"Baba da ka bar shi mun gode."
Ya ce "Don Allah ku shigo ai ku kamar ƴaƴana ne, bakomai don na sauke ku ka da ku ji tsoro ba zan cutar da ku ba, kuma da akwai wata magana mai muhimmanci da na ke so na yi da ke y'ata." Ya ƙarashe zancen ya na duban Zuhra ga dukkan alamu da ita ya ke zancen.
"Ni kuma Baba." Ta faɗa ta na nuna kanta da yatsa.
Ya ce "Eh ke."
"To shikenan." Su ka faɗa tare da buɗe murfin motar Ruma ta yi wuf ta shige gidan baya, da ta ga ba ta da zaɓi dole ta shiga gidan gaba ƙirjinta na harbawa a hankali, bakinta ɗauke da addu'ar neman tsari daga sharrin mutum ko aljan.
Jan motar ya yi su ka bar gun.
A cikin motar ne Alhj. Salman ya ke tambayar Zuhra sunanta.
Ta ce " Sunana Zuhuriyya."
"Dakyau kafin mu fara magana ina za ku je?"
Ruma ce ta ba sa amsa da cewa "Ita baƙuwa ce a garin za mu je shopping ne, kuma mu na so mu zazzaga guraren shan iska don ta ga gari sai dai Kamar lokaci ya ƙure."
Ya ce "To ta ina za mu fara?"
Yanzun ma Ruma ce ta yi kararaf ta ce "Mu fara daga ShopRite."
Gyaɗa kansa ya yi tare da juyo da kallonsa kan Zuhuriyya ya ce "y'ata daga wanne gari ki ke?"
"Kano." Ta ba shi amsa.
Wace unguwa?" Ya kuma jefo mata tambaya.
Ta ce "Tukuntawa."
Miƙa hannunsa ya yi ya janyo wani envelop da ke gaban Motarsa ya ciro wa su hotuna ƙwaya uku da ke ciki ya miƙa mata ya ce "Duba ki ga kin san wannan?.
Ta karɓa ta duba, zazzaro ido waje ta yi tare da kallon Ruma cikin al'ajabi ta ce "Ruma dubi wannan kamar ni, amma kuma ba ni bace don ban taɓa saka kaya irin wannan ba, kuma ban san sanda aka ɗauki hoton ba."
Ruma ta kalli hoton cike da mamaki ta ce "Sister kamar har ta ɓaci."
Su duka su ka mayar da dubansu ga Alhj. Da alama su na neman ƙarin bayani akan abinda su ka gani ne.
Kafin ɗaya daga cikin su ta yi magana tuni Alhj. Ya riga su da cewa "Na san ku na matuƙar mamaki da ganin wannan hoton, kuma ku na so ku san wacece wannan, to wannan yarinyar dai y'ata ce da na haifa, sunanta Ruqaiya amma mu na kiran ta da Mimie, kasancewar sunan mahaifiyata ta ci."
Numfasa ya yi sannan ya ci gaba da cewa "Ta rasu kimanin shekaru uku baya lokacin ta na da 13years a duniya, ina matuƙar ji da Mimie tare da alfahari da ita, kaf ƴaƴana na fi son ta, Mahaifiyarta da y'an uwanta ma su na sonta sosai, mun yi babban rashi da ya mayar ahalin gidana tamkar marayu, son da na ke yi mata ne ya sa duk inda na ke ina tare da hotunanta, kwatsam yau na taso daga office sai na gan ki." Ya na maganar idonsa na kan Zuhra alamar da ita ya ke maganar.
Shiru su ka yi ba baki sai kunne.
Shi ne ya ci gaba da cewa "Na kaɗu matuƙa da na gan ki bayan na tabbatar da y'ata ta rasu, kuma ni na binne ta da hannuna, kuma na yi imani da cewa wanda ya mutu ba ya dawowa, wannan dalilin ne ya sa na tsaya na nemi na yi magana da ke...
Ga mai buƙatar siya sai ya tuntuɓe Ni ta wannan number👇🏼
_08109634202_
Domin na masa bayanin yanda zai biya, kada ku manta N200 ne kacal.
Follow me on wattpad @ummu inteesar
Vote, share& comments
UMMU INTEESAR CE💙💚❤️💛💙💙
👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻
*A SANADIN KAMA*
👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻
*DAGA ALƘALAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL UMMU INTEESAR*
*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y'AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*DA KUMA*
*A SANADIN KAMA*
Wannan littafin na kuɗi ne akan Naira 200 kacal, ga mai buƙatar sayen wannan littafin sai ya mun magana ta wannan number👇🏼
_08109634202_
Domin na masa bayanin yanda zai biya kuɗin.
KADA KU MANTA KUMA ZAFAFA BIYU DAGA ƘAWAYE BIYU NA KUƊI, IDAN DUKA BIYUN KA KE SO *A SANADIN KAMA* DA *ƘURUCIYAR SAPNAH* TO N300 KACAL, IDAN KUMA WANNAN KAƊAI KA KE SO ZAKA BIYA KUƊIN KARATU N200 KACAL.
________________________
________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*
Free Page 1️⃣5️⃣↪️1️⃣6️⃣
Jikinsu ne ya yi sanyi qlau da jin labarinsa, haƙiƙa sun tausaya masa matuƙa, musamman ma Zuhra da ta yi sukuku kamar mara lakka.
A tare su ka ce "Allah ya mata Rahma, ya kyauta ƙarshen mu."
Ya amsa da "Ameen."
Ci gaba da tuƙinsa ya yi ya na ba su labarin Margayiya Mimie da irin soyayyar da su ke yi mata.
A haka su ka ƙarasa ShopRite, ba su so sun ɗebi kaya da yawa ba, saboda kuɗin hannunsu ba wani mai yawa ba ne sosai, amma haka Alhj ya dage sai da su ka ɗebe kayayyaki ma su yawa da tsada sa'annan ya je ya biya kuɗin su ka bar gun.
Har zuwa lokacin sun kasa sakewa dashi a ɗarare su ke, ganin yanda ya kashe ma su kuɗi ba tare da ya san su ba, hakan ya saka Zuhra ta shiga fargaba sosai, "ko dai ya na da wata manufar ne a kansu?" Zuciyarta ta raya mata, nan da nan fuskarta ta bayyanar da alamun firgici.
A dai-dai lokacin ne kuma ya nemi ta ba sa numberta.
Hannu ta saka a jaka ta fiddo y'ar ƙaramar wayarta ƙirar itel da nufin duba masa lambar domin ta manta ta.
Hannunta sai kyarma ya ke yayin da ta ke fito da wayar.
Da mamaki ya kalli wayar hannunta ya ce "Wannan ita ce wayarki?"
"Eh baba." Ta Amsa masa.
Bai kuma cewa komai ba sai murmushi da ya yi, ta karanto masa number ya kwashe, ya ci gaba da tuƙinsa.
Ta na cikin wannan yanayin ne kawai su ka ga ya tsayar da Motarsa a gaban wani Babban shagon siyar da wayoyi.
Juyawa baya ta yi su ka haɗa ido da Ruma cikin mamaki da tsoro, dawo da dubanta ta yi a kansa laɓɓanta na motsi alamar ta na son yin magana, amma ta kasa.
Murmushi kawai ya yi domin ya fahimci yanayin su kamar sun ɗan tsorata.
"Ina zuwa." Abinda ya faɗa kenan ya fice daga motar tare da nufar cikin shagon.
Juyowa ta yi gaba ɗaya ta fuskanci Ruma ta ce "Anyah! Ruma wannan dattijon ba wani abu ya ke nema da mu ba? Nifa na tsorata wallahi."
"Nima ɗin ina mamaki sosai, amma ki kwantar da hankalinki, insha'allah ba abinda zai mana sai alkhairi, kuɗin ne kuma da alama sun zauna masa kin ga zai iya yin fiye da haka bakomai ba ne a gunsa..."
Ta na kawowa nan a zancenta ta yi shiru tare da faɗar "Ga shi nan ya na fitowa, maza ki juya."
Juyawa ta yi ta gyara zamanta kamar komai bai faru ba.
Buɗe motar ya yi ya shigo hannunsa ɗauke da farar leda, da alama dai waya ya siyo.
"Y'ata na ga wayarki." Ya faɗa.
Ba musu ta miƙa masa.
Buɗe wayar ya yi ya ciro sim ɗinta tare da fito da kwalin waya ƙirar iPhone 6+ ya saka mata layinta a ciki, ya kunna, sa'annan nan ya miƙo mata.
Firfito da ido ta yi ƙululu kamar dunƙulen ƙuli baki na ɓari ta ce "Me zan yi da ita baba."
Faɗaɗa murmushinsa ya yi ya ce "Daga yau wannan ita ce wayarki, za ki iya cigaba da riƙe ƙaramar idan kin so, ko kuma ki kyautar da ita."
Kasa magana ta yi sai kakkarwa bakinta ke yi.
"Ki ƙarba mana y'ata."
Hannunta na kyarma ta ƙarba ta na faɗar "Nagode sosai, amma idan na je gida ta ya zan yi bayani?"
"Ki gaya ma su cewa Daddynki ne ya saya ma ki Mimie ta." Ya faɗa.
Daga haka bai kuma cewa komai ba har su ka ƙarasa *kelvin* guri ne na shaƙatawa mai matuƙar kyau wanda ba kowa ne ke iya shiga gun ba, sai ma su dashi.
Idan ka je gurin ma sai an duba yanayin motarka kafin a ba ka tikitin shiga gun.
Da ya ke Alhjn babban ɗan siyasa ne, shi senetor ne da ke wakiltar jihar Kaduna.
Kai tsaye su ka shige, Zuhra ta ji daɗi sosai ta san da ba don sun haɗu da shi ba, da ba su isa su shigo wannan
Wurin ba.
Sun ɗauki ɗan lokaci a gurin kafin ya kwashe su su ka kama hanyar zuwa wata super market ɗin da ake siyar da suturu ma su kyau daga can kuma zai mayar da su gida.
®®®®®®®®®®®
Bayan ya sauke su a ƙofar gidan ya juya don zuwa gida ya yiwa iyalansa Albishir mai daɗin gaske na kuma samun Mimiensu a karo na biyu.
®®®®®®®®®®®
Fitowar Mommy kenan daga bedroom ɗinta sai ganin ta yi su na shigowa da kaya niƙi-niƙi, mamaki ne ya bayyana ƙarara a fuskarta, ƙarasowa ta yi ta na faɗar "Sannunku da dawo, ku kuwa ina ku ka samo kaya haka?, Bayan na san kuɗin hannunku bai isa yin wannan siyayyar ba.
"Hmmm! Mommy kenan, ki kwantar da hankalinki, yanzu dai zauna ki sha labari." Ruma ta faɗa.
Guri ta nema akan kujera ta zauna su ma su ka Zazzauna, Ruma ta shiga Zayyano mata duk yanda su ka haɗu da Alhjn har zuwa dawowar su gida, ita kuwa Zuhra fito da wayar da ya siya mata ta yi daga jakarta ta nunawa Mommy.
Sosai Mommy ta yi mamaki sai dai murnarta ya fi mamakin yawa, saukowa ta yi akan center carpet ta zazzage ledojin kayan da su ka shigo da shi, don ganin meye aciki.
Atamfofi ne y'an ubansu a ciki za su kai guda Shida ma su tsadar gaske sai lace guda biyu, ɗayar sauran ledojin kuwa kayan maƙulashe ne aciki danginsu chocolate, biscuits, ice-cream, cakes da sauran su.
Washe baki Mommy ta yi ta ce "Ah! Lallai Alhjn nan da alama babban mutum ne akwai karamci agunsa."
A ranar ta kira iyayenta ta sanar da su labarin abunda ya faru ɗazu, sun yi murna kuma sun ɗan ji tsoron abin kaɗan.
Mama ce ta ce mata "To Zuhra ki dai bi a hankali kin san sanin halin mutum sai Allah, barin ma wannan zamani da ya rikice, don haka ki kula kuma ki tsare mutuncinki."
Godiya ta mata sannan ta katse kiran, ta na gamawa ne kiran Alhj Salman ya shigo wayar.
New number ta gani da ba ta yi niyyar ɗauka ba, komai ta tuna? Kawai sai ta ɗaga kiran.
Gaisawa su ka yi sosai, sa'annan ya bawa matarsa su ka gaisa itama, anan ya ke sanar mata jibi zai turo driver ya ɗauke su zuwa gidansa, don haka su zama cikin shiri.....
Ga mai buƙatar siya sai ya tuntubeni ta wannan number👇🏼
_08109634202_
Domin na masa bayanin yanda zai biya kuɗin.
Ka da ku manta N200 ne kacal.
Follow me on Wattpad@ummu inteesar.
Vote, share & Comment.
UMMU INTEESAR CE❤️💚💔💙💚💛❤️
👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻
*A SANADIN KAMA*
👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻
*DAGA ALƘAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU-INTEESAR)*
*MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH*
*Y'AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*DA KUMA*
*A SANADIN KAMA*
Wannan littafin na kuɗi ne akan Naira N200 ga mai buƙata zai biya kuɗin karatu N200 kacal ga mai buƙata sai ya tuntubeni ta whatsapp numberna👇🏼
_08109634202_
Domin na masa bayanin yanda zai biya kuɗin.
KADA KU MANTA KUMA ZAFAFA BIYU DAGA ƘAWAYE BIYU NE, IDAN DUKA BIYUN KA KE SO *A SANADIN KAMA* DA *ƘURUCIYAR SAPNAH* TO N300 KACAL, IDAN KUMA WANNAN KAƊAI KA KE SO ZAKA BIYA KUƊIN KARATU N200 KACAL.
________________________
________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*
Free Page 1️⃣7️⃣↪️1️⃣8️⃣
Yau ta kama Ranar Litinin a ranar ne kuma Alhj zai turo mota a kai su gidansa.
Kwance su ke a kan gadon Ruma su biyun su na barcin safe, Mommy ce ta shigo ɗakin ta tarar da su sun yi rashe-rashe akan gadon, barci su ke sosai da alama dai su na jin daɗin barcin.
Ta da kanta ta yi ta kalli agogon da ke sarƙafe a bangon ɗakin ta ga har 10:30am ta yi.
"Subhanallah! Wai har lokaci ya tafi haka." Ta faɗa tare da ƙarasawa gaban gadon ta na ƙwala ma su kira.
"Ruma! Zuhra! Ku ta shi lokaci ya tafi." Ta faɗa ta na ɗan bubbugarsu a cinyar ƙafa.
A maimakon su miƙe sai ganin ta yi kowaccen su ta juya tare da gyara kwanciya, da alama ma ba su san ta na yi ba."
Toilet ta shiga ta ɗebo ruwa a cup ta zo ta yayyafa ma su.
Ai kuwa su ka yi firgigit su ka tashi a tsorace su na zazzare ido, kamar ma su neman wani abu.
"Sannun ku kasa Sarkin barci, har lokaci ya tafi haka ba tare da kun shirya ba?, bayan kun san ƙarfe goma sha biyu na rana Alhj ya ce zai turo driver a ɗauke mu."
Ware ido su ka shiga yi su na duban agogo, cikin hanzari su ka sauko daga kan gadon.
Zuhra ce ta yi saurin cewa "Ki yi haƙuri Mommy wallahi ba mu san lokaci ya tafi haka ba, barci ne ya ɗauke mu."
"Ai ba laifinki ba ne laifin wannan kasar ne na san ita ta koya miki wannan barcin asarar." Ta faɗa ta na nuna Ruma da yatsa, ta ɗora da cewa "ku yi sauri ku je ku shirya lokaci na ƙurewa, kun ga ni har na gama shiryawa."
Su ka fice ba tare da sunce komai ba, Zuhra kuwa ta cika da mamakin yanda ta ga Mommy na zumuɗin tafiyar nan, ko da ya ke wataƙil don mijinta baya gari ne kuma ta jima bata fita ko'ina ba shiyasa yanzun da ta samu dalilin fitar ta ke zumuɗi.
®®®®®®®®®®®
A ƙofar gidansu sha biyu ta yiwa drivern Alhj, kiran Alhjn ya yi ya sanar masa tuni ya ƙarasa ƙofar gidan.
Alhjn ya kira Zuhra ya shaida mata driver na jira a ƙofar gida.
A tare su ka fito su da Mommy kowaccen su ta sha wanka na kece raini.
Zuhra sanye ta ke cikin doguwar rigar yadi mai kyan gaske kalar dark blue ta yane kanta da mayafi ƙarami kalar red, ɗan kunne, takalmi da jakarta kala ɗaya da mayafinta,ta yi matuƙar kyau sosai.
A hankali ta taka zuwa gaban motar ta shiga yayin da Mommy da Ruma su ka shiga gidan baya, drivern ya ja Zuwa gwarinfa domin acan gidan alhj Salman ya ke.
Zahiri duk Mommy tafi su zumuɗin wannan tafiyar, ko su da su ka taɓa ganin Alhjn ba su kaita rawar jiki ba.
®®®®®®®®®®
Su na shiga gidan kai tsaye parking space ya nufa, sai da ya dai-daita tsayuwar motar Sannan ya kashe ta tare da kiran Alhjn ya sanar masa sun ƙaraso.
Ya ce da shi ya shigo da su ciki.
Tun daga ƙofar shigowa gidan su Zuhra aka sake baki ana kallo, hatta Ruma da Mommy sai da su ka zama ƙauyawan gaske gurin kallon kyau da tsarin gidan.
Drivern ne ya ce da su "Bismillah Hajiya ku zo mu je ciki."
Gaba ya yi su ka biyo shi a baya su na kalle-kallen yanda aka ƙawata gidan da furanni ga baloons an ɗaɗɗaura kamar dai ana shirin yin wani biki.
Su na isowa ƙofar babban falon gidan driver ya ja ya tsaya, ya kalle su ya ce "ku ƙarasa daga ciki, ni iyakata nan."
Ya na gama faɗa ya juya ya koma, tun daga ƙofar su ke jiyo wani cool music na ta shi a hankali.
A hankali su ka fara takawa zuwa cikin falon a ɗarare domin ganin duhu da su ka yi a gun.
Su na ƙarasawa tsakiyar falon kawai sai su ka ga haske ya mamaye ilahirin katafaren falon, wanda tsayawa misalta ma ku kyau da tsaruwarsa ma ɓata lokaci ne, sai dai ku ƙiyasta dakanku.
Hasken ya bayyana tare da sautin mutanen gidan yayin da su ke faɗar "Welcome back to your home Mimie."
Dukkansu su ka tada kai su na ƙarewa mutanen da ke cikin falon kallo, Alhj Salman ne a tsakiyar mutanen guda biyar, huɗun duka maza ne ɗayar ce mace da alama ita ce matarsa, sauran kuma ƴaƴansa, domin kallo ɗaya za ka ma su ka fahimci cewa jininsa ne su, kasancewar dukkansu su na kama da shi ne ɗayan ne kawai ya ke kama da mahaifiyarsa.
Dukkan su tsaye su ke a gaban wani zungureren cake dogo wanda zai yi tsayin yaro ɗan shekara huɗu zuwa biyar.
Alhjn ne ya ke tahowa cike da fara'a sai murmushi ya ke ya iso gabansu ya na ma su sannu da zuwa.
Da sauri sauran mutanen su ka ƙaraso cike da al'ajabi su ka yiwa Zuhra ƙawanya su na kallon ta, tabbas ta yi matuƙar kama da y'ar uwarsu, maganar Daddy ta tabbata da ya ke cewa idan su ka gan ta za su iya rantsewa ita ce ƙanwarsu Ruqaiya.
Sun ɗau tsawon lokaci su na kallonta cike da fara'a a fuskokinsu kafin daga bisani Mamy ta janye ta ta na faɗar "Kurwar y'ata kur, sai dai ku ci kanku ku sha baƙin ruwa."
Ga baki ɗaya yaran su ka kalleta mai biwa babban ne ya ce lallai Mamy har an fara gaya mana magana akan ƙanwarmu don kawai mun kalle ta?, Mu ba ƴaƴanki ba ne kenan?"
"Eh ɗin, dole a gaya maku haka irin wannan kallon haka kamar za ku haɗiye ta."
Dukan mutanen da ke gun su ka saka dariya.
Ƙarasawa ta yi ta zaunar da ita akan kujera, sai a lokacin ta waigo ta kalli su Mommy da ke tsaye agun ta ce "Don Allah ku yi haƙuri Hajiya mun bar ku a tsaye mu na ta murnar ganin daugther mu, ku ƙaraso ku zauna."
Mommy da ke tsaye agun kamar an dasa ta tsabar mamaki, sai a lokacin ta iya daga ƙafarta ta ƙarasa gun kujera ta zauna.
Zuhra kuwa kasa gane a wanne yanayi ta ke ciki ta yi, tsabar mamakin ganin yanda mutanen gidan ke rawar jiki akanta da yanda kai tsaye su ka mayar da ita ta su.
®®®®®®®®®
Bayan gama gaishe-gaishe aka miƙe gaba ɗaya domin gabatar da bikin da su ka shirya mata na dawowa gida, domin su a ransu jin su ke kamar Mimie ce ta yi tafiya ta dawo bayan shekaru uku.
Ga baki ɗayan su su ka nufi gun cake ɗin da aka yi saboda ita, a hankali kiɗan da ke tashi ya karaɗe falon gaba ɗaya.
Zuhra ce tsaye a gaban cake ɗin Ruma na tsaye daga gefenta sai kuma Mamy da Alhj da sauran ƴaƴansu su ka tsattsaya a gefen su.
A dai-dai lokacin ne Camera man ɗin da su ka kira ya ƙaraso, saboda haka ya fara kashe masu hotuna yayinda Zuhra ke yanka cake ɗin fuskarta ɗauke da fara'a sosai.
Da ta yanko na farko ta sanyawa Alhj a baki aka saka tafi Camera man na daga gefe sai aikin ɗaukar hotuna da vidio ya ke, ta yanko a ƙaro na biyu ta sakawa Mamie a baki nan ma aka ɗau tafi, a haka saida ta bawa Kowa na gidan cake ɗin a baki suma su ka bata.
Bayan kammala yankan cake ɗin ne aka shiga gudanar da bikin na murnar dawowarta, a haka baƙin Mamy da ta gayyata su ka fara zuwa, su ma y'an samarin gidan sun gayyato abokanansu mafi kusa da su.
Anci ansha biki ya yi kyau, wuni ɗaya aka shafe ana wannan shagali kafin daga bisani baƙin su ka tafi, ya rage saura y'an gidan, da su Zuhra.
®®®®®®®®®®®
Wajajen ƙarfe shida da rabi Mommy ta dubi Mamy ta ce "to hajiya mu za mu tafi yanzu kin ga yamma ta yi, mungode sosai da karamci."
Mamy ta kalle ta ce "Ah! Haba dai, tun yanzun? Ga shi ko gabatarwa junan mu da kanmu ba mu yi ba ana ta shagali, ya kamata dai ku tsaya asan juna tukunna, sannan ina neman Alfarmar a bar mana Mimie anan ta yi mana kwana biyu don Allah."
Murmushi Mommy ta yi ta ce "To shikenan an zama ɗaya ai."
Anan Alhj ya gabatar da kansa da yayansa ga su Mommy ya ce "Ni sunana Alhj Salman Mukhtar Nni senetor ne da ke waƙiltar jihar Kaduna, Ni ɗan asalin jihar Kaduna ne, wannan ita ce Matata Hajiya Fariha ita ma yar asalin jihar Kadunan ce, Sai yarana guda Shidda, wacce ɗayan ta rasu ita ce wacce mu ke so Zuhra ta maye mana gurbinta, waɗan nan su ne Maza biyar da su ka rage mun, Sameer shi ne Babba yanzun shekarunsa 27 sai Saheen ya na da 24 years, sai Samar ya na da 21 years Salim ya na da 18 years , sai Margayiya Ruqaiya (Mimie) ta na da 13 years a lokacin da ta rasu, sai Auta Sagir ɗan 5years."
Shiru falon ya yi ana saurarar Alhjn yayinda ya ke koro bayani......
Ga mai buƙata sai ya mun magana ta wannan number👇🏼
_08109634202_
Domin na masa bayanin yanda zai biya kuɗin N200.
Follow me on wattpad @ummu inteesar.
Vote, share & Comment.
UMMU INTEESAR CE❤️💔💚💙💛💙💛
👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻
*A SANADIN KAMA*
👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻
*DAGA ALƘALAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU-INTEESAR)*
*MARUBUCIYAR:*
*SOYAYYAR MEERAH*
*Y'AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
*DA KUMA*
*A SANADIN KAMA*
Wannan littafin na kuɗi ne akan Naira N200 kacal.
Ga mai buƙata sai ya neme Ni ta whatsapp numberna👇🏼
_08109634202_
Domin na maku bayanin yanda za ku biya.
KADA KU MANTA KUMA ZAFAFA BIYU DAGA ƘAWAYE BIYU NE, IDAN DUKA BIYU KA KE SO *A SANADIN KAMA* DA *ƘURUCIYAR SAPNAH* TO N300 NE IDAN KUMA WANNAN KAƊAI KA KE SO ZAKA BIYA KUƊIN KARATU N200 KACAL.
________________________
________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*
Free Page 1️⃣9️⃣↪️2️⃣0️⃣
Bayan ya gama bayanin ne Mommy ta ɗora da bayanin kanta da matsayin Zuhra a gunta ta ce "Ni sunana Khadija musa, ni ƙanwar mahaifiyar Zuhra ce uwa ɗaya Uba ɗaya, nice na ke bin Yaya A'isha,ina da yara guda uku, wannan ita ce y'ar Autata Rumaisa'u, sauran bayanin kuwa nasan Zuhra zata maku acikin zaman da zata yi anan."
Da haka aka kammala jawaban, Mommy ta miƙe ta na faɗar "Ruma tashi mu tafi, Hajiya sai watarana saduwar alkhairi."
Har Ruma ta miƙe ta kamo hannunta ta riƙe gam ta na faɗar "Mommy don Allah ki barmun y'ar uwata anan idan har ki na so nima na zauna, idan ba haka ba sai dai mu tafi tare."
Jin wannan zancen ne ya saka cikin sauri Mamy ta ce "Me ya yi zafi haka Mimiena, ki yi haƙuri zata ta yaki zaman ko da ace ba zata yi hakan ba sai an biyata kuɗi to ina mai tabbatar miki da cewa ko nawa e zamu iya sadaukarwa saboda farin cikinki."
Juyawa ta yi ta kalli Mommy ta ce "Ina neman alfarma ta biyu, don Allah ki taimaka ki bar Ruma anan su zauna tare zata fin jin daɗin zama tunda ga y'ar uwarta anan zata fi sakewa."
Shiru ta yi na yan wasu daƙiƙu kamar mai tsoron wani abu .
Mamy ce ta kuma cewa ki yarda damu Hajiya ba zamu cutar da yaranki ba, mu ba macuta bane hasalima soyayyar da muke yiwa y'ar mu Mimie ba zata bari mu iya cutar da duk wani mutum makusancinta bare wacce ta ke tamkar ita."
Dogon numfashi Mommy ta sauke kana ta ce "Hmmmm! Ba fa haka nake nufi ba Hajiya, kawai ina tunanin idan na barsu su biyun anan ni wa zai ɗebe man kewa agida Ni kaɗai tamkar mayya."
"Ki dai ƙara haƙuri Hajiya." Ta faɗa ta na juyawa zuwa cikin Bedroom ɗin ta can bayan wasu mintuna sai gata ta fito hannunta riƙe da wasu zungura-zunguran ledoji guda biyu ta miƙa hajiyar ta na faɗar "Ga wannan Hajiya ki gaida gida mungode sosai Allah ya bar zumunci."
Shima Alhajin hannu ya saka a aljihu ya ciro bandir na ɗari biyar-biyar guda biyu ya miƙa mata, ba musu ta karɓa ta na ta zabga godiya ga wani lallausan murmushi kwance a fuskarta, aka saka driver ya maida ta gida.
®®®®®®®®®®®
A mota ta ke ta zancen zuci ita kaɗai ta na faɗar "Kai Alhamdulillah, gaskiya wannan yarinyar Zuhra Allah ya zuba mata farin jini ga shi tun zuwan ta sai alkhairai na ke ta samu, Haka Musaddiq ya ta kawo mana abun arziƙi saboda ya na sonta, ita kuma ta ƙi fahimta, yanzu kuma ga alhajin nan da alama za'a shana, ko ni da ba don kada su ga rashin hankalina ba, ai da ni za'a yi kwana biyun na more, na gode Allah ma da Zuhra ta buƙaci zaman Ruma a tare da ita ko ta nan na rage zafi tunda y'ata zata moru."
Sauke ajiyar zuciya ta yi ta cigaba da zancen zucinta "Ga shi yarinyar nan ta kusa tafiya bai fi saura kwana biyar ba ta koma Kano, inama-inama ace Ruma ce ta samu wannan gatan tabbas da na fantama nima, amma yanzu ta ya zan iya hana Zuhra komawa gida tunda acan ta
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 3 Chapter of 15