Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
lafiyar ta je gida kawai, amma haka ta kafe sai da ta kwana, sai dai ta yi waya ta shaidawa Mommy halin da ake ciki, ita kuwa Mommy ta kira Mamy da Mama ta shaida musu domin su taya su da addu'a. ©©©©©© Hankalinsu Daddy ya tashi fiye da tunani, a lokacin da labarin rashin lafiyarsa ya riske su daga nan suka duƙufa da addu'a ba dare ba rana. Daga ƙarshe Daddy kasa haƙura ya yi sai da ya shirya shi da Mamy suka je Dubai don duba lafiyar ɗan nasu. Alhmdulillah sun same shi jikin da sauƙi, amma hankalin Daddy bai kwanta ba don haka ya saka hannu kawai don a yi masa tieter, tunda wannan ita ce mafita ta ƙarshe da ake hangowa kafin abin ya yi nisa. Daddy da Mamy ba su baro Dubai ba sai da suka tabbatar an yiwa Sameer aiki ya ji sauƙi, da yake a can suna da kwararrun likitoci, an ɗora shi akan magani ya na sha, likitoci suka tabbatar masu da cewa insha'allahu cutar ta tafi kenan, muddin zai tsare magani don dama kaɗan ta fara kama hantarsa. A tare suka juya zuwa Nigeria da Mommy bayan ta share watanni a can. Bayan Sameer ya ji sauƙi rayuwar ta komo kamar da mai cike da annashuwa. Ruma ma ta kuma haihuwa ta biyu, ta samu ɗa namiji da ya ci sunan Salman ake masa inkiya da (Ashraf). ©©©©©©©©©©© Bayan Shekaru biyar Sameer ya zama ƙwararren likita a ɓangarensa, a wajen Mimie ma haka ne tuni ta gama masters ɗinta ta fara aiki a asibitin da mijinta ke aiki, kowannensu ya yi kyau abinsa, duniya ta zamar masu sabuwa kamar basu fuskanci wani ƙalubalai ba a baya. Mimie ta sake haihuwar ɗa namiji wanda ya ji sunan Abubukar Sadeeq suna yi masa inkiya da (Abba) kasancewar sunan babanta aka sakawa yaron. Affan da Afeef sun girma sun zama 'yan samari, yanzun su na cikin shekara ta tara kenan a rayuwarsu, su na primary4 amma wayon yaran ya wuce na shekarunsu, a lokacin ne kuma Little ta cika shekara biyar ta na nursery 2 yayin da Abba yake da wata tara a duniya. Sameer ya zama magidanci mai shekaru arba'in da ɗaya a rayuwarsa yayin da Mimie take da shekaru 31, kamar yanda gangar jikinsu da shekarunsu ke ƙaruwa haka kauna, soyayya da shakuwarsu take ƙaruwa. Ko waye kai idan ka ga iyalan Sameer dole su birge ka, don kuwa Sameer ba ya nuna bambanci tsakanin ƴaƴansa da na Bassam, duk da cewa ya na tsananin ƙaunar little a rayuwarsa sai ya ɓoye hakan a ƙasan ransa, domin a zahiri ya fi nuna ƙaunar 'yan biyu, hakan kuwa ba ƙaramin daɗi yake yiwa Mimie ba. Da yammacin wata ranar Lahadi dukkanninsu su na gida kasancewar ranar hutu ce. Alhaji Sameer ya na zaune a falo ya na karatun jarida, Mimie kuwa ta na kitchen ta na girkin rana, Affan ne ya shigo ɗakin da gudu yayin da Afeef ke binsa a baya, ƙarasowa yayi gaban Sameer ya zauna ya na faɗar "Dad don Allah ba ni ne Aliyu B. Aliyu ba, shi kuma Bassam B. Aliyu?" ya ƙarashe zancen yana nuna hausaininsa. Murmushi manya Sameer ya yi kana ya daga kai alamar tabbatarwa ya ce "Hakane." "Yawwa Daddy wai to me yasa a makaranta ake kiran little da Rukayya Sameer amma mu sai a ce mana B Aliyu?, Ga shi kuma kai sunanka Sameer ko Dad?" Afeef ya watso masa tambayar da ba zato ba tsammani. Jikinsa ne ya yi sanyi ƙalau, hakan ya saka ya miƙe tare da ajiye jarida ya shige ɗakinsa ya rufo ba tare da ya ba su amsa ba. Mimie dake kitchen ta na jin duk abinda suke faɗa, goge hawayen da ya zubo mata ta yi, ta na ganin lokaci ya yi da za su koma Nigeria domin sada su Affan da ahalinsu, saboda tun zuwansu ƙasar nan su Innarmu basu kuma ganinsu ba, har labarin mutuwar innarmun ya riske ta. Kashe gas ɗin ta yi ta sauke miyar, sannan ta nufi ɗakin mijinta mai tsananin tausayi da jinƙan marayun ƴaƴanta, ta masa magana akan tafiyarsu Nigeria. "Hakan shi ne dai-dai, ki bari sai mu ɗauki hutu daga gun aiki sannan mu saka rana." Ya na gama faɗa ya shige toilet don watsa ruwa. Mimie kuwa ta na nan a inda ya bar ta ta na tunanin rayuwa, ta na ƙara godiya ga Ubangiji buwayi gagara misali, wanda ya halicci bayinsa ya sanya wani sashensu yake kama da sashe, cikin hikimarsa da iyawarsa ya sanya siffofinta suka yi kama da na 'yar bayinsa masu jinƙai da tausayin talaka. Ga shi yau *A SANADIN KAMA* Rayuwarta da ta iyayenta da ƴaƴanta ta haskaka, ita kam tsakaninta da Margayiya Mimie sai dai addu'ar dacewa da rahamar ubangiji, domin a silarta ta samu wannan gatan da bata taɓa hasasowa ba ko da a duniyar mafarkinta. Tabbat bi hamdillah, duka_duka a nan na kawo ƙarshen wannan ƙayataccen labarin mai cike da faɗakarwa tare da wa'azantarwa da fatar masu karatu kun ɗauki darasi a rayuwar Mimie da sauran jarumai littafin. Ina rokon Allah ya yafe mun kuskuren dake ciki ya ba ni ladan faɗakarwa. Sai mun haɗu daku a cikin sabon littafi na, wanda zai zo da sabon salo littafin da zai ɗarsa tausayi da tsoron Allah a zukatanku *HALITTAR ALLAH CE* Shine sunan littafin ya na nan tafe very soon. Mai son farin cikinku ce. RUKY I LAWAL🌹🌹🌹🌹🌹 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 15 of 15