bangaren karatunsu.
Dukkan ƴaƴan nasa Allah ya saka ma su albarka su na iya ƙoƙarin su gurin ganin sun faranta ma iyayensu, kafin shigowar Alhj. Salman cikin rayuwarsu.
Alhaj Salman ya kawo haske a rayuwarsu don yanzun haka Baba ya na zaune da iyalansa a gida mai kyau cikin sukuni da walwala duk a sanadiyyar Alhj Salman.
Haƙiƙa *Sanadin kama* rayuwarsu da ta y'ar su ta haskaka, haɗuwar Alhj Salman da Zuhra ya za me ma su alkhairi a rayuwa.
Ga mai buƙata sai ya tuntubeni ta wannan number👇🏼
_08109634202_
Domin na masa garin bayani.
Follow me on Wattpad@ ummu inteesar
Vote,share & Comment.
UMMU INTEESAR CE❤️💛💙🧡💚
👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻
*A SANADIN KAMA*
👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻
*DAGA ALƘAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*
*MARUBUCIYAR:*
*SOYAYYAR MEERAH*
*Y'AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*DA KUMA*
*A SANADIN KAMA*
________________________
________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*
Free Page 7️⃣↪️8️⃣
Zuhra ta kasance kyakkyawar yarinya ta gaban kwatance, ita fara ce ba sosai ba, ta na da matsakaici tsayi, siririya ce amma bata cika rama ba.
Ta na da mayalwacin gashi da ya sauko a kafaɗunta ga shi da laushi da santsi, idanuwanta farare tas kamar madara.
A taƙaice dai ka na ganinta ka ga bafulatanar asali.
Ta na karatu a makarantar y'an mata da ke unguwar gandun albasa.
Duk da cewa ta na karatu a makarantar gwamnati ne amma hakan bai hana ta mayar da hankalinta akan karatunta ba, don ita ɗin mai ƙwazo ce, ta na da fahimta sosai ga basira, Allah ya yi mata tarin baiwa wacce ba ko wace yarinya ce ta ke da ita ba.
Labarin ya soma ne a lokacin da ta ke Ss1 a Secondary school.
A wata ranar Laraba da misalin ƙarfe 7:45 na safe tsaye ta ke a gefen titin unguwarsu ta na neman abun hawa, sanye ta ke cikin uniform ɗinta Riga da wando, da hijabinta iya gwuiwa.
Ƙafafunta sanye su ke cikin safa fara da sandals na makaranta, jakar makarantarta na rataye a kafaɗarta.
Ka na ganin ta ka san ta na cikin yanayin damuwa, ta ƙagu ta ganta a makaranta, don ta kusa ta yi latti, amma ga shi ta shafe kusan mintuna goma bata samu abun hawa ba.
Wata mota kirar Honda Civic ta zo wucewa a gabanta, har ya wuce sai kuma ya yi reverse ya dawo, a gabanta ya tsayar da motar.
Sauke gilas ɗin motarsa ya yi tare da cewa "Assalamu alaikum y'an mata."
Ta karɓa mishi da "wa'alaikumus salam." Ta na ƙoƙarin matsawa gaba.
Da sauri ya ce "Ba ki ji ba y'an mata."
Juyowa ta yi ta kalle sa ba ta ce komai ba.
"Idan ba damuwa ki zo na rage ma ki hanya na ga kamar kin kusa latti koh?" Ya faɗa.
Girgiza mishi kai ta yi alamar A'a ta ce "Ka barshi na gode."
"Da dai kin shigo na kai ki domin da alama yau abun hawa na wuya a gurin nan ga lokaci na tafiya."
Ta so ta yi gardama a karo na biyu amma sai ta ga idan fa ya wuce da wuya ta sami wani lift ga shi ta jima bata samu napep ba, saboda haka ta ƙarasa bakin motar ta buɗe ta shiga ta na faɗar "Nagode sosai."
Murmushi ya yi ya kalleta bai ce komai ba ya cigaba da tuƙinsa cikin nutsuwa da ƙwarewa.
Sun ɗan fara nisa a tafiyar ta ɗago ta kalle sa da alamar mamaki a fuskarta, da alama akwai Magana a bakinta.
Shima kallon tan ya ke, ya ce "Ki na mamaki ban tambaye ki wace makaranta za ki ba koh?"
Ɗaga masa kai ta yi alamar eh.
Murmushi ya kuma yi a karo na biyu ya ce "Saboda na sani ne, ko ba Makarantar yan mata ta gandun albasa ba?."
Kallonsa kawai ta ke cike da mamaki ta ce "Eh ita fa."
Daga haka bata kuma cewa komai ba ta mayar da hankalinta akan titi ta na saƙe-saƙe a ranta.
Shi kuma murmushi kawai ya ke lokaci zuwa lokaci ya na satar kallon ta "Ta na da kyau masha'allah." Ya faɗa a ransa.
A haka su ka cigaba da zaman kurame har su ka ƙaraso dai-dai gate ɗin makarantar.
Faka Motarsa ya yi agefen titi, sai a lokacin ta kalle sa sosai ta ce "Nagode sosai yanda ka taimakamin Allah ya taimake ka."
Daga haka ta buɗe motar ta fita ta na murmushi ta yi cikin makarantar a lokacin bai fi saura minti uku ba takwas ta yi.
Kallonta ya dinga yi har ta ɓace masa acikin sauran ɗaliban da ke ƙoƙarin shiga makarantar sannan ya tada Motarsa ya tafi ya na jin wani abu na masa yawo a ransa game da yarinyar har ya ƙarasa office ɗinsu da ke cikin gidan nepa na ƙofar ɗan agundi.
******************
Bayan shuɗewar kwana biyu zaune ya ke a office ɗinsu da safe ya yi shiru, ka na ganin yanayinsa ka san zuciyarsa ba ta gun aikin da alama ya zurfafa a tunani.
Can ya sauke doguwar ajiyar zuciya ka na ya janyo wayarsa ya kira wata number, har ta kusa tsinkewa aka ɗaga daga can ɓangaren abokinsa ne ya masa sallama.
Amsa masa ya yi a taƙaice sannan su ka gaisa ya ce "Yawwa almustapha na ce ai a makarantar y'an mata ta gandu albasa ka ke aiki koh?"
"Eh a can na ke wani abun ne?." Ya mayar masa da tambaya.
Bassam ya yi murmushi ya ce "Bakomai gobe zan zo da safe na same ka a makarantar akwai wata yarinya ce da na gani kuma acan makarantar ta ke, ta kwanta mun a rai."
Y'ar dariya Almustapha ya yi sannan ya ce "Wow! Wannan wace mai sa'ar ce? Gaskiya har na ji na ƙagu na ganta, ya sunan matar tamu ne?"
Shi ma dariyar ya yi ya ce "Kai Ni dai sai anjima, me ka ke yiwa sauri idan na zo ai za ka ji ka gani."
Dukkan su su ka saka dariya sannan su ka yi sallama ya katse wayar.
Ya kuma tsunduma a tunani.......
Ga mai buƙata sai ya tutuɓeni ta wannan number👇🏼
_08109634202_
Domin na gaya masa yanda zai biya.
Follow me on Wattpad@ummu inteesar
Vote, share & Comment
UMMU INTEESAR CE❤️💛💙💚🧡💚🧡
👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻
*A SANADIN KAMA*
👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻
*DAGA ALƘALAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*
*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y'AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*DA KUMA*
*A SANADIN KAMA*
WANNAN LITTAFIN NA KUƊI AKAN NAIRA N200 KACAL.
KADA KU MANTA KUMA ZAFAFA BIYU DAGA ƘAWAYE BIYU NE, IDAN DUKA BIYUN KA KE SO *A SANADIN KAMA* DA *ƘURUCIYAR SAPNAH* TO N300 KACAL, IDAN KUMA WANNAN KAƊAI KA KE SO TO ZAKA BIYA KUƊIN KARATU N200 KACAL.
________________________
________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*
Free Page 9️⃣↪️1️⃣0️⃣
Ya Kuma tsunduma a tunaninta, a ranar haka ya wuni sukuku.
Ko da ya je gida ma ba wani barcin kirki ya yi ba, saboda ya ƙagu gari ya waye ya je ya kuma haɗuwa da ita a karo na biyu, haƙiƙa idanuwansa na marin ganinta.
®®®®®®®®®
Washe gari da misalin ƙarfe goma na safe ya fito a shirye tsaf, jakar aikinsa ya ɗauka domin shirin kenan daga can makarantar zai wuce gun aiki.
Motarsa ya ja ya fita, bai tsaya a ko'ina ba sai a makarantar idanuwansa na mararin ganin wacce tunaninta ya hanawa ƙwaƙwalwarsa sukuni.
Ɗaga waya ya yi ya kira Almustapha ya shaida masa ya ƙaraso, shi da kansa ya fito ya ja Bassam har office ɗinsa, Dama shine Exam officer na makarantar.
Bayan sun gaisa ne ya kora masa bayanin abinda ya ke tafe da shi kamar dai yanda ya fara faɗa masa a jiya.
Almustapha ya yi murna sosai da jin wannan daddaɗan labarin, dama sun jima su na so Bassam ya yi aure amma da an ma shi magana sai ya ce bai ga wacce ta dace da shi ba ne.
Shi da kansa ya ce har Class ɗinsu don yin kiran ta, yayin da ya bar Bassam a ofishinsa ya na jiran dawowarsa.
®®®®®®®®®®
Ta sha mamaki Sosai lokacin da Malam ya zo ya yi magana da malamin da ke gabatar da darasi akan cewa ya na son ganin Zuhriyya Sadeeq Yusuf.
Malamin ya kira sunan ta tare da mata umurnin ta bi bayan Malam Almustapha.
Ficewa ya yi daga class ɗin yayin da ta bi bayansa a tsorace, ta bar y'an aji su na y'an gulmammakinsu irin na ɗalibai.
A hankali ta ke takawa kamar wacce ƙwai ya facewa a ciki, kana ganin ta ka san a darare ta ke, a haka ta ƙarasa ofis.
Sallama ta yi aka amsa daga ciki tare da mata izinin shiga.
Tsoro fal ranta domin ita bakinta da na malam Almustapha bai taɓa haɗuwa ba, shiyasa yau da ta ji kiransa ta firgice.
Sai da ta shafe kusan mintuna uku tsaye a gun sannan ta shiga bakinta ɗauke da sallama yayin da kanta ke sunkuye a ƙasa.
Tun shigowar ta ofis ɗin ya ke Bin ta da kallo tamkar maye, sai da Uncle ya ankarar da shi a inda ya ke sannan ya dawo.
Kowannen su zuciyarsa halbawa ta ke da ɗan ƙarfi- ƙarfi, Muryar Uncle ce ta dawo da su inda ya ke cewa: "Abokina Ni zan fita kaɗan, ina dawowa bada jimawa ba." Daga haka ya fice daga ofis ɗin ba tare da ya jira amsar Bassam ba.
Shi kuwa ya yi hakane don ya ba su dama su tattauna cikin nutsuwa.
®®®®®®®®®®®
"Habah! Yan mata zauna mana."
Cikin hanzari ta ɗago kanta da ya ke ƙasa tun shigowar ta, jin Muryar da ta kasa mantawa, idanunta ne su ka sauka akan kykkyawar fuskarsa yayinda ya ke ta tsabga wani tsadadden murmushi.
Da sauri ta ɗauke dubanta daga kansa ta ƙarasa ta zauna akan kujera, gudun kada ta faɗi a yi abin kunya, saboda ƙafafunta da su ka ɗauki rawa.
Kallon ta ya ke sosai ya kasa ɗauke idonsa akanta yayin da ta kuma Sunkuyar da kanta ƙasa.
"Y'an mata, ya ki ke? Ya karatu, Ya bayan rabo?"
"Alhamdulillah." Ta amsa murya na rawa.
"Dafatar kin gane ni, Ni ne wanda na rage maki hanya a kwanakin baya."
Sai zuwa lokacin ta yi murmushi ta ce "Hakane nagane, Nagode sosai Allah ya saka ma da alkhairi."
Murmushi ya sakar mata sannan ya ce "Sunana Bassam Aliyu, Ni ɗan asali jihar Kebbi ne, amma yanzu ina aiki anan gari anan gidan nepa na ɗan agundi."
Shiru ya ɗan yi don ya ji ko za ta yi magana, jin bata ce komai ba ya ɗora da cewa "ya sunan malamar."
"Zuhriyya Sadeeq Yusuf, amma ana kirana da Zuhra."
"Nice name." Ya faɗa sannan ya ce "A taƙaice dai Malama Zuhra bakomai ne ya zo da ni nan ba sai don na miƙa ƙoƙon barata a gare ki, tun ranar da na fara ɗora idona akanki Allah ya jarabce ni da ƙaunar ki mai yawa, idan har kin amince min ina so na je neman aurenki."
Ɗago idonta ta yi da sauri tare da zazzare su da alama ta na mamakin jin kalamansa ne.
Ganin hakan da ta yi ya sanya shi yin ɗan murmushi ya ce "Ƙwarai kuwa ba wasa a kalamai na idan kin amince ki bani adress tare da number wayarki, Zan zo har gidanku, domin ba na son shiga lokacin karatunki wannan ma don ya zama dole ne."
Anan ta sanar mashi ita ba ta da waya sai dai ta ba shi address ɗinta, a haka su ka yi sallama tare da alƙawarin zai je har gida ya same ta.
A jinsu ta koma cike da murna, ta rasa dalili haka kawai ta ke jin ta cikin tsananin nishaɗi a yanzu, ko dan ya ce ya na sonta ne oho.
Shi kuma ya na fitowa ya ja Motarsa zuwa gun aiki shima ka na ganinsa ka san ya na cikin farin ciki, da alama yarinyar ta amince masa, bai yi tunanin samun ta haka cikin sauƙi ba.
®®®®®®®®®®®
Washe garin ranar ya je gidansu su ka shirya kansu shi da ita sa'annan ya sami Babanta da maganar.
Sosai Baba ya yi murnar jin wannan labarin sai dai ya shaidawa Bassam cewa shi ba yanzu zai aurar da y'arsa ba sai ta kammala karatun sakandare ɗinta idan zai iya jira nan da shekara biyu ba matsala, zai iya ba shi Zuhra.
Duk da ba haka ya so ba, amma ba yanda ya iya ya na tsananin son ta saboda haka ya ce ya amince zai jira har lokacin in dai za'a ba shi.
®®®®®®®®®®®®
Kwanci tashi ba wuya a wurin Allah, yau har ga shi sun shafe tsayin wata uku su na Soyayya, inda mafi yawan hirar su ta kasance a waya don baba Bai cika son fita hirar nan ba, itama wayar daƙyar ya bari Bassam ɗin ya siya mata nan ma sai da ya ta roƙarsa sannan ya amince.
A dai-dai wannan lokacin ne su ka fara rubuta Exam ɗin third time wanda da sun kammala za'a yi hutu bayan an dawo kuma sai shiga sabon aji.
Cike ta ke da farin ciki zuwan wannan lokacin domin kuwa ta yiwa Mommy alƙawarin da an samu wannan hutun za ta je mata hutu a Abuja.
Hakan ya sa ta mayar da hankalinta ga karatu sosai, wayar ma ba ko yaushe su ke yi ba da Uncle dole ya mata uzuri domin shima dagewarta akan neman ilimi na burge shi.
®®®®®®®®®
Bayan kammala jarabawar ne Zuhra ta shiga shirye-shiryen zuwa Abuja tuni dama Mommy ta turo mata kuɗin mota.
Ranar Assabar da dare Zuhra ta na zaune a gefen y'ar katifarta,ta na haɗa kayanta a akwati.
Ƙaramar wayarta ƙirar itel da ke ajiye a gefenta ta hau ƙara.
Ɗaukowa ta yi ta ɗaga tare da ɗorawa a kunnenta ta na murmushi.
"Ohk gani nan zuwa." Shine abinda ta faɗa, sannan ta kashe wayar ta zari hijabinta ta yi waje.
A tsakar gida ta haɗu da Mama, Maman ta ce "A'ah Zuhra saurin me ki ke haka?, ina za ki?."
"Uhmm! Mama dama Uncle ne ya zo za mu yi sallama kin san gobe zan tafi."
Dama tun sanda ta gano abokin Uncle ne ta ke ce masa uncle domin sunansa ya yi mata nauyi a baki.
"To shikenan maza ki je, amma ka da ki daɗe kin ga dare ya fara yi."
Daga haka Maman ta yi ciki, ita kuma ta fita.
A ƙofar gidan ta Same shi ta mi shi sallama ya amsa da murmushi a fuskarsa ya na faɗar "Barka da fitowa kyakkyawa zakaran gwajin dafin dukkanin yan matan duniya ga baki ɗaya.."
Ga mai buƙatar sayen wannan littafin sai ya tuntubeni ta wannan number👇🏼👇🏼
_08109634202_
Domin na masa bayanin yanda zai biya kuɗin, kada ku manta N200 ne kacal.
Follow me on Wattpad @Ummu inteesar
Vote, share & Comment.
UMMU INTEESAR CE❤️💛💙💚💔🧡🧡💙💚
👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻
*A SANADIN KAMA*
👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻
*DAGA ALƘALAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU-INTEESAR)*
*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y'AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*DA KUMA*
*A SANADIN KAMA*
WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE GA MAI BUƘATA ZAI BIYA N200 KACAL.
KADA KU MANTA KUMA ZAFAFA BIYU DAGA ƘAWAYE BIYU NE, IDAN DUKA BIYUN KA KE SO *A SANADIN KAMA* DA *ƘURUCIYAR SAPNAH* TO N300 NE, IDAN KUMA WANNAN KAƊAI KA KE SO ZA KA BIYA KUƊIN KARATU N200 KACAL.
________________________
________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*
Free Page 1️⃣1️⃣↪️1️⃣2️⃣
Tafukan hannayenta biyu ta saka ta rufe fuskarta alamar ta ji kunya ta ce "Kai uncle! Wannan kirarin haka, duk ni kaɗai?."
Murmushin ya kuma yi ya ce "Ai kinfi haka ma Amaryata."
"Allah uncle?" Ta tambaya.
Ɗaga mata kai ya yi tare da kashe ido ɗaya ya ce "Sosai ma."
Yan da ya yi abun sai ya bata dariya sosai ta ke dariya shima ya kama mata su na yi.
Ganin ta yi ya daina dariyar nan ta ke fuskarsa ta canza daga walwala zuwa yanayin damuwa.
A razane Zuhra ta kalle sa ta ce "Lafiya dai Uncle?"
Shiru ya yi na ɗan wani lokaci kafin ya ce "Yanzu shikenan tafiya za ki yi ba zan ƙara ganin ki ba sai bayan sati uku?"
Ɗan murmushi ta yi sannan ta ce "Yanzu Uncle saboda wannan ne ka ke ɓata ranka?, Haba dai ai bai kamata ka damu ba..."
Katse ta ya yi da cewa "Me ya sa ba zan damu ba?, Bayan idan ki ka tafi Abuja wani zai iya mun ƙwace."
Yanda fuskarsa ta sauya kamar mai shirin yin kuka ne ya ba ta dariya, dariya ta yi sosai sannan ta ce "In dan wannan ne ka da ka damu Uncle, ni taka ce kai kaɗai ba wanda zai iya ƙwace ma ni, kamar yanda kai ma nawa ne ba wacce ta isa ta ƙwace mun kai insha'allah."
Dubanta ya yi ya ce "Dagaske?"
"Sosaima my king."
Sai a lokacin ya yi dariya ya ce "Yanzu na ɗan ji sauƙi a raina, kuma na yarda za ki kulamin da kanki.
"Oh! Uncle ashe tsoro ne da kai."
Su ka saka dariya a tare, ya ce "Yo ba dole na ji tsoro ba, na san Amaryar tawa kyakkyawa ce tamkar gold."
"Kamar yanda angon nawa ya ke kyakkyawa ba."
Ta na kai nan a zancenta ta ce " yawwa na tuna, ka ce za ka je birnin Kebbi koh?"
"Eh insha'allah." ya amsa mata.
"Yaushe za ka tafi?" Ta kuma jefo masa tambaya.
"Nan da kwana biyu."
Ta ce "Allah ya kaimu." "Ni zan shiga ciki."
"Tun yanzu?" Ya tambaya.
"Mama ce ta ce kada na jima ka ga dare ya yi."
Ya ce "Gaskiya ne je ki kawai, Allah ya tsare hanya ya kai mun ke lafiya."
"Ameen."
"Idan kin isa can ki kira ni." Ya faɗa tare da ɗagowa daga jikin bangon da ya jingina.
"To" ta ce tare da faɗar "Sai anjima hubbyna."
Ya ce "Me ki ka ce?"
Juyawa ta yi da gudu ta yi cikin gida ta na faɗar "Wallahi ka ji, ni za ka yiwa wayo?, Tab!.
Bayanta ya bi da kallo ya na murmushi ya ja Motarsa ya tafi.
®®®®®®®®®
Ta na shigewa gidan ta ci gaba da haɗa kayanta.
Asubar fari Zuhra ta tashi, Sallah kawai ta yi ta haɗa shayi ta sha sannan ta yiwa iyayenta sallama.
Akwatinta ta ja ta nufi tasha, ta hau motar Abuja.
Tafiyar awa huɗu ce ta kai su garin Abuja, su na sauka ta kira Mommy ta shaida mata ta iso, Mommy ta ce "Dama su Ruma sun tafi ɗauko ki, su na hanya."
Ba ta fi minti biyar da gama waya da Mommy ba sai ga motar su Ruma ta ƙaraso.
Sosai su ka yi murnar haɗuwa da juna, shiga motar ta yi driver ya ja sai Area 1 dama acan gidan Umman ya ke.
Bayan sun ƙara gidan falo su ka nufa kai tsaye.
Mommy ta na zaune akan kujera ta na kallon tashar Bollywood su ka shigo ɗauke da Sallama a bakinsu.
Da sauri ta juyo ta na faɗar "Wa'ailaikumus salam, oyoyo ga manyan baƙi, ƙaraso y'ata."
Ƙarasawa su ka yi tare da zama akan kujerar suma, ana ƙara gaisawa.
Mommy ta ce "Ya iyayen naki da y'an uwanki?."
Ta ce "Qlau su ke sun ce a gaishe ki, ya su Yaya Sunil da Suhail?."
Su ma qlau su ke Mommy ta faɗa.
Mommy ƙanwar mamace Wacce ke Binta sunanta Hajiya khadija ta na Aure a nan Abuja, ta na da ƴaƴa Uku Sunil,Suhail sai kuma y'ar auta Rumaisa'u wacce su ke kira da Ruma, ita ɗin sa'ar Zuhra ce shekarunta goma sha shida a duniya, su na ɗasawa sosai ita da Zuhran.
Mommy ta ce "Ruma je ki kawowa y'ar Uwarki ruwa da abinci ta ci ta samu nutsuwa kafin ayi zaman fira."
"Gaskiya kam, don yau kam akwai fira." Ruma ta faɗa tare da miƙewa ta shiga kitchen.
Bayan mintuna biyu sai ga ta ɗauke da farantin snacks da lemon kwakwa, dabino da madara.
Karɓar lemon ta yi ta sha ta dubi Ruma ta ce "Ke ni wannan snacks ɗin ba yi mun za su yi ba, kai ni ga abinci kawai."
Ruma da Mommy su ka saka dariya a tare, Ruma ta ce "to ta shi mu ƙarasa dinning ki ci."
Su ka ƙarasa, ta ɗale kujera ta ce "Sister zuba mun abincin mana, ko ni zan saka da kaina?"
"Angama rankiyadaɗe yallaɓiya Zuhra." Ruma ta faɗa ta na murmushi.
Serving ɗinta ta fara yi, ihu kaɗan ta saka don ganin abincin da tafi so ne aka girka, wato dambun shinkafa haɗin zogale, tare da chicken pepper soup, sai kuma juice ɗin kankana.
Bismillah ta yi ta fara cin abincin tare da kallon Ruma da ke tsaye kusa da ita ta ce "Sister wa ya girka wannan abincin?"
"Ni ce, ai na san ki na matuƙar son dambun shinkafa shiyasa na miki." Ta bata amsa.
"Wow! Nagode sister." Ta faɗa.
Ta na kammala cin abinci ta shiga ɗakin Ruma inda nan ne masaukinta, ta yi wanka ta sake kaya zuwa na shan iska.
Ta haye gado ta shiga neman layin rabin ranta, Ringing biyu ana uku ya ɗaga kiran.
"Assalamu alaikum warahmatullah wa barakatuhu." Ya mata Sallama cikin sanyayyiyar muryarsa.
"Wa'alaikamus Salam."
Gaisawa su ka yi cikin farin ciki da annashuwa sannan ya ce "Gimbiyata kin isa lafiya?."
"Lafiya qlau alhamdulillah." Ta amsa.
"Ya mutan gidan? da fatar kin same su lafiya."
Nan ma da "Qlau Alhamdulillah." Ta amsa masa.
Daga nan kuma su ka ci gaba da hirarsu irin ta masoyan juna kafin su datse kiran.
®®®®®®®®®®
Kwanci ta shi asarar mai rai, yau har Zuhra ta yi sati biyu a Abuja, tun zuwanta kullum sai sun fita ita da Ruma, sun zazzaga gidajen y'an uwa da abokan arziƙi na ɓangaren Babansu Ruma da ƙawayen Mommy , sun yawata cikin garin Abuja su biyu kaɗai da ya ke su Yaya Sunil ba sa garin a lokacin.
®®®®®®®®®®®
Yau ta kama Ranar Asabar ranan ne kuma su Zuhran ke da niyyan zuwa ShopRite, su na so su je guraren shan iska.
Da misalin ƙarfe uku na yamma ta shirya cikin wata haɗaɗɗiyar atamfa(wacce Mommy ta aika mata da ita har Kano) riga da siket kalar light purple and pink, ta sanya mayafi light pink, jaka da takalminta duk iri ɗaya.
Juyawa ta yi ga Ruma da ke zaune ta ce "Sister mu je koh?."
Wani irin miƙewa Ruma ta yi har bakinta na ɓari gurin faɗar "Wow! Sister kin yi kyau sosai fa."
Murmushi ta yi ta ce "Nagode, mu je mu yiwa Mommy Sallama."
Su na zuwa Mommy ta sanar ma su cewa ai ta aiki driver har yanzu kuma bai dawo ba, ko za su jira shi ne?.
Ruma ta kalli agogon da ke ɗaure a tsintsiyar hannunta ta ja wani siririn tsaki ta ce "Bari kawai Mommy, za mu hau taxi lokaci ya ƙure."
Daga haka su ka fice daga gidan.
Sun taɓa tafiya kaɗan su ka tsaya neman taxi, sun yi tsayin mintuna biyar a gun ba su samu taxi ba.
Su na nan tsaye su ka ga wata tsaleliyar mota ta zo ta wuce ta gabansu, sai kuma su ka ga motar ta yi reverse ta tsaya a gabansu..
Ga mai buƙatar siya sai ya mun magana ta wannan number👇🏼
_08109634202_
Domin na sanar dashi yan da zai biya, ka da ku manta N200 kacal.
Follow me on Wattpad@ummu inteesar.
Vote,share & Comment
UMMU INTEESAR CE❤️💙💚💚💛
👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻
*A SANADIN KAMA*
👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻
*DAGA ALƘALAMIN RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU-INTEESAR)*
*MARUBUCIYAR:* *SOYAYYAR MEERAH*
*Y'AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*DA KUMA*
*A SANADIN KAMA*
WANNAN LITTAFIN NA KUƊI AKAN NAIRA N200 kacal.
Ga mai buƙatar siya sai ya tuntubeni ta wannan number👇🏼
_08109634202_
Domin na masa bayanin yanda zai biya kuɗin.
KADA KU MANTA KUMA ZAFAFA BIYU DAGA ƘAWAYE BIYU NA KUƊI NE, IDAN DUKA BIYUN KA KE SO *A SANADIN KAMA* DA *ƘURUCIYAR SAPNAH* TO N300 NE IDAN KUMA WANNAN KAƊAI KA KE SO ZAKA BIYA KUƊIN KARATU N200 KACAL.
________________________
________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*
Free Page 1️⃣3️⃣↪️1️⃣4️⃣
Haka kawai ya na zaune a office ɗinsa ya ji kamar an tsikare sa da tsinke, miƙewa ya yi ya fita ba tare da ya nemi drivernsa ba, ji ya yi kawai ya na so ya je gida da kansa, ba tare da driver ba.
Ya zo wucewa a motarsa kenan kwatsam sai idanuwansa su ka gane masa abinda ya matuƙar razana sa gami da ba sa tsoro, ya kaɗu matuƙa da ganinta, amma hakan bai hana sa tsayawa ba don ya tabbatar da gaskiyar abinda idonsa ya gane masa ya saka ya yi reverse ya kuma ƙare mata kallo.
Tabbas kamar ita Mimie ce amma ta ya za ta kasance Mimie bayan ta rasu tsawon shekaru uku da su ka wuce, kuma da hannunsa ya binne ta? Wannan sai dai idan wata ce mai kama da ita,amma kamar har ta ɓaci.
Alhj. Salman kenan shi ne ya ke ta wannan tunanin a lokacin da ya ga Zuhra don ta yi matuƙar kama da y'arsa da ya fi ƙauna wadda ta rasu.
Da wannan tunanin ya saukar da gilashin motarsa ya ce "Assalamu alaikum y'an mata."
Suka amsa da "Wa'ailaikumus salam."
Ya dube su ya ce "Idan ba damuwa ku shigo na rage ma ku hanya."
Har su na haɗa baki gurin faɗar
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 2 Chapter of 15