shigo in gan ta ko na ji sauƙi."
Shiru ba wanda ya tamkasa duk sun yi jugum-jugum dasu.
Dawowa ya yi kusa da Mamyn ya zauna ya na kuka kamar wani ƙaramin yaro, acikin kukan ya ke cewa "Mamy ku gayawa y'arku Allah ina son ta, idan ban aure ta ba zan iya mut..tuwa ma, kawai ku aura min ita zan daina abunda nake na rantse."
Ya na gama zancen ya langaɓar dakai kan cinyar Mamynsa, kai daga ganin yanayinsa ba sai anga yama a buge yake ba.
Daddy ne ya miƙe ya je pridge ya ɗauko gwangwani madara ya hude, ɗaga bakin Sameer ɗin ya yi ya tsiyaye masa, ba musu ya shanye ta tas.
Shanyewarsa ke da wuya barci ya yi awon gaba da shi.
Ɗora shi suka yi akan three-sitter sa'annan suka gyara masa kwanciyarsa, Mamy ta miƙe jiki a saɓule ta shiga gyaran falon da ya yi dagaja-dagaja da datti yayin da Daddy ya fita harabar gidan cike da damuwa.
Bayan dawowarsa cikin hayyacinsa ne suka saka shi gaba da faɗa, su na yi masa nasiha a kan rayuwa tare da tsorartar da shi daga azabar Allah.
Cikin kuka ya ke ba su haƙuri tare da jaddada masu cewa shima ba laifinsa bane damuwa ce ta masa yawa da kuma zugar mugayen abokanansa da suka ɗora shi a kan hanyar da bata ɓullewa.
To dama an ce tsakanin ɗa da mahaifi sai Allah, nan take suka yafe masa tare da jaddada masa ba za su bar shi a nan ba, domin idan su ka bar shi ba susan wane hali zai shiga ba, bayan shaye-shaye da neman mata da yake.
Anan ya rantse masu a kan baya neman mata shaye-shayen ma ƙaddara ce ta saka.
©©©©©©©™™™™
Mimie na cikin wannan halin ne, Cikin iyawar Allah wata rana sai ta tashi da laulayi sai amaye-amaye take, komai ta ci sai ya dawo mata, nan take Innarmu ta fahimci ciki ne da ita.
A can cikin zuciyarta ta na farin ciki za ta samu jika amma a fili sai ta nuna rashin damuwa, domin zahiri soyayyar Zinnira ta mamaye zuciyar Innarmu(ko da yake aikin asiri ne) da yake shekara ɗaya baya kenan da Bassam ya auri Zinnira sai dai ba'a ƙauyen take zaune ba, ta na birni gidan da ya yi burin rayuwa da Mimiensa a ciki, anan a ka kai ta domin tun da lokacin bikin nasu ya ƙaraso ya sallami y'an haya ya sake gyara gidan tsaf don sanya amaryarsa.
Bayan auren ba irin rawar kan da su Shamsiyya ba su nuna ba, baƙar magana da habaici kam ta sha su, a ranar da za a kai amarya gidan ya cika maƙil da y'an biki, Mimie ce ta zo wucewa cikin dakakkiyar shaddarta bowa sai ƙamshi ta ke zubawa.
Sakina ce ta dubi Shamsiyya tare da yin karaf ta ce "Yaaya irin wagga kwalliya haka sai ina? Lallai babu laihi shaddakki mai tcada ta, sai dai matsalat baki gaban mijinki don ko ganin ki bai son yi, yau ya ɗauki sabuwar amarya dal, ba irinki ba da kit tsuhwa tun baki da ko ɗa guda ba."
A take y'an matan dake wajen suka bushe da dariya.
Shamsiyya ma dariyar ta yi ta ce "Ke dai bari ƙaunata, dole ki ga na ɗauki irin wanga wanka, kin san ɗiyar masu arziƙi nike, ga shi kuma dadirona babban sanata na ko uwayena basu turomin kuɗɗi ba shi ya na turo min..."
Ran Mimie ne ya yi mugun ɓaci da jin zancenta, duk haƙuri irin na Mimie ranar kam sai da su ka kai ta bango, idonta ne ya rufe har bata san lokacin da ta ƙaraso gun ta wanke Shamsiyya da mari ba, ji kake tas, tas, tas, ta wanke ta da lafiyayyun mari har guda uku.
Cikin firgici Shamsiyya ta miƙe zumɓur dafe da kunci ta na neman wanda ya mata wannan marin da sai da ta ga taurarin wuya.
Ido huɗu suka yi da Mimie ta na huci kamar zakanya, ta nuna Shamsiyyan da yatsa ta na faɗar "Ke ƙaramar y'ar iska, idan kina cin ƙasa ki kiyayi ta shuri, shiru-shiru fa ba tsoro ba ne, daina ganin duk abinda kuke na saka maku ido, zan iya jure ko wanne wulaƙanci da duk abinda za ku min, amma ban da zagin iyayena, mussanman mutumin da ya zame mini gata, ya ke goyon bayana acikin kowanne yanayi, ba zan taɓa jurar na ga ana cin mutuncinsa ba a gabana na yi shiru, a baya kin yi na ƙyale ki amma na fahimci ba ku san zuru ba, to duk wacce ta kai shegiya ta kuma gwada zagin Daddyna ta gani."
Ta na gama faɗa ta yi fuu ta bar gun cikin ƙonar zuciya ta shige ɗakinta tare da banko ƙofa, ta faɗa kan kujera tana kuka mai cin rai.
®®®®®©
A can waje kuwa har bayan mintuna biyar Shamsiyya bata dawo a hayyacinta ba, ta kaɗu iya kaɗuwa, "Ashe dama Mimie ta iya rashin mutunci haka? Ita dai tun zaman su da ita tsayin shekaru uku kenan bata taɓa jin ta faɗawa wani baƙar magana ba bare ta tada murya sai yau.
Sakina ma ta jijjiga da wannan al'amarin, cikinta ya ɗuri ruwa sosai, dai-dai lokacin ne inna ta fito ta na faɗar "Minana ka hwaruwa?, ina ɗaka nijjiyo hayaniya."
Anan y'an matan dake wajen su ka labarta mata.
Nan take ta hau ruwan bala'i, ta je ƙofar ɗakin Mimie ta na ta zazzagawa sauran mutan wajen su ka kama mata, ba su suka bar wajen ba sai da su ka lisafe mata haƙoranta tas sa'annan.
Ranar ta sha kuka kamar ba gobe, don duk ɗibar albarkar da suke ta na jin su, sauƙinta ɗaya yau ta samu ta fara ɗebe takaicinsu, da baƙin ciki ya karta a ránar.
Tun ranar yaran suke shakkar yi mata rashin mutunci.
Bayan tarewar amaryar Bassam ne suka tattara suka koma gidan da zama, ai kuwa sun ga rayuwa, domin a farko ta bi su lab-lab-lab komai yi masu ta ke lokacin da ta ke amarya, bayan kamar wata uku da auren, Zinnira ta fara sha masu ƙamshi ta na ɗaɗɗauke kai, irin ita ba sa'ar su ɗinnan ba ce, haka ma ba ta wani ganin girman Innarmu a zuciyarta, dama tun farko neman shiga ne yasa ta bita.
©©©©©©©©©
Abuja
A can Abuja kuwa tuni shirye-shiryen aure sun yi nisa tsakanin Ruma da Saheen, domin ita tausayinsa take ji ba da wasa ba, ta daɗe da gano cewa Mommynta asiri ta masa domin da kunnenta ta ji su lokacin da suke tattauna maganar a waya.
Wannan tausayin ne ya rikiɗe ya koma soyayya, don haka ta amince da auren, su ma su Daddy ba musu suka amince ganin cewa abun na gida ne duka.
Mommy kuwa kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha haka ta ji.
Lokacin da ya rage saura sati ɗaya bikin, Ruma ta saci hanya ta je gidan wata ƙawarta domin ta samu ta yi waya da Mimie da su Mama, don Mommy ta kasa ta tsare ta ce ba za'a sanar masu ba, sai dai su ji a dangin ango, ko su zo a matsayin dangin ango don sun fi ƙarfi can
®®©®®®®
Ko da Mimie ta samu labarin ta yi murna sosai, a nan ta kira Uncle ta sanar da shi, daƙyar ma ya ɗaga wayar don zuwa lokacin komai ya ƙara jagulewa tsakaninsu.
Ko da ya ɗaga ma bata samu amsar arziƙi ba don cewa ya yi "Ko Alhaji Salman ɗin ne ya koma saurayi za a yi aurensa ba za ta je ba, bare wani banzan ɗansa."
Ta ji ciwo sosai a ranta amma sai ta dake ta ce "Pls Uncle ko dan Ruma ka daure ka bar ni na je."
Nan fa ya fusata ya ce "Na ce ba za ki ba, ko da Hajiya khadija za a aurar ba Ruma ba, ke bari ki ji ƙarshen zance ko da Malam Habu bakanike da Malama A'isha mai ɗan wake ne su ka koma matasa za a aurar da su ba za ki je ba kin ji na gaya miki."
Sosai zagin nan ya mata ciwo nan take ta fashe da kuka tare da kashe wayar gaba ɗaya.
Haƙiƙa a yau da ba ta ɗauke da ruwan cikinsa, da a yau ɗin nan sai ta bar masa gidansa, ko da kuwa a ce idan ta je gida iyayenta za su koroto ne, ta gwammace ta shiga uwa duniya da ta zauna a na zagin iyayen da suka yi silar zuwanta duniya, kwata-kwata ma ita aurensa ya fice mata a rai, duk da idan ta ce ta daina son sa ita kanta ta san ƙarya take.
A ranar ta kira Babanta a waya ta saka mi shi kuka ta na neman gafararsa shi da mahaifiyarta....
Ga mai buƙata sai ya tuntuɓeni ta wannan number 08109634202
Follow me on wattpad @ummu inteesar
UMMU INTEESAR CE❤️❤️❤️❤️❤️
👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻
*A SANADIN KAMA*
👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻
*DAGA ALƘALAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*
*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y'AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
DA KUMA
*A SANADIN KAMA*
WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE AKAN NAIRA 200 KACAL
GA MAI BUƘATA SAI YA TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER 08109634202
DON ALLAH IDAN KA SIYA KADA KA FITARMIN HAƘƘIN MALAKA NAWA NE
*AREWA WRITERS ASSOCIATION*
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*
Page 6️⃣1️⃣↪️6️⃣2️⃣
A nan suka tabbatar mata da sun yafe mata, tare da yi mata addu'ar Allah ya yaye mata ƙuncin da ta ke ciki.
®®®©©©©
Shekara ɗaya kenan da auren Zinnira da Bassam amma ita ma ko ɓatan wata bata yi ba, haka ya saka innarmu cikin damuwa da alhini, har ta fara fitar da rai ga samun jika sai ga ɓullowar ciki a jikin Mimie.
Ga wani sabon salon iskanci da Zinnirar ta tsiro da shi, ko da Bassam ya zo gari sai ta hana shi zuwa Kalgo, da yake ta riga ta asirce shi ko kara ta ɗora baya tsallakawa, a haka ta gwaguye ɗan arziƙin da ya fara dawo masa ita da innarta mai shegen kwaɗayin abun duniya.
Su Sakina sun ga rayuwa domin zuwa lokacin Zinnirar da suke rawar ƙafa a kanta, ta saka yayansu ya masu korar kare daga gidan, bayan ta masu rashin mutunci ta zage su tas.
Da kukansu da hawayensu suka dawo gida, ko da Innarmu ta kira shi, hana shi ɗagawa ta yi, da Innarmu ta ga bai da niyyar ɗagawa sai ta kira Zinnira, nan fa Zinnirar ta dage ta cinyewa Innarmu mutunci tsaf, ko raga mata bata yi ba, don arziƙin zumuncin dake tsakanin innar da babanta, har da ce mata "tsohuwar banza, wacce take son lalata rayuwar ɗanta da kanta."
Ranar Innarmu ta ci kuka har ta bawa uku lada, ta yi nadamar yarda da ta yi aka haɗa kai da ita aka gurɓata rayuwar tilon ɗanta namiji.
Bayan ta gama kukanta ta kira innar Zinnira ta sanar da ita ɗibar albarkar da ta mata, maimakon ta bata haƙuri kawai sai ta bushe da dariya ta ce "Ta min dai-dai Lantana, ke dama tunaninki haka za mu ƙyale ki, mun dai gode miki da kika taimaka muna da kanki a ka mallake muna ɗanki, ga shi ke kanki mun raba ki da shi, yayan naki ma ko da ke hwaɗa mai baida abin yi don na gama da shi shi ma."
Ranar Innarmu ta yi nadama mara amfani, tare da tsinewa Hajiya Rabi(maman Zinnira) albarka.
©©©©©©®™™™™
Acikin shekara ɗaya da rabin, Zinnira ta tubure musu, ba irin cin kashin da bata masu, rashin mutunci sai wanda ta manta, ga shi har lokacin bata haihu ba.
A na tsaka da haka ne watarana Allah ya toni asirinta.
Bassam ya zo gida hutu kamar ko da yaushe, bayan ya fita gun abokanansa a cikin birnin, sai da yamma liƙis ya dawo, ya na shigowa ya tarad bata falon hakan ya sa kai tsaye ya nufi Bedroom ɗin su.
Cak ya tsaya a bakin ƙofa jin maganganun da take faɗa a waya.
Bakomai ya saka shi cin birki ba, sai don jin da ya yi ta na faɗar "Kai innata shiyyasa ni ka mugun son ki wallahi, ke san kan sheri, ke ga yanzu mun raba shi da uwatai da y'an uwa nai gaba ɗai, yanzu abu biyu yar-rage muna, mu samu a raba shi da shegiyar matan nan ta shi, don wallahi na tsane ta, dama na ɗaga mata ƙahwa na saboda azzikinta da muka ci, dan rabin kuɗɗinsa duk nata na shiyassa, amma yanzu anhwaninta ya ƙare, a sa ya saki y'ar banza."
Shiru ta yi alamun ta na sauraren abunda innarta ke faɗa, can kuma ta bushe da wata mahaukaciyar dariya ta ce "Kai inna! Wallahi ke ma hi ni mugunta, yanzu dai gobe ina nan shigowa gobe sai mu koma wurin boka Kokau, don ya cika muna ayyukan mu."
Nan ta ke hawaye suka fara gangarowa a idanunsa, ya saka hannu ya share.
Ita kuwa Madam ɗin bata ma ji shigowarsa ba, saboda hankalinta gaba ɗaya ya na kan wayar da ta ke da mahaifiyar ta.
Ta na kammala wayar ta juyo ta gan shi tsaye ya na bin ta da kallon tsana.
Hannu ta ɗora a kai tare da saka ihu, saboda tunawa da ta yi cewa boka ya ce duk ranar da suka bari wani ya ji wannan sirrin, ban da su da za su yi aikin tabbas asirin zai karye, musamman idan suka bari wanda a ke aikin a kansa ya ji ko ya gani to ba shakka suna cikin hatsari don bayan karyewar asirin, su jira bala'ukan da za su biyo baya a rayuwarsu.
Kuma a haka suka amince tsabar sun yi nisa basa jin kira.
Ihun ta ci gaba da yi tana kuka tare da riƙon gafararsa.
Kallonta ya yi cike da tsana sannan ya ce "Zinnira ko ban miki Allah ya isa ba, tabbas sai kin ga abinki, domin ko alhakin raba ni da mahaifiyata a ka bar ki da shi ba za ki iya ɗauka ba, ballantana har sakawa da kika yi na cutar da matata, amanata, tabbas sai kin ga abinki, ki je na sake ki saki biyu, kuma ba gyaran aure tsakaninmu."
Hankalinta ya kai ƙoluluwar tashi ihu kawai take ta na roƙonsa, amma ko sauraronta bai yi ba, ya bata umurnin ta tabbatar ta bar masa gidansa kafin ya dawo, daga haka ya fice ya bar mata gidan."
A ɗimauce ta nufi gidansu ta na kuka.
©©©©©©©©©©
Ita kuwa Mimie tun bayan da iyayenta suka tabbatar mata da yafiyar su agare ta, ta fara ganin haske a rayuwar aurenta domin an rage kyarar ta da hantarar ta da a ke a cikin gidan, sai dai har yanzu da sauran rina a kaba.
©©©©©©©©©©
Bayan wata tara, wata ranar lahadi da safe Mimie na kwance a ɗakinta ta na fama da ciwon mara mai tsanani.
Shamsiyya ce ta shigo ta tsaya a kanta ta na famar rafka mata kira amma saboda zafin ciwo ko jin ta bata yi ba.
Bata yi aune ba ta tsinto muryar Shamsiyya na faɗar "Ke! Wai ba ke aka kira tun ɗazu ba?,ki na ji ke ƙyale mutane, matsiyaciya kawai mai ƙaryar arziƙi."
Ita dai bata ce komai ba har ta zo ta wuce budurwar.
A hankali take takawa bayanta kamar zai tsage, (saboda cikin jikinta ya yi girma da yawa) a haka ta ƙarasa gun Innarmu dake zaune ta na ƙulla yaji ta ce "Inna gani.".
Wani kallon banza innar ta watsa mata sannan ta ce "To hitsararra na gan ki ai, da uwakki ta na san ba ki tsayawa kanta haka, amma da yake ni ke rena ni shiyassa kin ka wani tsaya ƙiƙam akaina."
Mimie dai ba ta ce komai ba, don in da sabo tuni ta saba da wannan cin mutuncin da mutan gidan ke mata, wai ma don yanzu abin ya yi sauƙi ne.
Innarmu ta kalle ta a gyatsine ta ce "Maza ki aza muna sanwa ga rana harta take kina ɗaki kwance, ke ga....."
Bata samu damar ƙarasawa ba saboda ƙarar da wayarta ƙirar Nokia ta yi.
Ɗaga wayar ta yi tare da ɗorawa a kunne.
Can ta ce "Eh ni ta."
Shiru ta ɗan yi can ta zabura tare da dafe ƙirji ta ce "Mee!?. Wane asibiti?, Wayyo Allah! ɗana Bassam."
Wayar hannunta ce ta suɓuce ta faɗi ƙasa, da sauri ta miƙe zuwa ɗakinta ta na kuka.
Mimie kuwa gabanta ne ya tsananta faɗuwa, "to me ya faru da mijinta ne ko hatsari yayi?"
Zuciyarta ta bijiro mata da wannan tunanin, tunowa da ta yi ya kira ta ɗazun ya sanar da ita yau zai dawo.
Daƙyar ta ɗaga ƙafarta ta bi bayan Innarmu don jin me ya faru.
A dai-dai lokacin da ta iso ƙofar ɗakin, ta jiyo muryar Innarmu na faɗar "Sakina yayanku ne ya yi haɗari, kan hanya tai ta dawowa gida, yanzu haka ya na asibitin binni rai ga hannun Allah, maza kira Shamsiyya ku taho mutahiya." Ta faɗa cikin kuka.
"Innalillahi wa inna'ilahir raji'un!
Bassam! Uncle! Mijina!"
Abunda ta iya furtawa kenan tuni ganinta ya ɗauke sai ji kake tim! Ta faɗi a kan cikinta.
Da gudu Innarmu ta ƙaraso gun tana salati cikin kuka ta ke faɗar "Innalillahi wa inna'ilahir raji'un!, Shamsiyya yi sauri ki kirawo babanku Isah ya taho da mota tai akai ta asibiti."
Ba musu Shamsiyya ta fice da gudu ta je ta kira sa, bayan kamar minti ashirin sai ga su, da gudu suka shigo gidan a ka cicciɓe ta tare da sakata mota.
Asibitin da a ka kai Bassam can suka nufa da ita, har zuwa lokacin bata dawo hayyacinta ba, don tun lokacin da ta faɗin ta suma.
Likitoci sun tabbatar masu da cewa dole sai an mata tieter, ba za ta iya haihuwa da kanta ba saboda ta jigata sosai.
Bayan an shigar da ita ɗakin tiater ne suka juya zuwa ɓangaren da Bassam ya ke, nan ma ba'a basu damar ganinsa ba saboda a lokacin likitoci ne suka duƙufa a kansa don ceto rayuwarsa.
Haka suka nemi guri suka zauna hankali a matuƙar tashe, duk sun yi jugum-jugum da su, kowannen su sai addu'a ya ke a ransa a kan Allah ya bawa majinyatan lafiya.
Bayan awa ɗaya aka kammala tieter, likita ya fito, nurses biyu mata su na biye da shi a baya a nan likitan ya yiwa Innarmu albishirin cewa an samu y'an biyu maza, daga haka ya wuce zuwa office ɗinsa.
Nurses ɗin ne suka nemi da a basu kayan da za su shirya jira-jiran da mahaifiyarsu a ciki, a nan suka sanar masu cewa sai an je annemo da ya ke ba fitar nutsuwa suka yo ba.
Innarmu ta ce da Sakina wadda ta kasance tare da ita agun "Yi sauri ki biya ta wurin su Babanku Isah, ki ce mai na ce ya kai ki gida ki ɗakko kayan haihuwa, idan kika je ki duba ɗakinta na san ba su rasa aje su."
Da "to." ta amsa, ta wuce a hanzarce, da yake sun baro shi tare da Shamsiyya a can ƙofar ɗakin da a ka kwantar da Bassam...
Ga mai buƙata sai ya tuntuɓeni ta wannan number 08109634202
Follow me on Wattpad @ummu inteesar
Vote share and comment
UMMU INTEESAR CE❤️❤️❤️
👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻
*A SANADIN KAMA*
👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻
*DAGA ALƘALAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*
*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y'AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
DA KUMA
*A SANADIN KAMA*
WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE AKAN NAIRA 200 KACAL
GA MAI BUƘATA SAI YA TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER 08109634202
DON ALLAH IDAN KA SIYA KADA KA FITARMIN HAƘƘIN MALAKA NAWA NE
*AREWA WRITERS ASSOCIATION*
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*
Page 6️⃣3️⃣↪️6️⃣4️⃣
Ƙarasa ta yi ta kira Baban suka wuce zuwa Kalgo don ɗauko kayan.
Bayan wucewar su a ka yiwa Shamsiyya izinin shiga ganinsa, sai da ta je ta kira Innarmu sannan suka shiga tare don duba lafiyarsa.
Kuka kam sun sha shi saboda ganin yanayin da Bassam ɗin ke ciki, wasu daga cikin gaɓoɓin jikinsa duk sun kakkarye, haƙiƙa ya na cikin zillah.
®®©©
Ɗaya daga cikin Nurses ɗin ce ta je ta samo madai-daitan towel guda biyu, ta naɗe jariran a ciki bayan angama shirya su, domin Allah ya jarafce ta da son 'yan biyu, mussanman identical twins(tagwaye masu kama da juna) shiyasa yaran suka shiga ranta sosai.
Bayan dawowar Sakina daga gida ne a ka shirya yaran a cikin kaya iri ɗaya, ita ma Mimien suka taimaka mata ta shirya, sai ga su sunyi ras abinsu.
©©©©©©
A can ɗakin da a ka kwantar da Bassam, Innarmu ce ta matso daf da shi ta na kuka ta na roƙa masa lafiya a gun mai kowa da komai.
Ko waye kai idan ka ga halin da Bassam ya shiga dole ka zubar masa da ƙwalla matuƙar ka na da imani.
Buɗe idonsa ya yi ya fara rarraba su ko'ina na cikin ɗakin, alamar ya na neman wani abu, can ya dawo da dubansa a kan innar, daƙyar ya buɗi baki ya ce "Innarmu ina matata?"
Cikin yanayin damuwar da take ta bashi amsa da cewa "Tana nan asibitin, bata jima da haihuwa ba."
Tun da ta fara maganar ya ke kallon ta don jin me ya kawo matarsa asibiti, bayan ta dire zancen ne ya yi hamdallah a zuciyarsa, daƙyar ya kuma cewa "Me a ka samu."
"Y'an biyu maza." Innar ta amsa.
Wai Wai Wai!!! Zo ku ga murna a gun Bassam, duk da cewa ya na kwance cikin azabar ciwo, amma hakan bai sa fuskarsa ta kasa bayyanar da farincikinsa ba.
A nan ya roƙi Inna Alfarmar ta je ta kawo masa matarsa da yayansa ya gan su, tun da shi ba zai iya tashi ba bare ya je, kasancewar kunkurunsa da ƙafarsa suna ɗaya daga cikin gaɓoɓinsa da suka karye.
Ganin basu da wannan damar ta ɗauko masa ɗaya daga cikin waɗanda ya nema ne, ya saka Baba isa ya je ya sanar da likitan buƙatar majinyacin nasu.
Sai da aka sha artabu kafin likitocin su yarda da wannan ƙudurin nasu, nan ma sai da su ka ji daga bakin majinyacin, ganin yanda ya ke ta masu magiya ga kuma halin da yake ciki na rashin tabbas ya sa suka amince da buƙatarsa.
©©©©©™™™™
Akan kujerar guragu aka ɗora ta, kasancewar ba ta iya tafiya da kanta saboda wahalar da ta sha gun haihuwa, nurse ce ke tura ta har zuwa ɗakin da ya ke.
Sakina da Shamsiyya ne suka ɗauki jariran su ka bi su a baya.
Su na isa nurse ɗin ta saki kujerar tare da juyawa ta fice daga ɗakin.
Tashin hankali ne ya ziyarce Mimie, ganin mijinta kuma masoyinta kwance magashiyan, baya ko iya kyakkyawan motsi.
Nan da nan idanunta suka fara ambaliyar ruwan hawaye, ta ma kasa cewa uffan tsabar firgicewa.
Su Sakina ne suka ƙaraso ɗakin riƙe da ƴaƴan, Inna ta karɓi ɗayan yaron, ta je saitin fuskar Bassam ta nuna masa ta ce "Ga ɗanka guda."
Shamsiyya ta matso da ɗayan kusa da na farkon yadda zai iya ganinsu sosai, shi kuwa sai murmushi ya ke a ransa ya na ƙara godewa Allah da wannan kyautar da ya masa ya na gaf da barin duniya, domin ya na ji ajikinsa cewa tasa ta zo ƙarshe.
Sosai ya ke jin ƙaunar yaransa na ratsa shi, da yake yaran duka da shi suke kama, komai da komai nasu iri ɗaya, ba inda suka bar shi har a kalar fata.
"Allah ya maku albarka." Shi ne kaɗai abinda ya faɗa ya na ta famar murmushi.
Bayan sun tabbatar da ya ga yaran da kyau, suka janye daga gun.
"Matata fa?" Ya tambaya.
Sakina ce ta je ta ƙara matso da Mimie daf da shi, dai-dai inda zai iya hangotan daga kwance.
Kallon ta ya yi ido cikin ido, sannan ya fara magana a wahalce ya na neman gafarar ta faɗar ya ke "Ki gafarta min uwar ƴaƴana, haƙiƙa na san na cutar dake, na ci amanar soyayya a baya lokacin da sihiri ke ɗawainiya da ni, ki yafe mun ki roƙa min gafarar su Abba da Alhaji Salman, ga amanar ƴaƴana nan na bar miki, na san za ki ba su tarbiyya mai kyau, don Allah ka da ki ce za ki rama abinda muka miki a kan ƴaƴana, pls ki yafe mun, Ni tawa ta zo ƙarshe."
Ya na maganar numfashinsa na sassarƙewa, sheɗarsa na yin sama da ƙasa.
Kuka take sosai ta ɗago da rinannun idanunta ta kalle shi ta ce "Na yafe maka Uncle, na yafe maka uban ƴaƴana, na yafe maka...."
Murmushi sosai ya yi a dai-dai lokacin da sheɗarsa ta zo daf da maƙogwaro ya ce "La'ilaha illallah, Muhammadu Rasulullah......"
Ya na zuwa nan rai ya yi halinsa.
Innalillahi wa inna'ilahir raji'un! Tashin hankali ba a sama ka rana, nan fa Mimie ta haukace, ta kai hannu
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 15