Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
tana jijjiga shi ta na faɗar "Uncle! Uncle ka tashi, wallahi na yafe maka ka tashi Uncle, ka tashi mu shimfiɗa sabuwar rayuwa mai cike da farin ciki tare da ƴaƴanmu. A ɗimauce take zancen, ganin baya motsi kuma idonsa ya kakkafe yasa ta juyo ga Innarmu wacce take ta faman salati ta na kuka ta ce "Inna ki ce ya tashi wallahi na yafe, ki faɗa masa." Sosai innar ta ji tausayin Mimien na ratsa ta, kawai sai ta zo ta rungume ta suka ci gaba da kukan. Shamsiyyan ce ta yi ƙarfin halin zuwa ta kira likita itama ta na kuka sosai. Ya na shigowa ɗakin ya ga abunda ke faruwa, kawai sai ya shafe masa fuska tare da jan mayafi ya rufe masa fuska. Ai kuwa Mimie na ganin haka ta tabbatar ya mutu, kawai sai ta kuma saka ihu tare da sumewa a kan kujerar da take.... Ga mai buƙata sai ya tuntuɓeni ta wannan number 08109634202 Follow me on Wattpad @ ummu inteesar UMMU INTEESAR CE❤️❤️❤️ 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *A SANADIN KAMA* 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *DAGA ALƘALAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)* *MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH* *Y'AR GANTALI* *RIKICIN MASOYA* DA KUMA *A SANADIN KAMA* WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE AKAN NAIRA 200 KACAL GA MAI BUƘATA SAI YA TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER 08109634202 DON ALLAH IDAN KA SIYA KADA KA FITARMIN HAƘƘIN MALAKA NAWA NE *AREWA WRITERS ASSOCIATION* ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com *BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM* Page 6️⃣5️⃣↪️6️⃣6️⃣ Iya tashin hankali Innarmu ta gani a ranar. A haka suka tura keken tare da mayar da Mimie ɗakin da take jinyar a ciki, likitanta suka kira don ya duba ta. Ko kafin ta farfaɗo har an wuce da gawarsa can gida don masa sutura. Dogon suma ne ta yi, don haka bata farfaɗo ba sai wajajen tara na dare. Bayan ta dawo hayyacinta ta cigaba da kukanta cikin dasasshiyar murya, rayuwar soyayyarsu ta baya da farkon aurensu kawai take tunawa, duk ta fita a hayyacinta. Innarmu dake zaune gefe kusa da ita rungume da hassan, ita ce ta dubi Shamsiyya ta ce "Ɗauki wayatta ki kira min innatta, ya kamata su san halin da a ke ciki." Ba tare da budurwar ta amsa ba ta miƙa hannu ta ɗauko wayar tare da miƙawa Sakina, da ido ta mata nuni da ta kira. Da yake Sakinan ita ce mai ɗan dama-dama, sai kuwa ta shiga jerin numbobin ta na dubawa. Can ta gano number da a ka rubutawa *Mamata* ai kuwa ta danna mata kira. Bugu biyu a na uku a ka ɗaga kiran, sallama ta yi, bayan ta gaishe da maman. Cike da mamaki Maman ta tambaya "Wacece? Ina Mimien?" A ɗan tsorace take zancen. Cikin matuƙar ƙarfin hali Sakina ta ɗan yi busasshen murmushi ta ce "Mama! Sakina ta ƙaunar Bassam, dama na kira na in sanar miki Anty Mimie ta haihu ɗazu da rana, amma c.s anka mata." Sosai mama ta yi murnar jin wannan labarin duk da ba komai take ganewa ba, saboda Hausar Sakinan ba ta kanawa ba ce. Cikin rawar baki Mama ta ce "Kai masha'allah, me a ka samu?" "Y'an biyu maza." Ta ba ta amsa. Nan fa murnan Maman ta daɗu, amma da ta fahimci kamar akwai yanayin damuwa a tattare da Muryar Sakinan, sai ta ce "Masha'allah! Allah ya raya, amma ina Mimien ban ji ta ba, ko da wata matsala ne, na ji muryanki wani iri." Guri ta nema ta zauna ta na matsar ƙwalla ta ce "Ita dai da dama, ga mu nan asibiti domin ta jiggata Sosai, amma kuma yayan ne...." Sai kuma muryarta ta fara rawa. Cikin tashin hankali Mama ta ce me ya sami yayan naku Sakina?" Cikin kuka ta ce "Bayan haihuwarta, ko awa ɗaya ba a yi ba, yaya ya rassu." Duk da cewa ba a son ranta a ka yi auren ba, amma ta girgiza sosai da wannan mutuwar. Cikin tashin hankali ta ce "Innalillahi wa inna'ilahir raji'un! Allah ya jikansa da rahama, yanzu ina Mimien? Don Allah idan ta na kusa ki ba ta wayar." Tashi ta yi ta je bakin gadon Mimie dake kwance cikin wani yanayi ta na sauraron wayar ta su, ta miƙa mata wayar. Karɓa ta yi amma bata iya cewa komai ba, ta na jin maganar Maman tata kawai sai ta fashe da matsanancin kuka. Lallashin duniyar nan Mama ta yi, amma kamar zuga ta take, duk yanda ta kai da son su yi magana Mimie bata ce uffan ba, sai kuka a kan dole ta kashe kiran, cikin wani irin yanayi na rashin jindaɗi. ®©©©©©©©© Kano Ƙarfe goma na dare Baba ya shigo gidan nasa, ya samu matarsa cikin wani yanayi na jimami. Tambayarta ya yi "Lafiya dai Maman Zuhra? Me ke damun ki?" Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ce "Mimie ta sauka ɗazu, an samu y'an biyu maza." Da fara'a a fuskarsa ya ce "A'ah to ai wannan abin farinciki ne, miye abun tada hankali a nan?" Cikin raunanniyar murya ta ce "Allah ya yiwa mijinta rasuwa bayan wasu mintuna da haihuwarta." Sosai ya ji wani shock ya ja shi, amma gudun kada ya karyar mata da zuciya sai ya ce "Allahu akbar! Allah ya jikansa da rahama." Ameen ta faɗa. Ya ce "Addu'a za ki yi masa Maman Zuhra, yanzu addu'ar mu kawai yake buƙata, amma damuwa ko kuka duk ba su da amfani." Da haka ya samu ya ciwo kanta, a nan suka zauna hira, cikin hirar ne suka yanke lokacin tafiya birnin Kebbi. Washe gari Mama ta kira Mamy ta sanar da ita abinda ke faruwa da kuma ranar da za ta tafi, a nan Mamy ta ce ta bari su tafi tare ranar talata a maimakon ranar Litinin da ta saka. Bayan ta gama waya da Mamyn ne ta kira Mimie, wannan karon Mimien ce da kanta ta ɗaga suka gaisa, don yanzu an samu ta daina kukan sai dai kukan zuci da ba ta tunanin za ta iya daina shi har ko yaushe. Sosai Mama ta mata nasiha, tare da janyo hankalinta a kan ta yi haƙuri da rayuwa a duk yanda ta zo mata. Bayan ta gama ne ta nemi da a haɗa ta da Innarmu a waya ta mata Gaisuwa tare da Barka. Mimie ta yunƙura ta zauna tare da miƙawa innar waya ta ce "Innarmu ga Mamana za ta miki gaisuwa." Jiki a sanyaye innar ta karɓa, don yanzu wata irin kunyar yarinyar da iyayenta take ji, saboda sanin abinda ta aikatawa yarinyar a baya. Gaisawa suka yi sannan ta mata gaisuwar mutuwar da kuma barkar haihuwar sannan ta kashe wayar. ©©©©©©© Haka kuwa a ka yi ranar talata tun safe Mamy ta taso zuwa garin Kano, da misalin ƙarfe sha biyu ta iso, abinci kawai ta ci suka ɗau hanyar zuwa Bk. Sai dare suka isa, kai tsaye asibitin da a ka kwatanta masu su ka nufa. A can suka tarad da yaran cikin ƙoshin lafiya sai abinda ba a rasa ba, domin innarmu da ƴaƴanta su na iya ƙoƙarinsu gurin kula da Mimie da yaran. Mimie ta ji daɗin zuwan Mamanta da kuma Mamynta sosai, hakan ya ɗauke mata wani ɓangare na damuwar da take ciki. Kwanansu biyar a asibitin a ka sallame su, ganin jikin nata ya yi kyau, Innarmu da kanta ta bawa su sakina maƙullan gidan Bassam na birni suka buɗe shi tare da gyarawa, a ka kai Mimie can don yin wankan jegonta cikin kwanciyar hankali da nutsuwa. ©©©©©©© Ranar juma'a su Baba, Alhaji Salman da Saheen suka zo don suna da kuma yin gaisuwa. Kalgo suka fara zuwa suka yiwa Innarmu da y'an uwanta gaisuwa sannan suka dawo gidan Mimie. yau ta kasance ranar Asabar a yau ne kuma za a yi sunan y'an biyu, tun da sassafe Innarmu ta je bayan gida inda turken dabbobinta ya ke, ta saka a ka kamo manyan raguna biyu tare da madai-daicin santa wanda ta ƙwallafa ranta a kansa, ta bayar a ka yankawa jariran tare da masu suna. Yara sun ci sunan Aliyu da Bassam wanda Mimie da kanta ta zaɓawa yaran suna. Hassan shine Aliyu wato takwaran baban Bassam, sai kuma Hussain wanda ya ci sunan mahaifinsa, amma ana masu inkiya da *Affan* da *Afeef* Duk da ba wani shagali a ka yi ba, saboda mutuwar mahaifin yaran, amma hakan bai hanawa mutane yin tururuwa zuwa ganin yaran ba. Washe garin ranar su Baba suka koma tare da Mama saboda ayyukansu, amma a nan suka bar Mamy tare da Sagir ƙarami domin ita sai Mimie ta yi arba'in za ta taho tare da ita gaba ɗaya. Bayan Mama ta koma Kano ne ta tura ƙanwarta Halima( da yake ita bazawara ce y'ar ƙanin babansu Maman ce da take zaune gidansu dake nan Kano)zuwa Bk don ta taya Mamy zama. Bangaren Innarmu kuwa yanzu ta na masifar son Mimie, ji take ina ma yanzu ne Bassam ya ke raye tare da matarsa? Da sun ga gata, amma inah! Mutuwa bata barin wani don wani. Kullu nafsin za'iqatul maut (dukkan rai sai ta ɗanɗani mutuwa) Don haka ta sakawa ranta dangana, yanzu sosai take kula da Mimie duk da y'ar tazarar dake tsakanin su, amma duk bayan kwana biyu take zuwa birni don duba lafiyarsu. Sannan ta ajiye ƙanwarta (Rashida) da Shamsiyya a can domin su riƙa taimakawa su Mamy. Sosai Mimie take mamakin sauyawar Innarmu, duk da cewa ba abun mamaki ba ne, saboda yanzu ta fahimci wancan lokacin asiri Zinnira ta masu, yanzu kuma ya warware. Wata rana da Innarmu ta je gidan, da kukanta take roƙon Mimie a kan ta gafarta mata abinda ta mata, hakama su Shamsiyya sun nemi yafiyarta, kuma duk ta yafe masu, yanzu komai ya dai-daita ba sauran tashin hankali. Bayan sati Uku, komai ya lafa an nutsu, Mamy ta je da kanta ta sami Inna da maganar gadon yaran, su na so a raba a bawa yaran na su, ba don komai ba sai don haka Shari'a ta tanada, domin so suke su tafi da Mimie gida ta ƙarasa takabarta a can. Ta yi hakan ne domin karɓarwa yaran haƙƙinsu, amma kwata-kwata su ba kuɗin ne a gabansu ba domin indan kuɗi ne kam ba za su nemi hakan ba don su na da shi har ba su san yawansa ba. Ba musu Innarmu ta karɓa mata tare da cewa "insha'allahu Hajjiya za a yi yadda yak-kamata, gobe-gobenga zan biɗo malammai, don su zo a san yadda za a yin rabon. Amma don Allah kak-ku raba mu da Mimie ku batta nan don Allah." Girgiza kai Mamy ta yi ta ce "A'a innar Sakina ba za a yi haka ba, dole ne mu tafi da ita, domin ta na gama takaba aure za ta yi." A firgice innar ta ɗago kamar za ta ce wani abu game da hakan, kuma sai ta fasa. Jiki a sanyaye ta ce "To don Allah Hajjiya ku bam-muna yaran, ke ga yanzu su ɗai su ka rage min jinin Bassam tunda shi ya mutu." Ta ƙarashe zancen kamar za ta yi kuka. Mamy ta ce "Hmmm! Mu bar muku su ku kashe su, yanda ku ka so kashe uwarsu da baƙin ciki koh?" Ware ido Inna ta yi da sauri, haƙiƙa bata ji daɗin zancen nan na Mamy ba, amma ta sani wata rana dole sai haka ta faru tun da su su ka ja. Cikin rawar baki ta ce "Hajjiya ku yi hanƙuri don Allah, abat tuna baya, ya riga ya wuce kuma insha'allahu za mu riƙe su da amana, ki tuna su ɗin jinina na, tayaya zan bari a walaƙanta su?...." Ga mai buƙata sai ya tuntuɓeni ta wannan number 08109634202 Follow me on Wattpad @ummu inteesar. UMMU INTEESAR CE😍😍❤️🌹🌹🌹 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *A SANADIN KAMA* 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *DAGA ALƘALAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)* *MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH* *Y'AR GANTALI* *RIKICIN MASOYA* DA KUMA *A SANADIN KAMA* WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE AKAN NAIRA 200 KACAL GA MAI BUƘATA SAI YA TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER 08109634202 DON ALLAH IDAN KA SIYA KADA KA FITARMIN HAƘƘIN MALAKA NAWA NE *AREWA WRITERS ASSOCIATION* ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com *BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM* Page 6️⃣7️⃣↪️6️⃣8️⃣ Bayan sun gama tattaunawar ne Mamy ta koma gidan Mimie. Innarmu ta shiga damuwa amma ba yanda ta iya dole ta haƙura da koma me za a musu, domin tsuntsun da ya ja ruwa dama shi ruwan kan doka. Har zuwa lokacin Zinnira da innarta ba su zo yiwa Innarmu gaisuwar mutuwar Bassam ba, hakan ba ƙaramin ƙona mata rai ya yi ba, damar abin dai yayan nata shi ya zo ya mata Gaisuwa kai tsaye ya juya abinsa. ©©©%%%%%©®®® Bayan wani ɗan lokaci malamai suka zo aka raba gadon Bassam, domin tuni Alhaji Sale ya siyar da komai da yake mallakin Bassam a kano, da kansa ya zo ya kawo kuɗin, lokacin da ya zo gaisuwar Bassam ɗin. Da yake ba wanda ya san zancen dukiyar Bassam da su Zinnira suka kwasa lokacin da take gidan, domin bai sanar da kowa ba, shi kansa bai san da wani abun ba, hakan ya sa ba wanda ya waiwaye su da zancen dukiyar Bassam, domin da ma ita Zinnirar ba ta da gado tun da ba ta da ko ƙwai a gidan, kuma bata masa takaba ba. An raba masu gadon kamar yanda Shari'a ta tanada, an bawa Innarmu kashi ɗaya bisa shida na dukiyar, yayinda a ka bawa Mimie kashi ɗaya bisa takwas na dukiyar, sauran kuma aka barwa tagwayen kasancewarsu maza. Bayan kammala rabon gadon ne a ka damƙawa mahaifiyar yaran nasu, aciki kuwa har da wannan gidan da suke zaune a ciki, don haka a ka siyar tare da bata kuɗin. Account a ka buɗewa yaran na musamman a ka zuba masu dukiyar gadonsu a ciki. A ranar da Mimie ta cika kwana hamsin da haihuwa a ranar Mamy ta ɗauke ta suka je yiwa Innarmu bankwana domin a washe garin ranar za su wuce Kano. Innarmu har da kukanta a kan ka da a raba su, amma inah! Haka ta haƙura dole, a nan ta ƙara roƙar gafara a gun Mimie su Sakina ma suka ƙara roƙar gafara sun sha kuka a ranar rabuwar su, Ba ma kamar Shamsiyya da tafi zaƙewa a lokacin da suke kan ganiyar rashin mutuncinsu. Mamy ta yiwa Innarmu alƙawarin za a dinga kawo mata y'an biyu lokaci zuwa lokaci don su ma su saba da dangin babansu. Haka rabuwar su ta kasance cike da alhini. Ranar wata Laraba suka wuce Kano, anan Mamy ta bar Mimie ta wuce Abuja. ©©©©©©© Tun washe garin Ranar da Mimie ta haihu, Abba ya kira Sameer ya sanar da shi ƙaruwar da aka samu, domin har zuwa lokacin Sameer baya Nigeria, wancan karon sun so su dawo da shi daga Dubai don ganin halin da ya shiga, amma sai ya dinga roƙar su a kan su yi haƙuri, ba zai iya komawa Nigeria ba, amma zai canza ƙasa domin ya nisanta da gurɓatattun abokai irinsu Rajbir, tun daga lokacin ya wuce Saudiyya ya na zaune a birnin Madina, dama ya gama karatun zaman dole ne kawai, tunda zaman Nigeria ya gagare shi. Ya yi murna sosai a zahiri, amma a baɗini ya ji ba daɗi ya so ace shi ta haifarwa waɗannan yaran har guda biyu, amma sai ga shi ƙaddara ta canza al'amarin. Anan ne kuma Daddy ke sanar masa cewa Mijin Mimien ya rasu. WOHOHO! Maimakon Sameer ya shiga jimami, sai wannan labarin ya zame masa tamkar Albishir, ji ya yi kamar an masa bushara da gidan aljanna, ya na ji cewa lokaci ya yi da farin cikinsa zai dawo tamkar da, ya na jin Allah ne ya dube shi da idon rahama shiyasa ya ɗauki rayuwar Bassam domin ya dawo masa ita a lokacin da ya gama fidda rai ga samun ta. Har sai da Daddy ya fahimci farincikin ɗan nasa a bayyane. Murmushi kawai ya yi ya kashe wayar, a ransa ya na yiwa ɗansa fatar samun nasara a karo na biyu, ya na masa fatar dawowar farincikinsa. %%©©©© Tun daga ranar Sameer ya fara shirye-shiryen dawowa Nigeria domin lokaci ya yi da zai dawo mahaifarsa. Cike da annashuwa yake shirinsa na dawowa, kallo ɗaya za ka masa ka san ya na cikin yanayi mai kyau. Nan fa Sameer ya haukace da siyayya komai ya gani mai kyau jibgowa Mimiensa da kuma twins ɗinsa yake, ku san duk rabin kayan tsarabar da ya siya nasu ne. ©©©©©©%%% A wata ranar Litinin da misalin ƙarfe uku na rana jirginsu ya sauka a filin jirgin Abuja. Cike da nutsuwa ya ke tako step ya na saukowa daga jirgin, ya yin da Saheen da Salim suke ɗan nesa da shi su na kallonsa cike da murnar sake saduwa da ɗan uwan nasu da suka yanke ƙauna da samun hayyacinsa. A haka ya ƙaraso gunsu suka rungume juna su duka suna murnar haɗuwa. A mota Sameer sai kalle-kalle ya ke, ya na ganin yanda garin nasu ya sauya, shekara biyar kawai da yayi ya dawo, ya ga sauye-sauye a birnin nasu. Haƙiƙa Abuja ta cika Babban birni mai kyau da tsari, ko ina gwanin burgewa. Haka yata kalle-kallensa har suka kusa isa gida, a nan ya kalli Saheen ya na tsokanarsa da cewa "Yaya Saheen baban Boy, ya boy ɗin namu da kuma Mamansa?." Y'ar dariya Saheen ɗin ya yi,bai ko amsa tambayar ba, ya ce "Kai yaya Sam! Yau kuma ni ne yayan naka?." Shima Sameer ɗin dariya ya yi ya ce "Eh, ai yanzu kai ne yayana tun da har Ka na da ɗa da mata ni kuma ba ni da, ka ga kenan yanzu ni ne ƙaninka." Ya ƙarasa zancen ya na ɗan murmushi da alama murmushin na jin ciwo ne. Dariya suka saka dukkansu, Salim dake zaune a bayan motar ya na sauraren dramar y'an uwansa sai murmushi yake saboda sun burge shi, sai a lokacin ya ce "Ai kar ka wani damu yaya Sam, kai ma kwanan nan za ka angwace, za mu sha shagalin aurenka da Mimienmu." Da sauri Sameer ya waigo bayan, ya na kallon Salim ya ce "Waya gayama haka?" "Ni na faɗa domin yanzu haka Mamy ta na can kuma kwanan nan za ta zo maka da ita, ina da tabbacin wannan karon ba za a samu matsala ba insha'allah." Murmushi kawai Sameer ya yi bai kuma cewa komai ba, ya juya ya cigaba da kallon gabansa, domin ya fahimci y'an uwan nasa su na so su saka masa rai ne da samun abinda zai yi wuyar samu a gare shi. Lokacin da ya ke saurayi mai ji da kyau da ƙuruciya ga Naira ma ba ta so shi ba, sai yanzu da duk ya yamutse kuma ya ƙara shekaru? A haka ya ci gaba da saƙe-saƙensa har suka ƙarasa gida. Rashin Mamy a gidan ya saka Sameer ya ji gidan ya yi wani iri, amma duk da haka ya ji daɗi sosai da ya dawo ya riski ɗan ɗan uwansa kuma takwaransa, wato Sameer ƙarami ɗan Ruma da Saheen." Kasancewar Sameer Ya na matuƙar son yara hakan yasa kullum Sam ƙarami ɗan 3months ya na cinyarsa ya na wasa da shi. Ko da Mamy ta dawo Abuja ta sami Sameer a gidan, sosai ta ji daɗin ganin yanda ya samu nutsuwa kuma da alama ya shiryu ya daina halayyarsa ta baya wato shan giya. ©©©©©©®®® Har zuwa lokacin Mommy bata bar Saheen ya huta ba, kullum ta na cikin ƙwaƙule masa aljihu, ga shi tun da ya auro Ruma ku san kullum ta na gidan, kasancewar Abbansu Ruma ba mazauni ba ne, kullum ya na hanyar wani gari ko wata ƙasa don kasuwancinsa. Duk wannan abun Saheen ba ya ganin aibun Mommyn kuma duk abinda take so shi a ke yi, da yake dai aikin asiri ne shiyasa. Sosai a bun ke damun Ruma yanda mahaifiyar tata ke takura masu, amma ba yanda ta iya dole ta yi haƙuri, domin dai duk yanda ta lalace ita ce dai mahaifiyarta kuma bata da madadinta a duniya. A haka ta cigaba da haƙuri da halayen mahaifiyar tata, kullum ta na roƙa mata shiriya a gurin Allah. ©©®®®©©©© Mimie ta zazzaga dangi na uwa da uba da kuma gidan yayyenta duk ta kai masu ziyara, ba wanda bai yi murnar ganinta ba, ga twins Allah ya zuba masu farin jini duk inda ta je kamar alashe su saboda ƙaunar da a ke nuna masu. Bayan wata ɗaya da zuwan Mimie Kano, hankalinta ya kwanta ta murmure jikinta ya yi kyau, haka ma Affan da Afeef sun yi kyau abinsu. A ranar da suka cika Wata uku a duniya, Mimie ta shirya ta je Abuja gidan Daddynta don kai masu ziyara. Murna a gun iyalan gidan ba a magana, Ba ma kamar Sameer da yake jin kamar ya haɗiye ta ita da jariranta saboda ƙauna. Ruma ma ta yi matuƙar farinciki da zuwa y'ar uwar tata a karo na farko bayan aurenta. Nan fa suka shiga murnar ganin junansu. Ita kuwa Mimie kunyar yaya Sameer take ji sosai, shiyasa muddin ta ji motsinsa a falo ba ta fitowa sai ya bar gun. Lura da hakan ya saka wata rana Yaya Sameer ya rutsa ta a ɗakinta dake gidan. Ta ɗan tsorata da ganinsa, su na haɗa ido ta sunkuyar da kanta ƙasa ta na wasa da hannun Afeef dake kwance kusa da ita a kan gadon. Matsowa ya yi ya na murmushi ya ce "Mimienmu sannu da zuwa." Shiru ta yi bata ce komai ba. Faɗaɗa murmushinsa ya yi ya ce "Da ma na zo ne na miki sannu da zuwa, tun da na ga alamar kunyar yayan naki kike ji." Ita dai ba baki sai kunne kuma har lokacin bata ɗago ba. Sunkuyowa ya yi ya ɗauki Affan dake kwance ya na wasarsa, ya ɗaga shi sama ya na murmushi ya ce "To ni bari na je, dama ina son ganin ƴaƴana ne, kuma kin ɓoye man su a ɗaki kin ga ko dole kenan na biyo sahu." Daga haka ya nufi ƙofar fita riƙe da yaron a hannunsa, ya na faɗar "Idan kin gama jin kunyar ki sanar da ni akwai maganar da na ke so muyi.." Ƙirjinta ne ya fara bugawa da ɗan ƙarfi, a ranta ta ce "Na shiga uku, me kuma zai faɗa yanzun?...." Follow me on Wattpad @ummu inteesar 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *A SANADIN KAMA* 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *DAGA ALƘALAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)* *MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH* *Y'AR GANTALI* *RIKICIN MASOYA* DA KUMA *A SANADIN KAMA* WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE AKAN NAIRA 200 KACAL GA MAI BUƘATA SAI YA TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER 08109634202 DON ALLAH IDAN KA SIYA KADA KA FITARMIN HAƘƘIN MALAKA NAWA NE *AREWA WRITERS ASSOCIATION* ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com *BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM* Page 6️⃣9️⃣↪️7️⃣0️⃣ Haka ta ci gaba da tuna abinda ta yiwa yaya Sameer a baya har tsawon wani lokaci kafin ta tashi daga gun. @@@@## Bayan sati biyu da zuwan ta Abuja, wata rana da misalin ƙarfe goma na safe Sameer ya sauko daga sama ya same ta a falo ita kaɗai sai waya riƙe a hannun ta na karatun wani novel mai suna cikin waye? na marubuciya Fatima sunusi Rabi'u (Ummu Affan) sai share hawaye take kasancewar jarumar littafin ta bata tausayi matuƙa. Matsowa ya yi daf da ita ya tsaya, ya yi kusan minti biyar tsaye a kanta ya na kallonta, amma bata ko san yana yi ba,saboda ta yi nisa a karatunta. Da ya ga alamar idan bai yi magana ba ba za ta san da tsayuwarsa agun ba, ya saka ya tafa hannayensa guda biyu. Firgigit ta yi ta kalle shi a ɗan razane domin bata ji isowarsa gun ba. "Kukan na mene sweet sis?" Ya tambaya. Share hawayenta ta yi ta ce "Ba komai Bro, jarumar littafin ce kawai ta ban tausayi." Guri ya nema ya zauna a lokacin da yake faɗar "Da ma sistern tawa ta na da tausayi, amma ta kasa tausayawa yayanta a lokacin da yake tsananin buƙatar hakan?" Sunkuyar da kai ta yi wani hawayen na gangarowa yayin da shi kuma yake kallonta ta ce "Ka yi haƙuri yaya a wancan karon soyayya ce ta rufe min ido na kasa hango girman kuskuren dake cikin abinda na aikata, haƙiƙa na maku butulci, amma insha'allah wannan karon a shirye nake da aikata duk abinda zai gyara kuskurena na baya." Wani sanyi ya ji a ransa, ya na ganin lokaci ya yi da zai shigar da buƙatar a karo na biyu. Wani lallausan murmushi ya yi ya ce "Ki share hawayenki sister ni na yafe miki, kuma a yanzun ma za ki iya gyara kuskurenki idan kin so." Da sauri ta ce "gaya min abinda zan yi don tabbatar da hakan." Ƙara murmusawa ya yi sannan ya ce "Za ki gyara shi ne ta hanyar karɓar soyayyata a karo na biyu, za ki gyara shi ne ta hanyar yarda da ni a matsayin mijinki na sunna.." Sai da gabanta ya faɗi da ta ji kalamansa, amma bata

Chapter 12 of 15