za mu yi kar a kama mu."
Ya na faɗen haka ɗayan ya kafta masa sara a kafaɗa, ɗayan ya ce "Alhaji Habibu me kwalli ne ya aiko mu, kar ka mutu ba ka san laifinka ba." bai iya cewa komai ba sai ma durƙushewa da ya yi a gabansu hannunsa dafe da inda su ka sare shi.
Cikin sauri su ka hau kansa da sare-sare da soke soke su na gamawa su ka fice don kar a kama su.
Gaba
daidai lokacin da aka tashi Sallar La'asar Akhiee ya shigo makaranta, sanye yake cikin ƙananun kaya riga da wando farare tarr! har ɗaukar ido su ke yi, ya kifa hula P-cap itama fara takalminsa ma fari tass.
a harabar makarantar ɗalibai su na ta hudimomin gabansu masu yin alwala na yi masu surutu na yi, duk wanda ya ankara da shi sai ya yi gefe ya bashi hanya don kuwa hanya ma ba wanda ya ke ƙaunar haɗawa da shi.
Sama ya hau inda ya saba tsayawa ya coge ya na kallon mutanen da ke sabgoginsu ɗaya bayan ɗaya.
Zahra ce ta yafito Husnee ta na murmushi ta ce "Kin damu da son ganin Akhiee ta kin ganshi ya dawo."
Kamar anyi mata albishir da kujerar hajji haka ta washe baki ta na cewa "Da gaske??"
Zahra ta ce "Da gaske mana duba sama ki gani."
Husnee ta sa hankicif ta danne idonta ɗaya da ke zubar hawaye sannan ta ƙyallara ɗayan ai kuwa ta na ganinsa kafin Zahra ta yi magana ta bar gurin ta nufi sama da gudu.
Zahrah ta zazzaro ido ta saki baki ta na kallon Husnee wadda tuni har ta fara hawa steps, rausayar da kai ta yi ta ce "Allah i tsare ki to."
Daga haka ta ci gaba da alwalarta.
Husnee na haki sabida gudun da ta yi ta isa wajen Akhiee cike da farin cikin ganinsa ta ce "Ya akai ka zo makaranta? ƴan-sandan sun sake ka?"
Kallonta ya yi ya kauda kai a ransa ya na ƙissima irin buyawar yarinyar gabaki ɗaya nema take ta sanya masa damuwa.
Jin bai ce komai ba ya sa ta matsa kusa da shi ta na cewa "Wai ciwon da aka ji maka ɗazu har ya warke??"
"Ikon Allah, ita kuma wannan kowa ya na guduna sai ƙara cuso kanta take ko ina ruwanta da ciwona??" aransa yake wannan surutun a zahiri kuwa bai ko motsa ba bare ta san ma ya ji ta.
Kasancewar Husnee akwai rawar kai ba ta damu da shirunsa ba ta ci gaba da zubo masa surutu, ba ta yi shiru ba sai da ta ji idonta ɗayan ya harbu kamar yadda ta ji ɗayan ya yi da safe nan take duka biyun su ka fara shararar da hawaye, idanun nata ta zuba masa zuciyarta na tsalle, tunanin kalaman Zahra ta fara yi nan take ta fara yarda don kuwa abin akwai ban mamaki ba gaira ba sabar idanu su kama zubar ruwa.
Ba ta ƙara cewa uffan ba ta ja dogayen ƙafafunta ta koma ƙasa jiki a sanyaye.
Zahra ce ta kalleta cikin tausayawa ta ce "Ba ki ji ba, ba ki gani ba za ki sa ayi miki abinda za ki bar iyayenki da jinya, kinga dai yanzu ɗaya idon ya kamu sai ki kula don nan gaba za ki iya rasa su"
Goge hawayen ta yi sannan ta ce "Ai yanzu na fara yarda don wallahi ni ban taɓa yin irin wannan ciwon ba; wai Zara shi ɗin kurma ne?"
Zara ta murmusa sannan ta ce "Ko ɗaya, ya na jinki kuma ya na magana idan kin ji bai yi ba to niyya ce bai yi ba."
Husnee ta ce "Anya kuwa? duk abinda na ce ai ya kamata ya ce wani abu ko ba yawa" Zara ta yi murmushi me sauti gami da rausayar da kai ta ce "Husnee kenan! ki na da rashin yarda sosai, amma yanayi zai nuna wataran za ki ga ya yi magana." Husnee ba ta ce komai ba ta zumɓuri baki don gani take ko me Zara ta faɗa akansa kawai don ba sa ƙaunarsa ne.
Bayan an idar da sallah aka koma karatu, kowa na ƙoƙarin yi amma Husnee ta kasa aikinta ɗaya goge ƙwallarta da ke zuba wata kan wata.
01:00AM
duk wannan daren IP Khalil ya kasa rintsawa sai bincike-bincike da nazarce-nazarce yake yi.
Wayarsa ce ta fara tsuwwa ya janyota tare da duba screen ɗin DCP shine sunan da ke yawo akai, da sauri ya ɗaga gami da karawa a kunnensa, DCP Khashim Bello ya ce "IP Ka na saurarena?" da sauri IP Khalil ya ce "Ina saurare"
"Na ji abinda ya faru tsakaninka da Sarƙa to ba na so hakan ya dameka, amma ina me gargaɗinka akan iya takunka idan ka bari Wancan CP ɗin ya ganeka shi kenan mun kaɗe, ka samu ka kawo ƙarshen duk tsagerancinsa kafin ya fi haka, zan turo maka kuɗi ka duba sannan kuma na yo aike ka kula min da komai.
"Yes sir!!" daga haka DCP ya katse wayar.
Zazzafar ajiyar Zuciya Inspector Khalil ya sauke sannan ya miƙe ya nufi makwancinsa.
Yau da yake Litinin ce
Husnee Ba ta zo Islamiyya da safe ba sai yamma, tin da ta zo take sa ran ganin Akhiee har ta fitar da rai gashi Zara ta ce mata bai zo da safe ba, haka kawai duk hankalinta ya tashi sai ta ke ganin kamar wani abin ne ya faru da shi, sai dai abinda ba ta sani ba sai ya bushi iska ya ke zuwa makarantar.
Haka aka tashi ta koma gida ba tare da ta sanya shi a idanunta ba.
Ta na zaune a Parlor ita da Mommy da Khausar su na kallo Yayanta Ahmad ya shigo, bayan ya zauna ya ce "Wai ke me hawaye ba kuka ba za ki haƙura da kallon ba sai idon ya ƙarasa mutuwa?"
Goge hawayen ta yi ta na murguɗa baki sannan ta ce "Kar ka takura min ai dai idon nawa ba ciwo yake ba." da ɗan mamaki Ahmad ya ce "Ba ciwo yake ba to uban me ya sa shi hawaye?" "Akh....." saurin rufe bakin ta yi ta na zazzare ido, jin irin katoɓarar da take shirin yi, Mommy da Ahmad su ka zuba mata ido cike da son jin abinda za ta ce "Gyara zama ta yi sannan ta ce "Ƙila tsakuwa ce ta faɗa."
"Wato ƙila tsakuwa ko? ki faɗa mana gaskiya idan ma tsokana ki ka yi aka rushe miki shi." Mommy ta faɗa ta na tsareta da ido, cikin sauri ta ce "Wallahi ban tsokani kowa ba Mommy, kawai dai ikon Allah ne " Ahmad ya ce "Ba ta da gaskiya fa, amma ki ƙyaleta idan ta ga uwar bari da tsefaffen gashi ai za ta faɗa."
Turo baki ta yi ba tare da ta mayar masa da martani ba, aranta kuwa cewa ta yi "Ba zan faɗa muku ba ku hana ni zuwa makaranta"
ya na tsaye hannunsa ɗaya riƙe da ƙugunsa ɗayan kuma wiwi ce bango yake kalla ya na nazari ya na yi yana zuƙa.
Ɗan Bakwai ne ya shigo tare da sallama daga ɗan nesa da shi ya tsaya ya rissina ya ce "Ubana Ubansu! Wata gyatima ce ta zo nemanka munyi munyi ta faɗi abinda ke tafe da ita ta ƙi wai sai ta ganka."
Hannu ya ɗaga ya yi masa alamar ta shigo, da sauri Ɗan Bakwai ya juya ba daɗewa su ka dawo tare da wata dattijuwar mata, rissinawa ta yi gami da cewa "Ina kwana!" shiru bai ce komai ba jin haka ya sa ta kalli Ɗan Bakwai kamar za ta yi kuka ta ce "Ka roƙa min alfarma ya saurare ni don Allah."
Ɗan Bakwai ya ce "Ai ya ji ki, ki je maganarki kai tsaye."
Gefen hijab ɗinta ta sa ta goge gumin da ya tsatstsafo a fuskarta sannan tace.....
*©️INDO*
[8/12, 4:56 PM] INDO: https://chat.whatsapp.com/FuB2OR4qBx189IdAM0hXbG
*🪻SAHUN KEKE🪻*
Ep 6
©️
Ayeesha Abdulkareem INDO
*Mikiya Writer's Association🦅*
"Sunana Karimatu sana'ata sayarda Abinci, tafiyayya na yo domin na haɗu da kai, ɗana ne bai fi shekaru 17 ba amma sai na ajiye kuɗi ya zo ya ɗauke ya je su sayi kayan maye shi da oganninsa manya da su amma ba su bashi ko sisi ba sai na sha wahala na nema ya zo ya sace ya kai musu, ya ƙi zuwa Boko ya ƙi Islamiyya aikinsa kenan yawo cikin ƴan shaye-shaye, shi ne sai ka ganshi da sigari ya na sha ba aikin fari ba na baƙi sai wannan, na yi faɗa na yi duka na yi nasiha amma duk ya ƙi ji, shine na samu labarinka, Ɗannan na yarda da kai ɗari bisa ɗari shi yasa na kawo maka shi ko da zai yi iskancin ma idan ya na ƙarƙashin kulawarka zan fi samun kwanciyar hankali."
sai a lokacin ya juyo ya ɗan kalleta cike da kulawa ya ce "Gobe ki zo min da shi."
murmushi ta yi sabida jin daɗin samun karɓuwa da ta yi, cikin sauri ta ce "Ai ba zai zo ba gardama gareshi."
Maida kallonsa ya yi kan Ɗan Bakwai gami da cewa "A haɗata da Zabira ita za ta iya zuwa da shi."
Ɗan Bakwai ya ce "An gama Uban gayya"
Godiya sosai matar ta yiwa Risslan har ta fice duk da bai ce komai ba ita kuwa ba ta fasa ba.
gaba
Misalin ƙarfe 10:37Pm
Garin Kwanar Ɗan Gora babban Titin shigowa KANO..
Ba wani dare ne ya yi ba amma da yake lokacin damuna ne tuni sahun bil'adam ya ɗauke sai ƙarar iska da ke kaɗawa ba ji ba gani, jefi-jefi motoci sukan wuce su ɗin ma in wata ta wuce wata takan jima ba ta zo ba.
Dirowa ya yi daga kan Dokinsa ya fara haske-haske da dalleliyar Fitilarsa ya na ƙarewa yanayin wurin kallo, ya ɗan ɗauki lokaci ya na haske-haske sannan ya kashe fitilar, dubensa ya kai ga Dokinsa gami da ɗan shafa shi, cikin daddaɗar muryarsa ya ce "Prince! calm down, ba daɗewa za mu yi ba yanzu zan gama mu koma."
Prince dai da yake baya magana bai ce komai ba sai sunkuyar da kai da ya yi.
Daidai lokacin wata ƙaramar mota ƙirar Taxi ta shararo da mugun gudu kamar wadda jiya ta wuce take shirin kamo gobe.
Dalleliyar fitilarsa ya kunna ya haska motar sannan ya kashe ya nufi kan titin, a tsakiya ya coge gami da riƙe ƙugunsa.
a cikin motar kuwa Direban ne ya kalli na kusa da shi gami da cewa "Ka na ganin abinda nake gani kuwa?" ɗan zaman banza ya ce "Menene?" "Ba ka ga wata fitila da aka hasko mu ba? kuma ka ga mutum fa a tsakiyar titi duk irin wannan gudun da nake yi ko ɗar bai yi ba."
Mutum ɗaya da ke a gidan baya ne ya ce "Kuma ba dai ace ƴan fashi ba, in su ne ma da sauki Oga zai iya da su."
"Kutumar Uba Sahun Keke ne!!!!!" Direban ya faɗa cikin firgici da razani, wani mugun burki ya ja wanda ya yi daidai da harbe tayar motar da Akhiee ya yi, tayar ta bada dammm!!!! ta tarwatse, motar ta yi dara ta yi tsalle ta hantsila sau biyu kana ta tsaya wuri ɗaya ta na juyawa samanta ya koma ƙasa.
cikin ƙasaitaccen takunsa ya gangara gefen titin inda motar ta ke, leƙawa ya yi ta glass ya cewa direban "Ba ni wayarka"
Direba da ke numfashi da kyar da kyar ya zaro wayar a aljihunsa na gaba, fizgeta Akhiee ya yi kana ya yi baya-baya ya saita wurin man motar da bindigarsa, bai damu da kuka da magiyar da Mutanen ciki ke yi ba ya bata ɗasss, nan take ta kama da wuta ba ƙaƙƙautawa.
ƴan danne-danne ya yi a wayar ba ɓata lokaci ya cire key ɗinta tamkar ta shi, kira ya tura gami da kara wayar a kunne, bugu biyu aka ɗauka, JD cikin farin ciki ya ce "Direba Dangin kura, ina fatan kun isa, na kasa rintsawa har sai na ji kyakkyawan Albishir."
"Ba kyakkyawan Albishir a wannan karon sai dai a tarawa gaba, na kamaka kuma na mamayeka!!!" Akhiee ya yi maganar cike da zarra.
Zumbur JD ya miƙe daga kan luntsumemiyar kujerarsa ta alfarma, a take guguwar tashin hankali da firgici ta tashi a cikin cikinsa, ido a burbuɗe ya ce "Sahun Keke!!! What do you mean!!???"
"Ohh! Nothing, i mean, your car had an accident, ka ga yanzu saura kai kenan.
Safa da marwa JD ya fara yi a tamfatsetsen falon nasa, ya kai tsayin minti ɗaya bai iya cewa komai ba sannan ya ce "Wallahi! Tallahi! ni ne maganin iskancinka, ni za ka yiwa wannan yankan ƙaunar? ka jira abinda zai biyo baya, billahillazi sai na jefaka a bala'in da za ka gwammace ba ka zo duniya ba."
"Ina jira idan har kai hafaffen cikin tsohuwarka ne kar ka barni na ƙara kwanan duniya, ina jiran duk abinda za ka yi.
daga haka ya katse wayar gami da jefata kan motar da take ci da wuta, juyawa ya yi ya haye kan dokinsa su ka ɗau hanya.
Kwantsam!!! JD ya maka wayarsa da ƙasa ya na huci, yatsansa manuniya yasa ya na nuna ƙirjinsa gami da cewa "Ni??? ni za ka yiwa haka? wallahi ko me ka ke taƙama da shi sai na azabtar da rayuwarka."
Dukan dafkeken kansa da ke juyawa ya fara yi hannu bibbiyu kamar sabon mahaukaci, sai da ya gaji da zagaye sannan ya jaɓe kan kujera gami da dafe kai ya fashe da wani azababben kuka wanda shi kansa ma bai san dalilin yinsa ba.
washegari
Fitowarsa daga ɗakin baccinsa kenan ya tarar da matan gidansu a tsakar gida sun kafa dandalin hirarsa kowacce ta na tofa albarkacin bakinta, bai kula su ba ya wuce hanyar fita, da gudu Zara ta ƙarasa inda yake ta na cewa "Akhiee Abhi na kiranka."
Bai yi magana ba ya juyo zuwa cikin gidan, ɗakinsa ya koma ya canja kaya ya sanya jallabiya da hula sannan ya nufi turakar mahaifin nasu.
Hamza na zaune kusa da Abhi ya na bashi labari Akhiee ya yi sallama, tsohon dake zaune kan kujerarsa ta marasa lafiya ya amsa fuskarsa ɗauke da yalwataccen murmushi, ƙarasawa ya yi ya durƙusa a gabansa gami da cewa "Good Morning Daddy!" Abhi ya amsa da cewa "Morning Dattijo! ka manta da ni ne kwana biyu? dama abinda ya sa na kiraka na ji a gidan ba zancen da ake yi sai naka, ba kwanciyar hankali a ƴan kwanakin nan naji sai cari su ke yi ba matan ba mazan, me ka yi ne Dattijo??"
Da sauri ya ɗago kai ya na kallon Mahaifin nasa cike da rashin sanin abin faɗa.
Murmushin gefen baki Hamza ya yi a ransa ya ce "Ai yau taka ta ƙare faɗen gaskiya ya zama dole."
kamar yadda Risslan ya ce a zo masa da yaron da ke yiwa ummansa sata hakan ce ta faru, tare su ka shigo da Zabira da Ɗan Bakwai da Salansa sai kuma Mama Karimatu mahaifiyar yaron sai yaron da ke ta famar rarraba idanu kamar an ɗaure zakara ana shirin yankawa.
Akhiee na zaune kan benci ya na aikin shan wiwi su ka shigo da sallama, duk su ka ja su ka tsaya su na jiran cewarsa.
Miyagun idanunsa ya zubawa yaron har na ɗan lokaci kafin ya ce "Mama faɗa masa laifinsa." da sauri ta ce "To" sannan ta ƙara maimaita abinda ta faɗa jiya.
Cike da tsageranci yaron ya ce "Ni ba na ɗaukar mata kuɗi, ai idan na yi musu aike ne su ke bani."
Mama Karimatu ta ce "Wallahi ƙarya yake Muhammad ba sile ɗayan da suke ba shi sai dai shi ya kwashi nawa ya kai musu."
A fusace yaron ya ce "Ni fa gaskiya ba na sata ni ba ɓarawo bane, akan me za ki ce ina ɗaukar miki kuɗi bayan ban ma san inda ki ke ajiyewa ba?"
Mama Karimatu ta riƙe haɓa ta na mamakin irin tsaurin ido na ɗan nata.
Cikin takunsa irin na toron giwa ya ƙaraso gabansa ya na binsa da wani irin kallo me sanya nutsuwa ko ba'a so, "Ya sunanka?" "Rabi'u" ya faɗa a ƙagauce, jinjina kai ya yi sannan ya ce "Me yasa mahaifiyarka ta na faɗe ka na faɗe? ka na nufin ƙaryata take maka??"
ƙara haurowa ya yi kamar zai doki Akhiee ya na cewa "Ni ban ce ƙarya take ba, amma ni ban taɓa ɗaukar mata kuɗi ba!!!!"
Akhiee ya kalli Mama Karima gami da cewa "Mama janye ɗanki don in na saka masa hannu za ki iya rasa shi."
Da sauri ta riƙo hannunsa ta na cewa "Matso nan" fizgewa ya yi ya ce "Ni rabu da ni."
Za ta yi magana Akhiee ya ce "Ƙyale shi" matsawa ta yi gefe ta zubawa sarautar Allah ido, Akhiee ya dube shi a tsanake ya ce "Yanayin tsaurin idonka ya burgeni, a kayan caji da me kake amfani??"
Ƙasa ya yi da ido ya ce "Sigari kawai nake sha"
miƙa masa Tabar hannunsa ya yi gami da cewa "Na san kana so, to gwada mana!" karɓa ya yi ba tare da ya ji ko ɗarr ba shi a dole ɗan zafin kai.
Ja ɗaya ya yi mata ya wurgar da sauran gami da dafe ƙirjinsa da hannu ɗaya ɗayan kuma ya dafe kai ya na wani azababben tari, nan take idanunsa su ka canja launi su ka ƙara yin ja sosai su ka firfito sabi da azaba.
tari yake ba ƙaƙƙautawa ƙafafunsa ma sun gaza ɗaukarsa har sai da ya durƙushe a ƙasa, Ummansa ce ta matso kusa da shi cikin tausayawa ta na yi masa sannu sai dai ba halin amsawa.
Salansa ya ce "Da ka ce kai shege ne, ai a zafin kan ma aji aji ne dan ubanka."
Akhiee ne ya durƙusa a gabansa cikin nutsuwa ya ce "Za ka ƙara ne??" da sauri ya girgiza kai alamar aa, Akhiee ya dubi Salansa gami da cewa "Ku haɗa shi da Laita."
ya na faɗen haka Salansa ya kama shi ya fice da shi daga gurin.
Ummansa ta raka su da ido har su ka fice.
"Ki na ba shi kuɗin makaranta?" girgiza kai ta yi alamar a'a ya ce "To ki dinga ba shi amma ba da yawa ba, rashin sakarwa yaro hannu yakansa shi fara ɗauke-ɗauke amma idan abin ya yi yawa ya na kawo lalacewa, In sha Allah zai shiryu, zan sa shi a Islamiyya nan da kwana biyu ko uku."
Mama Karima ta goge ƙwalla ka na ta ce "To Allah i sa, na gode sosai."
Kai kawai ya gyaɗa mata alamar ya amsa.
Kwance yake kan makeken Gado wanda zai iya kai girman wani ɗakin, gadon ya sha shimfiɗa da tafkeken bargo wanda ake kira duniyar kuliya, ko ina na gadon ado ne ya yi kyau gwanin sha'awa.
Baccinsa yake cikin kwanciyar hankali ba tare da wata damuwa ba.
Wani samɓalelen Maciji golden collor ya salallaɓo ya hau kan gadon, can tsakiya inda Akhiee yake ya nufa sai da ya hau kansa ya zagaya kana ya sauka gefe ya tsaya ya nannaɗe gami da ɗago kansa sama.
Sanyin Macijin da ya ji ne ya sa shi buɗe idanunsa cikin nutsuwa ya zubawa Macijin su kafin ya lumshe ido, a hankali ya ce "My Mother!!!"
SHARE FISABILILLAH
Na kuɗi ne....
09079885632
*©️INDO*
[8/12, 4:56 PM] INDO: *🪻SAHUN KEKE🪻*
Ep 7
©️
Ayeesha Abdulkareem INDO
*M.W.A🦅*
a hankali Macijin ya fara sauya kamanninsa daga maciji zuwa mutum.
Dattijuwar mace ce fara sol kyakkyawa, fuskarta ɗauke da murmushi ta ke kallonsa cike da kulawa, ɗan shafa kansa ta yi gami da gyaɗa masa kai alamar ta na sane ta tashe shi.
"What Happened my Mother?" ya faɗa yana zuba mata rikitattun idanunsa, cikin nutsuwa ta buɗe kyakkyawan bakinta ta magantu cikin zazzaƙar muryarta me cike da kamala da dattako, "It's time for prayer!"
Da sauri ya tashi zaune yana lumshe idanu, cikin sassanyar muryarsa ya ce "Okay Mommah!"
dafa hannunsa ta yi cikin nutsuwa ta ce "Ya na da kyau ka je makaranta yau"
"For what?"
"Calm down, akwai me jiranka ne idan ka je za ka san dalilin.
Gyaɗa kai ya yi sannan ya yunƙura ya miƙe ya nufi toilet wanda aka gina shi da zallar farin dutse, kuma aka yi masa ado da tsirrai da fulawoyi masu furrai kala-kala gwanin sha'awa.
Sai da ya watsa ruwa sannan ya ɗaura Alwala, ya na fitowa ya shirya cikin riga da wando na saƙi farare tass, a samansu ya ɗora doguwar Alkyabba me kyawun ado, itama fara ce an yi mata ado da launin baƙi da ja, ya yi kyau matuƙar kyau wanda zaman misaltashi ma aiki ne.
bayan ya idar da Sallah ya yi addu'a ya miƙe cikin taku irin na wahainiya ya fito daga makeken ɗakin, a bakin ƙofa ya tsaya ya na rarraba ido.
Gine-gine ne na dutse wanda aka yi ɗakuna da kuma madafa sai banɗakuna, ko ina a ƙawace yake da koren ganye fululu da fulawoyi masu furanni ja yalo pink milk da dai sauransu, idan ka kai dubenka nesa kuwa tsaunuka ne manya da ƙananu da ƙoramu masu gudana da ruwa fari ƙar me kyawun kalla, daddaɗan sanyi ne ke tashi ta ko'ina gami da ƙamshin furanni da tsirrai, abin ba a magana.
cikin cool voice nashi ya ce "Mother!" bata kusa amma ta ji kiran da ya yi mata kuma ta amsa, ba ɓata lokaci ta iso gabansa fuskarta ɗauke da yalwataccen murmushi "Amma za ka ci abinci kafin ka tafi.
Girgiza kai yayi alamar aa.
Ba ta yi masa musu ba don kuwa ta san ba zai cin ba, bai kuma cewa kanzil ba ya fara taka korayen tsirrai da ke shimfiɗe a ƙasa tamkar carpet, da ido ta bi shi har ya ɓacewa ganinta sannan ta ci gaba da aiyukanta.
Ana tsaka da karatu ya shigo ajin, cikin yanayinsa na jin kai ya isa gaban Sheikh Auwal ya durƙusa ya gaishe shi kamar yadda kowane ɗalibi ke yi wa malaman makarantar.
Sheikh Auwal ya zuba masa idanu shi kansa ya na yi masa bala'in kyau a irin shigar nan kamar mutumin kirki, sai dai kashh! albasa ba ta yo halin ruwa ba, Ya kasa amsa gaisuwar ya tafi tunani, ganin haka ya sa Risslaan miƙewa zai nemi gurin zama, "Dakata Akhiee! zauna" Sheikh Auwal ya faɗa cikin sauri.
da yake yau ba ƴan gardamar akansa zaman ya yi dafa'an murar kwaɗi ya na sauraren ƙalu-balen da Sheikh Auwal ya zo da shi don a cewarsa ba sa faɗen Alkairi kuma ba sa neman mutum sai ya yi laifi.
Sai da ya ɗan yi gyaran murya sannan ya ce "Me yasa kwana biyu kenan yau ba ka zo makaranta ba??"
"Ba na cikin yanayin zuwan ne" ya bashi amsa kai tsaye ba tare da shakka ba.
Sheikh Auwal ya jinjina kai sannan ya ce "Akhiee Don Allah ka zamo mutumin kirki ka watsar da harkar banzar nan, ba a son raina komai yake faruwa ba, ka duba ka ga tinda Allah ya sa ka zo duniya mahaifinmu ya ɗauki so da ƙauna ya ɗora maka, kuma har yake kiranka Malam, ya na da burin ka zamo malami babban mutum tamkar shi, dalilin da yasa ya raɗa maka sunansa kenan, sai gashi
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 3 Chapter of 19