yi ki ja ra'ayinsu ki dinga naniƙe musu, ki yi duk abinda ki ka ga za ki iya, ni dai burina ki cafko zuciyar ɗaya daga cikinsu daga nan sai ki bar komai a hannu na." (Wa'iyazu billah wai uwa ce ke yi wa yarta wannan huɗubar saboda son abun duniya, Allah ya kyauta.)
®®®®®®®®®®
Sameer kuwa damuwa ta zame masa mugun ciwo a zuciya, domin duk ya ƙwarjame ya rame, a ranar da Daddy ya kira shi ya sanar da shi cewa ya yi haƙuri da auren Mimie domin ta na da nata zaɓin kuma shi ya goyi da bayanta, ya roƙi Allah ya zaɓa mai mafi alkhairi, har suman zaune sai da ya yi.
Amma ba yadda ya iya haka ya haƙura domin shima ya fi son farin cikin nata akan kwanciyar hankalinsa.
Tun daga lokacin Sameer ya zama abun tausayi kullum likitansu na hanyar zuwa gidan Alhaji domin duba lafiyarsa.
Mamy duk ta shiga damuwa ta na cikin wannan damuwar ne kuma Mommy ta kwaso Ruma ta kawo mata, haka nan ba yadda ta iya ta nuna murnarta a fuska, amma a zuciyarta damuwar ciwon ɗanta ne fal aciki.
®®®®®®®®®®
Bassam kuwa ya na ta shirye-shiryen angwancewa, ga shi ya na son turo iyayensa amma Baba bai bada fuska ba.
Ita kuwa Mimie kowa ya fita sha'anin ta duniya ta mata ƙunci a haka su ka fara waec bata da kwanciyar hankali har yayyenta duk sun share ta, gaisuwarta kaɗai su ke amsawa ita ma sai sun ga dama.
Gidan yaya Farida kaɗai ta ke zuwa ta ji ɗan sanyi-sanyi, to can ɗin ma Baba ya hanata zuwa yanzu.
Ana cikin haka iyayen Bassam su ka ce za su zo kawo kuɗin aure, ta je da kanta ta samu Mama a sanyaye ta sanar mata.
"Ki je ki faɗawa babanki ni ba ruwana a lamarin." Mama ta faɗa.
Jiki ba ƙwari ta fice ta samu Baba a ɗaki ta sanar mai daka mata tsawa ya yi ya ce "Ki ɓace mun daga nan mutuniyar kawai, ki je ki nemi wani uban amma ba ni ba."
Cikin rashin madafa da mutuwar jiki ta miƙe ta bar ɗakin, zuciyarta ta riga ta ƙeƙashe a kan komai za'a yi ba za ta canza zaɓinta ba duk rintsi.
Mafita ɗaya ta rage mata ita ce ta kiran Daddy, don haka ba ɓata lokaci ta kira shi ta na kuka ta sanar mai abunda Baba ya ce da kuma halin da ta ke ciki a gidan.
Lallashinta ya yi ya sanar mata da kwantar da hankalinta insha'allah zai zo da kansa har Kano don yin magana da baba.
A cikin kwanakin kuwa Daddy ya dira Kano, lallaɓa Baba ya shiga yi, daƙyar ya shawo kan Baban sai dai duk da haka ya ce shi ko ƙwandalarsa ba za ta yi ciwo a auren Zuhra da Bassam ba.
Murmushi kawai Daddy ya yi ya ce "A haka ma mungode saka albarkarka kawai mu ke nema, ni ne zan yi komai na auren y'ata insha'allah."
Daddy da kansa ya kira Bassam ya sanar mai ya turo iyayensa, dama abu ga mai jira domin tuni ya shirya komai dama kawai ya ke jira abashi don haka ya na komawa gida ya sanar da Alhaji sale(Aminin babansa ne da ke zaune a nan Kano, a hannunsa Bassam ya ke.)
Tun kan Daddy ya bar garin su ka kawo kuɗin auren Mimie tare da sadaki gaba ɗaya kuma ta ke a gurin a ka saka rana wata ɗaya, da ya ke shima Daddyn Amaryar a shirye ya ke shiyasa ba'a samu wata tangarɗa ba.
Bayan an kammala da wannan ne Daddy ya koma Abuja, ya je ma su da Albishirin da ya zamewa Sameer gobarar zuci.
®®®®®®™™™
Murna a gun Mimie da Bassam kuwa ba'a cewa komai sai albarka su ke sakawa Daddy da masa fatar dacewa da alkhairai duniya da lahira......
Ga mai buƙata sai ya tuntuɓeni ta wannan number
08109634202
Follow me on wattpad @ummu inteesar
UMMU INTEESAR CE❤️❤️❤️❤️❤️
👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻
*A SANADIN KAMA*
👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻
*DAGA ALƘAMIN RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU-INTEESAR)*
MARUBUCIYAR SOYAYYAR MEERAH
Y'AR GANTALI
RIKICIN MASOYA
DA KUMA
A SANADIN KAMA
WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE AKAN NAIRA 200 KACAL
GA MAI BUƘATA SAI YA TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER 08109634202
DON ALLAH IDAN KA SIYA KADA KA FITARMIN HAƘƘIN MALAKA NAWA NE
Arewa writers association
Page 4️⃣3️⃣↪️4️⃣4️⃣
A cikin wata ɗayan da aka saka ne ta yi Candy, lokacin da ya rage bikin saura sati ɗaya Mama ta kira Mommy ta sanar mata duk da cewa ba'a son ranta za'a yi auren ba, kuma y'ar uwar tata ta share ta tun lokacin da aka hana ta rikon Mimie hakan bai hana ta sanar mata ba domin acewar ta itama ta na da haƙƙi ya rage nata ta zo ko akasin haka.
®®®®®®®®®®®
Abuja
Lokacin da ya rage saura kwana goma bikin, su Mamy ne da Daddy ke ta tsare-tsaren yanda bikin zai kasance domin wannan karon duka iyalan gidan za su je bikin shalelensu.
Duka ahalin gidan, su na zaune a makeken falonsu, amma banda Sameer da ke kwance a ɗakinsa ya na jinya, anata hirar yanda tafiya Kano za ta kasance wannan karon, domin tuni Daddy ya tura kuɗin komai na kayan ɗaki a account ɗin yaya Kabir an siyar mata komai.
Sameer ne ya sauko daga bene a hankali ya nufo inda su ke zaune, ka na ganinsa ka san cewa baya cikin hayyacinsa, ga shi duk ya rame ya yi baƙi..
A hankali ya ƙara so gun kamar mara lakka ya nemi guri ya zauna ya na faɗar "Mamy & Daddy barkan ku da dare."
"Yawwa Barka dai ya ƙarfin jikin?." Su ka amsa a tare.
"Alhamdulillah jiki da sauƙi." Ya faɗa.
Saheen da sauran ƙannensa su ka gayar da shi ya amsa sannan ya ce "Hirar me ake? Tun daga sama na ke jiyo dariyarku."
Mamy ta ce "Muna hirar yanda tafiyarmu kano bikin ƙanwarka za ta kasance ne, ka yi ƙoƙari ka shirya ina tsammanin duk gidan nan kai ne kaɗai baka shirya ba domin kwana uku ya rage tafiyar mu."
Wani busasshen murmushi ya yi wanda iyakacinsa fatar bakinsa ya ce "Uhmm! Ai Mamy ina ga tafiyar nan ba da ni ba."
Fiddo ido waje ta yi ta ce "What? To saboda me? Kenan idan Real Mimie ce a raye ba za ka je ɗaurin aurenta ba?"
Gyara zamansa ya yi ya na cije baki da alama ya na shan wahala a zuci da gangar jiki Ya ce "Ba haka bane, tafiya zan yi ne."
Bai jira jin me za ta ce ba ya juya ga Daddy, a dai-dai lokacin da ta ke tambayarsa Ina za ka je ne?
Bai bata amsa ba sai kallon Daddy da ya yi ya ce "Daddy ina neman wata alfarma a gunka, don girman Allah ka ba ni dama na bar ƙasar nan kafin cikar makon nan, ina so zan je wata ƙasa na ƙarasa masters ɗina acan."
Kallonsa kawai Daddy ya ke, bai yi yunƙurin katse shi ba sai da ya dire zancensa sannan Daddyn ya ce "Karatu a waje kuma da gaggawa haka? To miye Dalili? Na ɗauka a can baya kai ne ka ƙi wannan, lokacin da na so tura ka ka yi digiri a India me ka ce?"
Ƙara matsowa ya yi kusa da Daddy ya yinda duka Mutane falon su ka zubo mai ido don son jin dalilin wannan tafiyar ta gaggawa.
Ya ce "Daddy da ba na da buƙatar yin nisa da ƙasata, haka ban son barin mahaifata, amma yanzu tafiya ta kamani dole, akwai buƙatar na yi nisa da ƙasar gaba ki ɗaya ko zan manta da Mimie da abinda ya shafe ta duk da na san abu ne mai matuƙar wahala na iya manta ta, amma ba zan iya zama a ƙasar nan a ɗaura aurenta da wani ba alhali ina raye, don Allah Daddy ka da ka hanani." Ya na zancen idonsa na ciccikowa da ƙwalla kamar zai yi kuka.
Shi kaɗai ya san raɗaɗin da zuciyarsa ke masa.
Cike da tausayi da kulawa Daddy ya dubi ɗan nasa ya ce "Shikenan ka je ka fara shirin tafiyar Allah ya tsare ya kiyaye mun kai."
Godiya ya shiga yi, yayin da Mamy ta ce na san yanda ka ke ji, tabbas ba daɗi amma ka jure ka cire abun a ranka ka rungumi azkar insha'allah komai zai zo ya wuce kamar ba'a yi ba."
Miƙewa ya yi zai koma ɗaki Sagir ya ce "Yanzu yaya tafiya za ka yi ka bar ni?"
Murmushi kawai ya masa ya juya Daddy ne ya kira sunansa, na manta ban tambaye ka ba wace ƙasar za ka?"
"Ban riga na yanke shawara ba Daddy, idan na gama zan sanar maku." Ya faɗa murya na rawa, ya na gama faɗa kuma ya bar falon.
Ga ba ki ɗaya jikin mutanen gidan ya yi sanyi da wannan al'amari, sun tausaya masa matuƙa.
®®®®®®®®®®®
Amarya Mimie kuwa sai shirye-shirye ake ba kama hannun yaro, su yaya Farida da su Mama talatu ƙannen Baba su ka maye gurbin Mama a bikin domin su ke gudanar da komai da Ya kamata ta yi.
Ana saura sati ɗaya su Mamy su ka ɗira a Kano, su kam Mama ta tarbe su iya tarba da sakin fuska domin a cewar ta su kaɗai ne baƙinta a bikin, amma kowa ya zo zuwan kansa ya yi.
®®®®®®®®®®®
Sameer kuwa a ranar da su ka dira Kano a ranar jirgin su ya cira zuwa Dubai, ko makarantar da za shi bai sani ba, kawai ya tafi ne don ya bar kasar, ya tafi da zimmar idan ya na zaune a can sai ya nemi makarantar da ta dace da zarar anfara ɗaukar sabbin ɗalibai.
Ya bar gida cike da ƙunci, haka sallamarsa da iyayensa ta kasance cike da alhinin rabuwa da ahalinsa.
®®®®®®®®®®®
A ranar da su ka sauka Mimie anan ta kwana tare da Mamy sun sha hira sosai, anan ta ke tambayar Mamy, "Nikam Mamy ina yaya Sameer ne? Shi kaɗai ne ban gani ba acikin yayyena."
Mama da ke gefe ta na jin su sai harara ta ke watsawa Mimie, aranta ta ke mamakin irin wannan rashin kunya ta Mimie, ki ƙi mutum kuma ki dawo ki na tambayarsa? Ita ko kunyar Mamy bata ji da ta ƙi ɗan ta?
Murmushi Mamy ta yi ta ce "Uhmm! Ai yaya Sameer ya tafi Dubai gun ƙaro karatu, da a tare zamu taho amma sai tafiyar ta faɗo dai-dai da lokacin, shima yau ya tafi."
Ƙirjinta ne ya buga da ƙarfi dam! A zuciyarta ta ce "Na shiga uku, ka da dai ya tafi ne saboda zan yi aure."
A fili kuwa murmushin ta yi itama ta ce "Ayyah! Shiyasa ashe ban gan shi ba, shi ko yaya Sameer haka ake tafiya ba sanarwa?"
Dariya Mamy ta yi bata ce komai ba, a haka su ka kwana su na hirarsu gwanin burgewa.
Mama ta so ta kore Mimie daga ɗakin domin haushin da ta ke bata, amma Mamy ta ƙi ta ce ita sai a bar mata y'arta su kwana tare za su yi hirar yaushe gamo.
®®®®®®®®®®®®
Gidan Malam Habu ya cika da jama'a y'an biki duk da ba su yi wata gayya ba, amma hakan bai hana y'an uwa da abokan arziƙi cika gidan ba.
Su Mamy tuni an zama yan gida sai hidima ake.
Yaya Saheen, Salim da samar kuwa a gidan yaya Kabir su ke kwana can ne masaukinsu, domin Anty Zee a gidan Mama ta tare saboda hidima.....
Ga mai buƙata sai ya tuntuɓeni ta wannan number 08109634202
Follow me on wattpad @ummu inteesar
UMMU INTEESAR CE❤️❤️❤️❤️
👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻
*A SANADIN KAMA*
👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻
*DAGA ALƘAMIN RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU-INTEESAR)*
MARUBUCIYAR SOYAYYAR MEERAH
Y'AR GANTALI
RIKICIN MASOYA
DA KUMA
A SANADIN KAMA
WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE AKAN NAIRA 200 KACAL
GA MAI BUƘATA SAI YA TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER 08109634202
DON ALLAH IDAN KA SIYA KADA KA FITARMIN HAƘƘIN MALAKA NAWA NE
Arewa writers association
Page 4️⃣5️⃣↪️4️⃣6️⃣
A haka shagalin bikin ya cigaba da gudana, anyi shagali iya shagali kama daga kan party, kamu da Dinner ba abunda ba'a yi ba ko wanne biki ya ƙayatar domin an yi bukukuwan irin na ƴaƴan manya da ya ke Mamy da Daddy na garin duk wani abu da za'a nema don cigaban shagalin bikin a aljihunsu ya ke fita.
Tun ana saura kwana Uku ɗaurin aure iyayen amarya da wa su daga cikin danginta su ka je birnin Kebbi domin gyaran ɗakin Amarya da ya ke a can garin su Bassam ɗin za'a kai ta can ya yi gidansa, da ya so ya zauna da ita a Kano ko da a gidan haya ne saboda nan ya ke aiki, amma fafur mahaifiyarsa ta ƙi ta ce dole sai a garin zai zauna kusa da ita, bisa ga dole ya bi umurninta.
®®®®®®®®®®
Su mama Habeey (ƙanwar baba) da Mama sadiya (ɗaya ƙanwar Mama da ke garin kaduna ta na aure) su ne su ka je birnin Kebbi domin gyaran ɗakin Amarya kuma ba za su dawo ba har sai an kai Amarya.
Har zuwa lokacin Mommy ba ta zo bikin ba kuma bata turo ɗanta ko ɗaya ba, Ruma ta so zuwa kamar me amma Mommy ta hana, bisa ga dole ta haƙura ta kira Mimie a ɓoye ta mata Allah ya sanya alkhairi.
Sai dai Mommy ta turowa mama kuɗi Naira dubu talatin ta account ɗin yaya Kabir, wai ba zata samu damar zuwa ba a cewar ta.
Kuɗin ma ta turo ne don ka da a zarge ta da rashin zumunci kuma don kada duniya ta zage ta ace auren yar yayata guda ba ta ce ba, kuma ba ta yi aike ba shiyasa, amma hassada ce fal a ranta.
Da ma ta ji daɗin rashin auren Sameer da Mimie ta yi.
®®®®®®®®®®
A bangaren abokan ango na jihar Kebbi ma tun ranar Alhamis su ka diro garin Kano da su aka yi dinner.
Ranar Assabar da misalin ƙarfe takwas da rabi na safe dubbunan mutane su ka shaida ɗaurin Auren Bassam Aliyu da Amaryarsa Zuhuriyya Sadeeq Yusuf akan sadaki Naira dubu hamsin.
Murna a gurin Bassam ba'a cewa komai domin sai da ya yi sujudus-shukur a gurin ya godewa Allah da ya nuna masa wannan rana.
Da misalin ƙarfe goma sha ɗaya na rana aka kawo motocin ɗaukar amarya daga gidansu Bassam na nan Kano.
Nan fa aka zo fitar da Amarya, Mimie ta sha kuka kamar ranta zai fita, Mamy ce ta janyo ta, ta kaita har uwar ɗakan Mama, a gaban Mamar ta durƙusar da Mimie ta ce "To Hajiya ga y'ata nan na kawo ta ki mata huɗuba zan sadata da ɗakin mijinta."
Mimie kuwa banda kuka ba abinda ta ke sai yanzu ne ta ke jin kamar ta fasa auren nan saboda ba ta son yin nisa da iyayenta ga shi ba'a son ransu aka yi auren ba ta na tsoron me zai biyo baya.
Mama da ta ke zaune kan gado daga ganin ta ka san ta na cikin alhinin rabuwa da y'ar tata, ta ja numfashi ta sauke sannan ta ce "Hmmm! To Hajiya ni me zance? Duk abinda zan faɗa an riga da an faɗa mata sai dai na tunatar da ita abu ɗaya." Mayar da dubanta ta yi ga Mimie ta ce "Zuhra ki riƙe Allah a ranki, ki sanya tsoron Allah a cikin dukkanin lamuranki, rayuwar aure ibada ce ba wasa ba, ki yi haƙuri ki yi biyayya ga mijinki, duk da cewa ba'a son ranmu ki ka yi wannan auren ba amma hakan ba zai hana mu yi miki fatan alkhairi ba, Allah ya ba ku zaman lafiya mai ɗorewa."
Ta na kai nan ta kuma jan dogon numfashi ta sauke yayin da Mimie ta cigaba da rusa kuka kamar ranta zai fita.
Cikin ƙarfin hali Mama ta dubi Mamy ta ce "Hajiya za ku iya tafiya ka da ku makara, Allah ya tsare ya kaɗe fitina."
Mamy ta ce "Ameen mungode da addu'a."
Miƙewa ta yi ta ja hannun Abar sonta su ka bar ɗakin, falon Baba ta kaita acan su ka tarar da Daddy da kansa ya raka ta har gaban Baba don neman gafara da yin sallama.
Ko kallonta Baba bai yi ba, acan ƙasan ransa damuwa ce fal ta rabuwa da y'arsa duk da ya na jin haushin yanda ta bijirewa Umurninsa.
Daddy ne ya katse mai tunani da cewa "Ga y'ata na kawo ka mata huɗuba, yanzu za ta tafi ɗakinta."
Kawar da kai Baban ya yi ya ce "Kai ne Abbanta ai, kuma kai ka aurar da ita ga wanda ka ke so, don haka duk abinda zan faɗa na san ka riga ka gaya mata don haka ta tafi kawai Allah ya tsare."
Jikin Daddy ya yi laƙwas da jin zancen Baba, kawai sai ya yi shiru ya ma rasa me zai ce ma, sai yanzu ne ya tabbatar ran Baba ya kai ƙololuwar ɓaci da auren.
Juyawa ya yi ga Mimie da ke ta ruzgar kuka har jiyojin kanta sun yi ruɗu-ruɗu ya riƙo hannunta ya ƙara matsowa da ita daf da Baban sannan ya ce "Daddy's girl ki durƙusa ki bawa Babanki haƙuri, Babanki ya na fushi da ke sosai."
Durƙusa ta yi ta kama ƙafafun Baba cikin kuka mai tsanani, murya na rawa ta ce "Babana don girman Allah ka gafarce ni ka yafe mun, sai yau na tabbatar da na tafka babban kuskure a rayuwata na bijirewa umurnin ka da na yi, amma aikin gama ya riga ya gama, da na sani ƙeya ce kuma tuni na barta a baya, don girman Allah ka yafe mun, muddin na tafi ka na fushi da ni tabbas ba zan ga dai-dai a rayuwar aurena ba."
Ta na kai nan a zancenta ta kuma rushewa da wani marayan kuka, duk sai ta bawa Baban tausayi, sosai tausayinta ya ɗarsu a ransa don haka ya buɗi baki kamar wanda a ka yiwa dole ya ce "Na yafe miki tashi ki je, Allah ya miki albarka."
Kasa miƙewa ta yi har lokacin ta na riƙe da ƙafafun Baba sai da Daddy ya zo ya janye ta yayin da ya ke ƙoƙarin shanye ƙwallar da ta taru a idonsa don tausayin da su ka ba shi su duka.
Falon ya tarar da Mamy ya hannunta mata y'arta, dama tuni sun yi mata ta su huɗubar don haka Mamy da sauran iyayen Amarya su ka nufi motocin da za'a kai Amaryar dama tuni aka shirya amarya cikin shiga ta alfarma, shadda Maroon ce a jikinta sai alkyabba fara da aka ɗora mata akai, a haka su ka fito waje da ita hannunta na riƙe acikin na Mamy sai shasshekar kuka ta ke.
Anan parking space su ka tarar da su yaya Saheen Mamy ta ja ta har gabansu don su yi Sallama anan su ka ƙara sanyayar mata da gwuiwa, ba ma kamar zancen Samar da ke cewa "Allah sarki my sister, shikenan yanzu kin yi nisa damu koh? Shikenan yanzu rayuwar yaya Sameer ta tabbata a cikin duhu da ɗemuwa ta rashin ki a matsayin mata koh? Allah sarki yaya Sameer Allah ya ba ka ikon jure wannan ƙaddarar." Hawaye ne su ka sauko a kuncinsa, yayinda ita ma Mimie ta kuma fashewa da kuka, da har an samu ta tsagaita sai ga shi ya famo mata ciwon.
Mamy ce ta dakatar da shi ta hanyar ɗaga masa hannu ta ce "Ya isa haka Samar, ba na kawo y'ata don ku saka ta kuka ba ne sai don ku yi sallama, amma me ye haka ka yi kenan? Dawo da abinda ya wuce ba shi da amfani."
Daga haka ta ja hannun Mimie zuwa cikin motar da aka tanada don Amarya.
Dama tuni ƙawayen Amarya da y'an uwa da abokan arziƙi y'an rakiyar Amarya sun gama shiga Mota ita kaɗai ake jira, don haka ta na shiga direbobin su ka ja aka fara fita daga gidan domin zuwa Birnin Kebbi..
Ga mai buƙata sai ya tuntuɓeni
08109634202
Follow me on wattpad @ummu inteesar
👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻
*A SANADIN KAMA*
👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻
*DAGA ALƘAMIN RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU-INTEESAR)*
MARUBUCIYAR SOYAYYAR MEERAH
Y'AR GANTALI
RIKICIN MASOYA
DA KUMA
A SANADIN KAMA
WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE AKAN NAIRA 200 KACAL
GA MAI BUƘATA SAI YA TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER 08109634202
DON ALLAH IDAN KA SIYA KADA KA FITARMIN HAƘƘIN MALAKA NAWA NE
*AREWA WRITERS ASSOCIATION*
Page 4️⃣7️⃣↪️4️⃣8️⃣
Ba su suka isa birnin Kebbi ba sai wajajen ƙarfe takwas na dare, a hakan ma wai don motocinsu lafiyayyi ne,kuma ba abinda ke tsayar da su sai sallah.
Da isar su garin ko gidan Amarya ba'a tsaya ba, motar amarya da ɗaya daga cikin motoci uku na y'an rakiyar Amarya suka ɗauki hanyar Kalgo local government don zuwa gidan iyayen Bassam, acan za'a fara kai amarya gaisuwar iyayen miji kafin a miƙa ta ɗakinta, yayin da sauran motocin biyu su ka wuce gidan Amarya inda su Mama Habeey ke can su na dakon ƙarasowar su.
Dama tuni an kammala gyaran gidan na Amarya ita kaɗai ake jira komai ya yi zam-zam don kuwa Daddy ya narƙar da dukiyarsa gun gyara ɗakin y'ar lelensa Mimie.
®®®®®®®®®®
A ƙofar gidan su Ango motocin su ka yi parking inda Mamy ta fito daga motar Amarya ita da Raliya da gwaggwo talatu (ƙanwar baba,yar yayan mahaifinsa).
Mamy ce ta riƙo hannun Amarya, su Raliya na take ma su baya har zuwa cikin gidan, sauran matan ma su ka fito su ka bi su a baya.
A ɗan madai-daicin ɗakin Innarmu (mahaifiyar Bassam) su ka yi masauki, tarad da ita su ka yi tare da y'an uwanta da su ka zo taya ta murna.
Ba laifi sun samu tarba domin ko ba komai an masu shimfiɗar fuska wacce y'an iya magana ke cewa tafi shimfiɗar tabarma.
Bayan gaishe-gaishe iyayen Amarya su ka damƙa amanar y'arsu hannun iyayen ango, bayan wani lokaci aka kawo masu abinci da abin sha su ka ci su ka ƙoshi, su ma direbobin su Shamsiyya su ka kai masu na su abincin a ɗakin da aka masu masauki.
Ko kafin a ankara dare ya riga ya yi domin har 10pm ta yi, don haka Innarmu ta ce dole su kwana anan domin ba za su koma birni cikin daren nan ba, ko ba komai Amarya ta gaji Saboda zaman mota ga kuma tafiya mai tsayi da su ka yi, dole su na buƙatar hutu, su bari da safe sai akaita ɗakinta.
Haka kuwa aka yi anan su ka kwana, Amarya da ƙawarta Raliya tare da su Shamsiyya ƙannen ango su ka kwana a ɗaki ɗaya, sai nan-nan ake da ita.
®®®®®®®®©©®
Ango kuwa tun lokacin da aka tashi walimar tayashi murna da abokanansa su ka haɗa masa, ya addabi mutane da maganar tafiya Bk, har wasu daga cikin abokanansa su na yi masa tsiya wai ya cika azarɓaɓi ko da ya ke badamuwa shi sabon shiga ne a harkar.
Shi dai dariya kawai ya yi ya ce "na ji ai bakomai kowa da haka ya fara, azo a tafi don Allah Amarya na jirana."
Dukkansu su ka saka dariya da haka su ka ɗebi motoci shida abokanansa na can dama wasu daga cikin abokan aikinsa su ka masa rakiya zuwa gidansa.
Sun ma riga Amaryar yin gaba don haka tun su na hanya ya ke damun abokanansa direbobin motocin y'an Amarya da kira, "kun ta so? Ku na ina ne yanzu? A tuƙan Amaryata a hankali." Shine kaɗai abinda ya ke famar nanata masu, har su ka gaji su ka daina ɗaukar kiransa.
Don haka angon ma ya riga Amaryar isa gari, shima gidansu ya fara zuwa ya sadu da y'an uwansa su ka taya shi murna, daga bisani ya wuce gidansa don jiran Amarya.
Ganin har goma ta gota ba su ƙaraso ba ya sa ya shiga damuwa, ya fara neman layinta, ya kira ya fi a ƙirga bata ɗaga ba sai kawai ya kira number Antynsa Lami ita ta ke sanar mai Innarmu ta ce anan za su kwana, sosai ya ji haushi amma ba yanda ya iya haka ya haƙura, ya san dai komai ta daɗe sai an kawo masa ita.
®®®®®®®®®®®
A bangaren Sameer kuwa ya na sauka masaukinsa a ƙasar Dubai kawai sai ya saka layin ƙasar ya shiga neman layin Daddy, anan ya sanar masa ya sauka lafiya, shima Daddy ya sanar masa suna gidansu Mimie.
Tun daga ranar ko da yaushe su kan yi waya da shi su duka, don ma su na cikin taro ne ba sa samun sakewa sosai.
A ranar da aka ɗaura auren Mimie bayan komawar su masauki, Samar ya kira yaya Sameer a waya su ka gaisa kamar kullum,bayan sun gaisa Sameer ke cewa "Ku na nan lafiya dai koh? Kun koma gida ne ko har yanzu ba ku gama shan bikin sisternku ba?"
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 8 Chapter of 15