Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
su ka gauraye bukkar, kwata-kwata ba a ganin komai sai ƙarar guguwar wadda iyakacin cikin bukkar ta karaɗe, Hajiya Sauda da Hajiya Laure su ka haɗe kai su ka ƙanƙame juna. Guguwar ta kai tsawon minti guda 1 har da ƴan sakanni ta na juyawa sannan ta tsaya cak, wani jan haske ya tsago daga jikin bango sai ga boka Barore tsubul a zaune, sai kuma haske ya dawo daidai. a tare su ka numfasa musamman Hajiya Laure da ta yi tunanin abinda su ka zo shukawa ne ya fara tsiro ta kansu, ashe haka salon yake. "Boka Barore ya bada damar a zaunahhhhh!!" boka barore ya faɗa ya na dariya. Zama su ka yi a ɗan nesa da shi cikin rawar baki Hajiya Laure ta ce "Sannu da aik..." kafin ta ƙarasa ya katseta da cewa "Ba a zama nesa da mu, a dawo gabanmu a zauna" da sauri su ka ƙarasa can gabansa sannan su ka zauna su na fuskantat juna, ƙare musu kallo ya yi kafin ya ƙyaƙace da wata mahaukaciyar dariya da ta sanya su ka tsargu da kansu. "Kin zo akan batun wani yaro me suna Muhammadu wanda ya kashe miki miji, wannan Yaro ba zai taɓu ba sam! hhhhh" ya ƙara kecewa da dariyar mugunta. Kallon kallo Hajiya Laure da ƙawarta su ka yi kafin Hajiya Saudah ta ari baki ta ce "Boka Barore, ka na nufin mun zo a banza kenan ba yadda za ayi mu ci galaba akansa?" cikin tsawa ya ce "Keh!! wa ya gaya miki ana zuwa tsibirinmu a tafi ba biyan buƙata, dole ne sai mun yi masa illa, za mu taɓa shi ta hanyar waninsa, wanda in aka taɓa shi zai ji ciwon." Hajiya Laure ta ce "To ai inaga ma ba shi da mata bare ƴaƴa." "Ya na da ƴaƴa da yawa, ya na da ƴan uwa da yawa, ya na da mutane da yawa, nasara ta sameku!!!! Dole ne sai mun cutar da shi,,, za mu zami inda ya kamata mu tura ƙullinmu, ku ajiye kuɗi ku tashi nan da kwana uku ku dawo mini da kyakkyawan labari¡¡¡¡" jiki na rawa Hajiya Laure ta zaro ta dire masa ta miƙe ta na cewa "To mun gode Boka!" "Tsaya!!! a fita da tsalle!!!! wannan dokar baƙin Aljanin da zai muku aiki ce" Da ƙyar su ka iya kai kansu bakin ƙofa da tsallen sabida nauyin jikinsu dukkansu akwai ƙiba ba siririya. Sai da suka fita su ka yi ta maida numfashi, musamman Hajiya Laure ta fi shan wahala don ta fi Haj Saudah ƙiba. Haka su ka dawo gida cike da murnar yin nasara da su ka yi. Wuni da kwana Boka Barore ya yi yana fafata aiki har ya samu nasarar haɗa mugun tsafinsa kuma ya tura. Akhiee haka kawai ya tsinci kansa da son zuwa makaranta, ba tare da wani ya sa shi ba ya shirya ya je sai dai ko aji ya ƙi shiga, har aka tashi Husnee ta zo ta same shi nan a tsaye, tinda ta fara yi masa surutu bai ce ko kanzil ba har ta gaji ta yi shiru. Sun ɗauki lokaci a tsaye ba me yin magana sannan Husnee ta katse shirun da cewa "Za ka ci Ayaba?." Akhiee ya na tsaye a bakin wata ƙorama ya zubawa farin ruwan da ke gudana a cikinta ido, zuciyarsa kawai ƙuna da raɗaɗi take yi, tunanin me tsaurin idon da ke ƙoƙarin turo masa tsafi yake sai dai a iya nazarinsa ya kasa gane kowaye. Ya na cikin tunanin ya ji gurnanin Zaki a bayansa, juyawa ya yi ya na kallon Zakin wanda shima shi yake kallo, nan fa su ka shiga yiwa juna kallon-kallo kowa na ƙara fusata, Zakin ya yi wani huci gami da gurnani ya girgiza ya yo kan Akhiee da wani mugun gudu. Tsintsiyar hannunsa duka biyun ya sa ya kare fuskarsa tare da tsayawa kyam ya miƙa wuya ya saduda don kuwa bai san yadda zai yi ba sai dai abinda Allah ya yi. Wata muguqar kwasa ya yi masa ya bangaje shi su ka faɗa cikin ruwan tare, ko shurawa Akhiee bai ƙara yi ba tuni ya nutse a cikin ruwan ko alamunsa babu, Zakin ya yi wata girgiza gami da yin sufa ya yi gefe......... SHARE FISABILILLAH Na Kuɗi ne.... Nomarl Grp 300 Posting ba kullum ba. VIP 500 Posting Kullum. domin ƙarin bayani 👉🏽09079885632 *An fara Payment🤸🏾‍♀️ ku ƙoƙarta ku mallaki naku* *©️INDO* [8/17, 11:44 AM] INDO: *🪻SAHUN KEKE🪻* Ep 11 ©️ Ayeesha Abdulkareem INDO *M.W.A🦅* Zakin Ya na direwa a gefe ya zamo mutum, kamanninsa da tsayinsa da komai irin na Akhiee ne sak har kayan jikinsa, dariya ya yi hakan ya ƙara fito da tsantsar kyawunsa, cike da zolaya ya ce "Yau duk ina zafin kan naka?" Daidai lokacin Akhiee ya yo fitar burgu daga cikin ruwan tare da wurgo masa wata sharɓeɓuyar wuƙa fara tarr sai ƙyall da ɗaukar ido take, cikin hanzari ya yi gwauron tashi ya dire a gefe har lokacin dariya yake yi wadda take ƙara dugunzuma zuciyar Akhiee, jikinsa har kakkarwa ya ke yi sabida ɓacin rai, "Na rantse da Allah Russlan ka bari na kamaka sai na kakkarya ka, na gaya maka ba na son wasan banzan nan naka ko? ka barni da abinda yake damuna amma ka zo ka na ƙara tunzura ni; za ka sa na yi ɓarnar da ba za ta yiwa kowa daɗi ba wallahi." Ya yi maganar ba tare da alamun wasa ba, jin haka ya sa Russlan ya dakatar da dariyar, cikin sigar rarrashi ya ce "Yi haƙuri mana, ai abin bai yi zafi haka ba, ni ban san ranka a ɓace yake ba Allah i baka haƙuri jarababbe." jin ya kira shi da jarababbe ya sa ya ƙara hassala, ya buɗi baki zai ƙara zaro wata maganar Mother ta iso wajen, cikin yanayinta na kamala ta ce "Russlan ba ka san cewa ɗan uwanka ya faɗo daga sama ba ne? jikinsa na ciwo shine za ka ƙara zuwa ka tayar masa da hankali?" ido Russlan ya zazzaro gami da cewa "Da gaske? sannu Brother!" dogon tsaki kawai Akhiee ya doka ba tare da ya ce uffan ba, Mother ta kama hannunsa ta zaunar da shi gefe, Towel ta sa ta na tsane masa gashin kansa wanda ya sauka a gadon bayansa, fuskarta ɗauke da lafiyayyen murmushi kamar kullum, cikin sassanyar muryarta ta ce "Me yasa za ka faɗo daga sama haka? Domin wannan Yarinyar ne?" Ƙasa ya yi da ido kafin ya ce "Mother! sabida ni ne hakan ta faru, da ace ban je makaranta ba ma da Allah ne kaɗai ya san abinda zai faru da ita, Tsafi ne aka turo, kuma don ni aka turo shi amma ya tafi zai faɗa kanta, shine garin na janyeta na taka ɓawon ayaba sai muka faɗo, amma mutane gani su ke yi kamar wani abu na yi mata ko kuma ina sane na jawota" Mother ta jinjina kai alamar gamsuwa sannan ta ce "Amma me yasa ta suma?" "Ohh my god!" ya faɗa gami da dafe goshinsa, Mother ta lura tambayar ta-ta ce ba ta yi masa ba don haka ta ce " Please tell me my son" "It's not my fault, kawai zafin tsafin ne ya taɓa ta shine ta suma, na rasa gane me hakan yake nufi Uwa!" murmusawa ta yi kafin ta ce "Da sannu-sannu za ka gane, ka kula da kanka." Russlan da ke zaune ya zuba musu ido sai a lokacin ya ce "To wai ma Uwa! har akwai wanda ya isa? na yi mamaki da jin hakan gaskiya." Mother ta ce "Ba abin mamaki bane;, Risslan ka zo mu je ciki ka huta na san ka na buƙatar hakan." Bai ce komai ba ya miƙe ta na riƙe da hannunsa su ka wuce cikin tafkeken gidansu. Husnee Tinda ta koma gida ba wanda ta saurara ko da Mommy ta tambayeta abinda ya faru da ita sai ta ce ba komai don haka Mommyn ta zuba mata ido. Toilet ta wuce ta haɗa ruwan zafi me zafi sosai ta yi wanka sannan ta fito, doguwar riga mara nauyi ta saka kana ta koma kan gado ta duƙunƙune, jikinta ko ina ciwo yake amma da ta yi wankan ta ɗan ji sauƙi. Khausar ce ta shigo ta na cewa "Anti Husnee wai ba za ki ci abincin ba?" kamar za ta yi kuka ta ce "Ke dalla na ƙoshi" Khausar ta ce "Wallahi ba ki da lafiya, dole ma ki ga likita bari Daddy ya dawo." Husnee ba ta ce komai ba don maganar ma ba son yi take ba. Sai da aka yi kiran Sallar magrib sannan ta fito ta ɗaura alwala, Yaya Muneer ne ya dubeta a tsanake ya ce "Ya jikin naki?" da sauri ta ɗago ta na kallonsa a ranta ta na tunanin ''Wai ce musu aka yi ba ni da lafiya?" a zahiri kuwa cewa ta yi "Da sauƙi" Yaya Muneer ya ce "Ba ki da lafiyar amma ba za ki faɗa ba sabida Allura ko?" da sauri ta girgiza kai alamar a'a, kafin ya yi wata maganar tuni ta gudu ɗaki. Bayan an idar da sallar isha'i ta na zaune kusa da Mommy, duk sauran yayyenta dake Parlon su na hira da raha amma banda ita. ta yi nisa a duniyar tunani Ahmad ya yi sallama, ko zama bai yi ba ya ce "Ina Me hawaye ba kukan nan?, ya jikin?" ya yi maganar ya na dariya. Zumɓuro baki ta yi gami da cewa "Ni fa lafiyata ƙalau." Yaya Muneeb ya ce "A'a gaskiya dole akwai wani abin da ke damunki, ke da surutu kuma har a zauna hira ba ki ce komai ba?" Ahmad ya ce "Ku ƙyaleta ƴar zafi ce ta isheta, ai an gaya mini abinda ya sameta." Daddy ne ya dube shi a nutse ya ce "Zauna Ahmad" zaman ya yi a kan carpet ya na ƴar dariya ƙasa-ƙasa ya na kallota gami da yi mata gwalo, ita kuwa hankalinta duk ya tashi, fargabarta ɗaya a faɗi wani abinda zai sa su gane cewa ta gama yin zurfi a cikin shishshigewa Risslan. Daddy ya ce "Nutsu ka gaya mana abinda ya faru da ita, ba ma son shiririta." Ya ce "To Daddy, maganar gaskiya ko me ta ce ƙarya ta ke yi, daga saman makarantarsu ta faɗo, ba ma fa daga ƙafar bene ba daga can sama, in gaya muku gaskiya gwara ku kaita National Orthopaedic Hospital ta cancanci ganin likitan ƙashi." Ido warwaje Mommy da Khausar su ka furta "Daga sama???" Ahmad ya ce "Ƙwarai kuwa ga ta nan ku tambayeta." Mommy ce ta kama hannunta gami da cewa "Ke tashi in ganki, ai wallahi da gaskiyar Ahmad gaba da Orthopaedic ma sai a kaita." Husnee ta miƙe kamar za ta yi kuka ta na cewa "Ni fa ba na jin komai kawai ciwon jiki na ke ji kaɗan." Ba wanda ya tanka mata sai ma ido da suka zuba mata, Mommy ta ce "Taka in gani, jeki kusa da Ahmad ki dawo." ba dan ta so ba ta taka zuwa inda ya ke don dai kawai ta na son tabbatar musu ƙalau take. Ganin ta na tafiya sak! ba alamar ciwo ko buguwa ko ɗingishi ya sa Ahmad cewa "Kai anya kuwa Daddy yarinyar nan Aljanu ba su shafeta ba? ka ga ƴar da ta faɗo daga sama? tangaras abinta ko targaɗe babu? wallahi ni Aliyu cewa ya yi mini da ta faɗo ma suma ta yi sai daga baya ta farko amma kalleta don Allah." Daddy ya numfasa kafin ya ce "Kai fa Ahmad akwai ka akwai shiririta, wane irin Aljanu kuma ana zaune ƙalau?" Ya Muneeb ya ce "Abin dai da alamar tambaya akai, daga kan keke ma idan mutum ya faɗi jiki yake ji bare ta faɗo daga sama amma ta miƙe garau" Ya Muneer ya ce "To ai ma abin tambayar anan shine, asali me ya gusar mata da hankali har ta faɗo daga sama? ko tsokanar wata ki ka yi ta ɗebeki ta watso?" girgiza kai ta yi alamar a'a Mommy ta ce "Ni dai barkana, tinda ƙalau take ai ta kwana gidan sauƙi, mu ga hannunki" ta faɗa ta na miƙa mata nata hannun, ba musu ta miƙo duka hannayen nata, Mommy ta mammatsata ta ji dai ba ta yi ko gezau da sunan an taɓa mata inda ke mata ciwo ba, sakinta ta yi ta na cewa "Ikon Allah, Allah ya tsareki Husna" Khausar da ta saki baki ido da hanci ta na bibbinsu da kallo sai lokacin ta ce "Gaskiya ke ƴar baiwa ce Aunty dama ni ce" Ahmad ya ƙyalƙyale da dariya ya na cewa "To Bugun la'asar, ke daɗina da ke muguwar tafki ce, ta faɗo daga saman ki ce dama ke ce? to idan ke ɗin ce ki ka faɗo kuma ki kwararraɓe fa? ita ɗin ma ƙila Aljanu ne su ka shafeta." Zuwa yanzu surutan nasu sun fara ɓatawa Daddy rai, a tsawace ya ce "Kar na ƙara jin wani ya ce wai Aljanu gareta! ku ba ku san kiyayewar Allah ba? sau nawa ake yin haɗari har wasu su mutu amma a ciki sai ku ga wasu ma abin bai shafesu ba kamar ba sa ciki, amma don ta faɗo daga sama ba ta ji ciwo ba sai ku ce Aljanu ne? ba ku san cewa Allah na kare bayinsa ba? ya kuke abu kamar ba musulmi ba?" Ahmad ya ce "Ayi haƙuri Daddy mun dena." Husnee kuwa komawa ta yi ta zauna ba tare da ta ƙara bi takansu ba. Washegari ba wanda bai yi mamakin ganin Husnee ta dawo makaranta ba don a zatonsu ko za ta kuma zuwa sai bayan ta yi doguwar jinya, sai kuma su ka ganta katsam, su kansu malaman sun yi mamaki, su Yasayyadi Usman ɗaya bayan ɗaya sai tambayarta su ke yi abinda Akhiee ya yi mata, ita kuwa gaskiyarta take faɗa musu cewar ba ta san abinda ya faru ba dole su ka gaji su ka ƙyaleta. Yamma ce liƙis..... Tankar Yaƙi da Abokananta su na zaune a wani fili wanda suke kira Bakin Kwalta, anan su ka saba zaman shaye-shaye da hira. yau ma kamar kullum kowa na shan abin mayen da ya fi yi masa daɗi amma banda Tankar Yaƙi gabaki ɗaya ta kasa yin komai hankalinta ya tafi akan tunanin Risslan. Ɗan Kurada ne ya lallaɓo kusa da ita ya zauna, cikin murya me cike da maye ya ce "Meke faruwa ne Ta gidan Oga? waye ya taɓa mana ke mu taɓa shi?" kallonsa ta yi ta kawar da kai sannan ta ce "Tunanin wanda na ke so na ke yi, Wai Ɗan Kurada akwai wani abun kushewa a jikina??, shin me yasa Risslan ba ya sona? me yake so a wurin mace wanda Allah bai ba ni ba?" Ɗan Kurada ya wulƙita idanunsa da suke wani galmi-galmi kafin ya ce "Ba abinda ba ki da shi ta gidan Oga!!, amma fa ina ga zaren ne ba kalar yadin ba, kin san Oga na sonki fa amma ke kuma ki na son Abokin gabarsa, anya ki na ganin hakan zai yuwu?" shiru ta yi ta na ɗan nazari na ɗan lokaci sannan ta ce "Ɗan Karada!!! ni fa gaskiya zan iya rabuwa da Dodo akan Sahun Keke, kuma kai ma ka sani gabar da ke tsakaninsu ce ta sa na san shi ma har na ji na kamu da son shi, ko fa me za'ayi sai dai ayi amma ni ba zan bar abinda nake so ba, kuma wallahi indai ka ga bai aureni ba to ko shakka babu zai mutu ba aure don duk wadda ya so ko ta so shi sai na rabata da ranta." Ɗan Kurada ya yi dariya me isarsa sannan ya ce "Za ki aikata ta gidan Oga!! ni ina bayanki ki yi yadda ki ke so wallahi mun ɗaure miki abin." Murmusawa ta yi a ranta ta ma ƙissima abubuwa iri daban-daban. Jiki na ɗari-ɗari IP Khalil ya amsa kiran DCP Khashim Bello, don kuwa ya san kwanan zancen, shi kuwa abu ya fara fin ƙarfinsa, da kyar ya ce "Hello!" a ɗaya ɓangaren DCP ya ce "Na kasa samun kyakkyawan labari daga gareka, in ce dai ba ka manta ɓarnar da Muhammad Muhammad ya yi mana a kwanan nan ba, JD ya fusata iya matuƙa kuma ba abinda ba zai yi ba akan wannan dukiya ta shi da aka ƙona, bayan haka ma yanzu duk harkokinsa sun tsaya sabida takurawar wannan yaro, ya hana shi shigo da kaya ta kowace hanya sannan shi kuma ya na shigo da Wiwi ɗinsa ya na sayarwa, wai duk zaman me ka ke yi hakan ta ke faruwa?" miƙewa ya yi ya na takawa cikin sigar rarrashi ya ce "Ayi mini uzuri yallaɓai, ba dare ba rana idanuna na kansa kuma ina nan zan yi maganinsa don Allah a ƙara bawa JD haƙuri kwanan nan zan yi iya ƙoƙarina, zan kama shi a matsayinsa na Dilan Wiwi kuma dole doka za ta yi aiki akansa." "Hahahaha!" DCP ya yi dariya sannan ya ce "Wanda ba ya bin doka ai ba amfanin binsa a dokance, yanzu ba ta doka za mu bi shi ba, za mu yi masa zagon ƙasa ne ta yadda sai ya ji zaman duniya ma ya ishe shi, JD ya riga ya fusata kuma ya zuba kuɗi ayi masa aiki akansa, cikin kwanakin nan za mu ji kyakkyawan labari, kwantar da hankali Inspector Ibrahim Musa Rano, sai ka ji ni" daga haka ya katse kiran, murmushin farin ciki ne ya buwaya a fuskar IP Khalil ba ƙaramin daɗin albishir ɗin ya ji ba, ko ba komai shi yanzu zai samu kyakkyawan bacci shi kuwa Risslan lokacin nasa baccin ya ƙare. Tin ranar da su ka faɗo daga sama Akhiee bai ƙara ziyarta makaranta ba har sai da ya yi kwana tara. Husnee kullum zuba ido ta ke yi ko za ta ganshi sai dai har rana ta fito ta koma ga ubangijinta ko me kama da shi ba ta gani, gashi idan ta tambayi Zara sai ta ce itama ta daɗe ba ta sanya shi a idanunta ba. duk ta shiga damuwa har wani ɗan zazzaɓi take yi, ta yi wata ƴar rama ta yi wuƙi-wuƙi da ita. Yau ta sa a ranta indai bai zo ba ita ma ta dena zuwa makarantar sai bayan wani lokaci. haka nan take zaune cikin aji sukuti, karatun ma ba wani yi take ba, sai da aka fita sallah ta ɗan ji dama-dama, tare da Asiya su ka fito daga aji ta na riƙe da hannunta sabida ɗan jiri-jiri da yake ɗibarta sakamakon yawan tunanin da take yi, kamar ance kalli sama ta ɗaga kai ta na kallon inda ta saba ganinsa ai kuwa ta yi tozali dashi, ya na sanye cikin manyan kaya shadda ruwan toka me haske da hular Zanna bukar haɗaɗɗiya me ratsin ruwan toka, kam ta riƙe Asiya yayin da idanunta ke kan Akhiee mamakin yadda ya yi mugun kyau a cikin irin shigar ya kamata ga tambaya da take yiwa kanta "wai dama ya na sa manyan kaya irin wannan?" Asiya ce ta ankara da hankalinta ba a jikinta yake ba dalilin magana da take ta yi mata amma ta ji shiru, ɗaga kai ta yi ta kalli inda ta ga ta na kallo itama idanunta su ka yi alaragab da Akhiee nan take zuciyarta ta bada wani ɗurum!!!!!!!, cikin dubara ta zame jikinta ta ture Husnee wadda har lokacin kanta a sama yake, ba ta ce mata ƙala ba ta zame ta yi nata wuri. kamar wadda aka saukarwa ayar zuwa inda yake ba tare da ta sani ba ma ta fara tafiya ta na yi ta na kallonsa kamar ance in ta ɗauke ido zai ɓace. Sai da ta dangana da shi sannan ta dakata ta na ƙara ware masa idanunta da su ka yi zuru-zuru ko kwalli babu. Ya na ankare da zuwanta amma ko kallonta bai yi ba. Cikin sassanyar murya me kama da shagwaɓa ta ce "Akhiee! me yasa ba ka zuwa makatanta, hankalina ya tashi da rashin ganinka gashi ban san halin da kake ciki ba, don Allah ka dena ƙauracewa ganina, idanuna da zuciyata ba sa gajiyawa da kai, don Allah Akhiee ka dinga zuwa makaranta kullum" White Diamond Watch dake hannunsa ya kalla kafin ya yi magana cikin muryar da ba hayaniya ba tashin hankali "Asma'u! Please it's time for prayer, i'm going to the masque" "Please Akhiee Listen to me!" ta ƙarasa maganar gami da fashewa da kuka........... SHARE FISABILILLAH Na Kuɗi ne.... Nomarl Grp 300 Posting ba kullum ba. VIP 500 Posting Kullum. domin ƙarin bayani 👉🏽09079885632 AN FARA PAYMENT *©️INDO* [8/17, 1:12 PM] INDO: *🪻SAHUN KEKE🪻* Ep 12 ©️ Ayeesha Abdulkareem INDO *M.W.A🦅* "Ƴan Daba ne su ka sassari Akhiee jini sai Zuba yake a jikinsa amma ya ƙi yarda a kai shi Asibiti, shine duk su ka taru akansa, har babban yayanmu ma ya zo amma ya ƙi Amincewa kuma wallahi ya na shan wahala sosai jininsa zai iya ƙarewa" Ta ƙarasa maganar gami da fashewa da kuka mai taɓa zuciyar duk wani me imani. Husnee ta na jin haka ba ta bi ta kan Zara ba ta falla da gudu ta yo waje. Turmutsawa ta yi tsakankanin mutanen da su ka yi masa da'ira wanda yawancinsu yayyensa. Ya na tsaye ya jingina da bango sai ƙasa-ƙasa yake da idanunsa da su ka ƙara wani irin haske ƙwayar idon ta ƙara rikiɗa ta yi baƙi siɗik, fuskarsa ma kanta ta yi jawur sabida tsabar zafin rai da kuma azabar da yake ji a jikinsa, ganin yadda jini ya jiƙa shaddar jikinsa me ruwan toka ta koma ja ya sa Husnee fashewa da kukan da sai da ta sa shi ɗagowa ya zuba mata ido, ba ma shi kaɗai ba duk mutanen wurin idanu su ka zuba mata cike da mamakin tsaurin ido irin nata, ba su gama firgita ba sai da su ka ji Tassss!!!!! ƙarar marin da ta sheƙa masa ya karaɗe kunnuwansu, cikin shashshekar kuka ta ce "Akhiee me yasa ba ka san ciwon kanka bane!!!? don me ba za ka je asibiti ba ka na fama da wannan rauni a jikinka?" Cikin muryar da ke fita ƙyar ya ce "Asma'u! ki ƙyale ni ko mutuwa na yi ba su da asara tinda ba ƙaunata su ke yi ba." cikin tsananin ɓacin rai ta daki ƙirjinsa cikin tsawa tace "Ƙarya ka ke yi Akhiee!!! wanda ba ya ƙaunarka ba zai so lafiyarka ba!!, yanzu duk wannan tashin hankalin da su ka shiga ka na nufin ba ƙauna bace?? wallahi tallahi indai ba ka je ba nima sai na ji wa kaina, idan ka mutu kai ka tafi kenan mu za ka bari da tunaninka!!!!" ta ƙarasa maganar gami da fashewa da wani sabon azababben kukan, "Asma'u ba zan iya ba ki ƙyale..."

Chapter 6 of 19