi Aminee ta tashi ta tafi,babu abinda El-mustapha ke kallo da ya wuce dimples ɗin ta dake lotsawa a duk sanda ta yi murmushi. Aminee yarinya ce ƙarama da ba zata wuce shekaru sha huɗu zuwa sha biyar ba,baƙar fata ce ita,irin baƙin nan mai matuƙar kyau da ɗaukan idanun mai kallo,tana da cikar halitta ta kasa,tana kuma da gashin kai daidai misali irin na hausawa,bashi da santsi sai cika da tsawo,kama take yi da Malam sosai ta fuska,sai dai yanayin ƙirar jikinta sak irin na Tabawa ne. Wannan kyawun nata ba ƙaramin tsole idanun Delu yake yi ba,shi yasa a kullum ta ji matan Baffanin Aminee suna yi mata fatan auren mai kuɗi sai ta ce ba amin ba,in Allah ya yarda a ƙauye za ta yi aure,inda za ta je ta yi daka da surfe kafin ta samu abinda za ta ci. Shigarta gida tana murmushi ne ya sanya Delu ƙwala mata kira,cikin jin haushi ta rage murya ta yanda Malam da ya shiga banɗaki kama ruwa ba zai ji ta ba ta ce. "Ke uban me ki ke yiwa murmushi? Maza wuce ki hura min wuta na ɗora kalwata dare na yi kafin na ɓalla ki." Nan take fara'ar fuskar Aminee ta ɗauke,cikin sauri ta nufi wajen murhu ta tura itace saboda akwai sauran garwashin da ta yi girkin rana da bai gama mutuwa ba,nan da nan itace ya fara hayaƙi har ya sa Aminee fara yin tari,kafin Malam ya fito ta bar wajen cikin umarnin Delu saboda kar ya ganta tana hura mata wuta ya yi magana. A can ɗakin baƙi kuwa El-mustapha tin yana juya taliyar murji yana jin kamar a ɗakko masa abincinsa a mota,har sai da ya daure dai ya kai cokali ɗaya bakinsa,taliyar murji na shiga bakin balarabe sai ta sakar masa da tsinkakken yawu,nan take ya hau jera loma yana haɗawa da kifi soyayye,sai ga El-mustapha ya tashi da taliya da shi da su Mus'ab da Malam Isa har suna santi, suna kammalawa Malam Muhammadu ya dawo ya yi musu godiyar amsa gayyatarsa da suka yi, nan fa El-mustapha ya dinga zuba tashi godiyar sannan ya yabawa ƙoƙarin Aminee na girka musu wannan abinci mai daɗi,tukuici El-mustapha ya bayar a bata na kuɗi amma Malam ya ƙi karɓa,da ƙyar da magiya El-mustapha ya samu Malam ya karɓa suka fito ya raka su har bakin mota suka tafi. Bayan sun tafi da kwana biyu ne El-mustapha ya sake dawowa shi kaɗai,sannan ya sallamawa Malam Muhammad suka gaisa,ya tambaye shi makaranta da ɗalibai,Malam ya tabbatar masa da komai na tafiya yanda ake so,musamman da aka samar da abubuwan karatu,ga kuma sabbin gine-ginen da ake yi dan jin daɗin daliban wanda shi El-mustapha ne ya bada wannan taimakon. Hamdala El-mustapha ya yi sannan ya gyara tsayuwa ya ce. "A gaskiya Malam wannan zuwan ba zuwan ɗalibai da mabuƙata bane,zuwa ne na kaina,shi yasa ban taho da kowa ba na zo ni ɗaya,Malam a wancan zuwan da na yi na ga

Chapter 1 of 30