Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
bata koma bacci ba,shirin tarbon Afrah ta shiga yi kamar za ta sauki shugaban ƙasa a gidan. Momma sai mamakin yanda Lamyah take rawar ƙafa akan zuwan Afrah take yi,Abii kuwa sai ya zauna ya dinga basu labarin Afrah,da irin rayuwar da suka gudanar da Lamyah a baya,jinjina shaƙuwarsu Momma ta yi,sannan itama ta taya Lamyah shirin tarbon babbar baƙuwa Afrah....... [9/11, 10:50 AM] zee hussain: ƳAR RAWA. RUBUTAWA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✍️✨ PAGE 36. Lokacin da su Afrah suka iso Niger Lamyah ta so matuƙa aje ɗakko su da ita,sai dai Iya ta hana ta ce ta yi haƙuri har su ƙaraso gida,Mubarak kuwa gwalo ya dinga yi mata yana dariya,domin kuwa ya maƙale wa driver da shi aka je ɗakko su. A harabar gidan Lamyah ta tsaya sanye da riga da skirt na leshi wanda ya karɓi jikinta sosai,yau ce rana ta farko da ta fara sanya leshi a jikinta,jin kanta ta take yi kamar ta yi tsuntsuwa ta ganta a gaban Afrah da Bala,Zahrah sai dariya take yi mata,suna tsaye Aimana ƴar gidan Baffan Aminullahi wadda jininsu ya haɗu ita da Lamyah ta ce. "Ni fa ina ga ko sun fasa zuwa ne ma,don na ga har yanzu shiru." Hararar ta Lamyah ta yi tana zumɓura baki,dariya Zahrah da Aimanah suka sanya a tare suka tafa,ƙarar odar da driver yake ta dannawa ce ta ƙara sanya wa Lamyah zumuɗi da begen ganin masoyiyarta,ana wangale gate ta hango Afrah da Bala zaune a cikin mota sai ta fashe da kukan farinciki,mota kuwa na gama tsayawa ta kwasa da gudu ta nufi wajen su,Afrah ma da sauri ta ɓalle marfin motar ta yi wajen Lamyah,rungume junansu suka yi suna kukan farincikin sake haɗuwa da junan su. Da ƙyar Lamyah ta saki Afrah ta juya wajen Bala ta na dariya tare da share hawayenta,murmushi kawai yake zabgawa shima dan kuwa ba ƙaramin murna ya yi ba da ya sake ganin Lamyah a rayuwarsa,mace ce ita mai mahimmanci a rayuwarsu,yana jin ta kamar ƴar'uwasa ta jini,ɗan haɗe fuska ya yi da sigar wasa ya ce. "Wato ni ba za a min kukan murna ba,shine aka goge hawayen aka washe min haƙori ko?" Dariya kowa ya fashe da ita,sannu da zuwa Lamyah ta yi masa sannan suka rankaya cikin gidan,Mubarak kuwa ko da wasa bai sauka daga jikin Bala ba har suka gama gaisawa da kowa aka kai su ɗakin da za su zauna shi da Afrah,ita kuwa Afrah kayanta ta kwasa ta gudu ɗakin Lamyah,a cewar ta ta gaji da ganin fuskar Bala ta na buƙatar hutu. Barkwancinta da son mutanenta ne ya sa su Momma da ƴan'uwanta masu iyayi suka dinga nan nan da ita,Momma kuwa dama tun kafin ta zo take ƙaunar ta saboda labaranta da ta ji a wajen Abii da Lamyahn. Afrah ta ɗauki Iya kamar kakarta,dan haka banda tsokana da raha babu abinda suka dinga yi da junan su,Lamyah kuwa kamar wata jinjirarta,duk inda take tana wajen,ta wani manne a jikinta kamar wadda za ta gudu ta barta. Tare suka ci abinci suka dinga hira,bayan sun kammala sun koma ɗaki ne Lamyah ta kalli Afrah ta ce. "Masoyiya ban taɓa zaton za ki yi ƙiba ba a rayuwa,kin ga yanda kika yi kyau kuwa kika yi wani fresh? Ko dai na samu ɗa ne ba a bani labari ba?" Dariya Afrah ta yi sosai kafin ta natsu tana wani irin murmushi mai kyau ta ce. "A gaskiya Lamyah ba zan ɓoye miki ba a yanzu ina son Bala fiye da yanda nake son kaina,ina ganin zan iya bada rayuwata saboda shi ya rayu,Lamyah a baya rashin wayo da sanin ciwon kai ya so ya sanya na yi asarar nagartaccen miji,a duk sanda ya ce zai aure ni gani nake yi kamar ba da gaske yake so na ba,wannan tambarin iskancin da aka yi min yake son tabbatarwa,sai gashi ya aure ni godiya ta tabbata ga Allah,kuma ina gode miki da Abii da kuka yi sanadin tabbatuwar hakan." Hawaye ne suka fara zuba a idanunta,wanda za a kira su na farinciki,bayan ta kama hancinta ta ja majina sannan ta ci gaba da cewa. "Abii ya tura wa Bala kuɗi masu yawa,ya ce ya sai mana kayan abinci har su Mama Tani,sannan ya bashi gurbin aiki a kasuwa shima yana zaman shago yanzu,ƙarshen watan nan za a fara bashi albashi. Lamyah babu abinda na nema na rasa. Soyayya da kulawa tare da tarairayar da Bala ke yi min kuwa sukan mantar da ni na taɓa shiga ƙuncin rayuwa,ya zame mini sarki mai adalci,baya son damuwata,baya maraba da ɓacin raina,ke ban san ya zan bayyana maki yanda Bala ke kyautata min ba,kawai addu'a nake yi masa Allah Ya faranta masa duniya da lahira ya yi masa albarka. Kin ga kuwa ina samun waɗannan abubuwan dole na yi ƙiba ko da kuwa ni na kawo rama duniya Lamyah. Ya Yah Amee ɗin naki? Ina fatan dai kyakkyawa ne haɗaɗɗen gaye?" Afrah ta ƙarasa maganarta tana dariya sosai. Shiru Lamyah ta yi ta sadda kai ƙasa,idanunta ne suka tara hawaye har suka fara zubowa,cikin sauri da tashin hankali Afrah ta ja ta jikinta sannan ta ɗaga kanta,ganin hawaye na zuba a idanun Lamyah sai Afrah ta miƙe tsaye jikinta na rawa ta hau kallon bakin ƙofa ta ce. "Wanne ɗan rashin mutuncin ne ya ke ɓata miki rai a cikin gidan? Ki faɗa min ko wanene shi yau kashinsa ya bushe." Murmushi Lamyah ta yi sannan ta kama Afrah ta zaunar da ita ta kwanta a cinyarta,a hankali ta warware wa Afrah wanene Aminullahi da kuma abubuwan da suke faruwa a gidan,ranta a ɓace ta ce. "Amma ai ba haka alƙawari ya ce ba,me yasa ba su jira ki ba suka aura masa mace mara tarbiyya? Zan kuwa ci ubanta na gyara mata zama kafin mu koma,kar ki kuskura ki raga wa ko wacce ƙatuwa,ballantana kishiya irin wannan mara hankalin. A gaskiya ban ji daɗi da ta kasance Handsome da muke gani a hotel ɗin su Faisal ne Aminullahin ki ba,don gaskiya idan ya raina min hankali nima zan raina masa ah toh." Dariya Lamyah ta yi sannan ta ce. "Wato dama na ji Iya na cewa,idan ka jima baka ga mutum ba,to ka tambayi halinsa,ashe naki yana nan bai je ko ina ba." Ran Afrah a haɗe ta ja tsaki saboda har cikin ranta take son yi wa Aminullahi da matarsa rashin mutunci,amma bata so a ga rashin kyautawarta,sai dai ta yi alƙawari a ranta kafin ta koma sai ta yi maganin su. A wannan rana Lamyah da Afrah kwana suka yi suna hira,sai da suka yi sallar asuba sannan suka kwanta bacci. Basu suka farka ba sai sha ɗaya na safiya. Gyaran jikin da Iya ke yi wa Lamyah a kullum aka fara shirin yi mata,a haka suka karya jikinta shafe da haɗeɗden body scrub ɗin da suka yi order a wajen mai kayan gyaran jikin nan dake Nigeria mai suna Hamibrah,Afrah ce ta zo musu da shi,sai da aka gama murje mata fata da shi ta wanke da ruwan ɗumi,sannan aka mulke mata jikinta da skin oil,Afrah na ganin yanda Lamyah ke wani santsi da sulɓi a ido ta gigice,cikin murna ta ce. "Ai da na san da wannan mai gyaran jiki nima da na siya na yiwa Bala gyara,gaskiya da na koma nima zan nemeta na siyi nawa,ya aka yi kika santa?" "Momma ce ta santa,ita ce ta yi order da ta ji za ki zo ta ce akai can ku taho da shi,shi yasa ai kika ga an kawo muku a airport,don da wani yaron shagon Abii ɗan Niger mazaunin kano za a bawa ya kawo min." "Allah sarki,wannan ce No ta da aka kira ni da shi 09031416423?" "Ɗaurki ledar scrub ɗin ki tabbatar." Afrah na dubawa sai ta ga ashe ita ce,nan take ta yi saving No suka ci gaba da zuzuta yanda Lamyah ta yi kyau. Kwana biyar Iya ta ɗauka tana gyara Lamyah,banda abubuwan ci da sha da Momma kan shiga kitchen da kanta ta haɗa wa Lamyah,tana yi tana tina Aminee,domin kuwa haka ta dinga yi mata a da tana bawa Iya ta kai mata. Tinda aka fara shirye-shiryen hidima Aminullahi da Layuzah basu leƙa ba,sai dai da yake Layuzah ƴar bariki ce sai ta dinga yi wa Momma waya ta na bada uziri akan Aminullahi ne bashi da lafiya har yanzu,shi yasa bai leƙo ba. Duk abinda ke faruwa Afrah na ji kuma tana gani,fatanta kawai ta ɗora ido akan matar Aminullahin. Wata haɗaɗɗiyar walima aka gudanar a cikin gidan Abii,manyan mata ƙawayen Momma da ƴan'uwan Abii da nata sun hallara,sai ɓarin dukiya ake yi wa Amarya ana yi mata liƙi,an ci an sha an kuma taka rawa,sai wulgawar kyawawan mata da gwalagwalai mai rai ke gani,Afrah duk ta gigice ta ce wa Bala ya ji tsoron Allah kar ya yi mata kishiya kafin su koma Nigeria,dariya mutane sukai ta yi mata ana jin daɗin yanda take wayayyiya kuma mai son mutane. Da dare bayan an kammala walima mutane sun ragu sosai Hajiyan Layuzah ta zo da tata tawagar,ta ci kwalliya ta baza shadda mai mugun tsada da sarƙar zinare wadda take da ita tun mahaifin Layuzah na da rai,lokacin duniyar na yi da su. Haƙuri ta dinga bayarwa ta na faɗin bata da lafiya ne shi yasa bata zo da wuri ba,ganin ƴan'uwanta sun je mata murnar auren da Aminullahi zai ƙara ne ya sanya ta warwarewa shine suka zo. Wani mugun kallo Afrah ta yi mata,a ranta ta na ayyana. 'Lallai matarnan makira ce,wai an je yi mata murna mijin ƴarta zai ƙara aure,humm ayi dai mu gani idan tusa za ta hura wuta.' Haka dai aka kawo musu abinci da abubuwan da aka raba a taron bikin,basu wani jima ba sosai suka tafi. Lamyah na nan ta na ta kuka kamar ranta zai fita,kewar iyayenta da tinanin irin zaman ƙuncin da take hangowa za ta yi a gidan mutumin da ta rayu ta girma da sonsa a ranta take,tabbas ta sani za a sha yaƙi da fama kamar yanda Iya ta faɗa mata,amma haƙurin da za ta yi da juriya shi ne zai sa ta zamo mai nasara a gaba,to ta yaya za ta iya jure wulaƙancin Yah Amee ɗinta? Dafa ta Afrah ta yi ta zauna a kusa da ita Aimanah na ganin kallon da Afrah ta yi mata ta gane so take ta bar su su kaɗai,babu musu ta ajiye pillown da ke saman cinyarta ta basu waje. Aimana na fita Afrah ta yi gyaran murya sannan ta maida hawayen dake barazanar sakkowa daga idanunta ta ce. "Lamyah ke mai haƙuri ce,kuma mai juriya akan duk wani rami da kwazazzabe da kika dinga faɗawa ki na tashi a rayuwarki,kin rasa iyayen ki da suka kawo ki duniya,kika rasa majinginar da zaki jingina ta tallafa wa maraicin ki na tsawon lokaci,don haka na san wannan sabuwar rayuwar ma da za ki shiga zaki iya jure mata kuma tabbas za ki jajirce har ki zamo mai nasara a cikinta. A da na zaci idan na ga Aminullahi zan yi masa masifata da na saba,wataƙila ma har na yayyakushe shi na cije shi tinda ya fi ƙarfina,sannan na lakaɗawa matarsa duka,to sai na zauna na yi tunani na gane rayuwar nan ba komai ne masifa da bala'i ke baka shi ba,haƙuri shine ke ba wa ɗan Adam ƴanci na har abada, don haka ki ɗauki kaf shawarwarin da Iya take baki a koda yaushe,ki yi amfani da su za ki zamo mai riba watarana,za ki juya kambun sarautar gidan mijinki a hannunki,zai zamo a tafin ƙafarki,idan kin ga dama ki taka,idan kin ga dama ki shafa. Allah Ya baku zaman lafiya masoyiyata ya kawo zuri'a mai albarka a kurkusa ta yanda zan baro Bala a Nigeria na dawo,dan ni kyawawan matan nan sun tsorata ni,ba zan sake yarda ya zo kasarnan ba ya min kishiya." Dariya Lamyah ta yi idanunta fal hawaye,a haka masu kai Amarya ɗakinta suka shiga suka tarar da su,kuka Lamyah ta sake fashewa da shi tana wani kyaɓe baki,kai da ka gani za ka san na shagwaɓa ne. Dariya sosai aka dinga yi mata,Momma ce ta ratso cikin mutane sai baza kamshi take yi tana wani walwali saboda ƙyallin zinaren da ta yi ado da su,hannun Lamyah ta kama za ta kai ta wajen Abii,har sun fara tafiya Lamyah ta tuna da jakar da Baaba ya ce ta bawa Abii,da sauri ta juya ta buɗe inda ta ɓoye ta tin zuwanta gidan ta ɗakko ta,komawa ta yi wajen Momma mutane na yi mata tsiyar ko jakar kayanta ta ɗauka. A haka suka isa wajen Abii yana zaune a ɗakinsa a bakin gado,idanunsa sun yi jawur alamar ɓacin rai,wayarsa ya ajiye wanda hakan ya tabbatarwa da Lamyah waya ya gama. Yana ganinta ya saki faffaɗan murmushi ya miƙa mata hannu,kusa da shi ta je ta zauna a ƙasa ya ɗaga ta ya zaunar da ita a gefensa sannan ya rungume ta a ƙirjinsa,kuka ta dinga yi shi kuma yana hawaye,Momma ce ta isa gare su ta ce. "Habaa Abiin su ya za ka sanya amarya kuka a wannan rana mai matuƙar tarihi? Don Allah ku yi haƙuri,ka yi mata nasiha na kai ta wajen su Tanti su miƙa ta ɗakin mijinta." Hawaye itama ta share sannan ta juya da sauri ta bar ɗakin saboda kukan da ya taho mata a lokaci ɗaya. Lamyah abar a tausaya mata ne ƙwarai,sabon da ta yi da Aminee ne yake dawo mata a rai,yau ga ƴarta da suka bar musu amanarta ta za ta auri Aminullahi wanda suke matuƙar so,amma ko ƙeyarsa babu tin da aka fara taro har yau da za a kai amarya. Kuka Momma take yi sosai ana lallashinta amma ta kasa denawa. A can ɗaki kuwa Abii ne ya yi wa Lamyah nasiha sosai,yana yi yana sharar hawaye da goge majina da tissue,da ya goge sai ya yago ya miƙa wa Lamyah ta goge nata itama,a haka ya gama yi mata nasiha,cikin dasasahiyar muryar ta ta ja jakar dake kusa da ita ta zuge ta ɗauke littafinta da iyayenta suka bata sannan ta miƙa wa Abii jakar duka ta ce. "Baaba ne ya ce na baka a duk sanda muka haɗu,daga baya kuma ina karanta wannan littafin sai na karanta inda ya ce na baka idan an ɗaura min aure da Yah Amee. Abii na gode da duk abinda kuka yi min na kyautatawa a rayuwa ta,Allah Ya ƙara girma ya ƙara maku lafiya da imani." Takardar da ya ga tambarin kamfanin El-mustapha na Dubai Abii ya buɗe,a zuciya ya fara karanta takardar har ya gagara ci gaba saboda kuka da ya ƙwace masa mai tsananin ƙarfi,Lamyah kanta da bata san me takardar ta ƙunsa ba sai ta fashe da kuka,a haka Momma ta shiga ta tarar da su,cikin kuka Abii ya ce. "A'isha zo ki ga karamcin da Ɗan'uwana ya sake yi min duk da baya raye,ya rubuta anan ya ce na raba dukiyarsa da ke hannuna huɗu,na ɗauki ɗaya ni da Aminullahi,sannan na bawa Lamyah kaso ɗaya,na kuma bawa Mubarak kaso ɗaya idan ya girma,sannan kaso ɗaya a rabawa bayin Allah mabuƙata. Ya sanar dani cewar dukiyarsa ta Dubai a yanzu ba tashi bace na sanar da yaransa,kar su girma su ce za su yi rigima da kowa akan abun duniya,kowa da arziƙin sa yake zuwa,ya yafe wa ƴan'uwasa abinda suka yi masa,da ya san su ne za su kashe shi tabbas da bai faɗi haka ba,Allah Ya isa,Allah Ya isa,mutanen nan sun cuce ni da suka raba ni da Ɗan'uwana." Wani irin tari Abii ya fara yi yana kuka sosai,Lamyah faɗawa ta yi jikinsa ta na kuka tare da roƙon sa ya cire damuwa kar wani ciwon ya kama shi,cikin matsanancin kuka ta ce. "Don Allah Abii kai ma ka yafe musu kamar yanda Baaba ya yi,ta haka ne kawai zuciyar ka za ta samu salama,ni ma na yafe musu sauran su je su haɗu da hukuncin Allah akan abinda suka aikata. Abii ka ci gaba da sanya mana albarka,idan ka bari wani ciwon ya kama ka ka tafi ka barni ba zan yafe maka ba." Kuka sosai suka dinga yi babu mai rarrashin wani,da ƙyar Abii ya yi jarumta ya miƙe ya shiga banɗaki,wanka ya yi a gurguje ya ɗaura alwala sannan ya fito,izinin zama a parlour ya basu ya ce su jira shi,suna fita ya shirya cikin wata farar shadda ya baza turare,tare da kafa hula. Idanunsa sun yi jawur,don haka sai ya ɗakko baƙin tabarau ya saka,sai ya yi wani irin kyau kamar shi ne angon. A parlour ya gansu suna zaman jiransa,hannun Lamyah ya kama sannan ya ce wa Momma. "Ni zan kai ƴata ɗakin mijinta da kai na,ki sanar da matan nan su watse gobe sun je ganin ɗakin amarya." Ta ƙofar da zata sada shi da harabar gidan ya bi shi da Lamyah,a waje suka haɗu da Afrah da Bala,Afrah sai kuka take yi tana faɗin. "Ya za ka ce na dena kuka bayan jikina yana bani kuka take yi? Zuciyata ta kasa samun natsuwa,ina jin yanda take bugu da ƙarfi Bala." Sautin muryar Abii ce ta jawo hankalin su,kallon su ya yi ya ce. "Afrah mu je mu kai ƙanwarki ɗakin mijinta ko?" Cikin sauri ta riƙe Lamyah dake kuka sosai a mayafi,a baya suka zauna Abii ya shiga cikin haɗaɗɗiyar motarsa zai ja,Mubarak ne ya fito da gudu yana kuka tare da kiran sunan Lamyah,mota Abii ya buɗe masa shima ya zauna a gefe,Bala ne ya isa gaban Abii ya durƙusa ya ce. "Abii ina neman alfarma na zama direban ƙanwata a kaita ɗakin mijinta da ni." Murmushi Abii ya yi masa sannan ya fita ya koma mazaunin gefen direba ya ɗauki Mubarak dake ajiyar zuciya ya riƙe,nan da nan Bala ya shiga mota ya tada ta,mata sai suka firfito suka hau yi musu video suna ɗaga musu hannu,a haka motar amarya ta bar gida ta shilla saman titi. A can gidan Aminullahi kuwa tinda ya gama waya da Abii jikinsa ya mutu murus,gori da munanan kalaman da Abii ya dinga yi masa sune suka rikita kwanyarsa,kewar Ammi da Baaba ne suka kanainaye zuciyarsa har suka yi sanadiyyar zubar hawayensa,me yake damunsa ne ya ke ƙin jinin mutanen da suka yi sanadiyyar zamowarsa mutum mai ilimin addini da na zamani? Me yasa ba zai karɓi Lamyah a zuciyarsa ba koda kuwa ta kasance magajiyar karuwai ƴar shaye-shaye kamar yanda Abii ya ce? Shafa kansa ya yi sannan ya hau duba ɗakin da Abii ya shaƙewa Lamyah da kaya a cikinsa, parlourn su da aka zuba sababbin kujeru da sabbin kayan kitchen sai suka sake maida gidan ya zamo sabo. Ajiyar zuciya ya sauke sau babu adadi. Yana jin ƙarar buɗe gate gabansa ya faɗi,warning ɗin da Layuzah ta yanka masa ne ya dira a cikin zuciyarsa kamar a lokacin take yi masa. 'Aminullahi idan har kana son ka rayu cikin aminci babu nakasa ko kuma ka rasa ran naka ma gaba ɗaya to ka nesanta kanka da wannan yarinyar,idan ba haka ba zan kashe ka,na kashe ta sannan na kashe kai na,ka san dai zan iya ko? Dan haka ni na wuce ɗaki na,idan munafukan ƴan'uwanka sun kawo maka amaryar sun tafi ka shigo ka same ni.' Ƙarar buga ƙofar parlour ce ta dawo da Aminullahi daga hayyacinsa,kallon ƙofar ya yi kafin ya tinkare ta ya buɗe,gefe ya koma sannan ya sunne kai ƙasa,kallon da Afrah ke watsa masa ne ya sanya shi ɗaure fuska,Mubarak kuwa tsoronsa yake ji dama shi yasa ya maƙale a jikin Lamyah da ke kuka har a wannan lokacin. Sai da Abii ya cire tabaran idanunsa suka haɗa ido da Aminullahi sannan gabansa ya yanke ya faɗi,tabbas Abii kuka ya yi,jiki a mace ya duƙa ya gaida Abii. Cikin kakkausar murya Abii ya ce. "Ni ba zan roƙe ka ka sauke haƙƙin matarka da Allah Ya ɗora maka ba,gata nan na kawo ta gidan mijinta,na bar amanarta a hannun Allah da ya halicce ta,dan haka ruwanka ne ka keta alfarmar amanar da na bawa Allah,ruwanka ne ka kyautata tsakaninka da amanar da na bari a hannun Allah,amma ka sani ba baki nake yi maka ba,muddin ka munana zama da amanar da uba ya bawa Allah mai kowa mai komai,za ka sha wahala a rayuwar ka,butulu kawai,ke Afrah tashi mu tafi,Mubarak zo nan." Hararar Aminullahi Afrah ta yi sannan ta miƙe zata wuce,a gabansa ta tsaya ta ƙura masa ido ta yi masa nuni da yatsunta biyu,ta sanya su daf da idanunsa,alamar tana ganinsa ya kiyaye, ko waigawa wajen Lamyah dake kuka tana roƙon su bar mata Mubarak bata yi ba ta fita idanunta na zubar da hawaye. Suna fita Aminullahi ya bi bayan su yana godiyar munafurci tare da sake bawa mahaifinsa haƙuri. Babu wanda ya kula sa har Bala ya tada mota suka bar gidan. Yana komawa ya tarar da Lamyah ta takure ta na gunjin kuka,cikin ransa yake jin kamar ya rungumeta ya lallashe ta,sai dai wani abu mai nauyi yake jin yana yi masa katanga da hakan. Cikin haɗe fuska ya yi gyaran murya ya ce. "Ke ! Taso mu je na kai ki ɗakin ki ki kwanta bacci nake ji ni." Ko kula shi Lamyah bata yi ba,ba kuma ta tashin ba,sai da ya isa ƙofar ɗakin nata ya juya ya ganta zaune ko alamar tashi bata nuna ba,a hasale ya koma inda take cikin faɗa ya ce. "Ke ba da ke nake magana ba!" Ido Lamyah ta ɗaga a raunace ta ƙure shi da kallo,a zafafe ya sa hannayensa biyu ya ɗauketa ya nufi hanyar ɗakin da ita,yana zuwa ya buɗe ya shiga da ita,yanda aka gyara ɗakin ga ƙamshi na tashi sai ya saukar masa da kasala. A hankali ya durƙusa ya sauke ta,sai dai rashin samun cikakken balance da bata yi ba ne ya sanya ta zamewa za ta faɗi,ta gama saddaƙarwa za ta kai kasa tinda ya tsane ta ba lallai ya tare ta ba. Har ta kusa kaiwa kasa ya sanya hannunsa ya damƙi nata da ƙarfi,fatar hannunta da ya sake taɓawa a karo na biyu ne ya sanya shi jin wata iriyar wutar lantarki ta ja shi,da sauri ya fizgeta ya manna ta da ƙirjinsa,a haka Layuzah da ta ji shi shiru ta fito tana masifa ta riske su,wata iriyar ƙara ta saki kamar wadda ta ga kwarto a ɗakin ƙaramar ƴarta,a kiɗime Aminullahi ya juya suka haɗa ido da ita,sai dai duk yanda ya so ya raba hannunsa da jikin Lamyah da ya rungume ya kasa,cikin hargagi da matsanancin kuka Layuzah ta juya gefen da ta ga wata flower vase ƙarama ta rarumeta ta yi kan su a guje tana ihu kamar mai zuwa jihadi......... [9/11, 10:50 AM] zee hussain: ƳAR RAWA. RUBUTAWA HAMIDAH SUNUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✍️✨ PAGE 37. Da wani irin salo Lamyah ta raba jikinta da na Aminullahi ta tura shi gefe itama ta faɗa gado,vase ɗin ya tafi sai ya daki gini,a zuciye Layuzah da bata samu nasarar abinda take so ba ta nufi Lamyah ta ɗaga hannu za ta kai mata mari,cike da zafin nama Lamyah ta riƙe hannun gam a hannunta ta matse tare da ware yatsun ta lanƙwasa mata su,ƙara mai ƙarfin gaske Layuzah ta saki tana kuka ta kalli Aminullahi da ke kallon flower vase yana tinanin da a ce Lamyah bata raba tsakanin su da ƙarfi ba,da tini shi ko ita wani na kwance ko a mace ko a cikin mawuyacin hali. Da wata iriyar raunatacciyar murya ta ce. "Ka na ganin za ta karya min hannu ba za ka hana ta ba?" Jiki na rawa ya tashi ya nufe su,hannunsa ya sanya zai ɓanɓare na Layuzah a hannun Lamyah,wani irin riƙo Lamyah ta sake yi wa hannun har ta na jin nata hannun na yi mata zafi,sai dai ta yi alƙawarin ba za ta saki ba ko da kuwa za ta yi jinya daga baya. Ganin wahala kawai Lamyah ke sake bata sai ta kai wa hannayen dika cizo da niyyar ƙwatar kanta,cikin rashin sa'a ta cafki yatsan Aminullahi ta kafa masa haure ta gatsa kamar za ta cire,azaba ta yi azaba Aminullahi ya ɗaga hannu ya wanke ta da wani mugun mari,cikin tsananin gigita ta ƙwalla ƙara,majina da hawaye tare da zufa duk sun haɗe mata waje ɗaya,ita kanta Lamyah zufa take tsiyayarwa a cikin laffayar da aka naɗe ta da ita,amma tsananin kafiya da taurin rai

Chapter 22 of 30