sume ta wani irin ɗashe ta ƙara haske kamar ba jini a jikinta, da sauri ya sanya hannunsa cikin tafin hannunta ya damƙe jikinsa na wata irin tsuma sabida tsananin ɓacin rai.
"Me ka yi mata??" muryar Yasayyadi Jameel ce ta dawo da shi cikin makarantar saɓanin da da duk hankalinsa ya yi nisa, sai a lokacin ya lura da mutane sun yi da'ira akansu kowa ya zubawa sarautar Allah ido.
a fusace Yasayyadi Usman ya ƙaraso wajen ya riƙo ɗayan hannun Akhiee ya finciko shi, ba tare da nazari ba ya afka masa wani lafiyayyen mari, "Uban me ka yi mata?? ba tambayarka ake yi ba?? me yasa ba ka jin magana kai?"
ɗago hannu ya yi zai ƙara tsinka masa wani marin Akhiee ya fizge hannunsa ya doki ƙirjin Yasayyadi Usman da ƙarfi sai da ya yi taga-taga zai faɗi su Yasayyadi Jameel su ka daddafe shi.
Idanunsa da suka canja kamanni ya zubawa sauran ɗalibai ƴan kallo kafin ya ce "Kowa ya ɓace daga nan ko na illata masa rayuwa wallahi; kai kuma kar ka ƙara gigin marina in ba haka ba zan tarwatsa maka farin cikinka, idan ta tashi sai ku tambayeta idan akwai tsiyar da na yi mata."
Ya na gama faɗen haka ya koma inda Husnee ke kwance ba alamun numfashi a tare da ita.
Ƴan makaranta kuwa tuni sun fice da gudun ceton rai, sai ɗaiɗai da ba su ƙarasa fita ba. rungumarta ya yi a ƙirjinsa ya nufi cikin ajinsu ba tare da ya bi takan kowa ba, ajiyeta kawai ya yi ya fito ya sa kai ko kallon su Sheikh Auwal bai yi ba ya fice daga makarantar, tafiyar kawai yake yi amma bai san inda ma zai dosa ba don kuwa ransa ya gama kaiwa ƙololuwar ɓaci, bai san inda zai nufa ya ji daɗi ba.
Su dai sun tsaya curko-curko kamar dangin Kaji an rasa me yin ko ƙwaƙƙwarar magana.
"Za ka ci Ayaba?" ta faɗa gami da miƙa masa ragowar wadda take ci. girgiza kai ya yi alamar a'a, ta ci gaba da cin kayarta hankali kwance, jin bai ce ƙala ba ya sa ta cewa "Akhiee! yau ba za ka yi mini magana ba ne? ni fa so nake in ga dariyarka, kullum sai dai ka dinga haɗe rai kamar hadarin gabas"
Kyawawan idanunsa ya zuba mata cikin lallami ya ce "Ni fa ki ƙyale a yadda nake don ni ba na dariya." da sauri ta ce "To sabida me?" shiru ya yi kamar ba zai bata amsa ba sai kuma ya ce "Ta na karya min tambaya ne" "Iyye?!!" ta faɗa gami da sakin baki, "Ni fa ba na gane wannan yaren naka, ka faɗa min da hausa" ''Ai ba za ki gane ba sai dai ki wahalar da ni." turo baki ta yi cike da shagwaɓa ta ce "Don Allah ka yi dariya ko da sau ɗaya ne na san za ka yi kyau" banza ya yi mata kamar ba da shi take ba, jifansa ta yi da ɓawon ayabar da ta cinye gami da cewa "Sai ka riƙe abarka ba a so ma, kuma na yi fushi ba zan ƙara kula ka ba" daga haka ta juya fayau-fayau da nufin barin gurin cak!!!!!! ta tsaya sabida muryarsa da ta karaɗe kunnuwanta.
sun daɗe a tsaitsaye jiki duk a sanyaye kafin Yasayyadi Jameel ya ce "Mu dai mu na ganin takanmu a rayuwa, wannan yaro ko annoba?"
a sirrince Sheikh Auwal ya goge zazzafar ƙwallar da ta fara gangarowa daga cikin idanunsa, cikin dakiya da mazantaka ya ce "Kar ku damu in Allah ya yarda ba abinda zai faru, ku ci gaba da Addu'a watarana sai labari."
Yasayyadi Usman dafe da ƙirjinsa da yake jin kamar maɗaukansa (Ƙashushuwan haƙarƙarinsa) sun kakkarye cike da tsanar Akhiee ya ce "A tunaninku wannan shaiɗanin zai shiryu ne?? ai kuma ya yi nisa ba zai taɓa jin kira ba, Wai har Abhi ya ce wani kar a ƙara zuwa ana zancensa, ai abin faɗen yake yi ba dole a faɗa ba?"
Malam Zayd ma ya taya Yasayyadi Usman su ka ci gaba da yi, takaici da tashin hankali sun hana Sheikh Auwal yin magana, gashi ya na son shiga ya ga halin da Husnee ta ke ciki sai dai ya na tsoron abinda zai tarar.
Amadu direban gidan su Husnee ya shigo ya na ƙwalla sallama, Sheikh Auwal ne ya amsa ya na ƙoƙarin daidaita nutsuwarsa ya nufi hanyar ƙofa don ganawa da Amadu.
Musabaha su ka yi kana Amadu ya ce "Malam na ga kowane ɗalibi ya fita ne to banga Husnee ba shine na ƙaraso in tambaya ko ta yi laifi ne an tsareta?"
jim!! Sheikh Auwal ya yi kafin ya ce "Ba laifi ta yi ba kasan yau da gobe sai Allah, larura ce ta sameta."
Hankali tashe Amadu ya ce "To fa ikon me sama, me ke faruwa Malam?" "Ai ba wani abin tayar da hankali bane da sauƙi in sha Allah.
Amadu ya ce "To to to, ai ba komai Allah i bata lafiya, za ta iya fitowa mu koma gida ko?"
a hankali ta buɗe idanunta da su ka yi wani nauyi jingim kamar an ɗora musu dala da gwauron dutse, tunanin abinda ya faru ne ya fara dawowa mata, ba za ta iya cewa ga abinda aka yi ba don kuwa tin wannan kira da Akhiee ya ƙwalla mata ba ta ƙara sanin abinda ke faruwa ba.
Yunƙurawa ta yi ta tashi da ƙyar jikinta duk ya hau ciwo kamar wadda aka yiwa duka da sanda.
Cikin rashin ƙwarin jiki take takawa har ta fito harabar makaranta inda malamai suke tsaye duk sun rasa abin yi, ganin ta fito ya sa duk suka tsaya kallonta, Yasayyadi Usman sam bai so farkawarta ba,, ya so rigimar ta ƙara girma ta yadda zai huce takaicin ciwon ƙirjin da Akhiee ya sa shi.
Farin ciki ne ya lulluɓe Sheikh Auwal a ransa ya godewa Allah a zahiri kuwa ya cewa Amadu "To ga ta nan ma" Amadu ya washe baki gami da cewa "Ma sha Allahu ai da sauƙi sosai."
Husnee dai da ta duba gabas da yamma ta ga saura ita kaɗai a cikin ɗalibai sai ta fashe da kuka, hakan ya ƙara sanya zargi a zukatan su Yasayyadi Usman.
Malam Zaidu ya ce "Ke Husna me Akhiee ya yi miki?" girgiza kai ta yi alamar ba komai don kuwa ba za ta iya magana ba, Amadu ne ya ƙaraso wajen ya na cewa "Sannu Husna! Sannu Innata! Allah i sauwaƙe, mu tafi gida sai a je asibiti ko?" ba ta kula shi ba ta fice shima ya bi bayanta da sauri, gidan baya ya buɗe mata ta na shiga ta kwanta ta ci gaba da rera kuka.
Cikin sanyin jiki Amadu ya ce "Ki yi haƙuri Innata, kanki ke ciwo ne? kar dai wannan ɗan daban ne fa ya yi miki wani abun don na lura kamar malaman nan ba wata gaskiya garesu ba."
Jin surutun da yake ya sa ta danne kukan nata cikin muryarta da ta yi sanyi kamar yadda jikinta ya yi ta ce "Ba na so ka faɗa a gida cewar wani abu ya sameni, nima kaina ban san abinda ya faru ba kawai dai na fahimci cewar na suma ne, kuma ƙila ma Aljanu ne, ni yanzu ba abinda yake damuna don Allah kar ka faɗa za su hana ni zuwa makarantar ni kuma hankalina ba zai iya ɗaukar hakan ba" cikin tausayawa ya ce "To shikenan ba zan faɗa ba Allah i ƙara lafiya."
Ba ta ce komai ba sai ma ƙara yin lamo da ta yi ta na tunane-tunane.
baya........
Hajiya Laure har su ka isa gidan Aminiyarta Hajiya Saudah masifa take zazzagawa kamar zararriya.
A falo ta samu Hajiya Laure ta hakimce ƴar aikinta na yi mata tausa, jin muryar ƙawarta ya sa ta fara fara'a ta na cewa "Hajiya Laure manyan ƙasa me ke faruwa ne na ji kina ta ƴan surutai tin daga nesa?? wai ma ina takabar taki?"
"Hmm!! abinda ya fi haka ma ai zan yi, bar ni da batun takabar nan a cikinta nake, amma hankalina ba zai taɓa kwanciya ba indai wanda ya kashe Alhahi Salisu ya na yawo a gari, abinda ya sa ki ka ganni anan neman shawararki na zo yi don ke ce kaɗai za ki share min hawayena."
Hajiya Saudah ta ce "A'ahh ban gane ba ina kamashi da ƴan sanda su ka yi?" "Yo ƴan sanda ko ƴan iska? bayan kawai kuɗina Inspector ɗinnan ya ci ƙarshe ma ashe sun sake shi? ai cewa na yi na gaji da shigo-shigo ba zurfi gwara na zuba kuɗi a harraƙa min shi lokaci ɗaya."
shu'umin murmushi Hajiya Saudah ta saki kafin ta ce "Ke Baraka bamu wuri."
Miƙewa ƴar aikin ta yi ta basu wuri, Hajiya Saudah ta numfasa kana ta ce "To yanzu ta wace hanya ki ke ganin za mu bi?" "Ni fa wallahi ta kowace hanya ma zan iya bi, ni fa shawara na zo nema kawai ni ki bani shawara.
"To ai in hagu ta ƙi sai a koma dama, in da dama sai a dama, gobe in Allah ya kaimu ki shirya mu je ɗan tsibirin boka Barore, in gaya miki ba ya tsoron Allah ko kaɗan, kashe mutum a wurinsa ƙaramin aiki ne, Wai baki ga yadda na yi damfareriya da ni ba na yi ƙiba abina? ai wurinsa na je neman sa'a kuma na samu, wallahi in gaya miki Alhaji Bara'u yanzu ko ɗan ciki na sai haka, ita kuwa kishiya tini ma Allah na tuba wa ke zancenta? tuni na sa ya saketa shegiya dangin mayu, yanzu da ga ni sai Alhajina sai ƴan ƴaƴana kar ki ga yadda yake mini biyayya kamar ba shine me tsaurin ra'ayin nan ba."
Hajiya Laure ta tattaɓe baki ta na matse ƙwalla gami da cew "Allah i jiƙan Alhaji Salisu bawan Allah, wallahi ya na yi min iya bakin ƙoƙarinsa ni tin wancan zuwan da mu ka yi gangare shikenan muke zaman lafiya da shi, amma nima ina mutunta shi kuma ina yi masa biyayya, shine wannan yaron tsinanne ya kashe shi, ba ma dole hankalina ya tashi ba fisabilillahi fa!!"
Hajiya Saudah ta dafa ƙafaɗarta cikin sigar rarrashi ta ce "Kwantar da hankalinki ƙawata, indai Boka Barore ne sai ya kashe miki ko waye ki ke son ya kashe, ke dai ki shirya gobe mu je, sannan ki tanadi kuɗi kin san ni ba ni da matsala da Alhaji ko bai sani ba na fita ma ba zai ce komai ba, ai kina ƙoƙari ke ni ai na fi so miji ya zama shine zai nemi Aljannah a ƙarƙashin ƙafata ba dai ni na nema a ta shi ba, kwantar da hankali bar zubda hawayenki a banza ƙawata."
Cike da farin ciki Hajiya Laure ta ce "Na gode sosai Hajiya Saudah, wallahi gobe za ki ji ni da wuri ma kuwa don ba a bori da sanyin jiki."
"Yauwa ai gwara dai" Hajiya Saudah ta faɗa sannan su ka ci gaba da hira.
Tankar Yaƙi
farar budurwa ce kyakkyawa son kowa ƙin wanda ya rasa, ta na da dogon hanci da manyan idanu masu kyawu, da ɗan madaidaicin bakinta me ɗauke da lips coffee collor me duhu.
Sanye take cikin ƙananun kaya baƙaƙe, riga me dogon hannu sai matsatstsen jeans wanda ya kama jikinta sosai, P-cap ce akanta wadda ko gama rufe murtuka murtukan kitson doka da ke kan nata ba ta yi ba, idanunta sun ji kwalli rabajau tamkar da taɓarya ta saka, ba ko siririn abu a jikinta da sunan lulluɓi bare batun mayafi ko hijab.
Cikin nutsuwa take takawa cike da taƙama da izza gami da jin kanta, tura ƙaramar ƙofar dake maƙale a jikin ƙaton get ɗin kangon ta yi a sannu ta sanya ƙafarta ciki, mabiyanta na shirin bin bayanta ta ɗaga musu hannu su ka dakata.
Ciki ta ƙarasa ta na tafiya ɗagwas-ɗagwas kamar wadda ake ce ta fito ayi zaɓen sarauniyar kyau ta Duniya.
Laita na kwance kan benci ta yi matashin kai da cinyar Zabira hannunta riƙe da taba ta na zuƙa cikin salo da ƙwarewa, ita ma Zabira ta-ta na hannunta ta na ja ta na lumshe ido.
Kamar daga sama su ka ga Tankar Yaƙi akansu sai wani binsu take da kallon tara ahu, Cikin hanzari Laita ta tashi daga kwance ta zauna gami da ɗora ƙafarta ɗaya bisa ɗaya ta na zubawa Tankar Yaƙi mazajen idanunta.
Zabira ce ta miƙe kai tsaye ta tinkari inda Tankar Yaƙi ke tsaye ta karye ƙugu ta cilla ƙafa ɗaya gaba ta coge ta na kallonsu, "Ke kuma Kazar waye? rasa hanyar gidanku ki ka yi ne??" Zabira ta tambayeta gami da tsatstsareta da idanu.
Cikin shan ƙamshi da iyayi Tankar Yaƙi ta ce ''Babanku nake nema, Kazarsa ce ni!"
Zabira ta juya ta kalli Laita kafin su sa dariya su na binta da kallon sokunta, Laita ta ce "Tambayeta ta rasa tunaninta ne? amma fara tambayarta waye take nufi Babanmu?"
Zabira ta ce "Kin ji abinda ta ce ko??" Tankar Yaƙi ta ce "Sammin abar hannunki" ba musu ta miƙa mata tabar, ta karɓa ta ɗoshana a nata bakin ta yi mata wani mugun ja ta busar kana ta shiga takawa ɗaya bayan ɗaya, sai da ta yi taku biyar cif sannan ta juyo ta na kallonsu, ba tare da tsoro ko shakka ba ta ce "Ina nufin SAHUN KEKE!!!!"
"Sahun Keke!!!!!" Laita ta maimaita sunan cikin sigar tambaya.
SHARE FISABILILLAH
Na Kuɗi ne....
Nomarl Grp 300 Posting ba kullum ba.
VIP 500 Posting Kullum.
domin ƙarin bayani 👉🏽09079885632
*©️INDO*
[8/15, 2:32 PM] INDO: *🪻SAHUN KEKE🪻*
Ep 10
©️
Ayeesha Abdulkareem INDO
*M.W.A🦅*
Kafin ta ce "Ke dalla kar ki zo mana da raini mana, shi ai ba irinki bane ya na da kamun kai, ko me zai yi da ke ma ki na famar tafiya a karkace?" Zabira ta ce "Gaggauta fita daga nan kafin mu rabaki wallahi, mara kunyar banza ƙaramar ƴar kwalta!" wani shu'umin murmushi Tankar Yaƙi ta saki kafin ta ce "Idan ba ku san ni ba shi ya san ni, kuma ba wurinku na zo ba, ku gaya min inda yake tin kafin na shiga nemansa da kaina, koda kuwa ba ya nan zan jira har lokacin da zai dawo."
Zabira za ta yi magana Laita ta katse ta da cewa "Ƙyaleta, ita za ta sayowa kanta wahala barta ta jira shi, kuma yadda ta fito haka za ta koma."
Zabira ta koma ta zauna cike da takaicin Tankar Yaƙi.
Gwaja ne ya tankaɗo ƙeyar Rabi'u su ka shigo tare, Gwaja ya kalli Laita ya na cewa "Laita ga yaronki nan ya dawo daga makaranta!" Rabi'u da ke ta famar haɗe rai ya ce "Ni yunwa nake ji" Wani shegen kallo Laita ta zuba masa kafin ta ce "Zo ka yanka ni ka ci, ko ni zan nema sannan in sayo maka abincin? ka bada kuɗi a sayo maka mana"
Kamar zai yi kuka ya ce "To ai kuɗin nawa sun ƙare."
Harara ta zuba masa gami da cewa "Zo nan!" ya ƙarasa ya tsugunna a gabanta, fuska a ɗaure ta ce "Da ina ka ke samun kuɗin? ba ka ce ba ka sata ba?"
"To ai nawa ne da su na zo." Gwaja ya ce "Ƙarya ka ke yi munafuk..." ɗaga masa hannu ta yi kana ta ce "Je ka duba min kuɗin da nake ajiyewa a ɗakin kwanansa." Bai ce komai ba ya juya ya nufi ɗakin, Rabi'u kuwa ya yi wuƙi-wuƙi da ido duk ya tsorace.
Ba daɗewa Gwaja ya dawo ya sanar mata ba sa nan, ta kalli Rabi'u kamar za ta dake shi ta ce "Fito mini da kuɗina ko na harraƙa ka!" hawaye ya goge gami da cewa "Allah i baki haƙuri, wallahi idan na ji yunwa ne ki ka ce na kawo kuɗin abinci sai in ɗauka a cikinsu kuma yanzu sun ƙare."
Gyara zama ta yi kafin ta ce "Ka san Allah sai ka biya ni, in ba haka ba me rabani da kai sai Allah, kuma ba me baka kuɗin Abinci sai dai ka nema da kanka, ai ba ka san darajar nema ba shi yasa ka ke almabazzaranci da kuɗi har ka ke yin sata." fashewa ya yi da kuka ya na bata haƙuri ita kuwa ta ce ba ta san zance ba. sai da ya ga ba za ta tausaya masa ba ya ce "A ina ake neman kuɗi to?"
ta ce "Yanzu ka yi magana, ka ga waɗancan ciyayin? maza ka je ka dinga fige su ka na haɗa mini su wuri ɗaya, sai ka yi cikin hannu biyar zan ba ka Naira biyar, adadin yawan da ka tara adadin kuɗinka, idan ba ka yi ba kuma ba ka da Abinci, sai dai ka mutu, kuma da haka za ka biya ni kuɗina ko na yanke maka hannu".
Zuwa yanzu ya gane ba ta da imani ko na kobo, don haka ya tashi jiki na rawa ya fara tsigar ciyayi, ya na yi ya na kuka sabida yunwa da takaici da su ka haɗar masa.
Sai a lokacin Tankar Yaƙi ta magantu da cewa "Ke wallahi anyi mara imani, yanzu wancan ɗan yaron ne ki ke yiwa irin wannan, nawa ne kuɗin naki ni in biyaki?" Kallon sheƙeƙe Laita ta yi mata gami da cewa "Da wace kamar?? ke kina ganin ki na da kuɗin da za ki iya biyana ne? ai duk danginku ba me iyawa bare wata ke." A fusace Tankar Yaƙi ta ce "Kar ki yi mini rashin kunya fa, wallahi na fi ki dattin ƙwaƙwalwa." maida kallonta ta yi kan Rabi'u gami da cewa "Kai zo ka karɓi kuɗi ka ƙyale wannan Ƴar balaja'un" Laita ta murmusa gami da cewa "Maza zageni lokacinki ne"
Rabi'u kuwa ya zo da gudunsa ya karɓi kuɗin ya na murna, ko gama jin ɗuminsa bai yi ba Laita ta kira shi ta ƙwace su, bai gama tunanin abinda za ta yi ba ya ga ta yaga su gutsi-gutsi ta watsar, ai kuwa ya ƙara fashewa da kuka, tin kafin ta yi magana ya tashi ya ci gaba da aikinsa.
Rai ɓace Tankar Yaƙi ta ce "Ni za ki yagawa kuɗi? amma ba komai ku ci gaba wallahi indai na Auri Rissy za ku ga wulaƙanci da rashin mutunci duk sai na ƙasƙantar da ku" Dariya su ka sanya harda tafawa, daidai lokacin Salansa ya shigo ya na cewa "A gyara hanya me gayya ya shigo" Laita ta na jin haka ta fashe da kuka, ita kuma Zabira ta zuba tagumi ta yi wani kalar tausayi kamar itama za ta fashe da kukan.
Tankar Yaƙi dai sabida mamaki kawai ta saki baki ta na kallon ikon Allah don ta zata ma Aljanu garesu.
Har zai wuce ya ji ba wadda ta tanka masa ga sautin kukan Laita ya na ji don haka ya tsaya ya na zuba musu idanu, sai lokacin ya lura da Tamkar Yaƙi da ke tsaye hannayenta riƙe da ƙugunta, "Me yake faruwa ne?" ya tambayesu Laita ta ƙara sautin kuka, Zabira ce ta murje ido sannan ta ce "Wannan Matar ce ta zo wai ita Kazarka ce, don mun ce ba ka nan shine ta zazzage mu, nima don dai ina da juriya ne da tuni na fara kukan don zagin ƙare dangi ta yi mana" ta ƙarasa maganar tana tattaɓe baki.
Ransa in ya yi dubu ya ɓaci, maida kallonsa ya yi kan Tankar Yaƙi da ta kasa rufe bakinta, lallai yau ta shigo inda aka fi ta makirci, tunanin da take yi kenan, ya katse ta da cewa "Abin naki ya wuce kaina ya koma kan Iyalina kenan?" da sauri ta ce ''Wallahi ko ɗaya, ni fa ba abinda na yi musu ka tsaya ka saurare ni."
"Ina ƙyale ki ne kawai sabida ke macece, ki fita kafin na yi miki illar da ba za ki ƙara taka ƙafarki ba.
Cike da ɓacin rai ta ce "Na ji, zan fita amma sai lokacin da na ga dama tinda ba kai ka kawo ni ba, nifa wallahi duk abinda za ka yi mini ina sonka ba zan fasa ba sai dai in ba na numfashi, don ma ina son naka shine ka ke wani jiwa mutane kai, duk abinda ka ke taƙama da shi nima ina da shi, kuma ka sa a ranka ba za ka taɓa Aurar wata mace bayan ni ba, duk wadda ta so ka ma sai na kasheta kuma na kashe banza.
"Ki kasheta mana idan za ki iya, kuma idan ba ki kasheta ba ni zan kashe ki, fice mini da gani shashasha" ya yi maganar cikin ɓacin rai da takaici.
Dogon tsaki ta zabga kafin ta ce "Kar ka yi zaton ƙyale ka na yi, zan dawo, ku kuma waɗannan munafukan ku kuka da randa za ku shigo hannuna." ta na kaiwa nan ta fice cikin sauri kamar me shirin tashi sama.
Risslan kuwa bai bi ta kansu ba ya wuce ɓangarensa cike da takaicinsu da su da suka tsaya yi mata kuka da ita tsagerar."
Yana barin wurin Laita ta goge hawayen ta na cewa ''Ita ƙaramar ƴar bariki ce, ni sabida tsabar makircina aka raɗa min Laita, kuma wallahi in ba ta yi a sannu ba sai mun sa ya kasheta."
Zabira ta ce "Wa yake ta ta-ta ma har me akai aka yi ta? ai bigi sai bigi." Gwaja ya ce "Na tsorata da ku mutanen nan" Laita ta murmusa gami da cewa ''Kaɗan ma ka gani" hira su ka ci gaba da yi akan ta yadda za su koya wa Tankar Yaƙi hankali, kowa na bada ta shi shawarar.
Hajiya Laure
Kamar yadda ta faɗa tin wuri ta shirya ta nufi gidan Hajiya Saudah daga nan su ka rankaya zuwa wajen boka.
Ƴar bukka ce wadda tin daga waje ma za ka gane ba alkairi ake shukawa a cikinta ba duba da yadda aka yi mata ado da ƙashushuwa da kawuna ƙwarangwal-ƙwarangwal na dabbobi iri-iri.
Hajiya Laure ce ta turje ta kasa shiga, a tsorace ta ce "Hajiya Sauda wai ki na ganin abinda nake gani kuwa?? ni fa gaskiya ba kowane boka na yarda da shi ba, ki zo mu koma don ba na son wanda garin na cutar da wani ni sai ya cutar da ni" Hajiya Saudah ta ce "Ai kin ji inda ki ke bada mata wallahi, to bukkar boka barore ba a shiga a fito ba nasara kuma ki yi tambaya ga waɗanda su ka san shi ki ji, komai wuyar aiki inda kin kawo shi wajen boka barore kin gama."
Hajiya Laure za ta yi magana karsanar muryarsa mara daɗin ji ta karaɗe kunnuwansu, "Shaiɗanun Aljanu sun yi marhabin da zuwanku!!, ku ƙaraso ciki!!!!!!, ba a zuwa tsibirinmu a koma haka nan dole sai an gana da mu in ba haka ba a hau-kace!! hhhhh"
Hajiya Saudah ta ce ''To kin ji kaɗan daga cikin sharuɗansa gwara ma ki nutsu." jan hannunta ta yi kiiii su ka danna kai ciki.
Duhu gami da wata irin guguwa me ƙarfi
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 5 Chapter of 19