Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
inda ta fito,na yi wa ɗana matar aure wadda za ta yi min biyayya,ba zan aura masa matar da ko gane yare na da kyau bata yi ballantana na ce mata yi ta yi,ko na hana ta ta hanu." Musaddiƙ kuwa har cikin banɗakin ya shiga ya nuna wa Lamyah yanda za ta yi amfani da shi sannan ya fito ya na maida numfashi,sai da ya shiga ɗaki ya fashe da dariya ya ce. "Musaddiƙ fa ka yi matar aure,to ni idan na bar yarinyar nan ta tafi ban aure ta ba ai na tafka babbar asara,ai ni ne ya kamata na aure ta ko dan mu dinga tina wannan lamari muna shan dariya,ba zan ƙyale ta ba kuwa sai na leƙa ta na ji ya aka haihu a ragaya." Yana gama surutan sa ya sake buɗe labulen ƙofar ɗakinsa ya tsaya a bakin ƙofa yana ci gaba da dariya,Lamyah kuwa ta na can wari duk ya cika mata hanci ta rasa inda za ta saka kanta,dabarar cusa kanta cikin rigarta ce ta faɗo mata saboda ƙamshin turaren da ke jiki,cikin sauri ta zuge zip ɗin rigarta ta cusa kanta a ciki sannan ta sake zugewa,a haka ta gama lalurar da za ta yi ta yi tsarki ta fito,wata iriyar iska ta ji tana ratsa ta kamar wadda ta jima a kurkuku,bokiti ta ɗauka ta sake zuba ruwa ta koma banɗakin,wanka ta yi sosai kafin ta fito ta doshi hanyar ɗakinta, Musaddiƙ ta gani tsaye yana ta banka mata dariya har yana riƙe ciki,cike da jin kunyarsa ta hau shagwaɓa tana bubbuga ƙafa a ƙasa ta ce. "Allah zan faɗa wa Abbah kana min dariya." "To dariyar me za ki ce ina yi miki? Dariyar kin yi sati ɗaya cur da kashi a ciki sai yau ki ka zubar zaki ce na miki ko ta me?" "Yah Musaddiƙ." Yanda ta ambaci sunansa cike da shagwaɓa ne ya kashe masa jiki,a hankali dariyar tasa ta fara raguwa,suna tsaye a haka Larai ta fito hannunta riƙe da tocilan,haske su ta yi ta ce. "Ke Lamyah ba ki yi bacci ba dama? Me ku ke yi anan da wannan daren?" Innoh ce ta fito fuska a haɗe ta ce. "Ni ce nan na aike shi wajen ta ya ji ko ta yi sallah,ko kuma an hana tambayar baligi ya yi ibada ne?" Cike da ladabi Larai ta ce. "Ah ah Yaya dama..." "Bana son jin surutun banza,ku da komai sai kun maida shi ƙaramar magana,kai kuma idan ba za ta gaida ubangijin nata ba ba sai ka barta ba,gashi nan ka jawo za a yi muku muguwar fassara." Jiki a mace Musaddiƙ ya bar wajen ya koma ɗakinsa,lallai sai da Innoh ta yi wannan maganar ya gano illar abinda ya aikata,ba shi da dalilin da zai sanya shi keɓe wa ɗa yarinyar da ba muharramarsa ba ce,idan ta rasa yanda za ta sauke lalurar kashin da ya dame ta ne ya kamata ya sanar da Innoh ko ɗaya daga cikin matan mahaifin nasa ne,me ya sa sai shi ne zai shiga har banɗaki daga shi sai ita ya nuna mata yanda ake yi bayan ita ɗin ba muharramarsa ba ce? Daga tsallake maganar Allah fa sai dai a faɗa saɓon Allah,kar mutum ya raina abinda zai aikata komai ƙanƙantarsa in dai haramun ne,domin kuwa daga ƙarami ake faɗa wa babba. Zama ya yi yana nazarin hanyar da zai ɓullo wa lamarin,dan gaskiya ya fi son su fara haɗa kansu da Lamyah kafin ya tinkari mahaifinsa da maganar aurenta. Da wannan tinanin bacci ya ɗauke sa. Ita kuwa Lamyah tinda ta shiga ɗaki ta tarar Mubarak ya yi bacci,pampas ta saka masa sannan ta zauna tana sauke numfashi a natse,wata iriyar iska take jin tana ratsa ta da kyau,hamdala ta yi sannan ta sanya rigar da take yin sallah ta maimaita sallolin da ta ƙirga ana bin ta,dan kuwa ba a sallah da kashi ko fitsari a ciki,ko da ka yi ba su karɓu ba matsawar kashin nan ko fitsari ya matse ka sosai. Tana idarwa ta sauya kayan jikinta ta yi addu'ar bacci ta kwanta. Washegari da safe Lamyah ta fito da kayan wankin su ta zube a ƙofar ɗaki,sai ta wuce ƙofar ɗakin Mai Unguwa ta gaishe sa,daga nan ta shiga gaishe da Innoh,a daƙile ta amsa mata,har za ta yi mata maganar abinda ya faru jiya amma ta fasa ta sallame ta,ɗakin Asabe ta je ta gaishe ta daga nan ta gaida Larai. Tana gamawa ta dawo ta zauna a gaban wankin tana kallon su,nan dai babu alamar washing machine ballantana dalilinsa,yanzu ya za ta yi kenan? Musaddiƙ ne ya fito daga ɗakin sa idanun sa sai lumshewa suke suna buɗewa,alamu ne na bai jima da tashi daga bacci ba,banɗaki ya shiga ya ɗan jima kafin ya fito ya wanke bakinsa da fuskarsa,kallon hanyar ɗakin Lamyah ya yi yana murmushi,a zaune ya ganta da tulin wankinta sai ya ƙarasa wajenta,cikin sauri Lamyah ta gaishe sa tana kauda kai tana murmushi,domin kuwa wata iriyar kunyarsa take ji ba kaɗan ba. Murmushi shima ya sakar mata kafin ya ce. "Wannan wankin fa?" "Namu ne ni da Mubarak,so nake na wanke na ga kuma babu uhumm..." "Babu injin wanki ko? To mu ta nan hannu za ki saka ki dirji suturar ki yarinya babu maganar inji,ko kuma ki bari anjima zan ɗauka na kai gidan yayata suna da shi,sai na wanko muku na dawo da su ko zuwa yamma ne." Cike da murna ta juya tana kallon cikin idanunsa ta na yi masa godiya,a haka Innoh ta fito ta same su,cikin tsananin baƙin ciki Innoh ta ce. "Har ka gaida uwar ka ashe Musaddiƙ,ahh na ce har ka gaida Uwar ka,da kyau." Sosa kan sa ya fara yi yana bata haƙuri,hanyar ɗakin nata ya nufa ya na juyawa yana kallon Lamyah da take a takure kuma a tsorace,dan kuwa ba ƙaramin tsoron Innoh take ji ba saboda yawan yi mata masifa da take yi kullum. Sallamar sa kawai Innoh ta amsa ta hau shi da masifa,ta inda take shiga ba ta nan take fita ba,ƙarshe ta ce. "Har abada babu kai babu yarinyar nan,wanna shirmen da ka fara hasashe a tsakanin ku ba mai yuwa bane,Saddiƙa jikar Delu ita na zaɓa maka za ka aura,domin ka ceto ta daga wannan mummunar rayuwar da take yi,ka ga shikenan asirin ƙawata da jikarta ya rufu an yi abu tuwona mai na." Tsaye Musaddiƙ ya miƙe saboda tsananin tashin hankali da ya rufta masa a lokaci ɗaya. Cikin tsananin mamaki ya ce. "Kina nufin ni zan auri wannan yarinyar mara kamun kai? Yarinyar da ta zubar da ciki har sau uku? A yanzu haka fa idan aka shaƙe ta aka ce ta bayyana iya mazajen da suka kwanta da ita ba za ta iya ba,saboda ta zama shaddar kasuwa,shine za ki haɗa ta da ni Innoh?" Tabbas Innoh bata son wannan haɗin,to amma ya za ta yi tinda ƙawarta kuma aminiyarta ce ta nemi alfarmar? Sannan ko babu komai dan darajar taimakon Saddiƙa da suka yi ta dinga jin maganar ta,kuma ba za ta mallake mata ɗa ba tinda babu soyayya a tsakanin su. "Innoh don Allah ki saurare ni,ni fa babu wani abu a tsakanina da ita face alkhairi." "Kai rufe min baki,jiya alkhairin ne ya sa take biye da kai tana kuka? Uban me ka yi mata? To bana ma son na ji me ka yi mata,za ta tattara ta bar mana gida tin kafin kai ma a fara ƙirga cikin da ka zubar wa yaran mutane." "Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un Innoh abinda dama ki ke zargi na da aikatawa kenan? Bahaya fa take son yi ta rasa yanda za ta yi tinda ta zo gidan nan,ni kuma na fahimci hakan ne saboda na san irin yaran nan da suka taso cikin gata ba ganin irin banɗakin mu suka taɓa yi ba ballantana su san yanda ake amfani da shi,haba Innoh,idan kowa zai yi min mummunar fassara ai ke bai kamata ki yi min ba." Yana gama magana ya fita daga ɗakin cikin ƙunar zuciya,Innoh kuwa jikinta ne ya yi sanyi,sannan ta wani ɓangaren ta samu kwanciyar hankali,da ta gano babu abinda ya shiga tsakanin su,tashi ta yi ta leƙa ƙofar ɗakin Mai Unguwa,gani ta yi ya fita sai ta ƙarasa yaye labulen ta fito tana muzurai,a gaban Lamyah ta tsaya ta na bin ta da wani mugun kallo,wankin ta kalla ta ce. "Me kike jira baki fara wankin naki ba? Idan sun yi kaɗan ne bari na ƙaro maki wasu." Ɗakin ta ta koma ta kwaso mata hijaban ta masu datti ta watsa mata,kallon ta Lamyah ta yi tana mamakin halayyarta,to ita wa ya faɗa mata ta taɓa wanki da hannayenta ba da inji ba? Daurewa ta yi ta kwashi kayan ta nufi bakin randa ta ɗebi ruwa,jiƙa kayan ta yi ta hau jajjaɓa wankin da a kallo ɗaya mutum zai gane bata iya ba. Cike da ɓacin rai Innoh ta ce. "Yaran yanzu babu abinda kuka iya sai soyayya da shirmen banza,kafin ki bar gidan nan kuwa sai na tabbatar da kin iya duk wani abu da macen azziƙi ya kamata ta iya shi,kallo nan." Duƙawa Innoh ta yi ta hau wanke rigar Mubarak tana nunawa Lamyah yanda ake yi,ta na gamawa ta tura mata bokitin gaban ta ta ce. "To kama maza ki yi ki tashi." Babu ɓata lokaci Lamyah ta hau wanke kayan babu ji baby gani,duk ta zubar da fiye da rabin omon a wanke kayan Innoh,tana gamawa Innoh ta sake zuwa ta nuna mata yanda ake yin ɗauraya da shanya. Kafin Lamyah ta gama wankin azahar ta yi,jikinta kuwa babu inda baya yi mata ciwo,rigar jikinta ta jiƙe jagab sai atishawa take zabgawa,duk abinda ke faruwa Musaddiƙ na kallo ta labulen ɗakinsa,ran shi ba ƙaramin suya yake yi ba akan abinda Innoh take yi,ita mace ce da take da tsananin kishi,sai kuma jarabawar rayuwarta ta halasta mata zama da kishiyoyi,ta yi nasarar fitar da sabuwar amaryar da Mai Unguwa ya aura babu jimawa,dan ko haihuwar farko bata yi ba,Asabe da Larai kuwa babu wadda ba a saka ba saboda ita,shi yasa suke bala'in tsoron ta,suke yi mata biyayya,to a yanzu ya gane kishi take yi akan shi shima,girgiza kai kawai ya yi ya miƙe ya fita tsakar gidan,ido suka haɗa da Lamyah da ta jigata,cikin sauri ya kauda kan sa ya ɗauki buta ya yi alwala ya bar gidan. Alwala itama ta yi ta koma ɗaki,sai da ta cire jiƙaƙƙun kayan ta ta sauya wasu sannan ta faɗa katifa tana maida numfashi,hawaye ne masu zafi suke gangarewa gefe suna jiƙa katifar da ta ke kai. Yau matar da za ta iya ɗauka aiki ta biya ta maƙudan kuɗaɗe ita ce ta sanya ta wanki,lallai duniya a bun tsoro ce,wai shin ma me ta yi wa matar ne ta tsane ta? Kiran sallar da ta ji an tada a ƙofar gida ne ya zaburar da ita ta miƙe tsaye ta tada sallah,tana idarwa ta kalli Mubarak da ke ta ƙunci tin bayan da ya ga tana wanki,suna haɗa ido ya hau zubar da hawaye,cikin kuka ya ce. "Mommy mu tafi wajen Aunty Afrah,bana son nan,ina son na ci abinci." "Ba ka cin abinci ne anan Mubarak? Ba zan iya tafiya wajen Afrah ba ba tare da na haɗu da Abii ba,bayan haka ma na ga ka saba da su Baba Asabe,ko ɗazu fa ina hango ka a wajen su kana cin abinci,ka yi haƙuri mun kusa tafiya ka ji?" "Ni dai ina son na ci abinci bana son wannan da ake bamu anan." Hawaye Lamyah ta share ta miƙa masa hannu,wajenta ya isa da sauri ya faɗa jikinta ya na sake fashewa da kuka,itama kukan ta ke yi cike da tausayawa rayuwar su. A haka Innoh ta ɗaga labulen ɗakin ta same su,kama haɓa ta yi tana salati sannn ta ce. "Na shiga uku ni Innoh yau ina ganin baƙin munafurci wajen wannan balarabiya,ji yanda ta ƙwaƙume yaro suna zabga kuka kamar wanda aka aikowa da saƙon mutuwa,to taso ki zo mu shiga madafi,ki na nan ba zan wahala ba na hau girki ina miƙo miki,fito maza ki ga yanda ake hura wutar murhu,dan na san baki iya ba." Cikin sharar hawaye Lamyah ta yi ƙoƙarin ajiye Mubarak amma yaron ya ƙi,maƙale ta ya yi da kyau yana zunduma ihu,a hasale Innoh ta shiga ɗakin ta fizge shi daga jikin Lamyah za ta zabga masa mari,cikin sauri da zafin nama Lamyah ta kama hannun Innoh ta na binta da wani irin kallo,cikin gurɓatacciyar hausarta ta ce. "Zan yi miki duk abinda kike so,amma kar ki sake hannu ki ya sauka a jikin shi da Sunan duka,ba zan taɓa iya yi miki alƙawarin salama ba akan hakan." Kalaman Lamyah sun yi matuƙar sanyaya jikin Innoh,Mubarak kuwa tini ya haɗiye kukan sa saboda tsoro,borin kunya Innoh ta hau yi ta na masifa tare da zagin Lamyah,Lamyah kuwa bayan ta ta bi ta na so ta yi mata duk aikin da za ta saka ta,amma ta yi alƙawari babu wanda zai taɓa Mubarak su wanye ƙalau da shi ko wanene kuwa. ****************** Abu kamar wasa ƙaramar magana ta zama babba. Iyayen Aminullahi sun kai gaisuwa wajen iyayen Layuza,har an bashi ita tare da saka ranar aure sati uku masu zuwa,mahaifiyar Layuza da ta yi ƙorafin an saka lokacin kusa basu gama shiri ba,sai Aminullahi ya yi musu alƙawarin yi wa amaryar tasa kayan ɗaki,shi dai kawai a bashi matar sa. Nan da nan kuwa Hajiya ta shiga shirin bikin Layuza,gyara ta ke yi mata wanda ya dace da wanda bai dace ba,domin kuwa har wajen bokan su sai da suka koma dan a rufe wa Aminullahi baki akan duk abinda zai ji kuma ya gani bayan auren. Ta ɓangaren Iya kuwa kadaran kadahan ta karɓi abun bayan nasihar da Momma ta yi mata,amma har wannan lokacin ta na ji a jikinta Layuza ba tsarar auren Aminullahinta ba ce. Ango Aminullahi kuwa baya cikin walwala ko nishaɗi kamar yanda ake samu a wajen kowanne angon da zai yi aure,ba dan komai ba sai dan soyayya da ƙaunar Lailah da ta yi wa zuciyarsa yawa,ji yake yi kamar ya gudu Nigeria ya fasa auren Layuza,gefe ɗaya kuma tasirin asirin da su Layuza suka yi masa ya sanya shi jin ƙauna da son kasancewa da ita. Gaba ɗaya ya rame ya fita daga hayyacinsa,da ya zauna zai faɗa dogon tinani har sai an taɓa shi yake dawowa hayyacin sa. A haka ranar ɗaurin aure ta zagayo,wata bugaggiyar shaddar da ta ɗauki idanun jama'a Aminullahi da Abii suka saka,a wannan ranar Mus'ab ya yi kukan rashin El-mustapha har ya gode Allah,wanda wasu mutanen sun ɗauka tsananin murna ce yake yi saboda zai aurar da ɗan sa. Shi kan shi Aminullahi ya shiga damuwa mai yawa wadda ta haɗe masa ta dalilin abubuwa da dama dake damun ransa. Da misalin ƙarfe sha biyu na ranar asabar aka ɗaura auren Aminullahi da Layuza akan sadaki naira dubu ɗari biyu. Jama'a sun shaida an yi walima da yamma,da dare kuma Aminullahi ya aika motoci zuwa gidan kakannin Layuza aka ɗakko masa amaryarsa,a gidan su da Mus'ab ya jima da gina masa za su tare,gida ne mai masifar kyau,sannan aka ƙara ƙawata sa da kayan alatun more rayuwa. Layuza bata bari an ɗakko ta ba sai da ta gudu banɗaki ta yi matsi da wani magani da aka haɗa da jinin al'adarta sannan ta fito ta na muzurai ta shiga mota aka ɗauki hanyar zuwa gidan ango Aminullahi....... [9/11, 10:50 AM] zee hussain: ƳAR RAWA. RUBUTAWA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✍️✨ PAGE 25. Gidan Momma aka fara kai Layuzah,sai da ta yi mata nasiha sosai sannan ta yi musu addu'a duk da cewa Aminullahi baya wajen,sannan ta aika Iya cikin ɗakin ta ta ɗakko mata kyautar da ta tanada ta musamman domin ta sannan ta bata hannu da hannu,ƙannen mahaifiyarta ne suka yi ta godiya,sannan itama Layuzah ta durƙusa cikin wata siririyar murya ta yi wa Momma godiya,harara Iya ta banka mata a hankali ta ce. "Munafuka,sam ban yarda da yarinyar nan ba." Cikin ɗaga murya kuma ta ce. "To ubangiji Allah Ya kare su daga sharrin juna,Allah Ya haɗa ku da alkhairin junan ku." Babu wanda ya fahimci inda addu'ar Iya ta dosa sai Momma da Layuzan kanta. A haka dangin ta suka kama ta tare da dangin Momma suka raka ta har gidan su da bashi da nisa sosai da gidan Momman. Ko da suka je gidan sun tarar da motar ango a ƙofar gida daga ɗan nesa da gidan,Aminullahi na cikin motarsa a zaune kasancewar bashi da wasu abokai sai dangin Mommansa da suke mutunta juna,kuma duk sun yi masa ban gajiya tare da sanya alkhairi sun tafi sun bar sa da halin sa. Sai yanzu da bikin sa ya tashi ya gane lallai bashi da abokai,amma kuma hakan bai wani dame sa ba,duba da cewa yanzu rayuwar ta zama abinda ta zama,tara abokan ma wani lokacin bashi da wani amfani. Ƴan kai amarya na ajiye ta suka bar gidan tinda duk sun hango motar ango,wani magani Innar Layuzah ta damƙa mata a hannu,ta yi mata raɗa ta ce. "Mu na fita ki fasa ledar nan ki zuƙe ruwan cikinta,Allah Ya sa gidan zaman ki ne har abada Layuzah." "Amin Innah na gode." Sallama suka yi mata suka wuce,suna fita kuwa ta fasa ledar ta shanye ruwan dake cikinta wanda ta kasa tantance ruwan menene,cukuikuye ledar ta yi ta yar a bayan ƙofa sannan ta buɗe jakarta ta ɗakko wata kwalba ta ɓalle murfin ta goga turaren da ke ciki sannan ta mayar ta rufe,sake zama ta yi a tsakiyar gadon ta na jan mayafin kanta,sai da ta rufe ko ina na jikinta sannan ta hau addu'ar Allah Ya sa magungunan da suka kashe maƙudan kuɗaɗe akan su su yi aiki. Babu jimawa ta fara jiyo ƙarar buɗe gate da rufe shi tare da ƙarar mota,cikin abinda bai wuce minti biyar ba Aminullahi ya shiga gidan,direct ɗakin sa ya nufa ya watsa ruwa tare da ɗaura alwala sannan ya sanya doguwar jallabiyarsa ya fita zuwa ɗakin da Layuzah ke zaune kamar wata mutuniyar kirki,sanyin ACn dake ɗakin ne ya hana ta yin zufa,da tabbas yanda ta ƙunshe kanta da mayafin nan sai ta jiƙe sharkaf kafin angon ya shigo. Sallama ya yi mata da muryarsa mai sanya ta jin kamar ta dawwama a kwance a ƙirjinsa dan ta dinga jin fitar sautin ta,a hankali ta amsa masa sallamar tare da sake gyara mayafinta. Murmushi Aminullahi ya yi,wanda da ka gani ka san bai kai zuci ba. A zaton sa tinda ya auri Layuzah zai ji tsantsar farinciki kuma ya manta da Lailah ƳAR RAWA,sai gashi har yanzu da yake tsaye a gaban Layuzah gani yake yi da ya ɗaga mayafin Lailah zai gani zaune tana yi masa murmushin da ya ga tana yi wa wannan ƙashi da ran(Afrah). Cikin sanyin jiki ya zauna a gefen gadon sannan ya ɗaga mayafin nata,murmushi ta sakar masa ta sake sadda kanta ƙasa,kasa mayar mata da martanin murmushin ya yi sai kawai ya miƙe ya ce mata. "Ki je ki yi alwala ki zo mu gabatar da nafila,bari na je na ɗakko abu a mota na yi mantuwa." "To,a dawo lafiya mijina." Tsayawa Aminullahi ya yi yana maimaita kalmar Mijinta da ta kirasa da shi,jin abun ya yi wani iri,bai bar ɗakin ba har sai da ta miƙe ta cire mayafin da aka naɗa mata a jikinta ya rage daga ita sai wata yaluwar riga doguwa wadda ta ɗame ta sosai,rigar tana da dogon hannu da wuya mai faɗi sosai wanda da ta duƙa za a hango ƙirjin ta,Layuzah na sane ta durƙusa ta ajiye jakarta a gefen gadon,Aminullahi na ganin yanda ƙirjinta ya fito ya yi saurin barin ɗakin ya nufi motarsa,ya jima a tsaye ya na tinanin yanda zai kai kansa wajen wata macen da zuciyarsa sam bata son ta ballantana kuma ƙaunar ta,shi bai ma san me yake ji akan Layuzah ba,a hankali ya furta. "Me yasa na yi wannan auren ne wai?" Zuciyarsa ce ta bashi amsa da. 'Dan ka guje wa soyayyar Lailah da ta yi maka mummunan kamu ne.' Kaɗa kansa ya yi da sauri ya na ƙaryata zuciyarsa,cikin ɗaga murya ya ce. "Ina ba na son karuwa,Allah Ya min tsari da auren Karuwa,yanda ban taɓa zina ba ina roƙon Allah da ya tsare ni da auren Karuwa." Ledar da ya siyo kazar amarcin su da lemuka tare da fruits ya ɗauka ya sake kulle motar ya nufi cikin gidan. Ita kuwa Layuzah ruwa ta watsa a fuskar ta ta wanke kwalliyar da aka yi mata,sannan ta wanke ƙafarta da bakin ta,ko fitsari ta ki yi dan bata ji dama,ballantana ta wanke maganin da ke jikinta,tana fitowa ta saka wasu kayan bacci da ke cikin jakarta na musamman,dan ba ma a cikin lefenta suke ba,na musamman ta siyo su,sai ta ɗauki laffaya ta yafa ta shimfiɗa musu abun sallah ta zauna tana jiran dawowar sa. Da sallama a bakin sa ya shiga ɗakin,amsawa ta yi ya kalle ta ya ga yanda ta zauna tana jiran sa,murmushi ya sakar mata ya ajiye ledar a gefe sannan ya tada sallah,zamanta ta yi a bayan sa ba tare da ta tada sallar bama,sai da ya yi zaman tahiyar ƙarshe ne sannan ta gyara zamanta kamar mai yin sallah suka sallame a tare, addu'o'in da suka zo a sunnah kowanne ango yana yiwa amarya ya dafa kanta ya yi mata sannan ya jawo naman kazar suka fara ci,cike da jin kunya Layuzah ta dinga karɓar naman ta na ta narkewa a jikinsa,nan take Aminullahi ya hau tunawa da hannun Lailah da ya riƙe,shine hannun macen da ba muharramarsa ba na farko da ya fara riƙewa a duniya,kuma akan sa ne ya fara jin abubuwan da bai taɓa ji ba a rayuwarsa,yanayin jikinsa ne ya fara sauyawa, kamannin Layuzah ne suka juye suka koma masa kamar na Lailah,a zafafe ya ja ta jikinsa ya na aika mata da manyan saƙonni,da jin haka sai Layuzah ta saki jikinta ta fito da maitar ta a fili. Sun ɗauki kusan awa biyu suna abu ɗaya har sai da Aminullahi ya samu abinda yake so,cike da tsaki ya miƙe ya shige banɗaki,ruwa ya sakarwa kansa ya na jin baƙin cikin yanda ya samu Layuzah a cikin ransa,sai dai duk yanda ya so a lokacin ya janye daga gare ta ya kasa saboda wani irin abu da ya ke fizgarsa gare ta,ya na cikin wankan Layuzah ta shiga banɗakin tana wata karairaya,ta riga ta san sun kulle bakinsa babu yanda zai yi da ita dan ya same ta ba a budurwa ba,dan haka dole ne ta ɓarje amarcinta kafin ya koma Kano ya barta da kaɗaici. Manne masa ta yi suka sake ɓata lokaci a banɗakin. Daren ranar gaba ɗaya Layuzah bata bar Aminullahi ya rintsa ba har sai da ta sa shi makara zuwa sallar asuba. Cike da takaicin dake cin zuciyarsa ya tafi masallaci yana ta zabga tsaki,ya rasa yanda zai yi ya fitar da abinda yake ji a ransa,ji yake yi kamar ya kama ta ya rufe ta da mugun duka,sai dai ta ya zai doke ta bayan ko kalma ɗaya mummuna ya kasa furta mata? Bayan an yi sallah ya yi azkar ya dawo gida da misalin bakwai da rabi na safe,ya zaci zai ga Layuzah ta yi wanka ta yi sallah wataƙila ma ta gyara gadon da duka yamutsa a daren jiyan,sai ya same ta tana cin soyayyan ƙwai da shayin da ta haɗa mai bala'in kauri,kallon sa ta yi bakinta cike da ƙwai ta ce. "Mijina taho ka ci abinci dan ka samu ƙarfin jikin ka,ina shiga kitchen ai na ga akwai kayan abinci shi ne na soya mana ƙwan." Babu musu ya je ya zauna ta tashi ta haɗo masa shayin ta kawo masa tare da ragowar kazar da suka rage ta ajiye musu,abinci suka ci suka ƙoshi ta shiga banɗaki ta watsa ruwa ta yo brush,magungunanta ta ɗauka ta sha ta matsa na matsawa ta goga na gogawa sannan ta koma gado inda Aminullahi ya kwanta ya na lumshe ido saboda wani irin bacci yake ji,har yaji idanuwansa ke yi masa. Jin ta fara shafa shi ne ya sanya shi miƙewa ya na so ya yi mata magana dan ta barsa ya huta,sai ya ji ta haɗe bakin su waje ɗaya,tsananin mamakin yarinyar da aka ce ita ɗin budurwa ce yake yi,yanda Layuzah ta ke sarrafa shi ne ya mantar da

Chapter 14 of 30