fatar ta kuma aikata wani kuskure a karo na biyu, saboda haka ta ce "Ashirye na ke da gyara kuskure na, don haka na yi maka alƙawarin zan wanke maka dauɗaɗɗiyar zuciyarka da na yi silar ɓatawa da ruwan zallar soyayya, zan shafe maka ita da ƙyallen ƙauna domin dawo da ita a asalin yanda take kafin na gurɓata ta."
Ba ƙaramin farinciki Sameer ya ji ba, ya ma kasa magana sai bakinsa dake rawa daƙyar ya buɗi baki ya ce "Alhamdulillah!"
A yau wani irin farinciki yake ji wanda rabonsa da jin makamancinsa tun kafin shekara biyar da suka gabata.
Gyara zama kawai ya yi a gun yana ta kallon ta, har ta ji ta tsargu ta tashi ta gudu zuwa ɗaki.
Sai ranar ne kuma Sameer ya gabatar mata da tsarabarsa da ya yo masu a saudia ita da yaran.
A wannan ranar Sameer bai kwanta ba sai da ya shaidawa Daddy halin da a ke ciki, shima Daddy a ranar ya samu Mimie a ɗaki ya tambaye ta, ta tabbatar masa da hakan, ya yi farin ciki matuƙa don haka a ka yanke cewar da ta gama iddarta za a sanar da iyayenta sai a yi maganar auren.
Bayan wata biyu da rabi Mimie ta kammala iddarta, a ranar kuma ta juya zuwa Kano, tun kan ta isa kanon Daddy ya kira Baba ya shaida masa halin da a ke ciki, shi ma Baba ya yi murna sosai ya na ta sakawa Mimie Albarka.
Bayan sati ɗaya a ka biya sadaki da komai na aure a ka saka rana nan da sati uku masu zuwa.
A cikin satin farko a ka kawo lefen Mimie a Kano, lefe ne na gani na faɗa akwati goma sha biyar Sameer ya danƙaro mata, irin wanda ko a aurenta na fari bata samu irinsa ba.
Mutane sun yi ta al'ajabin wannan abun,
Ita kanta Mimie ta yi mamakin irin wannan kayan duk da ta san akwai abun yin fiye da haka, amma sai da ta kira Sameer ta na tambayarsa "Yaya miye haka?"
Ya ce "name fa?"
"Irin wannan kayan haka sai kace za ka auri wata budurwa?." Ta tambaya.
Murmushi yayi mai sauti ya ce "Sweetyna ai kin fi wata budurwar a gurina, matsayinki baya da misali, shiyasa ma na yi zaman jiranki har zuwa wannan lokaci."
Da alamun mamaki a fuskarta ta ce "To yanzu da ƙaddara bata ɗauke Uncle Bassam ba sai ka yi yaya kenan?"
"Da a haka zan cigaba da zama har zuwa lokacin da tawa mutuwar za ta riske ni, domin ba zan iya rayuwa da ko wacce 'ya mace ba bayan ke."
Jinjina kai kawai ta yi bata ce komai ba.
A haka suka cigaba da hirar har zuwa lokacin da suka kashe wayar.
©©©©©©
A bangaren ango shirye-shirye suke sosai, domin wannan shi ne karo na farko da za su aurar da babban ɗansu, bugu da ƙari kuma auren za a yi ne da 'yar lelensu, don haka dole a yi biki mai ƙayatarwa.
Ranar da ya rage saura kwana biyar bikin, wasu daga cikin dangin Mamy da Daddy na kaduna suka je Abuja don taya murnar wannan auren.
Bangaren Mimie ta ce ita ba wani shagali da za ta yi saboda ita a yanzu ba budurwa ba ce.
Jin hakan ya saka Mamy ta turo wasu daga cikin 'yan uwanta zuwa Kano a ka ɗauki Amarya zuwa Abuja don gudanar da shahararren shagalin da suka shirya a can.
Sameer kuwa ya ce shi komai na auren, so yake a gudanar da shi kamar yanda a ke gudanar da na saurayi da budurwa, don shi a ransa haka auren yake.
Su yaya Farida, Anty Zee(matar yaya Kabir da Anty yusrah (matar yaya Sagir) ne suka yiwa Amarya rakiya har Abujan, da yake wannan ne karon farko da za su je gidan Daddy.
Raliya ma ta je duk da cewa ta yi aure shekaru uku da suka wuce, amma sanin amintakar da ke tsakaninsu ya sanya mijinta bai hana ta zuwa Abujan ba.
Ranar Asabar da yamma liƙis ango da tawagarsa suka ƙara Kano domin ɗaurin aure.
Washe gari Ranar Lahadi Dubbunan mutane suka shaida ɗaurin auren Sameer Salman da Zuhuriyya Sadeeq Yusuf a kan sadaki Naira dubu ɗari.
Ɗaurin auren da ya samu halartar manya baƙi kama daga kan sanatoci, gwabnoni da manyan 'yan kasuwa abokanan Daddy har ma da 'yan uwan Daddy da Mamy na Kaduna da abokanan arziƙinsu.
Ranar murna agun Sameer ba a magana, wannan rana ce ta farin cikin Sameer, don haka ya yanke aransa duk wanda bai zo masa wannan ɗaurin auren ba acikin abokansa tabbas ya san zaman da zai yi da shi.
Bayan an gama shagalin ɗaurin auren da kamar awa huɗu jama'a suka ɗunguma zuwa Abuja don gudanar da sauran shagalin, su kuma baƙin Daddy kowa ya juya zuwa jaharsa.
Lokacin da suka isa garin Abuja a na ta kiraye-kirayen sallar la'asar, don haka suka tsaya suka yi salloli sa'annan suka ƙarasa masauki.
Bayan magriba a ka shirya amarya cikin wata tsadaddiyar Gown mai masifar kyau dark blue, ta yi kyau matuƙa fuskar nan ta sha make-up, dama abu ga jinin Fulani sai ta fito kamar yar tsana.
Idan ka gan ta sai ka rantse bata taɓa haihuwa ba, saboda gyaran da ta sha.
Shi ma ango ya shiryo tsaf cikin dakakkiyar shaddarsa dark blue ya sha babbar riga, mota ɗaya suka hau zuwa hall ɗin da za a yi dinner, sauran motoci suka rufa masu baya.
Su na isa parking space direban ya kashe motar, bayan samari da 'yan mata sun fir-fito, amarya da ango suka fito.
A tare suka jero zuwa hall ɗin sai ƙamshi suke zubawa.
Ka na ganinsu ka san sun dace da juna sosai.
Ƙarasawa suka yi cikin hall ɗin suka zauna, samarin ango suka kewaye su a na ta ɗaukar hotuna.
Bayan an natsa Samar ya fito domin bayar da taƙaitaccen tarihin soyayyar ango da amarya.
Bayan ya karɓi speaker ya dai-daita tsayuwarsa ya fara jawabi da turanci ga abinda yake cewa:
"Labarin soyayyar ango da amarya labari ne mai taɓa zuciya don haka nake so kowa ya nutsu don jin wannan labari."
Shiru ya yi na ɗan lokaci sai da ya tabbatar kowa ya nutsu sannan ya ci gaba da jawabinsa kamar haka:
"Soyayya ce mai cike da raɗaɗi da sanya ƙunci a zuciyar ɗaya daga cikinsu, yayana ya kasance ya na matuƙar ƙaunar amaryarsa fiye da tunanin mai tunani, shekara biyar ya kwashe ya na cikin ƙunci da raɗaɗin rashin masoyiyarsa tare da jiran ranar da za ta dawo gare shi, duk da baya da tabbaci a kan za ta dawo masa kuma bai saka rai ba, ya faɗa a cikin wani mawuyacin hali da ya sanya shi a cikin ɗemuwa da gigita, saura ƙiris ya rasa hankalinsa gaba ɗaya. Ya nisanci ƙasarsa da familynsa da kowa nasa duk a dalilin rasa soyayyarta da ya yi a karo na farko, saboda ƙaunar da ya ke yi mata ya sadaukar da farin cikinsa domin nata farincikin, ya janye zancen neman aurenta domin ta auri wanda take so."
Ya na zuwa nan a jawabinsa idonsa ya fara zubar da ƙwalla, share hawayensa ya yi da handkerchief dake hannunsa, sannan ya ci gaba da cewa "Tun da nake ban taɓa ganin soyayyar gaskiya irin ta yayana ba, haƙiƙa shi gwarzon sadauki ne mai haƙuri da juriya, ga shi a yau Allah ya dawo masa da sumammen farincikinsa ta hanyar maido masa da wacce yake tsananin ƙauna, ya kuma samu soyayyarta da ya rasa a baya, haƙiƙa mai haƙuri ya kan dafa dutse har ya sha romonsa."
Ya na kai nan a zancensa ya ajiye abin maganar tare da juyawa ya na sharar ƙwalla.
Suma jama'ar gurin haka suka yi ta goge ƙwalla, waɗanda suke da saurin kuka kuwa harda hawayensu.
Amarya Mimie ma sai da ta goge ƙwalla daƙyar ta iya haɗiye kukan da ya zo mata, sai kallon Sameer take, Ashe haka ya sha wuya a kanta? Da kansa ya janye maganar aurenta don ta rayu cikin farin ciki? Haƙiƙa ya kai akira shi da nagartaccen masoyi.
Yaya Farida harda kukanta da ta ji wannan labarin.
Dinner a ka yi ƙayatacciya, an ci an sha an yi bushasha da Naira kafin daga ƙarshe a ka tashi daga Dinner kowa ya koma masaukinsa.....
Follow me on Wattpad @ummu inteesar.
UMMU INTEESAR CE🌹🌹🌹🌹
UMMU INTEESAR CE🌹🌹🌹🌹
👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻
*A SANADIN KAMA*
👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻
*DAGA ALƘALAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*
*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y'AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
DA KUMA
*A SANADIN KAMA*
WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE AKAN NAIRA 200 KACAL
GA MAI BUƘATA SAI YA TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER 08109634202
DON ALLAH IDAN KA SIYA KADA KA FITARMIN HAƘƘIN MALAKA NAWA NE
*AREWA WRITERS ASSOCIATION*
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*
Page 7️⃣1️⃣↪️7️⃣2️⃣
A ranar kuma amarya ta tare a ɗakinta, da yake a cikin gidan a ka yi ma Sameer ɓangarensa.
Ya so ya je wata unguwar ya siyi gida, amma Daddy da Mamy suka ƙi, sune suka nace a kan sai dai ya ajiye musu 'yarsu kusa da su, inda suke jin motsinta, domin basa son ta yi nisa dasu a karo na biyu, suna fatar ta dawo cikin ahalinsu kenan har abada, don haka a ka gyara masa wani sashe na cikin gidan kamar yadda Saheen ya ke zaune a gidan, sai dai kowa part ɗinsa dabam.
An ƙawata part ɗin Sameer ɗin sosai, wannan karon ma Daddy ne ya zuba mata kayan furnitures, duk da Baba ya ce wannan karon su za su yi gyaran ɗakin ɗansu da kansu, suma sun zuba mata kaya dai-dai ƙarfinsu, duk da haka Daddy sai da yayi wani abun.
An gyara mata sashenta sosai, ta samu gyara irin wanda ko farkon aurenta ba a mata irinsa ba, tabbas ta ga bambancin auren da a ka ɗaura da son ran iyaye da kuma wanda a kayi ba tare da son ransu ba.
Washe garin ranar da amarya ta tare su yaya Farida suka juya zuwa Kano.
Sun so su wuce da twins kamar yanda Mama ta buƙata, sai dai fafur Sameer yaƙi, ya ce shi sai a bar mi shi yaransa domin ba zai yarda a raba su da mahaifiyarsu ba, gashi ma su jira-jirai ne 'yan wata biyar, ba a ma gama shayar da su ba.
©©©©
Wannan karon kam, Mommy ta zo bikin Mimie da ita a ka yi komai saboda kwaɗayi.
Yaya Farida ta yi mamakin ganin yanda Mommyn ta yi kamar bata san su ba, sai harkokin gabanta take, lallai Mommy ta yi nisa acikin ciwonta na hassada.
Don haka ko da suka koma Kano ma sai da ta bawa Mama labarin yanda Mommy ta nuna masu halin ko'in kula.
Ita kanta Mama sosai take jin zafin yanda 'yar uwartata ta wofintar da ita, kuma take wulaƙanta ta, amma ta zubawa sarautar Allah ido.
©©©©©©%%©©
A can Abuja bayan komai ya natsa, Sameer ne zaune a falonsa ya na bin Mimie da ido, yayin da take kai kawo tsakanin kitchen da dinning area ta na jejjera kulolin abinci.
Kallonta ya ke cike da so da ƙauna. "Sweety!" Ya kira ta.
Juyowa ta yi fuskarta ɗauke da murmushi ta ƙaraso tare da durƙusa a gabansa ta na faɗar "Ga ni ranka ya daɗe."
Shi ma murmushin ya jefe ta da shi, "Tashi ki zauna a nan." Ya faɗa ya na nuna mata kan kujera kusa da shi.
Zama ta yi ta na murmushinta mai burgewa, ya dube ta sosai ya ce "ke ba kya son hutawa, kin fi son kullum ki ta aiki, sai kace wacce ba ta da 'yan aiki?"
"Ai na saba da aikin ne yaya, idan na zauna haka ba na jin daɗi, kuma taya zan bari 'yan aiki su yiwa mijina girki? Ai ba zai yiwu ba."
Gyara zamansa ya yi ya ɗage gira sama irin ya ci serious ɗin nan ya ce "Daga yau ba na son na ji kin sake ce mun yaya, suna mai daɗi nake so ki mun."
'Yar dariya ta yi kaɗan ta ce "Sorry yaya, au na manta ka yi haƙuri Hubbyna." Ta faɗa ta na kama kunnenta da hannu biyu.
Dariya su ka yi dukkan su ya buɗi baki zai yi magana kenan Mamy ta shigo falon da sallamarta, ta na ɗauke da Afeef a hannunta ta ce "Sannunka da aiki Sam, wato ka riƙe mun "ya da surutunka ka hana ta ta zo ta bawa jikokina abincinsu koh?"
Miƙewa tsaye ya yi ya na faɗar "Sam ni ba ruwana a wannan maganar Mamy, laifin 'yarki ne, ita ce ta tsiri girki, nima yanzu maganar da zan mata kenan kika shigo."
Daga haka ya wuce cikin bedroom ɗinsa ya na murmushi, Mimie ta taso ta durƙusa gaban Mamy cike da ladabi ta ce "Barka da rana Mamyna."
"Yawwa sweet daugther, tashi ki karɓi yaron nan ki shayar da shi kafin na kawo maki ɗayan."
Miƙewa ta yi tare da karɓar yaron, ta koma kan kujera ta zauna ta na shayar da shi yayin da Mamy ta juya ta fice daga sashen.
@@@@@@
A bangaren Ruma abin da mahaifiyarta ke yiwa mijinta ya fara isar ta, don haka wata rana da dare a na zaune a babban falon bangaren Mamy ana ta hira, kowa ya na gun inka ɗauke Saheen da ya yi daren dawowa gida yau.
Ruma ce ta kalli Mamy ta ce "Mamy ina son na bawa a halin wannan gidan wata shawara idan ba damuwa."
Murmushi Mamyn ta yi ta ce "Ki faɗa kai tsaye 'yata."
Janye idonta ta yi daga duban Mamy ta sunkuyar da kai ta ce "Ina ganin ya kamata a ce kun nemi maganin tsari da kuma na karya sihiri, domin a irin shahara ta Daddy da zamansa babban ɗan siyasa ga shi kuma ɗan kasuwa, na san ba za a rasa magauta 'yan hassada waɗanda dukiyar da shaharar ta tsokale masu ido ba, wani zai iya jefar sa ko ya jefi ɗaya daga cikin ƴaƴansa da sharri don haka nake bada shawarar a nemo maganin sihiri saboda...."
Kasa ƙarasa zancen ta yi domin a ganinta hakan kamar fallasa asirin mahaifiyarta ne, sai dai ta na son mijinta kuma ta na tausaya masa dole ta nemo masa mafita.
Muryar Mamy ce ta dawo da ita daga tunanin da take, inda take faɗar "Gaskiyar ki ne, cigaba da zancenki saboda...?"
"Uhmm! Dama yaya Saheen ne nake ganin kamar da sihiri a jikinsa, saboda susucewarsa ta yi yawa, da za a nemo wannan maganin sihirin da kowa sai ya sha a huta." Ta faɗa.
Daddy da yake sauraren ta tun sanda ta fara zancen, sai yanzu ya ce "Gaskiyar ki Rumaisa'u, haƙiƙa kin cika mai hangen nesa, ni da kaina na hango susucewa a tattare da Saheen, insha'allah zan nemo mana magani."
Mamy ce ta karɓe zancen da cewa "Habah! Ai dole ma ki gaji Ruma, a ce mutum kullum ka na naniƙe a cikin gida? Daƙyar fa ya ke fita, yau ma sa'a a kayi ya fita har ya jima haka, ko gida fa ya raka ta ba ya barin ta, a haka zai zauna har sai ta tashi su taho tare, haka ranar da ƙawayenta suka zo, na shiga sashenta na tarar da shi zaune tare da su a falo ya ƙi ya ɗaga ya basu guri Habah! Ai abin ya yi yawa, wannan sai dai aikin asiri....."
Follow me on wattpad @ummu inteesar
UMMU INTEESAR CE🌹🌹🌹🌹🌹
👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻
*A SANADIN KAMA*
👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻
*DAGA ALƘALAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*
*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y'AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
DA KUMA
*A SANADIN KAMA*
WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE AKAN NAIRA 200 KACAL
GA MAI BUƘATA SAI YA TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER 08109634202
DON ALLAH IDAN KA SIYA KADA KA FITARMIN HAƘƘIN MALAKA NAWA NE
*AREWA WRITERS ASSOCIATION*
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*
Page 7️⃣3️⃣↪️7️⃣4️⃣
Daga haka suka ajiye hirar aka zaro wata ana yi, washe gari bayan Daddy ya je office yake labartawa abokinsa Alhaji sunusi maganar neman maganin asiri da suka yi jiya a gidansa.
Alhaji sunusin ne ya kira wani babban malamin addini don ya basu addu'ar karya sihiri.
Cikin abinda bai fi kwana biyar ba ya haɗa masu ruwan Ayatus-shifa kusan jarka ɗaya, ya ce abawa kowa na gidan ya sha ya shafe jikinsa safe da yamma.
Godiya ya masa tare da bada abun sadaka, ya saka aka kai masa ruwan gida.
A ranar da aka kawo ruwan, a ranar suka fara amfani da shi, musamman Saheen duk an fi ba shi mai yawa.
Bayan wasu lokuta ya ji canji a jikinsa, shi da kansa ya yarda cewa a baya ba ƙalau yake ba.
Bayan kamar sati biyu da suka fara amfani da ruwan addu'ar, wata ranar talata Mommy ta zo gidan tun sha ɗaya na safe kamar yanda ta saba yi duk sati.
Kai tsaye ɓangaren 'yarta ta shiga, bata same ta ba, da ta tabbatar bata sashen nata sai ta fito, da har za ta wuce part ɗin Mamy sai ta yi tunanin ko ta na ɓangaren Mimie ne?
Tunda aka kawo Mimie gidan bata taɓa leƙa bangarenta ba, yau ɗaya sai ta ji ta na so ta ga me waɗannan matsiyatan suka sakawa 'yarsu a ɗaki?
Domin tun lokacin da ta share su bata kuma bi takansu ba, bare ta san sun samu arziƙi yanzu.
Falon ta faɗa kai tsaye bako Sallama, ai kuwa Ruman na ciki, domin a falo ta same ta tare da Mimie su na hira, ga Affan riƙe a hannunta ta na masa wasa, yayin da Afeef ke cinyar Mimie ya na shan mama.
Tsayawa ta yi ta na ƙarewa falon kallo ganin yanda ya tsaru, kuma aka ƙawata shi da kayan more rayuwa iri-iri.
Nan take ciwon nata na hassada ya motsa a ranta ta ce "Kambuu... Yaushe waɗannan talakawan suka samu galihun siyen wannan kayan? Sai dai in su Alhaji ne suka mata."
Nan fa ta ƙara jin tsanar Mimie na ƙara ratsa ta, kenan hakan na nufin sunyi galaba a kaina? Ai ba za ta saɓuba, goben nan zan koma gun malam a aikace mun ku."
Ta faɗa a ranta.
Miƙewa suka yi dukkansu su na faɗar "Laah! ga Mommy, sannu da zuwa."
Ko kallon side ɗin da Mimie take bata yi ba ta dubi Ruma ta ce "Ke don baki da hankali shine za ki baro part ɗin ki ki dawo na wata ki zauna?"
Ruma ta buɗi baki za ta yi magana ta gwatsale ta, ta hanyar faɗar "Ni don Allah shige mu je wawuya kawai."
Har za ta wuce riƙe da Affan Mommy ta daka mata tsawa "Ki ajiye mata tsumman ɗanta ki wuce..."
Jiki a saɓule Ruma ta ajiye shi, tana jin zafin abinda Mommy ta yiwa 'yar uwarta a yanzu, ta juya suka fice a tare.
Sosai Mimie ta ji zafin abinda ƙanwar Mahaifiyarta ta mata a yanzu, ita ba wulaƙancin ne ya dame ta ba, kamar yanda ta kira ɗan Bassam da suna tsumma, a take tunanin mahaifinsa ya dawo mata a rai, tabbas da ya na raye da ba za a wulaƙanta masa ƴaƴa haka ba.
Komawa ta yi ta zauna ta rungume yaron ta na kuka sosai, a haka Sameer ya shigo ya same ta, ya yi ta rarrashi duk da bai san waya ɓatawa shalelen zuciyarsa rai ba.
©©©©©
Bayan shigarsu part ɗin Ruma Mommy ta nemi da ta zubo mata abinci da nama.
Jinjina kai kawai ta yi ta shige kitchen ta ɗauko mata, domin zuwa yanzu lamarin mahaifiyar tata ya fara bata tsoro.
Tana cikin cin abincin ne Saheen ya shigo gidan a hanzarce da alama ya zo ɗaukar wani abu ne.
Ganin Mommy ya saka ya tsaya ya gaida ta fuskar nan ba yabo ba fallasa, domin shi yanzu mamakin ma yake me ya hau kansa ya auro Ruma? Shi dai ba sonta ya ke ba, amma saboda darajar yaron dake tsakaninsu, da kuma zumuncin dake tsakaninta da Mimiensu ya haƙura ya ci gaba da zama da ita.
Sa kai ya yi zai shige cikin bedroom Mommy ta kira shi "Saheen!"
Tsayawa ya yi cak, tare da juyowa ya ce "Lafiya dai?"
Ta yi mamakin furucinsa amma sai ta haɗiye mamakin ta yi murmushi ta ce "Dama ƙawata ce Hajiya hafsat za ta aurar da 'yarta kuma bani da kuɗin da zan bata gudunmawa, shine na ce bari na zo na gayama na san za a samu a...."
Tun bata ƙarasa ba ya ɗaga mata hannu ya na faɗar "Dakata Mommy, ina ganin girmanki a matsayinki na ƙanwar mahaifiyar Mimie da ba don haka ba, yanzun nan sai na sakar miki 'yarki ku tafi tare. A kan me za ki mayar da ni kamar wani Atm machine, kullum cikin tatsata kike kamar kin samu wata shanuwa? To daga yau na daina baki ko sulena, wanda kika ci a baya ma ya isa." A hasale yake zancen ya na gama faɗa ya sa kai ya wuce abinsa.
Tun da ya fara jawabinsa Mommy ta saki baki ta na kallonsa, tama kasa haɗiye guntun naman dake bakinta tsabar mamaki, a bayyane ta ce "Aiki ya ɓaci? Shirina ya wargaje kenan? Malam baka mun adalci ba da ka bari sihirin nan ya warware da wuri haka, tun ban gama cika burina a kan Alhaji Salman da iyalansa ba."
Har ya kai ƙofar ɗaki ya jiyo ta ta na sambatu cikin alamar tashin hankali, juyowa ya yi ya na faɗar "Dama Allah ba azzalumin sarki ba ne, kuma ya na kallonki duk abinda kike yi, ya aramiki lokaci kaɗan ne, yanzu kuma ya toni asirinki."
Ɗan tsagaitawa ya yi kafin ya dubi Ruma ya ce "Na sake ki saki ɗaya."
Ya dawo da dubansa ga Mommy ya ce "Ke kuma ga Atm card ɗinki nan na sakar miki ita ku je, Allah zai saka mana."
Ya na gama faɗa ya fice daga gidan gaba ɗaya, da alama ya fasa ɗaukar abinda ya kawo shi.
Hannu Ruma ta ɗora a kai ta na kuka take faɗar "Shikenan Mommy burinki ya cika sai ki tashi mu bar masa gidansa."
Ta na gama faɗa ta shiga ciki ta ɗauko Sameer ƙarami, tare da mayafinta, sai ƙaramin akwatinta da ta janyo ta fito waje.
Ita kuwa Mommy dasƙarewa ta yi a gun, tama rasa me za ta yi? Kuka za ta yi ko takaici zata ji?
Fitowar Ruma yasa ta miƙe jiki ba ƙwari ta wanke hannunta suka fita, amma ta lashi takobin sai ta rama wannan wulaƙancin da Saheen ya mata.
Ruma kam tsabar damuwa da take ciki yasa ta manta da zaman wata Mimie ko Mamy a gidan bare ta masu sallama, bin bayan Mommynta ta yi suka bar gidan.
©©©©©©
Da la'asar bayan Mimie ta gama sallarta ta fito zuwa sashen Ruma don ta ga ko Mommy ta tafi?
Sai dai me? Bata tarar da kowa ba a haka ta ƙaraci sallamarta, da ta tabbatar ba kowa ta wuce sashen Mamy.
Nan ma bata tarar da ita ba, kasa haƙuri ta yi har sai da ta tambayi Mamy "Wai ni kam Mamyna ina Ruma ta shiga ne?"
A nan Mamyn ke shaida mata bata shigo ba, hankalinta ne ya tashi ta shiga neman layin Ruman sai da ta kira ta ya fi sau biyar amma bata shiga ba, nan hankalinta ya tashi fiye da da.
Bayan dawowar Saheen ne ya shaida masu abinda ya faru, ya sha faɗa agun Daddy da Mamy sosai, suka ce gobe ya je ya dawo da matarsa, ai ba ita ta masa laifin ba, sai dai ya basu haƙuri da cewa su yi haƙuri ba zai iya dawo da ita yanzun ba, sai Mommy ta gane kuskurenta, akan dole suka ƙyale shi domin 'mai ɗaki shi ya san inda ɗakinsa ke yoyo.'
Mimie ta yi mamaki matuƙa na jin halin shirkar da ƙanwar Mamanta ta faɗa don kawai hassada.
Ta na tausayawa makomar Mommyn tasu.
@@@©©©©
Bayan wata huɗu Sameer da Mimie su na cikin farinciki da kwanciyar hankali, aurensu abin burgewa ne da kwatance ga kowa.
A lokacin ne Sameer ya yi mata zance komawa Bk domin su nemi a mata transfer zuwa Abuja ta ci gaba da karatunta a nan, tunda dama saura shekara biyu.
Daga nan kuma sai akai twins dangin babansu su gan su.
Ta yi murna sosai da wannan tunanin na mijinta, don haka ta fara shirin tafiya ba ƙaƙƙautawa....
Follow me on wattpad@ Ummu inteesar
UMMU INTEESAR CE🌹🌹🌹🌹🌹
👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻
*A SANADIN KAMA*
👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻
*DAGA ALƘALAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*
*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y'AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*RASHIN GATA*
DA KUMA
*A SANADIN KAMA*
WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE AKAN NAIRA 200 KACAL
GA MAI BUƘATA SAI YA TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER 08109634202
DON ALLAH IDAN KA SIYA KADA KA FITARMIN HAƘƘIN MALAKA NAWA NE
*AREWA WRITERS ASSOCIATION*
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*
Page 7️⃣5️⃣↪️7️⃣6️⃣
A ranar
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 13 Chapter of 15