ya sa ni sakinta duk azabarsa, Allah ne ya halicceta kuma ya jefota cikin rayuwata kuma ina komai ne da ikonsa shine kaɗai zai rabani da Asma'u ta kowace hanya, ko a raye ko muce Russlan kai ma ka riƙe hakan."
Zuwa yanzu Russlan tsananin tausayun ɗan uwan nasa ya gama kama shi, ya san a zaman tare dole wataran za ta gane gaskiyar waye shi, kuma hukuncin wanda ya yi hakan kisa ne, bayan haka akwai ƙalubale da yawa a gabansu wanda shi Risslan ba ya hangosu sabida idanunsa sun rufe, "Risslan na yarda da kai kuma na san za ka aikata amma ka sani akwai sauran rina a kaba."
"Na san da hakan Russlan, ka koma gida kawai nima zan wuce gidanmu Gadon nan ka sa Dogarai su kwashe shi kar safiya ta yi Bil'adam su dinga karo da shi."
Russlan ya ce "Okay sai ka fito goben, Mu haɗu a Daji in an isa."
a hankali Risslan ya ce "Ka san fa ni ba kamar kai ba ne, musamman ina cikin wannan yanayin da akwai mutane da yawa waɗanda su ke buƙatar kulawata."
Russlan ya ce "Okay shi kenan see you later."
Risslan bai ƙara magana ba ya ɓace ɓatt! sai gashi a kusa da Dokinsa.
Prince na ganinsa ya fara haniniya ya na ɗaga ƙafafu sama ya na direwa, Risslan ya shafa shi cike da ƙaunarsa hakan ya sa ya sunkuyar da kansa ƙasa kamar ba shi ya gama dara ba yanzu, wata kyakkyawar sufa Akhiee ya yi ya dire akan Prince tare da Komawa asalin Suffarsa ta Ɗan'adam wanda kowa zai iya ganinsa saɓanin Da da ya koma Suffar mutanen ɓoye.
Hanyar komawa Hotoro yankinsu ya ɗauka ya na tafiya cikin kwanciyar hankali ba tare da wata fargaba ba.
Cijewa Prince ya yi gami da ɗangale ƙafafunsa ya na wata irin haniniya hakan ya tabbatarwa Akhiee wani abin ya gani.
Bai gama nazarta yanayin ba ya ga Alburushi ya nufo kansa gadan-gadan sunkuyawa ya yi ya wuce sannan ya ɗago, kafin ka ƙifta ido ka buɗe wasu murtuka-murtukan mazaje sun bayyano ta kowace kusurwa ta filin, sanye suke cikin baƙaƙen kaya kowanne fuskarsa a rufe, su na ɗauke da wasu lafiyayyun bindigu wanda suka rufe bakunansu ta yadda ba za su yi ƙara sosai Ba.
Harbi suka fara ba shi ta ko'ina ba ƙaƙƙautawa idanu a lulluɓe neman makasarsa su ke yi.
Abin da ya yi bala'in basu mamaki gami da dugunzuma hankulansu, kasancewar ƙwararrun maharba ne ba sa saɓa saiti bayan Alburushin farko ba wanda su ka harba masa ya faɗi duk sun same shi sai dai da zarar Alburushin ya sauka a jikinsa zai gangare ya faɗi ƙasa ba tare da ya ratsa shi ba, duk da suna ganin hakan kuma sun razana amma ba su fasa ba don kuwa ganu suke yi kamar za su iya cimma nasara in suka ƙoƙarta.
Wani wawan juyi ya yi gami da buɗa hannayensa ya yi wani wurwuro kamar fanka sannan ya diro ƙasa hannunsa riƙe da manyan bindigu guda biyu.
Turus su ka tsaya kallonsa ido a warwaje, sun kai maƙurar tsoro da firgici ganin bindigu sun bayyana a hannunsa bayan ba shi da su ba shi da dalilinsu.
Cikin rashin imani da tausayi Na Akhiee ya fara sakar musu harbi a matuƙar fusace, ganin haka ya sa su ka ci gaba da harbinsa su ka fara artabu tsakaninsu, sai dai shi harbi ɗaya yake yi musu su baje don dai su na da yawa.
ba ɓata lokaci duk ya ƙarar da su saura mutum ɗaya wanda Alburushi ba ya shigarsa don kuwa shi ma babban shege ne.
Akhiee ya yi wani ƙwaƙƙwaran taku gami da watsar da bindigun a gefe dandanan su ka ɓace ɓatt!! sai kuma wata lafiyayyar farar wuƙa ta bayyana a hannunsa, duk da dare ne hakan bau hana ƙyallinta da haskenta fitowa ba, kan Maharbin ya nufa gadan-gadan hakan ya sa ya arta da gudu domin ceton ransa, jefa masa wuƙar ya yi cikin sa'a kuwa ta ratsa ƙashin bayansa, ya saki ihu gami da zamewa ya kife a rubda ciki, Akhiee ya ƙarasa gabansa ya durƙusa kafin ya ce "Duk wanda ya ga wannan Sirrin nawa mutuwa ce makomarsa ba za ka iya tsere mini ba, amma kafin ka mutu ina son sanin wanda ya aiko ku." cikin ƙarfih hali Mutumin ya kama dariya ya na cewa "Wani Jarumi ne, kuma ya riga ya sa ka a tarko ta kowace fuska, ya yi mummunan shiri na kawo ƙarshen hatsabibancinka, kuma ina me tabbatar maka ruhina ba zai tafi a banza sai ya ɗaukar mini fansa, Gobe za ka samu gawar Ƴaƴanka mun ci moriyarsu don haka za mu dawo maka da su, ka shiga matsala Sarƙa, duk hatsabibancinka sai wannan Shu'umin ya ga bayanka shi ba kanwar lasa bane zazzafa ne, kuma jama'arsa daga kowane State na Nigeria har ma da Ƙasashen ƙetare sun shigo Nigeria sun yi maka ƙawanya, in ka isa ka tsira hhh!!!".
Ya ƙarasa maganar ya na ƙara ƙyalƙalewa da dariyar mugunta a wahalce.
A fusace Akhiee ya zare wuƙar da ke maƙale a bayan Mutumin ya suka masa ita a wuya, ko shurawa bai ƙara yi ba tuni ya mutu idanunsa a bubbuɗe.
Akhiee ya miƙe jikinsa na wata irin tsuma sabida ɓacin rai, tuni wani irin duhu ya mamaye idanunsa kansa ya fara wata irin yamutsawa.
Bai bi ta kan Dogarawan Aljanun da suka kewashi ba ya haye kan Prince ya ci gaba da tafiya.
Aljanun su ka koma kan mutumin da ya kashe daga ƙarshe shi ma su ka ɗauke gawar ta shi sauran kuwa tuni sun kwashe su sun kai su bakin wani Daji sun zubar.
Ba su gushe daga wurin ba sai da su ka gyara shi tsaf ba alamun jini ba alamar Alburushi ba ma me cewa wani abu ya faru a wurin.
ya na isa bakin get ɗin gidan ya dire daga kan Prince ya dafa ƙofar nan-take ta buɗe ba tare da hayaniya ba, ya shiga gidan tare da Prince sannan ya ƙara dafa ƙofar ya rufe, sakatu harda Pad lock ɗin da ake sawa get ɗin duk su ka koma su ka rufe kamar dama ƙofar tinda aka rufeta ba wanda ya ƙara taɓata.
Kawai sakin Prince ya yi ya tafi makwancinsa da kansa shi ma ya nufi na shi makwancin, ta bayan gidan ya bi inda ya fi kusa da ɗakinsa ba sai ya ratsa sassan gidan ba, ita ma ƙofar bayan kulleta ake yi amma ya na ɗora hannunsa akanta ta buɗe ya shige sannan ya rufeta, kwata-kwata a wannan daren bai yi bacci ba tunane -tunane sun yi masa katutu.
Husnee ta na gama waya da Akhiee ta ji wani irin sanyi na ratsa dukkan sassan jikinta har cikin Zuciya da Ƙoƙon ranta, nan take farin ciki ya ziyarce ta fara manta dukkan Damuwarta, ba ta daɗe cikin wannan yanayin ba Bacci me nauyi ya yi awon gaba da ita.
Cikin Baccin kamar yadda Akhiee ya faɗa mafarkansa ta dinga yi, har abinda ya faru tsakaninsa da waɗanda su ka farmake shi sai da ta gani, wani ɓangaren kuma soyayya su ka zuba a mafarkin kamar ba za a mutu ba, haka ta dinga yinsu kala-kala har Allah ya wayi gari.
Jiki a muce ta tashi yau hakan ya sa ba ta yi yunƙurin fita makaranta ba, sai da yamma ta shirya tsaf sannan ta fito, Amadu da me Gadi su na zaune su na hira ta fito ɗogal-ɗogal wai ita makaranta za ta je.
Baki a sake Amadu ke kallonta har ta ƙaraso inda suke, cikin siririyar muryarta ta ce "Malam Amadu Makaranta zan je fa"
jinjina kai ya yi gami da cewa "Tirƙashi!!!! ai kuwa ban amince ki fita ba har sai kin tambayi mijinki."
Kamar za ta yi kuka ta ce "Makaranta fa zan je". "Ko nan da ƙofar gida za ki je indai ni zan kai ki sai kin tambayi Mijinki bare makaranta, sai in ke kaɗai za ki fita to wannan alhakin bai shafe ni ba ko a wurin Allah ba ni da laifi, ai ya baki waya, ki kira shi ki tambaye shi."
Magiya ta shiga yiwa Amadu amma ya ce shifa bai ji ya gani ba, dole ta ɗauko wayar ta tura masa kira don kuwa ta na son fitar.
Ta kira ya kai sau goma su na gaya mata waya yake yi............
**************************
A nashi ɓangaren kuwa wayar ta na maƙale a kunnensa ya zubawa wuri ɗaya idanunsa wanda kallo ɗaya za ka yi masa ka gane ya na cikin matsanancin hali, duba da yadda suka rikice su ka koma tamkar ba na ɗan-adam ba, a memakon su yi ja sai ma farin ya ƙara wani irin haske wanda har ya wuce na muhammadiyya, baƙar ƙwayar kuwa ta ƙara yin baƙi siɗik sai ƙyalli take yi tamkar baƙin ɗan Maciji har wani irin abu take yi tamkar tiriri, ƴar ƙaramar ƙwayar ciki kuwa ta koma Golden collor me duhu hakan ya ƙarawa idanun nasa wani irin haske da kwarjini har ma da abubuwan Al'ajabi, fuskarsa kuwa ta yi jajir tamkar irin jariran da ake haifarsu kamar ana latsa fatarsu jini zai yi tsartuwa, duk da jan da fuskarsa ta yi hakan bai hana inda Alburushin jiya ya sauka a duk jikinsa nuna kansa ba, duk inda Alburushin ya sauka a jikinsa ya yi wani irin jajir har a fuskarsa ya yi tabbai; cikakken bil'adam kuma me lafiya ba zai iya haɗa ido da shi a wannan lokacin ba.
a ɗaya gefen kuwa Surayya ce ke yi masa kuka akan irin cin zarafin da aka yiwa Ƴan Uwanta Zakiyya da Farhana, ya kasa ce mata komai don kuwa ba za ta iya fahimta ba sai dai su yi cacar baki don haka ya yi mata banza har ta gama ta katse kiran.
Kafin Kiran Husnee ya shigo kiran Firdous ya shigo, ya na ɗauka ya kara a kunnensa ta fashe da kuka wanda ya sa tsigar jikinsa ta mimmiƙe a lokaci guda, Cikin shashshekar kuka ta ce "Daddy!! na gaji da zama a ƙasar nan ina ganin tashin hankali iri-iri, ka na kallon abinda aka yiwa ƴan uwana, an yi musu fyaɗe ba sau ɗaya ba ba sau Biyu ba, sannan an Kashe Zakiyya an ƙwaƙule mata idanu!! Farhana ma bayan keta mata haddi an yi mata izaya kala daban-daban yanzu ta faɗa godon suma ba tabbacin ma za ta rayu, kuma sun ce abin bai ƙare ba yanzu ma su ka fara, Nan gaba Allah ne kaɗai ya san abinda Za su yi Baba!!!! ni dai ka fitar da ni ƙasar waje in ƙarasa karatuna a can ba zan iya zaman nan ba!!!!!!" ta ƙarasa maganar cikin kuka me natuƙar rikita tunanin me saurarensa.
Da ƙyar ya iya ɗaga harshensa ya magantu "Ki Zaɓi ƙasar da ki ke son zuwa ki tafi tare da Raihana, ki kula da ita sosai, in kin zaɓa ki yi magana zan shirya miki komai."
Daga haka bai bata damar sake yin magana ba ya katse wayar, wani kiran ne ya ƙara shigowa ba tare da ya duba kowaye ba ya kara a kunnensa gami da yin shiru.
Cikin rawar murya ta magantu "Akhiee ina son zuwa makaranta n..." kafin ta ƙarasa faɗe ya katse ta da cewa "Ban yarda ki fita ko'ina ba indai ba tare da ni ba, idan kuma kin ƙi ji har ki ka yi mini asarar ranki ki sani sai na ɗauki Fansa akan Danginki!!!!!." daga haka ya katse wayar, daidai lokacin wani sabon kiran ya shigo, bai yi ƙasa a guiwa ba ya ɗauka, Zulaihat ce, itama kuka take yi wurjajan, cikin jin zafi da ciwon abinda ya faru ta ce "Baba don Allah ko waye ya aikata hakan ga su Zakiyya kar ka barshi da rai shima ki yi masa abinda ya yi musu don Allah Daddy!!."
Lumshe ido ya yi kafin ya ce "I Promise you Zulaihat!" Ya na faɗen haka ya katse wayar domin amsa wani kiran da yake shigowa a ɗaya wayar ta shi.
"Mukhtar!!" shine abinda ya faɗa cikin wata irin murya me ƙunshe da yanayi kala-kala, Mukhtar ya ɗan yi gyara murya sabida dashewar da ta yi, kamar zautacce haka ya fara magana "Daddy! yanzu shi kenan ba zan ƙara ganin Zakiyya ba? me ta yi musu da za su yi mata wannan ɗanyen aikin? Ji nake kamar zanyi hauka wallahi don Allah Daddy ka dakatar da wannan abin tin kafin ya yi nisa" ya ƙarasa maganar gami da sakin wani marayan kuka.........
SHARE FISABILILLAH
Na Kuɗi ne....
Nomarl Grp 300 Posting ba kullum ba.
VIP 500 Posting Kullum.
domin ƙarin bayani 👉🏽09079885632
*©️INDO*
[8/27, 11:19 AM] INDO: https://chat.whatsapp.com/FuB2OR4qBx189IdAM0hXbG
*🪻SAHUN KEKE🪻*
Ep 19
©️
Ayeesha Abdulkareem INDO
*M.W.A🦅*
Cikin tausasawa ya ce "Kwantar da hankali Mukhtar! Lokacinta ne ya yi ba yadda za mu yi dole sai mun rasata ko ba ta wannan hanyar ba, bai kamata ka yi kuka ba; kamata ta yi ka rarrashi ƙannenka, kai fa Namiji ne, ba na son ƙara ganin hawayenka, ka bar komai a hannuna kuma ka manta da abinda ya faru ina so komai ya wuce."
Mukhtar ya ja numfashi ya sauke kafin ya ce "Amma ba yadda za mu yi haka za su dinga yi mana?" "Ta ya kake tunanin wani ƙaramin abu zai dawwama a Duniya?? lokaci juyawa ya ke yi, Ka kula da ƙannenka a shirya jana'izar Zakiyya kafin na iso."
Daga haka ya katse wayar ya yi wurgi da ita ta faɗi can gefe, safa da marwa ya shiga yi a wajen ya kai mari ya kai gwauro, duk iya nazarinsa ya kasa gane kowaye yake yi masa wannan zagon ƙasan, kuma ya na buƙatar sani tin kafin tafiyar ta yi nisa.
Ya daɗe cikin yanayin tunane-tunane kafin ya shirya domin zuwa wajen Jana'izar Zakiyya.
Husnee jiki a saɓule ta sauke wayar daga kan kunnenta ta na kallon Amadu kallon da ya ke nuni da cewar bai barta ba, Ya kalli Ahajiji Me Gadi ya ce "Ahaf!!! Allah na tuba Shu'umin Mutum irin wannan Yaron ne zai bar matarsa ta dinga yawo a gari? ai shi yasa na yi azancin cewa ta Tambayi Mijinta."
Alhajiji ya ce "A'ah iko sai Allah, to ni na kasa gane me kuke nufi ai, ba ku ga tin ɗazu na ke kallonku ɗaya -bayan-ɗaya ba Ni ai a sanina Husnee ba ta da Miji."
Amadu ya ce "Na shafa maka lafiya to yanzu Matar Aure ce, ga shi dai a gabanka ai ta tambayi mijin nata fita ya hanata"
"Matar Aure??? Mijinta kuma?? ita Husnee ɗin???" Mommy da ta iso wurin ba tare da sun sani ba ta jefo musu tambayoyin a jere.
Rassss Gaban Husnee ya yanke ya faɗi har ƙasa, jikinta ya fara karkarwa ta zazzaro fararen idanunta akan Mommy wadda ta ke kallonsu ita da Amadu Ɗaya-bayan-ɗaya kallo me cike da tuhuma gami da mamaki da ɓacin rai.
Amadu ya ji tamkar Motar Gingimari ta hau kansa lokacin da ya ji tambayar Mommy. Lokaci guda duk su ka shiga firgici da tashin hankali.
a ladabce Alhajiji ya ce "Hajjaju Makkatu ikon Allah barka da fitowa."
Mommy ta ce "Ba ka ji tambayar da na yi ba ne? shine ka ke kawo mini taka idea?"
Ya rissina gami da cewa "Ayi haƙuri, wallahi Hajiya nima yanzu na ke tambayarsu yaushe ne ta yi aure ban sani ba, Allah i sanya Alkairi."
Cikin tsawa Mommy ta ce "Husna!!! Dan Ubanki ba kya jina ne???? yaushe ki ka zama Matar wani????" zamewa ta yi ta durƙushe a wajen gami da fashewa da wani marayan kuka wanda sautinsa ma ya ba ya fita sosai, ta na so ta magantu amma ta kasa.
Jiki na tsuma Amadu ya ce "Ina zuwa Hajiya" cikin Mota ya nufa ya ɗauko kuɗin Sadakinta wanda ke nannaɗe a cikin hankicif, ya dawo gaban Mommy ya durƙusa jiki na ɓari ya ce "Hajiya Allah ya baku haƙuri, Ga wannan" cikin mugun mamaki ta sa hannu ta karɓa ta na ƙarewa hankicif ɗin kallo, Amadu ya ci gaba da magana murya na rawa "Hajiya waɗannan kuɗi su ne Sadakin Husnee, Jiya Wanda take so ya aureta, Hajiya ba laifina ba ne, Tilasta mini ya yi akan cewar ni zan karɓi Aurenta, mun ɗaura Auren a Masallacin wani Malami, Malam Kabiru" iya abinda aka yi a gabansa ya kwashe ya gaya mata.
Kallon Husnee ta ke yi cikin tsananin mamaki da al'ajabi, ta na yi ta na jinjina kuɗin hannunta. Cikin murya me nuna tsantsar ɓacin rai ta ce "Husnee? har kin yi girman da za ki iya bin wani ɗan iska ya aureki? Ashe duk burin Mahaifinki na ki yi karatu me zurfi ba ya cikin tunaninki?"
Girgiza kai ta ke yi ta na wani irin kuka wanda ke fitowa tin daga ƙasan Zuciyarta, murya a dishe ta ce "Ƙaddara ce Mommy don Allah kar ki zargeni sam ba laifina ba ne, nima ban zata abinda zai yi kenan ba."
Amadu ya ce "Gaskiya ne haka ne Hajiya ita ma ba ta zata ba, sama taka ya aikata hakan"
"To wai shin waye shi ? Su waye iyayensa a ƙasar nan da har zai aure mini ƴa ba tare da Sahalewata ba??"
Amadu ya ce "Ranar wanka ba a ɓoyon cibi Hajiya, Sunansa Muhammad Risslan Sheikh Muhammad Risslan, Ɗa ne ga babban Malamin nan na duk Hotoro da kewaye, kuma shi ɗin Babban Tantiri ne na kaf Nigeria, wasu na kiransa SARƘA wasu na kiransa SAHUN KEKE, kowa ma da irin sunan da yake gaya masa, ko kwanakin baya an kamw shi da laifin kisa amma sai aka sako shi domin ya fi gaban nan, wannan shi ne kaɗai abinda zan iya faɗe a kansa."
Duhu-duhu Mommy ta fara gani nan take jiri ya fara ɗibarta ta tafi luuuu!!! za ta faɗi Husnee ta yi kanta da gudu da nufin tareta, kafin ta ƙarasa Muddassir ya rigata, ya rungumota a jikinsa ya na tambayar lafiya.
Hawaye ne su ka shiga tsiyaya akan kumatunta, da kyar ta ce "Husnee ce!!! mu na zaune a gida ashe ta je ta Auri wani bayan mun yi wa Zaheer Alƙawarin aurenta, wai yanzu har ta yi girman da za ta iya zuwa ta Auri wani Namiji ba tare da sanin iyayenta ba?? har yaushe ta fara zuwa makarantar da ya hure mata kunne haka?"
Muddassir ya zubawa Husnee ido ya na binta da kallon tuhuma, a masife ya ce "Ashe ba ki da hankali? me ya sa za ki aikata haka? akwai wanda ya fiye miki iyayenki ne duk son da ki ke yi masa? Kwantar da hankalinki Mommy kowaye sai ya saketa ni zan je in yi magana da shi, mu ba za a yi haka da mu ba, ba ma son tantiranci."
Mommy ta ce "Shi ɗin Tantirin gaske ne kuwa, kuma Shaiɗani wai Sunansa Sahun Keke" dimm!!!!!!! Zuciyar Muddassir ta yi wata muguwar bugawa wadda ta sa numfashinsa ɗaukewa na wucin gadi.
"SAHUN KEKE!!!!!!" Ya maimaita kalmar cikin kaɗuwa gami da tashin hankali da firgici.
idanunsa na kan Husnee wadda take wani irin galabaitaccen kuka, a hankali ya ce "Mommy shiga ciki ina zuwa."
Mommy ta ja jikinta da kyar da kyar ta shige cikin gida ta na kuka ta na faɗin "Ai ko waye shi, Allah i sa Iblis ne sabida hatsabibancinsa sai mun yi shari'a da shi sai ya saketa, ba za ta taɓa zama da ɗan Ta'adda ba."
A kiɗime Muddassir ya matsa kusa da ita ya durƙusa a gabanta su na fuskantar juna, cike da son tabbatar da abinda kunnensa ya jiye masa ya ce "Da gaske ne Kin zama Matar Sahun Keke???"
cikin shashshekar kuka ta ce "Amma ba laifina ba ne don Allah ku yi haƙuri kar ku yi fushi da ni!!" jinjina kai ya yi cikin wani irin yanayi na tashin hankali da ya riske shi, "Husnee ki na nufin Sahun Keke ya na sonki ne ko kuma ya yi hakan ne kawai don wata manufar? ke ma ki na son shi ne? a ina ki ka haɗu da shi??"
A jere ya zubo mata tambayoyin cikin kiɗima.
ba tare da ta dena kukan ba ta ce "Ba don wata manufa ya yi ba, sabida ina son shi ne ya sa shi yin hakan, don Allah Yaya kar ku rabani da shi ni ina son shi a haka duk da irin halayensa."
Muddassir tamkar zai fashe da kuka ya ce "Duk faɗin Duniya Husnee ki rasa wanda za ki so sai wanda bai ɗauki ran Mutum a bakin komai ba?? anya kuwa kin yi tunani? yanzu ƴaƴan da za ki haifa ya sunansu?? ki temaka mana ki temakawa kanki ki rabu da shi."
kai tsaye ta ce "Ba zan iya ba Yaya!!! ba yin kaina ba ne Allah ne ya jarrabeni da son shi, so me tsanani wanda na ke jin tamkar shine bugun Zuciyata Yaya!!!"
Miƙewa ya yi ya na bubbugar kansa da ya gama hautsinewa gami da juyewa, yarfa hannunsa ya yi ya na cewa "Kaih!!! Impossible ta ya-ya zan bari ya auri ƙanwata??" No ba zai yuwu ba!" ya yi maganar tamkar wanda ya fara zaucewa, kamar an tsikare shi ya zabga da gudu zuwa cikin gidan.
Husnee ta miƙe ta na ɗingisa ƙafa da ƙyar fa ƙyar ta bi bayansa.
Ya na shiga ya Zauna kusa da Mommy ya na cewa "Mommy ta ya-ya kenan? Ta ya Auren Husnee zai halatta ga wannan Ɗan ta'addan, ya zama dole mu ɗauki mataki!!" Mommy ta sa ɗan hankicif ɗinta ta fyace hanci sannan ta ce "Ai na kira kowa da kowa na sanar musu abinda ya faru, kwantar da hankalinka dole ne a raba Auren nan indai da gaske ne an ɗaura shi."
Da sauri Muddassir ya ce "Yess ta yuwu ma ba a ɗaura ba, ba ri in je in tambayo wanda ya ɗaura ɗin ko Ƙarya su ka yi mana."
Bai jira ta ce komai ba ya fice da gudu kamar ƙaramin yaro, Amadu ya tambaya bayanan wanda ya ɗaura Auren Amadu ya gaya masa komai, nan ya zabare shi da sunan ya raka shi wajen Malam Kabiru.
Husnee na tsugunne gaban Mommy ta na kuka ta na neman yafiyarta amma sam
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 12 Chapter of 19