Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
an wayi gari ka kasa zama ka sauke Alƙur'ani ko da sau ɗaya, zuwa makaranta ma ba ka yi, ka ga mahaifiyarmu ta rasu ta na me begenka tare da sa ran za ka zamo bango ga al'uma, don Allah ka canja rayuwa Akhiee!!!" Maza Gumbar dutse!! ba shakka nasihar Sheikh Auwal ta taɓa masa zuciya musamman da ya taɓo sashin iyayensa wanda ya fi ƙauna fiye da komai a rayuwarsa. Shiru ne ya ratsa tsakani kafin Rislaan ya ce "Mu ga tafin hannunka Ya Sheikh!" ba musu Sheikh Auwal ya buɗe tafin hannunsa, shima Akhiee buɗe nasa ya yi ya dangana shi da na Sheikh Auwal, cikin tattausar murya ya ce "Iyayenmu ɗaya, jininmu ɗaya, amma ka ga tsagar tafin hannunmu ma kaɗai ta bambanta, to akwai abubuwa da yawa ma waɗanda su ka bambanta, ba mu muka tsara hakan ba Allah ne ya tsara, tabbas sunanmu ɗaya da Abhi amma ruhinmu daban-daban ne, ka ga dole ƙaddararmu ta bambanta, kowa da kalar ta sa ƙaddarar; ni wannan ita ce tawa, ba zan yi muku Alƙawarin zan canja ba domin ba ni da tabbas akan haka, kuma ance jumu'ar da za ta yi kyau tin daga laraba ake ganeta, ni kuma babu alamar rayuwata za ta canja daga haka, ina me bada haƙuri Akhiee!!!" Tabbas zuciyar maza ta karye, Sheikh Auwal ya kasa cewa komai don kuwa idan ya furta zai iya rushewa da kuka, kalaman Akhiee sun yi mugun tasiri akansa, tsananin tausayin ɗan uwan nasa ya kama shi. Akhiee kuwa tashi ya yi ya nemi guri ya yiwa kansa masauki, ya na zama duk na kusa da shi su ka dare su ka bashi wuri su ka koma can nesa da shi, sai ya kasance shi kaɗai a wurin, bai damu ba don kuwa in da sabo ya saba kuma shi ma hakan ya fi masa daɗi don a arashi ma mutum zai iya ɓata masa rai ya illata shi a banza don haka ya fi so su dinga nesanta kansu da shi. Tinda ya zauna bai ce uffan ba shi bai yi karatun ba bai yi surutu ba. Hakan ba baƙon abu bane don komai yawan dukan da za'ayi masa ba zai taɓa yin karatun ba don haka Sheikh Auwal bai damu ba bare ma ransa ya ɓaci. Sai da aka tashi domin yin sallar la'asar sannan ya tashi ya nufi sama wurinsa na gado wato inda ya saba tsayawa. Husnee jikinta har rawa yake don son ta je ta iske shi, ta na shirin fita daga ajin Sheikh Auwal ya kirata, ba don ta so ba ta amsa kiran gami da zuwa ta durƙusa a gabansa, cikin yanayinsa na dattako ya ce "Me ke faruwa ne naga kamar a kwanaki biyun nan kullum cikin kuka kike?" maganar ta shi ma dariya ta bata amma sai ta maze ta ɗan murmusa gami da cewa "Ba kuka na ke yi ba Ya Sheikh Idona ne su ke ciwo" "Kin je asibiti?" gyaɗa kai ta yi alamar eh kafin ta ɗora da cewa "Na je sun ce ba komai a idon" Abin ya bawa Sheikh Auwal mamaki, jinjina kai ya yi gami da cewa "To fa! ikon Allah, to Allah i sauwaƙe tashi ki je." zumbur ta miƙe kamar wadda aka sokawa kibiya a mazaunai, cikin sauri ya dakatar da ita da cewa "Wani hanzari ba gudu ba." Durƙusawa ta yi cike da takaici ta ce "Ina ji Ya Sheikh" "An kawo min ke makaranta ne don ki yi karatu ki ƙara samun nutsuwa da tarbiya ba wai ki lalace ba, to don haka ki gujewa shiga hurumin Akhiee, shi wani irin mutum ne da ba wanda ke son mu'amala da shi, kinga ƴan uwansa maza ma ƙaurace masa su ke yi bare ke mace, ba zan so wani abu mara daɗi ya faru da ke ba don hakan zai zamo alhakinmu tinda amana aka bamu ke, lallai ki kula." Kai kawai ta gyaɗa masa ba don ta gamsu da kalaman nasa ba. Ya na bata izinin tafiya ta tashi ba ta zame ko ina ba sai kusa da Akhiee, lokacin da ta ƙarasa kusa da shi waya yake, abinda ta tsinkaya ya na cewa "Da wane irin makari kuka kashe shi??" ba ta ji abinda aka ce masa ba sai kawai ta ga ya kashe kiran, ta saki baki ta na kallonsa kafin ta ce "Dama ka saba kashe mutane? ashe har sawa ka ke yi a kashe??" gyaɗa kai ya yi alamar eh sannan ya ce "What are you doing hare?" Mantawa ta yi da zancen da takeyi cike da rawar kai ta ce "Me yasa jiya ba ka zo makaranta ba?" Kallonta ya yi kafin ya buɗe baki a nutse ya ce "Ke sabuwar zuwa ce?" gyaɗa kai ta yi gami da cewa "Yo eh mana, ranar asabar waccan na fara zuwa, kuma ba taɓa ganinka ba sai wannan lahadin, sai kuma naga ana ta dukanka abin tausayi" ta ƙarasa maganar ta na marairaicewa. "Ya sunanki?" Murguɗe baki ta yi cike da iyayi da feleƙe ta ce "Husna ko Husnee" "Asma'u! to shekararki nawa?" Da sauri ta zagayo gabansa suna fuskantar juna tsabar rawar kai da jin daɗin kulatan da ya yi har ji take kamar ta yi tsalle ta ɗafe shi. "Shekarata Goma sha bakwai, saura shekara ɗaya na yi candy!" daga yadda take magana ma kaɗai ya isa nuna irin tsantsar farin cikin da take ciki. Idanunsa masu matuƙar kaifi gami da kashe jikin wanda ya kallesu ya zuba mata, ƙara sassauata murya ya yi kana ya ce "Shekarunki sha-bakwai amma shine kamar akanki aka fara ƙuruciya aka ƙare?" "Ahh?! to me na yi na ƙuruciya?" "Wai kuka kike don an dokeni, ni da jin zafi ke da yin kuka, duk wannan ba ƙuruciya bace?" Rausayar da kai ta yi gami da jingina a jikin ƙarfen makari, a sanyaye ta ce "Ni wallahi tausayinka na ke ji." Dafa hannayensa ya yi akan ƙarfen gefe da gefenta ya sanyata a tsakiya ya na kallon kyakkyawar farar fuskarta, "Asma'u!!!" ya kira sunanta cikin wata irin murya me rikita lissafin ɗan adam, hakan ya tilasta mata ɗago idanunta da ke fama da hawaye ta jefa su cikin ƙwayar idanunsa. Ganin ta maida hankalinta kansa ya bashi damar ci gaba da cewa "Ni ba abin tausayi bane, kar ki ƙara tausaya min, ko ni bana tausayin kaina idan kika ce za ki tausaya min kuma ke za ki zamo abar tausayi, sannan ki dena yawan kallona, zuciya gareni kamar glass da ta buga shikenan zan iya illata miki rayuwa, wata rana za ki iya rasa ganinki indai ba ki dena ba." Kamar macijin da aka zarewa dafi haka ta ke jinta sululu, gashi dai ta na sauraren gargaɗin nasa amma ta kasa dena kallonsa kamar wadda ake ce ta na ɗauke idanunta zai ɓace ta dena ganinsa. Iskar bakinsa ya hura mata akan idanun nata ta yi saurin rintse su da ƙarfi ta na jan wani dogon numfashi.... SHARE FISABILILLAH Na Kuɗi ne.... Nomarl Grp 300 Posting ba kullum ba. VIP 500 Posting Kullum. domin ƙarin bayani 👉🏽09079885632 *©️INDO* [8/13, 7:40 PM] INDO: *🪻SAHUN KEKE🪻* Ep 8 ©️ Ayeesha Abdulkareem INDO *M.W.A🦅* Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta buɗe idanun nata, fayau babu shi a wurin, juye-juye ta fara yi ko za ta hango inda ya yi amma ko ƙyallinsa ba ta gani ba. riƙe haɓa ta yi cike da mamaki ta tambayi kanta "Wai har ya ɓace min?" Wata ƴar budurwa kamarta ce ta ƙaraso inda take ta na fara'a, Husnee ta bi ta da ido gami da cewa "Ya akai?" "Don Allah so nake mu zama ƙawaye, ni sunana Asiya ajinmu ɗaya ma da ke'' Husnee ta murmusa cike da jin daɗi, dama tinda ta zo ba ta samu ƙawa ba sai Zara ita ce su ke ɗan mutunci su ma anayi ana faɗa. "Ni kuma sunana Husnee, daga yau mun zama ƙawaye to" Da sauri Asiya ta ce "na ji daɗi wallahi na gode" Husnee ta ce "Mu je mu yi Alwala" da to ta amsa sannan su ka sauka ƙasa. Sai da ta je yin Alwalar ta lura hawayen idanunta sun dena zuba cak! kamar ba su yi ba, nan fa ta dinga murna kamar ta hau sama ta faɗo. zaune yake kan ɗan ƙaramin gado da aka yi shi da jan katako aka sanya masa ƴar katifa daidai da shi, sai shimfiɗar gado ta bargo me taushi. Salansa da Ɗan Bakwai na tsaye gefensa curko-curko, Waya ce a hannunsa ya na latsawa cikin kwanciyar hankali, Lambar IP Khalil ya lalubo gami da tura kira. Inspector Khalil na zaune kusa da matarsa su na kashe love wayarsa ta yi ƙara, ɗan ƙaramin tsaki ta yi gami da cewa "A daren nan ko waye me kiranka?" Murmusawa ya yi cike da son koɗa kansa ya ce "Nifa ɗan Sanda ne, ko da yaushe ma ana iya kirana, ba ki saba da hakan bane sabida ban riga na Aureki ba, amma yanzu tinda mun yi aure ai za ki ga abubuwa daban-daban" murmusawa ta yi kafin ta ce "Gaskiya ne Jarumina, ba ka ɗauka ba to har kiran ya katse, ko in baku wuri ne?" Da sauri ya ce "No zauna abinki" daidai lokacin wani kiran ya ƙara shigowa, latsa kore ya yi gami da aza wayar kan fala-falan kunnuwansa tubarkallah. "Ƙaramin Sufeto, Albishir zan yi maka akan mutuwar Abokin wanda case ɗinsa ke hannunka, Alhaji Habibu Mai Kwalli; na kashe shi." "What!!!!!!" IP Khalil ya faɗa cikin kaɗuwa da razani. "Yaushe? kuma ta ya? me ya yi maka?" "Idan ka matsanta bincike za ka zamo na gaba a waɗanda za su mutu don kai ma akwai tamu da kai, amma ba na son kasheka yanzu tamkar na kashe maciji ne ban sare kansa, har sai na kashe ƙashin bayanka sannan zan kasheka! na faɗa maka ne don ka rubuta a file ɗina ba wai don ka wahalar da kanka wajen kamani ba; na samu labarin ka yi Aure, waccan haɗuwar tamu ba ka zo min da maslaha ba bare in yi maka murna, Happy marriage to you, a gaida iyali. Ya na kaiwa nan ya katse kiran gami da miƙawa Salansa ita, Ɗan Bakwai ya miƙo masa wata gami da cewa "Gaba salamun baya salamun, Sahun Giwa me badda na Raƙumi, SAHUN KEKE Ba a Gane Gabanka!!!" Karɓar wayar ya yi ya na ƙoƙarin yin wani kiran ɗaya wayar tashi ta fara ƙara. IP Khalil, kamar sakatar sakarai haka ya saki baki, duk jikinsa ya yi sanyi kamar an zuƙe masa ruwa, nazari yake akan shaharar ta'addancin Risslan, ya rasa ma abinda zai yi masa ya kawar da shi, shi dama kowa ya san ba mutumin kirki bane bare ayi masa wani mugun sharrin, Zulaihat ba ta lura da halin da ya ke ciki ba don hankalinta na kan kiran da take son yi, "Nima bari in kira Babana mu gaisa, tinda mu ka yi Aure ba mu gaisa da shi ba ." IP Khalil dai ba baki sai kunne. Zaro wayar ya yi daga Aljihunsa ya zubawa screen ɗin ido har na ɗan lokaci sannan ya ɗauka ba tare da ya ce komai ba, "Baba!!!" muryar Zulaihat ta doki dodon kunnensa, kasa amsawa ya yi har sai da ta ƙara kiransa sannan ya ce "I'm So sorry my daughter! me kike yi har yanzu ba ki yi bacci ba? ina mijin naki??" ya jefeta da tambayoyin a lokaci ɗaya. zakuɗawa ta yi kana ta ce "Sorry for what my Daddy? kai fa ba ka laifi, ka ganshi nan ya na gaisheka, ko in ba shi ku gaisa?" Da sauri IP Khalil ya ɗaga mata hannu don kuwa ba zai iya magana ba a yanzu musamman da babban mutum wanda take kira Baba. Risslan ya ce ''No need, barshi kawai ina amsawa, na san ba kya rabuwa da ƙorafi shiyasa na fara baki haƙuri don na san dole za ki yi" Ta ce "To shikenan, amma Baba ba ka zo Aurena ba ya kamata ka zo ganin ɗaki, amma tinda duk ba ka zo ba Birthday ɗina ya kusa, amma za ka zo ko??" "Sai yadda yanayi ya nuna Daughter, ta yuwu ma ko na zo ba za ki ganni ba, amma kar ki damu kawai." Rausayar da kai ta yi sannan ta ce "To sai da safe" "Allah i kaimu" Bai jira cewarta ba ya katse wayar, ya ajiye gefe, Kira ya tura da ɗaya wayar ba ɓata lokaci aka ɗauka, kai tsaye ya fara da cewa "Zan shigo garinka gobe da daddare, a janye tsaro." IP Hussain ya ce "An gama sir!" Daga haka ya katse wayar, kiran CP ne ya shigo Salansa ya ɗaga kana ya miƙo masa "Yallaɓai" shine abinda ya faɗa sannan ya yi shiru don jin abinda CP zai ce "Na san ka sani ba sai na faɗa maka ba, kuma na san za ka aikata, fatan nasara ɗan nasarawa, ni kuma a ta nan zan dafe komai." CP ne ke yin maganar cikin hikimar harshe. Risslan ya ce ''Na lode kuma zan kaɗar, so na gana da IP Hussain ma ta ɓangarensa ba damuwa; Shu'umin Jami'i Yallaɓai CP Abubakar Ado Gezawa!" CP ya yi dariya me isarsa kana ya ce "Ja'irin Yaro Muhammad Risslan Sheikh Muhammad Risslan! sai na ji ka zuwa jibi don gobe na san ba ka da lokacina." Risslan ya ce "Ba shakka Bukar, amma ko me zai faru ka ɗauka kawai haɗari aka yi mota ta kama da wuta, banda tsananta bincike" "Yes sir!" CP Abubakar Ado ya faɗa cikin sigar Zolaya. Da haka su ka yi sallama sannan Akhiee ya miƙe ya na cewa "Yau da wuri zan shiga gida, ku dafe ko ina, ku kula da sauran Iyalina, ina Zare da Aci-bal-bal suke ne??" Salansa ya ce "Su na can su na bawa shegiya wuta Ya Babba! nake liƙa maka Zare ya kwashi harawa, ya kwashi harawa, shiruu!! ka ke ji, magana ma Ɗan iska ba ya iya yi." Risslan ya ce "Bari gobe zan ci Ubanshi, shi ga ƙaramin kai ga son ɗaukar kaya" Ɗan Bakwai ya ce "Inaa! lumbu-lumbu ce, yanzu ka kai masa sara nan za ka gane iskancin nashi na ƙarya ne, a sauka lafiya me gayya!" ya ƙarasa maganar tare da rissinawa Risslan, "Hmm!!" kawai ya ce sannan ya fice. Ƙaton kango ne me ɗauke da part part da ɗakuna daban-daban a ciki ma in ba zagayawa za ka yi ba sai ka yi kwana da kwanaki ba ka gamu da wani ba. ko da ya hau dokinsa ba su dena binsa ba har sai da ya fice daga tafkeken Kangon. Washegari Bayan Sallar Isha'i ya ɗauki hanyar Kwanar ɗan Gora a kan dokinsa. Bayan ya ƙone motar ya kama hanyarsa ta komawa gida ba tare da tsoron dare ko shakkar wani abu ya gifta masa ba. Da sauri ya ɗago kai ya na kallon mahaifin nasa cike da rashin sanin abin faɗa, Murmushin gefen baki Hamza ya yi, a ransa ya ce "Ai Yau taka ta ƙare faɗen gaskiya ya zama dole." cikin son kauda zancen Akhiee ya ce "Abhi! wani abin su ka ce na yi?" Abhi ya ce "A'a, na ji ne su na ta zancenka ba dare ba rana dole na san akwai abinda ka yi musu." Gyara zama ya yi sannan ya ce "Abhi! ka san dai ɗan Adam ba a iya yi masa, kawai fa kwana biyu ne ban je Makaranta ba shine ake ta wannan tashin hankalin." Abhi ya jinjina kai cike da gamsuwa sannan ya ƙara da cewa "Me yasa to ba ka zuwa? ka san fa kai Malam ne." "To ai abubuwan ne da yawa Baba, ka ga ana fita nema haka sannan ka ga yanzu damuna ce ina yawan zuwa gona, shi yasa amma ko jiya... au jiya ban je ba, amma shekaran-jiya na je, ka san fa ni manomi ne Abhi" Abi ya yi murmushi irin nasu na manya gami da cewa "Aff ƙwarai kuwa! ni ai na sani dama, ai wannan duk ba abin damuwa bane, amma da zarar ka dawo daga gona ka shirya ka je makaranta abinka, ka ji ko Malam?" "To Abhi in sha Allah" Hamza da baƙin ciki ya maƙale masa a zuciya kasa dannewa ya yi ya ce "Wallahi Abhi ƙarya yake yi" wani mugun kallo Akhiee ya zuba masa, wanda ya sa hantar cikinsa juyawa. Abhi ya ce "To fa! Dattijo!" "Na'am Abhina" ya amsa a ƙagauce, "Ɗan uwanka ya ce ƙarya ka ke yi, me ke faruwa bayan haka?" "Wallayi Abhi ranar nan ne aka samu akasi Yasayyadi Jameel ya doke ni shine fa na ji zafi raina ya ɓaci, sai na ɗan yi masa rashin kunya, shine fa wai a dole sai an gaya maka, kai ni naga ta kaina" ya ƙarasa maganar ya na jimanta al'amarin. Abhi ya jinjina kai kafin ya ce "A Kul! kar a ƙara yiwa manya rashin kunya, kuma shi malaminka ne ai, Malami kuwa ɗan uwan uba ne ya na da kima da daraja, lallai a kula, zan nemesu in gaya musu kar in ƙara jin ana zancenka." "Na gode Abhi, ni yanzu zan fita zan je gona in duba yanayin aikin da aka yi jiya." Abhi ya ce "To Allah i tsare, Allah i yi maka Albarka yaron kirki; kai Malam Hamza maza a je a zo min da Iyayen naku da sauran ƴan uwa." Ya ƙarasa maganar ya na duben inda Hamza yake. "To" Hamza ya ce sannan ya bi bayan Akhiee su ka yi hanyar fita. Cike da takaici ya ce "Amma kai anyi munafuki wallahi, ka iya ƙarya kamar ɗan duba, ka je ka yi kashe-kashe amma ka ce masa ka je gona." cikin ɓacin rai Akhiee ya ce "Ba babban munafuki sama da kai da ka ke shirin faɗa masa abinda zuciyarsa za ta buga, su fa iyaye kalamai masu daɗi ake gaya musu wanda hankalinsu zai kwanta, amma sabida ba ka san darajarsu ba za ka gaya masa abinda zai tashi hankalinsa, kuma na rantse da ubangijin Al'arshi idan aka samu wani ya gaya masa ainahin zahiriyyata har wani abu ya same shi sai na kashe kowaye ya faɗa, ba alwashi bane alƙawari ne kuma zan cika indai an saɓa min." Cikin ɓacin rai gami da tsana Hamza ya ce "Banza mara kunya, sai ka kashe ɗin in ran a hannunka yake" "To ɗan masu da kunya, ni lokacin da aka raba kunyar ban zo duniya ba, idan ka damu da in yi kunyar sai ka ban taka" Hamza ya ce "Allah i sauwaƙe!" Akhiee ya ce "Zancen banza, da kunyar ba ta isheka ba kake tallar ta? ai da ta isheka sai ka ɗeba min taka, gaso-rogo kawai" daga haka Bai bawa Hamza damar ƙara yin magana ba ya yi gaba cike da baƙin ciki da takaicin irin ƙyama da ƙiyayyar da ƴan uwan nasa suke nuna masa. IP Khalil na zaune kan kujerarsa ya kifa kai akan teburi ya na hucewa, kansa duk ya gama ɗaukar zafi, wani mugun ƙunci da damuwa yake ji kamar zai haɗiyi zuciya ya mutu, Risslan ya gama ɗaɗɗaure masa jijiyoyin jikinsa, ya je ya yi kashe wancan ya kashe wancan gashi ya ƙone motar ogansa, sai umarni yake samu daga sama na kawo ƙarshen Risslan, babban tashin hankalinsa bai san menene raunin Risslan ɗin ba bare ya yi masa illa, a yadda yake a rayuwarsa ba wani abu da ya zamo rauni a gareshi. Har baccin wahala ya fara ɗaukarsa wayarsa ta tashe, ya ɗago idanunsa da su ka koma kalar ja ya zubawa wayar, ganin Hajiya Laure ce ya sa shi ɗagawa don ya bata haƙuri ma ta dena takura masa. a masife ta ce "Kai IP Khalil na gaji da gafara Sa ban ga ƙaho ba, ina labarin wanda ya kashe mini Miji??" shiru ya yi mata don kuwa bai san me zai ce mata ba ya ji yau da bala'i ta hauro. "Tambayarka na ke yi fa??" Numfasawa ya yi sannan ya ƙoƙarta ya ce "Hajiya mun fi ki son mu ga mun yi aikinmu, amma ba mu da halin hakan, ki yi haƙuri mu na nan mu na ƙara bincike akan lamarin, wanda mu ka kama kawai zargi ne ba mu da hujjoji ƙwarara, amma da yardar Allah komai zai yi daida...." "Dakata Ibrahim!!" Hajiya Laure ta faɗa cikin tsawa, ɗorawa ta yi da cewa "Na gaji da yaudarar nan da kake yi mini, yanzu na ɗau haske na fahimci komai, ai bakinku ɗaya da kai da makasan dama, to wallahi da kaina zan ɗauki mataki, yanzu ba na buƙatar temakonka, don me za ka ce ba ka da hujja bayan ka san wanda ya aikata har ka kama shi sabida bakinku ɗaya sai ka sake shi, shine fa ya baƙunci mijina a ranar da aka kashe shi, to in ba shi ba waye zai yi kisan?" IP Khalil zai yi magana ta katse shi da cewa "Kar ka gaya mini komai!! ba na son ji, na haƙura da temakonka ka je ka yi Allah na nan kuma kuɗin da na biyaka Allah ya isa, ni zan bi ta wata hanyar in ɗauki fansar mijina, wallahi tallahi sai na jefa wannan yaro cikin bala'in da sai ya kashe kansa, kai kuma ta Allah ba taka ba munafukin banza" ta na kaiwa nan ta katse wayar ta na huci. IP Khalil ji yake tamkar ya yi ta bin layika da kwararo ya na zunduma ihu ko zuciyarsa za ta yi sanyi, nan take wani mugun zazzaɓi da ciwon kai na wahala da tarin tunane-tunane su ka lulluɓe shi. Huci Hajiya Laure ke yi kamar bujimin sa ya ga wuƙar yanka shi, Yazeed da ke zaune gefenta ya ce "Shima munafuki ne ɗan sandan nan ko??" "Yo eh mana, in ba haka ba ta ya za ka kama mutum ka sake shi bayan ka san shi ya aikata, wallahi zan ɗauki mataki akansa nan ba da daɗewa ba, je ka fito mini da mota fita zan yi." Yazeed ya miƙe ya na cewa "Amma da kin bari kin gama takaba sai ki yi ko me za ki yi." "Ubanka!! na ce ubanka kai da takabar! kamata ta yi ace ka fi ni damuwa da mutuwar ta shi amma sabida kai butulu ne duk wannan so da ƙaunar da yake nuna maka sai ka ce in bari in gama takaba? to kai da takabar na ci buhun ubanku, ƴan butar duma kai?" "Allah i bada haƙuri" ya faɗa cikin sanyi sannan ya fita domin gyara motar da za ta fitan. SHARE FISABILILLAH Na Kuɗi ne.... Nomarl Grp 300 Posting ba kullum ba. VIP 500 Posting Kullum. domin ƙarin bayani 👉🏽09079885632 *©️INDO* [8/14, 8:18 PM] INDO: *🪻SAHUN KEKE🪻* Ep 9 ©️ Ayeesha Abdulkareem INDO *M.W.A🦅* "Asma'u!!!!!!" kira ya ƙwalla mata da ƙarfi cikin tsananin kaɗuwa da tashin hankali, cikin zafin nama ya finciko hannunta da mugun ƙarfi hakan ya sa ta dawo kansa, garin daidaita tsayuwarsa ya taka ɓawon ayabar da ta jefo masa santsi ya ja shi, gabaki ɗaya su ka yi wata muguwar sufa su ka rikito daga saman benen su ka nufi ƙasa, rimmm!!!!! sai gasu a tsakiyar harabar makaranta. Ihu ƴan matan da ke kaikawo a wurin su ka sanya gami da tarwatsewa kowacce ta na neman wurin ɓuya. Hankali tashe Akhiee ya ture Husnee da ke kwance akan ƙirjinsa ya miƙe ya na zuba mata idanu don sanin halin da take ciki, hankalinsa ne ya ƙara dungunzuma ganinta a

Chapter 4 of 19