Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da komai ba, sai jefa shi a halaka da ta yi. Ya na cikin wannan halin ne Rajbir ya shigo ɗakin, ganin ya farka kuma ya na kuka ya saka ya buɗe shi, cikin harshen turanci ya ke cewa "A'ah! Mutumin ka farka ne? Me ya faru ka ke kuka?" Cikin zafin rai da ɗaga murya Sameer ya mayar masa da amsa da yaren da su ke amfani da shi idan za su yi magana da juna wato turanci ya ce "Bansaniba, tambayar me kake bayan kuka jefa ni a cikin wannan halin na saɓawa mahaliccina?" "Oh sam! Wannan fa ba damuwa ba ce shan barasa ai ba laifi bane.." Dakatar dashi Sam ya yi ta hanyar ɗaga masa hannu ya ce "A addininka hakan ba laifi ba ne, amma a addinina wannan haramun ne, kun cuce ni, daga yanzu na daina yarda da ku, don Allah ku fita rayuwata ku koma masaukinku." Ya na gama faɗa ya miƙe ya shige toilet ya bar Rajbir nan sake da baki. Tun daga ranar ya fara share su, ba yanda bai yi su bar masa gidansa ba su ka ƙi, a haka suka lallaɓa shi har su ka shawo kansa ya kuma faɗawa tarkonsu a karo na biyu, tun daga lokacin ya afka cikin baƙin tarkonsu daga lokacin rayuwarsa ta zama ta mashaya,har ta kai da ya fara tunanin Mimie ya ke buɗe bakin kwalba ya tuttula, a haka rayuwarsa ta gurɓace duk silar soyayyar Mimie da ke cunkushe a zuciyarsa. Har zuwa lokacin kuma ya kasa manta ta ko da ya sha giyar. ®®®®®®®®®®® Ɓangaren Mommy kuwa ta samu nasarar saka maganin a cikin abincin Saheen ta hanyar Nafisa mai kula da gyaran ɗakinsa, da duk wani abu da ya shafe shi. Hakan kuwa ta faru ne a lokacin da Mommy ta je gidan Alhaji Salman, kamar yanda ta saba, domin ta mayar da gidan tamkar gidansu. A lokacin ne ta samu keɓewa da Nafisa su ka haɗa kai, ta bata maganin tare da kuɗi dubu goma ladan aikinta, ita kuwa saboda kwaɗayi ta karɓa ta tafi. Mommy ba ta bar gidan ba sai da ta tabbatar an saka masa a abinci ya ci. Tun daga ranar Saheen ya susuce yake jin kansa cikin wani irin yanayi shauƙin soyayya na fizgarsa, shi da kansa ya saka Direbansu ya kai shi gidan su Ruma ba tare da sanin kowa ba, ya je ya furta ya na son ta, da ya ga kamar bata so har kuka ya saka mata. ®®®®®®®®®®® Bassam ya samu Mimie ya gaya mata hukuncin da mahaifiyarsa ta yanke, jikinta ya yi san yi laƙwas amma bata nuna ba, a haka ta nuna tsantsan farin cikinta, bayan kwana biyu su ka yi parking duk wani abu nasu, su ka koma gidan Innarmu da zama. Washe garin ranar da suka tare gidan, Bassam ya juya zuwa Kano yayin da ya bar matarsa cikin damuwa da zullumi, haƙiƙa ta na hangowa kanta matsala a zaman gidan saboda yanda mutan gidan su ka fara juya mata baya... Ga mai buƙata ya tuntuɓeni ta wannan number 08109634202 Follow me on wattpad @ummu inteesar UMMU INTEESAR CE❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️ 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *A SANADIN KAMA* 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *DAGA ALƘALAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)* *MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH* *Y'AR GANTALI* *RIKICIN MASOYA* DA KUMA *A SANADIN KAMA* WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE AKAN NAIRA 200 KACAL GA MAI BUƘATA SAI YA TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER 08109634202 DON ALLAH IDAN KA SIYA KADA KA FITARMIN HAƘƘIN MALAKA NAWA NE *AREWA WRITERS ASSOCIATION* ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com *BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM* Page5️⃣5️⃣↪️5️⃣6️⃣ A haka ta cigaba da haƙuri halayyar mutan gidan da suke cusgunawa rayuwarta a duk kwana duniya,aciki kuwa har da su Sakina da suka manta da tarin Alkhairanta a gare su suka rufe ido suna mata tijara iri-iri. Damuwa ta taru ta mata yawa ga shi ɗakin da ta tare ƙarami ne, daƙyar uwar ɗakan ta ɗauki gado da walldrop ɗin ta,sai madubi shima daƙyar ya samu mazauni a ɗakin, ɗan filin tsakar ɗakin da ya rage bai wuce inda mutum sai saka Sallaya ya yi Sallah ba, ga shi ba toilet a ciki. Falon kuwa saboda matsatsinsa daƙyar kujeru ƙwaya uku suka zauna a ciki, sai ƙaramin showglass ɗinta, ɗan filin da ya rage ba zai ishi kwanciyar mutum biyu ba, dole aka bar sauran kayan nata acan wancan gidan da suka taso, haƙiƙa ta na cikin ƙunci sai a lokacin ne ta tuna da auren bada yardar iyayenta aka yi ba, shima wanda ya mata auren don ba yanda ya iya ne, amma ta san ba don ya na so ba. Kusan ko da yaushe ta na waya da su Mama,yaya Farida da su yaya Kabir da matansu, Baba ne dai idan ta kira sai ya ga dama ya ke ɗagawa, nan ma da sun gaisa ya ke kashe wayar bai damu da tambayar lafiyarta ko yaya zaman su ita da mijin nata ba, don har zuwa lokacin ya na jin zafin abinda ta masa, ga wata mahaukaciyar kunyar Alhaji Salman da ya ke ji tun lokacin da abun ya faru, Mama ce ma ta ɗan sauko ba laifi tun da ita ta na tambayar lafiyarsu kuma ta sake su yi hira. Haka ma ta na waya da su Daddy Mamie, da su yaya Saheen, watarana su na waya da Daddy ta ke tambayarsa "Daddy wai ni kuwa yaya Sameer fa? Shiru ake jinsa ya shige Dubai ya manta da y'ar ƙanwarsa." Ta ƙarashe da sigar zolaya. Dariya Daddy ya yi ya ce "Cab! Wai kina nufin bai kira ya taya ki murnar aurenki ba? Na fa tura masa number na ce ya kira ku gaisa." Shiru ta yi ta na tuna lokacin da suka yi waya da shi ta ƙarshe da irin maganganun da ta gasa masa a lokacin da idonta ya rufe da Soyayyar Bassam, "Tab! Ta ya ma zai kira ni bayan duk wannan abun da na masa?" Ta faɗa a ranta. Tunawa da ta yi ashe ta na kan waya ne ya sa ts kirkiro murmushi ta ce "Ai kuwa Daddy bai kira ba, ina ga mantawa ya yi turon numbersa na kira shi." Ta faɗa cikin dakiya don ba ta so ya fahimci canjin yanayi daga gare ta. "Ohk, bye sai anjima, ina da wani aikin da zan yi." Daga haka ya katse wayar, ko ɗagawa bata yi daga gun ba, saƙonsa ya shigo wayarta. Nan take ta danna masa kira jiki a saɓule, ta na ji wayar na ring amma bai ɗaga ba sai da ta kuma kira da ya ke can ƙasar har dare ya fara. Shigowa lokacin ya na zaune a falonsa cikin yanayin damuwa da tunaninta, ko yaya ya rufe idonsa hotonta ya ke gani, lokacin bai jima da gama sallar isha'i ba, ya zauna agun cikin wani yanayi mai wuyar fassarawa. Ƙarar wayarsa da ke kusa da shi ya dawo da shi daga duniyar tunanin da ya shiga, ganin new number ne ya saka ya ƙi ɗagawa, sai ga wani kiran ya shigo, lura da ya yi cewa in bai ɗaga ba ba za'a daina kira ba, ga shi kuma number Nigeria ce da alama wani ne daga familynsa hakan ya saka ya ɗaga tare da karawa a kunne. "Assalamu alaikum." Ta faɗa cikin sanyayyiyar muryarta mai rikita tunani. Shi kuwa Sameer wata irin super ya yi ya miƙe tsaye tare da ƙara kallon sensor na wayar, tabbas ko ba'a faɗa masa ba, ya san Mimiensa ce ke magana domin ba zai taɓa manta muryarta ba, tunda kullum ya kan ji a mafarki. Mai da wayar kan kunnensa ya yi ya na faɗar "Baby da gaske kece,Sweet sis, anyah! Ba mafarki na ke ba." Ya faɗa cikin wani rikitaccen yanayi. Mamaki ne ya cika ta "Ashe ya gane ni? Taya ya yi saurin gano ni haka? Wannan na nufin bai manta da ni ba kenan?" Muryarsa ta dawo da ita daga tunani inda ya ke cewa "Baby ko ba ke bace? ko abinda na saba ji a kunnena ne yau ya zo min a kiran waya? Lallai na fara zaucewa." Ya faɗa cikin rawar murya. Jin haka yasa ta tattaro duk wata nutsuwarta, daƙyar ta haɗo kalmomi ta ce "Ni ce yaya Sameer, Mimienku ce, ya kake? Ya karatu? Da fatar kana nan lafiya." Cikin mutuwar jiki ta ke zance domin a kunyace take, saboda ba ta manta irin cin kashin da ta masa ba, a lokacin da yake neman aurenta. Komawa ya yi ragwaf ya zauna kan kujerar ya na faɗar "Sweety ba lafiya ba, ina nan ciwon son ki ya murƙushe ni, ba ni da aiki sai tunaninki, ba na iya karatun da ya kawo ni, Dubai ta kasance mun gurin jinya a maimakon gurin karatu, na shiga wani mugun yanayi Baby, na sani yanzu ki na can zaune ɗakinki cikin farinciki yayin da na ke cikin damuwa, idan ba ki manta ba a baya na gaya miki muddin ba ki aure ni ba tabbas zan iya rasa raina ko na rasa hankalina, to hakance ta faru ina daf da rasa hankalina Baby ki taimake ni..." Daga haka ya fashe da kuka cikin wani yanayi mai ban tausayi. Hakan ya kashe mata jiki sosai, lura da ta yi cewa idan ta cigaba da saurararsa tabbas su na daf da faɗawa halaka musamman shi, hakan ya sa ta fashe da kukan tausayinsa tare da kashe wayar ta ajiye. Cigaba da kukanta ta yi, a zuciyarta ta ke cewa "Shin yaya Sameer ya manta cewa ni matar aure ce ya ke faɗar waɗannan kalaman." Nan ta ke ta ji ta yi nadamar biyewa son zuciyarta, ga shi ta saka wannan bawan Allahn cikin tashin hankali da ɗimaucewa. "Kaicona ni Zuhra, Daddy baka cancanci wannan sakayar daga gare ni ba, yaya Sameer ku yafe min." Ta faɗa ta na cigaba da kukanta. ®®®®®®®®®® Sameer kuwa jin ta na kuka ya saka shi gigicewa faɗar "Ya ke Baby kuka ki ke?" Jin ta yanke kiran ya saka shi fara neman layinta hankali a tashe ya na kuka. Kusan sau biyar ya na kira amma bata ɗaga ba, hakan ya saka shi faɗuwa a ƙasa ya na cigaba da kuka ya na sambatun kiran "Sweety meyasa ki ka mun haka? Me na rasa da ki ka ƙi ni? Me wanda kika aura yafi ni da shi?" Wisam da Zaroon da su ke zaune a falon kowannen su ya na rungume da budurwarsa, kallonsa su ke cike da tausayawa. Wisam ne ya tashi, ya je gabansa ya fara rarrashinsa faɗar ya ke "Haba Sam! Me ye haka? Ka zama namiji mana, akan mace ne ka ke wannan kukan? Ka da ka ba ni kunya mana." Maliha budurwar Wisam ce ta ce "Haba my love, ka tausaya masa mana, shi kaɗai ya san me ya ke ji a zuciyarsa, ina ga kamar ba ka gama fahimtar miye so ba." Zaroon ne ya taso shima ya ƙarasa wurin su ka tayar da shi zaune, Zaroon ya dubi budurwarsa ya ce "Janan ba ni kwalbar barasar nan." Ɗaukowa ta yi ta na kwarkwasa ta iso gun ta miƙa masa. Buɗe bakin kwalbar ya yi ya miƙawa Sameer ya na faɗar "Karɓi wannan Sam, ga maganinka ka na sha shikenan." Ai kuwa ba musu ya karɓa ya kwankwaɗa tare da komawa ya lafe jikin kujera ya na cigaba da sambatun kiran sunan Mimie. ®®®®®®®®® Saheen kuwa ya gama susucewa kullum ya na gidan Mommy maƙale, abin har ya fara bawa Ruma tsoro, "Anyah! Mommy ba wani abun ta aikatawa Saheen ba kuwa?" Wannan tambayar ce ta faɗo ranta. Ras ƙirjinta ya buga da ƙarfi "in kuwa hakane tabbas Mommy ta cika mai son zuciya." Haka Saheen ya ke yiwa Mommy ɓarin kuɗi, ita kuwa Ruma tausayinsa ne ya saka ta fara kula shi. Farincikin Mommy kasa ɓoyuwa ya yi har sai da ta kira ƙawarta Hajiya hafsat ta shaida mata magani ya ci, su ka yi ta murna anan ta ke labarta mata irin barin naira da Saheen ke mata da ɗan abin hannunsa, kafin ta shiga dukiyar Mahaifinsa. ®®®®®®®®® A haka lokaci ya cigaba da ja, a wani zuwa da Bassam ya yi gida anan ne komai ya ƙara rikicewa Mimie, domin bayan komawarsa Kano ya tafka hasarori waɗanda ba sa faɗuwa duk ya fara tsiyacewa motar da ya ke hawa ma ya na gaf da zuwa gida aka sace ta. Da dawowarsa gida ya sami matarsa da zancen ta taimaka masa da kuɗi ya ja jari koda aro ne ya na so ta ba shi, ita kuwa saboda tausayin mijinta ta ba shi dama anan ta ke cewa "Uncle ai dukiyata taka ce, da ni da duk abinda na mallaka mallakinka ne, ka yi yanda ka ga ya dace." Ai kuwa ya yi farin ciki sosai, da wannan damar ya yi amfani ya je ya siyar da tarin kayanta da su ke a can gidansa ajiye ya karɓi kuɗi da zimmar ya na komawa Kano zai siyo wa su kayan a fara kasuwanci. Tun dawowar su gidan nauyi ya dawo kansu, domin duk wani cefane na gidan shi ke yi tun da babansu baya raye, matarsa kuwa ta kasance ita ke yin duk wani girkin da za'a ci agidan, sai dai idan ta gama ta kai masu na su, sauran kuma ta ci ita da mijinta. Duk wannan abin da ake bata sanar da kowa ba ta yi haƙuri ta jure, sai da ta ga abun ya fara yawa ne ta sanar da Mama ta na kuka tare da neman addu'ar ta da yafiyar ta. A wannan dawowar da ya yi ne kuma Zinnira ta zo ta tare a gidan, nan fa abubuwa suka ƙara caɓewa Mimie, domin baƙar magana da habaici kam kullum sai ta sha shi, kasancewar Zinnirar na matuƙar son Bassam tun kafin ya yi aure, shi ne bai ba ta fuska ba. Ana haka ne ta nemi izinin zuwa ganin gida daga can kuma ta na so ta wuce Abuja gun Mommy da kuma gidan Daddy, ba musu mijin nata ya amince mata, amma ita kaɗai za ta tafi kasancewar bai jima da zuwa ganin gidan ba lokacin komawar sa bai yi ba, dama can sun samu hutun makaranta. Da haka su ka yi sallama ta wuce Kano satin ta ɗaya anan ta wuce Abuja gidan Daddy ta sauka domin tunawa da ta yi cewa yanzu bata da gurbi a zuciyar Mommy, amma a ranar ba ta kwana ba sai da ta je gidan Mommy ta kwana biyu, a can ne ta ga irin susucewar da Saheen ya yi akan Ruma. Ta yi murna sosai da wannan haɗin, acewar ta idan ba ta auri yaya Sameer ba ga yar uwar ta za ta auri yaya Saheen ta san wannan haɗin zai rage ma su damuwar da ta jefa zuciyoyinsu aciki. A daddafe ta kwana biyu gidan saboda hantarar da ta ga Mommy na yi mata. ®®®®®®®®® Rashin sani ya fi dare duhu, da Mimie ta san cewa wannan tafiyar tata za ta bawa maƙiya damar shiga tsakaninta da mijinta tabbas da ba ta yi ba. Domin a lokacin da ta bar shi gida ne, Zinnira ta je gida ta karɓo magani hannun Mamanta wanda su ka karɓo gurin boka na karkato da hankalinsa zuwa gare ta ta kawowa Innarmu, su ka saka masa acikin abincin da ya fi so wato dambun hatsi aka basa ya ci, tun daga ranar ya fara mantawa da al'amarin matar tasa, kuma ya fara jin sabon al'amari game da y'ar uwar tasa...... Ga mai buƙata sai ya tuntuɓeni ta wannan number 08109634202 Follow me on wattpad @ummu inteesar UMMU INTEESAR CE❤️❤️❤️❤️❤️❤️ 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *A SANADIN KAMA* 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *DAGA ALƘALAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)* *MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH* *Y'AR GANTALI* *RIKICIN MASOYA* DA KUMA *A SANADIN KAMA* WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE AKAN NAIRA 200 KACAL GA MAI BUƘATA SAI YA TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER 08109634202 DON ALLAH IDAN KA SIYA KADA KA FITARMIN HAƘƘIN MALAKA NAWA NE *AREWA WRITERS ASSOCIATION* ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com *BISMILLAHI RAHMANIR-RAHIM* Page 5️⃣7️⃣↪️5️⃣8️⃣ Tun ta na Abuja ta fuskanci sauyi daga mijinta, domin ada kullum sai su yi waya sama da uku, amma a y'an kwanakin da ta yi a garin sai a kwana a yini bai kira ta ba, sai ita ce ta ke kiransa, nan ma suna gaisawa sai nemo wani uzurin ya faɗa mata, a kan dole take ƙyale shi. Bayan da Mamy bata yi ba don ta gaya mata damuwarta amma ta kafe a kan cewa ba komai, a haka ta ƙaraci zamanta a Abuja ta juyo zuwa birnin Kebbi. Ba ta ƙara shiga tashin hankali ba sai da ya zo ganin gida ta ga ya daina kula ta kamar da, sai ma wulaƙanci da ya ke mata, bashida wani lokaci ta sai na y'an uwansa. A gabanta zai je ya kira Zinnira su zauna a falonta su na hirarsu su na dariya. Hakan ba ƙaramin daɗi ya ke yiwa Zinnira ba, anan ne ta ke samun damar gasawa Mimie magana cikin ruwan sanyi, kuma a gabanta ta ke kanainaye shi da kalaman soyayya. Ba yanda ta iya dai dai idan abin ya dame ta ta shige ɗaki ta yi ta kuka har ta gode Allah, ta rasa wa za ta tunkara da matsalarta, a duniya bata da waɗanda su ka wuce su Baba,Mama,Daddy da kuma Mamy amma kuma rashin kunyar ta ba ta yi ƙwarin da za ta iya fuskantar ɗayan su da damuwarta ba, yaya Farida ce ta faɗo mata a rai, aikuwa ta kira ta tana kuka ta zayyane mata komai. Rarrashinta ya shiga yi kafin daga bisa ni ta ce "Komai ya faru dake ke ki ka ja Mimie, da kin karɓi zaɓin mahaifanki ina da yaƙinin da baki shiga wannan tashin hankalin ba, amma ba damuwa zan dinga taya ki da addu'a, ke dai abinda na ke so dake ki ci gaba da haƙuri kuma ki nemi yafiyar iyayenki akan saɓa musu da kika yi." A haka suka cigaba da tattauna matsalar ta na bata shawarori har tsawon wani lokaci kafin su katse kiran. ®®®®®®®®®® Bayan kamar rabin shekara da tarewar ta gidan abubuwan su ka ƙara tsananta a gare ta domin yanzu Uncle har zagin ta ya ke tas, kuma baya ganin laifin y'an uwansa akan duk wulaƙanci da suke mata. A bangaren Sameer ma ya na can cikin wani mawuyacin hali mai wuyar fassarawa, kuma ya ci gaba da shaye-shayensa ba tare da sanin iyayensa ba, Allah dai ya kare duk abinda ya ke baya neman matan banza. DAWOWA DAGA LABARI Bayan komawar Innarmu ɗakinta, ya ci gaba da rarrashin matarsa har ta ware, to kun san tsakanin mata da miji sai Allah, nan da nan ta sauko su ka dawo kamar ba abunda ya faru. Da ya ga hankalinta ya kwanta ne ya shirya ya fita, ya bar ta anan ta na tunanin rayuwar da ta tsinci kanta a ciki. Ita yanzu ga baki ɗaya auren ya fice a ranta, ba wai don ba ta son mijinta ba sai don damuwar da take ciki, tunawa da ta yi cewa aure ibada ne kuma zaman bautar Allah take da neman aljannarta a gidan, hakan ya sa ta haƙura ta cigaba da daurewa. Idan ta je makaranta ne ma take samun sassauci domin a can ne za ta haɗu da course mate ɗinta ai ta taɗi ana dariya, amma tana dawowa gida shi kenan ƙuncinta zai dawo. Akwai wata course mate ɗinta (Samiha) da suka shaƙu sosai ita ce ta lura da yanayin damuwar da ƙawar tata ke ciki, ta taya ta jimami kuma ta ba ta shawarwari gwargwadon yanda za ta iya, haka ta cigaba da takatsan-tsan a zaman gidan don ma tana da juriya sosai. ®®®®®®®®®® Lokaci ya sha kwanaki sun shuɗe bayan shekaru biyu, zaune take a ɗakinta abin duniya ya dame ta gorin haihuwa kawai ake mata, Innarmu faɗar ta ke Mimie ta ƙi yarda ta haihu ne saboda karatunta da yabawa muhimmanci akan komai. A haka ta duƙufa da addu'a kullum dare ta na kai kukanta a gurin mahaliccin bayi ta na neman sassauci da mafita a gunsa. Kallo ɗaya za ka mata ka ɗauke kai domin duk ta ya mutse ta lalace abinka da zaman ƙauye ga kuma uban aiki da take sha ba hutu. A shekarar da ta gabata Mamy da Daddy sun zo don duba lafiyar y'arsu, yanda su ka same ta ba ƙaramin ɗaga musu hankali ya yi ba, a haka su ka koma su ka bar ta a gidan mijinta don ba yanda za su yi, amma Mamy ta sha kuka, ko da suka koma Abuja ma hankalinta bai kwanta ba, saboda haka ta duƙufa da yiwa Mimie addu'a, domin ta na jin soyayyar yarinyar har cikin jininta. Shima Daddy ya saka malam ana ta yiwa Mimiensa addu'a da roƙon Allah a kan ya kawo mata sauƙi a cikin rayuwarta, domin duk da ba ta faɗa masu komai ba, a yanayin da suka ganta ma ya isa shaidar cewa ta na cikin tasku. ®®®®™™™ Bayan dawowarsu daga Birnin Kebbi ne Daddy da Mamy suka shirya don zuwa dubo Sameer, saboda tun lokacin da ya tafi hankalinsa Daddy ya ƙi kwanciya, ga shi har ya gama masters ɗinsa shekara uku amma ya ƙi ya dawo gida sai ya cigaba da zamansa a Dubai, inda Daddy ya yi-ya yi ya faɗa masa dalilin hakan amma ya ƙi sai cewa da ya yi, ya ji daɗin zaman ƙasar ne shiyasa. Wannan dalilin yasa suka shirya yi masa zuwan bazata, dama already sun san ya na Abu-Dhabi kuma sun san address ɗin gidan don haka su na sauka kai tsaye suka wuce can ba tare da saninsa ba. Abin da su ka tarar ya matuƙar ɗaga masu hankali, wani irin shork ne ya kama su to yaushe rayuwar ɗan na su ta gurɓace haka ba su sani ba? Ƙarasawa su ka yi cikin falon kai tsaye, idanun Daddy su ka ƙanƙance, cike da masifa ya dubi su Zaroon da ke zaune rungume da y'an matansu su na aikata masha'arsu tare da shan barasa, ya daka masu tsawa tare da Faɗar "Get out from here nonsenses." Su kuwa kamar ba da su ya ke magana ba don ko kallonsa ba sa yi, abinda su ka saka agaba kawai suke yi. Ran Rajbir ne ya yi mugun ɓaci ya buɗi bakinsa ya ce "Who Are you?, Kai wanene da za ka zo ka na yiwa mutane shouting aka?" Sameer da ke gefe riƙe da kwalbar barasa ya na sha, shi ne ya taso ya na layi irin na y'an maye ya ce "Your highly welcome my Dad, Mamy i miss You alot." Cikin Muryar mashaya ya ke zancen har ya ƙara so gun su, Daddy ne ya kife shi da wani wawwan mari, luuu ya yi ya faɗa jikin Mamy sharaf, ya na mashalo Mamy kuwa sai hawaye take wani na korar wani, tsananin tausayin ɗan nata ne ke ratsa ta, a haka ta riƙe shi gam! Sai hawaye ya ke. Daddyn ne ya juya ya fatattaki su Rajbir da y'an matansu su ka bar gidan ya na ja masu Allah ya isa tare da yi masu gargaɗi akan kada su sake shiga rayuwar ɗansa. A buge su ka bar gidan ba arziƙi, ya juyo ga Sameer ya ce "....... Ga mai buƙata sai ya tuntuɓeni ta wannan number 08109634202 Follow me on wattpad@ummu inteesar UMMU INTEESAR CE❤️❤️❤️❤️❤️❤️ 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *A SANADIN KAMA* 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *DAGA ALƘALAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)* *MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH* *Y'AR GANTALI* *RIKICIN MASOYA* DA KUMA *A SANADIN KAMA* WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE AKAN NAIRA 200 KACAL GA MAI BUƘATA SAI YA TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER 08109634202 DON ALLAH IDAN KA SIYA KADA KA FITARMIN HAƘƘIN MALAKA NAWA NE *AREWA WRITERS ASSOCIATION* ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com *BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM* Page 5️⃣9️⃣↪️6️⃣0️⃣ Ya ce "Sameer yaushe ka lalace haka?, Wannan ita ce tarbiyyar da muka baka? Ka ban kunya Sameer! Ka ban kunya!!" Ya na gama faɗa ya zauna shirim kan kujerar falon ya na share gumi da handkerchief ɗin da ya ciro a aljihunsa, sai maimaita kalmar "Innalillahi wa inna'ilaihir raji'un ya ke." Mamy kuwa ƙara rungume ɗan nata ta yi sosai a jikinta tare da neman guri ta zauna shima ta zaunar da shi, ta saka hannunta ta na share ƙwallar dake idonta. Shiru ya ratsa na ɗan lokaci baka jin komai sai sanyin a.c haɗe da warin giya dake tashi a ɗakin. Can Sameer ya zabura da ƙarfi ya miƙe ya na dube-dube har ya kai ƙofar falon ya leƙa waje, sannan ya dawo ya na tangaɗi cikin Muryar maye ya ce "Mamy ina ku ka baro mun ita? Ta ƙi ta shigo ciki, ki ce ta

Chapter 10 of 15