matsayin Yayan Matarsa kuma kar ka bari aiki ya buɗe."
Muddassir ya ce "Kamar an gama ne Oga."
Da haka su ka yi sallama kowa cike da farin ciki da jin daɗi samun babbar dama a hannunsa.
Hajiya Laurenku da Hajiya Saudarku ana zaune gaban Boka Barore wanda ya ke ta tuntsira dariya da zarar ya kallesu.
Hajiya Laure sai Zare ido ta ke yi kamar an jiƙa Kuliya sannan aka zaneta, jikinta sai wata masharshara ya ke yi, cikinta sabida yamutsin tsoro da ya ke yi har ta fara jin gudawa.
Cakk!!! ya tsaya da dariyar sannan ya ce "Ya riga ya auretaaahhhhh!!" ya ƙarasa maganar ya na wata sabuwar dariya har da nuna Hajiya Laure da yatsa, hakan ya bawa gudawar da ta fara matsota damar zillowa, ta na so ta yi magana amma tsoro ya hana don ba ta san abinda bakinta zai furta ba, sai ido take zazzarewa da ka gani ka ga mara gaskiya.
Hajiya Saudah ce ta yi ta maza ta ce "Boka mun yi munanan mafarkai yau, sannan gashi mun zo mun ji ka ce ya aureta ba mu fahimci me ke shirin faruwa da mu ba"
"Ita Yarinyar da mu ke bibiya ya riga ya aureta kuma ya na bata kariya da iyakar ƙarfinsa, yanzu dama ɗaya ce garemu, iyayenta sun shigar da ƙararsa Kotu don haka za mu yi duk wani ƙulli wanda zai sa Kotu ta raba Auren, da haka ne za mu fi jin daɗin azabtar da shi mun san zai ji ƙuna idan wani abun ya sameta Hahhhhh!!" ya ci gaba da dariyarsa ta rashin hankali gami da mugunta.
Hajiya Saudah ta ce "Mun shiga tara, To Boka wai dole sai ita ba wasu da za'a bibiya a ciki ko ƴan uwansa haka?"
"Babansu fa Malamin Muslimci ne sun riƙe ayoyin Allah ba za mu iya nasara akansu ba, ta hanyar wannan yarinyar kaɗai za mu yi galaba akansa, kuma dole sai mun yi nasara, dole ne auren nan zai rabuuu!!"
cikin rawar baki Hajiya Laure wadda take jin tamkar ta fashe da kuka ta ce "A yi mana duba a ga auren zai rabu ɗin?"
Wata muguwar kururuwa ya yi tare da baza hannayensa, Su Hajiya Laure su ka toshe kunnuwansu sabida amon muryar ta shi da ta karaɗe kunnuwansu har tsakiyar ƙwaƙwalwarsu.
Wani Haske ne ya bayyana a tsakaninsu wanda ya kashe musu idanu dole su ka ɓuɓɓuya a cikin gyalensu, muƙit hasken ya ɓace sai Boka Barore zaune a mazauninsa, bai jira sun yi magana ba ya fara cewa " Mun samu Tabbacin dole sai sun rabu don haka za mu ci gaba da ƙoƙari, Kotu za ta raba su da temakonmu!!! sannan shi ɗin Ba Mutum bane zai ma iya kasheta da kansa, kuma shi ɗin ya na da mata!! kuma matar ta shi muguwa ce, zan tashi Aljana Tsigai daga bacci zan aikata wajen Razia za su zamo abokai ta yadda za ta ƙara zugata akan ta cutar da Kishiyarta, waɗannan matakan su ne maƙurar Manuniyata, ku ajiye kuɗin sadaukarwa ga Aljanu ku tashi ku tafiiiiiiii!!!"
Hajiya Laure dai abin Duniya ya gama tsumata, ba ta iya ɗakko kuɗin ba ma sai Haj Saudah ce ta janyo jakartata ta zube masa kuɗin da ta gani a ciki sannan ta miƙe.
Da ƙyar da numfarfashi Haj Laure ta tashi sabida ƙafarta da ta yi wani mugun sanyi tamkar ba a jikinta take ba, ga gudawar da ta yi ta fara ɓata mata jiki, da ƙyar da ƙyar take takawa tamkar ƴar shayi har su ka fito.
Sai a lokacim Hajiya Saudah ta lura da abinda ta yi ta sanya sallallami ta na tambaya, Da ƙyar Haj Laure ta ƙwaƙulo muryarta da ta maƙale ta ce "Tsoro ne ya sa ni sakin gudawa Saudah yanzu ina zan samu ruwa in gyara jikina?" Haj Saudah ta ce "Wannan ai abin kunya ne Laure! haba don Allah, Daga kin tsorata sai gudawa?"
"Tashin hankali fa ba a sa masa rana, ina na yi zaton haka? na riga na tsorata tin a mafarkin da na yi bayan haka ga shi yau da wasu alamu na firgirtarwa Boka ya zo mana, ga kuɗina da nake ta zuba masa, Allah ya sa dai a samu nasara a wannan karon" ta ƙarasa maganar kamar za ta yi kuka.
Hajiya Saudah ta ce "Sannu to, mu yi gaba ko za mu samu ruwa."
Haj Laure ba ta ce kanzil ba ta ci gaba da jan ƙafa. Su na cikin tafiya su ka yi arba da wata wawakekiyar Rijiya, Hajiya Saudah ta ce "ga ruwa ya samu, riƙe min jakata."
Haj Laure ta karɓa ta na mutsiltsila idanu, ba ta hana Haj Saudah zuwa wajen ba don kuwa ita tsoro ba zai barta ta je ba.
Haj Saudah na isa wajen ta kai hannu za ta taɓa Gugan da ke ajiye a gefen Rijiyar ta ji an doka mata tsawa da wata irin murya me rarrabewa, sun kai sakanni biyar su na jin muryar na yawo a dukkan kusurwoyin wajen.
Ai Hajiya Laure ba ta san lokacin da ta fashe da wani mashahurin kuka ba, Haj Saudah kuwa garin gudu har da tuntuɓe da shirin faɗuwa, a memakon ta tsaya wajen Haj Laure sai ta wuce ta nufi hanyar da za ta sadata da mota, Ganin haka ya sa Haj Laure ta bita bayan ta tattaro ɗan sauran ƙarfin da ya rage mata ta fara gudu jagwab-jagwab.
Sai da su ka isa wajen Mota sannan Hajiya Laure ta samu confidence ɗin bajewa a ƙasa ta na ƙara sakin wani kukann gami da cewa "Na shiga uku na lalace yau zan biyoka Alhaji Salisu, shi kenan tawa ta ƙare nima yau mutuwar zan yiiiihihihiii" ta ja ƙarshen maganar gami da gaurayata cikin kukanta.
Hajiya Sauda kuwa haki ta ke famar yi kamar Zuciyarta za ta yi tsalle ta fito ta baki, Sautin kukan Hajiya Laure ne ya ƙara faɗaɗa ta rintse ido kawai faɗi take "Ga su nan sun biyomu Na mutu na lalace, Salisu gani nan gareka, na shiga ukuuuuuuhh!!!!!"
Haj Saudah kuwa ta zama tamkar bishiyar da ta yi shekara da shekaru a wajen, hatta idanunta sun ƙame ta zubawa abinda ta ke gani ido da haka ta tafi shuuuu!!!! jikake yiffff!!! ta faɗi ƙasa a sume..................
(Su Hajiya Laure yau an taɓowa kai😂 Oo! Ni INDO🤣)
Madarasatul-Nurool-Islam
Sheikh Auwal na zaune kan kujerarsa da ke a Office ɗin Malamai, ya zuba tagumi, gashi dai a zaune amma hankalinsa ya yi balaguro, tunanin Akhiee wanda ya kwana biyu bai gani ba yake yi, ko ranar da yazo makaranta zuwan ƙarshe sai dai labarin ya zo ya samu amma bai ganshi da idanunsa ba.
Sallama ake rafkawa a bakin Office ɗin amma sam bai ji ba har sai da aka buga ƙofa sannan ya yi zaram ya na rarraba idanu.
Wani Matashi ne da ke a ɗaya daga cikin gidajen Layin yake ta ƙwalla sallama, sai da ya kuma yin wata sannan Sheikh Auwal ya amsa, gaishe shi ya yi cikin girmamawa sannan ya sanar masa cewar wasu bayin Allah ne su ka zo neman shugaban makaranta wato dai Sheikh Auwal Ɗin.
Faɗuwar gaba asarar Namiji......... Sheikh Auwal na jin haka ba tare da ya san dalili ba gabansa ya faɗi kwantsam!!! amma da yake akwai taurin Zuciya sai ya daddafe ya ce "A sanar musu gani nan fitowa."
Saurayin ya ce "To shi kenan!" sannan ya juyawa zuwa waje, bayan ya sanar wa Daddy da wanda suke tare ya wuce nashi wuri.
cikin tantama da shakku Sheikh Auwal ya fito, ganin Daddy ne ya sa Zuciyarsa ta ƙara tsinkewa.
Bayan sun Gaisa Mutumin ya ce "Ko za mu iya ganin Muhammad Muhammad?" Sheikh Auwal ya ce "A'a Kwana biyu ma bai zo Makaranta ba yau ma bai zo ba, Lafiya kuwa?" miƙa masa wani ɗan envelope ya yi gami da cewa "Daga Kotu, Iyayen Yarinya sun shigar da Ƙararsa akan Auren Ƴarsu da ya yi ba tare da sun sani ba, in ya dawo gida sai a bashi." cikin kaɗuwa Sheikh Auwal ya ce "Aure?? kuma Akhiee ɗin??" Daddy ne ya yi saurin shiga zancen da cewar "Shi kuwa, na kawo ƴata don ta yi Karatu amma an ɓuge ga Aureta, maganar gaskiya ba zan ɗauka ba dole ne ya saketa."
"Wai Husna?" Sheikh Auwal ya ƙara tambaya don tabbatarwa, Daddy ya ce "Ita ɗin fa"
Sheikh Auwal kamar ya fashe da kuka, a sanyaye ya shiga basu haƙuri gami da rarrashi, Shi dai Daddy kawai jinsa ya ke yi don kuwa gani ya ke yi duk da laifinsu don haka ya ke jin haushinsu.
Har su ka yi sallama su ka tafi ya na ƙara jaddada musu ban haƙuri, bayan sun tafi ya koma Office ya zauna. duk ya rasa abin yi, ji ya ke inama ƙasa za ta tsage ya shige sabida tsabar kunya da takaici da baƙin ciki.
Husnee:
kwana biyu da ba ta fita ba sai ta ji tamkar ta shekara da yake akwaita da son yawo. Yau dai ta rantse sai ta fita don haka ta dinga kiwon Mommy da Amadu. Ta na samun dama kuwa ta zumbuɗa Hijab ta fice, kai tsaye ta nufi Makaranta duk da cewar da ƴar tazara tsakanin yankinsu da yankin makarantar amma yau ba ta buƙatar a kaita a Mota don ta san Direban nata zai hanata fita.
Ta na cikin tafiya Tankar Yaƙi da Tawagarta su ka sha gabanta.
Ta na sanye da wani mugun ɗamammen wandon Jeans blue wanda aka tsatstsaga wajen guiwarsa sabida tsabar gayu, rigar kuwa ta ciki fara ce sol itama ta mugun kama jikinta sai jacket da ta ɗora ita ma ta jeans, sai farar bandana wadda iyakacinta goshi, tsefaffen gashinta wanda ke ta zuba ƙyalli ya yi watsa-watsa kowanne ya kama gabansa, hannunta ɗaya a Aljihun riga ɗayan kuma ya na kusa da bakinta ta na zuƙar Wiwi ta na busawa.
Wani irin taku ta ke yi me cike da izza, zarra, jin kai, ƙasaita, tamkar ita ce Queen Elizabeth.
Husnee ta kallesu ɗaya bayan ɗaya ta ga zaratan ƙarti sai zaro mata na mujiya su ke yi su na huro mata hancika tamkar bujimayen shanu, Zuciyarta ce ta fara tsallle tsoro da razani da firgici haɗi da tashin hankali su ka kawo mata ziyarar bazata.
JanKai ne ya kalli shugabar ta shi cike da ƙagarar aiwatar da mugun aiki akan Husnee ya ce "Ya kika ce Zinaru! mu hau kanta ne ko kuwa??"
Jin haka ya ƙara ɗaga hankalin Husnee idanun nan nata kamar an danne tinkiya za'a yanka sun firfito waje tsuru-tsuru, Tankar Yaƙi ta busa hayaƙi a ƙasaice ta ce "Saurin me ka ke yi, ku kawo mini ita nan."
Ta na faɗen haka su ka nufi inda Husnee take dama a tsakiya su ka sata, ba tare da tunanin ita mace ce su maza ba haka su ka cicciɓeta ta na ihu ta na komai su ka direta a gaban Tankar Yaƙi.
Zabgegiyar wuƙarta me kama da Adda ta karɓa a hannun Jankai ta goge ta sannan ta zubawa Husnee idanunta da su ka koma launin ja, cikin murya me ƙunshe da manufofi da dama ta ce.................................
Akhiee, Ɗan-Bakwai ne ya miƙo masa wayarsa da take ta tsuwwa, ya karɓa bayan ya ɗaga kiran ya sa a saman kunnensa, a ɗaya ɓangaren me kiran ya ce "Ni ne dai Abokin gabarka Inspector Khalil, ina zarginka da aikata kisan kai na wasu Ƴan Yara guda biyu bayan ka yi musu Fyaɗe kai da yaranka, ba wanda zai aikata hakan sai kai."
Cikin Nutsuwa Akhiee ya ce "Aikin ne ka rasa da za ka biyo ta bayan gida kuma?? Ka san ina yin ɓarna da yawa, ko za ka iya yi mini ƙarin bayani?"
"Sunan Ɗaya Zakiyya Ɗaya kuma Farhana, an tsinci gawarsu kuma bincike ya nuna sai da aka yi lalata da su sannan aka kashe su, ɗaya a ciki ma har da ƙwaƙule mata ido, Ba wani kwalo-kwalo da za ka yi mini na san kai ne ka aikata, kuma mu na nan mu na ƙara bincike akanka."
Akhiee ya ja tsaki kafin ya ce "Shashashan banza".
A fusace IP Khalil ya ce "I'm Police fa ni zaka gayawa maganar banza? wallahi ka guji shigowa hannuna sai ka gane kurenka wallahi, har ni za ka cewa shashasha?? I will arrest you wallahi"
"Faɗi da Hausa" Akhiee ya faɗa cikin salon rainin hankali, ai kuwa IP ya ƙara haurowa da Masifa da faɗe-faɗe ta inda yake shiga ba ta nan ya ke fita ba.
Sai da ya gaji ya yi low sannan Akhiee ya ce "In kun shirya kamani ɗin ina jiranku da kai da iyayen gidan naka, in ka tashi zuwa ka tawo da IG ma."
daga haka ya katse wayar ya na mamakim Sharri irin na ɗan-adam, an kashe masa Mutanen sannan za a ɗora masa sharrin aikatawa.
Waya ya ɗauka ya kira Rahma don jin Halin da Farhana ta ke ciki don ya san in su ka gane ta na raye ma wata sabuwar gwaramar ce.
Rahma ta na ɗagawa cikin Muryar kuka ta ce "Dama yanzu na ke son kiranka Ɗan Manya"
''Why"
Cikin dauriya ta ce "Ita ma Farhana Allah ya yi mata rasuwa". "What?? Farha is dead??" ya faɗa cikin kaɗuwa da razani.
Sake fashewa ta yi da kuka ta na cewa "Yes! kuma na yi imani da Allah ita ma haɗa baki aka yi da Likitoci su ka kasheta................
LAST FREE PAGES
(Mutanen Akhiee da na Husnee zan gani ko zan iya Ƙidaya adadin Ƙaunar da za ku nuna musu ta hanyar jin labarinsu har ƙarshe😍)
ƘARSHEN FEJIN KYAUTA
Na Kuɗi ne....
Nomarl Grp 300 Posting ba kullum ba.
VIP 500 Posting Kullum.
domin ƙarin bayani 👉🏽09079885632
LAST FREE PAGE
*©️INDO*
[9/5, 5:29 PM] INDO: *🪻S-K🪻*
Ep 21
Shiru ne ya ratsa tsakani na ɗan lokaci kafin ya numfasa, cikin tattausar murya wadda ba ta bawa me saurarenta damar fahimtar halin da yake ciki ya ce "Shi kenan Zulaihart ki dena damun kanki, ko ma waye Allah ya na kallonsa, ko da ba mu yi masa komai ba Allah zai hukuntashi a bisa laifinsa" ɗan tsagaitawa ya yi kafin ya ci daba da ce "Ba lallai na samu halartar Jana'izarta ba; ki Faɗawa Inna ba na so ƙananun Yaran nan su san abinda ke faruwa."
Zulaihart ta amsa da "To" gami da ci gaba da kukanta.
Ajiye wayar ya yi ya na ci gaba da tunane-tunane, ji yake kamar kansa zai yi tsawa ya tarwatse sabida tsabar ruɗanin da ya shiga.
Wata muguwar bugawa Zuciyarsa ta shiga yi, wadda ke tabbar masa ba lafiya ba, karaf Husnee ta faɗo masa a rai, idanunsa ne su ka ƙara girma sabida razani. Daidai lokacin Ɗaya daga cikin Dakarun Aljanunsu ya ƙaraso wajen bayan ya gaishe shi ya sanar masa halin da Husnee take ciki.
Rai ɓace Akhiee ya nufi wajen Tare da Dakare Adnanu.
"Yau zan kasheki in huta da ɓacin ranki!!! Shishshigin naki har ya wuce yi masa magana sabida ke mayya ce sai da kika sa ya aureki; yau taki ta ƙare sai dai in na kasheki nima ya kasheni"
Tankar Yaƙi ta faɗa ta na zazzarowa Husnee garadan idanunta da su ka ci kwalli kamar a ciki aka haɗashi, Fuskarta sam babu alamun wasa.
Zuciyar sai bugun sama da ƙasa take tamkar za ta zillo ta faɗo ƙasa, sake fashewa ta yi da wani irin kuka me cike da tsoro razani da rashin sanin abin yi ga uwa uba nadamar kuskuren da ta yi na fitowa.
Jikinta duk ya ɗauki karkawa kamar ana kaɗawa ɗan tauri gangi, magiya ta shiga yi mata gami da ban haƙuri akan kar ta kasheta, ita kuwa tamkar shaiɗaniya haka ta yi kunnen uwar shegu da ita, Zuciyarta ta riga ta ƙeƙashe sam ba ta jin wani ɗumi-ɗumin imani bare tausayi.
"Rufe mini baki kafin na soka miki wuƙar nan a ciki!" ta faɗa cike da tsanar Husnee.
a memakon ta yi shirun sai ta ƙara ɓarke baki ta na cewa "Wallahi ba zan kuma fitowa ba don Allah kar ki kasheni ki ƙyaleni ba zan kuma ba."
Tasss!!!!! ta wanketa da wani bahagon mari wanda ya sa kukan nata da maganar da takeyi su ka ɗauke a lokaci ɗaya, gabaki ɗaya wutar kanta ta tsaya cak!!, ba ta gama dawowa hayyacinta ba ta ƙara wanketa da wani zazzafan marin.
Husnee ta durƙushe kan guiwoyinta ta na girgiza kanta da ke wata muguwa hajijiya, a take gefen bakinta ya fashe, fuskarta kuwa ta yi kozai-kozai shatin yatsu sun fito raɗa-raɗa kamar sa yi magana.
Cikin rashin imani ta ɗaga wuƙar hannunta gami da kaiwa Husnee suka a gefen wuyanta.
Husnee ta rintse ido da ƙarfi gabaki ɗaya ta saddaƙar, cikin Zuciyarta kuwa Kalmar Shahada take maimaitawa.
Caraf!!! ta ji an riƙe hannun nata katamau sabida azabar matsar da aka yi masa tamkar ƙashinta zai tsage.
Wata ƴar ƙaramar ƙara ta yi gami da sakin wuƙar ta faɗi.
Juyowa ta yi a zafafe don ganin wanda ya riƙeta, rass! Zuciyarta ta buga yayin da idanunta su ka yi alaragab da na Rislan.
Yaranta kuwa su na ganinsa su ka fara gudun ceton rai sai waigawa ta yi ta ga babu su ba alamunsu.
Ta rasa yadda za ta yi don haka ta fashe da kuka ta na cewa "Wallahi indai ba ka Aureni ba sai na kasheta na kashe kowa nima na kashe kaina."
A fusace ya watsar da ita can gefe ta zube kamar kayan banza,
Ko kallon inda take bai kuma yi ba, Jiki na tsuma ya matsa inda Husnee ke durƙushe ta na wani marayan kuka.
Cikin zafin nama ya finciko hannunta ta kusa faɗuwa amma da yake ƙazamin riƙo ya yiwa hannunta sai ta tirje.
tatass!! tass!!!!! ya watsa mata wasu lafiyayyun maruka har guda biyu a jere, cikin mugun ɓacin rai da zafin Zuciya ya ce "Ban ce kar ki sake ki fitowa ba?? Na rantse da Allah ko me ya sameki sai ya samu Danginki, na rantse da Ubangijin da ya halicci Duniya akan danginki zan ɗauki Fansa; kuma indai ba za ki ji magana ba to za ki gamu da ɓacin raina."
Ido kawai take zarewa domin kuwa zuwa yanzu azaba da tashin hankalin da su ka mamayeta ba za su barta ta yi kukan ba.
Jan hannunta ya yi gami da cewa "Mu je na mayar da ke gidan; kin san Allah kika ƙara fitowa sai ranki ya yi mummunan ɓaci, kuma ni faɗar zan yi nake yi, ba na shan Alwashi, indai na ce zan yi to zan aikata ."
ba ta iya amsawa ba shima daga haka bai ƙara magana ba ya shiga janta kamar kara, sauri take yi iya yinta amma duk da haka sai tuntuɓe take yi kamar za ta faɗi sabida ya fi ta zafin nama.
Bai damu da ana kallonsu ba haka ya dinga ratsa layika da ita har su ka dawo Ƙofar gidansu sannan ya tsaya.
Idanu ya zuba mata tamkar me yi mata kallon ƙarshe yayin da hannunta ke maƙale cikin tafin nasa hannun.
Sun daɗe su na kallon kallo kafin ya kawar da kai, ya sassauta murya sannan ya ce "Asma'u in na rasa ki ne akwai tashin hankali, zan yi ɓarna sosai domin kuwa haukacewa zan yi!!! don Allah ki tayani kula da kanki kar ki bari a illata mini ke."
Ƙasa ta yi da kai ba tare da tace komai ba, sai a lokacin zafafan hawayen da ke kawo-kora a cikin idanunta su ka samu nasarar zillowa su ka yo wajen.
lumshe idanunsa ya yi gami da sauke nannauyar ajiyar Zuciya.
A hankali ya buɗe idanun gami da zubawa kyakkyawar fuskarta su, cikin wata irin murya me rikita lissafin me saurarenta ya ce "Da gaske nake Asma'u, ba na iya ɓoye miki sirrin Zuciyata, tabbas idan aka cutar da ke an yi mini Lahani, ki tausayawa Mijinki Asma'utah!!."
wani mugun haɗaɗɗen shauki ne ya ratsata ta ko'ina, ba ta san lokacin da ta Faɗa cikin faffaɗan ƙirjinsa ta na ƙara sakin wani sabon kuka me ƙunshe da wani salo da sirrin shagwaɓa ba.
Dimm!!! dimm!!! bugun Zuciyarsa ya ƙara sauya salo, hannayensa ya sa duka biyun ya zagayota gami da gyara mata kwanciya a jikinsa, cikin sassanyar murya ya ce "Ba na son jin kukan nan Asma'u, ko so kike Zuciyata ta karye??"
ba tare da ta dena kukan ba ta girgiza masa kai.
A hankali sautin bugun Zuciyarsa ya fara sauya mata tunani hakan ya sa ta yi shiru ta na sauraren Zuciyar tashi.
Jin ta nutsuwa ne ya bashi damar zaro wani siririn Diamond ring ɗaya daga cikin Zobuka goma da ke hannunsa, ya riƙo hannunta na dama ya zubawa zaratan yatsun natsa ido kafin ya zura mata shi a na kusa da na tsakiya, wato na kusa da ɗan ƙaramin yatsa.
Ƙoƙarin zamewa daga jikinsa ta fara yi amma ya ƙi bata dama, cikin muryarsa me sanya mata nutsuwa a duk lokacin da ta saurara ya ce "Kasancewarki tare da Zoben nan tamkar kasancewa tare da Mijinki ne, kar ki bari ya fita daga hannunki komai wuya komai rintsi."
Gyaɗa kai ta yi alamar eh, don haka ya ya buɗe hannayensa gami da cewa "To jeki gida, kar ki ƙara fitowa fa."
"To" ta faɗa tare da sauke nannauyar ajiyar Zuciya.
Ya na tsaye har ta shige gida sannan ya ɓace ya yi nasa wuri.
Hajiya Laure Da Hajiya Saudah.....
Wani haɗaɗɗen Saƙago su ka gani ya na tinkaro su, ya na tafiya cokal!! cokal!!! cokal!!!! da siri-sirin ƙafafunsa tamkar za su karye, sai uban kai rangwameme kamar zai rinjayi Wuyansa, gashi ƙwargwan-ƙwargwan zallar ƙashi sai tarin muni, ga ramin ido zuru-zuru ga haƙora kacar!!! kamar tsangayar ƙashi.
Wannan Dalilin ne ya sa su ka ƙara shiga Firgici bayan wanda suke ciki, har ya jawowa Haj Saudah suma.
Hajiya Laure kuwa kururuwa kawai ta ke yi idanunta a rintse.
Ta daɗe cikin wannan yanayi na tashin hankali da fitar hayyaci idanunta a rintse, bayan ta ɗauki lokaci me tsayi ba ta ji ta mutu ko kuma ta shiga hannun Saƙagon ba ya sa ta sassauta ihun da take yi ta fara buɗe idanunta da suka ɗaɗɗaure suke wata azaba tamkar an yi dakan Barkono a cikinsu, a hankali a hankali har ta buɗe idanun nata garas! ta shiga ƙarewa wajen kallo, ganin babu wannan saƙago ba alamunsa ya sa ta sakin ajiyar Zuciya wadda ta tawo tare da wani sassanyan kuka na daɗi.
Da rarrafe ta ƙarasa wajen da Haj Saudah ke kwance kamar gawar sababi, ta fara jijjigata ta na kiran sunanta amma shiru, wani sabon kukan ta saki ta na cewa "Wayyo Allah yanzu ya zan yi idan Saudah Mutuwa ta yi ai na shiga uku."
Zama dafa'an ta yi ta na rero baitin kuka kamar don shi aka kawota Duniyar. Bayan wani ɗan lokaci ne ta tuna da Motar da su ka zo ba za a rasa ruwa ba don haka ta tashi
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 14 Chapter of 19