an tsayar mun da miji amma soyayyarka ta na neman zame mana Barazana a rayuwar soyayyarmu..."
Saurin dakatar da maganar ta ta yi gudun ka da ta yi kwaɓa.
Sameer kuwa tsikar jikinsa ce ta fara tashi, hankalinsa ya dugunzuma ba ki na kakkarwa ya ce "Ke ma don girman Allah ki yi haƙuri Sweety wallahi ba zan iya rayuwa ba ki ba, ban san cewa kina da wanda ki ke so ba, da na yi yunƙurin hana zuciyata faɗawa tarkon soyayyarki, amma yanzu ba ni da zaɓi da ya wuce aurenki ina matuƙar sonki ba zan iya rayuwa ba ki ba."
"Nima haka Sameer ba zan iya rayuwa ba Bassam ba soyayyarsa a gare ni bata da iyaka, ko da na aure ka ba zan iya kallon ka a matsayin miji ba, sai dai yaya don haka ya na da wuya na iya maka biyayyar aure, ka ga kuwa zan rayu cikin halaka ne don Allah ka yi haƙuri ka sanar da Daddy ka janye."
Jikinsa ne ya soma kakkarwa bakinsa na ɓari zuciyarsa cike da damuwa ya ce "Sweety Wallahi ina son ki ban san yaushe na kamu ba, amma na sani cewa idan ki ka guje ni rayuwata za ta zama mara amfani, idan ma na rayun kenan, amma ba damuwa idan haka ne zai sakaki farin ciki zan yi ƙoƙarin aikatawa, domin ki rayu cikin farin ciki zan iya haƙura da nawa farin cikin"
Daga haka ya kashe wayar zuciyarsa cike da ƙunci ya zube kan tiles tare da dafe saitin zuciyarsa.
®®®®®®®®®®®
Ita kuwa bin wayar ta yi da kallo, haƙiƙa ya matuƙar bata tausayi domin ta san zafi da raɗaɗin so, amma idan ta aure shi tamkar ta daɓawa cikinta wuƙa ne, domin ita za ta cutu, saboda yanda ya ke jin bai iya rayuwa idan bata itama haka ta ke ji akan Uncle.
Da wannan tunanin ta ajiye wayar ta ɗoro Alwala ta fara karatun Alqur'ani, nan da nan kuwa zuciyarta ta fara yin sanyi.
®®®®®®®®®®®
Har zuwa lokacin Bassam bai san me ake ciki ba domin ta kasa sanar masa, sai dai da yawan lokuta ya kan gan ta cikin damuwa idan ya tambaya sai ta ce Bakomai, amma zuciyarsa ta kasa nutsuwa da hakan.
A kan haka ya shirya wata rana ya zo hira gidansu da dare.
Isowar Motarsa ƙofar gidan ya yi dai-dai da ƙarasowa motar Baba.
Hon drivern ya ke ta tsabgawa amma ba Alamar za'a buɗe gate ɗin, ganin haka ya saka Bassam ya yi saurin ƙarasawa ya shiga ta ƙaramar ƙofa ya zuge ma su gate ɗin, bayan sun shige ya mayar ya rufe, sannan ya ƙarasa gun don gayar da Baba.
Baba na fitowa ya nufi hanyar cikin gida ba tare da ya kalli Bassam ɗin ba.
Da mamaki Bassam ke binsa da kallo, ganin ya na neman shigewa ya saka ya ɓoye mamakinsa ya yi sauri ya tarad da baba ya ce "Barka da dare Baba."
"Yawwa Barka dai." Baban ya bashi amsa ba tare da ya kallesa ba, ya yi shigewarsa.
Shi dai mamaki ya gama cika sa tambayoyi ne fal a ransa ya rasa mai ba sa amsa.
Waya ya ɗaga ya kira Mimiensa, ya na nan tsaye cikin mamaki sai ga ta ta ƙaraso da murmushi a fuskarta ta ce "Barka da zuwa kyakkyawan mijina."
"Yawwa sannunki da fitowa sarauniya" Ya faɗa jiki a sanyaye.
Kujerun roba guda biyu ta ɗauko ta saka ma su acikin gate ɗin sannan ta dawo ta ce masa "bismillah."
Ƙarasawa ya yi ya zauna har yanzun dai a sanyaye ya ke.
Lura da hakan da ta yi ya sa ta kallesa ta ce "Uncle ya dai na ga jikinka a sanyaye?"
Murmushin yaƙe ya yi ya ce "Ka da ki damu ba wani abu."
Ganin ya na ƙoƙarin ɓoye mata gaskiya ya sa ta yi narau-narau da ido ta ce "Don Allah menene ko Babana ya gaya ma ka wani abun ne?"
Girgiza kai ya yi ya na faɗar "A'a bai gayamin komai ba, akwai abinda ya ke son ya faɗa kenan? Ko shiyasa na ga ya..."
Zaro ido ta yi ta ce "Don Allah me ya maka?."
"Bai mun komai ba, amma na ga ya sauya mun ina gaida shi ya na kawar da kai kamar na masa wani laifin, idan kin san dalilin haka ki gaya mun gaskiya na shiga damuwa."
Sunkuyar da kanta ta yi ta na ƙoƙarin goge hawayen da ya fara gangarowa a idonta.
Kafe ta ido ya yi kasancewar da akwai haske a gurin ya na ganinta sosai.
Sosai hankalinsa ya tashi ganin ta na sharar ƙwalla ya ce "Don Allah ki gaya mun menene?." Cikin raunin murya ya yi zancen.
Share hawayen ta yi sannan ta ɗago ta ce "Ina cikin damuwa sosai, haƙiƙa Soyayyarmu ta na cikin barazana, domin ana neman raba ni da kai ƙarfi da yaji kuma ni......"
Bata ƙarasa ba saboda sabon kukan da ya zo mata shi ma hankali a tashe ya dube ta ya ce ".......
Ga mai buƙata sai ya tuntuɓeni ta wannan number 08109634202
Follow me on wattpad @ummu inteesar
Ummu inteesar ce💔❤️❤️❤️❤️❤️❤️
👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻
*A SANADIN KAMA*
👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻
*DAGA ALƘAMIN RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*
*MARUBUCIYAR SOYAYYAR MEERAH*
*Y'AR GANTALI*
*RIKICIN MASOYA*
DA KUMA
A SANADIN KAMA
WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE AKAN N200 KACAL
GA MAI BUƘATA YA TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER 08109634202
IDAN KIN SAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA MUN, IDAN KA BIYA MA KUƊIN KARATU NE KA BAYAR, HAƘƘIN MALAKA NAWA NE DON HAKA BAN YARDA KA FITARMIN BA.
DON ALLAH A KIYAYE.
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*BISMILLAH RAHMANIR-RAHIM*
Page 3️⃣7️⃣↪️3️⃣8️⃣
Ya ce "Menene? Ki sanar da ni da gaggawa don Allah."
Cikin rawar murya ta ce "Ana so a raba ni da kai masoyina ta hanyar aurar da ni ga wani, don Allah ka yi wani abun."
Wa su sababbin hawaye ne su ka sake tsiyayowa daga idonta su na sartu akan kumatunta.
Cike da tashin hankali ya miƙe tsaye daga zaunen da ya ke ya na faɗar "Waye ke son shiga tsakanina da burina? Wa ake son ba wa ke?"
"Sameer ne ɗan gidan Alhaji Salman." Ta ba sa amsa.
Wata uwar zabura ya yi ya ce "What!? Dama ba don Allah su ke ɗauke da ɗawainiyarku ba, dama su na da wata manufa a kai kenan?"
Huci ya yi sannan ya koma ya zauna bai ce komai ba sai ma dafe kansa da ya yi da hannayensa.
"Meye mafita yanzu?" Ta jefo mai tambaya.
Ya ce "Mafita ɗaya ce ki samu baba ki sanar da shi ni ki ke so, ki tuna fa shekara biyu na shafe ina rainon soyayyarki a zuciyata, sai yanzun da ta yi ƙwari kuma za ki bari a raba mu?"
Cike da rashin madafa ta ce "Na sanar da su haka, amma sun ce ba za su iya yiwa Alhaji butulci ba, dole na haƙura da kai."
Dogon numfashi ta ja ta sauke kana ta ce "Mafita ɗaya ce ta rage mun, idan ina son fita daga wannan matsalar, sai dai abun da kamar wuya in iya..."
Har ya sare ya sallama cewa ba zai kuma yin farin ciki ba a rayuwa matuƙar a ka raba su, jin wannan zancen da ta yi ya saka ya yi saurin jefa mata tambaya "Wacce hanya ce ta rage? "
Ɗago idanunta da su ka fara sauya kala zuwa ja ta yi ta ce "Mafitar ita ce na kira Daddy na sanar da shi cewa ni kai na ke so? Domin ya gaya mun ba tursasawa na kawo wanda duk na ke so shi zai shige mun gaba a yi komai, wannan hanyar ita kaɗai ta rage amma ka san kamar da wuya na iya...."
Saurin dakatar da ita ya yi ta hanyar cewa "Kawai ki ajiye kunya ko jin nauyi ki aika ta idan ba so ki ke ki rasa ni ba."
Ya faɗa kamar mai shirin yin kuka sannan ya ɗora da cewa "Na yi mi ki alƙawarin zan kula da ke da dukkan ƙarfina, zan yi iya ƙoƙarina don kare ki a ko'ina, ba zan bari a cutar da ke ba."
Ya ƙarasa faɗa cikin raunanniyar murya, daga haka ya miƙe cike da karayar zuciya, ko sallama ya kasa yi mata kawai sai ya juya a hanzarce ya fice daga gidan.
Ta na ganin haka ta miƙe da gudu ta shige cikin falo idonta na ambaliyar hawaye.
®®®®®®®®®®®
Sameer kuwa tun ranar da su ka yi waya ta ƙarshe da Mimie ta sanar da shi ba za ta aure sa ba, ya ke cikin tashin hankali, abinci ma yanzu ba sosai ya ke ci ba, ya rage fita sai dai ya ƙule a ɗaki ya yi ta kukan zuci.
A ransa ya ke cewa "ya Ubangiji ga bawanka, ka san halin da na ke ciki, kai ka jarabce ni da soyayyarta, Allah ka sassauta mun raɗaɗin da zuciyata ke yi."
Mamy ce ta shigo ɗakin nasa ta Same sa kishingiɗe akan gado, kallo ɗaya za ka masa ka fahimci ya fara fita a hayyacinsa.
Cikin hanzari ta ƙarasa kusa da shi ta na faɗar "Menene Sam? Kamar da zan shigo na jiyo muryarka ka na magana, ga shi na ga kai kaɗai ne a ɗakin, akwai wata damuwa ne?"
Saurin ta shi zaune ya yi ya na ƙoƙarin ɓoye damuwarsa ta hanyar ƙaƙalo murmushi ya ce "Ba fa komai Mamy me ki ka gani ne?"
Kallon tuhuma ta masa sannan ta ce "Na ga ko abinci ka rage ci kwanan nan, sai aukin kulle kai a ɗaki,tabbas akwai wani abun, Ni fa mahaifiyarka ce, ni nafi cancanta ka sanarwa matsalarka kafin kowa."
Nannauyar ajiyar numfashi ya sauke ka na ya ce "Mamy na gaya miki ba komai ki yarda da ni, ni Ko me zan ɓoyewa mahaifiyata a duniyar nan?" Ya faɗa ya na riƙo hannuwanta.
"Hmmm! To shikenan, Nagode Allah tun da ba matsala, ni bari na tafi dama na zo duba lafiyarka ne."
Bayan fitarta ya ja dogon numfashi tare da kwanciya kan gadon ya na faɗar "Ki yi haƙuri Mamyna ba na so ki shiga damuwa ne, amma na tabbatar za ku iya rasa ni idan aka wayi gari Mimie ta auri wani, na san ba zan iya jurewa ba."
®®®®®®®®®®®
Mommy ce kwance a gadonta da dare, ta na tufka da warwara, hanya ta ke nema mafi sauƙi da za ta shigar da y'ar ta gidan Alhaji Salman, sannan ta na son ta tunkuɗe Zuhra da iyayenta daga wannan daular, domin tabbas idan ta rasa suma dole sai sun rasa.
Babban takaicin ta shine abinda ta ke gudu ne ya faru, domin zuwa wannan lokacin ta daina samun Alkhairai sosai daga gidan Alhaji domin da alama sun manta da ita, haka ma musaddiq ya ma daina zuwa gaida ta bare ta saka ran samun abun hannunsa, ga ta da tsinan nan kwaɗayin abun duniya, duk da gwargwado su na da irin na su kuɗin."
Ta na kai nan a tunaninta ta ja dogon tsaki tare da yin ƙwafa a ranta ta ce "Ku jira ni ɗaya bayan ɗaya zan ɗau fansa a kanku, mussanman kai Habu domin kai ne silar komai da ya faru, matsiyaci kawai."
Tsakin da ta yi ne ya farkar da Abban Ruma daga sumammen barcinsa.
Juyowa ya yi ya ce "Lafiya dai khady? Me ki ke yiwa tsaki a tsohon daren nan? Dama ba ki yi barci ba?"
Ya jefo mata tambayoyin a jere.
Fuskarta ba yabo ba fallasa ta ce "Ba na jin barcin ne, ina zuwa bari na je kitchen na sha ruwa." Ficewa ta yi daga Bedroom ɗin, zuciyarta cike da hassadar y'ar uwarta da tunanin hanyar da za ta bi ta ƙuntata mata don ta rama.
®®®®®®®®®®®
Bayan sati ɗaya ansha artabu da Mimie akan ta a jiye burinta ta zaɓi zaɓin iyayenta amma fur ta ƙi, yayyenta sun yi iya ƙoƙarin su gun nuna mata illar bijirewa umurni ko shawarar iyaye, yaya farida har misalai ta bata da aurenta da alƙasim wanda da can ba shi ba ne zaɓin ta ba, Abbansu ne ya zaɓa mata shi, da ta yi haƙuri ta yiwa mahaifinta biyayya sai ga shi yanzu ta na ganin alkhairan da ke tattare da auren.
Duk wannan misalin bai saka Mimie ta sauko ba, tuburewa ma ta ƙara yi a kan lallai ita sai zaɓinta soyayya ta riga da ta gama rufe mata ido, har bata iya hango illar saɓawa iyaye, tuni ta manta tarbiyyarta da tsananin biyayyarta ga iyayenta a da.
Har fushi sai da Mama ta yi da Zuhra na tsawon mako ɗaya ba ta kula ta, amma bai sa ta karaya ba.
Haka ma Abbanta ya daina kula ta daƙyar ma ya ke amsa gaisuwarta, a bangare ɗaya kuma ga Bassam ya daina kiranta tun lokacin da ta shaida mai ba za ta iya sanar da Daddy Ba ta son ɗansa ba, idan ma ta kira shi tambaya ɗaya ya ke mata, kin sanar da shi? Da ta ce a'a ya ke katse wayar.
Abu duk ya taru ya caɓe mata, ta shiga damuwa sosai, ga waec na ƙara matsowa amma ta kasa karatu.
Kuma ta kyautata zaton Bassam Ya na cikin wani hali na kaɗaici da damuwa.
Ganin idan ta yi wasa za ta iya samun matsala harma a bangaren karatunta, hakan ya sa ta yanke hukuncin kiran Daddy kawai za ta yi komai ta fanjama fanjam, koma me zai faru ya faru gwanda a yita ta ƙare kowa ya huta.
Tashi ta yi daga zaunen da ta ke a falo, ta shiga ɗakinta tare da ɗaukar wayarta ta dannawa Daddy Kira.
Ta na shiga kuwa ba ɓata lokaci ya ɗaga ya na faɗar "Assalamu alaikum daddy's girl ya ki ke?"
Jiki a mace ta amsa masa Sallamar tare da cewa "Lafiya qlau." Cikin raunanniyar murya ta ke magana.
"Subhanallah! Y'ata me ya same ki ne? Ya na ji muryarki kamar ki na cikin damuwa? Sanar da ni menene? Da alamar tashin hankali a muryarsa ya ke maganar.
Samun kanta ta yi da kasa ba shi amsa kawai sai ta fashe da kuka mai cin rai.
Ai kuwa Daddy ya ruɗe iya ruɗewa sai tambayarta ya ke yana fadyar "Innalillahi wa inna'ilahir raji'un! Me nene? Waya taɓa y'ar Daddy?"
Kara karyar mata da zuciya zancensa ya yi kawai sai ta kashe wayar, ta cigaba da gursheken kukanta.
Hankali a tashe ya kuma kiranta, ganin har sau uku ya na kira amma ta ƙi ɗagawa, hankalinsa ya sake dugunzuma kawai sai ya kira Mama a waya da har zai kira babba sai ya tuna wataƙil ya na gun aikin yanzu haka ya saka ya mayar da kiran a number Mama.
Bayan ta ɗaga sun gaisa ya ke tambayarta me ya samu Mimie ne ya ji ta na kuka?"
Mama kasa cewa komai ta yi, ya ce "Ki kai mata wayar na rarrashe ta." Jiki a mace ta ƙarasa ɗakin Mimien ta bata wayar ta fice a ranta ta na jinjina girman rashin kunyar yarinyar ashe har za ta iya kuma kiran Alhaji ta kai masa kukanta bayan ta ƙi jininsa? Gaskiya ƴaƴan zamani ba su da ta ido."
®®®®®®®®®®
Karɓar wayar ta yi cikin sanyin jiki da rasa makama.
Daddy ne ya ce "Y'ata idan har kin ɗauke ni matsayin uba ina so ki sanar da ni me ke damunki, na mi ki alƙawarin ko menene zan yi iya ƙoƙarina gurin samar ma ki mafita, idan kuma abun yafi ƙarfina sai na taya ki da addu'a."
Kalamansa sun ƙara mata ƙwarin gwuiwa ta na ji wannan shi ne lokacin da ya dace ta gaya mai matsalarta.
Sai ta buɗi baki za ta yi magana kuma sai ta kasa.
"Ina jinki y'ata."
Daƙyar da siɗin goshi ta buɗi baki ta ce "Dama baba ina da wanda.... Am dama... Dama...."
Ga mai buƙata sai ya tuntuɓeni ta wannan number
08109634202
Follow me on Wattpad @ ummu inteesar
UMMU INTEESAR CE❤️💛💚💙
👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻
*A SANADIN KAMA*
👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻
*DAGA ALƘALAMIN RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)*
MARUBUCIYAR SOYAYYAR MEERAH
Y'AR GANTALI
RIKICIN MASOYA
DA KUMA
A SANADIN KAMA
WANNAN LITTAFIN NA KUƊI AKAN 200 KACAL
GA MAI BUƘATA SAI YA TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER
08109634202
DON ALLAH IDAN KINSAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA MUN, IDAN MA KIN BIYA KUƊIN KARATU KAWAI KI KA BIYA HAƘƘIN MALAKA NAWA NE BSN YARDA KI FITARMIN BA.
________________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
*BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM*
Page 3️⃣9️⃣↪️4️⃣0️⃣
Kasa ƙarasawa ta yi sai ta kuma rushewa da kuka.
Iya tashin hankali Alhaji ya gani ranar rarrashinta ya shiga yi, sai da ta yi shiru sannan ya ce "Ki faɗa mun ko minene insha'allah zan samar maki shi ko ɗan farin cikinki."
Cijewa ta yi ta ce "Dama Daddy ina da wanda na ke so na aura tun kafin haɗuwar mu, shine su Baba su ka ce ba zan aure shi ba tun da ga yaya Sameer, kuma wallahi Daddy zan shiga matsala in har ban aure shi ba." Murya a raunane ta ƙarasa maganar.
Duk da cewa Daddy ya ji ba daɗi akan wannan maganar da ta faɗa ma sa yanzu, amma farin cikinta ya fiye ma su komai saboda haka ya ce "Ki kwantar da hankalinki y'ata, in dai wannan ne ba ki da matsala, zan kira babanku mu yi magana, daga yau Sameer ya janye shi ma nasan ba zai so damuwar yar ƙanwarsa ba, ya sunan surukin nawa ne?" Ya ƙarasa maganar da sigar zolaya.
Dariya ta yi cike da kunya ta ce "Bassam." Ta na gama faɗa ta kashe wayar ta na sauke ajiyar zuciya lokaci ɗaya wani nishaɗi ya dirar mata.
Number Bassam ta lalubo a wayarta domin ta ma sa Albishir mai daɗi.
Cikin Sa'a kuwa ta na kira ya ɗaga tambayar da ya saba yi mata yau ma ita ya yi.
Sai da ta yi ɗan murmushi sannan ta amsa masa da cewa "Albishirinka!"
Cikin rawar baki ya ce "Goro."
Ta ce "Yanzun nan mu ka gama waya da Daddy ya ce sun janye saboda farin cikina ya fiye ma su komai, ya ce ma zai kira Babanmu ya sanar mai."
"Kai! Alhmdulillah, gaskiya na ji daɗin wannan Albishirin naki, kin ga shikenan sai na turo magabata na a gama magana, nan da wata ɗaya a ɗaura mana aure." Ya faɗa.
Y'ar dariya ta yi sannan ta ce "Da wuri haka uncle?
"Ko ya yi nisa ne na rage? Ke yanzu irin wannan tashin hankalin da mu ka shiga kwanan nan da ba don Allah ya taƙaita ba ai da na shiga tara."
Dariya kawai ta ke masa bata kuma cewa komai ba, daga haka su ka cigaba da wayar su har zuwa lokacin da su ka kashe wayar.
®®®®®®®®®®®
Abuja
Mommy ce tsaye a kan Ruma ta na surfa mata masifa a dalilin ta ce ba zata gidan Alhaji Salman ta kwana ba, wanda hakan na ɗaya daga cikin shirin da Mommyn ke yi domin nemarwa y'arta muhalli a gidan.
"Haba Mommy! don Allah me yasa dole sai na je can na kwana, bayan Zuhra bata nan?"
Harara Mommy ta watsa mata ta ce "Kin ji ki da wani shashanci, yanzu ne lokacin da ya kamata ki shiga rayuwar y'an samarin gidan domin samun soyayyarsu."
Ita dai Ruma ban da kallon Mommy ba abunda ta ke, tuni Mommy ta sauya mata ta zama wata iriyar mace, saɓanin yanda ta san ta a da.
"Maza ki je ki yi wanka, ga wannan kayan su na ke so ki saka, ina nan ina jiran ki." Ta faɗa ta na miƙa mata wata arniyar doguwar abaya ɓaka wacce ta ji ado stone a gabanta.
Baki a hangame ta karɓa ta wuce cike da tsananin mamaki "to wai me Mommy ke nufi da ni ne?"
Bayan ta fitowarta ne Su ka je gidan Daddy ita da Mommy drivernsu ne ya kai su, a mota take mata huɗubar yadda za ta ɗauki hankalin samarin gidan.
Ita dai Ruma ba ta ce uffan ba har su ka ƙarasa gidan.
®®®®®®©©©
Daddy kuwa bayan sun kammala waya da Mimie ya kira Baba a waya ya ke sanar masa cewa Sameer ya janye daga neman auren Mimie, sa'annan idan za'a zo neman aurenta ya sanar masa.
Baba na jin haka ya rayo aransa tabbas wannan aikin Mimie ne ita kaɗai za ta iya faɗawa Alhaji wannan zancen..
Lallai yayan zamani ba su da ta ido, yau ko za su haɗu shi da ita ne, a kunyace ya karɓa masa da to, sannan ya sauka daga layin.
Miƙewa ya yi a fusace ya fice daga shagon kasuwancinsa (wanda alhajin ya siyar masa tare da bashi jari).
Kallon yaran shagon ya yi ya ce "Ni zan tafi gida ku kula da shagon, idan lokacin tashi ya yi ban dawo ba ku rufe."
Da to suka amsa su na masa sauka lafiya, Motarsa ya hau ya wuce gida kai tsaye, ya cika fam! Ba abunda ya ke so kamar ya buɗi ido ya gansa a gaban Mimie, tabbas yau sai ta fuskanci hukuncin abinda ta aikata, shi za ta zubarwa mutunci akan wani banzan yaro?
®®®®®®®®®®
Ya na gama faka motar ya shige falon fuskar nan a haɗe tamkar bai taɓa dariya ba.
Da Mama ya fara cin karo a falon "kira min Mimie." Shine kaɗai abinda ya faɗa.
Ganin yanayinsa ya bawa Mama tsoro, hakan yasa ta ce "Lafiya dai Alhaji?"
"Kira mun ita dai idan ta zo ai za ki ji."
Jiki a saɓule ta je ɗakin Mimie ta yi kiranta a lokacin suna maƙale a waya ita da Bassam.
Haka kawai ta ji gabanta na faɗuwa da jin wannan kiran, hijabinta ta sako sannan ta fito.
A lokacin tuni mama ta dawo falon, dama ta na isar da saƙo ta juyo don jin me y'arta ta yi.
"Sannu da zuwa Baba ga...."
Bata samu nasarar ƙarasa zancenta ba, saboda saukar wani gigitaccen mari da ta ji a kuncinta na dama.
"Mu za ki maida mutane banza ko Zuhra? Ashe ba mu isa da ke ba?...."
Ga mai buƙata sai ya tuntuɓeni ta wannan number
08109634202
Follow me on wattpad@ummu inteesar
UMMU INTEESAR CE❤️💚💙💙
👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻
*A SANADIN KAMA*
👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻
*DAGA ALƘAMIN RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU-INTEESAR)*
MARUBUCIYAR SOYAYYAR MEERAH
Y'AR GANTALI
RIKICIN MASOYA
DA KUMA
A SANADIN KAMA
WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE AKAN NAIRA 200 KACAL
GA MAI BUƘATA SAI YA TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER 08109634202
DON ALLAH IDAN KA SIYA KADA KA FITARMIN HAƘƘIN MALAKA NAWA NE
Page 4️⃣1️⃣↪️4️⃣2️⃣
"Zaɓinki ya fi namu koh?, To mun gode Allah ya saka da alkhairi."
"Ashe rashin kunyarki har ta kai haka? Ina tarbiyyarki, ina iliminki, ina biyayyarki duk ina su ka je ne?"
Mama da tuni kanta ya gama ɗaurewa, kuma har zuwa lokacin ba ta fahimci laifin y'ar tata ba, sai dai ta san cewa ba yadda za'a yi Malam ya mare ta ba tare da ta masa komai ba, domin shi ba fitinanne ba ne, ko faɗa bai cikawa yaro ba sai da babban dalili.
Kallonsa ta yi tace "Malam me kuma ta yi ne?" A cikin wani irin wani yanayi ta yi zancen.
Baba ya na huci ya ce "Kin san wai yarinyar nan kiran Alhaji ta yi ta gaya mai ba ta son ɗansa, saboda rashin mutunci?"
A razane Mama ta ɗago ciki na kyarma ta ce "Me nene? Lallai Zuhra kin baɗa mana ƙasa a ido, ke ba ki duba halacci da karamcin wannan mutumin a garemu ba, kika mai haka?"
Mimie da tun lokacin da Baba ya mare ta ta durƙushe idonta na tsiyayar da hawaye sai a lokacin ta iya buɗar baki daƙyar ta ce "Ku yi haƙuri iyayena, soyayyar Bassam ta makantar da gani na, na ga ku na shirin raba ni da shi ne, wanda idan hakan ta faru tamkar kun ƙwace makullin farincikin rayuwata kun yi wurgi da shi ne, sanar da Daddy shine kaɗai mafita kuma....."
Cikin tsananin fushi Baba ya daka mata tsawa "Ya isa haka!, Ki je ki yi abinda ki ke so amma ba hannuna a ciki."
Ya na gama faɗa ya yi fuu ya fice cikin fishi, bin bayansa Mama ta yi itama rai a matuƙar ɓace.
®®®®®®®®®®®
Bayan Mommy da Ruma sun je gidan Alhaji Salman, Mommy ta sanar da Mamy cewa ta kawo mata Ruma ne ta yi kwana biyu don ƙarfafa zumunci.
Sosai Mamy ta nuna jin daɗinta wanda daga gani iya fuska ne bai kai zuci ba.
Anan Mommy ta tafi ta bar y'arta cikin tunani da al'ajabi, huɗubar Mommy ta tuna lokacin da su ke tahowa a mota inda ta ke cewa "Ki buɗe kunnenki da kyau ki ji ni, ba shashanci zan kai ki ba, zan kai ki ne domin ki siye zuciyar ɗaya daga cikin samarin gidan, ga kayan nan na saka miki a jakarki idan kin je su na ke so ki dinga sakawa, kaya ne masu ƙayatar da kwalliya, duk ɗa namiji lafiyayyan da ya gan ki a cikin shigar dole ki burge shi, saura ya rage na ki ki san yanda za ki
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 7 Chapter of 15