Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
wata Alhamis suka je Bk ita da Sameer da kuma twins, direban Daddy ne ya kai su. Gidan Innarmu suka sauka, domin Mimie bata da wanda ya wuce Innarmu a Bk, su kaɗai tasani. Innarmu ta yi murna da ganin jikokin nata yanda suka yi kyau abinsu. A can Mimie ta riski labarai kala-kala masu daɗi da akasin haka. Ko da ta je ta tarar an aurar da Shamsiyya ga wani magidanci mai shekaru arba'in, wata biyar kenan da auren, itama Sakina ana gaf da aurenta. Washe garin Ranar da suka sauka, suka je Jami'a domin yin abinda ya kawo su, kuma sun samu abinda suke neman, don haka suka juyo zuwa gidan Innarmu lokacin yamma ta riga ta yi. Suna dawowa hutawa kawai ta yi ta ci abinci, Sakina ta raka ta gidan Shamsiyya don ta ganta. Sosai Shamsiyya ta yi murnar ganin Mimie da ƴaƴan yayanta. Mimie kuwa har da ƙwallarta don ganin irin taskun da Shamsiyya ke ciki. Babban gida ne irin na family ɗinnan, mijinta ya na da mata biyu ita ce ta, gashi da ƙanne 'yan mata da kuma yaya matasa, sosai ƙannen mijin da kishiyoyi suke takura mata, cin mutunci har irin wanda bata san da shi a duniya ba yi mata suke, ga aiki da ake jibga mata kamar jaka. Ganin wannan halin da Shamsiyya ke ciki ya tunawa Mimie rayuwar aurenta da ta yi a baya, da yanda Shamsiyyar ta takura ta, tabbas Allah ba azzalumin sarki ba ne, domin ga shi ya saka mata ta wannan hanyar duk da ta riga ta yafe har cikin zuciyarta. Kallon Shamsiyya ta yi ta ce "ke kuwa Shamsiyya a haka kike jure zama da waɗannan mutanen?" Nan fa Shamsiyya ta fashe da kuka ta na faɗar "Ki yahe min Anty Mimie, na san sakamakon abinda na shuka ne na ke girba, a baya na wulaƙanta ki yau gani ƙannen miji suna walaƙanta ni na kasa yin komi, wannan ishara ce ga masu hali irin nawa, don Allah ki yahe min." Zancenta ya sanyayyarwa da Mimie jiki, duk sai ta bata tausayi don haka ta ce "Da ma ni tuni na yafe muku, Allah ya yaye miki damuwarki." Ba su suka baro gidan Shamsiyya ba sai bayan magriba. A hanyarsu ta dawowa ne Mimie ke tambayar Sakina labarin Zinnira. Sai da ta ja dogon numfashi ta sauke, sannan ta shiga bata labarin yanda rayuwa ta dawowa Zinnira da halin da take ciki na rashin lafiya ita da mahaifiyarta. Ta tausaya masu matuƙa don haka ta dubi Sakinan ta ce "Gobe ki shirya da wuri kafin mu wuce sai ki raka mu, mu dubo su." Da to ta amsa haka suka cigaba da hirarsu, Sakina ta na goye da Affan a bayanta har suka isa gida. Washe gari tun ƙarfe takwas suka shirya tare da shiga motarsu driver ya ja, Sakina na nuna masa hanya har suka isa gidansu Zinnira. Da sallamarsu suka shiga gidan, tun a ƙofar shiga ɗakin Mimie ta toshe hancinta, saboda wani ɗoyin bala'i da ya daki hancinta. Su na shiga suka same su akwance ita da mahaifiyarta, kallo ɗaya zaka musu ka fahimci su na cikin wani hali na azabar ciwo da raɗaɗi, jikinsu duk wasu marurai ne sun ja ruwa sun cika fam, wasu ma sun farfashe har da tsutsotsi ke zazzaga ta wani ɓangaren. Ɗakinsu kuwa ba komai sai ledar ƙasa da alama komai nasu ya ƙare garin neman magani. "Sannu Mama ya jiki?" Suka faɗa a tare Kai kawai ta ɗaga masu. "Sannu Zinnira." Mimie ta faɗa cikin tausayawa hawaye na gangaro mata. Daƙyar Sameer ya iya buɗar baki ya gaida su, sai alla-alla yake a tashi a tafi, domin cikinsa ya fara hautsinawa saboda a zaɓar ɗoyin ruwan maruran. Daƙyar Zinnira ta yunƙura zaune, tare da sakin wata ƙarar azaba saboda fashewar wani maruru a lokacin da take zama. Kallon Mimie ta yi idonta na zubar da hawaye ta ce "Don Allah ki yahe muna Anty Mimie, na san wannan ciwon shine ajalin mu nida innata, domin muna girbar sakamakon abinda muka shuka ne." Shiru ta ɗan yi na wani lokaci kafin ta cigaba "Mu at silar lalacewar farincikin rayuwar aurenki a gidan Bassam, duk abinda su Innarmu ka miki bayin kansu na ba, aikin sihiri na, wanda mu munka ƙulla shi don a hidda ke daga gidan ni in shiga, shi ma Bassam mu munka tahi wurin boka munka sa ya raba soyayyarku, sannan mun saci kuɗɗinai, waɗanda duk rabinsu naki na, amma a yau babu ko sisi duk sun ƙare wurin neman magani." Ta na gama faɗa ta fashe ta kukan nadama, tana ƙara neman yafiya a gun Mimie. Mimie ta tausaya masu matuƙa cikin kuka take faɗar "Na yafe maku duk abinda kuka mun na yafe, sai dai wannan ya zama ishara gareku, domin Allah ba ya yafe haƙƙin wani, kuma ya na karɓar addu'ar wanda aka zalunta, yau wa gari ya waya? Ni na yi aure na samu wani mijin wanda ya fi Bassam kamar yanda kika gani ke kuma fa?." Ta ƙarashe zancen ta na kallon Zinnira. "Na yi hasara, na cuci kaina." Zinnira ta faɗa cikin kuka. Kuɗi ta ciro a jaka bandir ɗin ɗari biyar, ta ajiye a gaban Zinnira ta ce "Ga wannan ku siyi magani." Daga haka suka miƙe suka fice, dama tuni Sameer ya bar gidan ya koma mota, saboda ba zai iya jure wannan azabar ba. A mota Mimie ta sha kukanta, dama can kuka baya mata wuya. "Allah sarki rayuwa! Allah kenan, sarki buwayi gagara misali ikonsa ya na kan komai, wai yau ni ce maƙiyana a baya suke kuka su na roƙon gafarata?, gaskiyar 'yan magana da suka ce mai haƙuri kan dafa dutse har ya sha romonsa." Mimie ce ke wannan tunanin a fili kuwa cewa ta yi "Kai! Allah ya raba mu da aikin danasani." Sameer ya amsa da Amin. Su na isa kalgo suka ajiye Sakina, ta yiwa Innarmu Sallama tare da ɗaukar kayanta ta fito waje gun mota. Har bakin mota Innarmu ta raka ta, ta na ta yiwa Sameer godiyar riƙe mata jikokinta da ya yi da amana, tare da masu addu'ar samun zaman lafiya mai ɗorewa. "Ai duk mai son Uwa dole ya so ƴaƴanta." Ya faɗa tare da ciro kuɗi a aljihun wandonsa ya miƙa mata. Ta karɓa ta na godiya. Suka yi Sallama suka hau mota sai Abuja. Bayan wani ɗan lokaci da dawowarsu daga Bk, ta koma bakin karatunta, yayin da Sameer ya ke zaune a gida zaman jiran aiki. ©©©©© Bangaren Mommy kuwa zaman Ruma a gida ya fara damunta, yanzu kimanin wata biyu kenan ta na zaune a gida amma bai zo ya maida matarsa ba, don haka ta shirya ta je gidan Hajiya hafsat domin ta raka ta gidan malaminsu a mata aikin da Saheen zai maida Ruma ɗakinta. Bayan sun je ne ta kokawa malamin nasu cewa wancan asirin da ya masu ya karye, kuma duk ɗan abinda ta samu daga hannun sirikin nata ta cinye, ga shi ya daina bata abinsa, har ma da guzurin saki ya haɗo 'yarta da shi. A nan malamin malamin tsibbun nasu ke mata bayanin sai dai ta yi haƙuri, domin yanzu akwai tsari sosai a jikin ahalin gidan gaba ɗayansu, ba wanda za su iya taɓawa. Nan fa suka yi cin mutunci tsakaninta da malamin, ta gaggaya mai maganganu, wai ya ci kuɗinta a banza, dama yasan aikinsa ba mai garantee bane don haka bata yafe ba, har da ce masa ɗan akuya, shi ko ya ce ta je za ta gani. Haka suka baro ƙauyen da yake, Hajiya hafsat na cike da tsoro, domin kalaman malamin nata sun ruɗar mata da ciki, ta san shi sarai zai iya yin komai akan wannan maganar, sai ƙirjinta ke harbawa da ƙarfi dama kuma ita ke tuƙi, su na shigowa garin Abuja kan babban titi motar ta ƙwace mata. Tun daga nan ba su kuma sanin inda kansu ya ke ba sai farkawa suka yi suka gansu a asibiti. Ko da labari ya riski Ruma hankalinta ya tashi matuƙa, da kukanta ta isa asibiti don ganin halin da Mommynta ke ciki. A asibitin ne ta kira Abbanta ta shaida masa, haka ta kira su yaya Sunil da Suhail, daga makaranta suka wuce asibitin don ganin Mommynsu. Abbansu ma washe gari ya zo. Su ma iyalan gidan Alhaji Salman sun girgiza, mussanman Mimie duk ta fi su shiga damuwa. Kowa na gidan ya damu inka ɗauke Saheen domin shi kam, ko a kwalar rigarsa. Washe garin ranar da suka samu labarin, da yamma suka je asibiti don dubiya a can suka tarar da Abban Ruma, anan ne kuma asirin Mommy ya tonu, domin Abban Ruma ya tambayi dalilin fitar da ta yi ba tare da saninsa ba har hakan ta faru. A nan Hajiya hafsat ta fallasa asirin duk wata badaƙala da ƙulle-ƙullen da suka yi tare, ta kuma roƙi gafarar Alhaji Salman da iyalansa. Abban Ruma ya ji zafi da raɗaɗin wannan abu matuƙa, take a gurin ya sake ta saki ɗaya, domin a cewarsa ba zai zauna da mushrika ba. Ya na sakinta ya juya abinsa, a ranar ma ya bar garin. Ƴaƴanta sun yi kuka har sun gode Allah. Mimie ta kira Mamanta ta na kuka, ta shaida mata halin da ƙanwarta ke ciki. Mama ta tausayawa ƙanwar tata matuƙa, don haka ta shaidawa Mimie zuwa jibi za su zo Abujan ita da Baba insha'allah, daga nan ma sai su ga ɗakinta. Bayan kwana biyu Mama da Baba suka zo Abuja, har lokacin Mommy na asibiti domin ta samu gocewar ƙashi a wasu gaɓɓanta. A wannan zuwa nasu ne komai ya dai-daita, a nan asibitin Mommy ta nemi yafiyarsu, cikin Sa'a kuwa dukkan su suka yafe mata, komai ya wuce kamar bai faru ba. Mama ta shirya da 'yar uwarta suka dawo kamar da. Bayan kwana biyu suka koma Kano. Mommy kuwa ta cigaba da jinyarta yayin da Ruma ke kula da ita. A cikin zaman jinyan da take ne wata rana Saheen ya zo har asibitin ya duba jikin Mommy, ya kuma ce ya mayar da aurensa da Ruma. Nan Mommy ta nemi ya fiyarsa ya kuma yafe mata. Bayan wani dogon lokaci aka sallame ta daga asibitin ta koma gida. Tun daga lokacin Mommy ta tuba, ta koma ga Allah ta na rokon gafararsa na shirkar da ta aikata a baya. @©©©© Mimie kuwa ta ci gaba da karatunta cikin kwanciyar hankali da nutsuwa yanzu ba ta da sauran wata damuwa, duk matsalolinta sun kau, tsakaninta da mijinta kuwa sai son Barka. Bayan shekara ɗaya Sameer ya samu aiki a ƙasar Dubai, don haka ya fara shirye-shiryen tafiya, amma ita Mimie a nan Abuja zai bar ta har ta kammala karatunta, wanda ya rage saura Shekara ɗaya. Twins kuma yanzu shekarunsu biyu, sun yi wayo abinsu har su na magana da gudu a ko'ina. A ranar wata Laraba Sameer ya yi Sallama da iyayensa da 'yan uwansa domin a ranar ne jirginsu zai cira zuwa Dubai. Bayan tafiyarsa Mimie ta sha kuka, domin ganin take kamar ba zai dawo ba, tunawa ta yi da lokacin da suka rabu da Bassam lafiya ƙalau, cikin ƙaunar juna sai gashi an dawo mata da shi cikin wani mawuyacin hali kuma ya mutu a gaban idonta, wannan abun ya tsaya mata a rai sosai, duk lokacin da ta tuna shi, sai ta zubar da ƙwalla tare da masa addu'ar samun gafara. To yau ɗin ma haka ne a bayyane ta ce "Allah ya jikan ka, Uncle, Allah ya maka rahama uban ƴaƴana, ka tafi ka bar ni da marayun ƴaƴanka, a yau wanda ke kulawa da su ma ya tafi, banda tabbacin sake haɗuwa da shi.." ta faɗa ta na rushewa da wani sabon kukan...... Follow me on wattpad @ummu inteesar RUKY I LAWAL CE🌹🌹🌹 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *A SANADIN KAMA* 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *DAGA ALƘALAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)* *MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH* *Y'AR GANTALI* *RIKICIN MASOYA* DA KUMA *A SANADIN KAMA* WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE AKAN NAIRA 200 KACAL GA MAI BUƘATA SAI YA TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER 08109634202 DON ALLAH IDAN KA SIYA KADA KA FITARMIN HAƘƘIN MALAKA NAWA NE *AREWA WRITERS ASSOCIATION* ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com *BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM* Page 7️⃣7️⃣↪️7️⃣8️⃣ 🔚🔚🔚🔚🔚🔚 Bayan tafiyar Sameer da kamar sati uku Mimie ta fara laulayi, ashe ko da Sameer ya tafi ta na da ciki wata ɗaya, sai dai duk a cikinsu ba wanda ya lura, sai yanzu ne ta lura da hakan, amma sai ta yi gum da bakinta bata faɗawa kowa ba, har shi Sameer ɗin gudun kada ɗoki ya sa ya kasa gudanar da aikinsa cikin nutsuwa. ©©©©©© A Dubai kuwa Sameer ya na gudanar da aikinsa cikin ƙwarewa da jajircewa, ya bada himma sosai ga aikinsa, domin yanzu zaman Dubai ya na masa daɗi ba kamar da ba. A yanzu ba yada damuwar komai, kullum ya kan yi waya da ahalinsa da kuma matarsa. ©©©©©© A bangaren Mimie kuwa ta ci gaba da renon cikinta da kuma tagwayenta ba tare da ta nuna gazawa ba. Mamy ce ta lura da yanda yanayin Mimien ya canza, abinka da manyan mata nan da nan ta fahimci cewa Mimie tana da ciki. A nan fa Mamy ke cewa "y'ata ko dai mun samu ƙaruwa ne?" Da murmushi a fuskarta ta ɗan dubi Mamy ta ce "Ta me fa Mamyna?" Ba wai don Mimie bata gane ba ne ta yi wa Mamy wannan tambayar, a'a sai dai don ta na tsananin jin kunyarta ne. 'Yar dariya Mamy ta yi ta ce "Yata kenan, ina nufin ko kina da ciki ne?" Ba ta amsa tambayar Mamyn ba sai ma sunkuyar da kanta ƙasa da ta yi, a nan Mamy ta fahimci hasashen ta ya zama gaskiya. Cikin matuƙar jin daɗi ta ce "Masha'allah! Allah ya nuna mana lokacin fitowar wannan Babyn lafiya, wannan daddaɗan labari ne, kin gayawa Sam kuwa?." Gyaɗa kai ta yi alamar a'a. Mamy ta ce "No wonder, shiyasa ban ga ya fara zumuɗi ba, ai ko ya kamata ya sani." Sai lokacin Mimie ta ce "Mamy na san halin Yaya Sameer ne, yanzun ana gaya masa, zumuɗi zai hana shi gudanar da aikinsa cikin nutsuwa shiyasa na yi shiru." Daga haka suka ajiye wannan maganar suka zaro wata chapter. A taƙaice dai Sameer bai samu labarin cikin Mimie ba sai da cikin ya kai wata biyar, a nan ma ba faɗa masa ta yi ba, shine ya lura da hakan lokacin da suke vidio call. Shine ya ke tambayar "Sweetyna yaya kodai mun samu ƙaruwa ne?" Bata ce komai ba sai murmushi da ta yi, a nan ya tabbatar da zarginsa, ai kuwa ya hau murna, farincikinsa ya kasa ɓuya. Tun daga ranar baya da aiki sai jibgowa Babynsa kaya, komai ya gani mai kyau na jarirai sai ya siyi wanda zai yi dai-dai da sawar maza ko mata ya ajiye, daga wannan ranar ne kuma ya fara irgen watannin da suka rage na haihuwa sai zumuɗi ya ke. Lokacin da cikin Mimie ya shiga wata na tara, Sameer kasa haƙuri ya yi har sai ta haihu sannan ya koma Nigeria, don haka ya harhaɗa kayansa ya dawo Nigeria zaman jiran Babynsa. A ranar da cikinta ya cika wata tara da sati biyu, ta haifi 'yarta ƙatuwa masha'allah. Sameer ya yi matuƙar farinciki da haihuwar nan, da yake a asibiti ne ta haihu, su Mommy da Ruma sai Mamy sune tare da ita a ɗakin bayan an gama shirya su ita da jaririyarta. Sameer ne ya shigo ɗakin fuskarsa cike da annuri, ba ya da burin da ya wuce ya ga fuskar 'yarsa. Cikin hanzari ya isa gun Mamy dake riƙe da 'yar a hannunta, ya miƙa mata hannu, ba ko kunya ya ce "Mamyna miƙo mun 'yata naji ɗuminta." Harararsa Mamy ta yi, ta nuna masa Mommy dake zaune a gun da ido, alamar ya gaida ta. Amma inah! Shi yanzu ba Gaisuwar ba ce a gabansa, 'yarsa yake muradin ji a tafin hannunsa, don haka ya yi mirsisi. Ita ko Mamy ganin ya yi kunnen uwar shegu da nuninta sannan yaƙi janye hannunsa, ya sa ta haƙura ta miƙa masa 'yar tana mai jin kunya, "yayan zamani basu da kitsen ido." Ta faɗa a ranta. Cikin azama ya karɓi 'yar ya rungume ta tsam a ƙirjinsa, sai ko ga hawaye shaaa! Faɗar ya ke "Alhamdulillah! Allah abin godiya, ashe ina da rabon ganin wannan 'yar" Matsawa kusa da Mimie da ta fito daga toilet ɗin ɗakin ya yi ya na faɗar "Sweety ashe da rabo a tsakaninmu? Ashe rabon wannan 'yar ne ya saka na nacewa soyayyarki? Shi kenan yanzu mun kuma zama jini da tsoka, dama can kina a cikin ahalinmu." Da alama ya ma manta da mutane a ɗakin. Ganin haka ya saka Mamy da Mommy suka bar masu dakin, Mamy na sharar ƙwallar tausayi, saboda tunawa da ta yi da rayuwar da ɗan nata ya shiga a baya. Tun a asibitin Sameer ya yiwa 'yarsa huɗuba da sunan *Rukayya* wato sunan ƙanwarsa Margayiya Real Mimie ta ci, za su dinga kiranta da Little Mimie. Bayan Mimie ta huta sosai aka sallame ta daga asibitin suka koma gida. Tun ranar da ta haihu Mommy ta tare a gidan, domin acewarta ita ce za ta kula da 'yarta da kanta kafin ƙarasowar mutan Kano, da yake har lokacin Abbansu Ruma bai sauko ba bare ya mayar da aurensa. Ana saura kwana uku suna 'yan Kano suka zo. Ranar suna aka yi shagali sosai, Naira ta yi kuka domin kam an kasheta a sunan 'yar gata, a gurin zanen sunan ma maroƙa sun yagi rabonsu. A wannan ranar gaba ɗaya iyalan gidan alhaji Salman su na cike da tsantsan farin ciki, kuma sun yiwa Allah godiya da ya dawo masu da walwalarsu a lokacin da basu yi tsammani ba. Da farko ya aiko masu Zuhra a matsayin wacce za ta zama jagoran dawo masu da sumammen farincikinsu, yanzu kuma ya azurta su da samun 'yar da take kama sak da Mimiensu daga tsatsonta, 'yar kuma da ba su da a familynsu, ba abinda za su ce sai dai su ƙara godewa mahaliccin bayi mai jinƙai da Rahama ga bayinsa. Bayan watse taron suna da kamar sati biyu, Daddy ya yi-ya yi Sameer ya koma bakin aikinsa amma ya ƙi, ya kafe shi lallai ba inda zai je sai tare da matarsa. Mamy kuwa ta yi tsayin daka akan cewa ba inda zai je da Mimie har sai ta yi kwana tamanin da haihuwa don haka ya je kawai. Wasa-wasa ƙaramar magana ta zama babba domin yanzu kusan wata ɗaya kenan amma Sameer ya ƙi ya koma, daga gun aikin nasa ma sai kiransa ake a na buƙatar ya dawo amma ya ƙi. Ganin haka ya saka watarana da yamma Daddy ya sami Mamy akan maganar, ya ce "Mamyn yara, ki yi haƙuri ki bawa Sam matarsa ya tattara ya tafi, domin wannan al'ada ce ba fa addini ba, kuma ma ai ta yi arba'in ɗaya, idan ma baki amince da hakan ba, sai Mommynta ta shirya su tafi tare hakan zai fi mana kwanciyar hankali." Da farko Mamy ta so ta yi gardama, amma kasancewar wannan ba dabi'arta ba ce yin musu da maigidanta, don haka ta haƙura ta ce "Shikenan Alhaji tun da ka faɗi haka, sai a nemawa Mommyn nasu visa ta bi su can, tun da ma ai batada miji a yanzu." Da wannan shawarar suka kawo karshen maganar tafiyar, kowa ya fice zuwa yin sabgar gabansa. Da dare Mamy ta kira Sameer ta shaida masa shawarar da suka yanke ita da Daddynsa. Bai Musa ba, saboda shi ma zai so matarsa da 'yarsa su samu kulawar da ta dace a wannan stage ɗin, wanda shi ba zai samu damar yin hakan ba saboda aikinsa. "Nagode Mamy Allah ya ƙara girma, sai a gayawa Mommyn ta shirya da wuri koh?" Ya na gama faɗa ya miƙe don zuwa makwancinsa. Alhaji Salman da kansa ya nemarwa Mommy visar, ta kuwa shirya tsaf, bayan sati biyu ta yi Sallama da ƴaƴanta ta bi su ƙasar Dubai. Da yake zuwa lokacin Mimie ta kammala digirinta, ta yi komai ta haɗa takardunta kawai ta bi mijinta ƙasar Dubai. %©©©© Bayan saukarsu a Dubai, Rayuwa mai daɗi suka shimfiɗa cike da so da ƙaunar juna, ganin twins sun yi baki sosai domin yanzu shekarunsu uku, hakan ya saka Sameer ya nemo masu makarantar nursery mafi kusa da gidansa a can, ya saka su. Bayan wani ɗan lokaci, Mimie ta shiga jami'ar da ya kammala, don yin masters ɗinta A nan. Su Mommy an zama mutanen Dubai sai shanawa take abinta, a zaune take ta na tunani "Allah karimun, yau gata a cikin dukiyar Alhaji Salman ko ta ce ta ɗansa ta na watayawa yanda ta so, tabbas da ta san da zuwan wannan ranar da ba ta yi gangancin faɗawa shirka ba, ashe gajin haƙuri ta yi, ta fitar da maitarta a fili, ashe wannan lokacin da take fata har ta kauce hanya akansa zai zo mata cikin sauƙi da ta kwantar da hankalinta. "Astagfurullah! Astagfurullah!! Allah ka yafe mun haƙiƙa a baya ina cikin ɓata mabayyaniya." Ta faɗa a fili. ©©©©©%%% Bayan kamar wata uku da komawarsu Dubai wani tashin hankali ya Kunno Kai acikin rayuwarsu. Bakomai ba ne ya ɗaga hankalin dukkanninsu face rashin lafiyar Sameer, a hankali ciwon ya fara shigar shi, abun ya fara mai da yawan kasala, wasa wasa ciwo sai daɗa gaba ya ke, domin yau kusan satinsa biyu kenan ba ya fita aiki, sai dai ya ba da uzurinsa akan cewa ba shi da lafiya ne. Duk da cewa a zahirin gaskiya ba wannan ne karo na farko da Sameer ya fara fuskantar irin wannan matsalar ba, tun bayan tafiyarsa Dubai a karo na biyu bayan aurensu kenan ya fara jin wannan yanayin, sai dai a tunaninsa ko gajiyar aiki ce da sauran abubuwan da ba a rasa ba. Amma zuwa yanzu ya tabbatarwa kansa cewa akwai wata cutar da take addabarsa, don haka ya yanke shawarar zuwa ganin likita. Ya na daga kwance kan gadonsa ya kalli Mimie dake zaune a gefensa ta na sharar hawaye ya ce "Ki daina kuka Sweety, cuta fa ba mutuwa ba ce, yanzu dai dauko wayata ki kira mun Abokina doctor Sadeeq, ki ce na ce ya zo ya kai ni asibiti." Ya ƙarashe maganar daƙyar da alama ya na shan wuya sosai. Hawayenta sun kasa tsayawa, bata iya cewa komai ba, sai janyo waya da ta yi ta dannawa doctor Sadeeq kira. Bugu biyu ana uku ya ɗaga, ta shaida masa saƙon abokinsa, cikin hanzari ya fito daga asibitin ya nufo gidan Sameer. Ganin yanayin Sameer ɗin ya ruɗar da shi saboda haka ba jinkiri ya saka shi a mota, Mimie ma ta faɗa motar hankali a tashe, Sadeeq ya tada motar cikin hanzari ya nufi asibitinsu. Yayinda suka bar Mommy a gida ita da yara sai masu aikin gidan. Gwaje-gwaje da aune-aune aka hau yi masa, sannan aka shiga ba shi agajin gaggawa, kafin fitowar sakamakon binciken. Hankalin Mimie a tashe yake ta kasa tsaye ta kasa zaune, sai zarya take a harabar asibitin ta na kuka, gani take kamar za ta rasa shi kamar yanda ta rasa Bassam a rana mai kamar ta yau. Bayan wani lokaci sakamakon gwaji ya fito nan take aka gano cutar hapatatis a jikinsa(wato ciwon Anta) a nan doctor Sadeeq yake mata bayanin hakan ta faru da shi ne sakamakon shan giya da ya ɗau lokaci ya na yi a baya. Hankalin Mimie idan ya yi dubu ya tashi, miƙewa ta yi daga kan kujerar office ɗin da take zaune, ta fara kai-kawo a filin ɗakin ta na kuka, doctor na ƙoƙarin mata bayanin mafita amma ina! Bata saurare shi ba sai ci gaba da kukanta ta ke ta na faɗar faɗar "Shikenan, yanzu kai ma yaya Sameer haka zan rasa ka kamar yanda na rasa Uncle? A baya na rasa uban ƴaƴana, yanzu kuma zan rasa wanda ya tarairaye su kamar ƴaƴan cikinsa, kuma zan rasa uban 'yata a karo na biyu? Ka da ka mutu kabarni a ƙasar da ba ni da kowa sai kai da ƴaƴana, Ya Ubangijina kada ka ɗora min ƙaddara da ba zan iya cinyewa...." Kuka ne ya ci ƙarfinta ta kasa ƙarasawa sai komawa da ta yi ta zauna a inda ta tashi daga farko. Anan doctor Sadeeq ya shiga rarrashinta, daƙyar ya ciwo kanta da kalaman tausasa zuciya domin ya tausaya mata matuƙa. A nan ya tabbatar mata cewa akwai mafita, mafitar kuwa ita ce a yanzu za'a ɗora shi akan magani domin cutar bata riga ta yi nisa ba, idan ya shanye maganin bai ji sauƙi ba za'a masa aiki. Ta ɗan nutsu amma ba don hankalinta ya kwanta ba, ranar a asibitin ta kwana, duk da doctor Sadeeq ya shaida mata su na masu kula da mara

Chapter 14 of 15