jikinsa yake ba bai bi ta kanta ba ya nemi wuri kan Sofa ya zauna gami da buga tagumi ya lula duniyar tunani.
A hankali sautin kukanta ya fara dawo da shi hayyacinsa ya yi saurin miƙewa ya na cewa "Mom what happened to you??"
Haɓar zaninta da ya kwance ta janyo ta face hanci sannan ta ce "Ba abinda bai faru ba ma, inuwar mata na gani ta na bina ta na tsorata ni, kai kuma ba ka tashi shigowa ba sai da ta tafi, inda kasheni ta yi sai dai ka zo ka ɗau gawata kenan ko?" zama ya yi a gefenta ya ce "Ke ce ba ki da aiki sai bin bokaye Mommy,, ƙila ma wani kika yiwa asiri ya dawo kanki, ai ga ranarta nan sai ki dena."
Ta ja numfashi ta sauke, cikin muryar kuka ta ce "Ba za ka gane ba ne Yazeed ka barni da abinda yake damuna!"
rai a ɓace ya ce "Nima ina da damuwa me tsanani ma kuwa, kuma ko shakka ba na yi kece tushen damuwar tawa; Allah ya sawwaƙe to" ya na kaiwa nan ya tashi ya bar mata Falon.
Ya na fita kuwa tsoro ya ƙara kamata ta yi sauri ta tashi ta fita can harabar gidan don kar ma a ƙara ritsata a ɗaki.
01:32AM kowa ya rintsa amma ita baccin ya gagari idanunta, kwanciyar ma har ta isheta don haka ta tashi ta zauna gami da zuba tagumi ta ci gaba da tunane-tunane, ta na cikin wannan Halin ta ji wayarta na ƙara a ƙarƙashin filo, jiki a sanyaye tamkar wadda aka zarewa laka ta zura hannu ta janyota, zuba mata ido ta yi na ɗan lokaci sannan ta ɗauka da wani kiran ya ƙara shigowa.
"Yau ma ba ki yi bacci ba Ko?"
cusa kanta ta yi a tsakankanin guiwoyinta ba tare da ta ce masa ƙala ba, jin ta yi shiru ya sa shi cewa "My wife!!"
ya yi maganar cikin wata kasalalliyar murya me ƙunshe da saƙonni daban-daban wanda kai tsaye ta fito tun daga ƙasan Zuciyarsa, ta yi saurin lumshe idonta gami da sauke sassanyar ajiyar Zuciya, cikin muryarta da ta dashe ta ce "Akhiee!! tunani ya hanani bacci, da na rufe ido nake fara mafarkai."
"Idan ki na gaya min haka hankalina gaza kwanciya yake yi Asma'u, ki samu nutsuwa don Allah."
Gyaɗa kai ta yi tamkar ya na kallonta.
Sun ɗauki lokaci su na sauraren numfashin juna ta wayar ba tare da kowa ya yi magana ba, Akhiee ne ya kaste shirun da cewa "Ki na da babban matsayi a wajena, kar ki cutar da kanki ta hanyar bin son Zuciyata, ki nutsu ki yiwa kanki zaɓi duk hukuncin da kika yanke na amince; Asma'u! ba wani abu da zai sa na sake ki sai dai in kece kika furta cewar ba kya sona ko kuma ba kya so ki rayu tare da ni, indai kin furta hakan a take nima zan sakeki, saɓanin haka kuma ba zan iya rabuwa da ke ba, indai kina son farantawa iyayenki ta hanyar rabuwa da ni kina da dama; Ki yi bacci sosai Sai mun haɗu a Kotu gobe."
Daga haka ya katse ba tare da ya bata damar ta yi magana ba, bin wayar ta yi da kallo kalamansa na dawo mata, nan take su ka shiga yi mata juyi a ƙwaƙwalwa, menene mafita? ta bi iyayenta ta rabu da shi? ko kuwa ta zaɓeshi a matsayin abokin rayuwarta??, shawarwarin da take nema kenan sai dai ba ta da me bata.
Cikin wannan yanayin bacci me nauyi ya yi awon gaba da ita.
Washegari jirgin su Abhie da Jaafar ya sauka kuma yau ne ranar komawa Kotu.
Tinda ya iso ya fara tambayar Akhiee, su Yasayyadi Usman masu jiran kaɗan suka fara rattaba masa abinda ke faruwa, ga mamakinsu sai su ka ga sam abin bai ɓata masa rai ba sai ma albarka da yake sawa Auren jin haka ya sa suka ja bakinsu su ka tsuke.
Kamar dai ranar nan kowane ɓangare sun halarci Zaman, kowa da nashi Burin a Zuci, duk da sun yi tarayya ta wajen son raba Auren sai dai daga cikin Dangin Akhiee akwai masu son ganin wani mummunan abun ya faru da shi bayan haka.
Abinda ya matuƙar ɗaure musu kai, bayan gabatar da ƴan Hujjoji da ƴan ƙalabusai daga bakin Lauyan da ke Kare masu ƙara kai tsaye Mai Shari'a ya ce "Bincike ya tabbatar da cewar Wannan Aure ya Ɗauru, yanzu Husna Matar Muhammad ce shi yake da hurumin sakinta, har sai ya Amince sannan Saki ya yuwu."
Turusss! suka yi kowa ya kasa wani kyakkyawan motsi, duk a tunaninsu Kotu za ta raba auren ta ƙarfin tsiya.
Ko da aka tambayi Akhiee buɗar bakinsa ya ce "Ni a karan-kaina ba zan iya rabuwa da Matata ba, amma indai ta ce in saketa zan saketa." daga haka ya ja bakinsa ya tsuke.
Asma'u kuwa ya jefata a wahala, ta shiga tsitstsilla ido ta na kallonsa ta na kallon Mommy da Daddy har ma da su Muneeb da suke ta yi mata muzurai, wasu zafafan hawaye ne suka shiga tsere akan fuskarta, ta zubawa Akhiee ido tamkar ba za ta ƙara ganinsa a Dunyar ba.............
*©️INDO*
[9/7, 8:15 PM] INDO: *🪻S-K🪻*
Ep 23
Ta daɗe ta na kallonsa shi kuwa ya ƙi bata damar su haɗa ido sai ya yi tamkar bai ganta ba, rintse ido ta yi da ƙarfi kafin ta fara magana cikin rawar murya "Ina son shi! da shi nake so na rayu har lokacin mutuwata, sai da na riga na zaɓeshi a matsayin abokin rayuwata kafin ya Aureni, don Allah kar ku rabamu.
Mai Shari'a ya numfasa ya gyara gilashin dake kan idanunsa sannan ya ce "A barwa me Mata Matarsa itama yarinya a Bar mata Mijinta, Kotu ta Amince da Auren Husna da Muhammad, a bisa sharaɗi na ci da sha tufatarwa da sauke haƙƙin iyali duk ya rataya a wuyansa, Kotu ba ta Amince wani daga ɓangaren Miji ko ɓangaren Mata ya tayar da wata hatsaniya akan Hukuncin da ta yanke ba.
Daga haka ya bubbuga ƴar gudumarsa Kotu ta tashi.
Cikin ƙasaitaccen takunsa ya fito daga inda yake tsaye, kai tsaye wurinta ya nufa ya kama hannunta ba tare da ya bi takan kowa ba ya nufi hanyar fita daga Kotun, ita dai ta bishi da ido sai ɓazga kuka take yi.
Suna fita suka yi karo da cincirindon jama'a har da ƴan Jarida, an zo kallo da samun labarai masu waya na ɗauka su ma Ƴan Jarida su na ɗauka.
Wani daga cikin Ƴan Jaridar ne ya bugi ƙirji ya matsa kusa da Akhiee ya na cewa "Ranka-yadaɗe Minti ɗaya don Allah ka amsa mana tambayoyinmu."
Tamkar da dutse yake magana haka Akhiee ya yi masa banza, sai ma wucewa da yayi wajen wata lintsumemiyar Mota me Numfashi, da ka ganta ka san ta manya ce ba ƙananu ba, nan ma mutane su ka bisu riiiiii don kar a yi ba su.
Cikin rawar murya gami da fargaba ta ce "Ina za mu je Akhiee!??"
Haɗata ya yi da jikin Motar ya yi mata rumfa ya na zuba mata idanunsa da ke ta sheƙi da walwali, cikin wata sirrintacciyar murya ya ce "Yau tare da ni za ki kwana, ba zan bari ki ƙara nesanta da ni ba". da Sauri ta ɗago idanunta da su ka kukkumbura sabida kuka ta jefasu cikin nasa tare da cewa "Akhie...." saurin rufe bakinta ta yi ganin ya rintse idanunsa gami da kamo gefen leɓensa ya cije shi da ƙarfin gaske, "Tell me!" ya faɗa a taƙaice bayan shuɗewar ƴan sakanni, ƙasa ta yi da kai kafin ta ce "Ban yi sallama da iyayena da Ƴan uwana ba, na san su na fushi da ni, ina buƙatar na nemi yafiyarsu, kuma su ya kamata su rakani ɗakina!!" ta ƙarasa maganar gami da sauke wata zazzafar ajiyar Zuciya.
a hankali ya buɗe idanun nasa ya zuba mata sannan ya ce "Yanzu ni kike buƙata ba su."
sharr!! hawaye su ka ci gaba da zubowa kamar dama jira suke ya yi magana, ta buɗe baki za ta yi magana ya dakatar da ita ta hanyar yi mata alama da idanunsa wanda zuwa yanzu ta fara karantar Yarensu.
Janyeta ya yi gefe sannan ya buɗe Motar, cikin sassanyar muryarsa ya ce "Look! she's my small Mommy."
Sai da ta goge ƙwalla sannan ta iya zazzaro ido ta na kallon cikin Motar, wata haɗaɗɗiyar Mata ce Babbar Mace wadda hutu da jin daɗi suka zauna, sanye take cikin dakakken Leshi Baƙi wulik an yi masa adon Orange me duhu, ya sha Beads work ta ko'ina, Mayafinta ma Orange ne an yi masa adon Beads work baƙi, komai ya ji banda tsiya in ji maroƙa.
Sassanyan murmushi ta sakar musu kafin ta ce "Come hare my daughter!" a tsorace Husnee ta yi baya ta na kallon Akhiee gami da cewa "Wacece??" "Mamata ce, kema Mamarki ce kuma ita za ta yi miki duk abinda Uwa take yiwa Ƴarta, a tare da ita kuma akwai Ƴan Uwana, tare za ku tafi, ni zan tawo daga baya."
Rushewa ta yi da kuka kamar an ce gobe za ta mutu, cikin shashsheka ta ce "Ni dai tsoro nake ji ka shiga mu tafi tare."
girgiza kai ya yi kafin ya ce "Ni wanene to Amsa'u?, ki na tare da kariyar Allah ba kya buƙatar kariyata, nima shi ne yake kareni."
Matar cikin Motar ce ta ce "Mutane dai su na kallonku Ƴata, ki bari idan kun haɗu a Ɗakinku sai ku tattauna."
Sai a lokacin ta tuna fa ashe da dubban idanu a kansu, shiga Motar ta yi ta zauna sannan ta ce "Akhiee don Alla....." zuba nata idananun da ya yi ne ya sa ta fasa maganar, bai ce komai ba ya rufe Motar gami da juyawa.
Ya na jin Mutane su na bidiyo su na bada labarin wannan shine Ɗan Daba mafi haɗari a Ƙasar Nigeria kuma yau ne Kotu ta mallaka masa Matar da ya aura ba bisa ƙa'ida ba, bai bi takan kowa ba ya ƙarasa inda su Salansa ke tsaye tare da Prince, su ma bai ce musu komai ba ya ya ci gaba da tafiya.
Motoci uku ne su ka yi Parking a Ƙofar gidan su Akhiee. Jin an dena tafiya ya sa Husnee ta ƙara sakin wani sabon kuka don yanzu ta tabbatar an zo inda za a watsar da ita.
Inna ce ta kalleta cikin nutsuwa ta ce "Ki dena kuka ki yi haƙuri, kowace ɗiya mace ta gaji haka, dole ne wata rana sai ta rabu da iyayenta ta tafi gidan Miji; ki ɗauka nan ma gidanku ne, kuma ina da yaƙini akan Ɗan Manya zai riƙe ki da daraja kuma zai kare haƙƙinki, Allah ya sanya alkairi ya baku zaman lafiya."
Ba ta iya cewa komai ba sai dai ta sassauta kukan. Mukhtar ya ce "Yanzu shiga ciki za ku yi ko sai kun jira an zo an shigar da ku?"
kafin Inna ta yi magana Rahma ta buɗe Murfin Motar ta na cewa "Mama ku fito mu shiga mana."
Maman ta ce "Okay mu je ɗin, kama hannunta."
Rahma ta murmusa gami da cewa "Allah Sarki yarinya mu ma haka aka yi mana muna ta kuka aka kaimu aka baro."
Husnee kuwa ta na jin haka ta ƙare ɓare baki, Inna ta ce "Ke Rahma kul! ki na tsorata yarinya a memakon ki rarrasheta?"
Dariya kawai ta yi ba tare da ta ce ƙala ba.
Sai da Inna ta yi rarrashi sosai sannan Husnee ta fito daga cikin Motar suka rankaya zuwa cikin gida tare da su Zabira da su Surayya.
Sun yi sallama a tsakar gidan ta fi sau goma amma an yi musu banza, Su Innajo da su Umma Uwani su Inna Huwaila su na zaune a can gefe sai kallonsu suke yi sama da ƙasa suna tsegumi.
Zahra da ke kwance a ɗakinsu ba lafiya ta lallaɓo ta fito ta na amsa sallamar. Umma Uwani ta ce "Ke ubanki! me za ki je ki yi musu?? kin san irinsu??" kamar za ta yi kuka ta ce "Amma ko ban san irinsu ba ai mu Musulmi ne ya kamata a amsa musu sallama, bare kuma na san ba wani mugun abun ne ya kawosu ba, Husnee ce dai ba kwa so kuma Allah ya yarda ta zama Ƴar gida sai dai ayi haƙuri." Inna Huwaila Matar Baba Sa'idu ta shiga tafa hannuwa ta na cewa ''La ilaha illallahu waɗannan ƴaƴa ba kunya, ku ji itama ta kangare yarinyar nan??" ta faɗa ta na kallon Innajo gami da riƙe haɓarta alamar mamaki, Innajo ta taɓe baki kafin ta ce "Shegiya me kama da tsintacciyar Mage, ai mun yi mata komai dole ta yi mana rashin kunya akan wannan ɗan Kukar."
Ba ta sauraresu ba ta wuce inda su Inna suke ta na fara'a ta ƙarfin hali, "Sannunku da zuwa, ku shigo in raka ku Ɗakin Akhiee inaga anan ne za ta sauka."
Inna da Aunty Rahma suka amsa sannan sannan su ka rufa mata baya.
Bayan sun huta a Ɗakin ne Laita ta ja dogon tsaki ta ce "Wallahi Allah na kusa hudawa Mace tumbi a gidan nan, in banda rainin hankali suna kallonmu amma sai kace mun zo musu da ajalinsu?" Zara ta ce "Allah ya baku haƙuri, halin gidan yawa ne sai Addu'a" Inna ta ce "Haka ne Ƴar nan, kar ki damu mu ba mu yi fushi ba, kema Faɗimatu ki bar zancen kar na ƙara ji" ta ƙarasa maganar ta na kallon inda Laita take tsaye tamkar shuka.
Nasihohi sosai su Inna da su Aunty Rahma su ka yi wa Husnee sannan su ka yi mata sallama suka tafi.
Ɗakin ya rage daga ita sai Zara sun yi jungum-jungum ba me tashin wani a tsakaninsu.
Tare suka zauna har dare ya yi sannan Zara ta yi mata sallama ta koma sashinsu.
zuwa yanzu ta ci kukan har ya yi mata karo ba za ta iya yinsa a yanzu ba, don haka ta yi shiru ta na sauraren ƙarar kaɗawar ganyen bishiyun da ke bayan ɗakin wanda iska take kaɗa su, tunane-tunane kala-kala suka sakota gaba, Jefi-jefi takan sauke ajiyar Zuciya don har yanzu ba ta gama dawowa daidai ba.
Cikin tsananin ɓacin rai Muneeb ya ce "Ai in ya san wata bai san wata ba, wallahi sai mun ɗaukaka Shari'ar nan in ya so a dinga yinta har Duniya ta tashi, shima ɗan iskan Alƙalin ai siye shi suka yi shi yasa ko bin Shari'ar akan ƙa'ida bai yi ba, ba wani bincike da ya yi tinda kawai ya yiwa mutane ƴar burum-burum ne."
Muneer ya ce "Ni babban baƙin cikina ma ka ga Yanzu Mommy ba ta da lafiya sabida baƙin cikin wannan abu, ka ga Daddy ma duk ya shiga damuwa, dole ne ma mu san abin yi."
Daddy ya yi gyaran murya kafin ya ce "Ni ba wanda ya ban mamaki irin Husna, ban taɓa zaton za ta iya riƙe hannun wani ɗa ta tsallake ta barmu ba."
Muneeb ya yi zaram ya ce "Kuma sai gashi ta yi ba?, ai dama wani ba a gane halinsa har sai ya aikata tukunna, in banda iskanci irin nata uban me za ta ci da wannan tantirin?, ba ku ga yadda jama'a suka taru suna ɗaukar labarai ba? inda za ku san ba ƙaramin ɗan iska ba ne, wai ni abinda yake ban mamaki ma duk hannun hukumar da ya shiga sala-sa'ilin saɓalula haka za ku ga sun sake shi ba tare da an ɗauki mataki akansa ba, yanzu ka ga Shari'ar nan ai duk me hankali in ya duba ya san ba Shari'a aka yi ba kawai an ƙara tabbatar da Aure ne."
Ahmad da ya zuba tagumi sai yanzu ya yi magana kamar zai yi kuka "To wai duk meye amfanin maimaita zancen? ta riga ta faru ta ƙare an yiwa me dami ɗaya sata, tinda har Allah ya sa kun gane cewa hukuma ba ta iya aiki akansa meye naku na wahalar da kanku? kun san ko kun ɗaukaka ƙara sai dai ku ƙara tozartamu a banza."
a fusace Muneeb yace "Yi mana shiru dan ubanka, kai ai mahaukacu ne ba ka san ciwon kanka."
Muddassir ne ya kalleshi cikin ɓacin rai ya ce "To kai da ka san ciwon kan naka kar na ƙara ji ka ɗaga maganar in ba haka ba ranka zai ɓaci, haba!! Yarinya ta na da ƴancin da za ta zaɓi wanda take so kuma ta rayu da shi, ina ruwanku da halayensa? ko ku za ku zauna mata da shi?"
Muneeb ya buntsire baki kafin ya ce "Amma ai ana duba kyakkyawan iri kafin a haɗa alaƙa, yanzu ina daɗi a ce ƙanwarka ce take auren wannan taƙadari....." katse shi ya yi da cewa "To sai ka yi duk abinda za ka iya, Daddy na roƙeka don Allah kai kuma ka ce ba ruwanka, ka ma dena sa damuwa a ranka kar kaima ka kama rashin lafiya, ita ma Mommy na ɗan lokaci ne za ta miƙe."
Daddy ya rausayar da kai gami da cewa "Toh!! Muddassir idan ban kwantar da hankalina ba ya zan yi?, ai ba kowane ya jawo min ba face ƴar cikina, na barta ta je ta yi rayuwarta Allah ya sa albarka, amma abu ɗaya nake so ku riƙe shine ba ruwana da ita ta yi rayuwarta in yi tawa, sannan ku ma ban yarda wani ya ƙara zumunci da ita ba, tinda ga wanda ta zaɓa ai sai mu barta da shi, kar ku ƙara ɗaga zancen tinda an riga an fi ƙarfinmu."
Muneer zai yi magana Muddassir ya hana shi, sai ma ya bisu da wasu ƴan nasihohi kamar gaske.
Wayarsa da take ruri ya ɗauka gami da karawa a kunne ba tare da ya yi magana ba.
a ɗaya ɓangaren me kiran ya ce "Sunana Abdulkadir Yahya Sumaila, ina fatan komai lafiya?"
Da sauri Akhiee ya ce "Respect ya Mai Shari'a, na gode da temakonka."
Mai Shari'a ya murmusa kafin ya ce "Ai ka wuce hakan a wurina, ai da ka sanar da ni abinda yake faruwa tin kafin ayi zaman farko da ba za a yi zama na biyun ba, sai da Abokina CP Abubakar Ado Gezawa ya sanar da ni komai sannan na gane."
"Yanayi ne ya zo da haka Yallaɓai!!, amma tinda komai ya yi daidai ina godiya."
Mai Shari'a ya ce "Ina yi maka fatan Alkairi tare da fatan Allah ya ida nufinka."
''Na gode" kawai ya ce ya katse kiran.
Yasayyadi Usman, Babban Yaya, Yasayyadi Jameel, Habu, Jaafar, Habibu, da sauransu zaune suke sun yi rukuni suna taɗi akan abinda ya faru a Kotu, Habibu ya ce "Ai na san dama haka za ta faru wallahi, ai wannan Yaro ya buwayi Duniya ya fi ƙarfin kowa." Yasayyadi Usman ya ce "Ai kuwa in ya san wata bai san wata ba, ai ta yaro kyau take ba ta ƙarko, in ya saye Alƙali ai mu ba za mu sayu ba, abinda nake so mu yi yanzu shine mu kama ƙafa da Baba Sa'idu mu samu mu zizziga Abhie ya ce bai yarda da Auren ba."
Babban Yaya ya ce "Ni fa har yanzu na kasa yarda Ɗan gidan nan ne Yaron nan, burina kullum bai wuce na ji ranar da Abhie zai buɗi baki ya ce ba ɗansa ba ne."
Jaafar ya yi saurin cewa "Wallahi nima haka, ni har Addu'a ma nake yi Allah ya nuna min wannan ranar."
Yasayyadi Jameel ya ce "Ai kuwa ba za ku ganta ba don wallahi Abhie ya ma fi son shi, kuma ban ga dalilin da zai sa ya ce ba ɗansa ba ne."
"Yanzu duk ba wannan ba, ya za ayi mu samu Abiee ya raba Auren?" ya jefa musu tambayar gami da yi musu zuru da ido don jin ta bakunansu, nan fa su ka fara tattaunawa kowa na kawo ta shi Idea.
Wayar Inspector Khalil ce ke ta famar ƙara yayin da yake banɗaki ya na watsa ruwa, Zulaihat ce ta ɗauka ta na cewa "Ana kiranka ko in ɗauka ne??"
Rass gabansa ya yanke ya faɗi, da sauri ya ce "Kar ki ɗauka ina zuwa."
Taɓe baki ta yi sannan ta mayar ta ajiye masa, ba tare da ya shirya ba ya ganganɗa ya fito, ya na fitowa ya aiketa kawo shayi don kar ta ji abinda zai ce, ta na fita ya yi sauri ya ɗauki wayar ya maida kiran ta na shiga aka Ɗauka, muryar DCP Khashim Bello ce ta ratsa kunnuwansa..... "Shi farin ciki yake yi abinsa ƙarshe ma har da Aure ya yi, kai kuma ka na kwance ka na bacci ko??"
"A'a yallaɓai, ai naga JD ya shiga lamarin ne shi yasa na janye jikina."
"Don JD ya shiga ai ba ya na nufin kai ka fita ba, hakan dama ce ta samu wadda za mu dinga rarraba masa hankali; a memakon ka hanashi sakewa a matsayinka na Jami'i amma ka bar shi sai abinda yake so yake yi, idan ba za ka iya ba za mu tuɓeka mu kawo wani; mu na buƙatar shigo da kaya amma ka ƙi yin komai a kai."
IP Khalil ya ce "Sorry sir, zan ci gaba da ƙoƙari, na ɗauka an bani hutu ne shi yasa." DCP Khashim Bello ya rafka tsaki kafin ya ce "Last warning, kar ka kuma yin sake kamar yadda ka yi."
"Yes sir!" ya faɗa cikin girmamawa.
Zulaihart da ke tsaye a bayansa ta na saurarensa ta kalleshi cikin ɓacin rai ta ce "Ni dama na san ba banza ba, na san ba tsakani ga Allah kake aikinka ba, yanzu meye ribarka don ka na yiwa ƴan ta'adda aiki suna biyanka kuɗi? da kai da su fa ba ku da wata maraba."
"Ni haka na ce miki aiki nake yiwa wasu? da DCP nake magana fa ba da wani ba kuma akan matsalar tsaro ne" ya faɗa cikin borin kunya da rashin sanin abin yi, murmushin takaici ta yi gami da cewa "Hmm! idan da gaske ne ai da CP ya kamata ka yi magana ba da DCP ba tukunna, kuma naga ya na yawan kiranka har da ma wani JD ko?, ko za ka shiga kogin rantsuwa ba zan yarda ba, kuma sai na gaya maka gaskiya, ka dena sabgar nan ka koma Jami'in ƙwarai tin kafin lokaci ya ƙure maka."
"Don Allah ni ki ƙyaleni, duk abinda na yi ai umarni na karɓa ko?, kar ki sa min ido akan aikina ki barni ni na san abinda zan
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 16 Chapter of 19