aikinta rakiya, su na zuwa su ka direwa boka ita su ka yi nasu wuri.
anan fa Ma'u ta ga tashin hankali, tin ta na kuka da hawaye har su ka gaji su ka dena zubowa.
Bayan kwana uku.
a cikin ƴar bukkar Boka Barore su na zaune gabansa sai fara'a su ke yi da alamu dai duniyar ta buɗe musu, Ma'u kuwa ta na gefe ta haɗe kai da guiwa tsirit da ita.
Hajiya Laure ta ce "Boka ɗana ya takura mini akan hakan, ban san ya zan yi masa ba." Barore ya yi dariya sannan ya ce "Za mu rufe masa baki, ba zai ƙara hanaki yin abinda ki ke so ba" ta ji daɗin hakan ta yi masa godiya kana su ka miƙe, yau ma kwana uku ya basu su dawo.
Ma'u dai da kyar da kyar take iya tafiya, duk ta zama kamar sokuwa ba um ba um-um, su Hajiya Laure ma ƙyamarta su ke ji da sun kalleta sai su tsartar da yawu su yatsine fuska, da haka har su ka dawo gida.
Hajiya Laure ta yi Sa'a da su ka shigo gidan duk ba kowa a kusa don haka ta yi sauri ta balbale Ma'u da masifa akan ta je ta yi wanka ta dawo daidai, cikin yanayinta me kama da sokunta ta aiwatar da abinda Hajiya Laure ta ce.
Ba laifi ta ɗan dawo hayyacinta sai dai tana nan sukuti da ita.
Husnee na kwance kan gado ta na malelekuwa kamar yadda ta saba don kwanan nan aikinta kenan, Mommy ce ta ƙwala mata kira, ta amsa cikin muryarta da ta gama dashewa, Mommy ta ce "Zaman ɗaki da kwanciyar nan naki ya isheni ya ishi kakata INDO ba dole cuta ta ƙi warkewa ba ki na famar kwanciyar kamar ɗan malele? anyi allura ansha maganin amma abu ya ci tira, fito ni ki tayani girki ko kya ji ƙwarin jikinki."
Da kyar ta iya amsawa da "to" sannan ta yunƙura ta tashi ta na bibango sabida wani ɗan jiri-jiri da ke ɗibarta.
Ta na fitowa daga ɗakin daidai lokacin ƙullin asirin Boka Barore ya nufota gadan-gadan, ƙiris ya rage ya faɗa mata Razia ta faɗo kanta da ƙarfin gaske hakan ya sa ta ƙwalla ihu gami da faɗuwa gefe ragab, a take ta sassanƙare kamar gawar sababi. tsafin Boka Barore kuwa ya faɗi ƙasa ya ƙone ƙurmus tuni ya bi iska ya san inda dare ya yi masa.
Hankali a matuƙar tashe Mommy ta yo kanta ta na kiran sunanta, ta na taɓata ta ji ta sandare komai na jikinta ya dena aiki sai zuciyarta ce kawai ke bugawa, Addu'o'i ta fara jerowa ta na tofa mata nan fa hankalinta ya ƙara ƙololuwa wajen tashi ganin Husnee ta fara kanannaɗewa ta na wani irin lanƙwashewa kamar jikin tsutsa gareta, ma'ana dai tamkar ba ƙashi a jikinta.
Mommy ta fashe da kuka ta na ƙara karanto addu'o'i gami da janyota jikinta ta rungume ta na ƙoƙarin hanata lanƙwashewar sai dai kash abin ya ci tira.
Ta ɗebi kusan minti shidda cikin wannan halin sannan kuma jikin nata ya dawo daidai ya wani saki lakaf kamar gawar da ta samu ziyarta lahira yanzu.
wani azababben kuka ta saki ta na cewa "Mommy zan mutu kaina zai fashe wayyo Allah na" jin haka ya sa Mommy ta ƙara rungumota ta na cewa "Ki yi haƙuri Husna ai cuta ba mutuwa ba ce, ki yi ta addu'a za ki samu lafiya in sha Allahu." inaa kukanta kawai ta ke yi ba ji ba gani don ko fahimtar inda Mommyn ta dosa ba ta yi ba bare ma ta yi addu'ar, su na nan zaune Mommy na Kuka Husnee na yi har wani lokacin kafin ta saki kai ta kama ciki ta na kukan cikinta na ciwo, ita dai Mommy ta ga tashin hankali, Ayatul Kursiyyu gami da Suratul Baƙarah da sauransu take karantowa in ta saki wancan sai ta kama waccan gabaki ɗaya ta burkice.
Ta na cikin haka ta ji wani hucin zafi ya bugeta itama ta zame ta kwanta a wajen a sume.
Russlan ne ya yi dirar mikiya a wajen ko ƙasa bai sauka ba ya fizge Razia daga jikin Husnee su ka yi sama, nan take Husnee ta ji kamar cirar ƙaya sai dai ko yatsanta ta kasa motsawa ji take kamar an daddatsa ta da adda, idanunta ma kansu sun yi mata nauyin da ko buɗe su ta kasa yi, Mommy kuwa itama ta na kwance a sumenta ba me tashin wani tsakaninsu.
Su na cikin wannan halin Muneeb ya shigo fakam-fakam tare da sallama bai bari an amsa ba ya ci gaba da cewa "Mommy kin ganni da wuri yau fita zan yi." da yake hanyar banɗakin tsakar gida ya nufa sam bai lura da su ba sai da ya leƙa banɗakin ya fito da nufin ajiye wayoyi da tarkacen jikinsa kafin ya shiga wankan, nan fa idanunsa su ka yi alaragab da su a sheme.
cikin hanzari ya yi kansu ya na tambayar lafiya.
Ya na taɓa Mommy ya ji ta a sume zuciyarsa ta bada rimm!! idanunsa ya kai kan Husnee da take zubda ƙwallar wahala ita ma ƴar siriri take bin gefen idanunta, hankali tashe ya ce "Ke Husnee lafiya??" ba za ta iya magana ba don haka bai samu amsa ba.
Ruwa ya lalubo ya yayyafawa Mommy ai kuwa ta ja wani gwauron numfashi ta sauke ajiyar Zuciya sai kuma ta ci gaba da kuka ta na cewa "Ina Husna, kar dai sun ɗauke mini ita" cike da mamaki da tsoro Muneeb ya ce "Me ya faru Mommy?? su waye za su ɗauketa??" ba tare da ta dena kukan ba ta ce "Yauwa gwara da ka dawo, ashe da gaske Aljanu sun hau Husnee kar ka ga irin wahalar da su ka bata" ta yi maganar ta na ƙoƙarin tashi zaune, temaka mata ya yi ta Zauna, ganin Husnee kwance a kusa da ita ya sa farin ciki ya kamata, goge hawayen ta fara yi ta na cewa "Kalleta nan kar ka ga yadda su ka dinga cukurkuɗa ta kamar ba mutum ba."
sunanta ya kira ya na shafa gefen fuskarta cikin tausayawa, a hankali ta buɗe ido ta na kallonsa sai kuma ta ɓare baki ta kama kuka ta na cewa "Jikina ciwo ya ke yi ji nake kamar zan mutu!" ya ce ''Sannu kin ji, Allah i sauwaƙe ki dena cewa za ki mutu ai mutuwa sai lokacinta ya yi." Mommy ta ce "Ɗauketa ka mayar da ita ɗaki, laifina ne ni nace ta fito." ta faɗa ta na goge hawaye.
Rungumarta ya yi ya kaita ɗaki ya kwantar ya na ƙara jaddada mata sannu.
SHARE FISABILILLAH
Na Kuɗi ne....
Nomarl Grp 300 Posting ba kullum ba.
VIP 500 Posting Kullum.
domin ƙarin bayani 👉🏽09079885632
AN FARA PAYMENT
*©️INDO*
[8/21, 11:31 PM] INDO: *🪻SAHUN KEKE🪻*
Ep 15
©️
Ayeesha Abdulkareem INDO
*M.W.A🦅*
A ɓangaren su Russlan kuwa ya na yin sama da Razia bai zame ko ina ba sai gaban Uban Dawa, ya na zaune kan haɗaɗɗiyar kujerarsa ta zinare ya na jiran dawowarsu.
Russlan ya durƙusa a gabansa gami da cewa "Ga ta nan Father" cikin ɓacin rai Father ya ce "Razia! waye ya Ƴantaki daga ɗaurin da aka yi miki har ki ka fita?" Cikin shashshekar kuka ta ce "Risslan fa......" dakatar da ita ya yi ta hanyar ɗaga mata hannu, shiru ta yi ta na ci gaba da ɓarza kuka kamar za ra mutu don yinsa.
ba tare da damuwa da hakan ba ya ce "Maza a ƙara ɗaureta ba na buƙatar ƙara ganinta." Russlan ya ce "To" kana ya damƙeta ya mayar da ita keɓantaccen ɗakin da aka ɗaureta a wancan lokacin, ta na kuka ta na komai amma haka ya yi mata banza ya aiwatar da umarnin da aka ba shi don kuwa shi ma ta gama kaishi maƙurar ɓacin rai.
Akhiee abin duniya duk ya ishe shi, koda Russlan ya ba shi labarin abinda ya faru ya kasa ma bambance tsakanin Husnee da Razia waccece ta fi hauka, a gefe guda kuwa ya ji daɗin zuwan Razia kan Husnee don kuwa ta zo a kan lokaci tinda har ta yi silar faɗuwar tsafin da aka turo mata ƙasa.
Bayan kwana uku
Hajiya Laure da Hajiya Saudah an koma wajen boka ana ta murna don duk a tunaninsu haƙar su ta cimma ruwa, sai dai kashh yau ma kamar waccan ranar sai da ya tilliƙi dariya ya ƙoshi sannan ya fara da cewa "Aikin ku ya tarwatse!! hhhhhh!!!" Hajiya Laure ta zaburo ta na kallonsa sabida jin abinda ya faɗa, ganin ya na ɓaɓɓaka mata dariyar mugunta ya sa ta jefa masa harara ta bayan ido a ranta ta na cewa "Azzalumin banza" shan kunu ya yi kana ya ce "Wata shaiɗaniyar Aljana ce ta zo ta ce-ceta, hhhhhhh Barore ba ya taɓa karaya ba ya taɓa sarewa, dole ne sai mun cimma abinda mu ka sa gaba, hhhhh, ku ajiye kuɗi ku tashi, zan ta buga aiki har sai na yi nasara, da kaina zan kira ku indai buƙatarku ta taso, a duk lokacin da ku ka yi mafarkina to ku tawo ina nemanku!!!" su ka amsa kana su ka zube kuɗi su ka tashi.
Kamar yadda Hajiya Laure ta saba mita kullum yau ma ta yi akan ta gaji da ajiye masa kuɗi kuma ba nasara, Hajiya Saudah ta lallaɓata ta kwantar mata da hankali.
Ana kwana ana tashi gashi yau duk da faruwa abubuwan baya watanni biyu kenan.
Risslan ya samu lafiya tangaras har tabbai ma sun fara ɓacewa don shi jikinsa ba ya ajiye tabo da zarar ciwo ya warke tabo ma zai warke tamkar bai taɓa jin ciwo ba, tini har ya fara baɗaɗin zuwa duk inda ya so kuma ya koma ruwa harkarsa ta da sai ma abinda ya ci gaba.
Razia dai ta na can a ɗaure an ma manta da ita don in ba masu kula da ita ba ba wanda ya san ma inda take.
Husnee ma da sauƙi ta samu lafiya, ba yawan zazzaɓi da ciwon jiki irin na da sai dai har yau ba ta koma makaranta ba, sai kuma tunane-tunane ba dare ba rana kwata-kwata ba ta walwala kamar dai ba ita ba.
Tankar Yaƙi da me gidanta kuwa har yau suna tare
da yake ya san hannunsa sam bai nuna mata ta yi kuskure ba akan abinda ta yiwa yaransa har ɗaya a ciki ya mutu, sai ma haƙurƙurtar da ita da yake yi ya na kwantar mata da hankali, a gefe guda kuwa abinda ya ke nuna mata a zahiri ba shine a zuciyarsa ba, ya riga da ya ƙudurce ɗaukar fansa akan Risslan kuma ba zai iya fasawa ba, burin da ya ke son cimmawa shine kashe Risslan ɗin ita kuma ya mallaketa.
a ɓangaren Iyalin Risslan kuwa sun ci gaba da gudanar da lamuransu cikin kwanciyar hankali, su na aiwatar da duk abinda ya umarcesu kuma su na barin wanda ba ya so, shigo da Wiwi da sayar da ita kuwa ba kama hannun yaro ba abinda ya ragu sai ma ci gaba, ga ɓarna kamar ƴaƴan ɓeraye.
Rabi'u tuni ya koma wajen Ummansa ya na tayata aiyuka kuma ya na zuwa makaranta ya bar iskancin da yake yi da.
Su Hajiya Laure dai har yau ba a amsa kiran Boka ba, kuma gashi dai Risslan ya na ta yawatawa abinsa, da alamu har yau ba wannan nasara da su ke ta fata.
JD ne zaune kan hakimar kujerarsa ta alfarma ya babbaje ƙafafu ya turo uban tumbi gaba ya na waya da DCP Khashim, wani irin shauki ne ke ɗibarsa har wani slow yake yi a maganar don ba ya so ta ƙare "Na gama tsara komai, a gobe Kano za ta yi baƙo, kuma a cikin satin nan al'amura za su fara gudana, kai dai ka zuba idanu za ka ga yadda zan ɗauki fansata ta hanyar da sai an gwammace fito na fito aka yi da ni."
DCP ya murmusa cike da jin daɗi ya ce "Wannan ai kyakkyawan Albishir ne JD ni kaina ina buƙatar hakan don na gaji da ji da ganin labarinsa, idan mu ka kawo ƙarshensha hukuma za ta zauna lafiya ba ciwon kai, haka kuma za mu dinga harƙallolinmu cikin kwanciyar hankali."
JD ya yi dariya irin ta ƴan duniya kafin ya ce "To kai DCP Banda abinka idan wannan ya na raye a duniya ai hawan jinina ba zai sauka ba, kwantar da hankalinka kawai ni na dafe kan."
Tattaunawa su ka ci gaba da yi sannan su ka yi sallama kowannensu ya na ta farin cikin sun samo mafita.
Daren yau kwana ta yi ta na mafarkin Akhiee da kuma Makaranta don haka duk ta tashi hankalinta akan sai ta je ko za ta ganshi, Mommy dai ba ta hanata ba.
cikin riga da siket na atamfa tsadaddiya ta shirya sannan ta zura hijab ɗinta light blue ta futo.
Shi kansa Amadu ya yi mamakin jin cewar za ta je makaranta amma ko kaɗan bai nuna mata ba don ya lura ta zama Sarƙa me rikicin gangan, yanzu ya na yin magana za ta iya ɓare masa baki daga haka sai zazzaɓi da ciwon kai su hau.
Risslan ya na tsaye Hannunsa ɗaya riƙe da Wiwi ɗayan kuma ya riƙe kwankwaso, cikin salonsa me matuƙar burgewa da jan hankali ya ke zuƙarta ya na busarwa ba tare da wata damuwa ba.
Acibalbal da Zare su ka shigo Tafkeken ɗakin tare, bakinsu ɗauke da sallama, ba su jira ya amsa ba su ka ci gaba da zabgo masa kirarinsa kamar yadda su ka saba.
a hankali ya fara takawa ya juyo ya na fuskantarsu kafin ya matsa gefen gadonsa ya sa hannu ya ɗebi wasu haɗaɗɗun IV wato Katin Ɗaurin Aure.
Cikin ƙasaitaccen takunsa irin na namijin Zaki ya isa gaban Zare ya na Zuba masa rikitattun idanunsa.
Ganin irin kallo me tafe da saƙonni da ya ke aika masa ya sa zuciyarsa ta fara tsalle tin kafin ya ce abinda zai furta.
Miƙa masa IV ɗin ya yi gami da cewa "Duba wannan" ya yi maganar cikin sassanyar muryarsa me daɗi kamar busar sarewa.
Idanu a waje Zare ya karɓa ya shiga dubawa cike da fargaba da tashin hankali.
Kafin ya gama karantawa zuffa tuni ta fara yanko masa ta ko ina, Bai yu ƙasa a guiwa ba ya zame ya dire guiwoyinsa a ƙasa, kamar zai yi kuka ya ce "Sarƙa Wallahi tallahi ba laifina ba ne ba ni na sa su buga ba, ga Acibalbal nan nasan zai shaideni, Allah ɗaya kenan ba ni na sa su ba."
Akhiee ya ja wiwi ta tsarga masa kana ya furzo da hayaƙinta ta baki da kuma hanci, a ƙasaice yace "Ba kai ne da Alhakin buga IV ba ai, ni ne don kuwa ka na ƙarƙashin kulawata, soyayya ka fara ni kuma ba na buƙatar shiririta shi yasa na buga Iv a wannan Jumu'ar na ke so a ɗaura auren"
"Innalillahi wa inna ilaihirraji'un!!!" shine abinda Zare ya shiga maimaitawa cikin kaɗuwa da tashin hankali.
Shiru wurin ya ɗauka kafin Zare ya samu ƙwarin guiwar cewa "A yafe min Ya Babba, Wallahi Tallahi ban tashi yin aure ba yanzu, ni da ko kaina ba na iya riƙewa ta ya zan iya riƙon iyali? a bari sai nan gaba ba yanzu ba don Allah" tassss!!!!! Risslan ya kwasa masa wani azababben mari wanda ya sa taurarin azaba su ka shiga gilma masa na wucin gadi.
Sai da ya juya musu baya kana ya ce "Ba na son yaudara kuma ba na son shiririta, ka san ba aurenta za ka yi ba ina ruwanka da ita? meye haɗinka da soyayya?? Ba na so ko na lokaci ɗaya ku bari Mata su shigo rayuwarku, Mace ba komai ba ce face Rauni, itace Lagon kowane Namiji, Mace haɗari ce ga Mutane irinmu zamanmu babu su ya fi mana Alkairi akan tarayya da su, daga yau sai yau kar wanda ya ƙara saurarar duk wata Mace, duk wanda ya yi hakan kuma zan sallameshi sannan zan zare hannuna daga huruminsa bayan na aurar da shi na yi masa duk abinda yake buƙata."
Jiki na tsuma Zare ya ce "An gama Sarƙa me rikicin gangan!!, Ba za a kuma ba, ba ni ba mace daga yau, umarninka shine abin dubawata Oga, Na tuba ba zan kuma ba."
Jinjina kai ya yi kafin ya ce "A ƙonasu, a kawo mini Prince!" haɗa baki su ka yi wajen amsawa kana su ka bar fadar ta shi.
Su na kawo Dokin ya hau ya fice kai tsaye ya nufi makaranta.
Husnee na tsaye wajen famfo ita kaɗai tamkar Aljana ta yi zugum ta na tunaninsa kawai ta ganshi kamar an jefo shi daga sama, murza idanunta ta yi ta ƙara zaro su wai ko gane-gane ta fara yi, cikin sauri ta kora sunansa "Akhiee!!!" cakk!! ya tsaya shi bai yi gaba ba shi bai yi baya.
Yanzu ta tabbatar shine ba gizo idanunta ke yi mata ba, saɗaf-saɗaf ta ƙarasa kusa da shi cikin sanɗa, har lokacin ya na tsaye sai dai ko kallon inda take bai ba, a gabansa ta tsaya ta na fuskantarsa idanunta na kanshi ta na binsa da kallon yaushe gamo, murmushin farin ciki tuni ya gama mamaye fuskarta, cikin sanyin murya ta ce "Akhiee ciwonka duk sun warke, na ji daɗi."
Sai a lokacin ya kalleta sai kuma ya ɗauke kai, a miskilance ya ce "Na zata ba zan ƙara ganinki ba? me yasa ba za ki girmama maganata ba? shin ba na ce kar ki ƙara bari na ga fuskarki ba?"
Murmushi me tafe da hawaye ta yi gami da cewa "Hmm!!! Risslan kenan, ka yi tunanin don ka yi mini wannan kurarin zan iya rabuwa da kai kenan? abin da kamar wuya in iya ɓamɓare kaina daga gareka, ba yin kaina bane haka kawai na wayi gari cikin mugun hali dominka, da alama Ruhina ya na buƙayar kasancewa tare da naka domin samun salama; Akhiee ko da Mutuwa zan yi ina so in mutu dominka ko kuma in ce ma tare da kai, ba zan iya bin umarninka ba domin na riga na yi nisa ba zan ji kira ba."
"Idan kuwa haka ne ki na cikin wahala, kuma ki sani ba za ki yi tsawon rai ba indai har ba ki nisance ni ba, na fi samun kwanciyar hankali da ba na ganinki, ina so Ki ƙara ɗaukar hutu kamar yadda ki ka yi a wannan lokacin." ya yi maganar cikin ɓacin rai,
Ya na kaiwa nan ya raɓa kusa da ita ya na ƙoƙarin wucewa ya barta.
"Akhee!!!!" rinannun idanunsa ya ɗaga ya zuba mata alamar ya amsa, rintse idanunta ta yi zuciyarta na dukan sha-lugude kamar ana shirin yin yaƙin duniya na uku a cikinta, cike da jarumta ta ce "Akhee! Ina sonka" "What!!!! are you serious???" ya furta gami da ƙara tsareta da tsibbabbun idanunsa.
a hankali ta buɗe idanunta da su ka canja launi sabida tsananin fargabar da take ciki, murya na rawa ta ce ''Yes, I'm Serious, I Love You Akhiee!! ba zan ƙi gaya maka ba ko da hakan zai sa ka kashe ni" cikin tsananin zafin rai Akhiee ya yi taku uku zuwa gabanta, idanunsa masu bala'in kwarjini ya ƙara warewa akanta fuskar nan a murtuke kamar hadarin ya haɗo yake rugugi ya na shirin zubda ruwa, "Kin fara hauka kenan Asma'u?? ko kuma dama ke mahaukaciyar ce ban sani ba????" cikin hargowa ya watso mata tambayoyin. cike da ƙarfin hali irin nata ta jefa idanunta cikin nasa tana cije gefen leɓenta, cikin tsananin rurin azabar da zuciyarta ke yi ta ce "Yes!! ni mahaukaciya ce amma akanka na hau kace, idan ba ka fahimta ba zan maimaita ina son.....!!" tassss!!!!!! ya wanke ta da wani fitinannen mari kafin ta ƙarasa furta kalmar da take son furtawa, cikin hanzari ta dafe kumatunta gami da sunkuyar da kai ta runtse ido kanta ya na wani irin juyi kamar an buga mata baƙin ƙarfe, a hankali muryarsa mai cike da barazana ta yi nasarar dawo da ita duniyar mutane saɓanin wadda ta faɗa "Shin mahaifiyarki a ruwan koko ta haɗiyi cikinki ta haifeki a lokcin?? ko ki na tsammanin iyayenki ba sa ƙaunarki?? ashe ke mahaukaciya ce ba ki san ciwon kanki ba?? ni a rayuwata babu mace domin mace ta riga ta mutu, saɓaninta kuma kowace macen Duniya rauni ce!! ina me umartarki ki fita hurumina'' murmushin ƙarfin hali ta yi wanda ya yi daidai da zubowar zafafan hawayen da suka cika kwarmin idanunta, sassauta murya ta yi sannan ta fara cewa "Akhiee!!!!!! kenan sonka kuskure ne da har ka fara tunanin ba haifata aka yi ba?? shin wane laifi mace ta yi maka da kake yi mata wannan kallon? wadda ta mutu ta yaudareka ne??" shiru ya yi na kusan 5 second sannan ya girgiza kai gami da cewa "No!!, She's my mother, and my confidence!! Tin daga kanta aka gama mace.." za ta yi magana ya katseta da cewa "Relax Asma'u, Listen to me! a gidanmu har guba ana zuba min a abinci sabida in mutu don ba a son alaƙa da ni, meyesa ke za ki kawo kanki ga hallaka?? za ki mutu indai ki ka shigo rayuwata, kuma ba zan iya baki farin ciki ba, ni ba ni da shaukin So ko na wani abu ni ba namiji ne kamar kowanne ba ɗaukar rai kawai na sani bayan shi bansan komai ba, ba na so iyayenki su rasa ki shiyasa ba zan yarda ki shigo rayuwata ba, idan kika matsa kuma, madadin na bari wasu su kashe ki da hannuna zan kashe ki, kafin ayi da kai ka yi da kanka!!" murmusawa ta yi gami da gyara tsayuwarta. hallau cikin tausasawa ta ce "I'm very happy that it was you who will kill me. I'm listened to you, it's good to listen to me!"
Wani mugun tsaki ya doka cikin matuƙar ɓacin rai ya ce "I Don't have time for that!!" ya na faɗen haka ko kallonta bai ƙara yi ba ya juya ya nufi get ɗin tafkekiyar makarantar, cikin ɗaga murya Asma'u ta ce "Why Akhiee??" ko gezau bai yi ba bare ta san ya jita ya ci gaba da tafiyarsa.
har ya fice idanunta da ke faman zubar da hawaye tamkar an kwance dam na kansa.
"Me ki ke yi a nan??" muryar Sheikh Auwal ce ta karaɗe kunnuwanta, sai da nunfashinta ya ɗauke na wucin gadi sabi da tsananin tsoro da razani.
Rai a ɓaca ya ce "Ba magana na ke yi miki ba??"
Sai da kyar ta iya girgiza kai gami da magantuwa cikin muryar kuka, "Ba komai Ya Sheikh" "Don me za ki ce ba komai bayan gashi na ga ki na kuka?? wai ba na taɓa gargaɗinki akan shiga hurumin
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 19