An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻
*A SANADIN KAMA*
👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻
*DAGA ALƘALAMIN:*
*RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*
*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y'AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*DA KUMA*
*A SANADIN KAMA*
Wannan littafin na kuɗi ne akan nera 200 kacal duk mai buƙata sai ya mun magana ta wannan layin 👇🏼
_08109634202_
Domin na sanar da shi yanda zai biya kuɗin.
KADA KU MANTA KUMA ZAFAFA BIYU DAGA ƘAWAYE BIYU NE, IDAN DUKA BIYUN KA KE SO *A SANADIN KAMA* DA KUMA *ƘURUCIYAR SAPNAH* TO N300 KACAL, IDAN KUMA WANNAN KAƊAI KA KE SO N200 KACAL.
________________________
________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
GODIYA: Dukkan godiya ta tabbata ga Ubangijin talikai buwayi babban sarki, wanda ya bani dama da iko na rubuta wannan littafin domin fadakarwa, cikin hikimarsa da iyawarsa.
Tsira da aminci su ƙara tabbata ga Manzon tsira Annabi Muhammad (saw), da iyalan gidansa da sahabbansa.
GARGAƊI: wannan labari ƙirƙirarren labari ne, na rubuta shi domin faɗakarwa da kuma nishaɗantarwa, ban yadda wani/wata ya juyamun labari ta kowacce fuska ba.
Dafatar Allah ya sa wannan rubutun ya amfani al'umma.
BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM
Free Page 1️⃣ ↪️ 2️⃣
Y'an mata ne guda biyu a tsakar gidan, dambe su ke Sosai, hayaniyarsu ce ta fito da ita daga ɗakinta, kai tsaye gunsu ta je domin ta raba faɗan, a lokacin har kowaccen su ta ja da baya sun yi carko-carko kamar zakaru sai haƙi su ke.
Tsayawa ta yi a gabansu ta na faɗar "Don Allah ku yi haƙuri." Mai da dubanta ta yi ga Babbar ta ce "Habah! Ke kuwa shamsiyya kiyi haƙuri mana, ke da ƙanwarki bai kamata ki bari aji kanku ba, don kawai ta saka kayanki ai...."
Bata ƙarasa maganar ba saboda saukar wani gigitaccen mari da ta ji a kuncinta.
A firgice ta ɗago don ganin waya aikata mata hakan.
Idonta ne su ka sauka akan Shamsiyya ta na huci ta fara magana kamar haka "Ke Malama ki hita harkata ban kasa da ke balle ki ce za ki kwasa, banza y'ar matsiyata, da ba a san asalin balbela ba sai ta ce daga Makka ta ke, mun san komai da ki ke cewa bai kamata na yi faɗa akan ta sa kayana ba, na ga ai ba ubanki ne ya siya ba, da kuɗin yayana ne balle amin gori."
Har ta juya za ta tafi, Shamsiyya ta yi saurin riƙe hannunta ta na faɗar "ina za ki tahiya? Ai ban gama ba takwan, na san dai da wannan Baban bugin na ki ki ke taƙama, wassani ma ko zaman dadiro kin ka yi gidansa a Abuja anzo an cuci yayanmu wai *A sanadin kama* aka samu wannan arziƙin..."
Fincike hannunta ta yi daga riƙon da ta mata don zuwa lokacin ji ta ke kamar ta maƙure ta, kalaman sun mata zafi matuƙa, tabbas idan ta ƙara ko da mintuna biyu ne a gurin za'ayi ɓarna don a yanda ta ke ji za ta iya shaƙeta ko ta mata dukan Kawo wuƙa, sai dai wannan ya zama ƙarshen zamanta a gidan.
Babban baƙin cikinta shine Innarmu ta na zaune a gurin tun lokacin da Shamsiyya ta fara mata ɗibar albarka, amma ko motsawa bata yi da zimmar hanata ba.
Da gudu Mimie ta ƙarasa ɗakinta ta na matsar ƙwalla, har ta shige ƙaramin falonta mai kama da kurkuku saboda zaman sa ƙarami, ta na jiyo ihunsu su na mata dariya da izgili kala-kala.
Mijinta ta tarar a zaune kan kujerar falo ya na danna wayarsa, ya ɗage labulen kofar domin ɗakin akwai zafi, da alama ya ji komai da ya ke faruwa a wajen.
Guri ta nema ta zauna akan ɗayar kujera da ya ke kujera uku kawai ce a falon.
Kifa kanta ta yi akan hannun kujerar a hankali ta fara rera kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro.
Har izuwa lokacin ko ɗago kansa bai yi ba bare ta saka ran zai kulata har ya bata haƙuri, sai danna wayarsa ya ke abunsa.
Da ya ga za ta dame shi da kukanta kawai sai ya miƙe yabar mata ɗakin gaba ɗaya.
Kuka ta ke sha sosai zuciyarta cunkushe da baƙin ciki kala-kala, haƙiƙa ta riga ta saba da irin wannan cin mutuncin da mutanen gidan su ke yi mata, sai dai na yau yafi baƙanta mata rai, Daddynta wanda ta ke matuƙar girmamashi da sonsa a ranta, wanda duk duniya banda iyayenta a yanzu ba ta da tamkarsa, wanda ya kyautata rayuwarta, shi ne yau ake alaƙantata da shi ta hanyar alfasha gaskiya ba za ta iya jura ba.
Abunda yafi yi mata ciwo ma shi ne Uncle ya na Zaune ya na ji amma bai yi yunƙurin ɗaukar mataki ba hasalima ko rarrashin ta bai ba, to ina ƙaunar da ya ke mata ina son da ya ke iƙirarin ya na yi mata.
Shine fa wanda ta bijirewa shawara iyayenta saboda shi domin ta na ganin cewa ya fi kowa sonta, amma yau shine ya ke wulaƙanta ta.
Haƙiƙa ta yi nadamar bijirewa iyayenta da ta yi a shekarun baya.
Ta na kawowa nan a tunaninta ta kuma rushewa da wani matsanancin kuka.
Kukanta ta ke sha sosai babu mai rarrashi, ta na cikin wannan halin ne kiran Daddy ya shigo wayarta.
Dakatar da kukan ta yi tare da ƙoƙarin sai-saita nutsuwarta kafin ta ɗaga kiran.
Cike da fara'ar ƙarfin hali su ka gaisa, anan ta ke tambayarsa "Ya su Momy da yaya Saheen? Na yi missing ɗin su da yawa"
"Su na qlau." Ya karɓa mata, sai dai ya fahimci da akwai yanayin damuwa a muryarta duk iya ƙoƙarin ɓoye hakan da ta yi kuwa.
Saboda haka ya ce "Mimiena meke damunki ne?"
Cikin in.. ina ta ce "Bakomai Daddyna me ka gani ne?."
"Bakomai kawai dai ina ji a jikina cewa da akwai wani abun da ki ke ɓoye mun, amma dai shikenan tunda kince bakomai, fatana shine ko da yaushe ki kasance cikin farin ciki."
"Lah! Daddyna ba fa komai, ta ya ka ke tunanin zan ɓoye maka wani abu?." Ta faɗa ta na y'ar dariya kai da gani ka san ƙarfin hali kawai ta ke.
"Shikenan ina Bassam, ki ba shi mugaisa."
"Yanzun nan ya fita Daddy, sai dai idan ya shigo zan sanar masa."
"Ok idan ya zo ki ce ya kirani, ina son magana da shi, ki kula da kanki Mimiena sai anjima."
"Ok Daddyna bye, ka gaida mutan gidan."
Daga haka ya kashe wayar, kamar jira ta ke ta na ganin tsinkewar wayar ta kuma rushewa da wani kukan ta na faɗar "Allah sarki Daddyna mai yawan ƙaunata, ka yi haƙuri ba zan iya sanar da kai halin da na ke ciki ba, ina tsananin jin kunyarka na ƙin jininka da na yi, ta yaya zan gaya maka cewa wanda na ƙi ɗanka akansa ya na wulaƙanta ni yanzun? Inah! Bazan iya ba."
Wata doguwar ajiyar zuciya ta ja ta sauƙe sannan ta ci gaba da cewa "Allah sarki! Yaya Sameer Allah ya baka lafiya, ka gafartamin na saka rayuwarka acikin garari da na yi saboda son zuciyata, ga shi yau wanda na guje ka a kansa ya juya min baya, rayuwa ta mun ƙunci ba shakka alhakinku ne ke bibiya ta na butulce maku.."
A haka ta wanzu ta na waɗannan sambatu cikin kuka har zuwa wani lokaci mai tsawo.
®®®®®®®®®®®
Bassam ne ya shigo ɗakin a kufule, inda ya barta anan ya same ta sai dai zuwa lokacin ta daina kukan sai dai sheshsheƙa, ta yi zurfi a tunaninta ta tsinto muryarsa ya na faɗar
"Ke! Ke!! Ke!!!." Cikin tsawa.
Firgigit! Ta yi ta na kallonsa a tsorace.
"Ke! Wane irin iskanci ne wannan, ki zo ki ƙunshe a ɗaki har zuwa wannan lokacin ba tare da kin ɗora mana girki ba? Sarai kin san ba na son ɓata lokaci a dukkan lamurana."
"Ka yi haƙuri uncle ba na jin daɗi ne yanzu zan je na ɗora."
"Da ya fi miki kam." Ya faɗa ya na ƙoƙarin zama akan kujera.
Cikin hanzari ta miƙe ta nufi waje, domin ta san abinda zai iya faruwa idan ta ƙara ko da minti ɗaya ne, domin da alama an zugoshi shi isa ya zo zai balbaleta da bala'i.
Tsakar gidan ta nufa gurin murahu ta na ƙoƙarin haɗa itace, a bayanta ta jiyo ana Faɗar........
Ya kuka ji readers? Wannan salonsa dabam ne da sauran, amma sai na ji daga gareku yawan Comment ɗin ku shi zai nu namin yanda ku ka karɓi abin,
Acigaba ko yaya?
Ga mai buƙata zai tuntubeni ta wannan number👇🏼
_08109634202_
Domin karin bayani.
SHARE & COMMENT.
UMMU INTEESAR CE❤️❤️❤️❤️❤️
👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻
*A SANADIN KAMA*
👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻
*DAGA ALƘALAMIN:*
*RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*
*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y'AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*DA KUMA*
*A SANADIN KAMA*
Wannan littafin na kuɗi ne akan farashi mai sauƙin N200 kacal, duk mai buƙata sai ya mun magana ta wannan number👇🏼
_08109634202_
Domin na sanar da shi yanda zai biya kuɗin.
KADA KU MANTA KUMA ZAFAFA BIYU DAGA ƘAWAYE BIYU NE, IDAN DUKA BIYUN KA KE SO *A SANADIN KAMA* DA *ƘURUCIYAR SAPNAH* TO N300 NE KACAL, IDAN KUMA WANNAN KA KE SO ZA KA BIYA KUƊIN KARATU N200 KACAL.
________________________
________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*
Free Page 3️⃣↪️4️⃣
A bayanta ta jiyo ana Faɗar "To Malalaciyar banza shi haɗa itacen shi aw-wani aiki? Da kin ka tsaya ki na abu solai-solai kamar mara lakka?."
Shiru ta yi bata tamka ba, Innarmu ta cigaba da cewa "ki yi sauri ki gama ki ba mu murhu y'ar hutu, ai ki za mu yi aiki ."
Daga haka ta juya ta koma inda ta fito.
Girgiza kai kawai ta yi ta cigaba da aikinta ƙwaƙwalwarta cunkushe da tunani iri-iri.
Sai a lokacin ta tuna da saƙon Daddy, rufe tukunyar ta yi bayan ta haɗa komai sannan ta wuce ɗakinta don sanar da shi saƙon.
®®®®®®®®®®
Ɗagawar ta daga gun ke da wuya Shamsiyya ta laɓaɓo ta zabga mata gishiri mai yawa a miyar, ta rufe tukunyar kamar yanda ta same ta a farko, ta juya ta bar wajen ta na murmushin mugunta.
Ƙarasawa ta yi gun Zinnira da ke tsaye can gefe ta na kallonta , hannu ta ba ta su ka tafa ta ce "Kai anma gaskiya ke iya mugunta Shamsiyya, shiyassa ni ka bala'in sonki, yau za mu yi kallon casu a gidan nan."
Ƙara tafawa su ka yi su na dariya da shewa ta ce "Ai wallahi Zinnira ba ki san yanda na tsani matagga ba, ni wallahi ke kaɗai na ke so yayana ya aura na san za mu shana, da ba don mu na cin arziƙinta ba agidan nan da tuni ta bar gidan wallahi."
A haka su ka ta gulmar su su na dariya.
®®®®®®®®®®®
A uwar ɗakanta ta Same sa ya na kwance da alama yunwa ce ke nuƙurƙusarsa, ƙarasawa ta yi kusa da shi ta ce "Dama na manta ne ɗazu mu ka yi waya da Daddy ya ce ka kira shi idan ka dawo."
Miƙewa zaune ya yi a fusace ya ce "Me zan ma shi da ya ke nema na? Ni fa wannan mutumin ya fara takura mun, ko Baba da ya ke mahaifinki ba ya mun takurar da wannan mutumin kemin Why?"
Sassauta murya ta yi sannan ta ce "Na ga wata ya zo ƙarshe ƙila kuɗi ya ke so ya tura ma ka ne kamar ko wanne wata."
Washe baki ya shiga yi, shi ya manta shaf da ƙarshen wata ya zo dama ya na cikin buƙatar kuɗi don haka ya ɗauki wayarsa ya shiga neman layin Daddy.
Kafin ta shiga ya kalleta ya ce "Na manta wallahi, kin san Daddy akwai ƙoƙari ba ya gajiya da hidimta mana, ko ke ce *Real Mimie* iyaka kenan.
Har ta tsinke ba'a ɗaga ba ya shiga nema a karo na biyu tare da Faɗar "Mimien Daddy kenan y'ar Albarka tafi abinki ki cigaba da aikinki bari mu yi waya."
Ficewa ta yi daga ɗakin ta na murmushin yaƙe "Hmmm! Uncle kenan an ji zancen kuɗi daɗin baki ya tashi, Daddy bai san cewa wacce ya ke turo kuɗin saboda ita ko ƙwandala bata mora aciki ba." Ta faɗa a ranta.
Ta na ida sa isowa gun girkinta su ka bushe da dariyar mugunta Sakina da ta fito yanzu daga ɗakin su ta dubi Mimie ta bushe da dariya, mayar da dubanta ta yi ga Shamsiyya ta ce "Kai gaskiya yaya amma fa ke y'ar hutu ce, duba fa tsabar hutu da sabon zaman gidan daula ko itace baki iya sawa ba ga murhu."
Dukkan su su ka bushe da dariya.
Ita dai bata tamka su ba duk da ta sani sarai da ita su ke, girgiza kai kawai ta yi ta cigaba da aikin gabanta.
Tabbas ta tabka babban kuskure a rayuwa sai yanzu ta gasƙata zancen malam ba haushe da ya ke cewa duk abinda babba ya hango yaro ko ya hau Rimi ba zai hango shi ba, a baya soyayya ta rufe mata ido ta kasa hango abinda iyayenta su ke nuna mata ga arziƙi na kiranta amma ta rufe ido ta saka ƙafa ta murje, ta tabbatar cewa da yaya Sameer ne a matsayin mijinta yanzun tabbas da ba zai mata irin wannan wulaƙanci ba, ko dan yawan soyayyar da ya ke yiwa *Real Mimie* da kuma kamar da su ke yi, shiyasa su ka mayar da ƙaunar akanta.
Da yanzu ta na kwance miƙe da ƙafa acikin sanyin A.C sai dai a mata duk abinda ta ke so bare ma har ta yi wani girki can.
Haka ta cigaba da tunani da kukan zuci har ta kammala girkinta, kuloli ta ɗauko ta ɗibarwa kanta mijinta sauran kuma ta zube a babbar kula ta ɗauka ta kaiwa Innarmu.
®®®®®®®®®®®
Bayan ta kai ma shi abincin ta zuba ma shi a plate, durƙusawa ta yi agabansa ta ajiye, shinkafa ce da miya.
Saukowa ƙasan ya yi ya na wani ciccin magani, wai shi a dole ransa ya ɓaci na rashin gama girkin da wuri, ko uffan bai ce mata ba ya ɗauki cokali ya ɗiba abincin zuwa bakinsa.
Da sauri ya furzar da lomar bakinsa, sakamakon wani zau da ya ji har cikin kunnuwansa.
A gigice ya miƙe zuwa waje ya ɗebi ruwa ya na kuskure bakinsa.
Su Zinnira da ke gefe su na kallonsa sai ƙunshe dariya su ke don kada ya ji.
Ita kuwa Mimie tun lokacin da ya furzar da abincin ta ke binsa da kallo har zuwa lokacin da ya bar ɗakin, biyo bayansa ta yi don ganin me ya same shi, idonta ne ya sauka akan su Shamsiyya da ke famar ƙunshe dariya, nan da nan ta zargi wani abu akansu.
"Me ya faru uncle?" Ta tambaye shi.
Juyowa ya yi a fusace ya zabga mata wata uwar harara ba shiri ta koma ɗakinta cikin hanzari.
Shima bin bayanta ya yi a kufule, nan fa y'an matan su ka bushe da dariya harda k'yalk'yalawa.
Tafiya ta fara yi ta na nufar ɗakin, cikin zafin nama Zinnira ta yi taku ɗaya ta damƙo ta ta na faɗar "Ina za ki?."
Dariya ta yi ka na ta ce "Bin su zan yi in ga yadda za'a kwashewa."
Fiddo ido wa je ta yi ta ce "Ashe ba ki da hankali Shamsiyya? In ya gane ki hwa?."
"Ke taho mutahiya in kuma ba ki zuwa banni Ni in je."
Daga haka ta fusge hannunta ta ƙara gaba abinta.
®®®®®®®®®®
A can cikin ɗakin kuwa bayan shigewar su Bassam ne ya rufe ta da masifa inda ya ke shiga ba nan ya ke fita ba Faɗar ya ke "Wannan wane irin abinci ne haka? Wato zaman Abuja ya lalata ki har kin manta yanda ake girki koh?"
"Wai me abincin ya yi Uncle?"
"Au tambaya ta ma ki ke? Ai ki na da harshe sai ki ɗanɗana ki ji." Ya faɗa a tsawance.
Da sauri ta je gun Abinci ta ɗanɗana ba shiri ta furzar da shi tare da zaro ido waje, ya akayi haka? ita fa gishiri kaɗan ta san ta zuba a girkinta, nan ta tuna sanda ta ga su Shamsiyya na dariyar ƙeta ba ko shakka su su ka mata wannan aikin.....
Kada ku manta wannan book ɗin na kuɗi ne akan N200 kacal, ga mai buƙata sai ya tuntubeni ta whatsapp number ɗina👇🏼
_08109634202_
Follow me on Wattpad @ UMMU INTEESAR
UMMU INTEESAR CE❤️💚🧡💙💛
👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻
*A SANADIN KAMA*
👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻
*DAGA ALƘALAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*
*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y'AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*DA KUMA*
*A SANADIN KAMA*
Wannan littafin na kuɗi ne akan Naira 200 kacal, duk mai buƙata sai ya mun magana ta whatsapp number na👇🏼
_08109634202_
Domin na sanar da shi yanda zai biya kuɗin.
KADA KU MANTA KUMA ZAFAFA BIYU DAGA ƘAWAYE BIYU NE, IDAN DUKA BIYUN KA KE SO *A SANADIN KAMA* DA *ƘURUCIYAR SAPNAH* to N300 ne kacal, idan kuma wannan kaɗai ka ke so za ka biya kuɗin karatu N200.
________________________
________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*
Free Page 5️⃣↪️6️⃣
Ɗagowa ta yi a firgice fuskarta ta bayyanar da firgici ƙarara ta ce "Wallahi Uncle ba haka na yi girkina ba, ban san ya aka yi gishiri ya yi yawa ba ka yi haƙuri don Allah ba......."
Ba ta samu damar ƙarasawa ba saboda jin saukar wani lafiyayyen mari da ta yi a ƙuncinta.
A tare su ka zazzaro ido shi da ita, ita ta na mamakin yanda ya mare ta abinda bai taɓa yi mata ba a rayuwa.
Shi kuma ya na mamakin tayaya ya mare ta? Me ya hau kansa? Allah ya gani bai ɗaga hannu da nufin marinta ba sai don ya mata gargaɗi.
Shamsiyya da ke laɓe ta taga ta na kallon bidirin da ake a falon ta bushe da wata ja'irar dariya har ta na riƙe ciki.
Jiyo sautin dariyar ne ya saka ya yi saurin dubar gurin da sautin ke fitowa, cikin hanzari ta juya da zimmar barin wajen ƙirjinta na lugude, "Shikenan yau kashina ya bushe." Ta faɗa a ranta.
Ke! Ta jiyo sautin muryarsa ya na daka mata tsawa, yi ta yi kamar bata ji ba, za ta wuce ya ce "Da ke na ke munafuka zo nan."
Jiki na ɓari ta ƙarasa ya zazzare mata ido ya na faɗar "Uban me ki ke leƙe a tagar?"
Shiru ba amsa, ya kuma daka mata tsawa a karo na biyu ya ce "Na ce uban me ki ke leƙe? Wato dama ashe laɓe ki ke mana koh?."
"Ya...yaya kayi hak ƙuri." Ta faɗa cikin in Ina.
Wanke ta da mari ya yi sannan ya ce "Don ubanki gobe ma kya ƙara mana laɓe, ɓace mun da gani munafukar banza."
Sum, sum ta ja jiki ta bar gurin tamkar wata munafuka(ko da ya ke munafukar ce ma).
Ɗakin ya koma ya na bawa matarsa haƙuri Faɗar Ya ke "Don Allah Mimiena ki yi haƙuri ban san me ya hau kaina ba har na mare ki wallahi ban aikata hakan da niyya ba, ina son ki matata amma na rasa me ya sa na ke mi ki irin haka, sanda mu na wancen gidan na birni ai ba haka zaman mu ya ke ba dawowa nan ne ya sa....."
Bai ƙarasa maganar ba saboda Muryar Innarmu da ya jiyo tun daga waje ta na sababi ita don me za'a dakar mata y'a akan wata jaka, fitowa ya yi ya bata haƙuri ya lallaɓata a ka wuce gurin.
FLASH BACK
WACECE MIMIE?
Cikakken sunanta shine Zuhriyya Sadeeq Yusuf, amma iyayenta da y'an uwa su na kiranta Zuhra.
Zuhra y'a ce ga Malam Sadeeq Yusuf Bicci, haifaffen ƙauyen Bicci ne ta jihar Kano.
Shi talaka ne mai ƙaramin ƙarfi sana'arsa ita ce kanikanci, da kuma wannan sana'ar tasa ne ya ke ciyar da iyalansa da duk wata buƙata ta su wacce bata fi ƙarfinsa ba.
Shi Mutum ne mai wadatar zuci hakan ya sa ba ya hangen abin hannun kowa ciki harda y'an uwansa da su ka kasance ma su rufin asiri sosai saɓanin shi.
Matarsa ɗaya Malama A'isha wacce ta kasance uwar ƴaƴansa wato maman Zuhra.
Ta na da yayye maza guda biyu, Kabir wanda ya kasance shine babban yayansu sai Sagir wanda ke binsa, sai farida sai kuma ita Zuhran sai ƙaramin ƙanensu Ma'aruf wanda shine ƙarami daga kansa Malama A'isha bata ƙara haihuwa ba, yanzu har yara sun girma.
Inda Kabir ya yi aure da matarsa mai suna Zainab su na kiranta da Anty Zee, su na da yara Uku Khalifa wanda ya ci sunan Baba wato (Abubakar Sadeeq). Siddiqa da kuma ƙaramin Lameer, Shekara Shida kenan da aurensu.
Yaya Sagir kuwa ya yi aure 2years ago matarsa bata haihu ba har yanzu.
Yaya farida ma ta yi aure tuni da mijinta mai suna alƙasim ta na da ƴaƴa Uku Salim, Safnah da Amir ga cikin na huɗu kuma.
Sai ita Zuhran da ta ke da Shekara biyu da aure, an mata aure ne bayan ta kammala Secondary school ɗinta anan jihar kano lokacin ta na da Shekaru goma sha takwas a duniya.
A lokacin Ma'aruf ya na jss3, a wannan shekarar zai kammala Secondary.
Duk da cewa mahaifinsu talaka ne hakan bai saka rayuwarsu a ƙunci ba sun ta so cikin kulawa da tarbiyya mai kyau, mahaifinsu ya na iya ƙoƙarinsa gurin kula da karatunsu dukkannin su a makarantar gwamnati su ke karatu, baya wasa da abinda ya shafi ilimi, saboda haka ƴaƴansa su ka kasance ma su ilimin zamani da na addini dai-dai gwargwado.
®®®®®®®®®®
Yaya Kabir malamin makaranta ne ya na koyarwa a wata Secondary school anan cikin garin Kano, shine ya ke taimakawa mahaifinsa gurin kula da wasu buƙatun gida a wancan lokaci.
Duk wata idan ya karɓi Albashinsa ya ke rabawa biyu, rabin ya yi bukatarsa da ta iyalansa sauran kuwa ya siyo ma su kayan abinci ya ajiye.
Yaya Sagir ma ya na iya ƙoƙarinsa duk da cewa a lokacin bai samu damar cigaba da karatu ba sai ya ke aikin ƙarfi.
Da ɗan abinda ya ke samowa ya ke biyan buƙatarsa da taimakawa ƙannensa ta
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 1 Chapter of 15