rawa yake sabida tsabar ɓacin rai kamar ya fashe da kuka.
Akhiee kuwa jin wannan furucin ya sa shi saurin ɗago gwarazan idanunsa ya zubawa Sheikh Auwal ba tare da ko ƙiftawa ba, Murtukekiyar Dorinar bulalarsa ya zara cikin rufewar ido na ɓacin rai ya shiga zabga masa ta ko ina ya na faɗin ''Dena kallona mara kunya!!!, har sai yaushe na za ka shiryu ka dena abinda ka ke yi??" ya zuba masa kyawawa aƙalla goma shabiyar a jere sannan ya tsagaita ya na huci tamkar an watsawa garwashi ruwa.
Ko uffan Akhiee bai furta ba haka kuma baiyi ko motsin kirki ba, sai dai ya yi ƙasa da idanunsa saɓanin da da ya yi wa Sheikh Auwal ƙiri-ƙiri da su.
Sheikh Auwal ya na ja baya, Sayyadi Muhsin ya ƙara ararsa, dukansa yake ba ji ba gani tamkar ba ɗan mutum ba, sai da daka iyayinsa ya gaji kana ya yi gefe, Shima Yasayyadi Jameel ya zabareshi.
Duk yawan malaman ba wanda bai dake shi ba sai dai wani ya fi wani yi da yawa.
Duka suka yi masa wanda in wani aka yiwa ba zai iya miƙewa daga gurin ba sai dai a ɗebe shi, in an ɗebeshin sai Asibiti don sai ya yi jinya.
Ba don sun huce takaicinsu ba dole su ka ƙyale shi don in su ka ci gaba da dukansa ma su za su ci gaba da shan wahala.
Akhiee kam ya na durƙushe a inda yake bai yi yunƙurin guduwa ko ramawa ba haka bai buɗi baki ba bare ya ce su yi haƙuri, ba za a ce dukan baya shigarsa ba duba da yadda fuskarsa ta yi wani irin jaa, idanunsa kuwa sun rikiɗe sun canja kala sunyi murtuk, farar Jallabiyar jikinsa ta sirka da jan jini sabida farfasa masa fata da su ka yi.
Mutanen aji kuwa tamkar ba a taɓa halittarsu ba, sun yi tsitt wasu na kuka wasu hawaye wasu kuwa da yake sun saba gani ba su yi kukan ba sai dai jiki ya mutu liƙis.
Cike da kyara Sheikh Auwal ya ce "Tashi ka fice min daga aji ba na son ganinka!!!"
miƙewa ya yi tangargar kamar ba shi aka yiwa wannan mugun lahanin ba, bai ce kanzil ba ya fice daga ajin, inda ya ke tsaya da ya koma ya tsaya idanunsa a ƙasa, zuciyarsa na wani irin tuƙuƙi da ruri tamkar za ta tarwatse, hannu ya sa cikin aljihunsa ya zaro haɗaɗɗiyar Wiwinsa tare da leta, ya bata wuta ya fara zuƙar abarsa ya na fesarwa cikin salo da ƙwarewa.
Sheikh Auwal ya ma rasa abin yi don haka ya yi wa ajinsa addu'a cikin gaggawa ya tashe su.
Husnee wadda take kuka kamar an sanar mata mahaifinta ya mutu ta miƙe da ƙyar ta na jan ƙafafunta da su ka yi sanyi su ka maƙale ta nufi hanyar fita, a tsawace Sheikh Auwal ya ce "Keh!!! kukan me kike wa mutane??"
Kasancewar tsoronsa ya gama kafa sansani a zuciyarta ba ta san lokacin da ta tsayar da kukan ba, cikin sauri ta ce "ba komai"
"Dawo ki zauna dokar makarantar nan ba a fita ana yi mana kuka, ko kuma ki tafi ajin sama a ci gaba da karatu da ke."
baki na rawa ta ce "Zan je saman" a cewarta da ta zauna tare da wannan azzalumin gwara ta je ajin saman ta ci gaba da karatu.
Ƙafafunta na karkarwa ta hau sama, ta zo giftawa kenan hayaƙi gami da warin wiwi su ka ziyarceta, cakkk ta tsaya ta zuba masa ido cikin tsananin tausayinsa, ta yi zurfi a tunani ba ta san lokacin da ta fara cewa "Bawan Allah me yasa ka ke yi musu laifin da za su yi maka irin wannan dukan?? meyesa su na gama yi maka faɗa ka ke ƙara maimaita wani kuskuren? nan fa Islamiyya ce ka ke shaye-shaye a cikinta" ta yi maganar cikin sigar nasiha da lallami.
idanunsa masu barazanar kauda ganin duk wanda ya kallesu ya zuba mata har na wani lokaci sannan ya kauda kai ba tare da ya ce kanzil ba.
Rausayar da kai ta yi za ta ci gaba da magana ya yarfa hannunsa gami da yin taku biyu ya matsa gefe.
Tsillll!! ta ji wani abu tamkar kibiya ya soki ƙwayar idonta ɗaya, ta yi saurin dafe idon tare da yin ƴar ƙaramar ƙara, Akhiee ya sake kallonta ya kauda kai ya ci gaba da busa hayaƙinsa.
Murza idon ta fara yi sai ta ji zafin ya ɗauke kamar cirar ƙaya sai da wani irin hawaye sharr!!! sharrr!!! da ya fara zuba daga iyakacin ido ɗayan kamar almara.
Ta kuma ɗaga ido za ta kalleshi ta ji an finciketa, wani aji da babu mutane Zara ta ja ta, sai da ta ɗan sarata kana ta ce "Kar ki kuma zuwa kusa da wancan, kin ga ya lahanta miki ido ɗaya idan ki ka ƙara kallonsa zai lahanta ɗayan, ke kinyi sa'a ma wata ana kiranta Husaina Isah wallahi makantata ya yi dulum, sanadin dena zuwanta makarantar nan kenan, amma daga baya ta warke, ki yiwa kanki arziki kar ki ƙara yi masa magana kar ya cutar da ke a banza."
Husneee ba ta ɗauki batun Zara da gasken gaske ba a cewarta ta ya daga kallonsa zai makanta mutum? kuma tayaya ma za a ce shine ya lahanta mata ido bayan ko kusa da ita bai zo ba hasalima sai ƙara matsawa can ya yi.
a halin yanzu tausayin Akhiee shine a gabanta don haka ta ce "Ni ba na son ƙarya, haba don kun tsane shi sai ku yi ta yi masa abinda kuka ga dama? wai shin shi ba shi da ƴan uwa da iyaye ne da malamai ke yi masa wannan dabban dukan??"
Murmushi me tafe da hawaye Zara ta yi sannan ta ce "Sheikh Auwal, Yasayyadi Jameel, Yasayyadi Usman, da kuma ni kaina da ki ke tunanin ƙazafi na yi masa, duk ƴan uwansa ne, ni ƙanwar Akhiee ce su kuma yayyensa ne, dalilin da ya sa ma muke ce masa Akhiee sunan Babanmu ya ci, amma wasu za ki ji suna kiransa Muhammad Muhammad, wallahi ina son ɗan uwana ba zan iya yi masa sharri ba da gaske nake shine ya makanta Husaina, ina gaya miki ne ba don komai ba sai don kar ki kai kanki inda za ki illata, Akhiee haɗari gare shi fiye da zaton masu zato."
Cikin takaici Husnee ta ce "Amma kun ji jiki wallahi, ashe ku ne ƴan uwansa amma kuke masa wannan abin?? to ni ba zan taɓa yarda shi ya makantata ko kuma shi ya tsokane min ido ba har sai na gani da idona ko kuma ya faɗa min da bakinsa."
Rausayar da kai Zara ta yi ta na shirin yin magana su ka ji jiniyar ƴan sanda, durummm!!! zuciyarsu ta buga a tare, Husnee ta yo waje cikin sauri, ta na fitowa ta tarar Akhiee...
©️INDO
[8/12, 4:55 PM] INDO: *🪻SAHUN KEKE🪻*
Ep 4
©️
Ayeesha Abdulkareem INDO
*Mikiya Writer's Association🦅*
Har ya sauka ƙasa, binsa ta yi da kallo cikin tsananin tausayinsa, ji take da da yadda za ta yi ta hana su tafi da shi da ta yi, Zahra ce ta ƙaraso wajen jiki a sanyaye, har ya fice daga makekiyar harabar makaranta idanunsu na kansa, sun kasa ko da cewa ƙala.
Wajen da ƙoshashshen Dokinsa ke ɗaure ya nufa ba tare da ya bi takan Inspector Khalil ba, ganin haka ya sa Inspector Khalil cewa "Kai dakata min!! Kama ka fa mu ka zo yi amma ka ke shirim guduwa, kar ka wahalar da ni kasa in harbeka.
Kalaman nasa in da dama dariya Akhiee zai yi don kuwa sun fi kama da haka, sai dai dariyar haɗari ce gareshi, ya kalleshi ya kauda kai sannan ya buɗi baki cikin nutsatstsiyar muryarsa ya ce "Ba zan hau muku mota ba, ka barni zan je akan dokina."
Fakam-fakam Inspector Khalil ya yo kansa a fusace ya na cewa "Mu za ka rainawa hankali? ya za mu kama tantirin ɗan ta'adda irinka amma sabida ka maida mu masu ƙwaƙwalwar yara sai ka ce za ka tafi a doki??"
Cikin sigar lumana ya ƙara cewa "Ba na son ku cutu ne shi yasa ba zan hau motarku ba!"
Inspector Khalil ya ƙara hayayyaƙowa kamar zai doki Akhiee, jin suna taƙaddama ya sa Sheikh Auwal matsowa gurin, fuskar sa ba alamun wasa ya ce ''Ba su san hatsabibancinka bane da ka ke tunanin su barka ka tafi kai kaɗai? wuce ka shiga ko ranka ya ɓaci."
Cikin kurari Inspector Khalili ya ce "Bar ni da shi Ya Sheikh, sai na nuna masa bambancin ɗan sanda da ɗan ta'adda."
Duk wannan kurarin da Inspector ya ke yi damisar takarda ce kawai don a gaskiyance tsoron ma kallon fuskar Akhiee yake a wannan lokacin bare har ya je daf da shi hakan ne ya sa ma ya basar da labarin handcuff.
Akhiee ba tare da ya ce komai ba ya koma ya shiga motar Ƴan Sandan hankali kwance.
Sheikh Auwal ne ya dubi Inspector Khalil cikin ɓacin ran abinda ɗan uwan nasa ya aikata ya ce "Ba na so ku sake shi har sai kun hukunta shi a bisa laifinsa, kar ku biyewa son Zuciyarsa ku barshi ya dawo ba tare da kun ƙwatowa wanda aka cuta haƙƙinsa."
Inspector Khalil ya shaƙi iskar da ke kaɗawa ya busar sannan ya ce "Calm down Ya Sheikh! hakan fa aikina ne, don hakan na kama shi."
Da haka su ka yi sallama, Inspector ya shiga mota zuciyarsa fari ƙal kamar anyi masa Albishir da Aljannah.
Ƙoƙarin kunna motar direba yake amma ina ta ce ba ta san zance ba ko motsi ba ta yi da sunan ta na da rai, abun kamar wasa mota ta ƙi ko da harbawa sau ɗaya har an kwashi lokaci me tsayi ana ta fama, Inspector Khalil sai kai kawo ya ke yi hankalinsa duk ya tashi ya rasa yadda zaiyi ga jama'a da su ka taru domin kallo sai dariya su ke masa, zuwa yanzu ya fahimci cewa Akhiee ne matsalar motar don haka ya lallaɓa kusa da shi, cikin muryar raɗa ya ce "Muhammad ka sauka to ka hau dokin naka ka ga motar ta lalace mu ma tawo daga baya amma don Allah kar ka gudu kawai tambayoyi zan yi maka ba wani abu ba." cikin zuciyarsa mugun ƙuduri ne akan Akhiee kawai ya faɗi hakan ne a ganinsa ya lallaɓa shi zai fi zuwa.
cikin ko in kula Akhiee ya ce "Ƙaramin Sufeto, ka je ka canja shiri ka zo ka same ni a Office ɗinka na riga na yi niyar zuwa so zan je ba sai ka yi min ƙarya ba, kuma ina so ka sani ba a shiga dawa don ƙarya."
Ya na gama faɗen haka ya dire ya bar Inspector da buɗaɗɗen baki ya na kallonsa.
Bai saurari kowa ba ya haye dokinsa ya zabure shi.
Inspector Khalil a tunaninsa Akhiee ya na sauka daga motar za ta dawo daidai sai ya ga saɓanin haka, yanzu ya tabbata motar ta riga ta mutu kenan don haka hankalinsa ya kai ƙololuwar tashi, abubuwa da dama ya ƙudurce a ransa wanda zai yiwa Akhiee don ya huce baƙin cikin abinda ya yi musu.
Wurin su Sheikh Auwal ya koma ya nemi alfarmar su kai shi Office da motarsu, ba su yi masa gardama ba su ka amince masa.
Sai da akuyar cikinsa ta juya da ya yi alaragab da Rislaan zaune kan kujerarsa ya ɗora ƙafa kan teburin gaban kujerar ya na zuƙar murzazzar wiwinsa, baki sake ya ke kallonsa tare da shuɗawa duniyar tunani.
Wayarsa ce ta dawo da shi haiyacinsa ya yi saurin ɗauka, a ɗaya ɓangare Corporal Halil ya ce "Sir! yanzu mu ka kammala da gawar nan mun tafi hanyar maida ita gida".
"Wane bayanai aka samu akai??"
"To gaskiya dai ba wata hujja illa iyaka dai rauni ne na wuƙa ba wani abu, sai kuma cewar tin daren jiya ne abin ya faru."
Katse watar ya yi cike da takaici ya soketa kana ya ƙarasa cikin ofishin ya na takun isa da ƙasaita, cikin sigar wulaƙanci da ƙasƙantarwa ya ce "Ka zo ka miƙe ƙafa a teburina kamar na tsohonka, office ɗin nan fa ba gidan manyanka bane da za ka zo ka na min shaye-shaye a ciki, ka na ƙazami da kai ma har ka isa ka zauna kan kujerata? ka sauka ko kuma na yi maka abinda zaman ma sai ya gagareka."
Yadda dutse ba ya magana haka Akhiee bai ce komai ba hasalima ko motsi bai yi ba.
Inspector Khalili ya dinga maganganu amma hakan bai sa Akhiee ya yi ko ɗar ba, gajiya ya yi ya nemi guri ya zauna ya na nazarin ta inda zai ɓullowa lamarin.
"Yanzu ka tsaya mu yi magana, dole kai ne ka kashe Alhaji Salisu don kai ne ka gana da shi a daren jiya.
"Don na gana da shi ba shi ya ke nufin ni zan tsara masa ƙaddararsa ba.
"Kar ka yi min zancen banza, kawai ka amsa laifinka ba sai ka wahalar da hukuma ba, ko ka na nufin ka ce ba kai ne baƙonsa na jiyan ba?"
Jan hayaƙinsa ya yi ya busar cikin salo sannan ya ce "Na baƙunce shi jiya, kuma ni na fara yi masa Albishir da mutuwarsa, amma don ance maka a daren jiya aka yi kar ka yi tunanin irin 12:00am ɗinnan, No daidai lokacin da ruwan sama ya sakko aka shiga gidan ana tsaka da ruwa kuma ruhinsa ya bar jikinsa, na so na ceceshi sai dai kashhh! bai yi min abinda ya dace ba shi yasa na bari ya mutu, Ƙaramin Sufeto ka ƙara bugu don ba ka buga a daidai ba."
Zuciyar Inspector Khalil tsalle kawai take yi kamar za ta ɓalle ƙirjinsa ta fito sabida ɓacin rai,
"Wannan gadarar taka da rainin hankali za ta jefaka a matsala, bayan duk wannan ka na nufin in yarda ba kai ka kashe shi ba? ka faɗa min gaskiya kai ka kashe shi ko?? sai fa ka amsa mini sannan za ka samu hutu daga gareni in ba haka ba ka shiga uku da ni.
Banza Akhiee ya yi masa ya ci gaba da zuƙe-zuƙensa sai da ya gama zamansa akan kujerar Inspector Khali kana ya tashi ya na cewa "Haka ake kama mai laifin ba ko handcuff?"
Sai a lokacin ma Inspector ya tuna da hakan, ya fara cika bakin cewa "Ai so nake na bika ta maslaha shiyasa nake maka tambayoyi cikin lumana, amma tinda abin naka ya zo da haka dole ne ai na rufeka, me ka ke ci na baka na zuba?"
Ko kanzil Akhies bai ce masa ba.
Tin safe har Azhar ta doso Inspector Khalil na famar tambayar Akhiee amma shiru ba amsa, duk wata barazana da zai yi ya yi amma shiru.
Wayarsa ce ta fara ruri a ƙagauce ya janyota gami da ɗaga kiran ba tare da ya duba me kiran ba.
"Waye ya sa ka kama wannan? ya ka ke abu kamar ba ka san abinda ka ke yi ba? yanzu ka na da hujjar da za ka nuna wa duniya ta shaida shine ya aikata?"
Cikin girmamawa Inspector Khalil ya ce "Sorry sir, amma alamu ne su ka nuna shi ya aikata don kuwa shine ƙarshen ganawa da Alhaji Salisu."
a ɗaya ɓangaren ya ce "Wannan rashin lissafi ne irin naka, maza ka sake shi sannan ka ba shi haƙuri, in ba ka yi hakan ba kuma zan cire hannuna daga ciki ko me ya faru kai ka jawa kanka"
"Okay Sir!!!" bai ƙara magana ba ya katse kiran, Inspector Kalil ya bi wayar da kallo ya na mamakin hakan.
"Yallaɓai me ya faru? waye ya kira?" Constable Saleh ya jefo masa tambayoyin a jere.
Cike da tsoro gami da shakka ya ce "Abin mamaki kira ne daga CP da kansa wai na saki wancan ɗan ta'addar."
Constable Saleh ya ce ''Yallaɓai dama na gaya maka ko wuni ba lallai ya yi a hannunka ba bare kwana, na gaya maka dabi da wancan shaiɗan ɗin haɗari ne, nan gaba ma za ka iya ganin takardar kora daga aiki ko ta canjin wurin aiki."
Cikin ɗaurewar kai Inspector Khalil ya ce "Anya ba shi ka ke yiwa aiki ba Constable? na ga sai faɗa min kausasan kalamai ka ke yi akansa." cikin sauri Constable Saleh ya ce "Yallaɓai wallahi ka ji na yi rantsuwa ta muslmi ba na yi masa aiki ban taɓa karɓar kuɗin wani na yi masa aiki ba, Yallaɓai ka tuna da iyalina kar ka sa aikina ya lalace ba ni da hanyar samu sai wannan, kawai anyi a gaban idona ne ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba shiyasa na shaida kuma na ke baka labari Yallaɓai."
IP Khalil ya koma ya zauna jaɓar gami da furzar da zazzafar iska, "Ku sake shi!" ya faɗa kamar zai fashe da kuka don takaici.
ya na bada umarni su ka buɗe Akhiee, ya kakkaɓe jikinsa ya tashi, wurin Inspector ya nufa ya tsaya akansa sannan ya ce "Kai ƙaramin Sufeto, idan ka ce uwarka Madam ce to mu haɗu a Coci, ina son ganinta."
Daga haka ya juya, har ya fice Idanun IP Khalil na kansa, dogon tsaki ya zabga gami da dukan teburibɓn gabansa ya miƙe kamar wanda aka cakawa Allura.
"Ya Zama dole ma na san da abinda ya ke taƙama Yaron nan, ya zama dole na gane dalilin da ya sa CP ya ce na sake shi" wannan lissafin IP Khalil ya ke yi cike da ɓacin rai.
Akhiee kuwa tuni ya ɓata a wurin ya san inda dare ya yi masa.
Baya
Cikin sauri sauri Alhaji Salisu ya shigo Falon,, a kusa da Hajiya Laure ya zauna sannan ya ce "Hajiyata na yi baƙo za mu tattauna da shi, to kar ki shigo part ɗina har sai na dawo na same ki"
"To sabida me Alhaji?"
"Kar ki tsananta bincike don Allah kawai ki yi abinda na ce"
"To shikenan Alhajina ka dawo da wuri"
Hajiya Laure ta faɗa ta na kwarkwasa.
gaba ya yi ya na cewa "In sha Allahu"
Akhiee na zaune ƙafarsa ɗaya kan ɗaya Alhaji Salisu ya shigo da sallama, bai amsa ba har ya ƙaraso ya zauna kan kujerar da ke fuskantar wadda Rislaan ya ke kai......
SHARE FISABILILLAH
Paid book ne...
09079885632
*©️INDO*
[8/12, 4:56 PM] INDO: https://chat.whatsapp.com/FuB2OR4qBx189IdAM0hXbG
*🪻SAHUN KEKE🪻*
Ep 5
©️
Ayeesha Abdulkareem INDO
*Mikiya Writer's Association🦅*
Washe baki ya yi kamar gonar Auduga, cike da farin cikin ganin baƙon nasa ya ce "Na ji daɗi da ka amsa gayyatata don ban zata za ka yarda ka zo cikin sauƙi haka ba, me za ka sha in kawo maka?"
Ba tare da ya kalle shi ba ya ce "Ba ka da abinda zan sha a gidanka, je maganarka kai tsaye."
Gyara zama Alhaji Salisu ya yi kafin ya yi gyaran murya, duk ya rasa ma ta inda zai fara faɗe, sai da ya tattaro duk nutsuwarsa sannan ya fara da cewa "Kai sananne ne ta fannin kisan kai na san da haka, to ina so a kashe min wani ne don haka na nemeka, na san kai kaɗai za ka iya kashe shi ba tare da kowa ya sani ba, sunansa Alhaji Habibu mai Kwalli, ya addaba min a kasuwa wallahi shi ne ya ke hanani arziki da yanzu na fi haka, ka temaka min ka kashe shi, ko dubunnai nawa ka ke so zan biyaka indai har zai mutu."
Tin da ya fara maganar Risslaan ya zuba masa juyayyun idanunsa ko ƙiftawa babu har ya kai ƙarshem maganar, lumshe ido ya yi sannan ya ce "Ina kashe duk wanda na so amma abinda ya kamata ka sani ni ba'a sa ni na yi abinda ban yi niyya ba, inda na yi niyyar kasheka to fa a yanzu zan kashe ka amma ban yi niyyar hakan ba, ni ba matsiyaci bane ka sani ba ka da arzikin da za ka iya siyan ra'ayina" ɗan tsagaitawa ya yi kafin ya ci gaba da cewa "Ka na ta naka haukan ba ka sani ba ma kai ne gawar fari, I mean, you will die today"
Rasss!! zuciyar Alhaji Salisu ta buga a razane ya ce "will you kill me??"
"It's not me, shi wanda ka ke son kashewa shima ya na son kasheka kuma ya rigaka shiryawa a yau za ka mutu, do you understand?"
duk da irin sanyin Ac da ke yawo a falon amma sai da zuffar wahala ta fara keto masa, kamar Zai yi kuka ya ce "Na fahimta, ashe shima irin tunanin da nake akansa ya ke yi? Muhammad Muhammad! ka temaka min ka ceci rayuwata kar ka bari ya kashe ni, wallahi ba na son mutuwa yanzu ina son ganin jikokina, ɗana guda ɗaya ne kar ka bari a maida shi maraya, don Allah kar ka bari ya kashe ni, na san kai me arziki ne ba zan iya biyanka ba amma nayi maka Alƙawarin ko me ka ce inyi zan yi."
Akhiee ya kalle shi sama da ƙasa kana ya ce "Barin irinka ƙalu-bale ne wa duniya, ba zan ceceka ba, amma ka kwantar da hankalinka bayan ka mutu shi ma zai mutu, ka godewa Allah kai ba ni zan kashe ka ba da sai ka gwammace ba ka zo duniyar ba ma, ba ni da lokacin zaman saurarenka ni zan wuce, idan ka na da wasiyya ko fatan ƙarshe sai ka gayawa iyalinka amma kai kam ba za a kai gobe da kai ba."
Jiki na tsuma ya ce "To wai ta ya akai ka san zai kashe ni??"
"Idon Mikiyana na kansa" daga haka bai ƙara cewa kanzil ba ya miƙe ya nufi hanyar fita.
Zamewa ya yi daga kan kujerar zuwa ƙasa, duk duniyar ta tsaya masa cakk gabaki ɗaya ma ya rasa tunanin me zai yi, nan ya zauna ya buga tagumi sai zuffa yake kamar wanda aka sanya a tukunyar dambu, ya rasa abin yi kuma tinda ya ji Risslaan ya faɗa ya yarda dole ne sai ya mutu don haka ya susuce.
Wannan tashin hankalin ne yasa ya kasa komawa wajen Hajiya Laure kuma ya hana ta zuwa bare ma ta san halin da yake ciki.
Duk tsawon daren ya kasa rintsawa sai sukuwa yake a falon shi kaɗai, kansa duk ya gama kwarkwancewa.
a kowane minti jiran shigowar me kashe shi ya ke sai dai ya ji shiru har ruwa ya ɓalle, zama ya ƙara yi ya buga tagumi ya na jiran ya ga abinda Allah zai yi.
Ya na nan zaune ya ji motsin ƙofa ya yi saurin miƙewa jikinsa na karkarwa idanunsa zuru-zuru ya na tsaye suka lalata key ɗin ƙofar su ka shigo, mutum uku ne fuskarsu duk a lulluɓe hannunsu ɗauke da manyan wuƙaƙe masu bala'in kaifi, ya kasa ko da motsa ƙafafunsa da ke karkarwa bare ya gudu har su ka ƙaraso su ka sanya shi a tsakiya.
Ɗaya daga cikinsu ne ya ce "Mu yi abinda
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 2 Chapter of 19