Ya ƙarashe maganar cikin murmushin yaƙe.
Samar ma murmushin ya yi ya ce "Uhmm! Yaya ba mu tafi ba muna Kanon, ai ɗazun nan ma aka ɗaura auren, yanzu haka Mamy sun je Bk don raka Amarya ɗakinta."
Ɗif, wuta ta ɗaukewa Sameer, nan take damuwa da tashin hankalin da su ka ɗan ɗaga masa ƙafa na kwana biyu su ka dirar masa, kasa magana ya yi saboda yanayin tashin hankalin da ya ke ciki "Shikenan ta tabbata na rasa ki Mimieta? Ke wani ɓangare ce ta jikina ba zan iya rayuwa baki ba, ko da na rayu to zan rayu ne bisa ga mummunar ƙaddara, kuma rayuwata za ta kasance mara armashi tamkar miyar da ba gishiri." Ya faɗa a ransa.
Bai san cewa ashe afili ya faɗa ba sai da ya jiyo sautin Muryar ƙanin nasa cikin damuwa ya na faɗar "Ka yi haƙuri Yayana, komai ya yi zafi maganinsa Allah, mu kanmu muna cikin irin wannan damuwar, ada muna farinciki Mimie ta dawo gare mu a karo na biyu ashe ba haka ba ne, duk wanda ka rasa ta silar mutuwa ka riga ka rasa shi kenan sai dai ka samu makamancinsa..." Ya na kai nan ya ji wani irin kuka ya zo ma sa kawai sai ya katse kiran.
Shi kansa Sameer ya shiga wani hali, don haka ya gyara kwanciyarsa akan kujerar da ya ke tare da rumtse idonsa ya na cigaba da karanto *Innalillahi wa inna'ilahir raji'un* a zuciyarsa...
®®®®®®®®®®®
Washe gari da misalin ƙarfe goma na safe aka sada Amarya da gidan mijinta.
Ango da dama ya gama ƙosawa a kawo masa Amaryarsa ya na jin dirar motarsu ya fito waje.
Anan ya samu ya keɓe da Raliya ya haɗa kai da ita domin ta kawo masa Amaryar ɗakinsa ba tare da sanin kowa ba.
Haka kuwa aka yi daƙyar ta samu ta yi dabara ta fito da Mimie zuwa ɗakin Bassam, su na shiga ta dawo da baya ta rufo ƙofar ta baya, ta wuce abinta ta na dariya.
Da sauri Mimie ta juyo ta na zare ido ta miƙa hannu don buɗe ƙofar amma inah! Ta kasa buɗewa.
Jin ƙarar taku a bayanta yasa ta yi saurin juyowa, wa za ta gani?, Uncle ne ke nufo ta da murmushi kwance a fuskarsa sai ƙamshi ya ke zubawa.
Ba ta san ya aka yi ba kawai sai ta samu kanta da jin tsoro, fargaba duk ta bi ta ishe ta, ƙirjinta sai lugude ya ke, a ranta ta ke mamakin Raliya ashe wayo ta mata kenan haɗa baki su ka yi don ta kawo ta nan?.
Ba ta gama zancen zucinta ba ya ƙara so daf da ita ya na faɗar "Sannu da zuwa kyakkyawar Amaryata, ina miki Barka da shigowa wannan gida mai albarka, gidan da na ke fatar ki tsinci farincikin da za ki rayu da shi har abada."
Ja da baya kawai ta ke ta kasa magana ma, yanzun ma shi ne ya yi dariya ya ce "Haba! Ka da ki tsora ta da angonki mana princess, kin san ba zan cutar da ke ba, kawai na yi missing ɗinki da yawa ne shiyasa na kasa haƙuri har jama'a su watse na saka aka kawomin ke nan."
Haka dai ya ci gaba da tsokanarta harta ɗan ware ta na murmushi.
To da ya ke a yau ne dukkannin su za su juya don haka Mamy ta shiga neman Amarya don su yi sallama ga mamakinta ba Amaryar ba Raliya ƙawarta, anan ta shiga neman dukkansu, can ta hango Raliya a waje ta ce "Ya'ta ina Amaryar ne nemo min ita, kuma ki zo ki shirya yanzu za mu tafi."
Da to ta amsa.
Ita ce ta je ta dawo da Mimie, su ka yi Sallama sannan su ka juya su ka bar Amarya cike da fargaba har hawaye sai da ta yi, da za su tafi.....
Ga mai buƙata sai ya tuntuɓeni ta wannan number
08209634202
Follow me on wattpad @ummu inteesar
Ummu inteesar ce❤️❤️❤️❤️❤️❤️
UMMU INTEESAR CE❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤
️
👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻
*A SANADIN KAMA*
👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻
*DAGA ALƘAMIN RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU-INTEESAR)*
MARUBUCIYAR SOYAYYAR MEERAH
Y'AR GANTALI
RIKICIN MASOYA
DA KUMA
A SANADIN KAMA
WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE AKAN NAIRA 200 KACAL
GA MAI BUƘATA SAI YA TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER 08109634202
DON ALLAH IDAN KA SIYA KADA KA FITARMIN HAƘƘIN MALAKA NAWA NE
*AREWA WRITERS ASSOCIATION*
Page 4️⃣9️⃣↪️5️⃣0️⃣
A haka kowa ya watse aciki kuwa har da su Mama Habeey da su ka kwana uku anan.
Aka bar Amarya ita kaɗai sai fatar Allah Ya ba su zaman lafiya.
Bayan wata biyu da kai Amarya Mimie ta na zaune a gidanta cikin kwanciyar hankali da jin daɗi damuwarta ɗaya ce ita ce komawar angon nata Kano domin aikinsa, sati uku kawai su ka yi a tare hutun angoncinsa ya ƙare bisa ga dole ya koma Kano ya bar ta a gidan ita kaɗai, sai dai ya kawo mata ƙannensa y'an mata guda biyu Shamsiyya da Sakina domin su taya ta zaman gidan.
Bayan tafiyarsa aka fara ɗaukar sabbin ɗalibai a jami'a don haka ta kira shi ta sanar masa, bai yi gardama ba domin kuwa dama can kafin a ba shi ita sai da Daddy ya sanya masa sharadin barin ta ta ƙarasa karatunta kuma ya amince da hakan.
Waya su ka yi ita da Daddy ta shaida masa anfara bayar da admission a jami'a, don haka Daddy ya turo mata kuɗi Naira dubu ɗari biyu account nata, ya ce ta saka mijinta ya nema mata makarantar da ta dace da ita sai ta yi amfani da kuɗin gun hidimar makarantar idan sun ƙare ta sanar masa.
Godiya ta yi masa sosai, bayan sun gama wayar ne ta nemo layin Bassam ta shaida masa, sosai ya nuna jin daɗinsa tare da yiwa Daddy addu'a.
Anan ya sanar mata zai san yanda za'a yi a nema mata admission ɗin duk da baya gari.
Waya ya yi da ɗaya daga cikin abokanansa da ke nan Birnin Kebbin ya shaida masa buƙatarsa anan ya ce ba damuwa ya sanar mata ta shirya takardun shi zai yi iya ƙoƙarinsa.
Bayan wani ɗan lokaci Al'amin abokin Bassam ya kammala komai, lokacin fara karatu kawai Mimie ke jira.
Universityn da ta ke cikin local government na Kalgo anan za ta yi karatun, hakan ba ƙaramin daɗi ya yiwa Bassam ba domin ko bakomai cikin garinsu ne za ta yi karatun, daga nan zuwa gidansu Naira hamsin ne kuɗin Babur, ya san hakan zai sauƙaƙa mata wasu abubuwan.
A lokacin da ta cika wata huɗu a gidan ta fara attending school, inda za ta karanci Medicine.
Ko da yaushe ta kan je makaranta,yayin da su Shamsiyya su ke zaune a gida, su ne masu yi mata duk wani aikin gidan kafin ta dawo, sai dai ta zo ta tarar an gama girki ci ne kawai nata.
Kullum kwanan duniya ta kan yi waya da angonta abun alfaharinta, a rana sai su yi waya sau goma ko ƙasa da hakan, ta na jin daɗinta har ta sakankance cewa ta samu gurin zama na har abada, kuma zaɓintan dai tabbas shi ne alkhairi a gare ta, ragowar fargabar da ta ke ji akan yin aure ba tare da amincewar iyayenta ba duk ta gushe a zuciyarta, ba ta san cewa akwai sauran rina a kaba ba, ba ta san cewa tarin matsaloli da tashin hankali su na gaba ba.
®®®®®®®®®®®
Sameer da ya je Dubai da niyyar karatu sai Dubai ta kasance masa gurin jinya, domin tarin damuwa da ɓacin rai da ya ke ciki ya fara haifar masa da matsala a zuci da gangan jiki, mussanman ya nemi likita acan mai kula da lafiyarsa, kullum ciwonsa daɗa yi gaba ya ke, ya kasa samun mafita, ya na so ya manta da ita amma ya kasa.
A waɗannan wata huɗun da ya yi duk ya zama abun tausayi, maimakon ya yi kyau, sai ma ya daɗa lalacewa.
A ranar da ya ji ya samu sauƙi ya ɗan warware a ranar ya fita domin fara zuwa ɗaukar darasi domin tuni ya kammala duk wani process na makarantar.
Khalifa University da ke babban birnin Dubai wato Abu dhabi, ita ce makarantar da ya fara attending domin yin masters ɗinsa a ɓangaren Medicine.
A ranar farko da ya fita acan ne ya haɗu da wasu aboka nai su uku biyu y'an Nigeria ɗayan kuma ba indiye ne, daga farko ya ƙi ya kula su, amma a haka suka cigaba da bibiyarsa har zuwa ranar da ya amince musu, ba tare da sanin cewa wata rana za su saka shi yin dana sani mara amfani ba a rayuwa.
®®®®®®®®®®
Bangaren Mommy kuwa ta cigaba da cusawa Ruma mummunar aƙidar tsanar Mimie da kuma saka ta bibiyar rayuwar ƴaƴan Alhaji Salman, sai dai ita Ruma ba ta ɗauki ko ɗaya daga cikin wannan akiɗar ba, sai dai a fuska ta ke nunawa Mommy kamar ta amince kuma ta na yin abunda ta saka tan.
Ita kuwa Mommy ganin ba cigaba ta wannan ɓangaren ya saka ta je gidan wata aminiyarta Hajiya hafsat, domin ta bata shawaran yanda za ta ɓullowa lamarin, inda hajiyar ta sanar Mata cewa ta na da wani Malama, sai dai ba'a nan ya ke kusa da su ba, idan ta amince za ta kira shi a waya domin asan yanda aka yi aka cusa Soyayyar Ruma a zuciyar ɗaya daga cikin yaran.
Da farko kamar ba za ta amince ba, Hajiya hafsat ta dinga mata huɗubar tsiya, da hakan ta yaudare ta har ta amince, ita kuwa ta ɗora ta a keken ɓera.
®®®®®®®®®®®
Ga mai buƙata sai ya tuntuɓeni ta wannan number
08109634202
Follow me on wattpad @Ummu inteesar
UMMU INTEESAR CE❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻
*A SANADIN KAMA*
👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻
*DAGA ALƘALAMIN RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*
*MARUBUCIYAR:* *SOYAYYAR MEERAH*
*Y'AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*DA KUMA*
*A SANADIN KAMA*
WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE AKAN NAIRA 200 KACAL
GA MAI BUƘATA SAI YA TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER 08109634202
DON ALLAH IDAN KA SIYA KADA KA FITARMIN HAƘƘIN MALAKA NAWA NE
*AREWA WRITERS ASSOCIATION*
Page 5️⃣1️⃣↪️5️⃣2️⃣
A haka Mimie ta cigaba da karatunta cikin kwanciyar hankali da nutsuwa, duk da cewa mijinta baya gari amma ba ta da wata matsala ta kuɗi ko makamancin haka, kasancewar Daddynta ya na tura mata kuɗi a account ɗinta duk wata, hakan ya sa ba ta ɗaurawa mijinta lalurar komai, abinci kuwa sai kalar wanda su ke son ci ita da ƙannen mijin nata, yayin da mijinta ke zuwa duk bayan wata biyu ya yi sati biyu ya koma bakin aikinsa.
Sosai ta ke jin daɗin zama da ƙannen mijin nata domin su na yi mata biyayya Sosai, kuma su ne ke mata duk wasu aikace-aikacen gida, iyaka ta kwanta ta huta sai karatu su kaɗai ne aikinta acikin gidan, kasancewar Shamsiyya sa'ar ta ce hakan ya yi mata daɗi sosai, tamkar ƙawaye haka ta ɗauke su.
Haka zalika idan ta je Kalgo Innarmu sai nan-nan ta ke da ita, ko kuɗa bata son ya hau kan Mimie saboda yanda ta ke nuna mata soyayya da kulawa.
Ganin irin wannan ƙaunar da uwar miji da danginta ke nuna mata ya saka ta saki jiki da su ta ke sakar masu Naira, bata jin ƙyashin yi masu komai, tuni ta manta da rashin biyayyar da ta yiwa iyayenta a lokacin auren, ta ɗauka ta ci bilis, kuma bata tunanin akwai wata mummunar ƙaddarar da ke tafe a rayuwarta ta gaba.
A ranar da ta cika shekara ɗaya da rabi a gidan miji a ranar ne ta fara fuskantar matsala daga ɓangaren uwar mijinta, domin Innarmu ta fara sauya mata fuska, yanzun bata murna da ganinta ko kaɗan, zancen da Innarmu ta yi mata a ranar shi ya fi komai ɗaga mata hankali.
Da yake aranar sun je gidan ita da su Sakina, ta na zaune a ɗakin Innarmu, innar ta shigo ta kalle ta a ɗage ta ce "Wai ni yarinyagga har yanzu baki samu ciki ba? Ko dai wata ƙwaya ki ka sha ta hana haihuwa?"
Sunkuyar da kanta ƙasa ta yi gabanta na tsananta faɗuwa ba ta dai ce komai ba.
Innarmu ta kuma matsowa tare da zama kusa da ita ta ce "Ki amsa min tambayata."
Ƙara sunkuyar da kanta ta yi ɗakyar ta ce "Inna Wallahi ba na shan komai, Allah ne dai bai kawo ba." Ta ƙarshe cikin raunanniyar murya.
"To in ma ki na sha ki dakatar, ina so ki sani cewa ɗana Bassam shikenan ni ke da shi ɗa namiji wurina, dan haka ina ɓukatar jininsa a matsayin jikokina kahin in mutu." Ta faɗa cikin yanayin faɗa-faɗa.
Jikin Mimie ya yi sanyi laƙwas da ganin yanayin Innarmu A ranta ta ke cewa "Na shiga uku, su waye ke ƙoƙarin shiga tsakani na da sirikata, na san an cusa mata wannan aƙidar ne."
Wunin ranar dai kwata-kwata Mimie ba ta ji daɗinsa ba, da yamma ta ja su Shamsiyya su ka koma gida, jikinta ya yi sanyi qlau, damuwa ta fara shigarta nan ta ke ta tuna da iyayenta, aranta ta ce "Allah ya sa ba sakamakon bijirewa iyayena ne na fara gani tun yanzu ba."
®®®®®®®®®®®
DUbai
Kishingiɗe ya ke akan wata kujera irin waɗannan ake ajiyewa bakin swimming pool.
Idonsa sanye da wani makeken baƙin glass ya kafe ruwan da ido, hannunsa riƙe ya ke da wani glass cup ƙarami da alama lemo ne a ciki.
A gefensa na dama Wisam ne zaune riƙe da kwalbar barasa ya na kwankwaɗa, a gefen hagu kuwa Zaroon ne zaune Shi ma da kofin barasar a hannunsa, yayin da Rajbir ya ke cikin swimming pool ɗin ya na wanka abinsa.
Shi kuwa Sameer zaune kawai ya ke kamar an dasa shi agun, da alama damuwa da tunani sun gama zama jikinsa, domin a yanzun ma baya hayyacinsa ya tsunduma tsulum a kogin tunani, har sambatu ya ke yanzun ma faɗar ya ke "Why Mimie? Meyasa ki ka mun haka? Ga inda kika kawo ni a yanzu, kin yi silar barin mahaifata, Why?, Shin ashe laifi ne don na ƙaunace ki?.
Cikin wani irin yanayi mai wuyar fassarawa ya ke furucin.
Cikin Muryar y'an maye Wisam ya ce "Haba guy, ni wallahi ka na ba ni kunya, yanzu akan mace ka ke wannan abun? Ga maganin damuwa na baka ka ƙi ka sha, ban san meyasa kaƙi ka waye ba."
Zaroon ne ya cafke zancen da cewa "Ka bar shi kawai, tun da baya so sai ya zauna damuwa ta kashe shi, tun da haka ya ke so." Shima cikin Muryar y'an ƙwaya ya yi zancen.
Rajbir da ya fito daga cikin ruwa yanzu ya nufo su ya na goge jikinsa, faɗar ya ke "Sam tun daga nesa na hangoka, na san yanzu ma damuwar ce?, karɓi wannan ka sha, ka na sha za ka nemi damuwar ka rasa." Ya faɗa tare da karɓar kwalbar giya a hannun Wisam ya na miƙa masa.
Sameer kuwa jin su kawai ya ke domin shi baya tunanin zai iya aikata saɓo irin, wannan bai taɓa shan giya ba, kuma ba ya son ya sha.
Tunawa ya yi da hadisin Manzo Sallallahu alaihi wasallam inda ya ke cewa "Kullu muskirun khamrun, wa kullu muskirun haramun."
Ma'ana (Duk abinda ke saka maye giya ne, kuma duk abinda ke saka maye haramun ne.)
Haka kuma ya tuna ayar da ta yi magana akan haka, nan ta ke ya ji ba zai iya aikata wannan saɓon ba.
Kimanin watanni takwas kenan da haɗuwarsa da su Wisam, da farko ya ɗauka yaran arziƙi ne shiyasa ya amince musu, sai bayan ya shaƙu da su sannan ya fahimci halayyar su ta shaye-shaye da neman mata, ga shi ya kasa rabuwa da su amma kuma shi baya aikata ɓarnar da suke yi, kullum ya na neman tsari a gurin mahaliccinsa daga sharrin su.
Rajbir ne ya dawo da shi daga tunanin ya na miƙa masa kwalbar giyar, karɓa ya yi ya ajiye a gefe.
A haka su ka cigaba da masa huɗubar tsiya, su na nuna masa ya sha ko sau ɗaya domin maganin damuwarsa.
Cikin rashin Sa'a su ka yi nasarar cafko zuciyar Sameer tare da karkato da shi zuwa gurɓatacciyar hanya.
Nan ta ke ya manta da hadisin da ya tuna ɗazu ya karɓi kwalbar ya ɗaga ya kwankwaɗa sai da ya ku san shinye ta sannan ya ajiye.
Wani shu'umin murmushi su ka yi dukkansu, murmushin mai nuni da alamun cin nasara.
"Ko kaifa?" Yanzu ya ka ke ji?" Su ka haɗa baki gun tambaya.
Ganin ya yi mankas abunka da sabon shiga kawai sai suka janye shi zuwa ɗakinsa, suka kwantar dashi.
®®®®®®®®®®®
Ita kuwa Mommy bisa ga huɗubar ƙawarta ta saka a ka kira mata Malam a waya, ya haɗa masu maganin sanya soyayya a zuci, Hajiya hafsat da kanta ta je har ƙauyen da ya ke ta karɓo tare da zabge masa kuɗin aikinsa ta juyo.
Daga can kai tsaye gidan Mommy ta wuce ta kai mata, ta yi mata bayanin yanda za'a yi amfani da shi.
"Danƙare maƙari! To yanzu ni khadija ina ma za mu ga abincin ɗayansu bare a saka masa har ya ci?, Duk da wanda na so yin aikin akansa ya bar ƙasar, amma sai a juya ga ƙaninsa ai duk ɗaya ne." Mommy ta faɗa yayinda ta ke karɓar kullin maganin.
"Ke kika san yanda za ki yi, har a samu ya ci, amma ya na ci angama magana." Hajiya hafsat ta mayar mata da amsa.
Dogon numfashi Mommy ta ja ta ce "Wannan ja'irar yarinyar na san ko na saka ta ba za ta aikata ba, amma bari zan nemo mafita, yanzu zuwa yaushe ya kamata ya ci maganin?"
Da haka su ka cigaba da tattaunawarsu har zuwa lokacin da Hajiya hafsat ta bar gidan.
®®®®®®®®®®
Zuwa wannan lokacin damuwa ta fara yiwa Mimie yawa ganin su ma su Shamsiyya sun fara juya mata baya, yanzu iskanci su ke mata iri-iri, sai ta je makaranta ta dawo ta tarar ba abinci kuma ba su gyara gidan ba, idan ta tambaya sai su ce ba su dafa da ita ba, iya cikinsu su ka yi, aiki kuma ba za su yi ba, domin ba bayi aka kawo mata ba, a haka za ta yi haƙuri ta yi aikin dole, idan ta na son ganin gidanta tsaf.
Duk wannan abin da ake Bassam bai sani ba ya na Kano zaune abinsa, sai dai idan su na waya ya na yawan tambayarta ko lafiya ya ji Muryarta tamkar tana cikin damuwa, sai ta ce ba komai kawai yanayin karatun na su ne, ko ta ce gajiya ce.
Anan cikin haka ya shirya ya zo hutu gida inda ya tarad da ita cikin damuwa sosai, juyin duniyar nan ya yi ta ƙi gaya masa akan dole ya haƙura.
Dama da ya shigo garin su Sakina ke komawa gida sai zai tafi su dawo da yake su zauna gari banza ne, daƙyar Shamsiyya ta gama Secondary, Sakina kuwa tun ta yi jlce ta ƙi komawa makaranta wai ba za ta iya wahalar boko ba, da ya ke innar tasu ma ba wani wadataccen ilimi ne da ita ba sai ta ƙyale ta.
A yan kwanakin hutunsan nan ta na cikin jindaɗi da nishaɗi domin ya na ƙoƙarin faranta mata.
Ya na zaune a ɗakin matarsa aka kira shi daga Kano aka shaida masa cewar Shagonsa na kasuwar Rimi inda ya ke siyar da takalmi da jakunkuna ya yi gobara komai ba a tsira da shi ba. (Da ya ke ya na taɓa kasuwanci tun lokacin da ya ke karatu a Kano, abokin babansa da ya ke zaune a gidansa ya saka shi a cikin kasuwancinsa, zuwa yanzu yana da shaguna biyu ɗaya a Rimi ɗaya a kwari, sai dai ya zuba yara ne aciki tunda shi yana aiki a nepa.)
"Innalillahi wa inna'ilahir raji'un!" Ita ce kalmar da ya ke ta maimaitawa, anan ta ke tambayarsa lafiya ya shaida mata abunda ke faruwa, ta ji matuƙar ba daɗi na wannan hasarar da mijinta ya tafka.
Ko da ya je gida ya sanarwa Innarmu maimakon ta jajanta masa sai cewa ta yi "Ai ga irinta nan, ka tai ka kwaso ma kanka mai hwarar ƙahwa, da alama kuma juya ta, dan tun da ta shigo gidanka hay-yanzu ko ɓari ba ta taɓa yi ba, bayan nan kuma ga hasarori an hwara tafkawa." Cikin yanayin faɗa take zancen.
Bassam ne ya ce "Haba Innarmu, ba laifin ta ba ne fa, ƙaddara ce, kuma ni na yi imani da ita, kuma maganar haihuwa da kike, ai ita kanta haihuwar nufin Allah ce idan ya ƙaddara zan......"
"Kai ruhemin baki, shashashan banza."
Innarmu ta katse mi shi zancen ta ɗora da cewa "Ita ta san ƙwayar da tassha ta hana ɗaukar ciki dan ta yi karatunta hankali kwance, mu mun san tciyar y'an boko."
Ganin abin na shiri hakan zame masa ɗan zane ya saka ya fice daga gidan rai a jagule...
Ga mai buƙata sai ya tuntuɓeni ta wannan number
08109634202
Follow me on wattpad @Ummu inteesar
UMMU INTEESAR CE❤️❤️❤️❤️❤️
👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻
*A SANADIN KAMA*
👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻
*DAGA ALƘALAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*
*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y'AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
DA KUMA
*A SANADIN KAMA*
WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE AKAN NAIRA 200 KACAL
GA MAI BUƘATA SAI YA TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER 08109634202
DON ALLAH IDAN KA SIYA KADA KA FITARMIN HAƘƘIN MALAKA NAWA NE
*AREWA WRITERS ASSOCIATION*
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*
Page 5️⃣3️⃣↪️5️⃣4️⃣
Wata rana Zinnira ta shirya daga gidansu ta zo gidan Bassam domin sun yi waya da su Shamsiyya su ka shaida mata suna nan.
Da yamma liƙis ta zo gidan a lokacin Bassam ya na nan, wai zo ku ga iyayi agun Zinnira, sai wani yauƙi ta ke.
Dama can tun bata kai girman haka ba Allah ya jarafce ta da son ɗan yayar mahaifinta wato Bassam, ta na jarabar son sa, har kowa ya shaida hakan a familynsu, amma shi Bassam kwata-kwata baya nuna ma ya san me ta ke.
Da ta juya sun haɗa ido da Mimie sai ta zabga mata harara,shi kuwa idan ta juya garesa sai ta yi masa murmushi.
A haka ta ƙaraci iyayinta da habaici da hare-harenta, bayan magariba ta tattara ta koma gidansu da ya ke cikin garin, bayan ta ƙara yiwa su Sakina huɗubar tsiya akan su cusgunawa matar yayan nasu a lokacin da baya gari.
Bayan kwana biyu ya na shirye-shiryen komawa Kano Innarmu ta kira shi zuwa gida, da ya je ne ta ke ce masa "Dama ba komi yassa nikkiraka ba, sai dan wata magana mai muhimmanci da muka son mu yi."
Gyara zamansa ya yi akan ledar ƙasa dake shimfiɗe a ɗakin ya na sauraronta.
Innarmu ta cigaba da cewa "Dama na ga kana yawan tahiye-tahiye ka na barin matarka can binni gashi babu kowa kusa da ita, sai su Shamsiyya, ga shi duk su na taron zani-zaka, ƙurciya na cin su, kuma nan an banni shiru, shina nicce me zai hana ka maida Matakka gidan ga?, in yasso gidanka na binni sai ka sa y'an haya, ka ga dannan ma ya hi mata sauƙin zuwa makaranta."
Gyara zama ya yi ya na cewa "Amma Innarmu, miye amfanin gidan da na ke da shi kenan, idan iyalina ba za ta zauna ciki ba?, Kuma nan na ga ya matse ba wani ɗaki da za ta iya zama aciki, ku kanku bai wadace ku ba."
Cikin tsawa Innarmu ta ce "Kama min bakinka, ba ga wancan tsohon ɗakin na babanku ba, tunda yarrasu ɗakin ya ke ruhe, sai a buɗe shi ka ƙara gyarawa kasa Matakka ciki."
Da mamaki a fuskarsa ya ɗago ya na cewa "Amma Innarmu ɗakin fa ƙarami ne kuma....."
Bai samu damar ƙarasawa ba saboda tsawar da ta daka masa ta ce "Ka ga ɗan nema mai shegiyar gardamar tciya? To tashi ka ban wuri hukunci na riga na yanke kahin ka wuce Kano za ta dawo nan umurni ne ba shawara ba, ya rage naka ka bi ko akasin haka."
Ta na gama faɗa ta miƙe ta shige uwar ɗakanta ta bar shi a gun sake da baki.
Shima miƙewa ya yi cike da damuwa ya bar ɗakin, a ransa ya ke mamakin me Innarmu ta ke nufi da hakan? Da farko ta tursasa shi zama birnin Kebbi, yanzu kuma ta na yunƙurin nuna ƙarfin ikonta ta hanyar tursasa shi zama gidan family abinda baya burge shi kwata-kwata.
Jiki a saɓule ya bar gidan.
®®®®®®®®®®®
Dubai
Bayan farkawar Sameer daga bugaggen barcin da ya yi sakamakon kwankwaɗar barasa, ko da ya farka ya dawo hayyacinsa, da ya tuna abinda ya faru kawai sai ya fashe da kukan nadama.
Ya yi kuka sosai tare da Allah wadai da halin su Wisam shi kam tarayya da su bata amfane sa
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 15