Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ba ta bashi damar ƙarasa maganar ba ta ƙara kwarfa masa wani shegen mari wanda ya sa ganinsa ya ɗan ɗauke na wucin gadi, kamar za ta yi hauka ta ce "Kar na ƙara jin zancen banzar nan a bakinka! in ba haka ba zan yi abinda ba zai yi maka daɗi ba wallahi." sassautawa ya yi kafin ya ce "Asma'u Calm down cuta fa ba mutuwa ba ce, amma ba na so ki cutu sabida ni, zan so a ce kin rabu da ni kawai" "In dai ka na so hankalina ya kwanta ka bi ƴan uwanka su kai ka asibiti, in ba haka ba nima...." katseta ya yi da cewa "Na yarda zan je amma ki gaggauta tafiya gida." Daga haka ya raɓe ta kusa da ita ya wuce, a kusa da Sheikh Auwal ya tsaya ba tare da ya kalle shi ba ya ce "Mu je" Sheikh Auwal ya riƙe hannunsa su ka nufi wajen mota, su Yasayyadi Jameel da IP Khalil wanda aka gaiyato tin ɗazu su ka mara musu baya. a wurin Husnee ta zube ta na ƙara sakin kuka me tsuma zuciya. Zara ce ta dafa kafaɗar ta na ƙwalla ta ce "Na gode Husnee kin temakemu ba don ke ba na san ko me zai same shi ba zai taɓa yarda ya je ba, ki tashi ki tafi gida ki dena kuka anan kin ga mutane su na kallonki." Husnee ba ta iya cewa komai ba sabida kukan da take yi, sai da Zara ta yi da gaske sannan ta yarda ta shiga mota Amadu ya ja su ka nufi hanyar gida. har su ka isa ba ta dena kukan ba ta na shiga gidan ta wuce ɗaki ta faɗa gado ta ci gaba da abinta, Mommy da hankalinta ya gama tashi ta yi mata tambayar duniya amma ta yi banza, jikinta ya yi sanyi tuni ta fara tunanin ko dai da gaske Aljanu ne su ka shafeta. Tunanin Amadu Direba ne ya faɗo mata don haka ta yanke shawarar tambayarsa, ya na zaune ya yi jugum akan ɗan bencin me gadi ta iso wajen cikin sanyin jiki, gaisheta ya yi ta amsa ba yabo ba fallasa kana ta ce "Na ga Husnee ta shigo gida ta na ta kuka, na yi tambayar duniya ta ƙi yi mini magana." Amadu shima kamar zai fashe da kukan ya ce "Wallahi Hajiya tashin hankali ta gani wanda dole ta yi kuka, ko ke Hajiya in ki ka gani ƙila sai kin yi hawaye don mata kuna da rauni sosai." hankalin Mommy ne ya ƙara tashi, ta zaro idanu gami da cewa "Me ya faru ni Salamatu!" Amadu ya ce "Hajiya Yaron masu makarantarsu ne ƴan daba su ka sassare shi, kar ki ga yadda su ka yi masa jina-jina amma sabida zafin rai da gardama yaron nan sai ya ƙi a kaishi Asibiti, da kin ganshi kin san ya galabaita amma wallahi sabida taurin kai irin na ɗan daba sai ya ƙi, in ki ka ga jinin da ya zubar za ki koka masa Hajiya." Mommy ta ce "Ikon Allah, Allahu Akhbar Allah i bashi lafiya, kowa dai da irin ƙaddararsa shi kuma irin ta shi kenan! Allah ya bi masa haƙƙinsa in cutarsa su ka yi." Amadu ya ce "Amin Hajiya" jiki ba ƙwari ta koma cikin gidan, wajen Husnee ta koma ta zauna gefenta ta fara rarrashinta gami da kwantar mata da hankali. Ba su suka dawo gida ba sai ƙarfe 11:00 na dare, a hakan ma gado asibitin su ka so ba shi amma ya tubure ya ce indai su ka kwantar da shi duk sai ya ƙarasa sauran marasa lafiyan da suke tare jin haka ya sa su ka tarkata shi su ka dawo da shi gida. Sheikh Auwal da Zara ne su ka gyara masa Ɗakinsa su ka yi masa kyakkyawar shimfiɗa gami da ajiye masa abubuwan ciye-ciye na marmari kala daban-daban sakamakon jinin da ya zubar. Sauran mazan kuwa duk sun watse sai matayensu da matan Abhi da kuma sauran ƴan uwan nasa su ke ta leƙo shi, wasu su ce Allahi i sauwaƙe wasu su yar masa da magana su yi gaba. Shi dai ko kanzil bai furtawa kowa ba hasalima ba ya ɗora hankalinsa akansu don in ransa ya ɓaci duk zai iya yi masa illa. Da zazzaɓi Husnee ta kwana, amma hakan bai hana ta shiryawa don zuwa makaranta ba kasancewar ranar lahadi ce ba za ta je boko ba don haka ta shirya tin sassafe. Ta na fitowa Mommy ta ce "A'ah Husnee lafiyarki ƙalau kuwa? da zazzaɓi ki ka kwana fa har da surutai marasa kan gado amma yanzu kin ɗauki uban hijabi kin zurma kin ce za ki je makaranta, kya bari ai jikinki ya yi ƙwari." "Ni na ji sauƙi Mommy, ba zan iya zama a gida ba hakan shine zai ƙara mini zazzaɓin ma, don Allah ki barni in tafi Mommy. Mommy ta rausayar da kai kamar marigayin zakara gami da cewa "Allah i tsare sai ki kula sosai, ni ban taɓa ganin makarantar da ki ke so da ƙauna ki ka nacewa zuwanta irin wannan ba, Allah ne masanin abinda ke ɓoye a cikin hakan" Husnee dai ba ta ce ƙala ba tuni ta wuce hanyar fita. Ta yi sa'a ba ta yi karo da wani ba har su ka fice daga gidan ita da Amadu direba. "Innata ya jikin naki na ji Khausar ta ce ba ki da lafiya" ya faɗa cikin tausayawa "Na ji sauƙi Malam Amadu, don Allah ka kaini gidan su Akhiee idan ka sani. Durumm!! Bom ɗin zuciyarsa ya tashi sabida jin abinda ta faɗa, cikin sauri ya ce "A'a Innata ki shafa min lafiya in kai ki makaranta don nan aka sa ni in dinga kai ki." "Malam Amadu kai ma ka shafa mini lafiya ka kaini in ganshi ko hankalina zai kwanta, zazzaɓin da na ke yi kawai tunanin halin da yake ciki ne ya kawo hakan, kwana na yi ina mafarkai kala-kala akansa, har mafarki nayi ni ce me jinyarsa ina kusa da shi ina yi masa komai, sai da na farka na ga mafarki ne sai na ji haushi don na so ace da gaske ne. Amadu ya jinjina kai cike da tausayinta, zuwa yanzu ya lura gabaki ɗaya hankalinta ya koma kan Akhiee, me kuwa za a yi mata wanda ya wuce a tausaya mata, ta na da ƙuruciyarta da hankalinta amma za ta lalata ta hanyar wannan babban tantirin, abin da yake tunani a zuciyarsa kenan, a zahiri kuwa bai ce mata uffan ba. *************************** White diamond watch da ke hannunsa ya kalla kafin ya yi magana cikin muryar da ba hayaniya ba tashin hankali, "Asma'u Please! It's time for prayer, i'm going to the masque" "Please Akhiee you listen to me!" ta ƙarasa maganar gami da fashewa da kuka........ Fararen idanunsa masu tamkar nono ya zuba mata har na ɗan lokaci sannan ya ce "Kukan naki zan saurara kenan??" girgiza kai ta yi ta na ƙoƙarin goge hawayen cikin sauri, dandanan ta tsayar da kukan ta goge ƙwallar kamar ba ita ke kukan ba sai dai da an kalleta za a gane ta yi, ido ta zuba masa sai kuma ta rasa abin ce masa, sai da ya ce "Go ahead!" sannan ta yi zumbur ta sauke nannauyar ajiyar zuciya gami da tattaro dukkan nutsuwarta, cikin sanyin jiki ta ce "Akhiee ban san abinda ya faru ba ranar nan, na ji su Yasayyadi Usman sai tambayoyi su ke yi mini, na ga mutanen makarantar nan sai wani irin kallo su ke yi mini, gashi kai kuma ka ƙi zuwa bare na ji daɗi, ina ƙoƙarin zuwa makaranta kullum sabida in ganka, amma kai ba ka son ganina." Lumshe idanunsa ya yi ya buɗe a hankali ya ce "Za ki faɗi ne shine na yi ƙoƙarin tsayar da ke sai kuma na taka ɓawon ayabarki mu ka faɗa ƙasa duka, saɓanin fahimta ne sun yi zaton wani abu ne ya faru bayan haka, Asma'u ke ƴa macece kuma me daraja, ki na da hankali, tarayya da ni duk zai tarwatsa miki wannan, duniya za ta kalleki a matsayin mara kamun kai, iyayenki ma kansu ba za su so ki dinga kusantar inda nake ba, bayan haka ni kaina ba na so domin kasancewar ki a kusa da ni haɗari ne, every time wani abu zai iya faruwa da ke, takan iya bayuwa har ki rasa ranki ko kuma ki samu nakasar da ba za ki iya morar kanki ba ma, don Allah ki fita daga rayuwata." shiru ta yi ta na tunani kamar ta ɗauki abinda ya ce, jim kaɗan kuma sai ta murmusa sannan ta ce "Indai akan haka ne Akhiee ba ni da matsala, kowa ya zageni ko ya faɗi mummunar kalma a kaina, Allah shine me hukunci akan kowa kuma ya san me gaskiya ba zai hukuntani akan abinda ban aikata ba don mutane sun faɗa, zan yi farin ciki idan na zamo abokiyarka, ka yarda da ni Akhiee ban damu da rasa rai ba, don Allah ka barni na yi farin ciki." Girgiza kai ya yi cikin murya me kama da ta raɗa ya ce "Asma'u ki fahimce ni don Allah. ...." ba don ya gama faɗen abinda zai faɗa ba ta dakatar da shi ta hanyar ɗaga masa hannun, ƙara matsowa ta yi kusa da shi ta na zuba masa zaratan idanunta fuskarta ɗauke da murmushi me matuƙar kyau da ɗaukar hankali, cikin muryarta me zaƙi da daɗin saurara ta ce "Akhiee yau ɗaya ina son ganin dariyarka ina so na ga ka na yin abu kamar kowane mutum ." Rausayar da kai ya yi kafin ya ce "Ni ba mutum ba ne kamar kowa, kar ki sa ni dariya please" tattaɓe fuska ta yi a shagwaɓe ta ce "Ni fa ban yarda da hakan ba, ni dai yau ko ka yi dariya ko kuma in dinga kuka ba zan yi shiru ba kuma." "Akan wannan sai ki yi kuka? ko za ki jarraba in gani?" ya faɗa ya na kasheta da kaifafan idanunsa. Dire-dire ta fara yi tana gungunin kuka ta na ce "Ni wallahi ka bar tsokanata da gaske nake ba da wasa ba, in ba haka ba wallahi za ka ga abinda zan yi sai na kwana ina kuka kuma ko abinci ba zan ci ba." "Hmm!!" kawai ya ce ba tare da ya yi magana ba, ai kuwa ta taƙarƙare ta rushe da kuka har da dafe kai kamar an sanar mata iyayenta sun mutu. har ga Allah ma tsorata shi ta so yi don kuwa har hankalinsa ya gusa ya tafi wani tunanin, ganin yadda take ɓarzar kuka akan shiririta ya ƙara bashi damar gane lallai ba hankali ta cika ba, bai san ma lokacin da dariyar ta kufce masa ba, ya na dariyar ya ce "Na ce ƙuruciya na damunki amma kin ƙi yarda." Tsam!!!! kukan nata ya tsaya tamkar ba ta taɓa yinsa ba sai hawaye yare-yare akan fuskarta, idanunta kuwa su na kan kyakkyawar fuskarsa wadda ainahin kyawunta ya ƙara baiyana fiye da ko yaushe, wani irin haske gami da kyawu tsananin kyawu ta ga ya ƙara yi kamar ɗan aljanu. dariyar ta fara yi a take farin ciki ya lulleɓeta ta ko ina, cikin wata kasalalliyar murya ta ce "Akhiee! ashe zan iya sa ka dariya? hakan na nufin ina da muhimmanci a rayuwarka? amma a hakan ka ke tunanin zan iya juya maka baya?" Kallon kallo su ka shiga yiwa juna kowa da abinda yake tunani, shi sai yanzu ma ya tuna wai ashe dariya ta sa shi yau kenan ba lafiya gareshi, ya cika da zullumin ta inda iftila'i zai afko masa amma bai nuna mata alama ba. hankicif ya zare cikin Aljihunsa ya miƙa mata cikin tattausar muryarsa ya ce "Goge hawayen fuskarki, na san yau kin yi farin ciki, zan so ki ɗore da haka amma na san ba lallai ne ba, Asma'u in da hali ki tafi gida yanzu don Allah ba don ni ba." Ba don komai yake son ta tafi ɗin ba sabida ko ma me zai sameshi kar ya same shi ta na nan, don ya san sai ta tayar da hankalinta shi kuwa zai so farin cikin da take yi na yin dariyarsa ya ɗore har wani dogon zango. Karɓar hankicif ɗin ta yi ta goge fuskarta sannan ta miƙo masa ta na cewa "Ba zan tafi ba har sai an tashi, idan ba ka son ganina ne ba komi ba za ka ƙara ganina ba sai gobe, ka yarda?" gyaɗa kai yayi alamar "eh" a zuciyarsa ya yanke shawarar fita ya bar mata makarantar. Zara ce ta iso wurin ta na cewa "Sai kin daku a wurin Yasayyadi Muhsin, ba ki da labarin har an idar da sallah ko?" ido warwaje ta ce "Na shiga tara ni Asma'u! shi kenan na kaɗe wallahi ba na so a taɓa lafiyata." jan hannunta Zara ta yi murya ƙasa-ƙasa ta ce "Ai kuwa sai kin daku don kinsan haushinki su ke ji dama sabida ki na kula Akhiee" tsaki ta doka kafin ta ce "Ni wannan tijara Allah i kawo mini ƙarshenta, kawai don Allah ya jarabci mutum sai a ɗauki karen tsana a ɗora masa, ba kusan cewa tsangwamar mutum na sa shi ya faɗa wani mugun halin ba? ƙila ma baƙar masifar ƴan gidanku ce ta sa shi ya zama haka don kun cika jaraba." sam Zara ba ta ji daɗin furucin Husnee akan ƴan gidansu ba amma ba yadda za ta yi don su su ka jawowa kansu, ita ma kanta abin ya na ci mata rai irin ƙiayya ta zahiri da suke nuna masa, ko dan wasu daga ciki ba Uwa ɗaya suke ba?.. Su na sauka shima ya sauka ya bar makarantar, kasancewar yau ba a kan dokinsa ya ke ba a ƙafa ya ke tafiya cikin nutsuwa ya na yi ya na nazarta duk wani motsi da yake jin ya gilma. Mursali ya na ganin fitarsa daga makaranta ya tambayi malamin cikin ajin cewar zai je famfo ya sha ruwa, cikin sa'a ba tare da dogon bincike ba ya barshi ya fita duk da cewar ba a daɗe da komawa karatu ba. Ya na fita daga makarantar ya bi sahun Akhiee har ya gane hanyar da zai bi sannan ya tsaya, wayarsa ya zaro keypad ƴar kamfanin Airtel ya turawa Ɗan Kurada kira, ya na ɗagawa ya ce "Ya ne Idon Mikiyar Oga!" "Sai da kai Ɗan Kurada Gatarin saran nama ba! Sahun Keke ya fito daga makaranta yanzu, kuma ya yi hanyar Lungun Shege, ina fatan kun gama shirinku" "Hhhh!! Wihuhu!!!! ina yinka yaron nan, wallahi kai ɗan iska ne, Allah i kamaka Ɗan Mursali!!! yau Sahun Keke dole ne mu gane gaban sa da uwassa!!! wihuhu!!! Dodon Lunguwa uban ƴan sarari me nasara ɗan nasarawa!!!" Ɗan Kurada ne ke maganar cike da tsananin farin ciki. Ya na katse wayar ya dubi sauran riƙaƙƙun ƴan daban da suke tare ya ce "Ku shirya mu shiga Lungun Shege Sahun Keke ya tawo." Dukkansu ba wanda bai yi murna ba kuma su ka sa a ransu sai sun yi nasara akansa ko dan su ƙara samun shiga a wajen ogan nasu. Ba zato ba tsammani ya na cikin tafiya su ka yi masa da'ira sun kai su goma sha biyar kowa sai muzurai yake yi a dole jan wuya. Ɗaya bayan ɗaya ya ƙare musu kallo kafin ya ci gaba da tafiyarsa. Ɗan Kurada ya ce ''Kai ƙaramin Tsako duk ka tattaro ƴan yangu-yangun naka ku taru duk sai mun ga bayanku, Mun ƙara samun horo daga Oganmu kuma yanzu za'a fara wasan dolen doliya sai mun tureka mun gaje karagarka mun gaje duk wani iskanci naka, ka yi sake ɗan zaki ya girma, da ka ke nasara akan Dodon Ɓoye amma yanzu shine zai binneka!!" cikin kurari da cika baki Ɗan Kurada ke maganar, Akhiee dai bai ce musu komai ba, Ɗan Kurada ya ce ""Yara ku hau min kansa." Mutum biyar ne su ka nufe shi. wani ɗan buda ne a hannunsa, mutum biyu wuƙa kamu uku me azababben kaifi, ɗaya kuma dogon ƙarfe ne wanda aka yi masa wasu kibiyu cako-cako a jiki, ɗayan kuma Wuƙa ce me zarto samɓaleliya. Wata ƴar ƙaramar wuƙa wadda ba ta wuci tsayin ɗan yatsan tsakiya ba Akhiee ya zare gami da yin cikinsu. ta ko ina hari su ke kawo masa ya na kaucewa cikin zafim nama, duk idanunsu ya rufe kowa alla alla ya ke yi a ce shine zakara, ba su ankara ba Akhiee ya zame ya tsugunna da ƴar wuƙarsa, ba su ankare ba sai jini su ka ji ya fara tsiyaya daga ƙafafunsu ga azaba na ratsa su tin daga sama har ƙasa, kowa ya saki makamin hannunsa ya riƙe wurin ya na ihu. mugun yanka ya yi musu wanda indai ajalin mutum ya yi zai iya mutuwa nan take don kuwa kan jijiyar agara ne. Ganin haka ya sa hankalin Ɗan Kurada ya tashi nan fa suka afka masa su duka. faɗa ne ya kaca me a tsakaninsu wasu ya yayyanke su wasu kuma in ya kai harin sai su kauce. Ɗan Kurada ne ya shammace shi ta baya ya kafta masa sara da wata ƙatuwar wuƙa me kama da Adda sabida faɗi da tsayinta, dandanan wurin ya dare jini ya fara zuba kamar an yanka bujimin sa SHARE FISABILILLAH Na Kuɗi ne.... Nomarl Grp 300 Posting ba kullum ba. VIP 500 Posting Kullum. domin ƙarin bayani 👉🏽09079885632 AN FARA PAYMENT *©️INDO* [8/19, 11:04 AM] INDO: *🪻SAHUN KEKE🪻* Ep 13 ©️ Ayeesha Abdulkareem INDO *M.W.A🦅* A take wani irin duhu ya rufe masa idanu ganinsa ya fara ɗaukewa, hakan ne ya basu damar ci gaba da yankarsa; yanka uku su ka yi masa ƙwarara ya zube a wurin jini na shatata. su na ganin haka su ka ara a ta kare su ka bar wajen cike da farin ciki da murnar sun yi nasara. a sannu-sannu duhun da ya mamaye ganinsa ya fara washewa har ya buɗe idanunsa tangaras, cikin ƙarfin hali da tsaurin zuciya irin na shi ya miƙe ya na takawa a hankali a hankali ya nufi makaranta, kafin ya kai ga zuwa tuni waɗan da su ka ganshi a hanya sun je sun kwanzamawa su Sheikh Auwal nan fa duk hankalinsu ya tashi su ka bar cikin makaranta su ka fito wurinsa. Cikin tausayawa Sheikh Auwal ya ce "Akhiee maza mu je a kai ka Asibiti don ka na guƙatar temakon likita." Kamar ba shi da kunne haka ya yi don kuwa ko alamar ya ji ma bai yi ba, Yasayyadi Usman ne ya dubi Sheikh Auwal cike da takaicin baƙar gaddama ta Akhiee ya ce "Ka ga irinta ko? ya na ji fa ba wai ba ya ji ba amma sabida ɗan iska ne ya yi banza, ka je ka mutu ma mana ina ruwan wani?" Yasayyadi Muhsin ya ce "Ai shi dama hadari ɗaya ba ya yi masa ruwa, Kai Akhiee ka zo tin da girma da arziki a kai ka Asibitin nan don wallahi jini na zuba a jikinka sosai." Cike da zafin rai gami da zafin ciwo ya ce ''Ku ƙyaleni abina, ba ruwanku da ni tinda ba a jikinku ciwon yake ba kuma in na mutu ba ku da asara, duk ku watse ku ba ni wuri." Yasayyadi Jameel ya tausasa murya cikin sigar rarrashi ya ce "Yanzu ba lokacin wannan ba ne, duk ƙara ɓata lokacin da ka ke yi ƙara cutuwa ka ke yi, don Allah ka bar labarin yasayyadi Usman ka ƙyale surutansa ka zo mu je." wani dogon tsaki ya doka ba tare da ya ƙara ce musu ko kanzil ba, sai lumshe idanu yake ya na cije gefen leɓensa. Sheikh Auwal da Yasayyadi da sauran wasu daga cikin malaman har ma da maƙota sun taru akansa sai rarrashi su ke yi su na haɗa shi da Allah da Annabi amma ya yi kafus, ya ce murje shi fa allambur ba wanda ya isa ya kai shi wani Asibiti. Haka su ka yi ta fama da shi har Tashin hankali ma ya sa sun manta sun baro ɗalibai a ciki gashi har lokacin tashi ma ya wuce ana ta turnuƙu da shi. shi kuwa har lokacin girarsa ɗaya ba ta karayaba. Magriba ce ke shirin rufawa amma a yau MADARASATU NOORUL ISLAM ba alamun za a sallami ɗalibanta. Tin su na karatun da aka koyar da su cikin ƙwarin guiwa har su ka gaji wasu su ka fara yin shiru, ƙananu kuwa tuni wasu sun fara kuka sabida tsoro don sun yi tunanin anan za'a bar su su kwana. Husnee ce ta shafa cikinta da ke kukan yunwa kafin ta ce "Asiya wai lafiya kuwa? ace har yanzu ba malamin da mu ka gani bare ya sallamemu?" Zara ce ta leƙo tsakaninsu gami da cewa "Bari na je na duba ni dai wallahi na gaji a zo a sallamemu haba!" Husnee ta yi dariya ta na cewa "Yauwa ƙanwar masu abin jeki don Allah." Harara ta maka mata kana ta fice. Ba ta wani daɗe ba ta dawo hankali a matuƙar tashe, ganin haka ya sa zuciyar Husnee ta fara dukan sittin saba'in tamanin casa'in ɗari da hamsin! "Ƴan Daba ne su ka sassari Akhiee, jini sai zuba ya ke yi a jikinsa amma ya ƙi yarda a kai shi Asibiti, shine duk su ka taru a kansa, har babban Yayanmu ma ya zo amma ya ƙi Amincewa, kuma wallahi ya na shan wahala sosai jininsa zai iya ƙarewa" Ta ƙarasa maganar gami fashewa da kuka mai taɓa zuciyar duk wani me imani. Husnee ta na jin haka ba ta bi ta kan Zara ba ta falla da gudu ta yo waje. Turmutsawa ta yi tsakankanin mutanen da su ka yi masa da'ira wanda yawanci Yayyensa ne.......... Gaba Da tambaya su ka isa ƙofar gidan jikinta sanyi salam haka ta fito daga mota ta na ƙarewa tafkeken get ɗin gidan kallo, yadda gidan yake tamfatsetse idan na shiga ina zan fara tinkara? tambayar da zuciyarta ta ke yi mata kenan. Kamar Amadu ya sani ya ce "Innata shiga za ki yi da Bismillah ki na addu'ar Allah i haɗa ki da wanda ki ka sani kawai." Jinjina kai ta yi gami da sauke ajiyar Zuciya sannan ta nufi get ɗin gabanta na ƙara faɗuwa. Sallama ta yi a haraba ta na rarraba ido don ganin ta inda za'a ɓullo. Ji ta yi an amsa sallamar daga can gefenta ta yi saurin kai dubenta wurin, Hamza da Adamu ne zaune kan wata makekiyar tabarma sun tasa kofuna da fulas ɗin shayi gaba da alama karin kumallo su ke yi ko kuma za su yi. Danne fargabarta ta yi ta ɗan dubesu gami da cewa "Ina kwana!" duk idanunsu na kanta Hamza ya yi zaram ya amsa ya na fara'a. Cikin kame-kame ta ce ''Um!..in..ina ne... zan ga Akhiee?" Idanunsu ne su ka ƙara girma su ka yi kallon kallo cikin madarar mamaki, Adamu ne ya yi saurin shiga zancen da cewa "Waye kuma Akhiee ? daga ina ki ke meye haɗinki da shi??" baki na rawa ta ce "Muhammad Risslan

Chapter 7 of 19