Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ƙarfin halin mayar da kayan ta na yi ta na sharce ƙwalla don kuwa ita ma abin ya taɓa Zuciyarta matuƙa gaya, kowane ɗan-adam idan ya ga waɗannan kaya kuma a ce sun samu ne daga wurin Akhiee sai ya dasa alamar tambayoyi ba ma tambaya ba. Bayan ta kammala Mayarwa ta koma kusada Husnee ta zauna, kafin ta yi magana a sanyaye "Anti Husnee ki yi haƙuri don Allah ki dena kukan nan, shi dama Akhiee haka yake, ko a karan kansa idan ya saka kaya sau ɗaya ba ya ƙara saka su, idan aka lissafa kayan da yake sawa yau da gobe kinga waɗannan ma ba komai ba ne, Ba sata yake yi ba don ban ga alamar shi ɓarawo ba ne, kuma ya na da sana'a sai dai sana'ar ta shi ba me kyau ba ce tinda Dilan Wiwi ne, yanzu ki kwantar da hankalinki idan ya dawo ki ce masa ya rage kayan ko ajiyewa ne ya yi a wani wurin in ya so in wasu suka tsufa sai ya kawo miki sauran kin ji?" ta ƙarasa maganar cikin sigar rarrashi, gyaɗa kai Husnee ta yi alamar ta gamsu da hakan, Zara ta ƙara da cewa ''Yawan kukan nan zai kawo miki wata larurar, don Allah ki rangwanta, kuma kar ki ce ba za ki yi amfani da kayanki ba don ransa zai iya ɓaci, kuma sai kin dinga lura don za a iya a dinga ɗaukar miki abubuwanki, Ni yanzu zan tafi in kwanta sai Allah ya kaimu" ta ƙarasa maganar tare da tashi ta nufi hanyar fita. Haɗe kai da gwiwa ta yi ta na sauke Ajiyar Zuciya akai-akai, a haka wani yamutsatstsen bacci ya yi tafiyar ruwa da ita. Ya na shigowa ɗakin ta yi firgigit ta buɗe ido sabida jin motsi da ta yi, ba ta yi zaton shi ne ba kawai sai ganinsa ta yi tsaye a kanta, ta zazzaro masa idanu ta na binsa da kallon tuhuma, ya buɗi baki zai yi magana ta katse ahi da cewa "Kai Ɗan fashi ne Rislan??" sai da idanunsa suka ƙara girma sabida jin tambayar tata don kuwa ta zo masa a bazata, cikin nutsuwa ya zauna a gefenta daga kan gado sannan ya ce "Ni ban taɓa sata ba Asma'u, ina da sana'o'i daban-daban, kuma bayan haka ina da masu yi mini komai ko da ba ko sisina a ciki." Cikin disashshiyar muryarta ta ce "To amma ba ka ganin wannan kayan da ka kawo mini zai jawo matsala? har da Diamonds da Golds fa? kuma ba kaɗan ba, ba ka ganin ma ɓarayi za su dinga shigowa gidan??" hannunsa ya ɗora a kanta ya na binta da wani sihirtaccen kallo, cikin murya irin ta raɗa ya ce "Ba wanda zai iya taɓa miki kayanki ko da a gidan yake in sha Allah." ta noƙe kafaɗa a shagwaɓe ta ce "Don Allah ni dai ka kwashe wasu sun yi yawa, nan gaba sai ka kawo mini sauran." "Kalleni!" ya faɗa a taƙaice, ɗago kai ta yi ta na kallonsa hakan ya bashi damar sanya idanunsa cikin nata "Zara ce ta faɗa miki hakan ko??" saurin girgiza kai ta yi gami da cewa "A'a, dama ko ba ta faɗa ba zan ce hakan, ni dai don Alla....." katseta ya yi da cewa "Ba na buƙatar jayayya! da ba ni da shi da ba zan yi miki ba, kuma kin fi ƙarfin hakan a wajena, idan kika yi mini haka ba zan ji daɗi ba, Please ki yarda da ni." kasancewar ya na da matuƙar tasiri akanta tuni jikinta ya yi sanyi ƙalau, ba ta iya cewa komai ba sai dai ta gyaɗa kai, sassanyar ajiyar Zuciya ya sauke sannan ya tashi ya nufi toilet domin watsa ruwa. Tankar Yaƙi!! Ɗaki ne shantalele babba amma ba kaya a cikinsa sai wata ƴar yaloluwar Katifa, a gefe ɗaya manyan jakunkuna ne wanda ake kira ganamazgo, duba da yadda suke a ƙoshe da alamu kaya ne a cikinsu. Ko fenti babu a Ɗakin, Silin ɗinsa ma wani wurin ya ɓaɓure har idon rana ya leƙo ta ɓulolin Kwanon saman silin ɗin. Ta na kwance akan wannan ƴar katifa magashiyan tamkar babu rai a jikinta, sai ka ƙura mata ido za ka ɗan cikinta me kama da bawon wanka sabida yadda ya rufta ya na motsawa alamar tana numfashi. Wata Matashiyar budurwa ce ta shigo ɗakin wadda da kaɗan Tankar Yaƙi za ta fita shekaru, hannunta riƙe da Robobi guda biyu irin na masu sayar da abinci, wajen Katifar ta nufa ta na magana cikin muryarta irin ta ƴan maye "Yaya ga Abinci nan na sayo in za ki ci, don ni yunwa nake ji, kuma ni ba Budurwar manya ba bare nace aai Shawarma ko Pizza." Sai a lokacin ta yi da gaske wajen juyo da fuskarta don ta kalli Ƙanwartata. Ina ruwan ranƙwal..... Cikin ƴan kwanakin da ta yi a kwance ba lafiya ta yi wata muguwar ramewa tamkar wadda ta shekara goma a kwance, ba komai ne ya jawo cutar ba face Aure da Rislan ya yi kuma ta rasa ta inda za ta shanyo kan lamarin har ranta ya yi sanyi, uwa uba jin Kotu ta amince da auren saɓanin tunaninta da take yi akan Kotu za ta raba, tana jin haka ciwo ya ƙara ƙaimi ya ce salama alekum. Cikin murya irin ta mara lafiya ta ce "Ki duba cikin baƙar jakata akwai kuɗi ki ɗauka ki sayo Taliya ki dafa mana, ki sayo kifi daga nan." Ta ƙarasa maganar a matuƙar wahalce, Siddiƙa ta ce "Sannu Yaya gaskiya kina shan wahala, gashi an yi maganin an yi Allurai kuma duk a banza." wasu zafafan hawaye ne suka shiga tsiyaya ta gefen idanunta, cike da sarewa da yanke tsammani da rayuwa ta ce "Ni ciwona ba me jin magani ba ne, Mallakar Rislan itace maganin idan ban sameshi ba ba lallai na tashi ba" Siddiƙa ta ja numfashi tamkar za ta yi kuka ta ce "Ai wuya ba ta kisa Yaya; ; amma gani nake tinda Dodon Lungu ya na sonki sosai gwara kawai ki manta da Rislan ki Aureshi, na san zai kula da ke sosai, Ummanmu kuma ni zan ci gaba da kula da ita ni ba sai na yi Aure ba ma." Tankar Yaƙi ta numfasa cike da tausayin kansu ta ce "Ba yin kaina ba ne Siddiƙa! da zan iya da tuni na yayewa kaina, domin a koda yaushe ƙara yi mini nisa yake yi, gashi ya fi ƙarfina ba ni da wani ƙarfin da zan iya juyo da hankalinsa gareni, gwara kawai na yi ta cutar har Allah ya ɗauki raina na huta, Ni dai fatana ko ba na raye ki kula da Umma, kuma kar ki fasa nema mata lafiya domin shi magani dace ne." Siddiƙa ta share ƙwalla gami da gyaɗa kai, ba tare da ta ce komai ba ta ɗauki kuɗi ta tafi sayo taliya kamar yadda Tankar Yaƙi ta faɗa. Yazeed, ana sallamo shi daga Asibiti ya aiwatar da abinda ya ce zai yi duk da cewar Haj Laure ba ta yarda ba, amma da yake ya fita tasiri a cikin Dukiyar dolen hakan aka yi. Da aka bincika an samu waɗanda suke bin Alhaji Salisu bashi sosai kuma duk an biya su, sannan aka kasafta Dukiya kowa ya ja ɓangarensa. Yazeed dai ba jira ana sallamar shi ya tarkata ya watsar duk abokanansa na banza ya shiga temakawa marasa ƙarfi tare da duk abinda ya kamata. Ma'u na tsugunne a bayan gidan ta buga tagumi da duk hannayenta, zaman cikin gidan jinsa take tamkar akan ƙaya don haka ta kewayo nan ko za ta samu sauƙi, ta na cikin tunani ta ji muryar Yazeed kamar daga sama "Ke kaɗai anan Ma'u?" sai da ta ɗan zabura don kuwa ba ta yi tsammanin ganin kowa ba, ta kalleshi kafin ta kauda kai gami da doka tsaki wanda ya sa shi ya fara raina kansa. Can gefe da ita ya tsugunna cikin sanyin jiki, hallau murya a raunane ya ce "Me yasa kike son ƙauracewa idanuna Ma'u? shin ban cancanci ki yafe mini ba? na san ni me laifi ne amma na dena wallahi, na dena shan giya kuma na dena neman mata har abokaina wanda ba na ƙwarai ba na rabu da su, Ma'u ki tallafawa rayuwa, ni maraya ne Ba ni da galihu, ki temaka min ki zamo silar tsayawar hawayena! ta sanadinki na fara tsaftatacciyar rayuwa idan kika kasance da tare da ni har abada Allah ne kaɗai ya san Alkairin da zan yi ta dalilinki, ki temaka min Ma'u" ya ƙarasa maganar ya na share hawayen da suka kasa jure zama a cikin idanunsa suka fara saukowa. Tin da ya fara magana idanunta na kansa, yau ne karon farko da kalamansa suka samu tasiri a Zuciyarta, haka kawai ta tsinci kanta da farin cikin shiryuwarsa, ba tare da ta sani ba murmushi ya suɓuce mata wanda ya yi daidai da zubowar hawayenta. Cikin raunin murya tace "Na ji daɗi da ka zamo mutumin kirki, amma hakan kai kaɗai zai amfana domin ni ba zan iya soyayya da kai ba bare Aure, in na yarda na aureka na cutar da kai domin bansan iya najasar da ke tare da ni ba, kuma ban dace da zamowa Sirika a wajen Mahaifiyarka ba don ba za ta taɓa ƙaunata ba, ni ma ba zan ƙaunaceta ba, ka ƙyaleni kawai na je can na yi rayuwata inda ma ba wanda ya san ni." da sauri Yazeed ya matso kusa da ita ya na cewa "An zo wajen! yau dai ki yi haƙuri ki ba ni labarin abinda ya faru da ke da har ya ke jefaki cikin irin waɗannan tunane-tunanen, shin ba kya da iyaye ne? me ya faru da rayuwarki? me yasa kika tsaneni? shin menene abinda mahaifiyata ta yi miki?" Girgiza kai ta shiga yi yayinda kukanta yake ƙara ƙarfi, cikin shashshekar kukan ta ce "Ba zan iya ba! ba zan iya gaya maka ba, da zarar na buɗe baki da nufin gayawa wani sai kaina ya fara ciwo, ba na iyawa, don Allah ka ƙyale ni" (Ba ni da lafiya🥺🥹) *©️INDO* An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 19 of 19