yi "
"Au haka ne? to Allah ya temaka, amma ina yi maka fatan shiriya, kuma na san wata manaƙisar kuke shiryawa.
Banza ya yi mata itama sai ta bashi wuri.
Tin ta na sa ran ganin Akhiee har ta dena bacci me cike da mafarkai daban-daban ya yi awon gaba da ita..........
*©️INDO*
[9/8, 12:07 PM] INDO: *🪻S-K🪻*
Ep 24
Misalin ƙarfe 03:00 na dare ya shigo ɗakin cikin tafiyarsa me kama da sanɗa, wajen Drower ya wuce ya ajiye duk wasu tarkacen makamai na jikinsa sannan ya buɗe sif ɗinsa, kamar kullum sabuwar riga fil ya ɗakko don kuwa ba ya saka kaya kuma ya maimaita su, da ya yi sawa ɗaya sai dai ya bayar ko ya jefar, sai dai in ya na son irinsu ma ya kuma yi.
Doguwa ce har ƙasa maɓallanta guda uku ne a jiki kacal a iya tsakiyarta, sama da ƙasanta a buɗe yake, sai ɗan ƙaramin wandonta iya guiwa.
A gefen gado ya ajiyeta sannan ya shiga toilet, bayan ya fito ya zura rigar sannan ya nufi kan Gado.
A gefenta ya zauna ya zubawa fuskarta da take a cukurkuɗe idanu tamkar don ita kaɗai aka halitta masa idanun ko son ƙiftawa ba ya yi, daga yanayinta ya fuskanci a cikin damuwa da takura take yin baccin da alamu ma ba jin daɗinsa take yi ba, gashi ta duƙunƙune cikin lafkeken Hijab wanda ko likafani za a yi mata da shi zai isa.
Cikin nutsuwa ya ɗora tattausan hannun akan fuskarta ya na shafata a hankali a hankali, "Asma'u!! ji nake tamkar tamkar garkuwa ce ke gareni, zan so na kasance me sanya ki farin ciki a koda yaushe, sai dai ba zan iya ba rayuwata cike taf da abubuwa iri-iri, a memakon ki yi farin ciki sai dai ki kasance cikin zubda Hawaye Asma'u" a zahiri yake maganar ya na yi ya na kewaye hancinta da kan idanunta da babban yatsansa, har zuwa lokacin kallonta yake yi tamkar wata sabuwar halitta ba mutum ba.
Ya ɗebi ɗan lokaci cikin wannan yanayin kafin ya janyota jikinsa ya rungumeta a cikin ƙrijinsa ya fara ƙoƙarin cire mata hijabin a hankali ta yadda ba za ta farka ba, har ya cire ya ajiye shi can gefe ba ta farka ba sai ma numfashi dogaye da take ja ta na ƙara linƙaya a cikin baccin, ga dukkan alamu ta samu sauyin yanayi wanda ya sa Zuciyarta ta samu sakewa, har ila i yau bai dena kallon fuskarta ba kai ka ce haɗiyeta yake shirin yi, idanunsa sai wani irin sheƙi da ƙyalli suke yi su na ƙara canja kala.
Hannunta ya riƙo ya zuba masa ido, ganin zobensa ya na nan a jikinta ya sa shi sauke wata sirrintacciyar ajiyar Zuciya, "Asma'u ina buƙatarki a rayuwata, ki kasance tare da ni ."
Ya faɗa cikin wani irin yanayi wanda ya na da nasaba da shaukin sonta, wanda shi kansa bai san da hakan ba.
Har 04:00am daidai ya na rungume da ita sannan ya zameta daga jikinsa ya kwantar da ita, sai da ya ƙara ɗibar lokaci me tsayi ya na kallonta sannan ya sauka daga kan gadon, Alwala ya ɗauro sannan ya canja rigar jikinsa ya zura wata sabuwar jallabiya Brown ya sanya hula ƴar ƙarama taɓani ka ji hadisi sannan ya fara Sallar nafila.
Sai lokacin da aka kira Sallar farko sannan ya tashi daga kan dardumar ya fice daga gidan bakiɗaya.
Sai bayan an idar da sallah a masallatai Allah ya bata ikon farkawa firgigit kamar wadda aradu ke shirin faɗowa a ka.
Zazzare ido ta shiga yi ta na duba ko'ina ko za ta ga Akhiee amma fayau ko ƙyallin rigarsa ba ta gani ba, wayarta ta jawo ta duba agogo ganin lokacin salla na neman ƙure mata ya sa ta yi saurin direwa ta fito daga ɗaki ta na dube-dube ko za ta ga banɗaki, ɗaki biyu ne a wajen daga wanda ta fito daga ciki sai wani da alamu dai ba banɗaki, gashi ko ina a bushe yake ba alamun akwai ruwa.
Komawa ta yi ɗaki da zummar ɗaukar waya ta kira Rislan don jin inda za ta samu ruwan ta na komawa idonta ya sauka akan ƙofar toilet na cikin ɗakin, duk da ba ta da tabbas amma ta na kyautata zaton shi ne don haka ta nufi wajen domin ganewa idanunta.
Sai da ta sauke ƴar ajiyar Zuciya ta jin daɗi sannan ta ɗauro Alwala ta fito, ta na idar da sallar ta yi addu'a ta zame ta kwanta akan dardumar daga haka bacci ya sake surarta.
Yazeed kwana biyun nan sam ba ya iya baccin kirki sabida tunanin Ma'u, har ƙagara yake a kira Asbah da ya fita masallaci ya dawo ko ɗakinsa ya ba ya komawa sai dai ya zauna a harabar gidan don kuwa in ya koma ma ba shi da abin yi sai damuwa anan kuwa ko shuke-shuke ya kalla zai rage zafi.
Yau ma kamar kullum ya na zaune ya buga tagumi kamar a mafarki ya ga gilmin Ma'u da ƴan ƙullin kayanta a hannu ta nufi wajen get.
Zundum!!! Zuciyarsa ta yi wata mummunar bugawa wadda ta yi daidai da tashinsa tsaye, razanar da ya yi gami da bugun Zuciyarsa suka bada gudun mawa wajen juyawar kansa hakan ya haifar masa da jiri idanunsa su ka fara ganin duhu kansa na wata irin majaujawa tamkar ana girgizar ƙasa a cikinsa.
Cikin wata wahaltacciyar murya ya shiga kiran sunanta duk da ba shi da tabbacin za ta ji shi kuma ta saurare shi, da yake suna linzami ne kamar gizo haka ta ji an kira sunanta, gabanta ya yanke ya faɗi har ƙasa, kasa juyowa ta yi don kuwa ba ta san me kiran nata ba, a wannan lokacin kuwa ba ta son kowa ya ganta don so take ta gudu, in ma ba inda za ta je gwara ta dinga tafiya ko ba ta da wurin zuwa, a tunaninta Allah zai haɗata da waɗanda za su temaketa, Ta ɗauki ƴan sakanni a tsaye ba ta ƙara jin an kirata ba don haka ta ci gaba da tafiya cikin sanɗa har ta isa bakin get, sai dai abinda ba ta sani ba ko kuma ta manta da shi, me gadi ya na sa mukullai a ƙofar kuma ba wanda zai bata su sai shi ko Haj Laure, turus ta tsaya Zuciyarta ta karaya tamkar za ta fashe da kuka.
Juyawa ta yi ta na kallon ɗakin me gadi tare da tunanin ko zuwa za ta yi ta roƙi alfarmarsa?
Kamar saukar aradu haka ta ji lokacin da muryar Yazeed ta karaɗe Fadar cikin Masarautar Kunnuwanta, sabida firgici sai da Zuciyarta ta ɗan tsaya na wucin gadi yayin da numfashinta ya sarƙe kamar me shirin sumewa.
Da rarrafe ya ƙaraso inda take don kuwa ya na miƙewa zai iya faɗuwa, sai da ya dangana da inda take sannan ya tsaya durƙeshi akan gwiwoyinsa, idanunsa da ke gani dishi-dishi ya ɗago ya na kallonta kafin ya fara magana cikin sarƙaƙƙiyar murya tamkar an shaƙare shi, "Ma'u kar ki gudu ki barni, don Allah ki tafi da ni duk inda za ki je zan biki, kuma akanki zan iya jurewa kowace irin rayuwa wallahi!!"
Yadda yake maganar tamkar zautacce ya sa Ma'u ta ƙara tsorata da shi, salon bugun zuciyarta ya ƙara canjawa daga sauri zuwa gudu, kai kawai take girgizawa don kuwa yadda numfashinta da Zuciyarta suka burkice ba za ta iya furta ko uffan ba.
"Ma'u zan mutu idan ki ka gujewa rayuwata, wallahi zan iya makancewa idan idanuna suka dena ganinki, iya tashin hankalin nan da suka gani har sun fara dena nuna mini daidai, duhu nake gani, ƙwaƙwalwata ta na juyawa alamar hauka ta fara tabbata a gareni, wallahi Ma'u ina sonki so me tsanani, irin azababben son nan da yake tarwatsa rayuwar ɗan adam, ki jiƙaina ki tafi da ni ko zan samu sassauci.
Abin nasa haushi yake bawa Ma'u a gefe guda mummunar tsanar da ta yi masa na ƙara zigata akan ta ci mutuncinsa ko zai gane da gaske ba za ta taɓa ƙaunarsa ba, cikin sassarƙewar murya gami da ƙarfin hali ta ce "Ni ba zan taɓa son watsatstse irinka ba, mazinaci ƙazami mashayin giya wanda bai san daraja da kimar kansa ba bare ta wani, ka fita daga rayuwata in ba haka ba kashe kaina zan yi wallahi, ni na tsaneku bakiɗayanku kuma Allah sai ya saka min."
Wasu zafafan hawaye ne suka yiwa fuskarsa mugun wanka, ya girgiza kai gami da dafe ƙirjinsa daidai saitin Zuciyarsa, "Ma'u Zuciyata shirim fashewa take yi, don Allah kar ki hukuntani akan laifin da ba ni na aikata ba, idan wani ne ya yi miki laifi don Allah ki ƴantani daga ɓangarensa, ni ban kasance irinsu ba, kuma wallahi tallahi ba na iya zama na sha giya tin daga ranar da na furta miki kalmar so kika jefani cikin tashin hankali, a da na ɗauka abinda nake yi shi ke kawo nishaɗi na ɗauka tarayya da matan banza shine more rayuwa, amma tinda na kamu da sonki na gane martabar mace, na gane duk abinda nake yi ba shine ke sanya farin ciki ba, na dena ba zan ƙara ba na tuba ki yafe min; yanzu rayuwata da mutuwata sun rataya a wuyanki Ma'u!! ina fatan ki yi mini kyakkyawan zaɓi."
Ya ƙarasa maganar gami da rushewa da wani susutaccen kuka tamkar ƙaramin yaron da ke neman Mahaifiyarsa.
Dogon tsaki Ma'u tafka me cike fa ɓacin rai da tsantsar ƙiyayya, ba tare da ta sake kallon inda yake ba ta ja ƴan ƙullin kayanta ta koma cikin gida cike da baƙin ciki da takaicin yi mata silar rashin guduwar da ta yi niyya.
A take a wajen wani mugun azababben tari ya sarƙe shi wanda ya haifar masa da shiɗewa daga haka bai ƙara sanin inda kansa yake ba.
Tin da safe da Baba Sa'idu ya je gaisawa da Abee ya gyara zama ya tankwashe ƙafa kamar me shirin kwasar taushe, ya karya harshe ya rattabawa Abee maganganun son rai akan Auren Rislan da Husnee, Abee ya gama saurara sannan ya jinjina kai ya ce "Duk ina ƴan uwan nasa?, a zo min da su don in ji menene aibun da suke gani a cikin hakan?" Baba Sa'idu ya ce "To Yaya" tashi ya yi ya fita don nemosu, da Adamu ya fara karo don haka ya ce masa ya je ya tarkato sauran.
Da yake duk jiran kaɗan suke yi da wane gayawa wane dandanan suka cika tafkeken Ɗakin Abee ɗin, ciki kuwa harda Umma, Innajo, Umma Azima, Umma Uwani, matan Abee, sai Matan Baba Sa'idu su biyu, Inna Huwaila da Inna Kulu, sai iyalinsu cunkus amma banda Sheikh Auwal da Zara da Sauran waɗanda ba sa kusa.
Duk yawansu sai da Abee ya saurari ta bakin kowa wanda yawancinsu bayan nuna rashin goyon baya akan Auren sai sun ƙara da sharri da ƙarya, wasu kuma suna faɗen iya abinda suke tunani, wasu kuma dai suna tsakatsaki su basu ce a raba ba ba su ce a bari ba, bayan ya gama saurarensu tsaf sannan ya yi gyaran murya ya fara da cewa "To duk na saurari kokenku, amma ni ba ni da ƴancin Sakar masa mata ko kuma na tilasta shi akan sakinta, amma zan yi magana da shi, don haka kowa ya tashi ya tafi uzurinsa, masu zuwa makaranta maza su shirya masu fita kasuwa su ma su shirya."
Kallon kallo suka shiga yiwa juna cike da baƙin cikin furucin Abee sun san tinda abin ya zama haka, ko ana ha maza ha mata ba ta yadda za a yi haƙarsu ta cimma ruwa, don haka wasu suka fara saɓewa su na fita cike da takaici.
Su Innajo da su Inna Huwaila kuwa suna fita suka dasa zancen su da sirikansu, irin Su , Ummu Nusaiba, Matar Babban Yaya, Yaya Lantana, Matar Yasayyadi Usman, Yaya Asiya, Matar Yaya Habibu, Yaya Fiddausi, Matar Yaya Aminu, Umman Azima, Matar Yasayyadi Jameel. Matar Sheikh Auwal wadda ake kira Yaya ita ce ba ta fito ba ita ɗin ma Sheikh Auwal ne ya hanata banda haka da ita za ayi.
Hasan na shirin fita ya na ƴan gungunai Abee ya kira sunansa don haka ya tsaya, Abee ya ce "A zo min da Magajin Malam" wato Sheikh Auwal kenan, sunan nan da Abee ke gaya masa ma baƙin cikin hakan suke ji, don gani suke yi tamkar ya fi sonsu. Ko to bai ce ba ya zunguri uban kai kamar damin gumama ya ci gaba fa tafiya.
cikin ƴaƴansu da ke ta sha'anoninsu ya aika ɗaya Ɗakin Sheikh Auwal ya kira shi, bai ƙara bi ta kai ba ya fice daga gidan baki ɗaya.
Abee ya na dariya irin ta yaro man kaza ya ce "Magajin Malam yanzu aka gama kawo min ƙarar ɗan uwanka akan Aurensa, sai dai ban ji ta bakinka ba."
Sheikh Auwal ya rissina a ladabce ya ce "Abee kuskuren da ya aikata shi ne Aurenta ba a kan ƙa'ida ba, bai kyautu ya je ya yi gaban kansa ba, mu ba mu sani ba iyayenta ba su sani ba, sannan duk ba mu amince ba, sannan ya gardame akan shi ba zai rabu da ita ba duk da cewar iyayenta suna son hakan." ɗan tsagaitawa ya yi kafin ya ci gaba da cewa "Abee! in da Akhiee ya na jin magana kuma ya na ɗaukar shawara, ba wanda zai ce dole sai an raba Aurensa, su kansu iyayenta da ya na yin abinda ya kamata na san ba za su ƙi ba shi ƴarsu ba, amma yanzu ka ga abinda ya yi kowa bai ji daɗi ba, raina ɓaci yake yi idan na ji irin maganganun da ake faɗe akanmu, amma ina ganin indai har ba zai dinga cutar da ita ba kawai kar a ce za a rabasu don hakan ma wani aikin ne babba, kuma ta riga ta faru sai haƙuri, ko an rabasu dai abin ya riga ya shiga kundin tarihi ba wanda zai manta."
Abee ya yi murmushin manyance kafin ya ce "Wannan gaskiya ne, ya yi kuskure amma ana buƙatar yafe masa; Wai ni ko akwai abinda kuke ɓoye min dangane da shi ne Magajin Malam?, a gidan nan kowa ba ya laifi sai shi kaɗai? ba a faɗen aibun kowa sai na shi, anya kuwa ba wani abin kuke ɓoye mini ba?, ko kuma don shi Maraya ne yasa ku ke yi masa hakan?"
Hawayen da suka cika idanun Sheikh Auwal suka samu damar zubuwo, goge su ya yi cikin sauri kafin ya ce "Abee nima fa maraya ne, da ni da shi da Zahra Mahaifiyarmu ɗaya kuma ba ta raye a Duniya, kawai dai shi ya bambanta da kowa ne, ya fi son ya yi abinda ra'ayin kansa ne ba ya jin bari, kuma irinsu su na da wuyar sha'ani".
Abee ya ce "Allah ya jaddada Rahma garesu ita da sauran Ƴaƴanta da mu ka rasa, amma akwai abinda ba kowane ya san shi ba a tare da Dattijo, kuma ba wanda zai iya fahimta har sai wanda Allah ya bawa iko; a gaya masa ina buƙatar ganinsa."
Sheikh Auwal ya amsa sannan ya miƙe.
Yazeed a hankali ya fara buɗe idanunsa da suka yi masa nauyi suka rirriƙe kamar an yi yaƙin basasa a cikinsu, da ledar ruwa da Allurai ya fara yin tozali hakan ya tabbatar masa a gadon Asibiti yake, wani marayan kuka ya saki me cike da tausayin kansa, "Me rayuwa take nufi da ni? me yasa zan kamu da son wadda ta tsaneni? me yasa ba za ta tausayi min ba?" tambayoyin da wani sashi na Zuciyarsa ke yi masa kenan sai dai ba shi da amsarsu.
Hajiya Laure da ke zaune a gefen gadon ta zuba tagumi ta yi saurin juyowa gareshi sabida jin sautin kukansa, "Sannu Yazeed, Allah ya baka lafiya, me ya jawo maka ciwon Zuciya Yazeed?" ta ƙarasa maganar a marairaice tamkar da ance ar za ta fashe da kuka.
a hankali ya riƙo hannunta kam ya na cije leɓensa, da alamu azabar da yake sha ta wuce kwatance, cikin sarƙaƙƙiyar murya ya ce "Mommy! mutane nawa kika zalumta a Duniya? Mutane nawa kika wulaƙanta a Duniya?? Da ni da ke na san har da Daddyna mun kasance baragurbi a cikin Al'uma, ban taɓa ganin inda muka gina Alkairi ba; Daddyna kulluyaumin burinsa ya za a yi ya kere Abokin kasuwancinsa ko ta hanya me kyau ko marar kyau, ban taɓa ganin inda ya kyautatawa marasa ƙarfi ba, ko Islamiyya bai taɓa ginawa ba bare Masallaci, Haka kema burinki kawai kar ya yi miki Kishiya, muradinki ki kere sa'a a cikin Ƙawaye, aikin kenan biye-biyen bokaye, ba ku da tunani sai haka, shi yasa kuka manta da ni kuka kasa Ba ni tarbiyar ƙwarai wadda kowa zai gani ya yaba, na kasance mazinaci ɗan shaye-shaye; ban taɓa yi muku nasiha akan abinda ku ke yi ba, nima duk da na samu damar da zan kyautata amma ba na kyautatawa kowa sai abokan taƙadirancina, Kaiconmu Mommy!!, rayuwa ta riga ta sauya kuma daga yanzu har wani lokaci a koda yaushe kina iya rasani, kuma na yi imani da Allah ire-iren kusakuran nan namu su ne suke bibiyarmu, shi sharri ɗan aike ne da zarar ya isa zai juyo zuwa ga wanda ya aika shi, ni dai Mommy ba na buƙatar ki ƙara bawa wani boka Dukiyata, da ita zan gina Alkairin da muka kasa ginawa a baya ko hakan zai sa mu samu sassauci, zan nemi Malamai da Shaidu a biya waɗanda suke bin Daddy bashi sauran kuma a sallameki nima a sallameni, in ya so sai ki yi duk abinda za ki yi da naki."
Jikin Haj Laure ya yi sanyi salam tamkar an zare mata laka, wani sashin na Zuciyarta ya na son gazgata zantukansa musamman idan ta tuna irin abubuwan iftila'i da masifa da ta fara gani ta silar bin bokaye, wani sashin na Zuciyarta kuwa zigata yake yi akan cewar zafin ciwo ne ya sa Yazeed yake waɗannan surutan, ba ta iya ce masa ƙala ba sai ma tagumi da ta buga ta linƙaya a cikin duniyar nazari.
Sai misain ƙarfe goma na dare ya shigo don zuwa kiran da Abee ya yi masa.
Husnee na zaune a bakin gado ta zuba tagumi da duk hannayenta, jin motsi ya sa ta ɗagowa ta zubawa bakin ƙofa idanunta da su ka kumbura tulu-tulu sabida kuka, har ya ƙaraso ya zauna a kusa da ita idanunta na kansa, shi ma ya zuba mata nasa idanun na ɗan lokaci kafin ya ce "Kuka kika yi ko? me yasa ma ba ki yi bacci ba?" cikin muryar kuka ta ce "Ta ya ba zan yi kuka ba Rislan? ta ya zan iya bacci bayan tin jiya rabona da ganin iyayena da ƴan uwana? kuma ban san halin da suke ciki ba, kai ma kanka sunan ina tare da kai amma tin jiya ba ka ƙara waiwayata ba ni kaɗai na kwana a ɗakin nan, gashi ban san kowa ba kuma na ga ba sa ƙaunata ƴan gidanku Zara ce kawai take tausayina, haka suka dinga liƙowa suna kallona kamar ni ba kutum bace, kowa da irin kalma marar daɗi da yake faɗe a kaina, kai kaɗai zan gani Zuciyata ta yi sanyi amma ka ƙi bani damar hakan!!!" ta ƙarasa maganar gami da fashewa da wani kasalallen kuka me taɓa zuciyar me saurarensa.
Mashin tausayinta tuni ya daɗe da huda Zuciyarsa, a hankali ya sanya tattausan tafin hannunsa ya shiga goge mata ƙwallar sai dai da ya goge da wata ta zubo. cikin nutsuwa ya ce "Kinsan ba na son ganin kukanki, za ki sa na yiwa kaina tsatstsauran hukunci."
*©️INDO*
[9/10, 1:17 AM] INDO: *🪻S-K🪻*
Ep 25
"To ai kai ne tinda ka tafi ka bar ni jiya ba ka ƙara nemana ba, ko kaya fa ba ni da su da na yi wanka ma sai na jikina na mayar, don Allah ka kai ni gida in ɗauko kayan daga nan sai na yi magana da su Mommy."
Tsirawa bakin nata ido ya yi ya na kallon yadda take maganar cikin yanayi me kama da shagwaɓa. Ga abinda take faɗa masa amma shi tunanin da yake yi daban, a hankali ya sauke babban ɗan yatsansa zuwa kan laɓɓanta ya na shafasu cikin nutsuwa da wani irin salo, cak!! kukan ya tsaya ta ɗago ido ta zuba masa ta na jin wani irin yanayi har cikin ranta, sassanyar iskar da ya hura mata a fuskarta ta sa ta yi firgigit ta ɗan tsorata gami da faɗawa jikinsa ta ƙanƙame shi ta na sauke nannauyar ajiyar Zuciya.
"Zan sa a kawo miki kayanki gobe, ba zan bari ki je gida yanzu ba."
ya faɗa cikin wata kasalalliyar murya me sigar raɗa.
Sake cusa fuskarta ta yi a cikin ƙirjinsa ta ƙara lafewa sannan ta yi magana cikin sanyin murya, "Me yasa ƴan gidanku ba sa sona???"
Hannunsa na dama ya sanya ya tallafo haɓarta hakan ya bashi damar kallon fuskarta, cike da tausayinta ya ce "Ba ke ce ba sa so ba ni ne, ba ki da wani aibu wanda zai sa a ƙi sonki Asma'u, ba sa so na yi farin ciki ne shi yasa suke son rabuwata da ke, Babana ya na gidan nan Da shi da Zara su kaɗai ne danginki; ko da Zara ba ta nan ki dinga zuwa wajensa ki na zama kin ji ko?"
"Amm...." saurin katse mata hanzari ya yi ta hanyar girgiza mata kai don haka ta yi shiru gami da yin ƙasa da kanta.
Sun ɗauki ɗan lokaci a haka ba tare da kowa ya yi magana ba, Rislan ne ya katse shirun da cewa "Ki duba a cikin kayana akwai Jallabiya na san akwai wadda za ta yi miki sai ki sakata, zan je wurin Abee na dawo sai mu je ki gaisar da shi."
Yanzu ma kai ta gyaɗa masa ba tare da ta ce komai ba, cikin nutsuwa ya zameta daga jikinsa ba don ta so ba, bai ƙara kallon inda take ba ya fice ya nufi sashin Abee.
Sai da ta daɗe a
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 17 Chapter of 19