Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
fa ni...ni..a..." kasa ƙarasa maganar ta yi sabida kuka da ke shirin kufce mata. Hamza ya karkaɗe mazaunar rigarsa ya miƙe ya na cewa "Abin ya ƙara girma kenan, bari dai in matso in ji yadda ake ciki." "Ƴar ajinmu ce ita, kuma ta zo duba lafiyarsa ne, Husnee sannu da zuwa mu je in raka ki wurinsa." Zara da ta iso yanzu ta basu amsar tambayarsu, kana ta ja hannun Husnee su ka kutsa kai ciki. Riƙe haɓa Hamza ya yu ya na cewa "Iyye? neman mata ma ya fara yi kenan? to Allah i sauwaƙe lallai Abhi ya haifi bala'i." Adamu ya taɓe baki ya na cewa "Ƙaddararre ni wallahi na so ma sun kashe shi kawai mu huta aikin banza, kullum sai ya yi mana baƙin tambari ya gada mana abin magana sannan ya ke jin daɗi, ya gama gurɓata kima da mutuncin Ahalinmu." Hamza ya ce "Ni ma da hakan ta faru ai sai na fi kowa murna wallahi, yanzu ga dai wannan yarinya har yarinya amma ya lalatata." Adamu ya ce "Umm! to ya za mu yi haka za mu suba ido har sai ya mutu sannan mu huta, ɗan wahala kawai." Masifa su ka ci gaba da zazzagawa kowa na tofa albarkacin bakinsa wanda yawanci ba alkairi su ke faɗe akan Akhiee ba. Sai da su ka ƙara shiga ciki Husnee ta ƙara tabbatar da girman gidan, sashi kala daban-daban ga ɗakuna rututu haka mutane yara manya maza mata duk gasu nan a hakan ma wasu sun tafi makaranta, matan gidan da ƙananun yara sun fi yawa sai samari su na ta shirin fita kasuwa. Ita dai kamar ɓarauniya haka ta ke tafiya saɗaf-saɗaf sai fiƙi-fiƙi ta ke yi da idanu kamar an tarfa munafuka. Duk wanda ya lura da su sai ya tambayi wacece da uwar safiyar nan ta zo musu gida musamman matan gidan, sai Zara ta yi zaram ta ce Ƴar ajinsu ce sai kuwa su taɓe baki. Da haka su ka isa can ƙarshen gidan. inda ba mutane wuri ne a ɗan kewaye wanda za a iya kiransa gida ɗan ƙarami me ɗaki ɗaya sai banɗaki da wani ɗan ƙaramin ɗaki wanda bai kai a kira shi ɗaki ba sai ɗan tsakar gida ba wani babba ba, wurin shiru sai iskar safiya da ke kaɗawa a hankali a hankali don kuwa wurin ya yi nesa da cikin jama'a sosai kwata- kwata bai alaƙanci wani sashi na mutan gidan ba. Husnee dai da bata iya gani ta yi shiru sai da ta kalli Zara ta ce "Ni ban taɓa ganin ƙi da tsangwama ba sai a gidanku, wato ɗakin nasa ma shine a can bayan gari inda ba mutane, wajen kwanan ma sai an nuna bambanci ko?" Zara ta ce "Ai ba laifina ba ne Husnee nima tinda na yi wayo a nan na ga ya na kwana tin kafin ya girma shima, ban sani ba ko shi ya zaɓi hakan ko su su ka zaɓa masa, amma ba me shigowa ma sai in baya nan ko kuma dai wani babban abu ya kawo mutum." Daidai lokacin Zara ta kutsa kai cikin ɗakin nasa tare da sallama, Husnee kuwa dakatawa ta yi domin a bata izini sannan ta shiga. Turus Zara ta yi ganin Wata kyakkyawar budurwa wadda ba ta wuce shekaru daidai na da na Husnee ba zaune ku sa da shi idanunta sun yi jajir sun yi ɓulu-ɓulu da zarar me hankali ya kalla ko ba a faɗa ba ya san kuka ta ci har ta godewa Allah, har yanzu ma akwai sauran hawayen akan dogayen gargasar idanunta. Akhiee kuwa ya na zaune bisa ƙaramin gadonsa wanda aka shimfiɗe shi da kyakkyawan bargo duniyar kuliya. abin ya bala'in bawa Zara mamaki don kuwa kaf shirin ɗakin da su ka yi ita da Sheikh Auwal an canja shi ciki kuwa har da wasu abubuwan irin su bedsheet pillows da sauransu. Idanu ya zubawa Zara alamar tambaya, ta yi ƙasa da kai zuciyarta sam ba daɗi ta ce ""Husnee ce ta zo dubaka shine na rakota." Juyawa ya yi ya zubawa ƴar budurwar ido a na yi mata wani shegen kallo me cike da alamomi daban-daban. Zirrrrrr!!! hawayen su ka ƙara biyo kan kumatunta. Tsaki ya yi kafin ya buɗi baki a hankali ya ce "Ta shigo kawai." Zara ta juya gami da cewa "Ki shigo Husnee" ba za ta iya komawa ba don haka ta ce "Ni kam bari in je wajen su Umma" gami sa yin gaba. Husnee ta ce "To" gami da turmutsa kai ɗakin tare da Sallama. a inda yake zaune a nan yake bai ko motsa ba, Husnee kam ba ta ga abinda Zara ta gani ba don haka ta ƙarasa gefen gadon nasa ta zauna ta na murmushi me tafe da ƙwalla. Ido ta zuba masa har na lokaci yayin da nasa idanun su ke a ƙasa ko ɗagowa ya kalleta bai yi ba. Cikin rawar murya ta ce "Akhiee! ba ka son ganina ko? ya jikin naka? ka yi haƙuri don Allah wallahi ba a son raina na ɗaga maka hannu ba jiya, hankalina ne ya tashi na rasa yadda zan yi don gani nake tamkar za ka rasa ranka." "Wannan bai ɓata mini rai ba a kan rashin jin maganata Asma'u, me ya kawo ki har gidanmu? shin bance ki fita daga rayuwata ba ne? kin ga abinda ya faru da ni jiya cikin ƴan mintuna ki sani idan ki na bibiyata watarana ke za'ayiwa abinda aka yi mini don za a ɗauka ne kamar ke wata ce a wurina." Hijab ta sa ta na goge ƙwalla cikin shashshekar kuka ta ce "Ina so in yi abinda ka ke so amma na kasa, Akhiee tausayinka da son kasancewa tare da kai ba zai barni na yi abinda ka ke so ba, ka barni kawai idan an kashe ni ka ga dole zan dena bibiyarka" "Ke mahaukaciya ce wai Asma'u? meye haɗina da ke da har ki ke tunanin a kashe ki a kaina? me yasa ba za ki yi ƙoƙarin gyara rayuwarki ba sai ki yi ƙoƙarin lalatata??" "To Akhiee kai me yasa ko na rana ɗaya ba za ka kwatanta zamowa mutumin ƙwarai ba? ba ni da wata alaƙa da kai amma akwai ƴan'uwantaka ta muslimci Akhiee ko dai kai ba muslmi ba ne? me yasa za a dinga haɗa ka da Allah akan abu amma ka rufe idonka? Akhiee!! indai ba ka zamo mutumin kirki ba to fa ba na jin akwai ranar da hankalinka zai kwanta, da ba ka shiga harkar banzar nan ba da babu wani ɗan ta'adda da zai cutar da kai, amma ka shiga harkarsu, ƴan gidanku duk malamai ne kai ɗaya ne ka zamo daban, ba ka jin nauyin yin kisa, ka ɗauki jini tamkar ruwa kwata-kwata zubarsa ba ta tsorata ka, ka yanki wancan ka kashe wancan Akhiee meye ribar wannan rayuwar? ka tarawa kanka maƙiya da masu son ganin bayanka, ƙarshenta fa haka za su yi maka kisan wulaƙanci mu da mu ka damu da kai kuma ka bar mu da shan wahalar rashinka; Akhiee!!! Ka yi min haƙuri amma ba zan iya fita daga rayuwarka ba ina son zamowa Abokiyarka, don Allah ka yarda da ni" ta kai ƙarshen maganar ta na wani irin kuka me tsuma zucuyar me saurarensa. Rintse idanunsa ya yi da ƙarfi gami da haɗe kansa da guiwa, zuwa yanzu ji yake kamar ya kasheta ya huta don kuwa ya tabbatar indai ba za ta fita daga rayuwarsa ba za ta sha baƙar wahala ta ko'ina. Sai bayan wani lokaci zuciyarsa ta ɗan lafa sannan ya ɗago idanunsa ya zuba mata "Asma'u Babana kawai na yarda da yiwa ƙarya, Babana kaɗai na ke iya saurara kuma na ke iya amfani da kalaminsa, sai dai ko shi bai taɓa sa ni dariya na yi ta ba sai ke Asma'u, ban sanki ba bansan wacece ke ba nan san daga ina ki ke ba, lokaci ɗaya kin shigo rayuwata kuma ki na son haifar min da matsaltsalu a cikinta, iya abinda ki ka samu a baya ki yi haƙuri da shi amma daga yanzu ki daure ki ɗauke kanki daga gareni, rayuwata rayuwata ce ba na jin za ta taɓa canjawa, ki tashi ki tafi." "Amma Akhiee ai....." dakatar da ita ya yi da cewa "Ba na son jin komai daga bakinki, na riga na gama maganata ki tashi ki fice mini da gani, ba na son ƙara ganin fuskarki haka ba na son ko da ƙara jin sunanki, da so samu ne ki yi mini tazarar da har abada ko labarinki ba zan ƙara ji ba, ki fita tin kafin raina ya ɓaci na yi miki abinda hankali ba zai ɗauka ba." miƙewa ta yi ta na tafiya da baya da baya idanunta da ke famar zubda ruwa su na kansa, wani irin abu ne ke turnuƙo mata tin daga ƙahon zuciyarta har maƙogoro hakan ya sa ba za ta iya cewa komai ba, yadda take shashshekar kuka kuwa ka ce duk ƴan gidan su ne su ka yi haɗari su ka mutu. Sai da ta fice daga ɗakin kana ta juya ta ci gaba da tafiya a hankali a hankali. a haka ta dinga ratsa shafukan gidan daban-daban ba tare da damuwa akan kallon da su ke binta da shi ba har ta fito waje inda Amadu ke ta safa da marwa cike da zullumin abinda zai faru da ita a ciki, ganin ta na wannan mugun kuka ya ƙara ɗaga hankalinsa ya shiga yi mata tambayoyi sai dai ko uffan ta ƙi ce masa. a ɗakin Akhiee kuwa Husnee na fita Razia ta bayyana a gabansa ita ma ta kafa aradun nata kukan, cikin shashsheka ta ce "Risslan ina raye kuma ina tare da kai amma ba ka taɓa yi mini abinda ka yiwa wannan yarinyar ba, ka faɗa cikin wannan halin ne fa dominta ka yi abubuwan da ba wanda ya taɓa saka ka yi su sai ita, ta ya-ya hankalina zai iya ɗauka? billahillazi huwar rahmanu Sai na kasheta indai ba ta gaggauta fita daga rayuwarka ba!!!, in ban kasheta ba kuma zan yi mata illar da duk duniya sai ta Zame mata tamkar wuta, da ita da danginta sai sun gwammace mutuwa ta yi akan irin izayar da zan yi mata." Jikinsa kawai karkarwa ya ke yi jijiyoyinsa jikinsa sun wani irin mimmiƙe sun firfito, kansa na wani irin juyi da gwamutsi tamkar karon Babbar mota da ƴar uwarta, Zuciyarsa wani irin tuƙuƙi ta ke yi wanda ya ke jin tamkar ba za ta ƙara minti ɗaya ba za ta yi bindiga ta tarwatse. Leɓensa na ƙasa ya kame ya cije gami da dafe kansa da dukkan hannayensa. ganin irin wahalar da ya faɗa bai sa Razia ta saurata masa ba, ta ci gaba da surutai cikin fitar hayyaci da tsananin ɓacin rai, baƙin kishi ya sa duk ta zamo tamkar mahaukaciya, ta daɗe ta na faɗar duk maganar da ta zo bakinta sannan ta gaji ta yi shiru ta ci gaba da zabga kuka. sai a lokacin Akhiee ya samu damar tofa tashi "Asma'u ba ta da laifi kuma muddin wani abu ya sameta sai na jefa ki a masifar da har ƙiyama ta tsaya ba za ki fita daga cikinta ba wallahi!!!! tashi ki bar min wuri kuma za ki je ki haɗu da Father." rikiɗaɗɗun idanunta ta zuba masa cike da tsananin mamakin furucinsa. Cikin tsawa ya ce "Ki tashi na ce!!! ko kuma ni in baki wuri!!!" Ya na rufe baki ta ɓace ɓat!! kamar ba ta taɓa wanzu a wurin ba. Zafi, ƙuna, raɗaɗi, ciwo, azaba, uƙuba, ba abinda zuciyarsa da kansa ba sa yi ya rasa ma abinda zai yi ya samu sassauci. Zabira da Laita Da sauran iyalin Akhiee su na zaune sun yi jungum-jungum kowa na tunanin halin da yake ciki, Rabi'u kuwa kuka yake ta ɓarzawa tin jiya da ya ga halin da Uban gidan nasa ke ciki tsoro da tashin hankali su ka hana shi sakatt, a kyauta Laita ta ba shi abinci amma ya ƙi ci sabida ya gama firgicewa, da kuka ya yi bacci da shi ya tashi, har kawo yanzu ma ya kasa denawa, su kuwa sai ƙara tsorata shi su ke yi, a take ya ji harkar daba ma gabaki ɗaya ta fice masa daga rai, nan take ya sa a ransa zai yi karatu tuƙuru kamar yadda mahaifiyarsa ta ke so zai watsar da dukkan wata shiririta. Zabira ce ta ɗan yi gyaran murya sannan ta ce "Wai yanzu zuba ido za mu yi kenan ba za mu ɗau fansa ba??" Gwaja ya ce "To in ba da umarnin Sarƙa ba wa zai yi hakan? sai mun je mun tambayeshi mun ji me zai ce" Laita ta ce "Ya kamata a gaggauta tambayarsa; anjima kaɗan ku shirya mu shiga gidan nasu." Salansa ya ce "Hakan ma za ayi, amma ya zama dole mu ɗaukar masa fansa ko ba ya so sai mun yi bai sani ba." Ɗan Bakwai ya ce "Asalin gaskiya kenan nima haka zan ce" tattaunawa su ka fara yi kowa na faɗen abinda ya kamata su yi. Tankar Yaƙi.......... (To sai gobe😒😒 su balolo har an baza kunnuwa a ji Tankar Yaƙi a wane Hali take😒🌝) SHARE FISABILILLAH Na Kuɗi ne.... Nomarl Grp 300 Posting ba kullum ba. VIP 500 Posting Kullum. domin ƙarin bayani 👉🏽09079885632 AN FARA PAYMENT *©️INDO* [8/19, 7:24 PM] INDO: *🪻SAHUN KEKE🪻* Ep 14 ©️ Ayeesha Abdulkareem INDO *M.W.A🦅* Kamar daga sama aka jefota haka ta faɗa ɗan madaidaicin Kangon da su Ɗan Kurada ke zaune su na ƙidaya kuɗin da Dodon Lungu ya basu na aikinsu, sai murna su ke yi kamar an yi musu Albishir da Aljanna. Ba wanda ya ankara sai ganinta su ka yi akansu, fuskar nan ta-ta ba annuri, cikin tsananin ɓacin tai ta ce "Wai har da kai za'a ci amanata a karɓi kuɗi a kashe wanda na ke so, to wallahi duk sai kun gane kurenku!" Ɗan Kurada ya yi saurin miƙewa ya na tausa kuɗinsa cikin wata ƴar lalita, cike da son kare kansa ya ce "Wallahi kin san dai ba yin kaina ba ne, Dodo ne ya samu kuma kinga aikinsa mu ke yi ba zai lamunce mu ƙi yi don ki na son Sahun Keke ba, wannan kuɗin ma da ki ka gani ba nawa bane na waɗannan ne" ya faɗa ya na nuna abokan aikin nasa wanda su ke zazzare ido kamar na mazarin tsire a kasuwa, sun tsorata da ganinta don dukansu ba wanda bai san halinta ba, ana cewa mace akwai tausayi amma ita ta fi wani namijin rashin imani. Ƙwafa ta yi kafin ta ce "Ɗan Kurada ka je don kanka kai ba zan taɓa ka ba amma tabbas sai na tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro." Jin haka ya sa sauran miƙe su na neman wajen tsira, a hankali ta taka ta doshi inda suke, baya-baya su ka fara yi su na bata haƙuri gami da bata yadda aka yi amma ko saurarensu ta ƙi yi, sai da su ka ƙure da bango sannan su ka dakata. Cikin dakakkiyar muryarta ta ce "Da ku da suwaye ku ka aikata??' Asabubu ya ce "Wallahi Ɗan Kurada ne babbanmu, sai wannan sai sauran yaran Oga, ni ba abinda na yi masa wallahi." ya ƙarasa maganar ya na yi mata nuni da na kusa da shi. Wata lafiyayyar wuƙa ta zare a ƙugunta ta na zuba musu idanunta masu ban tsoro, sai da ta goge wuƙar sannan ta ce "Ya zama dole ku ɗanɗana!!" ta yi maganar tare da ketawa Asabubu wuƙar akan cikinsa, ihu ya zunduma sabida azabar da ta ratsa shi har cikin ƙoƙon ransa, cike da rashin tausayi da imani ta ƙara kafta masa sara a kafaɗarsa hakan ya sa dole ya zube a wajen. Takawa ta yi da gudu ta bi ɗayan da tuni ya tsela a ta kare ya na neman ceto, kafin ya kai ga fita ta cimmasa, ta na danƙo shi ta shata masa yanka a hannunsa kan jijiyar gaɓar hannun ai kuwa jini ya ce salama alekum, riƙe hannun ya yi ya na wulwula shi cike da azaba, ba ta saurara masa ba ta burma masa wuƙar a ciki ta zareta gami da sa ƙafa ta harbatsa shi can gefe. Ɗan Kurada da jikinsa ke ta tsuma ta kalla ta na huci kamar wadda aka danne za'a yanka, "Wallahi Tallahi indai ka ƙara taɓa Sahun Keke sai na raba kanka da gangar jikinka, ka je ka gayawa Dodo na ɗauki mataki akan yaransa, duk hukuncin da zai yi mini ina jira, don Uwar babassa ko me zai yi ya yi, kuma daga yau na bar aiki a ƙarƙashinsa, nima ƴar kaina ce kuma ina da tawa dabar, ku iya takunku tin kafin na hallaka ku." Ɗan Kurada ya jinjina kai alamar ya fahimta, da kyar ya harhaɗo magana ya ce "Amma bai kamata ki bar ƙarƙashin Dodon Lungu ba, na san ma don kin yi haka ba zai ce komai ba." "Idan ma ya faɗa ba ni da asara ka je ka gaya masa saƙona." ta na gama faɗen haka ta fice fuuuuu kamar iska. Husnee Ko da Amadu ya kai ta makarantar cewa ta yi ba za ta shiga ba gwara ya kaita wani wurin idan lokacin tashi ya yi sai su koma gida. Cikin sanyin jiki ya ce "Innata ni yanzu ina zan kai ki don Allah?" "Mu je bakin titi kawai ka ajiye motar zan zauna a ciki" Amadu kamar ya fashe da kuka ya ce "Hakan fa bai da amfani ki yi haƙuri mu koma gidan dai tinda ba kya son makarantar." "Ba na son gardama don Allah kawai ka yi mini abinda na ke so." rausayar da kai ya yi sannan ya kunna motar gami da fara tafiya. Sai da ta kimanta lokacin tashi sannan su ka nufi gida, Mommy na harabar gidan ta na duba shuke-shuke su ka shigo, baki a sake ta tsaya kallon Husnee wadda ta yi jemai-jemai da ka kalla za ka gane a bala'in wahale take. "Ikon Allah kwanan nan dai duk in ki ka fita ba kya dawowa ƙalau, me yake faruwa ne??" Numfashi ta ja ta sauke shi tare da nannauyar ajiyar zuciya, cikin muryar da ke ƙara nuna tsantsar damuwar da take ciki ta ce "Ba zan ƙara zuwa makarantar nan ba har sai bayan wani lokaci." "Oo ni ƴasu, to dalilin me?" "Mommy Ba ni da lafiya kuma shine su ka doke ni, don Allah Mommy kar ki matsa mini akan hakan ki barni duk ranar da na yi niyya zan koma." Mommy ta rausayar da kai kamar kazar da ke jin yunwa, a sanyaye ta ce "Shi kenan, Allah i ba ki lafiya, dama ke ki ka zaɓi makarantar ai ba ni na zaɓa miki ba, ranar da ki ka ga dama kya je, kuma idan yayyenki su ka tambayeki dalilin rashin zuwanki sai ki san abin gaya musu." Gyaɗa kai kawai ta yi alamar ta yarda da hakan, ba ta ƙara cewa kanzil ba ta wuce ciki, tinda ta zauna ta doka tagumi ba abinda take tunani sai irin tsatstsauran matakin da Akhiee ya ɗauka akanta, a yanzu ba ta da zaɓin da ya wuce ta ƙaurace masa na wani lokaci, kuma ta dinga addu'ar Allah i yaye mata duk abinda ta ke ji akansa, tunane-tunanen da ta ke yi kenan gabaki ɗaya hankalinta ya tafi akai. Hajiya Laure da Hajiya Saudah ne zaune a gaban Boka Barore sai tsitstsilla idanu su ke yi sabida tsoro da fargabar abinda zai fito daga bakinsa. shi kuwa Dariya kawai ya ke tilliƙawa kamar an yi masa wahayinta, ya kai aƙalla minti biyar ya na yi sannan ya ci mur kamar ba shi ba, kallonsu ya yi ɗaya bayan ɗaya kafin ya fara magana ya na yi ya na zare musu munanan idanunsa, "A kwana uku na ce ku dawo, shine ku ka ƙi dawowa sai yanzu da ku ka yi niyya, to aikinku ya tarwatse, wadda mu ka turawa aikin a lokacin ta na tare da shi kuma ya temaketa ya hana aikin shiga jikinta, kuma ba ku dawo lokacin da mu ka ce ba kun tarwatsa komai, Shaiɗanun Aljanu sun Fusataaa!!!!" ya kai ƙarshen maganar tare da wani ƙaraji da gurnani tamkar mahaukacin zaki. Kallon Kallo Hajiya Saudah da Hajiya Laure su ka yi cikin tsoro da shakku kafin Hajiya Laure ta ce "Ranka ya daɗe Boka Barore me zamani, wallahi rashin lafiya ce ta kama ni ba zato ba tsammani kawai sai na tashi da cuta har ba na iya ko tashi zaune sai an temaka mini, amma yanzu na ji sauƙi shine fa na yi maza na garzayo, abin dai ya na raina amma tsautsayi ne ayi haƙuri manyan mutane" ta ƙare maganar cikin sigar rarrashi. "Hahahahahahaha! Ta baya ta wuce, za ayi aiki me wahala kuma za mu ƙara tura shi ne kan wannan yarinya, amma muddin ku na so aikinku ya yi kyau sai kun cike sharuɗana" Hajiya Saudah ta ce "Meye sharaɗin? ai tinda da akwai mafita komai me sauƙi ne Boka" ''Ina buƙatar yarinya ƴar shekara ƙasa da ashirin, za ku kawota gobe bayan ta yi kwana uku za ku zo ku ɗauketa, muna buƙatarta!!!!." Hajiya Laure cikinta ya bada wani ƙulululu!! ita duk irin wannan manyan asirce-asircen ba iya yinsu ta yi ba, abinda ta fi ganewa ƴar mallakar miji da ɗan abinda ba a rasa ba shima mallakar ba irin ta muguntar nan ba. Ganin ta ruɗe ya sa Hajiya Saudah ta ce "Za mu kawo Boka, indai za mu yi nasara dole ne za mu nemo mu kawo." Boka ya yi dariya me isarsa sannan ya ce su zube kuɗi ya sallamesu. Suna fitowa Hajiya Laure ta ce "Haba Hajiya Saudah, yanzu ina zan bi in samo yarinyar mutane in kawowa boka? haba a dinga tunawa fa a duniyar muslimci muke ba ta kafirai ba." Hajiya Saudah ta yi wani Shu'umin murmushi kafin ta ce "Hmm!! kin ɗauki duniya da wasa Ƙawata, ki na son ɗaukar fansar mijinki, amma ki na tsayawa sanya, samun budurwa ba wani abu ba ne ba fa, kuma ba wai kasheta zai yi ba kawai ina tunanin zai ɗan ci amarci da ita ne" ta ƙarasa maganar ta na dariya, ita ko a ƙasan silifas ɗinta. Hajiya Laure dai har yanzu abin bai yi mata ba, cikin sanyin jiki ta ce "To yanzu wa zan samu in kawo masa a goben nan?" "Ba ki na da Ƴar aiki ba? ƙila ma ba ɗaya ba to a cikinsu za ki zaɓa ki darje kawai ki ce ta zo ta raka ki, indai boka ne da ya gama abinda zai yi ya rufe bakin shegiya shi kenan." Hajiya Laure dai ba ta iya cewa komai ba sai tunane-tunane, wannan Damar Hajiya Saudah ta samu ta zizzigata ta kwantar mata da hankali har ta ji ta yi na'am da hakan. Washegari kamar yadda su ka shirya tin wuri Hajiya Laure ta ci ado ta gaiyaci Ma'u ƴar

Chapter 8 of 19