su ji haushi su ce ya mayar musu da kuɗin su,wasu kuma su bar masa,shi dai ya san koma ina aka je aka zo zuwan Lamyah rayuwarsu babban arziƙi ne.
Rawa suka yi ta kimanin awa ɗaya sannan suka sauka daga stage suka koma ɗakin da suke zama idan sun gama Faisal ya sallame su,babu ɓata lokaci kuwa ya shiga yana washe baki,cike da farin ciki ya sanar da Afrah abinda ke faruwa na kuɗaɗen da ake bashi akan su,yamutsa fuska ta yi cike da gajiya ta ce.
"Kai ma ka san ba ɓangaren mu bane wannan,kawai bamu kason mu mu yafce gida."
"Yes na sani,amma..."
"Babu amma a wannan maganar,ka bamu kasonmu mu ware."
Lamyah na gefe ta na zira abayarta ta ɗauki wayarta ta kira Bala,babu bata lokaci ya ce su bashi minti goma zai iso dan ya riga da ya kamo hanya dama.
Bayan Faisal ya sallame su da manyan kuɗi,wanda har ta account ɗin Afrah ya tura musu wasu sai ya raka su har waje yana ta yi musu daɗin baki koda Lamyah za ta yi magana ya sake jin muryarta,haka kawai ya ji yana so ya haɗa ta da abokinsa na Niger,dik da cewa ya tsani hulɗa da mata to fa tabbas zai so wannan,cike da bugun ciki ya ke son ya ji asalin Lamyah,dan sam bata yi masa kama da mutanen mu na Nigeria ba,a iya maganar da ya ji ta yi tin haɗuwar su zuwa yau ya fuskanci babu cikakkiyar hausa a bakinta,ya yi zaton buzuwa ce sai ya ji tana jefa turanci da larabci a maganar ta kuma hausar ta ba irin tasu bace,sannan kuma bata yi masa kama da fulani ba balle ya ce ko mutuniyar Yola ce,ya rasa a ajin da zai saka ta, shi yasa yake ta nacin son sanin wacece ita,amma sam Afrah ta ƙi bashi dama,ƙarshe ma ce masa ta yi asalin sunan ta LAILAH,shi yasa take son waƙar Lailah,kuma a kano aka haife ta unguwar su ma ɗaya.
Lamyah na tsaye a wajen aje motoci motar Aminullahi ta shiga cikin hotel ɗin,cike da tsantsar farin ciki Faisal ya nufi Aminullahi yana washe baki,sai da ya gama parking motarsa ya fito fuskar nan babu ɗigon annuri a cikinta sannan ya miƙa wa Faisal hannu suka gaisa. Cikin haɗe fuska da ɗan jan tsaki ya kalli Afrah ya kauda kai,itama tsakin ta ja sannan ta ce.
"Sister zo mu bar nan mu jira Bala a waje,wannan ɗan rainin ya iso,ita dai rayuwar nan bawa bai isa ya ce baya aikata zunubi ba koda kuwa ɗan gidan limamin makka ne shi."
Tana gama faɗar haka ta ja hannun Lamyah da ke kallon Aminullahi cike da son gano inda ta taɓa ganin fuskarsa,wani irin bugu zuciyarta take yi mata kamar za ta tsaga ƙirjinta ta fito waje,lumshe kyawawan idanunta ta yi a saman fuskar sa a daidai lokacin da ta zo giftawa ta gabansa,da sauri Aminullahi ya kaiwa idanunta da ke a waje kallo, wani irin bugawa zuciyarsa ta yi da ƙarfi har sai da ya jingina a jikin motarsa ya na ci gaba da bin bayan Lamyah da kallo,Faisal na ganin haka sai ya tintsire da dariya ya tafa hannayen sa,cike da shaƙiyanci ya kalli Aminullahi ya ce.
"Kai ma ka ga abinda kowa ya gani ko? Man idan ka amince kana son yarinyar nan,zan shiga na fita ko ta halin ƙaƙa ne ta amince da kai,saboda ba ƙaramin dacewa kuka yi da juna ba."
Tsaki Aminullahi ya sake ja a karo na babu adadi sannan ya ɗauke kansa daga kallon Lamyah da take ƙoƙarin shigewa mota,abinda ta rufe fuskarta da shi ta sake ja ta rufe sosai,sannan ta duƙar da kanta tana kallon dogayen yatsun hannayenta,idanunta da zuciyarta cike suke da hoton fuskar Aminullahi,daf Bala zai juya da mota Aminullahi ya sake ɗaga kai ya kalli Lamyah da ta ɗaga kai ta sake kai dubanta gare shi,a tare suka sauke wata ajiyar zuciya kafin Bala ya take motar ya bar harabar hotel ɗin.
Cikin wata iriyar murya Aminullahi ya ce.
"Yunwa nake ji,na rasa abinda zan ci a gida shi yasa na shigo na ci abinci,dan Allah kar ka sake yi min tallar matan da basu san darajar kan su ba,ni idan zan yi aure sai na zaɓo yarinya mai tarbiyya,ƴar gidan mutunci,ballantana ma ni da ka ganni ɗin nan na riga na siyar,dan kuwa ina da matar da zan aura,ƴar gidan manyan mutane masu karamci da mutunci,Allah Ya yi min tsari da auren ragowar titi."
Girgiza kai kawai Faisal ya yi,dan ya kula babu abinda zai cewa Aminullahi ya yarda su Lamyah ba karuwai bane,wajen cin abinci Aminullahi ya wuce shi kuma Faisal ya koma wajen sana'ar sa,sai da Aminullahi ya gama komai sannan ya kira Faisal a waya,yana ɗauka ya ce masa.
"Ka gama mu wuce ne ko kuma na yi tafiya ta?"
"Ah ah ɗan jira ni dan Allah,yanzu zan sallami su Saly na zo."
Tsaki Aminullahi ya ja sannan ya ce.
"Allah Ya sa su Sady ne ba Saly ba,dalla kar ka ɓata min lokaci bacci nake ji."
Kashe wayarsa ya yi yana sake riƙe ledojin da ya yi take away zai kai wa Malam Isa da kuma wanda zai ɗumama da safe ya ci kafin ya shiga kasuwa. A haka Faisal ya riske shi zaune yana sauraron karatun ƙur'ani a motarsa,wasu mata ƴan bariki na ta kaiwa da komowa a gefensa wai ko da zai kira su. Faisal na zuwa ya ja tsaki ya tada motar sa,yana shiga ya ce.
"Wai kai baka gajiya da jan tsaki ne,sai ka ce wani tsaka?"
"To da alama tsakar ne."
Daga haka babu wanda ya sake cewa komai har suka bar hotel ɗin,suna zuwa unguwar su ya ajiye Faisal a farkon layin su,wanda ya kasance gida ne na mutanen da ba su da ƙarfi sai rufin asirin Allah,da wannan sana'ar ta kawalci da kai mata su yi rawa a hotel Faisal ya ke amfani ya ci da iyayensa har ma ya gyara musu gidan musamman sashensa. Duk da cewa iyayensa sun san abinda yake aikatawa basu taɓa zaunar da shi sun hana shi ba,mutanen unguwa sun yi magana har sun gaji. Aminullahi kuwa har ya gaji da yi masa wa'azi,har cewa ya yi zai ɗaukesa aiki a manyan shagunan su yana biyansa albashi mai tsoka amma ya ƙi,a cewarsa a fita ɗaya ma sai ya samu babban kuɗin da Aminullahi zai bashi a wata,duk da cewa har yanzu idan ya samu manyan kuɗin ba zai ce ga a inda yake kashe su ba,amma dai ya fi son ya dinga ganin manyan kuɗi kullum akan ya je ya yi wahala da jikinsa sannan ya jira sai wata a bashi.
Aminullahi na ƙarasawa gida ya miƙawa Malam Isa ledar hannunsa sannan ya wuce cikin gida,duk wani motsin da yake yi idanun Lamyah ne ke gilmawa a zuciya da ƙwaƙwalwarsa,tsaki ya ja mai ƙarfi kafin ya rufe fridge ɗin da ya buɗe da ƙarfi, ɗakinsa ya wuce ya watsa ruwa sannan ya fito ɗaure da babban towel ɗin da ya rufe tin daga saman cibiyarsa har ƙaurinsa,ba tare da ya shafa mai ba ya fesa turare ya sa roll on sannan ya saka kayan bacci,abun sallah ya shimfiɗa ya yi nafila dan kuwa ya jima da yin sallar isha'i tin sanda lokacinta ya shiga,yana idarwa ya yi addu'o'in da ya saba yi,tare da fatan Allah Ya bayyana masa Lamyah da Mubarak cikin ƙoshin lafiya,sannan ya miƙe ya kashe fitilun ɗakin ya haye gado, addu'ar bacci ya yi sannan ya kwanta da ɓangaren damarsa ya kulle ido yana karanta ƙulhuwallahu-ahad guda goma,wadda duk daren duniya yake karantawa idan ya zo bacci saboda kwaɗayin samun ginannen gida a aljannah da Allah Ya alƙawartawa masu karantawa.
****************************
Su Lamyah basu isa gida ba sai da misalin sha biyu na dare, Baba Musa ransa bai yi masa daɗi ba,amma haka ya ɗauke kai saboda ya sani bashi da ƴancin hana Lamyah yin abinda ta ga dama a matsayinta na uwar ɗakinsa,sai dai ya ƙudirta a ransa zai yi mata nasiha,ko da rawar za ta yi to fa kar ta dinga jimawa a waje,dan kuwa zamani ya sauya,kiwon mutum ake yi yanzu ba dabba ba,kafin su farga mutane za su sanya musu ido ta jawa mahaifinta da yake mutumin kirki zagi a unguwa.
Kwance suka tarar da Mubarak a cikin net a tsakar gida a saman katifar Bala,nan take Lamyah ta ji gabanta ya faɗi,anya kuwa ta kyauta abinda ta yi? Mubarak fa amana ne a wajenta,iyayenta sun ce ta kula da shi kamar yanda za ta kula da ɗan cikinta,to yanzu idan ɗanta ne haka za ta dinga fita rawa ta na barinsa wajen masu gadi? Cikin sauri ta durƙusa ta ɗauke yaron ta wuce da shi cikin gida,idanunta na kawo ruwan hawaye.
A gado ta kwantar da shi kafin ta hau duba jikinsa,da alamun baya tare da yunwa ya ci abinci,zama ta yi a gefensa ta na dafe goshin ta tare da shafawa a hankali,fuskar Aminullahi kawai take gani,shiru ta yi tana sauraren bugun zuciyarta,ta jima a haka kafin ta fita parlour,Afrah ta gani tana sallah,cikin sauri ta wuce ta ɗauro alwala itama ta tada sallah,sai da suka idar ne sannan suka zuba abinci suka ci,suna tsaka da hira ne Lamyah ta ce........
[9/11, 10:50 AM] zee hussain: ƳAR RAWA.
RUBUTAWA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✍️✨
PAGE 20.
"Me zai hana mu samo wadda za ta dinga kula da Mubarak idan mun fita? Dan gaskiya jiya ban ji daɗin yanda na dawo na gansa a waje yana bacci ba,kula da yaro ƙarami kamarsa dole sai mace,ba aikin maza bane,kuma kin ga Bala zai fara jarabawa,zai iya ɗauke masa hankali daga karatunsa."
"Haka ne,ki bari zuwa gobe da yardar Allah zan yiwa wata dattijuwar kirki dake bayan gida na magana,matar tana da mutunci ƙwarai,babu ruwanta da shiga sabgar da babu ruwanta,shi yasa duk zagina da mutanen unguwa suke yi kallon su kawai take yi,a duk sanda ta ga na yi wani abu da ba daidai ba har gida take kirana ta yi min faɗa,gata da wadatar zuciya, talaka ce tilif kamar ni,dan gidan da take ciki ma ɗaki ɗaya ta karɓa haya da ƙyar take biya,amma sam bata damu da abun hannun kowa ba,neman na kanta ta sa a gaba."
"Allah sarki,ina mijinta da yaranta to?"
"Sun rabu da mijinta sakamakon duk ta haihu yaran na yin wabi,abinda ake nufi da hakan shine idan mace ta haihu sai yaran su koma tin suna yara,to sai ya ƙara wani auren suke cin duniyar su da tsinke da amaryarsa ita kuma ya sake ta,sanin cewa bata da kowa ne ya sa ya ci gaba da biya mata haya,daga baya kuma sai ya dena,to shine ta miƙe take sana'o'inmu na cikin gida,a haka take samun taro da sisi."
"Allah sarki,ta bani tausayi sosai,a tambayota ta zo mu zauna anan ta dinga kula mana da yaro idan mun fita hankalin mu zai fi kwanciya akwai mai kula da shi,sannan dole ne mu rage lokacin dawowa,tinda gaba ɗaya idan mun je ba ma yin aikin da ya wuce na awanni biyu,me zai hana ki sanar da Faisal za mu dinga hawan farko, kin ga duk abinda za mu yi tara zuwa goma na dare mun dawo gida."
Cike da murna Afrah ta ce.
"Kaiii amma na ji daɗin shawarar nan taki Lamyah,me yasa da ban taɓa yin wannan tunanin ba?"
Murmushi Lamyah ta yi sannan ta ce.
"To ai gashi nan yanzu an taya ki yi."
Daga haka suka tattara komai suka shige ɗaki domin yin bacci,Afrah ta yi mamakin babban ɗaki da ke ɗauke da ƙaton gadon da Lamyah ta ce ta kwana a ciki, addu'a ta dinga yi kar ta makara sallahr subh saboda daɗin gadon.
Washegari da asuba bayan sun yi sallah a tare suka zauna suka yi karatun ƙur'ani,Lamyah ta yi mamaki sosai da ta ji yanda Afrah ke baiwa kowanne harafi haƙƙin sa,azkar suka yi suka tashi,Afrah ta hau gyaran gidan duk da ba wani datti ya yi ba. Ta na gamawa ta hau yi musu abun karyawa,babu jimawa ta kammala,suna zaune suna karyawa Mubarak ya farka daga bacci ya fito yana murza idanunsa,gashin sa irin na larabawa ya hargitse,a shagwaɓe ya ce.
"Mommy zan yi pupu."
Da sauri Afrah da Lamyah suka miƙe a tare suka nufe sa,cikin barkwanci Afrah ta ce.
"Kai bawan Allah kashi ake cewa meye wani pupu? Yau tinda gani ai ni zan wanke maka idan ka gama ba Mommyn taka ba."
Noƙe kafaɗa yaron ya yi ya isa wajen Lamyah ya faɗa jikinta yana yiwa Afrah dariya,rungume shi Lamyah ta yi tana dariya tare da sumbatarsa ko ta ina kafin daga baya ta ce.
"Yi zaman ki ki huta ƴar'uwa,yau yaron Mommy ita yake so ta wanke masa pupu ko?"
Ɗaga mata kai ya yi yana dariya kumatunsa na lotsawa,ƙara sumbatarsa Lamya ta yi saboda hango tsananin kamanninsa da Baaban su da ta yi,wanda a da sai ta rasa shin da wa Mubarak ya fi kama ne,Ammin su ko Baaban su? Ko kuma ita yayarsa? Da wannan tunanin ta kai sa banɗaki ta gyara shi bayan ya gama uzirinsa ta wanke masa baki sannan suka fito parlour. Abinci ta haɗa masa shima ya fara ci yana ta bata labarin abinda ya faru bayan tafiyar su,wani ta gane inda aka dosa wani kuma haka za ta yi ta gyaɗa kai tana dariya,dan bata gane komai ba.
Da misalin goma da rabi Afrah ta nufi gidan Tani,tana zuwa ta same ta ta yafa mayafi tana kara ƙofar ɗakinta za ta fita,gaishe ta Afrah ta yi,Tani ta amsa cike da matsanancin farin ciki,zuciyarta na son Afrah. Buɗe ɗakinta ta yi suka shiga,ruwan koko ta ɗakkowa Afrah ta miƙa mata,murmushi Afrah ta yi ta ce.
"Mama Tani a ƙoshe nake na gode,yanzun nan na tashi daga kan kwano,kin san ƴar taki bata wasa da abinci."
"Allah sarki,to sannu da zuwa,na ji daɗi da kika tuna da ni kika kawo min ziyara yau."
"Nima na ji daɗin ganin ki mun kwana biyu bamu haɗu ba,ammm dama na zo ne neman alfarma a wajen ki."
"Too alfarma Afrah? Kuma a waje na? Ni kuwa me nake da shi da zan yi miki?"
"Ke kuwa ki ke da komai,ga ki da rai da lafiya? Yauwa ina wannan sabon gidan nan na ƴar Maitaimakon Balaraben nan?"
Shiru Tani ta yi tana nazari,kafin daga baya ta ce.
"Eh na gane shi,na layin ku ko?."
"Yauwa shi,dama yarinyar ce take neman wadda za ta dinga taimaka mata da aikace-aikacen yau da gobe da kula da ƙaninta,sai kika faɗo min a rai na ce bari na zo na sanar da ke."
Ƙwalla ce ta taru a idanun Tani,cike da murna ta hau godiya tare da sanyawa Afrah albarka,cikin kukan da ya ƙwace mata ta ce.
"Dan Allah ina neman alfarma na dinga yi mata aikin kwana,ni ko a tsakar gida ne aka barni zan kwana,kuɗin haya na ya ƙare,gashi ana bina na watanni uku ban biya ba,to ana ta abinda za a sanya wa hanji wa yake ta kuɗin haya? Da wanne bawa zai ji? Gashi aikin da nake yi a gidan Alhaji Sammani babu,sannan yanzu bani da ƙwaƙƙwarar sana'a."
Hawayen tausayin Tani Afrah ta share kafin ta ce.
"Mun gama magana da ita dama,ta ce idan kin amince aikin kwana za ki dinga yi mata tana biyan ki dubu goma duk wata,za ki ci za ki sha a ƙarƙashin ta,sannan za a baki ɗakin ki na musamman,fatan ta kawai ki riƙe amana kuma ki kular mata da ƙaninta yanda ya dace."
"In dai wannan ne babu damuwa."
Da haka Afrah ta miƙe ta yiwa Tani sallama,sun tsayar da cewa zuwa anjima za ta gama duk abinda take yi ta zo. Afrah na komawa sai ta sanar da Lamyah yanda suka yi da Tani,cike da farin ciki ta ce.
"Alhamdulillah,kin ga idan ta zo sai ta ɗauki wancan ɗakin kusa da kitchen da store,akwai babbar katifa da duk abinda zata buƙata a ciki,Allah Ya sa zuwanta ya zamo mana alkhairi."
"Amin Ya Allah."
Tin daga wannan ranar Tani ta dawo aiki a gidan Lamyah,basu wani jima ba suka shaƙu da junan su,kasancewar Tani mace mai nastuwa da kamun kai,Lamyah kuma yarinya mai biyayya sai zaman nasu yake daɗi,matsala ɗaya suka samu ta ɓangaren Mubarak,kafin ya saba da Tani sai da aka kai ruwa rana da shi,kyautatawar da take yi masa ne ya sa ya dena gudunta yana kiranta da dodo,saboda baƙinta da ya yi yawa. Lamyah kuwa dariya ta yi sannan ta ce.
"Allah Ya jiƙan Ammin mu yaro,da tana raye da ka gane daga tsatson da ka fito."
Cike da mamaki Afrah ta ce.
"Kina nufin mahaifiyar ki ba fara bace?."
"Ƙwarai da gaske,ai da yanda take haka nake,daga baya ne na washe na yi haske haka,ai saboda duhu na ne yasa Yah Amee ke ce min Lamyah."
Bayan watanni uku Afrah da Lamyah na zuwa wajen rawa,wanda a wannan lokacin duk wata rawar Africa da irin ta kaɗe-kaɗen mutanen kudu babu wanda Lamyah bata iya ba,ita kuma Lamyah ta koyawa Afrah irin rawarsu ta Larabawa. Da wannan suke hawa stage su tashi kan ƴan kallon su.
Ta ɓangaren Aminullahi kuwa daidai da rana ɗaya bai taɓa cire tunanin Lamyah daga ransa ba,wanda har ta kai ta kawo ya kan je hotel ɗin ko da kuwa bashi da abinda zai yi,sai ya samu nesa da su ya zauna ya na kallon shige da ficen su,daga ƙarshe ma har tambayoyi ya dinga yiwa Faisal akanta,sai dai idan Faisal ya nuna masa lallai fa ya kamu da soyayyar Lamyah sai ya ƙaryata hakan,tare da neman tsari akan auren karuwa. Ita ma Lamyah a duk sanda ta gansa ko ya faɗo mata a cikin ranta sai ta nemi tsari da hakan,saboda ta riga da ta san har abada ba zai taɓa son ta ba,tinda ya tsane su,kuma kallon karuwai yake yi musu,sannan kuma ta riga da ta dasawa zuciyarta har abada bata da miji sai Yah Amee ɗin ta,dan haka bata ga dalilin sakewa zuciyarta ba har ta kamu da soyayya daga baya ta zo tana shan wahala.
Yau ma kamar kullum su Lamyah ne ke shirin fita da misalin bakwai da rabi na dare. Sai da suka kammala komai suna shirin fita marar Afrah ta riƙe gam,zama ta yi a bakin kujera tana taɓe baki kamar za ta yi kuka,cike da damuwa ta kalli Lamyah da ta rikice ta na tambayar ta me yake damunta ta ce mata.
"Shikenan sai dai ki tafi ki barni,ba zan je ba."
Zaro ido Lamyah ta yi kafin ta ce.
"Me ya sa?"
"Yau ma baƙona ya zo ba tare da na shirya ba,ina ga dai kwanakin ne suka sauya min."
Tura baki Lamyah ta yi gaba tare da faɗin.
"A gaskiya sai mun je,sai dai idan mun je ki zauna a mota ni kuma na shiga yi idan na gama mu dawo gida tare."
Ganin Afrah ta miƙe a kujera bata da niyyar tashi ne ya sanya Lamyah haɗe fuska ta sumbaci Mubarak ta ɗauki jakarta ta bar parlourn,dan kuwa ta sam duk abinda za ta ce wa Afrah to fa tana da amsar bata a daidai wannan lokacin,Afrah na ganin haka sai ta kwashe da dariya tayi wucewarta banɗaki ta gyara jikinta. Lamyah kuwa mota ta shige Bala ya wuce da ita hotel,suna zuwa ta wuce wajen sauya kaya dan ta yi ta kammala da wuri ta koma gida,tinda tun a hanya ta yiwa Faisal message ta ce tana so ta yi hawan farko. Tana kammala sanya kayanta wanda suka fito da fatarta da ta sha gyaran jiki da cucumber,carrot,zuma, ƙwai,coffee,madara,sugar,gishiri,da kuma kurkur,sai sheƙi da ɗaukar ido take yi.(Za ku iya samun kayayyakin gyaran jiki ciki da waje har ma da koyon sana'a a littafina na MAIDA TSOHUWA YARINYA,wanda yake akan farashin 1500,ku neme ni a wannan lambar 09031416423)A haka ta ratse mutane ta haye stage aka fara sanya mata waƙoƙin zamani da ke tashe,ita kuwa sai rawa take yi cike da ƙwarewa da jin wani tsantsar farinciki saboda cika burin rayuwarta da ta yi na zama cikakkiyar ƳAR RAWA. Wasu matasa ne suka taso su uku suka zo daf inda take rawa suka hau watsa mata kuɗi kamar basa so,kallon su ta yi taga yanda suke yi mata wani irin kallo kamar sun ga naman miya. Da sauri ta ɗauke kanta daga kallon su ta ci gaba da taka rawar ta. Ɗaya daga cikin matasan nan ne ya yi dabarar wurga mata kuɗi har yana shafar cinyarta,cikin sauri ta kalle shi tare da kafe shi da ido cike da takaici,shi kuwa jin tsananin laushi da santsin fatar ta ne ya sanya shi sake kai hannunsa a karo na biyu ya gogi ƙugunta,Lamyah kuwa bata ɓata lokaci ba wajen juyawa ta zabga masa wani irin zazzafan mari. Ajiyar zuciya tare da buɗe baki mutane suka yi,sanin wanene Khalil da halayyarsa ne ya tsorata Faisal cikin sauri ya je ya yiwa Lamyah nuni da ta sakko daga stage ɗin haka, babu musu kuwa ta sauka ta wuce gaba ranta a matuƙar ɓace. Kuɗin ta Faisal ya bata sannan ta shirya ta ɗauki wayarta ta bar wajen tana kiran Bala dan ya zo ya maida ita gida. Tana fitowa Khalil da abokansa suka sha gabanta cikin wani irin yanayi da ke fitar da tsantsar ɓacin ran sa,murmushi ya sakar mata wanda yake ƙunshe da ma'anoni masu yawa. Kallonsa ta yi rai a ɓace ta ce.
"Bani hanya na wuce."
Nan take Khalil da abokansa suka kalli junan su,Khalil ne ya ce.
"Ai na faɗa muku ba tamu bace,daga ƙetare ta ƙetaro,kun ji wata murya? Sai kace sarewa?"
Ratse su Lamyah ta ke ƙoƙarin yi,amma Khalil ya ja mata mayafin doguwar rigarta da ta rufe kanta da shi,nan take kuwa ya zame gashinta da bata ɗaure ba ya baje ya na ƙoƙarin rufe mata fuska,baya suka ja cike da tsoron ganin tsawo da yawan gashin nata,a hankali Khalil ya fara takawa ya isa gabanta ya riƙe ƙarshen gashin nata yana taɓawa,cikin wata iriyar murya ya ce.
"Baby ki yarda dani ko na mintuna talatin ne,ni kuma na yi miki alƙawarin zan baki duk abinda kike so a duniyar nan."
A wulaƙance Lamyah ta kalle shi ya tofa masa yawu a fuska,sannan ta gegare shi ta wuce,hannu ya sa ya dangwalo yawun nata ya shinshina yana wani lumshe ido,cike da ƙwarewa a harkar bariki ya ce.
"Ka ji wani yawu mai ƙamshin banana? Na rantse ko nawa ne zan kashe na samu yarinyar nan,kai Bunyamin ku yi mata ɗaukan amarya ku kawo min ita ɗaki na."
Lamyah na jin haka gabanta ya yanke ya faɗi,duk da bata san menene ɗaukan amarya ba,amma tabbas ta ji kalmar a ɗauketa a kai masa ita ɗakinsa,dan haka cike da matsanancin tsoro ta ƙara sauri za ta bar wajen,wanda Khalil ya kira da Bunyamin ne ya isa gabanta ya sa hannu zai ɗauketa,mari Lamyah ta zabga masa,bai yi wata-wata ba kuwa wajen kwaɗa mata wani gigitaccen mari,ƙara ta ƙwalla ta faɗi a wajen tana kuka,Faisal ne ya fito wayarsa riƙe a hannusa ya ce.
"Kai Khalil dan Allah ku rabu da ita,na faɗa maka ita bata wannan layin,ga mata nan kala-kala ka zaɓa mana a cikin su,dole ne sai ita?"
Murmushi Khalil ya yi kafin ya kalli Faisal,sannan ya kalli Lamyah da ke kuka ya nunawa Faisal ita ya ce.
"Kai yanzu idan aka baka wannan,sannan aka baka matan nan namu ragowar caro white wacce za ka ɗauka?"
Shiru Faisal ya yi yana kallon hanyar shiga hotel ɗin kamar mai jiran wani,har ya buɗe baki zai yi magana motar Aminullahi ta shiga hotel ɗin,murmushi Faisal ya yi sannan ya ce.
"Na ce muku ku ƙyale ta kun ƙi ko? Na tabbata yanzu dole ku rabu da ita ai ko ba don Allah ba."
Daidai lokacin da Bunyamin ya ɗauki Lamyah a ka Aminullahi ya ɓalle marfin motarsa da bai gama kashewa ba ya fito,ya na zuwa bai tsaya ɓata lokaci ba ya kwashe Bunyamin da mari,ganin haka sai Bunyamin ya dire Lamyah ƙasa. Cike da hargagi Khalil da ɗaya abokin nasa suka yi kan Aminullahi da zuciyarsa ke tafarfasa da baƙin ciki,a harzuƙe Aminullahi ya dinga loda musu naushi da duka,ganin ba za su iya masa bane ya sanya su guduwa suna faɗin.
"Idan kere na yawo zabo na yawo watarana za su haɗu ne."
Ba tare da Aminullahi ya ce komai ba ya damƙe hannun Lamyah dake kuka ta na ɗaukan wayarta a ƙasa zata sake kiran Bala ya ja ta ya buɗe motarsa ya wurga ta ciki. Zagayawa ya yi mazaunin direba ya shiga tare da juyawa da
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 30