Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
wannan mummunan mafarki." Ko me Sameer ya gani a mafarki? Me zai faru tsakanin Mommy da y'ar uwarta bayan komawar Zuhra garinsu? Hmmmm! Sai ku tare ne a page na gaba don cin amsar Waɗannan tambayoyin. Ga mai buƙata sai ya tuntuɓeni ta wannan number👇🏼 _08109634202_ Domin na maku bayanin yanda za ku biya. Follow me on Wattpad @ummu inteesar. Vote, share & Comment. UMMU INTEESAR CE❤️💛💚💙💛💚💛 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *A SANADIN KAMA* 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *DAGA ALƘALAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU-INTEESAR)* *MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH* *Y'AR GANTALI* *RIKICIN MASOYA* *DA KUMA* *A SANADIN KAMA* Wannan littafin na kuɗi ne akan Naira 200 kacal. Ga mai buƙata sai ya tura kuɗin ta wannan account ɗin. Account name: Rukayya Ibrahim lawal Account no:0431343346 Gt bank. KADA KU MANTA KUMA ZAFAFA BIYU DAGA ƘAWAYE BIYU NE IDAN DUKA BIYUN KA KE SO *A SANADIN KAMA* DA *ƘURUCIYAR SAPNAH* TO N300 NE, IDAN KUMA WANNAN KAƊAI KA KE ZA KA BIYA KUƊIN KARATU N200 KACAL. ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com *BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM* Free Page 2️⃣5️⃣↪️2️⃣6️⃣ A daren ranar Mamy ce Zaune a gefen gado, yayin da Daddy ke kwance akan gado da shirin barci da alama ya fara jin barci. Mamy ce ta ce :Alhaji gobe ne fa yarinyar nan za ta koma gidan Mommynta Saboda jibi za ta koma gida, ya kamata ka yi wani abun, gidan nan kowa na cikin damuwa saboda tafiyar da za ta yi." Da damuwa a fuskarta ta ke zancen. Ajiyar numfashi ya sauke cikin alamun fara jin barcin ya ce "Haba Mamyn yara ki daina damun kanki a kan wannan, ni na san me zanyi, Ni da kaina zan maida ta gida Kano jibi idan ya so sai na roƙo alfarma gun iyayenta ko za su bar mana ita na ɗan wani lokaci." Ganin jikin Mamyn ya yi sanyi qlau, ya saka shi miƙewa zaune ya ce "Haba my wife, ki kwantar da hankalinki, ki kwanta yanzu ki yi barci, na miki alƙawari komai zai tafi dai-dai insha'allah." Ba ta ce komai ba sai ajiyar zuciya da ta sauke ka na ta kwanta akan gadon cike da tunani iri-iri. ®®®®®®®®®®® Kashe gari wuraren ƙarfe goma Sameer ya ɗauko ƙasa cikin shigar ƙananun kaya jins da red t-shirt, ba hula akansa anma ya yi matuƙar kyau da ya ke shi fari ne sai kayan su ka amshe fatarsa sosai. Kai tsaye ɓangaren Mimie ya nufa, don tun da ya ga ba ta falon ya tabbatar ta na ɗakinta. Tarar da su yay su na fira ita da Ruma, ga tulin tufafinsu da su ka samu a gidan su na jerawa a akwati. Da sauri ya ƙaraso ciki baki na ɓari ya ce "me kuke haka?" Bai jira sun amsawa ya ware murya ya na kwalawa su Maryam kira "Maryam! Maryam!! Fariha! Fariha." Daga can ƙasa su ka jiyo ana ƙwala ma su kira da gudu su ka hauro sama har su na yar rige-rige. Cikin fushi ya kallesu ya ce "Wannan ba aikinku ba ne?" Yay tambayar ya na nuna masu kayan hannun Mimie da yatsa. "Eh ranka yadaɗe." su ka faɗa baki na ɓari." "Shine kuma dan ku na isassu ku ka bar ƙaramar yarinya da aiki irin wannan?." "Ayi haƙuri yallaɓai wallahi ba mu san za ta yi ba ne." Su ka faɗa tare da ƙarasawa gunta su ka janye akwatin su ka fice daga ɗakin domin ba za su iya tsayawa gu ɗaya da oga Sameer ba saboda kwarjininsa. Zuhra da Ruma kuwa tun lokacin da ya shigo ɗakin su ke kallonsa cike da mamakin abin da yayi yanzun. Guri ya nema ya zauna akan ɗaya daga cikin kujerun da ke ɗakin sannan ya dubi Zuhra ya ce "My sister akwai Magana mai muhimmanci da na ke so nu yi da ke." Jin hakan ya sa Ruma ta miƙe ta nufi hanyar fita daga ɗakin. "A'ah! Ina za ki kuma sister?" Cewar Mimie. Murmushi ta yi sannan ta ce "Zan sauƙa ƙasa ne gun Mamy." Daga haka ta yi ficewarta ba tare da ta sake cewa komai ba. Shi ko Sameer Sosai ya ji daɗin abinda Ruma ta yi, haƙiƙa kanta na ja tun da har ta fahimci cewa ya na son kaɗaicewa da Mimie, haka kawai sai ya ji ta burge shi. Bayan fitarta Zuhra ta sunkuyar da kanta ƙasa ta na wasa da y'an yatsun hannunta, yayin da ta ke zaune a kan carpet. "Sweet sister!" Ya kira ta cikin sanyayyiyar muryarsa. Ɗagowa ta yi ta na kallonsa. Shiru ya gifta na wani ɗan lokaci, can ya ce "A yau ɗin nan zan sanar da ke sirrin zuciyata, na sani kin riga kinsan cewa Margayiya Mimie ƙanwata ce uwa ɗaya Uba ɗaya kuma ina matuƙar ƙaunarta, amma ina so ki sani soyayyar da na ke mi ki ta na da banbanci da tata." Da sauri ta ɗauke idonta daga na sa ta kuma Sunkuyar da kanta ƙasa. Bai damu da hakan da ta yi ba ya ci gaba da cewa "Daga zuwanki zuwa yanzu na tabbatarwa kaina cewar na faɗa soyayyarki, saɓanin yanda na ke tunani daga farko, a farko na ɗauka cewa soyayyar y'an uwantaka na ke maki, sai a yanzu na tabbatar cewa, Soyayyar aure na ke ma ki." A razane ta ɗago idonta ta na kallonsa da mamaki a fuskarta, bakinta sai motsi ya ke alamar ta na son yin tambaya amma ta kasa. Murmushi ya yi ya ce "Ƙwarai da gaske, ina matuƙar sonki, ina ji a raina idan ban same ki ba Zan shiga wani mummunan yanayi, ki taimake ni ki so ni Mimie, ina so ki dawo cikin ahalinmu har abada." Ganin ba ta da niyyar ba da amsa ya sa ya miƙe ya bar ɗakin cikin wani irin yanayi da mutum bai isa ya fassara sa ba, shin farin ciki ne ko akasin haka." Zuhra kuwa ta shiga ruɗanin jin maganganunsu, tabbas ta na cikin wani yanayi, yanzu ya za ta yi kenan? A haka Ruma ta shigo ta Same ta. ®®®®®®®®®®® Da Azahar driver ya ɗauke su zuwa gidan Mommy. A ƙofar gidan ya sauke su sa'annan ya fito ma su da akwatinsu daga but ɗin motar tare da wasu kayan arziƙi da Mamy ta haɗosu da su. A falo su ka sami Mommy zaune ta na kallo cike da mamaki ta ke kallonsu, wai yaranta ne su ka yi kyau haka? Lallai hutu abu ne na musamman. Da sauri ta taso ta rungume Ruma ta na faɗar "Oyoyo my daughter." Su ka rungume juna su na murna. Zuhra ce ta ƙarasa jikin Mommy ta na faɗar "Oh! Mommy ta Ruma kawai ki ke kin manta da y'ar lelenki Zuhra." Mommy zame jikinta ta yi daga na Zuhra ta na taɓe baki, ba ta ce komai ba, ta ja hannun Ruma ta zaunar da ita kan kujera su na cigaba da hirarsu. A ranar Abbansu Ruma ya turowa Mommy kuɗi dubu talatin ya ce abawa Zuhra ta yi kuɗin mota kamar yanda ya saba idan ta zo. Amma saboda tsabar hassada irin ta Mommy ta kuɗurce a ranta ba zata bata kuɗin duka ba, tunda ita Habu zai yiwa haka. Daga Zuhra har Ruman mamaki su ke irin wannan sauyin hali da Mommy ta yi lokaci ɗaya, "To me ya faru bayan tafiyarsu?" Ranar dai a haka aka kwana cikinsu ba wanda ya gane kan Mommy. Shigowar su yaya Sunil da dare ne kaɗai ya rage mata damuwar da ta ke ciki. Washe gari Tun bakwai na safe Mommy ta tattarowa Zuhra Komai nata ta ajiye a falo, sannan ta wuce ɗakin Ruma don ta da Zuhra. Bayan ta shirya Mommy ta ba ta dubu biyar wai ta yi kuɗin mota. Cike da mamaki Zuhra ke kallonta can ta ce "Uhmm! Mommy da kin barsu kin manta tare da Daddy zamu tafi?" Ba musu ta kwashe kuɗinta ta mayar jaka, dama ba da niyya ta bayar ba don kawai ka da duniya ta zarge ta da rashin kirki ne ta gwada bayarwar. Shiru-shiru har takwas da rabi Daddy bai zo ba, Mommy ce ta yi gajin haƙuri ta ce "Wai nikam sai ƙarfe nawa ne za ku tafi?" "Uhmm, nima bansani ba Mommy bari na kira shi." Zuhra ta faɗa ganin ana mata kora da hali. Wayarta ta ciro ta danna mai kira bayan sun gaisa ta ce "Yawwa Daddy na ce ƙarfe nawa ne tafiyarki? Na fa shirya." Murmushi mai sauti yay ya ce "Yar gidan Daddy kenan, Sarkin zumuɗi, to ki ƙara haƙuri kaɗan nima shirin na ke nan da 30mins za ki ganni." "Ohk Daddy sai ka zo." Daga haka ta kashe wayar. Mommy kuwa sai taɓe baki ta ke ta na wurga mata harara. Ita dai bata kuma magana ba domin daga jiya zuwa yau jinta ta ke kamar kan ƙaya, gidan yayi mata zafi saɓanin da, da ba inda ya fi mata daɗin zama sama da nan. Sai ta ke ganin kamar Mommyn ta tsaneta, kuma bata san me ta yi mata ba. ®®®®®®®®®®® A can gidan Daddy Kuwa da misalin 9:12am ya fito a shirye tsaf domin tafiya zuwa garin Kano. Iyalansa ne gaba ɗaya su ka yo ma su rakiya cike da alhinin tafiyar Sisternsu. Har zai shiga Mota Sagir ya rugo da gudu ya riƙe babbar rigarsa ya na faɗar "Daddy ni dai zan bika, ka kaini gun sisterna." Mamy ta je ta janyo shi jikinta ta na lallaɓasa, amma fur ya ƙi daga karshe ma ya saka ma su kuka, shifa lallai sai an tafi dashi gidansu yayarsa. Ganin ya ƙi daina kuka da rigimar ya sanya Daddy ya ce Mamy ta je ta haɗo masa kayansa, ai kwana biyu ne kaɗai zai yi ya juyo. Shi ko Sagir faɗawa motar ya yi ya na murna yayin da Mamy ta shiga ciki don cika umarnin mijinta. Sameer sai kallon autansu ya ke ya na murmushi sai ya ji inama ace shi ma ya na da dama irin ta Sagir, tabbas da ya aikata hakan. Can bayan wani ɗan lokaci sai ga Mamy janye da akwatin Sagir, aka saka ma su but, drivern Daddy ya ja su ka bar gidan. Sai ɗaga ma su hannu su Saheen ke yi. Kai tsaye su ka wuce Area 1 don ɗaukar Mimie. A ƙofar gidan su ka faka ya kira ta a waya sai gata ta fito su Mommy harda to mata rakiya. Ta ƙarasa gaban motar Daddy ta na mishi sannu da zuwa tare da Faɗar "Alhaji mun gode da karamci, Allah ya ƙara girma mun gode, mungode, Allah ya kai ku lafiya." Kuɗi ya ciro bandir ɗin 500 guda ɗaya ya bata, ba kunya ta amshe ta na washe haƙora........ Ga mai buƙata sai ya tuntuɓeni ta wannan number👇🏼 _08109634202_ Domin na masa bayanin yanda zai biya kuɗin. Follow me on Wattpad @ummu inteesar. UMMU INTEESAR CE❤️💛💚💙💔💛 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *A SANADIN KAMA* 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *DAGA ALƘALAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU-INTEESAR)* *MARUBUCIYAR:* *SOYAYYAR MEERAH* *Y'AR GANTALI* *RIKICIN MASOYA* *DA KUMA* *A SANADIN KAMA* Wannan littafin na kuɗi ne akan Naira 200 kacal. Ga mai buƙata sai ya tura kuɗin ta wannan account ɗin: Account name: Rukayya ibrahim lawal Account no:0431343346 Gt bank. KADA KU MANTA KUMA ZAFAFA BIYU DAGA ƘAWAYE BIYU NE IDAN DUKA BIYUN KA KE SO A SANADIN KAMA DA ƘURUCIYAR SAPNAH TO N300 NE, IDAN KUMA WANNAN KAƊAI KA KE SO ZAKA BIYA KUƊIN KARATU N200. ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com *BISMILLAH RAHMANIR-RAHIM* Free Page 2️⃣7️⃣↪️2️⃣8️⃣ Ɗaga Zuhra hannu ta ke ta na faɗar "Ki gaida gida da iyayen naki, Allah ya sauke ku lafiya." Ruma da ke tsaye jikin motar ta na bankwana da y'ar uwarta sai hawaye ta ke ta na ɗaga mata hannu. A haka drivern ya ja su ka bar ƙofar gidan. Tafiya su ke a nutse, banda sanyin a.cn motar ba abinda ke tashi, Sagir ne ya ke ta damunta da surutu, Daddyn na jinsu sai dariya ya ke masu, anan shima ya sako bakinsa a hirar ta hanyar ƙara tambayarta wasu abubuwa da su ka shafi tarihin rayuwarta., Ita kuwa ta na bashi amsa. Tafiyar awa uku da rabi ce ta sada su da garin Kano kasancewar motar da su ke ciki lafiyayya ce, sabuwar mota ce dal ƙirar Land cruiser prado. Ita ce ta ma su kwatancen hanya har su ka ƙarasa unguwarsu, su na zuwa ƙofar gidansu ta cewa driver "Nan ya yi ai mun zo gidan." Cike da fara'a a fuskarta ta yi zancen. Cike da mamaki Alhajin ke ƙarewa gidan kallo a ransa ya na mamaki "Ashe akwai mutane da ke rayuwa a irin wannan wajen." Driver ne ya zagayo cikin sauri ya buɗe ma su motar, ta sauka cikin zumuɗi ta na faɗar "Daddy bari na je na sanar masu mun ƙaraso." Daga haka ta nufi cikin gidan da gudu, Sagir na ganin haka shima ya bita a baya da gudunsa. Fitowar mama daga banɗaki kenan, ta na riƙe da buta a hannunta, ta ga yarinya ta shigo gidan da gudu ɗauke da Sallama a bakinta. Kallon yarinyar ta yi ta ce "Lafiya dai yarinya, biyo ki akayi ne da ki ka faɗo mana gida da gudu haka?" Dariya sosai ta yi ta ce "Kai mama ki na nufin baki gane Zuhranki ba?" Sai a lokacin ta ƙare mata kallo tabbas ita ce da sauri ta rungumeta ta na faɗar "Allah sarki Zuhrana ki yi haƙuri banganeki bane, tabbas zaman Abuja ya karɓe ki, kinga yanda ki ka mulmule ki ka yi haske kuwa?, Kin ƙara kyau." Zame jikinta ta yi ta na faɗar "Allah mamata?" "Ƙwarai da gaske." Maman ta bata amsa. Af mama kinga har zan sha'afa, kin san fa tare mu ke da Daddy ya na waje, shine na zo sanar daku, Baban namu yana nan kuwa?." "Allah sarki! Gashi kuwa babanki ya na gun sana'arsa Kira mun shi a waya na sanar masa, bari na shimfiɗa tabarma je ki shigo da alhajin." Sai a lokacin su ka lura da Sagir da ke tsaye a bayan Zuhra. Mama ta ce "Wannan yaron fa?" Da murmushi shimfiɗe a fuskarta ta ce "Ƙanina ne ɗan autan Daddy." Ta faɗa ta na janyo shi a cikinta. Kafin ta ƙarasa ƙofar gidan ta kira baba a waya ta sanar masa sun iso. Kayan aikin da ke hannunsa ya watsar tare da miƙewa ya sanar da yayansa su kula da gurin shi zai je gida yanzu. ®®®®®®®®®®® A ƙofar gida Zuhra ta same sa har gumi ya fara karyo masa saboda zafin rana, ta ce "Ayyah! Yi haƙuri Daddyna na Barka ka sha zafi koh?, Muje daga ciki." Ba ta jira amsarsa ba ta juya ya bita a baya, tun shigarsu zauren gidan ya ke ƙarewa gidan kallo, kallo ɗaya za ka yiwa gidan ka gano waɗanda ke rayuwa ajikinsa talakawa ne, filasta ce kawai a bangon gidan ko fenti babu, simintin gidan duk ya tashi ta wasu ɓangarori na gidan. A haka su ka ƙarasa ciki,yayin da ya ke cike da al'ajabin yadda su ke iya rayuwa acikin wannan gidan. A kan tabarma ya zauna su na gaisawa da Mama. "Sannu da zuwa Alhaji, ya hanya? Ya iyali?" Mama ta faɗa cikin sake fuska. "Alhamdulillah, iyali kuwa su na nan ƙlau." "Alhaji mungode da ƙoƙari fa, Zuhra ta na ta bamu labarin abubuwan alkhairin da ku ke mata, mun gode, mungode Alhaji." "Ah! Bakomai wallahi, ai yiwa kaine ita ɗin tamkar y'a ta ke a gurina." Har mama zata ƙara magana su ka jiyo Sallamar Baba da ya ke shigowa gidan yanzu. Ƙarasowa ya yi ya na miƙawa Alhaji hannu. Duk da cewa daga wurin kanikancinsa ya ke, ko wanke hannu bai yi ba ya zo, hakan bai hana Alhaji miƙa masa hannunsa su ka yi musabiha ba. Nan fa Baba ya zauna aka cigaba da gaisawa, yayin da Zuhra da mama su ka tashi zuwa cikin ɗaki. Kuɗi mama ta bata N1000 ta ce "Kinga na manta ba a siyo lemo ba, maza kije kantin ɗan liti ki Karɓo masa lemo mai sanyi da ruwan roba." Karɓa ta yi ta fito tsakar gida, har ta kai ƙofar fita Sagir ya biyo ta da gudu. Alhajin ya ce "Ai fa yanzu aiki ya same ki Mimie, duk inda za ki sai ya bi ki." Yar dariya ta yi ta ce "Ai bakomai Daddy autanmu ne fa, dole a masa yanda ya ke so." Ta na gama faɗa ta sunkuce shi su ka bar gidan." Mama kuwa kitchen ta koma ta harhaɗa sauran abubuwan da su ka rage ta kawo ɗaki ta ajiye ta na jiran dawowar Zuhra. Bayan ta dawo ne Mama ta fito da abincin da aka shirya saboda shi kawai a tiren silver babba, cikin wasu kuloli ma su damar kyau da ta aro a maƙwafta kasancewar ita bata da su, a ɗakin Zuhran ta dire kayan. Baba ya ja shi zuwa cikin ɗakin domin ya ci abinci. Ba laifi sun yi ƙoƙari sosai gurin karrama baƙon na su domin a abincinsa harda kaza biyu a ciki. Su na cikin cin abincin ne wayar Alhaji ta hau ƙara. Ɗagawa ya yi tare da faɗar "Assalamu alaikum." Jim ya ɗan yi alamar ana magana a ɗaya bangaren, can ya ce "To madallah, kayan sun haɗu kenan? Nan ma ya ɗan yi shiru can ajima ya ce "Shikenan Kabir yanzu zan turo maka da address ɗin sai ka aiko mun da kayan, ba na son ɓata lokaci fa kasani." Daga haka ya kashe wayar,ya cigaba da cin abincinsa don ba laifi abincin ya yi daɗi sosai, dama Mama gwana ce a ɓangaren girki. Su na gama cin abincin su ka wuce masallaci don gabatar da sallar Azahar. Bayan dawowar su daga masallaci ne saƙon Alhaji ya iso. Dawowarsa kenan daga gun abokanansa dai-dai kan layinsu ya ga wata babbar mota cike da kaya ta na tafiya a hankali da alama su na neman wani guri ne, cigaba da tafiyarsa ya yi har ya zo ƙofar gidansu ya shige abinsa. A dai-dai lokacin ne kuma Alhaji ya gama waya da Kabir ya sanar mai kaya sun iso kwatancensa sai dai ba a gane gidan ba. Ƙarasawa yaron ya yi ya gaida mahaifinsa da baƙonsu har ya miƙe baba ya Kira sunansa "Ma'aruf!" "Na'am baba." Juyawa ga alhajin Baba ya yi ya ce "Alhaji ka kwatanta masa mutanen sai ya je ya zo da su." Kallon Ma'aruf Daddy ya yi ya ce "Za ka ga wa su mutane a wata babbar mota mai cike da kaya su za ka...." Ai tun bai gama rufe bakinsa ba ya ce "Wata ƙatuwar mota wacce ta ke cike da kayan abinci koh?" Da mamaki a fuskar Daddy ya ce "Eh ita, ko ka gansu ne?" "Na haɗu da su a farkon layi su na tafiya a hankali, bari na je kafin su kai kayan wani guri mu shiga uku." Ya faɗa cikin yarinta da rashin wayo, ya fice da gudu. Jim kaɗan sai ga su sun ƙaraso tare, aka fara sauke kayan abincin. Alhaji da Baba ne su ka fito ƙofar gida baba ya tara yara aka fara shiga da kayan ciki sai godiya ya ke ta yi Wa Alhaji, harda hawayen farin ciki. Tun da ya ke a rayuwa bai taɓa tunanin zai ajiye irin wannan kayan abincin a gidansa lokaci ɗaya ba. A kwai wani ɗaki a gidan wanda ke jikin kitchen da basa amfani dashi, sai tarkace ne kawai a ciki a ciki a ka saka kayan abincin. Da la'asar Daddy ya hau Motarsa ya ma su sallama za shi ya kama ɗaki a hotel inda zai kwana. Nan ma Sagir ya ƙi ya bi Daddy ya laƙewa Zuhra, bisa ga dole Alhaji ya haƙura ya tafi. ®®®®®®®®®®® Y'an uwa da abokanan arziƙi ne su ka cika gidan su Zuhra a na ta yi mata sannu da zuwa..... Ga mai buƙata sai ya tuntuɓeni ta wannan number👇🏼 _08109634202_ Domin na masu ƙarin bayani. Follow me on Wattpad @Ummu inteesar. UMMU INTEESAR CE❤️💙💚💛💔💙 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *A SANADIN KAMA* 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 DAGA ALƘALAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU-INTEESAR) *MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH* *Y'AR GANTALI* *RIKICIN MASOYA* *DA KUMA* *A SANADIN KAMA* WANNAN LITTAFIN NA KUƊI AKAN NAIRA 200 KACAL. GA MAI BUƘATA SAI YA TURA KUƊIN TA WANNAN ACCOUNT ƊIN: Accnt name: Rukayya Ibrahim lawal Accnt no:0431343346 Gt bank. Ko a tura katin Mtn ta wannan number 08109634202 KADA KU MANTA KUMA ZAFAFA BIYU DAGA ƘAWAYE BIYU NE IDAN DUKA BIYUN KA KE SO A SANADIN KAMA DA ƘURUCIYAR SAPNAH TO ₦300 KACAL, IDAN KUMA WANNAN KAƊAI KA KE SO ZAKA BIYA KUƊIN KARATU ₦200 ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com *BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM* Last Free Page 2️⃣9️⃣↪️3️⃣0️⃣ Haka ma yaya farida da matar yaya Kabir duk sun zo sai murna ake. Washe garin ranar da su ka zo da misalin ƙarfe sha biyu na rana Daddy ya zo gidansu Zuhra domin su tafi banki a buɗe mata account dama ya sanar da ita ta shirya kuma ta nemi ɗan rakiya. Saboda haka ko da ya zo ta gama shiryawa dama tuni yaya Kabir ya zo, zuwan Daddy kawai su ke jira, don haka koda ya zo mota kawai su ka hau suka wuce Gt bank. Cikin ƙanƙanin lokaci aka gama komai take anan Daddy ya yi mata transfer kuɗi dubu ɗari zuwa account ɗinta, su ka juyo gida. Jin kanta ta ke yi kamar tafi kowa ce yarinya Sa'a a rayuwa, wannan kuɗin da ya tura mata jin su ta ke tamkar miliyan goma sai ta ke ji yanzu ita da iyayenta sun samu waraka daga talauci. A kwana biyun da su ka yi Sagir ya shaƙu sosai da Zuhra da kuma ɗan uwanta Ma'aruf, saboda yanda su ke kula da shi da tarairayarsa tamkar ƙwai. Kwana biyu Daddy ya yi a garin Kano sannan ya yi shirin komawa. A ranar da zai tafi ya tara iyaye da y'an uwan Zuhra domin neman wata alfarma a gunsu. ®®®®®®®®®®® Ga baki ɗayan su zaune su ke akan wata ƙatuwar tabarma a tsakar gidan, kowa ya hallara in ka ɗauke Ma'aruf da ya janye Sagir ƙarami su ka fita zuwa wajen abokanansa. Anan Daddy ya dubi Kabir ya ce "To yaya babba sai ka buɗe mana taron da addu'a." Ba musu Kabir ya yi addu'ar aka shafa, sannan Daddy ya fara jawabi kamar haka " Da farko dai abinda ya sa na nemi mu taru anan shine, ina neman Alfarma guda biyu a wajenku, duk da na san ta farkon za ta yi matuƙar wuya amma zan roƙa." Ɗan dakatawa ya yi da zancen ya na kallonsu, Ganin duk sun zura mashi ido Alamar shi su ke saurare ya saka shi nisawa sannan ya ɗora da cewa "Alfarma ta farko shine ina so ku bar mun Mimie ta dawo hannuna domin ta maye mun gurbin Real Mimieta, na yi ma ku alƙawarin zan riƙe ta da amana, idan hakan bai samu ba to ina roƙon ku da ku ba mu damar zama iyayenta na biyu ta yadda za mu dinga sanin duk wani abu da ya shafi rayuwarta, in ya so duk aka yi hutu sai ta je mana, wannan abun zai sanya iyalina cikin tsantsan farin ciki." Tun da ya fara magana ba wanda ya ce ƙala, jin Alfarmar da ya nema ya sanya jikin Baba ya yi sanyi domin har ga Allah ya san ba zai iya barin Zuhra ta koma hannun wa su ba, domin da ya na buƙatar hakan da ba wanda yafi cancanta a baiwa riƙonta sai ƙanwar mahaifiyarta, tun da kuwa ya hana ta tabbas ba ya jin zai iya bawa Alhaji duk da ya na matuƙar jin nauyinsa. Ganin kowa ya yi shiru kuma ga Baba da alama ya zurfafa a tunani ya sanya Daddy ya ce "Ka kwantar da hankalinka malam Habu, idan ba zai yiwu ba ni na haƙora ka da ka ji kunyar faɗamin gaskiya." Dogon numfashi Baba ya ja ya sauke sannan ya ce "Ka yi haƙuri Alhaji ba wai ban yarda da kai ba ne ko kuma ba na son baka Zuhra ba ne a'a, dalilin da ya sa ba zan yi hakan ba shi ne kafin ka nemi wannan Alfarmar, ƙanwar Mahaifiyarta Khadeeja da ke Abuja ta nema ban yi mata ba, ka ga yanzu idan ta samu labarin na ba ka Zuhra tabbas ba za ta ji daɗi ba, don Allah Alhaji ka yi haƙuri, ka da ka ga kamar na maka butulci." Haƙiƙa Daddy ya ji zafin hanashin da aka yi sosai, amma ya masa uzuri domin ya san yanda zafin rabuwa da ɗa ya ke. Murmushin yaƙe ya yi ya ce "Kar ka ji komai Malam Habu, sai alfarma ta biyu da na ke nema ina fatar zan samu." "Insha'allah Alhaji." Ya amsa. Gyara zamansa ya yi sannan ya ce "Alfarma ta biyu kuwa ita ce daga yau ina so ku dinga kiran Zuhra da Mimie domin ina so ta maye min gurbin y'ata Mimie." Cikin hanzari Mama ta ce "Ah! Wannan ai ba damuwa tun yanzun ma za mu fara faɗa." Anan Daddy ya yi godiya sosai sannan ya sanar da su cewa ya na so ya haɗa auren Sameer da Mimie domin ƙarfafa zumunci. A razane Zuhra ta

Chapter 5 of 15