Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ɗago ta kalli Daddyn su na haɗa ido ta kuma sunne kai ƙasa. Iyayenta ma da yayyenta haka su ka ji maganar a bazata. Lura da yanayinta yasa Daddy ya ce "Ki kwantar da hankalinki y'ata, shine ya sanar da ni ya na sonki, amma duk da haka ba zan takuraki ba, ba tursasawa idan kin gama shawara ma yi magana daga baya." Daga haka ya tashi ya ma su sallama zai tafi, a dai-dai lokacin ne kuma Ma'aruf ya dawo gidan tare da Sagir. Nan fa kallo ya koma sama domin Sagir saka rigima ya yi shi ba inda za shi, zai zauna da Sisternsa anan, aka yi-aka yi fafur ya ƙi, sai da Daddy ya kira Mamy a waya ya gayamata tare da bawa Sagir wayar. Komai ta gaya masa oho, sai ga shi ya amince zai bi Daddy su koma gida. Anan ya masu Sallama Dukansu su ka ɗunguma zuwa kofar gida don su ma sa rakiya. Motarsa ya hau driver ya ja zuwa abuja, a ransa ya na da ƙudurin canza ma su gida, amma so ya ke sai komai ya dai-daita tukunna. Tun daga ranar aka fara kiran Zuhra da Mimie kowa haka ya ke kiranta, domin a ɗabbaƙa Alfarmar da aka yiwa Daddy. Bayan tafiyar Daddy Zuhra ta shirya zuwa gidansu Raliya domin ta kai mata kayan arziƙin da su ka samu a matsayin tsaraba. Raliya ƙawarta ce tun a primary ajinsu ɗaya kuma kujera ɗaya har yanzu su na tare kuma aji ɗaya duk da cewa Raliyan ta girme ta amma sun shaƙu sosai. Ta na matuƙar tausayawa rayuwar ƙawartata, kasancewar mahaifiyarsu ta rasu shekara uku da su ka wuce, kuma mahaifinsu mai ƙaramin ƙarfi ne kamar babansu, ga shi har zuwa lokacin bai ƙara aure ba, sai su kaɗai a gida, yayarta ɗaya ƙannenta huɗu duk ita da yayarta ke kula da su. Sai da ta ɗibar mata komai na kayan abincin kama daga kan shinkafar har kayan maggin sannan ta nufi gidansu. ®®®®®®®®®®®®® Bayan wata Ɗaya Zaune ta ke a tsakar gida akan ƙaramar kujerar katako ta na wanke-wanke. A zahiri wanke-wanken ta ke amma kallo ɗaya za ka mata ka fahimci cewa hankalinta ba ya gun, ta yi nisa acikin tunanin wannan sabon al'amari da ya tunkaro rayuwarta, mafita kawai ta ke nema. Ta na nan a haka bata ankara ba sai ji ta yi an dafa kafaɗarta, ta juyo aɗan razane sai ta ga ashe ƙawarta ce. Da mamaki a fuskarta ta ke kallon tasleem tare da cewa "Tasleem! Yaushe ki ka zo ne? Ban fa ji shigowarki ba." Tasleem ta ce "Dama yaushe za ki ji shigowa ta? Tun da ki na nan ki na wannan sababben tunanin na ki, ni na rasa meke damunki ne, Soyayya hauka ce, da za ki mayar da kan ki haka?, Ke kenan kullum tunani.?" Ɗan murmushi ta yi bata ce komai ba, Tasleem ta cigaba da cewa "Na san dai ki na tunanin Rayuwarki ne wato Bassam, Wai ni kam ƙawata wane irin so ne ki ke yiwa Bassam haka?" Ta tambaya tare da janyo wata kujerar da ke kusa da ita ta zauna kusa da Mimien. Sai da ta ɗauraye kular da ke hannunta ta kife a cikin kwando kafin ta yi murmushi ta ce "Ba za ki gane ba ne ƙawata, ina son Bassam fiye da komai a rayuwata, ni kaina ba zan iya kwatanta iya adadin son da na ke yi masa ba, Abun da nasani shine duk duniya ba wani fa namijin da na ke so sama da shi, duk da cewa ba shi ne na farko da ya furta min kalmar so ba, Amma akansa na fara soyayya, kuma ba wanda na kamu da tsananin sonsa har na amincewa zuciyata ba zan iya rayuwa idan ba shi ba sai Bassam." Murmushi sosai Tasleem ta yi ta ce "To ƙawata Allah ya bar ƙauna ya sa shine abokin Rayuwarki na har abada." Miƙewa ta yi adai-dai lokacin da ta kammala aikin da ta ke tare da ɗauke kwandon ta na washe baki ta ce "Ameen ƙawata Allah ya bar mun ke." "Ba zai bar ni ba wallahi sai na mutu." Ta faɗa Ƙyalƙyalewa da dariya ta yi ba ta ce komai ba. Miƙewa tsaye Tasleem ta yi tare da Faɗar "ke ba fa zama na zo yi ba, dama zan je gidan yaya Khalil ne, shine na ce bari na biyo mugaisa,kin san tun dawowar ki daga Abuja ban samu shigowa ba saboda muna exam ne, amma zan samu dama na yi miki zuwa na mussanman." "Nagode sosai ƙawata sai kin zo, mu je na taka mi ki koh?." Ta faɗa. "No da kin barshi tare muke da direba." Tasleem ɗin ta faɗa. Duk da haka ba ta hak'ura ba sai da ta raka ta har k'ofar gida. Mimie ta ce "Nagode sosai ƙawata a sauka lafiya, Allah ya kiyaye hanya." Ameen ta ce tare da shigewa cikin motar direba ya ja su ka bar ƙofar gidan. ®®®®®®®®®®® Juyawa ta yi ta koma cikin gidan ta cigaba da Aikace-aikacen ta dama Mama ba ta nan ta fita saboda haka ba kowa a gidan sai ita kaɗai tsintsiya ta ɗauka ta share tsakar gidan gaba ɗaya da ya ke gidan ba wani mai girma ba ne sosai cikin mintuna ƙalilan ta kammala Sharar. Ruwa ta ɗiba a bokiti ta nufi banɗaki ta yi wanka, tana fitowa ta ɗora Alwala kasancewar lokacin Sallar Azahar ya yi. Ɗakinta ta shige ta saka kaya tare da zura dogon hijabinta ta shimfiɗa Sallaya ta tada Sallah. Sallamewar ta keda wuya ta ji ƙarar wayarta ƙirar iphone 6+ da ke gefe ɗaya a kusa da ita. Da sauri ta ɗauki wayar don ta riga ta san mai kiran ko bata duba ba, Bassam ne ke kira. Murmushi ne ya bayyana a fuskarta yayin da ta ke ɗaga kiran, Wayar ta kai saitin kunnenta tare da yin Sallama. A ɗaya bangaren Bassam ne ya Amsa Sallamar cikin zazzaƙar muryarsa mai kama da sautin kanari. Faɗaɗa murmushinta ta yi su ka gaisa sosai daga nan kuma su ka fara kashewa juna zuciya da tausasan kalamai masu ratsa zuciya sai da su ka shafe kusan minti Arba'in su na wayar kafin su ka yi Sallama da juna su ka datse kiran. Dogon numfashi ta ja, haɗe da faɗawa akan ƙaramar katifarta ta tsunduma kogin tunani "Oh! Allah ga Mimie, Allah ka dube ni da idon rahama." Ta faɗa a bayyane. Bakomai ne yasa ta faɗin haka ba sai dan tunawa da ta yi cewa Daddy Ya na so ya haɗa ta aure da babban ɗansa wato Sameer, kuma ba za ta iya tozarta Daddy ba, ba ma yadda za'ayi ta ƙi jininsa Tun da ya so ta ya nuna mata gata ya ɗauke ta tamkar y'ar cikinsa (Real mimie) da ya haifa, ita kam ta na jin kamar ta karɓi zaɓin sabon Abbanta da ya nuna mata gata fiye da kowa a duniya, to amma ya za ta yi da zaɓinta babban masoyinta a duniya? Dole ne dai ɗaya za ta aura acikinsu ko dai Sameer ko Bassam. Ta na kai nan a tunaninta ta kuma jan dogon numfashi tare da dafe kanta da Tafin hannunta ta na faɗar "Oh! Ni Mimie ina mafita?, Allah ka fitar da ni daga wannan matsalar." Mirginawa ta yi akan katifar ta na cigaba da cewa "Amma fa ya kamata na yi tunani sosai tsakanin masoyan nan nawa guda biyu, waya kamata na aura ne?" Ajiyar zuciya ta yi kana ta ci gaba da tunaninta. Sameer dai ɗan Alhj ne kuma ko da bai faɗa ba ta san shine zaɓinsa tun da ba zai ƙi ɗansa ba, amma fa ya gaya mata ba tursasawa idan dai har bata son Sameer ka da ta ji kunyar gaya masa don ta na ganin cewa Sameer ɗansa ne, ai itama y'ar tasa ce da ya ke ji da ita wacce ta ke a matsayin Mimiensa y'a ɗaya tilo da ya ke da kuma ya ke ji da ita tamkar Rayuwarsa, sai ga shi mutuwa ta masa yankan ƙauna. Ya yi baƙin cikin matuƙa a lokacin mutuwarta, amma yanzun da ya sami wace take a madadinta sai ya ji baƙin cikinsa ya gushe to me zai saka ya tursasa Mimiensa? Ya gaya mata cewa idan da wanda ta ke so ta sanar da shi, shi zai shige mata gaba ayi komai na auren. Sai dai ita fa ta na matuƙar jin kunyar Alh Salman, ta ya za ta buɗi baki ta ce ba ta son ɗan cikinsa? Inah! Ba zai yiwu ba. A zahirin gaskiya kallon yaya ta ke masa ba masoyi ba ba zata iya aurarsa ta bar Bassam ba, idan ta yi haka tamkar ta yaudari masoyinta Bassam ne. Duk da cewa iyayenta suna ƙarfafa mata gwuiwa ta auri Sameer domin ƙin aurensa kamar butulcewa Alhaji ne, amma inah! Sam ita ba za ta iya ba ko alama... Ta na ganin daurewa kawai za ta yi ta fuskanci Daddy ta sanar da shi gaskiyar lamari cewa....... 🤔🤔tirƙashi! Idan baku manta ba a farkon labarin kunga Mimie a gidan Bassam ana gallaza mata. Tambayar anan ita ce: Shin ina yawan ƙaunar da ya ke mata ta tafi? Me yasa ya juya mata baya? Ina kuma labarin Sameer? Tayaya ta auri Bassam ta bar zaɓin iyayenta? Domin jin cigaban wannan ƙaryata cen labarin sai ku biya kuɗin ku 200 ba yawa. Ga mai buƙata sai ya tuntuɓeni ta wannan number👇🏼 _08109634202_ Domin na masa ƙarin bayanin yanda zai biya kuɗin. Ka da ku manta wannan shine last free Page duk mai buƙatar jin cigaban wannan labarin sai ya biya kuɗin da ₦200 kacal ba yawa, a tura katin ta number da ke sama. Follow me on wattpad @ummu inteesar. Vote, share& Comment UMMU INTEESAR CE💚💙💛💙 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *A SANADIN KAMA* 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *DAGA ALƘALAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)* MARUBUCIYAR SOYAYYAR MEERAH Y'AR GANTALI RIKICIN MASOYA *DA KUMA* *A SANADIN KAMA* WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE AKAN NAIRA 200 KACAL. GA MAI BUƘATA YA TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER 08109634202 KA DA KU MANTA WANNAN PAGE ƊIN NA WANDA SU KA BIYA NE SU KAƊAI, IDAN KA SAN BAKA BIYA BA KADA KA KARANTAMUN DOMIN HAƘƘI NA NE, IDAN MA KA BIYA KUƊIN KADA KA FITARMIN DA LITTAFI DOMIN KUƊIN KARATU KA BIYA BA MALLAKA NA BAKA BA. ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com *BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM* Page 3️⃣1️⃣↪️3️⃣2️⃣ Cewa ita fa gaskiya Bassam ta ke so shine cikar burinta kuma farin cikinta. A haka ta wanzu ta na ta tunanin mafita har bata san ta shafe tsawon lokaci haka ba, sai da ta ji kiran sallar la'asar. Miƙewa ta yi ta tada Sallah dama da arwallarta, a haka Mama ta dawo ta same ta. ®®®®®®®®®®® A haka rayuwa ta cigaba da gudana ko yaushe Mimie na cikin zullumi da tunanin mafita don gudun kada a rabata da masoyinta.. Dama tuni an koma hutu don haka ta cigaba da zuwa makarantar ta kamar lokutan baya sai dai yanzu rayuwarta ta samu sauyi ba kamar da ba, domin yanzu su na da wadataccen abinci da suturu masu kyau sakamakon shigowar Alhaji Salman cikin rayuwarsu. ®®®®®®®®®® A bangaren Mommy kuwa ta gama cika fam! Fashewa kawai ya rage ta yi, domin yanzu wata tsanar Mama da ƴaƴanta ta ke ji, domin a ganinta su suka hanata damar cika burinta na shiga cikin daular dukiyar Alhaji Salman. Bayan tafiyar Mimie Mommy bata kira su ta ji ya su ka sauka ba, duk ta watsar da su saboda hassada, yanzu babban target ɗinta shine ya za'a yi ta aurar da y'arta Ruma a gidan Alhaji Salman?, Domin a gaskiya ba zata iya ƙyale wannan daular ta wuce ta na ji ta na gani ba, saboda haka akai-akai takan kira Mamy su gaisa a waya, shima Alhajin haka wani lokaci ma har su mata kyautar kuɗi, domin su nuna musu ta ke duk duniya ba wanda yafi ta son Mimie. ®®®®®®®®®®® Alhaji Salman kuwa ya na matuƙar son ya ga aure ya ƙullu tsakanin Mimie da Sameer domin ta dawo cikin iyalansa kamar baya, amma ba ya son ya takura ta, hakan ya saka ya yi gum da bakinsa ya ƙara bata dama daga nan zuwa lokacin da za ta yi candy. Mamy da ta ji zancen soyayyar da Sameer ke yiwa Mimie ba ƙaramin daɗi ta ji ba, don haka a kullum ta kai goshinta ƙasa sai ta roƙi Sarkin talikai da ya ƙaddara wannan aure na yaranta. ®®®®®®®®®®® Zancen soyayya tsakanin Mimie da Uncle Bassam ɗinta kuwa sai ma abinda ya ƙaro, ya na tarairayarta gami da bata kulawa baya son damuwarta ko kaɗan. Wata rana da dare Mimie na kwance akan katifarta (sabuwa da ta siya da kuɗin da Daddy ya tura mata) Kawai sai wayarta ta hau ruri, acikin magagin barci ta lalubo wayar ta katse kiran tare da koma kwanciya, domin ta tsani abinda zai katse mata barci mai daɗi irin wannan. Wayar ce ta kuma ruri a karo na biyu a ɗan fusace ta ɗaga wayar ta ɗora a kunnanta bata ce komai ba, still idonta na rufe. Daga can ɓangaren Sameer ne ya ce "Assalamu alaikum warahmatullah wa barakatuhu, da fatar ban katsewa sweet sis daddaɗan barcinta ba." Zumɓur ta yi ta tashi zaune ta na waro ido a ranta ta ce "Yaya Sameer?" "Meyasa zai kirani kuma a wannan lokacin?." Mamaki ta ke sosai, domin wannan ne karo na farko da su ka fara magana a waya. A daƙile ta amsa mai da cewa "Wa'alaikamus Salam, Yaya Barka da dare." "Yawwa Barka dai, kin fara barci ne?" "Eh." Ta basa amsa a taƙaice. Ya ce "Ayyah! Sorry sweet sis, na katse maki barci amma ki yi haƙuri a bar ƙaunata zuciyata ce ta azalzalamun akan son jin muryarki har ta saka na manta cewar yanzu dare ne, mai yiwuwa kuma Sweety barci ta ke." Kalamansa sun bata mamaki duk da cewa bai kamata ta yi mamakin ba domin ya riga ya sanar da ita cewa ya na sonta. Mamaki da fargaba ne ya hanata maida masa da amsa. Shi kuwa jin shirun ya yi yawa ya saka ya kashe wayarsa domin a zatonsa ko barcin ne ya wuce da ita tunda dama ta fara. Murmushi ne kwance a fuskarsa yayin da ya katse wayar, ko ba komai dai ya yi farin ciki tunda ya ji muryarta kuma ya tabbatar ta na lafiya, a bayyane ya ce "Allah ka mallaka mun zuciyar wannan yarinyar, Allah ka bani ita a matsayin uwar ƴaƴana, ameen." Ita kuwa bayan katse wayarsa barci ne ya ƙauracewa idonta ta rasa ma tunanin me za ta yi, tabbas ta na cikin sarƙaƙiya, ƙwaƙwalwarta na dab da tsayawa cak akan tunanin mafita, to ita yanzun wa za ta aurah, Sameer ko Bassam? Dogon numfashi ta ja tare da mirginawa ta sauka daga kan katifar ta je ta ɗoro Alwala ta tada Sallar nafila ta na roƙon Allah da ya kawo mata mafita acikin wannan lamarin (dama Mimie yarinya ce mai ibada sosai, wannan na daga cikin ɗabi'unta duk lokacin da wata matsala ta tunkaro ta, tana mayar da dukkan lamuranta ga Allah ta hanyar yin nafilfili da riƙon Allah domin ya kawo mata mafita) A kullum iyayenta su na ƙara ƙarfafa mata gwuiwa da bata shawara akan ta auri Sameer ko don halaccin da iyayensa su ka mata, amma har zuwa yanzu bata jin za ta iya barin Bassam domin a ganinta ba zata taɓa jin daɗin rayuwa in ba shi ba. ®®®®®®®®®®® Bayan shekara ɗaya da rabi, abubuwa da yawa sun faru a ciki kuwa harda sabon gidan da Alhaji ya siya ma Baba a unguwar geza, gidan bene ne babba, dai-dai wanda zai ishesa yin rayuwa da iyalansa cikin farin ciki, wancan gidan na Tukuntawa Baba ya saka yan haya aciki, yanzu kam alhamdulillah komai ya wadata agaresu. Yan uwan baba da su ka guje shi saboda talauci da ya ke fama dashi, yanzu duk sun laɓaɓo sun bashi haƙuri su na neman yafiya a gareshi na gudunsa da su ka yi abaya don suna ganin sun fi shi arziƙi(Rayuwa kenan, dama duk lokacin da baka da shi to kai ba kowa bane, yan uwanka ma gudunka su ke amma daga lokacin da ƙofofin arziki suka fara buɗe ma kuma sai ka dawo kaine abun girmamawarsu.) A lokacin kuwa Zuhra ta na Ss3 a shekarar za ta yi candy, har yanzu dai ta na nan a makarantar y'an mata ta gandun albasa, ba yadda Daddy bai yi ba ta bari a canza mata makaranta amma ta ƙi, acewarta ko a makarantar gwamnati mutum ya ke zai iyayin karatu idan ya so." Zahirin gaskiya ba ta so a raba ta da ƙawarta Raliya da su ka ta so tare tun ƙuruciya, sosai Zuhra ke son Raliya ta na kyautata mata, barin yanzu da su ka fara samun abun duniya komai ta kwasa Raliya ta ke kaiwa, ba ƙaramin daɗi Raliyan ke ji ba, domin su ma sun shaida cewa su Mimie sun samu. Ko da yaushe Daddy da Mamy cikin turawa Zuhra kuɗi su ke a account domin yanzu sun ƙara shaƙuwa fiye da da, domin a shekaru biyun da su ka gabata duk hutu a Abuja ta ke yinsa, sai hutu ya ƙare ta ke dawowa kano. Saboda haka yanzu koda yaushe tana cikin yin vidio call da su yaya Saheen da Salim a laptop ɗinta ko a wayarta. Lokacin da ya rage baifi saura sati uku ba afara weac a lokacin ne kuma yaya Sameer ya tayar mata da ƙayar baya akan zancen aurensu, shima Daddy a lokacin ya tuntuɓe ta don son jin shawarar da ta yanke, a bangare ɗaya kuma ga Bassam sai zumuɗi ya ke akan alƙawarin su ya kusa cika harma ya sanar da iyayensa domin su zo neman aure. Nan fa hankalin Mimie ya tashi ta rasa yanda za ta yi, gabaki ɗaya hankalinta a tashe ya ke gashi har zuwa lokacin ta kasa samun mafita. Ana cikin wannan halin ne wata rana da daddare iyayenta su ka yi kiranta zuwa falon Baban nata domin su nusar da ita akan wannan lamari. Zaune ta ke a ƙasa kan carpet ta sunkuyar da kanta ƙasa yayin da Baba ya fara magana kamar haka:Zuhra ina so ki nutsu sosai ki saurare ni, lokaci ya yi da za ki sanar mana wa za ki aura acikin manemanki biyu, kin sani dole ɗaya za ki aura don haka wa ki ka zaɓa?" Sunkuyar da kanta ta yi ƙasa idonta ya fara tara ƙwalla ta na tunanin ita ta ina ma za ta fara? "Muna sauraron ki" mama ta faɗa. Buɗi baki ta yi daƙyar ta ce"Baba ni......... Follow me on wattpad @Ummu inteesar UMMU INTEESAR CE❤️💔💛 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *A SANADIN KAMA* 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *DAGA ALƘALAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)* *MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH* *Y'AR GANTALI* *RIKICIN MASOYA* *DA KUMA* A SANADIN KAMA ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com *BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM* Page 3️⃣3️⃣↪️3️⃣4️⃣ Daƙyar ta ce "Baba ni a gaskiya gani na ke kamar idan ban auri Bassam ba na yaudare shi kuma gaskiya ni...." Maganar ce ta laƙe a kasan maƙogwaronta ganin a gaban iyayenta ta ke. Baba ya tari numfashinta da cewa "Ai dama tun farko ba mu mai alƙawarin cewa za mu ba shi ba, kuma ba mu ƙarbi komai nasa ba, don haka ba yaudara, zan kira sa na bashi haƙuri." Ɗago kai ta yi zuciyarta na rawa ta ce "Amma Baba gaskiya ni fa kallon yaya na ke yiwa yaya Sameer ba zan iya aurarsa." Mama ce ta cafe zancen da cewa "Yaro man kaza, idan bakya sonsa yanzu, a hankali idan kuna tare za ki so shi amma da kunya, mu gayawa Alhaji cewar ba za ki auri dansa ba, don haka ki haƙura kawai." Hawaye mai zafi ne ya fara bin kuncinta ganin ana neman raba ta da mutum da ta shaqu dashi sama da kowa, kuma mutumin da ta shafe shekara biyu wutar ƙaunarsa na ruruwa a ranta, gaskiya ba za ta iya ba. Ta na ganin za ta ajiye kunyar nan kawai ta fito musu da abinda ke ranta. Gyara zamanta ta yi ta sunkuyar da kanta ƙasa ta ce "Baba, Mama ku yi haƙuri ka da ku ce na maku rashin kunya, Amma gaskiya Ni dai Bassam na ke so shi kaɗai zan iya....." Mama ce ta katse mata zance yayin da ta ke cewa "La'ilaha ilallah! Malam ka ga yaran zamani koh?" Ta faɗa ta na tafa hannu tare da kallon baba. Numfashi ya ja "hmmmm" sannan ya kalli Mimie ya ce "Zuhra! Ɗago idonki ki kalleni." Ba musu ta ɗago madai-daitan idanuwanta masu haske ta zuba mi shi su. Ya ce "Zuhra kin sani cewa mu iyayenki ne, mu muka haife ki muka sha ɗawainiyar rainonki tun kina jinjina har kawo yanzu da ki ka zama budurwa, kin sani cewa ba yadda za'a yi mu zaɓa maki abinda zai cutar da ke saboda muna sonki sosai." Ɗan tsagaitawa ya yi yana kallonta don ya ga ya ta ƙarbi zancen. Sai dai ita tuni ta sunkuyar da kanta ƙasa hawaye na cigaba da yin sintiri a kumatunta. Bai damu da hakan ba ya ci gaba da cewa "Sau tari Kakan so abu ya kasance ba alkhairi bane a gareka, ko ka ƙi Abu ya kasance shine alkhairi a gareka, shiyasa ake so duk lokacin da mutum zai yi wani abu makamancin wannan to ya yi istikhara ya mayar da lamarinsa ga Ubangiji. Don haka a matsayina na mahaifinki ina mai ba ki shawara da ki auri Sameer ko don karamcin iyayensa a garemu, idan ki kai mana haka zamu ji daɗi sosai ni da mahaifiyarki kuma kin mana biyayya, amma zaɓi ya rage na ki ba zan maki auren dole ba." Ya na kai nan ya yi shiru alamar ya kawo ƙarshen zancensa. Tun lokacin da ya fara maganar ta ke jin kanta ya na mata masifar ciwo kamar zai fashe, kalamansa sun matuƙar gigita ta da bata mamaki har ta fara zargin iyayen nata kodai...? Don haka ko da ya kai ƙarshen zancensa miƙewa kawai ta yi tare da dafe kanta ta fashe da matsanancin kuka yayin da ta ke barin gun ta na faɗar "Ni dai wallahi uncle Bassam na ke so, za ku iya rasa ni idan....." Bata ƙarasa zancen ba sakamakon kukan da ya ci ƙarfinta. Da mamaki iyayen nata ke Binta da kallo abun na ba su mamaki da tsoro ace wai y'arsu ce a gabansu ta na gaya masu haka? Yarinyar su mai matuƙar kunya, ladabi da biyayya ita ce yau ta ke faɗa masu haka a gabansu? Tabbas akwai aiki ja a gabansu. ®®®®®®®® Ita kuwa bayan shigewar ta taƙinta anan ƙasan tiles ta sulale ta na kuka mai cin rai, "Meyasa su Baba za su yi mana haka? Anyah! Sun ɗauko hanyar adalci kuwa? Meyasa su ke son rabani da Bassam bayan su da kansu su ka ba mu damar zama masoya? Da ba su yarda za su basa ba ai da ban faɗa tarkon sonsa harna shaƙu da shi haka ba? Sai yanzu da na kai ƙoluluwa a kan bishiyar ƙaunarsa za su nemi yado ni ƙasa? Wannan abun ba zai taɓa yiwuwa ba wallahi, ba zan yi biyayya wa wannan maganar ba, indai akan Sameer ne na san yanda zan yi." Ta na kai nan a tunanin zucinta ta rarrafa ta janyo wayarta da ke kan bedside drower ta shiga neman layin Sameer don yau so ta ke ayi ta ta ƙare domin ba zata taɓa saɓuwa ba bindiga a ruwa. Har ta ƙaraci burarinta bai ɗaga ba, nan fa ta ƙara ƙuluwa a bayyane ta ce "aikin banza wai a hakan ka ke so a baka ni, bayan ka kasa kula da wayarka ma bare ni. Su ƴaƴan ma su kuɗin nan me su ka ɗauki kansu ne?" Ta na cikin wannan mitar ne sai ga shi ya biyo kiran, ɗagawa ta yi a gadarance ko sallamarsa ba ta tsaya amsawa ba ta ce ....... Ku yi haƙuri da wannan kun san daga tafiya na ke so agajiye na ki wallahi shiyasa, don kawai na ga shirun ya yi yawa na ce bari na maku. Follow me on wattpad @ummu inteesar UMMU INTEESAR CE❤️💔💛💔❤️ 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *A SANADIN KAMA* 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *DAGA ALƘALAMIN RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)* *MARUBUCIYAR SOYAYYAR MEERAH* *Y'AR GANTALI* *RIKICIN MASOYA* *DA KUMA* A SANADIN KAMA WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE DON ALLAH IDAN KA SAN BAKA BIYA BA KADA KA KARANTA MUN. IDAN MA KA BIYA DON GIRMAN ALLAH KADA KA FITARMIN DA SHI DOMIN KUƊIN KARATU KA BIYA HAƘƘIN MALAKA NAWA NE ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com *BISMILLAH RAHMANIR-RAHIM* Page 3️⃣5️⃣↪️3️⃣6️⃣ Ta ce "Don girman Allah Sameer ka yi haƙuri ka janye maganar aurena da ka ke so ka yi, tun kafin haɗuwata da kai

Chapter 6 of 15