Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ke karatunta?, Kuma tabbas idan ta koma duka wannan kulawar da arziƙin da na ke samu a dalilinta kan iyayenta zai koma." A haka ta wanzu ta na ta tunani kala-kala har drivern ya sauke ta a gida ta shiga. ®®®®®®®®®® Su Zuhra kuwa ana nan baje a falo, sai hira mutanen gidan ke mata amma har zuwa lokacin bata sake jiki da su ba, sai Ruma ce ta ke tamkasu, gata kam sun sha shi, ko motsi su ka yi sai ɗaya daga cikin mutan gida ya matso don jin ko lafiya. A ranar dai yara mazan gidan ba inda su ka tafi duka su na falon ana hira sun tasa ta a tsakiya har wuraren 11:00pm na dare, kowa idon shi na kanta musamman yaya Sameer da ko kyaftawa ba ya yi ya na jin ƙaunarta har cikin jinin jikinsa. Fara mitsittsika ido ta yi alamun ta fara jin barci, yayin da Ruma ta fara gyangyaɗi, su ko mutan gidan ba su da niyyar tashi, tuni Sagir ya yi barci a cinyar Mamy. Ganin haka ya saka Mamy ta kalle samarin na ta ta ce "Ku tashi ku je ku kwanta dare ya yi kun ga ƙanwarku ta fara mitsitsika ido." Miƙewa su ka yi a tare dama sun fara jin Alamun barci Saheen da Samar su ka haɗa baki gurin cewa "Good night Mamy& Daddy." Su ka haura sama zuwa ɗakunansu, Shi ma Salim miƙewa ya yi ya bi bayan su, Sameer ne kaɗai ba ya da niyyar tashi agun. Mamy ta kalle shi yayin da ta ke ƙoƙarin tada su Zuhra su je su kwanta, ta ce "Kai ba ka jin barcin ne ka tsaya a nan?." Sosa ƙeya ya yi sannan ya ce "Uhmm! Dama zan tashi ne ina jira ne Lovely sis ta farka na mata sai da safe sannan na tafi." Murmushi kawai Mamy ta yi ta lura cewa Sameer duk ya fi su zaƙewa gurin nuna soyayyarsa wa sabuwar Mimiensu. Tada su ta yi a hankali Ruma ta buɗe idonta yayin da Zuhra har ta miƙe tsaye kasancewar lokacin ne barcin ya fara surarta bai yi nisa ba. Kallonta Sameer ya yi ya ce "Good night lovely sis." Daƙyar ta iya buɗar ba ki ta ce "Good night." tsabar barci da ke idonta. A haka su ka watse kowa ya nufi sashensa, Mamy ta raka su ɗakin da ta saka aka gyara masu... ®®®®®®®®® Shi kaɗai ne kwance a ɗakinsa kan makeken gadonsa, amma barcin ya ƙi ya ɗauke sa, da ya rufe idonsa ita ya ke gani tana gifta masa fuskarta ɗauke da murmushin da ke ƙara ruɗar da shi, sai juyi ya ke ya rasa yanda zai haƙiƙa so ya masa Shigar sauri, domin abinda ya ke ji akanta ya tsarce soyayyar yan uwantaka, sai dai soyayyar aure, domin a lokacin da Real Mimie ta ke raye ba ya jin irin wannan feelings ɗin akanta...... Ga mai buƙata sai ya tuntuɓeni ta wannan number👇🏼 _08109634202_ Domin na masa ƙarin bayanin yanda zai biya. Ka da ku manta N200 ne kacal. Follow me on Wattpad@ ummu inteesar. Vote, share & Comment. UMMU INTEESAR CE❤️💛💚💙💔💚 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *A SANADIN KAMA* 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *DAGA ALƘALAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU-INTEESAR)* *MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH* *Y'AR GANTALI* *RIKICIN MASOYA* *DA KUMA* *A SANADIN KAMA* Wannan littafin na kuɗi ne akan Naira 200 kacal, ga mai buƙata sai ya tuntuɓeni ta wannan number👇🏼 _08109634202_ Domin na masa bayanin yanda zai biya. KADA KU MANTA KUMA ZAFAFA BIYU DAGA ƘAWAYE BIYU NE IDAN DUKA BIYUN KA KE SO *A SANADIN KAMA DA *ƘURUCIYAR SAPNAH* TO N300 NE, IDAN KUMA WANNAN KAƊAI KA KE SO ZAKA BIYA KUƊIN KARATU N200 KACAL. ________________________ ________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com *BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM* Free Page 2️⃣1️⃣↪️2️⃣2️⃣ A haka Sameer ya kwana cike da mafarki iri-iri akan Zuhra. Washe gari da tun da safe ma su aiki su ka kammala komai na break fast su ka gyaggyara guri kamar dai yanda aka saba. Mamy ce ta fito Sanye da wa su kayan barci riga da wando ma su kyau da tsadar gaske, cikin hanzari ma'aikatan su ka zube a gabanta su na kwasar Gaisuwa. Fuskarta cike da fara'a ta amsa ma su tare da kallon biyu daga cikinsu ta ce "Fariha da ke da Maryam ku je ɗakin Mimie ku kai mata break fast ɗinta acan, sa'annan bayan sun tashi ku gyara ɗakin, daga yau ku ne ma su hidimarta har zuwa lokacin da zata tafi kun ji koh?" Waɗanda aka ambata da waɗannan sunayen su ka ɗaga kai sama alamar gamsuwa su ka ce "Insha'allah Hajiya za'a yi yanda ki ka ce mun gode sosai." Cike da zumuɗi su ka miƙe za su nufin ɗakinta, domin sun tabbatar kakarsu ta yanke saka tun da aka mayar da su ma su kula da y'ar gatan gidan sun san za su fantama, albashinsu ma ninkuwa zai yi. Har sun fara tafiya Hajiya ta dakatar da su da cewa "Ku dakata." Tsayawa su ka yi cak, tare da juyowa su na jiran umurni. "Idan ku ka same ta bata tashi daga barci ba kada a tayar da ita ba na so a takuramin yarinya, ku tabbatar kun faranta mata ta hanyar yin duk abinda ta umurce ku da yin abunda ta ke so." Ɗaga kai su ka yi alamar gamsuwa su ka ce "insha'allah, wannan shi ne aikinmu." juyawa su ka yi su ka nufi cikin, yayin da Hajiya ta juyo ga sauran ta ce "Ku duka kowa ta san aikinta ba sai na jaddada ma ku ba, abu ɗaya na ke so ku sani shi ne kun dai ga ga y'armu Mimie Allah ya dawo mana da ita a karo na biyu, ku tabbatar ba ku yi abun da zai baƙanta mata rai ba, domin idan haka ta faru kun san kwanan zancen ba sai na gaya ma ku ba, ku tashi ku tafi." Miƙewa su ka yi jiki a saɓule su ka fice kowaccensu a ranta ta yi fatar ace ita ce mai kula da Mimie. ®®®®®®®®®® A cikin ɗakin kuwa Zuhra ce ta fara farkawa da misalin ƙarfe bakwai da rabi na safe, dama ita bata fiye nauyin barci ba, kuma da lokacin Sallah ya yi komai barcin da ta ke za ta tashi ta yi, mussanman sallar asuba bata taɓa wuce ta ba, bayan ta gama ne ta koma barci shi ne sai yanzun ta farka. Kallon Ruma ta yi ta ga ko motsawa ba ta yi ba bare ta saka ran za ta tashi, saukowa daga kan gadon ta yi ta nufi bathroom, wankanta ta tsala sa'annan ta fito. Sai dai me? Ta yo wankan amma ba ta san ina za ta samu kayan da za ta saka ajikinta ba, tun da ba su zo da shirin kwana anan ba. Ta na nan a tsaye ta na tunanin mafita ko dai kayanta za ta mayar? Kawai ta ji an turo kofa an shigo, ga shi iya towel ne a jikinta, saurin durƙusawa ta yi ta ƙanƙame jikinta ta na kyarmar sanyi saboda sanyin a.cn da ke ratsa ta. Cikin hanzari su ka ƙaraso kanta a ruɗe su na faɗar "Rankiyadaɗe lafiya dai? Da fatan ba ki ji ciwo ba." Sai a lokacin ta ɗago ta na faɗar "Bakomai qlau na ke, don Allah ku nemo mun kayan da zan saka." Ai tun ba ta gama rufe bakinta ba, Maryam ta fice da sauri, can bayan mintuna Kamar biyar sai ga ta ta dawo riƙe da wata leda ta miƙa mata. Wani tsadadden material ne aciki, ficewa su ka yi daga ɗakin dan su haɗo mata abincin break, kafin su dawo kuwa ta saka kayan. Duk wannan bidirin da ake Ruma bata ma sani ba barcinta ta ke sha, dama ita haka ta ke Allah ya yi ta da mugun son barci ita ko ƙasusuwanta ma ba sa ciyo saboda kwanciya. Bayan sun ajiye mata sun tabbatar bata buƙatar komai su ka fice daga ɗakin. Nan fa Zuhra ta tada kai ta dubi girman ɗakin da ake kira da nata, da kuma kyau da tsaruwarsa, da yadda ake tarairayarta a gidan. Ta kuma tuna yanda gidan iyayenta ya ke da yanda ita ce mai kula da duk wa su aikace-aikacen gidan, anan kuma ga shi ita akewa hidima. Dogon numfashi ta ja ta sauke, a bayyane ta ce "Alhamdulillah, Allah nagode ma ka da irin wannan baiwar da ka mun, Allah ka ƙaro mun daga falalarka." Shiru ta yi na ɗan lokaci komai ta tuna oho, sai ganin na yi ta miƙa hannu ta ɗauko wayarta. Numbersa ta kamo ta danna masa kira, har ta tsinke bai ɗaga ba. A ranta ta ce "kodai Bai tashi daga barci ba ne.." Kafin ta ƙara sa zancen zucinta ta ga kiran shi na shigowa wayarta, ɗagawa ta yi ta na faɗar "Amincin Allah ya tabbata ga angona farin cikin zuciyata." Murmushi mai sauti ya yi kafin ya ce "Ameen tare da ke mai sona, ya ki ke ya kwana biyu? shiru ake jin ki Hajiya Mimie, kin yi kuɗi kin ɓoye." Y'ar dariya ta yi ta ce "Lah! Ka ji Uncle ban son sharri fa, ni ce na ɓoyen?." Shima dariyar ya yi ya canza ma su salon hirar da cewa "To ya abujan ya su Mommy da Ruma?" "Qlau su ke Mommy na gidanta, Ruma kuma ga ta a kusa da ni barci ta ke." Ta amsa masa. Da mamaki a fuskarsa ya ce "A'ah bangane ba ku ku na ina ne?, Ki na nufin bakwa gida?." "Eh haka na ke nufi, mu na gidan Daddy ne ko ince Alhaji Salman daga zuwa kawo ma su Ziyara su ka riƙe mu sai Mommy ce ta koma gida, ba ka ga yanda su ke nan-nan da ni ba, ko Ni ce Real Mimie ɗin sai haka, gaskiya su na son Margayiya Mimie da yawa, anyah! Kuwa za'a samu iyayen da su ke son y'arsu sama da su a duniya kuwa?" "Hmmm! Ikon Allah, ke kam Allah ya kashe ya baki, kin ji daɗinki." Ya faɗa sannan ya ɗora da cewa "Wai sai yaushe ne za ki dawo?" "Saura kwana biyar, kai fa.?" Ta mayar mai da tambaya. Ya amsa da cewa "Ai ni tuni na dawo Kano, sati ɗaya na yi a gida saboda yanayin aikina, kuma na gaya maki, ina ga daular da ki ke ciki ne ta mantar da ke." Ya ƙara sa zancen ya na dariya. A haka su ka cigaba da firarsu a waya har zuwa lokacin da su ka yi Sallama, sai a lokacin ne kuma Ruma ta farka. Kallonta Zuhra ta yi ta ce "Barka da tashi sarauniyar barci ta duniya, da girman kujerarki, ga break fast nan tun ɗazu ke ya ke jira." A dai-dai lokacin ne Sagir ya faɗo ɗakin da gudunsa tare da yin tsalle ya ɗale cinyar Zuhra ya na faɗar "Good morning my lovely sister." Murmushi ta yi ta na faɗar "Morning sweet bro." Tare da shafa sumar kansa don haka kawai ta ji yaron ya na matuƙar burge ta, ya shiga ranta nan take. A dai-dai lokacin ne kuma Mamy ta ƙaraso ciki ta na faɗar "Wai miye haka ka ke yi Sagir? zo mu je, ka da ka takurawa Yayarka." Jin haka ya saka ya ƙara lafewa a jikinta kamar wata mage. Mayar da dubanta ta yi ga Zuhra ta ce "Barka da safiya daddy's girl, dafatar kin tashi lafiya, don Allah ki yi haƙuri ya zo zai takura ki koh? Wallahi tun da asubar fari ya farka ya saka rigima, shi sai a kai sa gurin Sisternsa, daƙyar Sady ta lallaɓa sa ya koma barci." Murmushi ta yi ta ce "Ayyah! Mamy, ai bakomai shi ai ƙanina ne." Ba su an kara ba kawai su ka ji motsi daga ƙofa, Mamy ta juya don ganin ko waye yayin da Zuhra ta ƙura masa ido domin itama bata ankara da zuwansa ba sai yanzu, amma da alama ya jima tsaye agun. ®®®®®®®®®®® Ita kuwa Mommy tsaye ta ke a gaban gas ta na Shirya break fast, Amma kallo ɗaya za ka mata ka fahimci hankalinta baya kan girkin, ta yi nisa a tunani. Mafita kawai ta ke nema ta yanda za ta yi ta zaunar da Zuhra anan domin tsakani da Allah ba ta so wannan daular ta fita daga hannunta, "to ko zan riƙe ta anan ne idan ya so sai ta ci gaba da karatunta anan?" "Shawara mai kyau" wata zuciyar ta faɗa mata nan da nan ta kashe gas ɗin ta kwashe dankalinta da ta gama soyawa, wanda ke cikin man kuwa anan ta bar shi ta yi waje don kiran yayarta a waya. A falo ta dire kayan tare da ɗaukar wayarta ta dannawa Mama kira. Mama na ɗagawa su ka gaisa sosai cike da fara'a sannan ta fara inda-inda ta na son ta roƙe ta su bar mata Zuhra, amma ta na jin tsoron ka da su ƙi amincewa. Can dai ta dake ta yi ta maza ta ce "Am, Yaya dama ina so na roƙi wata alfarma Allah ya sa zan samu." "Insha'allah, indai zan iya kuma bai fi ƙarfina ba zan miki." Murmushi ta yi ta ce "Yaya dama ina so na roƙi Alfarmar ku bar mun Zuhra a hannuna, na yi ma ku alƙawarin zan kula da ita sosai tamkar yan da za ku mata." "Khadija me ki ke nufi da mu bar ma ki Zuhra? Kin san dai ta na karatu anan koh? Kuma bata riga ta kammala ba, ta ya ki ke ganin za mu bari ta rasa karatun da daƙyar da taimakon Allah mu ke ɗaukar nauyinsa?" "Uhmm! Indan wannan ne ba damuwa yaya ni zan saka ta makaranta mai kyau anan, ina mai tabbatar mi ki za ta samu ingantaccen ilimin da za ta taimaki Rayuwarku gaba ɗaya anan." "To na ji ba ma wannan ba Khadija, kin san yarinyar nan fa ta na da miji, ta na gama sakandare aure za mu mata, kafin wannan ma ita kaɗai ce ta rage mun y'a mace a gabana ita ke taimaka mun gun ayyukan gida da sauran su, idan ki ka ɗauke ta ya zan yi?" "Ka da ki damu yaya Ni zan iya ɗaukar maki y'ar aikin da za ta taya ki aiki a gida, ni dai buƙatata kawai ki bar mun Zuhra don Allah, don Allah yayata, ni da ke fa duka abu ɗaya ne." Jikin Mama ya yi sanyi sosai, haka kawai ta ji ta kasa amincewa da Khadijah tabbas da kwai lauje acikin naɗi tun da har Khadija ta dage haka, amma sai ta ce "Shikenan ki kira Babanta a waya ki sanar mai, duk yan da ku ka yi da shi ki sanar min." Ta na gama faɗa ta kashe wayar ba tare da ta tsaya saurarar godiyar da ƙanwar tata ke mata ba. Murmushin cin nasara Mommy ta yi ta ce "Habah! Ko ke fa khadijatu? Amma ta ya yarinya za ta samu arziƙi ta dalilinki ki bar ta ta tafi ta kai wani gurin dabam, ina ai ba za ta saɓu ba bindiga a ruwa." Wani murmushin ta kuma yi wanda ita kaɗai ta san fassarar kayanta sa'annan ta zauna ta fara cin abinci ta ta na ƙissima irin abubuwan da........ Ga mai buƙata sai ya tuntubeni ta whatsapp numberna 👇🏼 _08109634202_ Domin na masa bayanin yanda zai biya. Follow me on Wattpad @ummu inteesar. Vote, share & Comment. UMMU INTEESAR CE💚💙💛❤️💚 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *A SANADIN KAMA* 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *DAGA ALƘALAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU-INTEESAR)* *MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH* *Y'AR GANTALI* *RIKICIN MASOYA* *DA KUMA* *A SANADIN KAMA* Wannan littafin na kuɗi ne akan Naira 200 kacal. Ga mai buƙata sai ya tuntuɓeni ta wannan number👇🏼 _08109634202_ Domin na masa bayanin yanda zai biya kuɗin. KADA KU MANTA KUMA ZAFAFA BIYU DAGA ƘAWAYE BIYU NE, IDAN DUKA BIYUN KA KE SO *A SANADIN KAMA DA *ƘURUCIYAR SAPNAH* TO N300 NE, IDAN KUMA WANNAN KAƊAI KA KE SO ZAKA BIYA KUƊIN KARATU N200 KACAL. MASOYA NA A DUK INDA KU KE INA MATUKAR K'AUNAR KU,ALLAH YA BAR ZUMUNCI. ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com *BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM* Free Page 2️⃣3️⃣↪️2️⃣4️⃣ Ta fara cin abincinta ta na ƙissima irin abubuwan da za ta yi da zarar burinta ya cika na riƙon Zuhra. Bayan ta kammala ne, ta kira Baban Zuhra a waya ta sanar mai da buƙatarta. Kai tsaye ya nuna mata rashin amincewarsa ba wani nuƙu-nuƙu. Sosai ta ji haushin hakan a ranta ta ke cewa "Ku ji mun wannan mutum na saka shi a inuwa ya na ƙoƙarin tura ni rana, tun da ya ga alkhairi ya doso ni ta dalilin y'arsa shi ne zai mun baƙin ciki, to wallahi ba ka isa ba Habu, in ka san wata ai ba ka san wata ba." Dogon tsaki ta ja ka na ta bar gun cike da ɓacin rai. ®®®®®®®®®®® "A'ah! Sam me ka ke yi tsaye agun? Ƙaraso ciki mana." Ƙarasowa ya yi da fara'a sosai a fuskarsa ya na faɗar "Good Morning Mamyna." "Morning dear Sam, dafatar ka tashi lafiya." "Alhamdulillah, qlau na ta shi Mamyna." Ya faɗa tare da mayar da dubansa ga Zuhra fuskarsa cike da murmushi mai ƙayatarwa ya ce "Barka da Safiya Sweet sis." Murya a kasalance ta karɓa masa da "Barka dai." Saboda yanayin yanda ta ga ya ƙura mata ido ba ya ko kyaftawa. Daga jiya zuwa yau ta lura cewa ya fi kowa tsinannan kallo duk a gidannan. Kafin ta gama zancen zucinta ta tsinto muryarsa ya na faɗar "Sweet sis me ku ke jira ne har yanzu ba ku yi break ba." "Uhmm! Za mu yi yanzun." Ta amsa masa. A lokacin ne kuma Ruma ta gyara zamanta ta na faɗar "Ina kwana yaya Sameer, na ga kamar ka manta da ni saboda ganin sisternka?" Ta faɗa ta na dariya kaɗan-kaɗan. Firgigit ya yi tamkar wanda ya farka daga dogon barci kallon ta ya yi ya ce "Yi haƙuri y'ar uwarmu, ba wai na manta ki ba ne dama... Dama....ina so ne na..." Ya na maganar idonsa na kan Zuhra duk sai ya daburce ya rasa ma me zai ce. Dariya sosai Ruma ke yi yayin da Mamy ta yi murmushi ta ja hannun Sagir ta ke kan cinyar Zuhra za su fice daga ɗakin domin ta fara ɗago jirgin ɗan nata, har ta kai ƙofa ta juyo ta na faɗar "Mimiena don Allah ku sauko ku ci abincin ka da ya yi sanyi, don Allah ka da ku bari na dawo na samu ba ku ci ba, shiyasa na saka aka kawo maku har nan domin ku fi sakewa." Ta na gama faɗa ta juya ta fice still ta na riƙe da hannun Sagir da ke ƙoƙarin ƙwace hannunsa daga riƙon da ta masa. Mamy na ficewa shima ya bi bayanta a daburce ganin an fara yi masa dariya, ba ya so ayi saurin kwaɓo jirginsa shiyasa ya fice, saboda ya tabbatar muddin ya na ganin Mimie a gabansa ba a bunda ba zai iya aikatawa ba, saboda ƙaunarta da ta masa dirar mikiya a zuciya. @@@@@@@@@@ Bayan kwana biyu da zuwan Zuhra gidan Alhaji Salman, ta saki jiki sosai domin ta sakankace cewa su ma su ƙaunarta ne, ko da iyayenta ne sai haka su na ririta ta sosai, haka y'an samarin gidanta su na matuƙar son ta ita kuwa ta na girmama su sosai. Fatarta ta murje ta yi kyau sosai acikin kwana biyun nan saboda canjin cima da kuma hutu da ya zauna mata, ko Ruma da ta ke y'ar rakiya ta ƙara kyau sosai har bata so su bar gidan. ®®®®®®®®®®® Shi kuwa Sameer wata irin ƙauna mai zafi ce ta shiga zuciyarsa, sosai wutar soyayyarta ke ruruwa a zuciyarsa. A ranar ne kuma Mommy ta kira Mamy a waya ta ke tambayarta "Yaushe ne su Zuhra za su dawo?" "A yau ne ya kamata su dawo domin kwana biyu ki ka ce." Anan Mamy ta kuma roƙarta da ta ƙara ma su kwana biyu don Allah. "Hmmm! Hajiya ba na so na ce miki a'a, amma ya kamata su dawo haka kin ga yarinyar nan saura kwana biyu ta koma gida akwai shirye-shiryen tafiya a gabanta." Mommy ta faɗa. "Hajiya ka da mu yi haka da ke don Allah ki ƙara haƙuri, ba ki ga yanda iyalan gidan nan ke cikin farin ciki ba saboda dawowar Mimie cikin rayuwarmu, da son samun mu ne ma a bar mana ita anan gaba ɗaya amma na san da wuya iyayenta su amince, amma ki ƙara haƙuri don Allah, insha'allah nan da kwana biyu za su dawo." "Uhmm! Shikenan Allah ya kai mu amma gaskiya dan ke ce kawai shiyasa zan bar su su kuma kwana." "Shikenan Nagode sosai Hajiya, ki turomin da account number na ki yanzu." Ta na gama faɗa ta yanke kiran. Mommy kuwa murna duk ta gama cikata, har hannunta na ɓari gun tura account number ɗin, don ta tabbatar kuɗi ne za'a turo mata. Can kamar bayan mintuna biyar da turawar sai ga alert ya shigo wayarta daga account ɗin Mamy. Naira dubu hamsin ne, sai da ta yi y'ar ƙara kaɗan don murna a bayyane ta ce "Hmmm! Lallai ma Habu, wato wannan arziƙin ne ka ke mun baƙin cikin samu?, Kar ka ji komai ni na san me zan yi a kai." Ta ƙarashe zancen, leɓenta ɗauke da wani busasshen murmushi wanda ita kaɗai ta san fassararsa, ƙwafa ta yi tare da jan dogon tsaki, ta nemi guri ta zauna ta na ayyano abubuwan da ya kamata ta yi, domin ta shiga cikin dukiyar Alhaji Salman ta wataya. ®®®®®®®®®®® A can Kano kuwa mama ce ta ji shirun ya yi yawa, Mommy ba ta kuma kiran ta akan maganarsu ba, hakan ya sa ta ɗaga waya ta kira ta. Har ta tsinke ba ta ɗaga ba, ta kira ta ya kai sau uku amma ba ta ɗaga ba, mamaki ne ya cika ta me wannan matar ke nufi da ƙin ɗaga wayarta? Ko dai ta na fushi ne?, To me aka yi na fushi?. Mama ta shiga jerowa kanta tambayoyin da ba mai amsa mata su, hakan ya sa ta haƙura ta ajiye wayar tare da komawa kan aikin sana'arta ta ɗan wake da ta ke. ®®®®®®®®®®® Ita kuwa Mommy ta na sane ta ƙi ɗaga wayar domin dukkansu haushi su ke ba ta har yayar Tata tun da sun hana mata riƙon y'arsu. A ranta ta ce "Jibi-jibin nan zan tattaro ma ku y'arku na maida ma ku, Nagode Allah da ya sa nima ina da tawa y'ar, da ba ni da ita ne abun zai fi yi mun ciwo, dama shi talaka tsiyarsa kenan ka saka shi a inuwa ya yi ƙoƙarin turaka rana." Ƙwafa ta yi sannan ta ce "Za ku sha mamakina, domin wannan karon ko kwanɗalata ba za ta yi ciwo ba gurin hidimarku da ta y'arku, za ku san kun yi da khadijatu." Ta ƙarashe zancen ta na huci. A ranar ne kuma Sunil da Suhail su ka dawo daga tafiyar da su ka yi. Mommy na ƙoƙarin yi ma su sannu da zuwa, su kuwa ko wannensu ƙoƙarinsa ya ga Zuhra sai raba ido su ke. A tare su ka haɗa ba ki gurin faɗar "Mommy wai ina Zuhran? Ko har ta koma ne?. Harara ta zuba ma su ta na faɗa "Bansaniba, wannan wane irin iskanci ne ina ma ku sannu da zuwa amma ku na tambayar wata can dabam." A tsorace su ke kallon mahaifiyar tasu, fuskarsu ta bayyanar da mamaki ƙarara, to yaushe Mommynsu ta sauya haka? Ita ce fa ta koya ma su ɗokin y'an uwansu tun su na yara, amma yanzu don sun nuna kuma sai ta yi fushi?, Tabbas da wani abu a ƙasa, ruwa baya tsami banza. Daga haka su ka ba ta haƙuri su ka wuce ɗakinsu don watsa ruwa.. A dai-dai lokacin ne kuma kiran Zuhra ya shigo wayarta. Kallon wayar ta yi tare da zubawa screen ɗin harara kamar dai Zuhran ta ke gani a ciki, har ta tsinke bata ɗaga ba, domin zancen gaskiya ita yanzu har Zuhran haushi ta ke bata matuƙa, ta matsu su dawo ta tattara ta ta mayar gidan faƙiran iyayenta kowa ya huta. ®®®®®®®®®®® Washe garin ranar Sameer ne ya farka daga barci a razane duk ya ruɗe sai maimaita faɗar "Innalillahi wa inna'ilahir raji'un!" Ya ke, kallo ɗaya za ka masa ka gano cewa a gigice ya ke, da alama ya yi wani mummunan mafarki ne, gaba ki ɗaya ya gama jiƙewa da gumi duk da a.c da ya ke ƙure a ɗakin nasa. Cikin hanzari ya sauka daga kan gadon ya nufi banɗaki don watsa ruwa. A ransa ya ke cewa "Ya zama wajibi a gare ni, na sanar da Mimie yawan ƙaunar da na ke mata kafin ta tafi gobe, domin gujewa faruwar abinda na gani a

Chapter 4 of 15